Author : Cwt Sumiey Category : African Stories & Novels
d`auko ni mu ka taho nan".
" Hmmmmmm Richal kenan idon ka kenan sai yanzu sai yanzu ka tuna da Gida sai yanzu ka tuna kana
da Mahaifiyar ,sai yanzu ka tuna kana da wasu ahali da su ke buk`atar ganin ka a kusa da su,shekaru har
nawa almost five years tun mutuwar Mahaifinku ba ka sa ke d`ora k`afarka a cikin k`asarnan ba, Na
dad`e da daina yi maka Maganar Aure na barka da hankalinka ka yi duk abinda ka ke ganin shine dai-dai
a gare ka".....
"Haba Momy ya isa haka for God sake, yanzu ba ga shi na dawo ba,I'm begging you ki manta da komi,I
promise hakan ba zai sake faruwa ba,kuma ga su Martin duk suna gun".
" Da alama ba kasan zafi da rad`ad`in abinda ka aikata min ba, Ni kad`ai fa na koma rayuwa,I live the
whole yers lonely tamkar wata mara gata,kuma da ka ke Maganar Yara ai nasan da su,ina maka fad`a ne
a gaban su dan su san abinda ka ke aikatawa ba abu ne mai kyau ba,ina iya iyawa akan in ga ka sauya
amma hakan ya faskara,ba zan so wani a cikin su ya rik`a aikata irin haka ba,ko kasan sai daga bayanan
Gloria ta dawonan da zama ita da Zuri'arta duk dan saboda ni,da ba dan haka ba da bansan ta yarda zan
cigaba da gudanar da rayuwata ba",ta kai zancen ta na mai had`iye wani abu mai zafi da d`aci .
Zaraf Richal ya baro wurin da ya ke zaune ya iso inda Mom Rebecca ta ke zaune ya na mai duk`awa
saman gwuiwowinsa,fuskarsa har ta fara canjawa ya ce,"Momy na rok`e k`i ,for the sake of Father Lord
ki bar tada wannan zancen I swear to the Jesus name haka ba za ta sake faruwa ba,I promise zan zama
d`a na gari zan yi duk abinda ki ka ce amma dan Allah ki bar bayyana fushin ki a kaina ,tsinuwar Yesu
Almasihu za ta iya riska ta in har haka ta kasance,da gaske Na shirya yanzu zan yi Aure zan haifa maki
Yaran da za su yi ta wasa a gaban ki ko Sweet Daughter ?",ya kai zancen yana mai maida hankalin kan
Jadeeda .
Kamar wacce ta ke jira a sata a zancen haka ta iso ta na mai duk`awa kamar yanda Uncle d`inta ya
duk`a kafin ta ce,"Da gaske Granny Uncle miey ba zai sake tafiya ya barmu ba kuma zai yi Auren kamar
yanda ki ke so,ni da kaina ma zan samo masa macen da ta dace da shi,amma sai kin daina fushi da shi".
Allah sarki Zuciyar Uwa nan da nan tai sanyi sai ga shi ba a d`au wani lokaci ba har murmushi ta ke
daga k`arshe ta ce da shi ta,"Ban ta`ba ganin irin shak`uwa da Soyayya irin ta ku ba,ina ganin yanda
hankalin ta ya tashi saboda ina yi maka fad`a ko ita na ke yi mawa sai haka".
Murmushi su duka su kayi daganan Jedeeda ta fara sarving d`in su lunch d`in da Easter ta kawo ma
su,suna nan har dare ,sai dai ba su sake samun damar da za su ga Gloria ba ,dole sai su ka hak`ura sai
zuwa gobe da safe.
*JADEEDAH*
(It's a story of two love birds who are so different from each other )
STORY & WRITTEN BY :
(*Cwt~Sumiey*)
Marubuciyar littafin
MENE NE ABIN YI ?
KARAGAR MULKI
And now.....*JADEEDAH*
*YATA*
BOOK 1
PAGE 21❤
"Kin ga na fa gaya maki gaskiya ba zan sake dawowa Gidan ki dan yanzu ba,ki aikata duk abinda ki ke
ganin shine dai-dai a wajen ki,amma wallahi ba goyan baya na a ciki,kuma kar wani abu ya faru ku sako
sunana a ciki".
"Eh Na sani Fadeelah,kuma na yarda amma dan Allah ki zo ,akwai maganar da na ke son mu
tattaunawa akanta da ke"....."Hmmmmm Na san fa abinda ki ke nufi, kina tsoran kar in sanar da Fulani
ko ki kwantar da hankalin ki ba wanda zai ji na yi maki alk`awari".ta Na kaiwa k`arshe zancen ta katse
kiran.
A fusace Gimbiya Ayush ta ciro wayar daga kunnenta ta na mai cewa,"Kai wai ni wannan Yarinyar za ta
katse ma waya saboda tsabar rainin da ya shiga tsakanin na da ita,har yaushe ta kai matsayin haka?".
" Hmmmmmm ke ki ka siya da kud`in ki,Dan me za ki rik`a lalla`bata akan me,ba rayuwar ki ba ce
ba,ko a jikin ta cikin ya ke,tun jiya Na ke ce miki ki sha pills d`in nan cikinnan ya yo waje kowama ya
huta ,amma kin kasa,ko dai kin fasa ne saboda tsoran zugar da za tai maki ? ".
"Hmmmmm tsoro kuma Anesa,sai ka ce ba Gimbiya Ayush ba,kin tabbatar ba abinda zai sa in bar
cikinnan, kawai dai ina son in bi komi a hankali don gudun afkuwar wani abu mara dad`i tsakanina da
Mijina ko kuma Fulani".
Wata `yar gajeriyar dariya Anesa ta saki gami da cewa," Ai na sha kin hak`ura domin har na fara gano
ki,kina tafe da tirtsetsen ciki sai faman zama da k`yar ta shi da k`yar ki ke"......katseta tai ta hanyar kai
mata duka tare da cewa,"God for bid ,Allah ya tsare ni bakin ki ya koma kan ki,ba ki san iya girman tashin
hankalin da na ke shiga idan har na tuna cikinnan har yanzu ya na jikina ba, kuma kullum k`ara girma ya
ke,kar ki so ki ga irin murna da farincikin da Imam ya nuna a lokacin da ya samu labarin cikinnan ga
kulawa ta musanman da ya ke bani,ina hakan a raina duk sai in rasa ina zan sa kaina da kuma tunanin
irin halin da zai shiga in ya ji labarin babu cikinnan ".
" To ki bar shi mana in kina ganin tashin hankali a fuskar Mijinki sai ki jure duk wani challenge da zai
biyo wajen rainon cikin da kuma bayan kin haife sa".
"A'a Anesa hakan ba zai yiwu ba domin da akwai shagulgula da manyan taruka da za a gudanar a
Masarauta bayan sallah ,a lokacin cikin ya Isa yai girman da zai hanani samun damar lashe kanbun
Gimbiya da ta fi kowacce Gimbiya kyawu, Ado da kuma saka kaya masu tsada,bazan ta`ba barin wannan
damar da na samu ta kubce daga hannuna ba na sha wuya kuma na d`au lokaci mai tsawo kafin in kawo
wannan matakin dan haka ba zan yi wasa da ita ba".
" In ko har haka ne ki na da gaskiya bai kamata ki bar cikinnan ba domin ina da yak`inin ko Alkyabba ba
za ki sa ta yi maki kyau ba,balle a kai kan sauran kayan Ado,cha`b Ai ko mutum goma ba za ki samu
wanda za su ya ba ta ki kwalliyar ba,wata k`ila kuma a samu amma a cikin Bayi amma ba dai `yan cikin
Masarauta ko wad`anda ake gayyatowa ba".
"Na shiga uku in haka ta kasance da ni ban san ina zan sa kaina ba,ina mai tabbatar mi ki da ba zan
sake nuna fuskarta a irin wad`annan taron ba in har haka ta kasance".
Wani murmushin gefan baki Anesa ta yi kafin ta ce,"In ko haka ne kar`bi ki sha ya fito waje kowa ma ya
huta", ta kai zancen ta na mai d`auko ma ta ruwa a d`an k`aramin fridge da ke ku sa da ita.
Amsa Gimbiya Ayush tai ta aje ta na mai kauda kanta can gefe ba tare da ta ce mata komi ba,cikin
mamakin attitude d`in da ta yi Anesa ta ce da ita,"Me hakan ke nufi,kin sa ni a rud`u,ko dai so ki ke ce
min duk abubuwan da ki ke fad`a ba gaskiya ba ne ba,ko kuma maganganun Gimbiya Fadeelah ne suke
son wasa da hankalin ki,Fadeelah ba kowa ba ce face k`anwar ki,har ita wace ce,wanne matsayin ta ke
da shi,me ta taka".....
A fusace Gimbiya Ayush ta dakatar da ita,sai dai ba ta iya ta ce mata komi ba har Saida ta saita
kanta,ta rage fushin da take ciki gami da sassauta zancen da ke d`auke a bakin ta," Kin ga Anesa na gode
da shawarwarin ki da kuma lokacin ki da ki ka ba ni,Na gode da hakan ki zo ki tafi Gida ,zan kira ki daga
baya".
"Mene! ki na nufin korata ki kai daga Gidan ki,akan me,me na aikata,ko shine sakamakon kasancewar
da ke da na yi ?....ni...na ma rasa ne zan ce da ke".
Ko motsi Gimbiya Ayush ba ta sake yi ba,har dai Anesa ta gaji da kallonta da ta ke,ta zari Jaka da car
keys d`in ta yi hanyar barin bedroom d`in Na ta.
"Ki gaishe da Baba Waziri da kuma su Umma Karema", Gimbiya Ayush ta ce da ita,Ko jiyowa ba tai ba
balle ta sa ran za ta bata amsa.
Kwanciya Gimbiya Ayush ta yi hannunta d`aya a saman cikinta ta na shafa shi,a hankali kamar mai
rad`a ta ce," I'm sorry My Unborn Baby,ina son ka so mai yankan shakku dole ce kawai za ta sa in rabu da
kai,Zuciyata ba za ta ta`ba bani goyan bayan in barka ba,zan yi fatan nan gaba bayan wasu shekaru ka
sake dawowa a matsayin d`ana".
~~~~~~~~
"Momy kin tsorata ni,Na yi kuka na yi Addu'a,har sadaka na yi duk dan son in ga kin warke kar ki tafi ki
bar ni".
Gloria hannunta ta kai saman kan Jedeeda, cikin muryar majinyaci ta ce mata,"Haba `yata Jedeeda,
ina za ni in tafi in barki,zan yi ta rok`on Allah da ya bani tsawon rai inga har `ya`yanki".
Wata dariya ce ta kwace ma Jedeeda farinciki fal a cikin ranta," Zan so haka ta kasance ace har jikokina
kin ga ni ba ma iya `ya`yana ba".
"Momy I beg you kar ki k`ara barin ciwo yaci k`arfin ki har haka,mun shiga tashin hankali da damuwa a
saboda haka", Nora ta fad`a ta na mai sake shigewa jikin ta.
" I'm sorry kin ji Auta ta,I promise to you daga yau zan rik`a kula da kaina da zaran Na ji wani abu da
ban gane shi ba,zan yi saurin yin magana akai ba zan k`ara barin family na su shiga cikin tashin hankali a
kai na ba".
Shigowar Granny tare da Uncle Rechal ce ta sake dawo da murnar farkawarta ta sabuwa.
"Kin ba ni tsoro My Daughter Gloria, wannan wanne irin ciwo ne mai firgita ahali haka?".
Cikin muryarta ta majinyata ta ce,"Mom ai yanzu komi ya wuce tunda gashi yanzu na warke,kuma wai
kun manta da ake cewa,a woman who gets her strength from God can never ever be broken, don haka
ba abinda zai same ni tunda ina tare da albarka Yesu Almasihu da kuma ta ki".
Fuska d`auke da annuri Revered Anderson da shi da Martin su ka shigo ,hannun Martin d`auke da
sabbin magungunan da aka sake rubuta ma Gloria, da sauri ya aje ledan ya matsa kusa da ita suka sa ta
tsakiyar shida Nora.
" Papa ya ake ciki ya Doctorn ya ce wanne mataki take a cike yanzu?".
"Thanks to the Father Lord, ya ce kiji da sauk`i ,ga sabbin medicine nan ya rubuta mata ya ce ta sha na
kwana biyu kafin daganan sai a sake check up d`inta daganan sai ya sa mana ranar sallamah".
Fuskar kowa sai da ta nuna farincikin jin wannan batun,Granny ce ta kai dubanta kan su Martin ta ce
da su," Kun ga `yan jikokina ku taso ku bata wuri ta d`an huta in ta k`ara samun sauk`i sai ku je ko ciki ne
sai ta mai da ku,kun fa girma da wannan halin ak`allafa kun kusa 19 years ai kwa barma yara wannan
d`ab'ar ko".
Sake shigewa jikinta su duka biyun su kai,Wanda hakan ya sa Gloria ta sake rungume su kafin ta
ce,"Mom ki bar su suna kewata ne ,kwana nawa ba su samu irin wannan kulawar daga gare ni ba".
Jayayya ce ta `barke tsakanin Rechal da Revered Anderson kowa a cikin su na san ta fad`a mi shi me ta
ke sha'awar ci ya je ya siyo mata,ganin da gaske ba Wanda zai hak`ura a cikin su sai kowa ya je ya siya
abinda ya ke ganin za ta so shi.
~~~~~~
"A'ah Bibah yau ke ce a Gidan na mu", Ummu Nurain ta tambaya fuskarta d`auke da murmushi.
" Wallahi kuwa Aunty Zeenat, ya Gida ya aiki ina Nurain ya ke?".
Ta`be baki tayi kafin ta ce yanzu na kora shi ya bani wuri saboda ya dame ni,sai faman bari-bari na
ke,ya su Umma Hanne fatan duk suna lafiya ?".
"Eh ta na lafiya ta ce ma a gaishe ki,Yah Hameed ne ya je Gidan ya ce baki jin dad`i shiyasa ta ce in zo
in da wani abun da zan taimaka mi ki da shi".Bibah ta kai zancen ta na mai wara idanun ta cikin
Parlourn, tun kafin ta shigo cikin Parlourn ta tana tsakar Gida ta san yau za ta gaya ma `yan garinsu da
aiki.
" Shi Hameed d`in ne ya gaya miki ba ni da lafiya?",Ummu Nurain ta tambaya cike da mamaki.
"Eh haka ya ce,ya mace daga nan Gidan yake kuma "....
Tun kafin ta kai k`arshen zancen tai zumbur ta mik`e ta na mai nufar bedroom d`inta in da wayarta ta
ke,jikinta har rawa yake wajen lalubo Number sa ta fara Kira,Ringing d`aya biyu Ana uku yai picking,
muryar sa d`auke da sallama tare da gajiya isowar shi masaukinsa kenan daga Hospital.
" Yaushe za ka barni in huta ne,eyeh Abu Nurain, me na maka,shin ba ka jin tausayina ko kad`an,
k`aramin cikinka na ke d`auke da shi ga kuma hidimar Nurain da ta taru tai min yawa a kaina, amma duk
da hakan ba za ka barni in ji da iya wad`annan ba har sai ka koma kana had`a ni da iyaye da `yan'uwana,
so ka ke dole sai sun tsane ni kamar yanda ka tsane ni kaina ,so ka ke sai sun mai da ni saniyar ware
kamar yanda ka maida ni a cikin Gidan ka".ta d`an daka ta sakamakon jin wani abu na k`ok`arin tokare
mata mak`oshihakan ne ya bashi damar cewa da ita wani abu, "Zeenat me kuma ya faru wad`anne irin
maganganu ne su ke fitowa daga bakin ki,me na aikata maki bayan nisa da tazarar da ke tsakaninmu da
ke,ina ga fa tunda na zo wannan Garin wannan itace waya ta biyu da mu kai to me nayi maki,ina nan ina
ta fad`i tashi duk dan in samu abinda zan rufa mana asiri amma hakan be sa kin ji tausayina ko Addu'a
mai kyau ki rik`a biyo ni da ita ba,sai dai tashin hankali da fitina".
" Oh iya adalcin ka abinda ya gani ma ka kenan laifina ma ka ke gani,to na gode,amma ina so ka sani
daga rana mai irin ta yau kar ka k`ara turo min wani cikin Gidan in har da zummar ka zubar min da
mutunci da k`ima ne,ba sai ka k`ara `bata min suna kamar yanda ka yi a baya ba,in kuwa ba haka wallahi
zan hauka ce maka a cikin Gidannan "....
" Ki hauka ce mana Zeenat, Dan Allah ki haukace d`in wai ke wacce irin Mace ce, me ye a cikin
kwakwalwa da tunanin ki Anya kuwa kin ma san me kalmar Miji da Zaman Aure ta ke nufi,to ki sani Na
shirya tarbar duk kalan haukan da za ki zo da shi,dai-dai na ke da ke".yana kaiwa nan ya kashe wayar
gami da cillar da ita saman kujerar da ta ke kusa da shi,hanunshi ya kai saman goshi shi yana mai dafe shi
tare da furta kalmar Innalillahi wa'inna ilaihir raju'un a hankali,k`arar knocking d`in da ya ji ne ya sa ya
bud`e idanunsa wanda har sun fara sauya kala,haka ya ja k`afarsa ya je ya bud`e ma eanda ya ke son
shigowar.
"Lafiya dai Imam Na ga yanayin ka duk ya sauya", Doctor Nass ya tambaye shi bayan ya ra`ba ta jikin
shi ya shigo Parlourn.
" Uncle Nass Zeenat ce,nema ta ke ta tarwatsa min tunanina,so ta ke sai ta samin cutar damuwa ta
k`arfi da yaji,Wai Dan Allah haka dama Auren Zumincin ya ke,wannan bala'i har ina?".
Sai da Uncle Nass d`in ya kama shi ya zaunar da shi sannan ya ke ce mi shi,"Duka Mata kowa na da irin
na ta k`alubalen ba wai sai iya Auren Zuminci ne ake samun tasgaro a cikin sa ba ,ita Zeenat wannan
shine na ta k`alubaken,ka yi hak`uri ka dage da addu'a,in sha Allah komi zai wuce wata rana".
"Amma Uncle Gimbiya Ayush ba ta min irin abinda ita Zeenat d`in ta ke mani,duk da ita tafita a komi
ga dukiya ga Sarauta amma iya abinda na ce mata kawai ta ke yi".
Wannan Allah ne ya so ka da rahama ya sauya ma ka da ita don ka samu natsuwa daga gareta,don
haka sai kai Godiya kuma ka k`ara da hak`uri", da kai Imam ya amsa ma sa ba tare da ya kuma cewa komi
ba.
"Na je can Hospital d`in akace min ka taho masaukinka shine fa na zarto nan ga launch d`inka can
Madam ta ce a kawo ma ka".ya sanyo wani zancen da zai sa su bar wancan.
Murmushi mai tafe da yak`e ya yi tare da cewa," A mik`a min godiya ta wajen Aunty tawa ina ta sa ta
d`awainiya tun zuwana".
"Oh wannan Ai kun fi kusa,yauwa ya Maganar Mrs Anderson ya jikinta a wanne Condition ta ke
yanzu ?".
System d`in shi ya janyo ma shi tare da cewa," Ga file d`in ta nan duba ka gani kafinnan bari in d`an
watsa ruwa ina fito sai mu tattaunawa yanda ya kamata".
*JADEEDAH*
(It's a story of two love birds who are so different from each other )
STORY & WRITTEN BY :
(*Cwt~Sumiey*)
Marubuciyar littafin
MENE NE ABIN YI ?
KARAGAR MULKI
And now.....*JADEEDAH*
*YOTA*
BOOK 1
PAGE 22❤
"Momy mun yi waya da Papa ya ce ya Isa lafiya ya na saran tomorrow early in the morning zai baro
Lagos ya dawo ,domin gabad`aya hankalin shi yana nan ya na son ya ji yanda last result d`in nan zai fita".
" Eh nima ya kira ni amma tun bayan isar sa Airport ne daganan ba mu sake yin waya da shi ba,a
lokacin ina gab da shiga d`akin Test d`in".
Granny ce ta amshi zancen da cewa,"Ya kamata