Author : Cwt Sumiey Category : African Stories & Novels
kai zancen ta na mai d`ora masa card d`in nata a saman wayarsa da yake k`ok`arin
kiran number Police ta ko ta `baci.
" To hell with your card, har ke wace ce,me ki ka d`auki kan ki da har ki ke iya fad`ar duk abinda ya zo
maki a bakin ki ba tare da Kin yi duba da irin asarar da ki ka janyo min ba,dubi fa ki ka ga yanda motata
ta koma duk a saboda ke ,ita fa ce hanyar da nake ci da ahalina da ita,ke kawai hankalin ki na kan lokacin
da za ki `bata,mai yasa ba za ki tsaya ayi ficzing d`in matsalar da ke ki kayi causing d`inta ba, Don haka na
rantse mi ki sai Na yi reporting d`in ki ko ke yar wace ce kuma ko da hakan na nufin ba za a biya ni
hak`ik`i na ba,ko ba komi zan `bata maki lokacin da ki ka nuna kin fi martaba shi fiye da komi"......
"A'a let her be kyaleta ta tafi,ni zan biya duk abinda ya kamata ayi,ko ba komi kai Namiji ne kuma
sama da ita ka ke,ka fita nisan hankali da kuma sani abinda ya kamata,just one thing da na ke so daga
gare ka ka samar mani da wata tacxi d`in da zan idasa inda za ni cikin sauri",Cewar Muh'd Jaheed da ya
iso inda su ke.
Da hanzari Jedeeda ta d`ago kanta ta na mai sauke idanunta akan shi,eh tun d`azu ta san ba iya Driver
d`in ne kawai a cikin motar ba, amma hankalin ta bai sake komawa a kan shi ba,rasa me ma za ta ce da
shi tai,sai juyawa tai ta nufi inda ta ta motar ta ke domin barin wurin.
Cikin d`acin rai da zafin abinda ta aikata Drivern ya bita da kallo ji yake inama wata kyakykyawar isaka
zata taso ta yi gaba da ita ,da ya ji dad`in hakan, hakan ya d`ar su a ransa ne sakamakon yanayin k`irar
halitta da ta ke da ita,kwata-kwata bata da k`iba shi is slim girl,ta Na da matsakaicin tsawo,wacce ba zaka
iya kiranta gajera ko kuma wacce ta cika tsawo ba,irin medium d`in nan haka take,plazon wando ne a
jikinta sai kuma wata `yar riga `yar k`arama da iya gabanta kawai ta rufe mata daga baya kamar belt ne
ya rik`e ta kawai,ta tara gashin kanta wuri guda sai faman reto yake.
"Kaga kira Mechanic d`in da zai iya gyara maka motar ka,domin ina son in bar wurinnan da wuri".....
K`arar da wayarsa ta fara ne ya dakatar da shi, picking call d`in yai muryarsa d`auke da sallama.
" Jaheed lafiya dai ko?,ka ce min ka kusa isowa tun d`azu amma har yanzu na ji shiru,Matarnan fa
tana cikin critical condition ne fa?".
"Uncle Nass mun samu accident ne",....." Subahanallahi kana lafiya dai ko ba abinda ya same ka ko ?".
"Ina lafiya ba abinda ya same ni har ma da driver d`in da mu ke tare motarce kawai ta samu Matsala".
"OK Masha Allah I will be here right now ka jira ni,tura min location d`in inda ka ke ganinan zuwa",
Uncle Nass ya fad`a ya Na mai barin duk abinda ya ke.
Kamar wacce aka hankad`o ko kuma wacce aka biyo haka ta shigo cikin room d`in da Mahaifiyarta ta
ke kwance ba tare da ta san inda hankalin ta ya ke ba.
" Nora ya jikin Momy a wanne mataki ta ke a yanzu ?",shine abinda ya fara fitowa daga bakin ta.
Da d`an gudun wacce a ka Kira da Nora ta k`araso kusa da ita idanuwanta na fara zubda ruwa,"Anty
she is still in unconscious situation, tun jiya a haka muka kawota",..."What tun jiya a cikin wannan halin
take kuma kuka zauna a cikin Hospital d`in,where is Papa ina ya tafi ?","Ammmm Asibitin suna iya bakin
k`ok`arin su yanzu haka Ana jiran zuwan wani Special Doctor ne,Wanda yake kula da `ban garen masu
lalura irinta Momy,to jin shirun yayi yawa ne ya sa Papa ya tafi ya dubo ko lafiya har yanzu bai iso ba".
Jadeeda rasa me ma za tai tayi sai kai da kawo ta cigaba da yi a cikin d`akin Asibitin.
Sheshshekar kukan Norah ne ya dakatar da ita tayi kanta da sauri,"Norah lafiya ki ke,me ya same ki,ko
kema ba ki da lafiya ne,why are you crying ?",duk ta jero mata wad`anban tarin tambayoyin a hargitse.
Cikin muryar kuka ta bata amsa da cewa,"I'm so afraid, ina jin tsoro kar wani abu ya samu Momynah,
ina jin tsoran haka,wannan wanne irin ciwon kai ne haka mai tsanani da azaba Wanda har ya ke
d`aukewa mutum ji da ganinsa ,Momy fa har fita tai daga cikin hayyacinta tai bata San mun iso wannan
Asibitin ba fa".
"Kin ga Nora ki kwantar da hankalin ki ba abinda zai faru da ita da sunan Yesu Almasihu, cuta ba
mutuwa ba ce,Allah ya na aiko ma bawanda da ita ne don ya jarrabe shi,ya ga zai iya cinye wannan
jarabawar ko ba zai iya ba,ko kin manta ISAIAH Chapter 43 Verses 19 yana cewa "Do not lose hope in
time of trouble, for God is working in the unseen.His hand is steady, and his timing is perfect in bringing
good out of difficulty", haka ma a cikin MATTHEW Chapter 7 Verses 7 yana cewa," Ask and it will be
given to you, seek and you will finds,knock and it will be opened", don haka bai kamata ki sa damuwa a
ranki ba kin ji ko".
Wata sassanyar ajiyar Zuciya Nora ta saki Wanda hakan ke nuni da ta samu sassaucin abinda ta ke jin
tsoran game da ciwon Mahaifiyar ta ta,bayanin `yar'uwarta Jedeeda ya kore mata shakku da kuma jin
tsoran da ta ke cikinsa a baya,hannu Jeddeda ta sa ta janyo ta kusa da ita tana mai kwantar da murya ta
duk dan ta samu ta kwantar mata da hankali,"Let's prayer for her, in Jesus name za ta samu sauk`i kin
ji",a tare su ka nufi inda take kwance akan gado,a tare suka kai gwuiwowin su a k`asa gami da runtse
idanunsu tare da kama hannun Mahaifiyarsa da ke mafi kusa da su suka rik`e tare da cewa,"Heavenly
Father, I seek your healing touch
We come before You with hearts full of hope,Our sweet mother lies here, weak and silent.But we know,
O Lord, that You are the Great Healer.Please touch her body with Your healing power.Restore her
strength, renew her spirit.Let Your peace cover her like a blanket.We still need her, Lord. Please don’t
take her from us yet.
We trust in You, Lord.
Your ways are higher than ours.
Even in pain, we will praise You.
Heal our mom, dear God, if it be Your will.
And help us be strong while we wait.
Amen"
Bayan sun gama addu'ar ne sai ga shigowar Papa da hanzari Jedeeda ta matsa kusa da shi ta na
tambayarsa da cewa,"Ya ake ciki Doctor d`in ya k`araso ko?","Ki kwantar da hankalin ki my Daughter bai
iso ba motar shi ta samu matsala amma ga Doctor Nass can ya tafi ya taho tare da shi da zaran ya zo
Mahaifiyar ku za ta samu sauk`i".
"Oh har hankalina ya kwanta tunda komi zai yi sauk`i da zaran ya zo"," By the grace of God ".
A can `bangaren Jaheed hankalin shi kacokan Na kan duba file d`in patient d`in da zai duba tun bayan
had`uwar su Dr Nass," Uncle Nass hankalina ya tashi Matarnan she is in critical condition, wannan
wanne irin ciwon kai ne mai matuk`ar rikitarwa haka ?","Kai dai bari ni kaina ranar farko da aka fara
kawota na ga halin da take ci,shiyasa ma na ce ka zo ko zaka taimaka mata".
"To Allah ya taimaka mana,ya kuma bamu ikon aikata alkairi muga abinda za mu iya akan hakan", da
haka dai suka cigaba da tafiya har suka isa,ba tare da `bata lokaci ba suka fara shirin zuwa su ga patient
ta su.
Esther ce ta shigo hannunta rik`e da baskets na abinci Momy Rebecca na biye da ita a bayanta,wan da
suma sai yanzu da safe su ka sami labarin rashin lafiyar .
Kanta Momy Rebecca tayi tana mai cewa," Oh My Daughter Gloria me ya same ki,wannan wanne irin
ciwo ne haka,Yarinya ace ba a wani dogon lokaci da ita sai ace gata can kwance ba ta san inda kanta
yake ba"......,"Mom ki yi hak`uri za ta samu lafiya in the name of Jesus Christ, kar ki damu kan ki kin ji".
"Haba Revered Anderson ta ya za ka ce kar in damu kana kallon halin da ta ke a ciki kuwa,ko ko..motsi
ba ta yi ba ta ma fa san na zo nan ba",
" Akwai Doctor yananan zuwa zai dubata,idan har ya dubata naga ba wani improvement sai in fidda ta
wata k`asarnan kawai".
"Hakan shi ya fi Papa,ni kaina hankalina bai kwanta da wannan Hospital d`in ba", Cewar Nora,shigowar
wani Doctor da kuma Nusses guda biyu janye da gadon d`aukar marasa lafiya," Mr Anderson Doctor d`in
da zai dubata ya iso yanzu haka an umarce mu da shigar da ita Emergency, Sanan ku kuma a canza maku
d`auki kafin a fito da ita"Cewar d`aya daga cikin su.
"Okay ba matsala nan ", Nusses d`in su ka wuce da ita Emergency shi kuma ya tafi ya nuna masu sabon
d`akin da aka ce ya kai su.
After some hours," Congratulations Revered Anderson mun samu mun shawo kan matsalar da ke
damunta yanzu haka muna saran farkawarta ta nan da wani d`an lokaci ",shine furcin da Dr Nass ya fara
yi bayan fitowar su daga Emergency d`in.
" Praise be to Allah,the one who control everything around the world,blessed be to the God Father of
our Lord Jesus Christ, wannan shine abinda tun d`azu muke dako da kuma fatan ji daga gare ku",Nan fa
kowa dake cikin d`akin su ka fara nuna jin dad`i da kuma godiyar su,don Jedeeda kuwa runtse idanunta
tai tana mai had`e hannayenta wuri guda, ita kad`ai ta San me take cewa a cikin Zuciyarta,daga bisa ni ta
kai hannunta saman goshi da kuma gefe da gefan kafad`unta.
Bayan sun d`an natsa Dr Nass ya ce da shi, "Am Doctorn da ya dubata yana buk`atar ganin ka a office
d`in sa","Okay ba damuwa ma iya tafiya yanzu ?"," Yes uppcourse yana can ya na jiranka".
Har sun kusa fita Jedeeda ta dakatar da su da cewa,"Papa in biyo ka mu tafi tare ?","A'a ki zauna I will
be back soon kin ji my Daughter ".jiki a sanyaye ta koma ta zauna domin Maganar gaskiya ta so ta ji
musabbabin wannan ciwon Na Momynta.
A mutunce Muh'd Jaheed suka gaisa da Revered Anderson kafin Jaheed ya ce da shi,"Sir ina so ne in
san shin Madame ta ta`ba fuskantar wani hatsari ne ko kuma wata buguwa haka akanta ?",
Sai da Revered Anderson ya d`an d`auki lokaci kafin ya ce da shi," Yes uppcourse ta ta`ba had`uwa da
accident shekaru baya,but amma a lokacine mai tsawo ta ce min ta ta`ba fad`owa daga kan bene,bayan
haka ban san komi ba,kuma ba na tunanin an d`auki wani action mai kyau akan wannan lamarin ".
" Ayyyah I'm so sorry to say,saboda wannan incident d`in ta samu wani ciwo a cikin kanta Wanda
shine ya ke ja za mata yawaitar wannan zazzafan ciwon kan muna kiran wannan ciwon a likitance da
Neurogical disorder but amma it minor in sha Allah Na maka alk`awari zamu iya shawo kan matsalar
anan".
"Jesus Christ Doctor ta ya za ai haka ta faru,it's almost sama da shekaru Ashirin da biyu,ta ya za ai ace
sai yanzu illar hakan ta bayyana a yanzu".
" Sir ka fahimce ni,ko ba ka ji me Na ce ba tunda farko,it's a minor a baya ba ta kai shekaru haka ba,a
yanzu jikin ta ba zai iya jure rad`ad`i da zafin ciwon kan ba kuma ina mai tabbatar maka wannan ciwon
kan ba yau ta fara shi ba ,sai dai abinda na ke so da kai ka bincika ka gani za ka tabbatar da abinda na ke
fad`a maka".
Shiru Revered Anderson ya k`arayi na wani dogon lokaci, kafin ya ce,"Zan yi iya k`ok`arina wajen ganin
na binciki abinda ka ce,yanzu wanne mataki ku ka d`auka akan wannan ciwon, sannan me kuke buk`ata
daga gare mu ?".
"Ta na buk`atar hutu ba ta san hayaniya, don haka mun kai ta d`aki na musanman ,sannan akwai the
same case irin wannan wanda ya ke a k`ark`ashi na don haka zamu d`orata kan irin wannan treatments
d`in har zuwa sanda za muga k`arshen abun da izinin Allah,Sannan da akwai shawarwari da zan ba ka
Wanda su ke da buk`atar a kula da su ,amma yanzu lokacin sallah ya yi zan je in dawo in ya so sai mu
sake zama anjima".
"To shikenan Doctor Na gode I will wait you", da haka dai suka sallama su ka fito domin zuwa su
gabatar da sallah azhur
*JADEEDAH*
STORY & WRITTEN BY :
(*Cwt~Sumiey*)
Marubuciyar littafin
MENE NE ABIN YI ?
KARAGAR MULKI
And now.....*JADEEDAH*
*YOTA*
BOOK 1
PAGE 18❤
"Wallahi Momynah kar ki so ki ga Matar,na yi mamaki matuk`a the same irin case d`in Uncle banbancin
d`aya ita it's minor ne".
" Ya Salam My son na tausaya ma ta nasan zafi da kuma yanayin jigata ga wanda Allah ya jarabta da
irin wannan ciwon na juyewar kwakwalwa, Allah ya bata lafiya ".
"Amen Momynah sauk`in ta d`aya Hedeache kawai ciwon ya fara sakar mata a matsayin sing d`insa".
" To da d`an sauk`i za ace sai ka natsu ka fara fahimtar a wanne mataki take akai shin
Epilepsy,ADHD,Multiple sclerosis ko kuma Autism Spectrum ne daganan sai kusan wanne mataki ya
kamata ku d`aura ta akanta".
"Eh na duba hakan sai dai na ga ta mataki na Epilepsy mataki Generalized seizures wanda hakan ya ke
sa tai loss of consciousness".
" Da kyau that's my boy,yanzu a cikin matakai uku da ake d`auka game da wannan cutar wanne
matakin za ka fara amfani da shi,Medications to control seizures,Surgery ko Lifestyle changes ?".
"Momy I think i chose the number one ,kamar zai fi in hakan bata faru ba sai mu janza da wani options
d`in".
Sai da Hibba ta nisa kafin tace,"Focus on the person first not their condition. Treat them with dignity
and respect ka ji ni?", ta cigaba ba tare da ta tsaya ba,"When referring to someone with a brain-related
issue, it's essential to use respectful and person-centered language.By using respectful language, we can
promote understanding, empathy, and inclusivity".
" In sha Allah Momynah zan kasance kamar yanda ki ka tarbiyantar da ni ina k`arami ba zan ba ki kunya
ba zan yi kamar yanda ki ka ce ".
" Momynah ko dai za ki zo ki yi takin over akan wannan case d`in"....
"A'a ba zan zo ba kai ma ka sani,kuma ni ma nasan you will do better"...." Mom da gaske na ke fa ".
" Hmmmmmm Jaheed ta ya zan bar Kano in taho Abuja in duba wata bayan nima ina da nawa patient
d`in ai haka ba mai yiwuwa ba ne ba".
"Momy please shi's in unconscious condition she need your help"
"Ka ga Jaheed abu d`aya ni ke ganin zan iya shima sai in ka ga `bullowar wata Matsala ne wacce ba ka
gane ma ta ba, ko dai ta ziyarci ni anan a Hospital d`in da na ke aiki ko kuma in cigaba da treating d`in ta
online while kai kuma kana monitoring d`in,shi ne kawai abinda zan iya".
" To au ba matsala tunda har za ki iya bata wani d`an lokaci daga cikin lokuttan ki ai hakan ya wadatar
mana,mun gode da wannan alfamar",ya kai zancen ya na mai saluting d`inta.
Murmushi ta yi kawai ba tare da ta ce da shi komi ba,sai shine ya ce da ita," Ina Uncle yau ba ki bani shi
mun gaisa ba".
"Jaheed kenan Uncle d`inka yananan yanda ya ke kamar kullum", ta kai zancen ta na mai maida akalar
Camerar wayar yanda zai samu damar ganin sa ta Video Call d`in da su ke,an samu canji akan da don
yanzu yana iya zama ba kamar da da sai an kwantar an tayar ba,ya kan nuna alamar in yana jin yunwa ko
k`ishir ruwa amma daga ba haka ba ba abinda zai iya yi maka ko kalma d`aya daga cikin bakin SA ba ya
iya furtawa.
" Momy mai yasa ba za mu yi jump to the next level ba akan Uncle, an kwashi tsawon shekaru masu
yawa ya kamata ace improvement d`in da aka samu ya fi haka".
"Hmmmmmm My son nima na yi irin wannan tunanin amma Dr Liyo ya dakatar da ni ya ce in bari
muga zuwa k`arshen wannan year d`in daganan sai asan abinda za ai".
"Hakan ya kamata domin ni kaina ma k`osa in ga Uncle d`ina ya dawo kamar yanda na san shi a
baya"...... Ya dakata sakamom jin knocking d`in da aka fara yi mishi,ya mutsa fuska ya yi kafin ya ce da
ita,"Momy i have a visitor ya katsemin jin dad`i na, Allah har na k`osa lokacin tashi yayi in tafi Gida don
ma matsalar ba zan iske daddad`an abincin ki ba mai kamshi da saukar da natsuwa ga wanda ya ke ci".
" Au za ka fara tsokanar ta ka ko,yaushe rabon ka ma da cin abincin nawa ?,bayan ga matan ka can
`yan zamani wanda su ka fi ni iya girki".....kasa hak`ura yai da cigaba da saurare ta sai d`aga mata hannu
yai yana mai cewa,"By Momy I will call you letter da zaran na koma Gida",Ya kai k`arshen Maganar ya,na
mai ending call d`in.
Sake Knocking d`in akai a wajen karo na uku,"Yes come in",ya fad`a ya na mai gyara fuskar sa ya,koma
asalin Iman kuma Dr Muh'd Jaheed,ka sa iya sakin k`ofar tai ta shigo sakamakon yin tozali da fuskar da
ba tai zato da tsanmani ba.
Ba ita da ta shigo office d`in ba har shi Muh'd Jaheed d`in sai da yai mamakin ganin ta.
"May I come in", ta sake tambaya muryarta a rarrabe," Yeah you can come in, have a seat",ya kai
zancen ya na mai nuna mata kujerar da za ta zauna.
"Da me zan iya taimaka maki",ya tambayeta yana mai tsura mata ido da tattara hankalin shi akanta.
Sai da Jedeeda ta tattaro d`an sauran natsuwa da kuma kwarin gwuiwarta kafin ta ce da shi,"