Author : Cwt Sumiey Category : African Stories & Novels
Nurain ya na so Na ,to ya akai na I saka ki da damata ,tabbas Na d`aura d`amara can za
duk wani abu mara kyau da na ke aikatawa ko dan dawo da martaba da k`ima ta a idon sa, ke kuma da ki
ka shiga ki ka fita ki ka raba ni da Mijina ganinan gare ki ko ni ko ke mu zuba mu gani"...
Bai kai ga fita ba sai da ya sake zuwa ya gano jikin Gimbiya Ayush ya ga da sauk`i kafin ya nufi can
Babban Gidan.
Lokacin da suka isa bai iske su Malam K`arami ba sun tafi wani taro hakan ya sa kai tsaye cikin Gidan
ya nufa,bayan yai parking d`in motar sa a parking space Gidan gabad`aya an gyara shi an k`awarta shi da
kayan zama ni dai-dai gwargwado,sashen Ummie Maryam ya nufa a zaune ya iske ta cikin ladabi ya
zauna a gabanta tare da fara gaishe ta,"Jiya na dawo na biyu tanan aka ce ba kunan ke da Mama",ya ce
da ita bayan sun gama gaisawa.
"Eh mun d`n fita ne an yi rasuwa nan bayan layi,ya can gurin aikin Na ka komi dai lafiya ko,kuma Na
Hibba ta sanar min Na ce wata k`ila gajiya ce ta hanaka ka tsaya ka jira mu?"," Alhmdllh Ummie,ina cikin
shirin zuwa in gaishe ku sai ga kiran Momy ta na son gani na","Tooooo Allah ya sa dai lafiya ,ya mutanen
Gidan,ina Nurain d`an rikici?",murmushi ya yi kafin ya bata amsa da cewa,"Tare fa da shi Na taho amma
tunda mu ka shigo ya saki hannuna yai gaba ban san ina ya shiga ba".
"Too Yana can ya shiga wajen yaraka tashi ka tafi wajen nata ,Na San yanzu tana can ta na jiran ka,amma
kafin ka tafi ka zo ka amshi wani sallahu da gare ni,ka kai ma mara Lafiyar ",da to ya amsa kafin ya nufi
hanyar da za ta kaishi Part d`in Momynta shi..
A tsaye ya iske ta sai faman kai da kawo ta ke, wanda hakan. Yasa ya ya ida sa kusa da ita da d`an
saurinsa tare da cewa," Momynah lafiya dai ko ,ya jikin Uncle,, ina fatan ba abinda ya same shi ko ?".duk
ya jero mata wad`annan tambayoyin ba tare da ya tsaya ba.
Sai da ta dafa shi kafin tace da shi"Ka ga Yarona kwantar da hankalin ka ba abinda ya faru, zo zauna ka
ji komi ".
" Am ina Maganar taron k`aramar juna sanin da na ke ta ce maka za a yi a Canada to yau sun fidda nan
da two days za a fara hakan ne ya sa na nira ka domin ka zo mu tattaunawa yanda komi zai tafi,Na Kira
Yayah Nasir ya ce min zai shigo ko da zuwa yamma ne,daga yanzu sai ka kasance cikin shiri ,domin kai ne
za ka je taron". Hankalin shi ya maido kanta ya na mai mamakin abinda ta ce ,"Momy ni kuma dama can
tun tuni ni ki ke ma wannan shieye-shiryen tafiyar? ".
" To AI dama kai ya kamata ka je ba ni ba,kai ne dubbunan al'uma su ke amfana da iliminka amma ba
ni da kaina kawai na ke amfanawa ba".
"Amma....Momy".....ta katse shi da cewa,"Ya isa haka tashi ka tafi Gidan ka fara shiri,ka sallami iyalan
ka ,ni dama tuni Na riga da Na sanar ma da Baba K`arami, don har Na fara k`ok`arin yi maka booking d`in
flight, amma dai na ga da yiwuwar sai dai ka bi jirgin yawo domin kamar akwai k`arancin tashin jirage a
wannan satin sakamakon sauyin weather da mu ke a ciki".
Ba tare da ya yi mata mu su ba ya amin ce da barinta nan ya zauna suka cigaba da tsara yanda komi zai
tafi,kusan tare da Ummie Maryam su ka tsara komi ,har su Baba K`arami su ka dawo bai tafi ba ,kowa sai
murna da farin cikin samun wannan babbar damar suke gani suke kamar hanyar ko damar samun
sauk`in Abubakar ta zo,sai gab da la'asar ya bar Gidan.
Page 41
Kiran dare ya ratsa kunne. An riga an gama addu'ar dare, an kashe fitilu. Dukkan gidan ya yi tsit kamar
kabari. Sai dai Jadeeda ba ta iya barci ba. Kamar kullum, zuciyarta cike da damuwa da tambayoyin da ba
su da amsa.
A yau, wani abu daban ya faru,ta kasa iya mantawa da duk abinda ya faru tsakanin ta Bro
Edwin,yanayin bugun zuciyar ta har yanzu ya ƙi komawa dai-dai,idan ta runtse idanunta,sai ta ji inama da
ace komi zai gushe a cikin su,inama da komi zai gushe kamar bai taɓa wanzuwa ba,taya hankali da
tunanin ta zai iya ɗaukar wannan lamarin,tsawon yaushe zata iya mantawa da abinda ya faru,wasu
zafafan hawaye ne suka sake kwaranyowa da ga idaniyarta
Motsin shigowa ta ji ya sa ta ɗan waiga,Uncle Miey,ya kama hannun ta ya yi, ya zauna da ita a ɗaya daga
cikin kujerun da su ka yi ma Parlon ƙawanya. Akwai nutsuwa a fuskarsa kamar koyaushe, sai dai idonsa
yau sun bambanta. Yana kallonta tamkar ba mutum ba ne.
"Jadeeda," ya fara da murya mai laushi,"wannan yanayin bai kama ce ki ba,ki manta da da duk abinda ya
faru ki ɗauka duk zancen da Edwin yai mi ki tamkar sun gudana a mafarki ne,kar ki bar su su zama wani
dalili da zai lalata miki rayuwa ko ya jefa ki a cikin,ki manta da shi"......"A'a Uncle Miey wannan lamarin
mai girma ne,ya fi ƙarfin in manta da shi haka da sauri, babban lamarine,a ce ɗan'uwana na jini ya bijiro
min da batun soyayya ta ya hankali zai iya ɗaukar hakan da sauƙi?".
"Shakka babu nasan maganganunsa suna da girma da saka nauyi a cikin zuciya amma bai kai ki bar sa
ba,domin hakan zai iya yi miki illah",......."Illah kuma ta nawa Uncle Miey ai sai dai kar a kuma amma Bro
Edwin ya dasa miki mai zafi da zurfi a cikin Zuciyata wanda ban san dare ko ranar da zan warke ba".
"Zan cutu matuƙa idan har ki ka ce za ki cigaba da rayuwa a haka,cikin tunani da damu,ki sani kwata-
kwata hakan bai dace da ke ba,na ji baƙin cikin faruwar wannan lamarin,ina so ki sani,ba zan iya jurar
ganin ki a cikin wannan tashin hankalin ba,ki sani ba abinda ke damun Edwin sai hauka da kuma ƙuruciya
da ke damunsa,in Banda haka ta ya zai iya fuskantar ki da irin wannan kalamin mai girma,tabbas ya
aikata kuskure,ki manta da komi I'll handle everything kin ji".
"Ba ni tunanin zan iya fita waje in haɗa ido da ɗaya daga cikin mutanen Gidannan,nauyin su na ke ji ina
tsoran jin wani labari da baza iya ɗauka ba,bana son jin wani sabon labari wanda zai sake tada min da
hankali,don haka ka bar ni na fi son kaɗaici a yanzu"
"A'a a duk sanda na ke cikin damuwa ko tashin hankali ki na tsayawa tare da ni har sai na koma dai-dai
don haka ba zan bar ki ba,zai fi kyau mu fita wurin ƴan'uwa, su kan su suna cikin damuwa da tashin
hankali akan wannan lamarin".
Cikin ƙarin tashin hankali ta fashe da kuka tare dacewa,"Uncle Miey ka bar ni,na fi son zama ni
kaɗai,Mommy ta saka ni tsaka me wuya,ta kawo jerin sunayen samari wai dole sai na zaɓi ɗaya daga
cikin su ,a matsayin wanda zan aura,ga Bro Edwin ya zo da wata sabuwa a cikin rayuwata,don haka zai fi
Min kyau in samu wuri in keɓe ko na samu damar da zan sama ma kaina mafita"..….
A firgice Uncle Miey ya kusanto ta tare da cewa,"No....no..no ...kar ki ce dani Sister Gloria na neman
haɗa ki Aure da wani ba tare da na sani ba,don me ya sa zata aikata hakan ?."
Ya sake ta gami da fara kai kawo a cikin Parlon,zuciyarsa sai aiyana masa abubuwa kala daban-daban ta
ke,tabbas gab ya ke da yin sake,me yasa ya cika zurfin ciki,me yasa ya ke son ɓoye gaskiya gami da son
tauye kan shi,don me yasa Sister Gloria za tai yunƙurin kawo wani ko wasu da nufin son zaɓama Jadeeda
Mijin Aure bayan dakon sonta da yake ɗawainiya da shi tun shekaru Ashirin da suka wuce.
Ganin yanda hankalin shi ya tashi yasa Jadeeda tsura mashi idanunta,ganin tamkar ya na shirin zaucewa
ya sa ta nufe shi gami da kamo hannunsa ta ce,"Uncle Miey kana lafiya wannan sauyin na mene ne,na ga
duk ka rikice da ga jin wannan zancen nawa duk ka ruɗe har ma kafi ni shiga tashin hankali me yake
faruwa?."
Kasa ce mata komi yai sai jan hannunta yai ya zaunar da ita akan seater ya tsura mata idanu,zuciyar shi
na tsananta bugu wani ɓangaren kuma na ingiza shi akan ya sanar da ita sirrin da ke binne a cikin Zuciyar
sa tun da daɗewa kar ya bari ayi mishi Sakiyar Ciki,wani ɓangaren kuma na cewa da shi a'a kar ka aikata
hakan domin za ka sake cilla rayuwar ta cikin wata sabuwa kuma ruɗaɗɗiyar ƙaddara,za ka ɓalle wani
sirri mai girma na cikin rayuwarta,hakan kuma ba ƙaramin illah zai mata ba,to idan har ka ɓoye ka kasa
faɗa mata ya zaka yi a randa ka wayi gari wani daban wani bare ya Aure ta ya bar ka da dakon sonta da
ya ginu a cikin rai da rayuwar sa?, wannan lafazin da ya zo mi shi a raine ya ƙara hargitsa shi gami da
sake lulawa cikin dogon tunani.....
"Uncle Miey say something mana,shirun ka ya fara tsorata ni,ka sanar da Ni abinda ya ke faruwa ka
sanar da ni,na roƙe ka"....ta kai zancen muryarta na rawa.
"Kar ki yi kuka Jadeeda,ba zan so ganin zubar hawayen ki ba zan faɗa mi ki komi sai dai na roƙe ki kar ki
ce zaki guje Ni no meter how,za ki tsaya tare da Ni"......"Ka sanar da ni koma meye domin Zuciyata ta
ƙarfi da yasan mene ne dalilin da ya sauya ka kuma ya jefaka cikin irin wannan yanayin".
"Za ki iya tuna ranar da na ce ki shirya zamu fita zan yi Surprise ɗin ki sai rashin lafiyar Sister Gloria ya
tashi wanda hakan ya sa mu ka fasa fitar ?","Eh na tuna",ta bashi amsa ta na mai ɗaya kanta alamun ta
tuna ɗin
"Jadeeda ina son ki, I mean I love you,I love you since day one da na fara ganin ki,na ji Muryar ki,na ji
kukan ki ya ratsa kunnuwan,tun rana ta farko da na fara ɗaukar ki na danganta ki a jikina,ina son ki da
gaskiyata", wannan shine abinda na ke so in sanar dake a ranar".
Jadeeda ta yi murmushi mai cike da ladabi, amma jikinta ya fara rawa ba tare da ta san dalili ba. Sai
kawai ta ce, "Na gode Uncle Miey."
"Ban ce hakan don yabawa ba kawai Jadeeda....." Ya tashi daga kujerarsa, ya matso kusa da ita.
"A'a...Jadeeda... ina son ki ne. A zahiri, ni dai ina sonki dakuma dukkan gaskiya ta,ina nufin ina son ki da
Aure."
Kamar an zuba mata ruwan sanyi haɗe da zafi haka taki sanyi da zafi na keto mata ta rako 'ina . Gaban
ta ya fadi. Idonta ya lumshe, zuciyarta ta fara dukan uku-uku,ta fara jin wata hayani da kuma ƙara na
zagaye saman kanta, ƙafafuwan ta suka fara raurawa tamkar suna ƙoƙarin kayar da ita.
"Uncle Miey… ka ce me?"
Ya sa hannunsa kan kafadarta. "Ki fahimce ni, wannan ba laifi bane. Mun riga mun san halayyar
juna,na fahince ki kin fahimce ni. Ba na kallonki a matsayin ‘yar ƙanwata. Ina son ki a matsayin matar da
nake so in aura."
Duhu ya ƙara yin duhu. Sanyi ya fara ratsawa cikin kasan ƙafarta. Tana jin numfashinta ya yi nauyi.
Idanun Uncle Miey sun dushe da wani irin ƙiyayya da rudani. Bai kama da mai gaskiya ba. Bai kama da
Kirista ba.,"Ni ba zan iya ba!" Ta miƙe da hanzari, tana jin kamar ta fara zufa. "Kai… kai ƙanin mamana
ne. Wannan zunubi ne!"
Yai dariya da wata murya da ba ta saba jin sa ba. "Zunubi? Menene zunubi, Jadeeda? Ko kina nufin
addini zai hana mu soyayya?, to idan kina wannan tunani ki bari don Aure na da ke halattaccen Aure ne
kamar ma anyi anga domin har na fara gano ki sanye da wedding gwon sanye a jikin ki an kai Gidana a
matsayin Mata ta"
Da wani irin gudu ta tafi zuwa cikin bedroom ɗin ta tana kuka. Tana jin ana kiranta da murya, amma
ba ta waiga ba. Ranar nan ba ta runtsa ba. Tana jin tamkar duhu ya shige mata rai. Ta fara shakku shin
anya ba duka Gidan ne shaiɗan ya shafa ba kuwa ?.
Kasa haƙuri Uncle Miey yai ya bi bayanta har cikin Bedroom ɗin na ta yana mai cewa,"Me hakan ke
nufi,kar dai ki ce za ki bari ko ki guje Ni,kar ki ce ba zaki amshi tayin soyayya ta domin hakan babban
kuskure ne da bazan iya jurar faruwar hakan ba,ki sani My Angel zan iya aikata komi in har akan ki ne ciki
har da kisa,ki sa hakan a ranki da gaske na je ina son ki na shirya in rayu ko in mutu duk akan ki",ya kai
zance a matuƙar tsawace wanda har sai da Jadeeda ta tsorata gami da dunƙule kanta a jikin
gwuiwowinta.
Momy ta shigo a hargitse, ruwan zufa na gangarowa daga goshinta, hannunta na rawa, idonta sun yi ja
tamkar wacce ta fito daga mafarki mai muni.
Ba ta iya furta kalma ko ɗaya ba. Sai dai bakinta yana motsi, zuciyarta na bugawa da ƙarfin da har ana iya
jin sa daga waje. Kamar ta faɗi. Sai da ta dafa bango tana neman numfashints,Richal ƙaninta wanda
ƴarta Jadeeda ta ke kira da Uncle Miey, yana tsaye a gabanta cikin kwanciyar hankali, kamar wanda ya
gama cin nasara akan wani yaƙi.
Momy ta ɗaga idonta, ta kalle shi da wani irin yanayi da ya haɗa ƙiyayya, firgici, da bacin rai.
"Kana cikin hankalinka kuwa?! Ka san me ka ke faɗa?!”,Tayi ƙoƙari ta doshi gabansa, hannunta na girgiza
kamar za ta watsa masa mari.
Uncle Miey ya zuba mata ido yayi,sai ya saki murya mai sanyi da kasaita,"Ina cikin hankalina sosai,
Gloria. Kuma duk abin da na faɗa, na faɗa ne da zuciyata duka. Ina son Jadeeda. Ina son ta fiye da komi.
Kuma babu wani mutum ko wani dalili da zai hanani Aurenta."
Momy ta girgiza kai da hawaye a idonta, "Ta yaya za ka faɗi haka? Kai fa ƙanina ne! Kai ka sani da kyau
ita ‘yar cikin da ba za ka iya kallon ta da ido mai tsarki ba ce! Kana kallon kanka a mata Krista na gari
kuwa?,idan har haka ne ta ya zaka riƙa irin wannan tunani mafi muni fiye da na wulakantaccen
mutum?".
"Da gaske Ni mabiyan Yesu Almasihu ne,na gaskiya da gaskiya amma hakan ba yana nufin zan bar
soyayya ta ta farko ba".
Ya ɗan dakata kafin ya ɗora da cewa,"Wai ke duk a tunanin ki kulawar da na ke bama Jadeeda don ta
kasance ɗiyar da ki ka haifa ne,na liar wannan ƙarya ne,ki sani son ta na ke Aurenta na ke buri ko da
kuwa zai sa ki rasa hankali ki shiga hauka ne wannan bai dame ni ba."
Ba Mommy ba hatta da Jadeeda duƙe riƙe tana daman gursheƙen kuka sai da tai saurin ɗagowa gami
da dakatar da kukan nata,daga ina Uncle Miey ya samo wannan sabbin halaye,shine tsayar da ta tsaya
masu ai su duka biyu,sai daga baya Momy ta iya motsawa gami da cije leɓenta har ya fara zubar da jini.
Sai ta juya kamar za ta bar falon, amma sai ta dawo da karfi.
"Tabbas ka zo da wani sabon batu Richal wanda ko a cikin jerin mahaukata ban taɓa jin wanda ya aikata
irinsa ba,ina so ka sani daga yanzu na shirya ma duk irin haukan da ka zo da shi,ba kai ba ba Edwin ɗin ba
dukkan ku a tafin hannuna ku ke,mu zuba mu gani,na yi maka alƙawarin sai na dakatar dakai na kuma
ƙaryata duk wasu kalaman ka,zan aikata haka in har na cika kuma ina amsa suna na Gloria"
"To Ni kuma ina mai tabbatar mi ki da sai na fallasa ki!,domin a gare ni ba ki da wata daraja tun lokacin
da kika boye gaskiya. Ni zan nemi farin cikin rayuwa ta ,a tare da Jadeeda ta kasance,don haka ba
makawa Aurena da ita zai kasance!",ya ɗan dakata ,kafin Uncle Miey ya ce da rawar murya, "Na fi kowa
sanin wanene ni! Na fi kowa sanin irin wutar da ke ci a zuciyata. Ba zan bari wani ya hana ni son da ya
wuce duk wata doka a gare ni ba!"
Momy ta tsaya cak. Hannunta na rawa. Idonta ya rine da shudi. Zuciyarta ta fara bugawa da ƙarfi da
ƙarfi fiye da da. Sai kawai ta dafe ƙirjinta, ta ce da karamin murya
"Ya kamata Richal ka gane kuskure ka ke aikatawa,bai kamata ka ce" .......Kafin ta kammala, ta fadi kasa
da wani ƙara mai tsuma zuciya.
“Momy!!”,“Gloria!!”,a tare Jadeeda da ta ke cikin mugun halin da ya faskara da ita da Richal suka fara
kiran sunanta
Suna fadan haka su ka nufe ta domin kai mata agaji. Sai faman jijjigata suke a rikice. Amma ina ba ta iya
magana ba,bata motsi. Idonta ya cika da hawaye amma kuma ba kalma ko guda da ke fita daga bakinta .,
“Call an ambulance!!”, Richal ya faɗa a kiɗime, wannan ƙarar da ya yi ce ta jawo hankalin mutanen gidan
A nan aka fara gaggawa. Aka fito da mota. Gami da nufar asibiti da ita, zuciya cike da firgici da tambayoyi
masu ɗaci.
Page 42
Jadeeda na tsaya, hawaye na zuba a idonta,Momy na cikin ICU, kwance tamkar gawa mai numfashi.
Tana fama da bugun zuciya da matsanancin hawan jini
Daga bayan Jadeeda,Nora ce ta iso cikin sanyi da tausayi. Ta rungume Jadeeda da ɗan ƙarfi tana
fadin,“Ki kwantar da hankalinki, 'yar uwa… Ki tuna ba laifinki bane.for the sake of the Jesus name za ta
samu sauƙi ,komi zai koma Normal",ta kai zancen ta na goge mata hawaye da yatsun ta tana ƙoƙarin yin
murmushi duk dan ta kwantar mata hankali ,kafin ta cigaba da cewa,“Rayuwa tana cike da
jarrabawa,Aunty Jeeyyyy Wata rana komai zai dawo daidai.”
Hannu Jadeeda ta sa ta tureta. Idonta ya cika da ɓacin rai da matsanancin jin ciwo da kuma raɗaɗin da
Zuciyata ta ke mata,“Kina tunanin daɗaɗan kalamanki zasu sauya gaskiya?!Noora ba ki san azabar da ke
ci min rai ba. Ba ki san irin abin kunyar da na shiga ba!”
Kasa iya cewa komi Noora ta yi sai bin Jadeeda da idanu da ta yi
“Bro Edwin… shine ya fara. Shine ya rikita komi Shine ya bude wannan ƙofar da sheɗan ya samu damar
shigowa da