Author : Cwt Sumiey Category : African Stories & Novels
Gidan waye kin san Maganar da kika fad`a ba za ta haifar da d`a mai Ido ba,kin
ma ga tafiya ta ba zan so wannan maganar tai tsawo ba",ya na kaiwa nan ya bar ma su Parlourn, ya nufi
Part d`in Zeenat Ummu Nurain.
Da shigar shi cikin Parlourn da sallama ya fara cin karo da tarin sharar da akayi ba a kwashe ba da
kuma kayan sawa zuzzube a k`asa har ma da,kwaninkan abinci.
" Dan Ubanka ba za ka tsaya ba,ka tsaya in cire maka rigar ko kuma in bar ma ka kayan tsiyar ka in ba
ka son wanka",shine zancen da ya fara ji a,kunnensa bayan shigarsa Parlourn.
A sanyaye ya yi sallama Wanda Nurain Na jin Sallamar ya kwace daga hannun Umansa da gudu ya nufi
wurin sa ya Na kiran Oyo yo Uncle Oyo yo ,d`aga shi sama yai yana murnar ganin sa da yai ,"Oyo yo my
son ya ka ke ya rashin ji ya `barna"....d`an dakatawa yai yana mai sake kai hancinsa jikin Yaron kafin ya
ce da shi,"A'aha Nurain kwata ka fad`a ne da Na ji irin wannan wurin na ta shi a jikin ka?".
"A'a ba kwata na fad`a ba,Umma ce ta dai na yimin wanka,sai ta ga dama",idanu kawai Hameed ya
zuba mata wanda nan da nan ta sha jinin jikinta ta ce da shi," Ka ga shirmen shi ne kawai fa, ka san yanzu
lokacin sanyi ake shi kuma akwai yawan ciwo ga Nemonia da ta ke yawan addabar sa shine fa na koma a
sati bai fi in yi nasa wanka sau d`aya ko sau biyu ba duk dan kula da lafiyar sa".
Shiru Hameed yai ya na mai k`ok`arin danne abinda ya ke jin ya na taso ma sa a cikin Zuciyarsa,da
k`yar ya iya ya ce da ita,"Ya Imam ne ya aiko ni ya ce in tambaye ki ko da akwai wani abu da ki ke so ko
kuma ya k`are a Gidan sai in siyo ma ki".....
"Ka koma, ka ce ma sa bama buk`atar komi daga gare shi ya bar mu mutu,in tunani ya,ke don abinda
ya ke bamu mu ke Raye har yanzu dan Allah ka ce ya daina bamu komi,ba ma buk`ata".
" Subahanallahi Ummu Nurain mai yai zafi haka,ta ya za ki rik`a fad`in irin wad`annan munanan
maganganun kan wannan `yar Maganar?,kar ki manta shifa Wanda ya aiko ni a matsayin Mijin ki fa ya
ke".
"Ka ga ba ruwan ka kai d`an aike ne,ka koma ka sanar da shi abinda na ce da kai,za ka zo ka wani tasa
ni da wani k`auli da ba'adi ", ta kai k`arshen zancen ta Na mai figar hannun Nurain,nan ta ke ya fashe da
kuka ya na kiran sunan Uncle d`insa.
Ko minti d`aya Hameed bai k`ara a Parlourn d`in ba ya fita Zuciyar shi cike da tausayin d`an'uwansa da
kuma irin rayuwar da ya ke gudanarwa.
"Yauwa Anesa ina sak`ona fatan ke ma baki manta ba kamar yanda Autar Fulani ta man ta min da
sak`o", Gimbiya Ayush ta tambaya.
" Wa ina ni ina mantawa da sak`on ki Ai ban Isa ba gashi na taho da shi",ta kai zancen ta na mai zuge
zif d`in Jakarta ta mik`a mata tare da cewa,"Doctorn ta rubata yanda za ki sha shi sannan ta ce da zaran
kin sha zai yi waje ba jira"......
"Anty Gimbiya kar dai ki ce min Maganar Abortion d`innnan har yanzu ta na nan ba,kuma ba Gimbiya
Bahijja ta dakargta da hakan ba tunda farko ?".Fadeelah ta katse su gabad`aya da sigar tambaya a cikin
lafazinta.
"Kin ga Fadeelah wannan rayuwata ce ni ce ahak`k`u da in yanke ko in tsarama kaina yanda na so da
ita,ni ba zan bari in yi sakaci har in kai ga aikata kuskure irin wanda ko wacce mace ta ke aikatawa
ba,shin ko baki ga misali akan Ummu Nurain ba,tun bayan haihuwar Nurain duk ta bi ta lalace k`azanta
kamar ba mace ba,kar ma yanzu da ta ke d`auke da wani cikin,don haka ni ban shirya haihuwa yanzu
ba,ina son Mijina ta yanda zan iya aikata komi akan haka,ban shirya tara tarkacen tara yara a yanzu ba".
" Ke Fadeelah ki ja bakin ki ki yi mana shiru anan mu sa'annin ki ne, kuma wai ma ina ruwanki da
wannan Maganar wa ya kasa da ke,da har ki ke shirin d`auka,shin ko cikin a jikin ki ya ke ?".....Cewar
Anesa
"Dan Allah ki dakata min Anesa da `yar'uwata na ke magana ba da ke ba dan haka ki d`an saurara min
kuma da kike maganar ciki ba a jikina ya ke ba,Na ga kuskuren da ku ke son aikatawa a fili ne,wands son
Zuciya da kuma dogon buri ya makantar da ku wannan cikin fa halastaccen ciki ne me ye laifin sa me ye
aibu dan kun bari ya zo duniya kamar kowanne d`a,wannan fa ba shi ne karo na farko da ki ka zubar da
ciki a cikin Gidannan ba shin ba za ki ji tsoran wani abu ya same ki wajen zubar da cikin ba ko kuma asirin
ko ya tonu ?".
Da zafi Anesa ta sake ta so mata da niyar ta dakatar da ita,da sauri Gimbiya Ayush ta dakatar da ita da
cewa," Kin ga bita a hankali,don gudun samun wata matsalar kin Santa za ta iya yin komi don ganin ta
lalata mana shiri gara mu fahimtar da ita ta fuskar da za ta gane ".
Kallon ta mai da kan Gimbiya Fadeelah cikin fuskar tausayi sai da ta zauna ku sa da ita ta dafa ta
sannan ta ce da ita,"Mun ta so tare ni da ku,duk da kasancewar na girme ku amma ba wata tazara ba ce
a tsakanin mu,muna tsaka da karatunmu Me martaba ya katse min karatu ya bada Aure na,duk da bana
son Aure a wannan lokacin haka na haƙurƙuntar da kaina na danne dogon burin da ke a cikin rai da
zuciyata, Na ji a yanzu ina son Mijina ina son yin rayuwa da shi,shin a matsayin ki na k`anwata kuma
`yar'uwata ba za ki taimaka min da hakan ba, Kalle ni fa ki gani duka shekaruna nawa ne da za'ace in fara
tara yara yanzu, shikenan fa da zaran na haihu ba ni da sauran lokacin kaina,shikenan duk inda zani zan
tafi da yara buuuuuu daga wannan ya ce Momy yunwa na ke ji,Momy toilet za ni,Momy zan sha
ruwa,Momy ki dafa min ka za Momy ki siya min ka za,Momy this Momy that,Haba ba zan iya d`auka
ba".ta kai zance ta na mai yamutsa fuska.
Baki sake Gimbiya Fadeelah tai ta Na kallonta har sai daga k`arshe ta ce mata," A haka ki ka fahimci
abun ashe,lalle kin jahilci kan ki,Haba Ayush me ya ke damun ki wai what is on your mind Anya kuwa da
gaske ki ke ki Na son Mijin ki kuwa ?,indai har dagaske ki na son shi za ki so tara Zuri'ah da shi in ba
shima d`anyen tunani ne da shi kamar na ki ba,ko da ya ke nasan ba shi da masaniya akan wannan
lamarin na ki ba,Dan haka ina mai ba ki shawara da ki ji tsoran Allah ko dan gudun kar lafiyar ki ta samu
matsala nan gaba".
"Kin ga kar ki yi mata baki in sha Allahu lafiya lau zai fita ba abinda zai faru da ita, duka-duka sau nawa
aka yi abortion d`in ba sau uku ba ne ba kawai".
Mik`ewa tsaye Gimbiya Ayush ta yi tafara juyi a gaban Fadeelah ta nai mai cewa da ita," Kalle ni da
kyau tundaga Sama har k`asa kalli irin kyakykyawar hallitar da Allah yai min,ta ya zan bari in fara haihu
tun yanzu,structure d`in jikina ta canja, tafi-tafi k`irjina ya kwanta saboda tsabar tsotso ya koma tamkar
sleepers, banda hayaniyar yara,bari-barin su da kuma sa aikin tsiya,gara ban haifa ba balle ace ban kula
da suba,hakan yafi min sauk`i".....
Mik`ewa tsaye Gimbiya Fadeelah ta yi ,"Ya isa haka dan Allah ki yi duk abinda ki ka so na bar ki da
hankalin ki amma kar ki kuskura ko da wasa ki neme ni in ta kwa`be mi ki",ta na kaiwa nan ta sa`ba hand
bag d`inta tai hanyar waje.
Cikin tarin funshin da Gimbiya Anesa ta ke a ciki ta ce da ita, "Ki gaida na gaba na baya su san da uni",
ta na mai maida hankalinta kan Gimbiya Ayush ta na mai mik`a mata maganin ta ce da ita ," Afa shi kafin
nan da anjima ayo waje da kayan banza ko kin huta".
A yanda Gimbiya Fadeelah ta fita a cikin `bacin rai ko gabanta ba ta gani wanda hakan ya sa ko kad`an
ba ta ga Hameed ba da yake k`ok`arin shiga ta shi motar,cikin d`an d`aga murya yai mata magana,"Ya dai
kina lafiya kuwa ?",shine Maganar da ta biyo baya daga bakin shi.
Cikin inda-inda ta bashi amsa, "Normal lafiya me ka gani?".
Cikin siga ya wayance mata da cewa," Kin fito ki yimin rakiya zuwa supermarket d`in ne ko?","A no ba
haka ba ne ba,I have something urgently ne shiyasa zan tafi".
Sai da Hameed ya gyara tsayuwarsa kafin ya ce da ita,"A'a gaskiya ban yarda ba na ga hakan a cikin
idanun ki ne shiyasa Na fad`a dan haka kawai ki biyo ni mu tafi".
Yak`e kawai Gimbiya Fadeelah ta ke domin babban burin ta taga ta bar Gidan tun kafin wani abu ya
faru a ce da sa hannunta a ciki.
"To shikenan in ba zaki yi min rakiyar ba shigo sai in maida ke Gidan", ya katse mata gajeran tunanin
da ya ke son ribatarta.
" Kar ka damu Na gode this my car ni na zo da ita,don haka in sha Allah zan Isa Gida lafiya ".
" Yes I know It's your car but amma Sister d`in ki fa,ita a wacce za ta tafi ba sai ki bar mata wannan ba
ni in sauke ki a Gida","Idan na isa Gida zan sa Driver ko d`aya daga cikin fadawa ya zo ya d`auketa".
Sai da Hameed ya d`aga hannayensa sama kafin ya ce"Okay okay Na fahimci you did not enjoy my
company so I will leave you ".
Idanuwa a waje Fadeelah ta zaro ta na mai rasa me kuma za ta ce mi shi,yanayin yanda ta yi ne ya sa
ya fara yi mata dariya ya na nunata ,sai da su ka d`an d`auki lokaci mai tsawo kafin kowa ya shiga motar
shi yai gaba,bayan ya tabbatar ya rage mata damuwar da ta fito da ita.
*JADEEDAH*
(It's a story of two love birds who are so different from each other )
STORY & WRITTEN BY :
(*Cwt~Sumiey*)
Marubuciyar littafin
MENE NE ABIN YI ?
KARAGAR MULKI
And now.....*JADEEDAH*
*YOTA*
BOOK 1
PAGE 20❤
"Granny I'm serious I hate this country, ke ce kawai ki ka matsa akan sai mun dawo ,but tunda,mu ka
dawo ban ga wani abu da dawowarmu ta amfana maki ba,tunda mu ka dawo Momy sai ciwace-ciwace ta
ke, kullum ba ta da lafiya"...
"Gidan ku Na ce Nora,haka ake yi ma nagaba da ke magana dama,mene ne ya shiga cikin kan ki,ko
kina son ki zama disobedient gilr ne?", Revered Anderson ya katse da tsawa.
"Ka ga kar kai mata tsawa,she is my granddaughter ,hankali da tunanin ta bai nuna ma ta amfanin
jajircewar da na yi akan ku dawo ba".
" Eh duk da haka bai kamata ta yi magana da ke a cikin irin wannan lafazin ba dan haka ya zama wajibi
ta baki hak`uri don Gobe kar ta kuma ko kuma ta fuskanci hukunci na".
Sai da Nora ta matsa har kusa Mom Rebecca sannan ta bata hak`uri, janyo ta jikinta tai ta na mai
rungume ta tare da cewa,"Ba ki yi komi ba my love rashin sani ne amma ki sani iya ganin ku kawai da
nake a idona abu ne mai matuk`ar muhimmanci a gare ni,ina buk`atar ku a kusa da ni,duk mace da ta kai
shekaru kamar irin nawa ba abinda za ta so face ta rik`a yin tozali da `yan jikokinta a kusa da ita".
"Na fahimce ki Granny im sorry ba zan k`ara fad`ar irin zancena na baya ba", Nora ta fad`i ta na mai
sake shigewa jikin Mom Rebecca.
" Yauwa ban tambayeka ya jikin Gloria yake ba,ina zuci-zuci in samu in iso kafin time d`in ganin
patient ya wuce amma haka bai samu a gare ni ba sakamakon goslwo da ya rik`e ni".
"Mun samu damar ganinta,Jadeeda ce ma farkon shiga kin santa da k`ulafu cin uwa,tunda su ka dubata
su ka ce tana cikin yanayin da zamu iya shiga mu ganta ta fara kuka, har twins Nora da Martin sun fi ta
dakakkiyar Zuciya da ta shiga ta dad`e ta na yi mata Addu'a bayan ta fito sai su Martin ,Ni kuma lokacin
da Na shiga time ya k`ure dole ganin ka kawai na yi na fito,amma jikin da sauk`i sosai domin sun ce yanzu
a kowanne lokaci za ta iya farkawa".
" Thank God ,Thank you Jesus, thank you for what Haven done for us",ta fad`a ta na mai had`a
hannayenta wuri guda idanuwanta Na kallon sama,kafin ta cigaba da cewa,"Na ji dad`in wannan labarin
hankali na har ya kwanta",Mom Rebecca ta kai k`arshen zancen.
Jadeeda ce ta matso kusa da ita tare da cewa"Ba k`aramin relief na samu ba da na ji Doctorn ya ce
Momy should be okay za ta samu lafiya ta warke mu koma gida,don da fari har ma fara jin dama bamu
baro UK ba, domin sanda muna can Momy bata fuskantar irin wad`annan ciwace-ciwacen".
"Na ga alamun yarannan ba sa san zaman ku cikin k`asar ku ta gado ku ke ba,sai yanzu na K`ara
tabbatar da gaskiyar Mom da ta ke cewa kowa ya bar Gida Gida ya barsa,ba Dan barin Nigeria da mukai
ba da ba yanda za ai ku sa son wata k`asa fiye da ta ku a cikin ranku har haka ba,har ku ke jin zaman can
ya fiye mu ku nan", Cewar Revered Anderson.
" Haka ne Revered nima gani nai ba wani relative nawa a kusa da ni na koma rayuwa kamar wacce ba
ta da wani gata,shiyasa fa na nace har sai kun dawo,iya ganin ku kawai ma da nayi hankalina ya dawo
jikina,Na daina jin kad`aice da kewar Pastor Emeka, duk da har yanzu mutuwarsa ba ta sake ni ba".
"Mom I'm sorry domin na gane kuskuren tafiyar da mu ka yi muka barki,Na rasa me ye ya shige min
kai da har na biye ma Gloria mu ka kwashe wad`annan shekaru masu tarin yawa, ba tare da mun dawo
Gida ba".
Shigowar Martin ce ta dakatar da su daga hirar da su ke Wanda a hankali sai ga Easter da kuma Uncle
Richal ya biyo ba, sosai shigowarsa ta ba su mamaki, kar ma Momy Rebecca, kanta gadan-gadan yai da
sauri ta dakatar da shi ta na mai cewa,Stop! Don't ever touch me,kar ma ka matso kusa da ni,kai mutum
ne mai son kan shi da yawa".
Bai saurare ta ko kad`an ba har sai da ya dangana da inda ta ke yana mai cewa," Haba Mom ya za ai ki
ce haka,ko kin ta`ba ganin inda d`a ya rabu da Mahaifiyarsa ai duk inda ya je zai dawo".
Da k`yar ta samu ta cire shi daga jikinta ,sai faman zabga mashi harara ta ke,cikin Girmamawa su ka
gaisa da Revered Anderson Mijin yayarsa,sannan daga baya Nora ta gaishe shi,Kafin Jadeeda itama ta
gaishe shi ,wacce tun shigowar shi ta fara tsalle murnar ganin shi,bai amsa ba har sai da ya janyo ta
jikinsa,"My love fatan dai ki na lafiya ba ki bari firgici da tashinhankali ciwon Momy ya cutar min da ke ba
?".
Cikin farin ciki da jin dad`i Jadeeda ta rik`e hannunsa kafin ta bashi amsa da cewa,"Gaskiya Uncle miey
hankalina ya tashi,Na ji tsoro sosai,amma yanzu komi ya wuce tunda Doctor Imam ya ce ta na samun
sauk`i","Doctor Imam waye kuma haka ?",ya tambaye ta a tak`aice," Doctorn da Asibitin ya d`auko ne
Dan ya dubata ya san me ya ke sosai da ba dan shi ba da yanzu ba mu san a wanne hali Momy ta ke a ciki
ba".
"Oh thanks to the Lord Jesus da ya kawo ma na shi domin ya zama silar samun lafiyarta".
" To the best Uncle in the world ka samu wuri ka zauna ka bar wannan parrot d`in d`iyarnan ta ka ka
zauna ka huta ga abincinan Easter ta zo da shi a zuba ma ka ka ci",Revered Anderson ya ce .
"A'a kai ma kasan inhar ina tare da My daughter ba Na gajiya haka kuma yunwa ba ta da tasiri a
kaina,saboda ita d`in ta daban ce komi na ta na daban ne a gare ni"....
Nora ta katse shi ta hanyar kiran sunan shi," Uncle ni fa,ba fa ita kad`ai ce Daughter d`in ka ba",ta yi
Maganar cikin shagwa`ba.
"Wane ni Nora Kema ta daban ce a wurina,in ina kiranta da Princess ke kuma bari mu ga da me zan
kira ki", ya kai zance ya na mai tafiya dogon tunani
Turo baki Nora ta fara yi ,Wanda hakan ya sa Momy Rebecca janyo ta jikinta tana mai lallashin ta tare
da cewa," Rabu da su, can wata rana zamu gan su a rana,shima Richal d`in ai ba wani Garin arzik`i ba ne
ba,wai ma ya akai kasan muna wannan Hospital d`in kuma yaushe ka yanke shawarar dawowa k`asarnan
bagatatan ba tare da wani ya sani ba,bayan mun kwashe sama da shekaru muna Kira da son ka dawo ka
k`i ?".Momy Rebecca ta kai zancen ta tana mai mai da akalar zancen akan Uncle Richal da sigar tambaya.
"Momynah kenan Na yi niyar surprise d`in ki ne kawai shiyasa na yo wannan tafiyar ta bazata,na samu
labarin rashin lafiyar Sister,hakan ya sa na ji dole ina son in dawo Gida in ga halin da ta ke a ciki,bayan
jirginmu yai landing Martin ya fara zuwan min a rai don haka sai na Kira shi a time d`in ya ke sanar da ni
ya na Gida yanzu haka ya zo yai Fresh up sai ya koma Hospital d`in kawai sai Na jira shi, har ya gama
sannan ya zo ya