Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Jadeedah Complete Hausa Novel by Cwt Sumiey

Author :  Cwt Sumiey Category :  African Stories & Novels

Chapter   27 / 37

78K to 81K   out of 108.5K words

sani I'll not open ba zan buɗe ba,ka koma inda ka fito"...."Ni.no
don't say that,Bai kamata ki aikata haka ba,na yi ta bin ki tun a Church Amma ki ka ƙi ssurarana kin ga
bai kamata in zo nan ba ki sake watsamin ƙasa a ido ba".

"Okay ka cigaba da tsayuwar a wurin in ka gaji ka tafi",ta na kaiwa nan ta kwashi abubuwan da za ta
buƙata ta nufi bedroom ɗin ta haka ya cigaba da bugawa ya na magiya har daga ƙarshe ya haƙura ya
tafi ,bayan ya tabbatar ba za ta buɗe ba duk da haka a cikin ransa bani wani abu da ya sauya game da ita
ba,don haka ma ya ƙudurce a cikin ransa gobe ma zai dawo.

Washegari Ester Monday haka suka cigaba da gudanar da event ɗin su kala-kala,kafin daga bisa ni su
tashi,taron ya koma gidajensu,irin taron family, friends da sauran su.

Ita kanta Jadeeda hankalinta ya yi Gida ta ƙosa ta tafi cikin family ɗin ta su yi Shagali kamar yanda su
ka saba,haka ta nufi Room ɗin ta ta fara haɗa luggage ɗin ta domin jirgin safe ta ke son ta bi.

"Blood of Jesus!", shine abinda ta faɗa cikin firgici da tashin hankali bayan ta ci karo da Fedrick zaune
akan ɗaya daga cikin kujerun da suke a Parlonta.....
Part 33

"Wai tsaya kar dai ki ce min tafiyar da na ji Mahaifin ku yana magana akanta ita ce wannan munafukar
kishiyar ta ki ta shiga ta fita aka tafi da ita?",Mama ta tambayi Zeenat.

"Tafiya kuma Mama dama kin san da maganar tafiyar ne ke","Shakka babu na san da wannan tafiyar
amma ban taɓa tunanin zai ce zai tafi da wata a cikin ku ba,domin na ga bai cika tafiya da ku ba in har ba
ko aikin Hajji bane ya kama shi","To ai gashinan yanzu ya tafi da matar so ya bar ta ki ƴar da tarin baƙin
ciki,da kin sanar da hakan ai da tani ta kasance cikin shirin ko ta kwana".

"Taɓ Allah Aunty Zeenat kar ki yarda kar ki kuskura ki bar su ,su ji daɗin zaman garin,ki kira shi ki tada
mashi hankali",cewar Asiya.

"Ai kuwa haka zan yi barinsa in kira shi","Yauwa Aunty Zeenat kar ki wani yi duba dare ya yi maza kira
shi ".

Haka ta fara kiran shi amma ana ce mata user busy,shi yana can ya na waya da Baba ƙarami yana ba shi
labarin yanda taron ya ke shirin kasancewa.

"Abbu komi lafiya,yanzu ma haka dawowata kenan,mun fara tattaunawa akan yarda taron zai kasance
zuwa gobe da safe ma in sha Allah za'a fara taron,za'a gudanar da taron live ne ma","Masha Allah a
labari ya yi daɗi,ina maku fatan nasara,zuwa da safe zan sake kira,daganan ma sai in haɗa ka da Baba
Malam domin ya damu yana son jin muryarka","Allah sarki nima ina kewan rikincin sa,na yi kewan ganin
sa",....."Gidan ku Muh'd Jaheed yanzu mahaifin nawa ka ke kira da mai rikici,sai dai ko Hibba ce
rikitacciya ba shi ba,shin ko kun haɗu da Alƙasim?","A'a ba mu haɗu da shi ba mun dai yi waya ya ce zai
ɓullo mu haɗu da shi","Hakan ya yi in yaso in ka sami dama sai ka leƙa Companyn ka ga yanda ake
gudarnar da shi","To in sha Allah zan yi ƙoriri in ga naje",da haka su ka gama hirar ta su,ya nufi Room ɗin
sa mai Number 264,kafin ya ƙara sa wayar shi ta sake wani ringing ɗin, dakatawa ya yi,yana mai picking
ɗin call ɗin ,"Ka sa a dawo min da Yarona kamar yanda ka ɗauke shi da kan ka",shine lafazin da ya fara
ratsa dodon kunnensa,dan ne abinda ya ji yai ta hanyar cewa,"Ummu Nurain ki na lafiya kuwa?,da irin
wannan kalamin ya kamata ki tarbe ni,ko kin manta tafiya nai,tafiyar ma mai cike da da hatsari,eh mana
hatsari mana tunda na hau flight ne,amma kuma sai ki rasa da me za ki tarbe ni sai da irin waɗannan
zafafan kalaman ?".

"Zafafan kalamai ai su suka fi dacewa da kai,shin kai ka manta abinda kai min kafin barowar ka Gidan
ne ?","Hmmmmmm Zeenatu kenan ,ban san sai yaushe za ki sauya wannan halin na ki ba",...ta katse shi
da cewa,"Ka ga ni ba wannan ce ta sa na kira ka ba,kawai ka sa a dawo min da ɗana ko kuma wallahi in je
har Gidan inyi tijara iya ta kuɗi Sannan in ɗauko ɗana","Zeenatu dan Allah kar ki fasa ki je Gidan,ki je ki
aikata duk abinda ki ka so,ba dai Nurain bane je ki ɗauko shi,Ni kuma ina mai tabbatar maki da sai na
raba ki da shi ,ke ko da makarantar almajirai ce sai na kai shi".....

"Ɗan nawa za ka kai makarantar almajirai?",ta tambaye shi cike da mamaki,"Oh kina ganin hakan ba zai
yiwu ba ne ba,to ki gwada ki gani,daga nan sai ki ga zan iya aikatawa ko ba zan iya ba".
Kuka ta fashe da shi da iya ƙarfinta tare da cewa,"Wallahi Yaya Jaheed baka isa ka raba ni da ɗana
ba,ina nan ina jiran ka ba zan bar duk abinda ka ke min ya tafi a banza ba,na rantse sai ka riski tashin
hankali,musiba da kuma fitinar da baka taɓa zato ba a cikin Gidan ka ,ina jiran ka ka dawo ka iske ni,abu
ɗaya zai hana faruwar duk abinda na lissafi maka ka sa a dawo min da ɗana gabana",tana kaiwa nan ta
tsinke wayar gami da ƙara ƙarfin kukanta,tare da cewa,"Mama wai kinji in har na je na ɗauko Nurain sai
ya kai shi makarantar allo don ya nuna min ya fini isa da iko akan shi","Makarantar allo kuma akan me ba
gatanan ana yi a Gidan su ba mai zai sa ya tafi uwa duniya?".

Saboda ya nuna min ni ba a bakin komi na ke a wurin sa ba shiyasa","A'a wannan lamarin ya yi nisa bari
Baban ku ya dawo sai na sanar da shi don ayi ma abun tufkar hanci tunda wuri.

Sai faman kai kawo Jaheed ya ke,a harabar ƙofar Room ɗin nasa shi bai shiga ba,sai saƙawa da kwance
Wa ya ke,shi a nashi tunanin a iya abinda ya aikatawa Zeenat kafin tahowarsa ya isa tai hankali gami da
shiga cikin taitayin ta,ya yi tunanin ,za ta zauna ta gano dalilin da yasa ya ke nuna mata irin waɗannan
sabbin halayen da kuma ko in kular da ya ke yi mata,amma da alama ya ga hakan ba lalle ne ya yiwu
ba,tunanin shi kuma kacokan ya koma wajen samun hanyar da zai nusar da Ummu Nurain kuskuren da
ta ke aikatawa,a baya dai yasan ya yi lallashin ya yi mata alkunya,ya fito fili ɓaro-ɓaro ya nuna mata
kuskurnta,har ta kai shi ga ƙaro mata abokiyar zama,yanzu kuma ya fara nuna mata halin ko in kula
amma duk da hakan ba a samu wani canji daga gare ta ba sai ma ƙoƙarin ƙara fanɗarewa da take,a
kullum sake tsiro da sabbin halaye take,a da iya ƙazanta ce kawai ta ke fama da ita,yanzu kuma ta kai har
ta iya fuskantar fuskar shi ta gaya masa duk kan kalan maganganun da su ka zo mata a baki,rashin kunya
kamar me,ba tare da ta yi la'akari da matsayin shi a wurinta ba,to yanzu ta ina ya kamata ya ɓullo
mata ?, shine abinda ya tsaya masa a Zuciya hana shi samun matsaya ko madara akan haka.

"Ka ga Fedrick ka fitar min a ɗaki,I said get out of my room,ni na rasa ta wacce hanya ka bi ka shigo min
ɗaki","Kin ga Jadeeda babu inda za ni inanan har sai ki faɗa min wanne matsayi na ke a cikin Zuciyar
ki,na gaji I'm tried,son ki ya daɗe da yi min illah,yanzu nema ya ke ya haukata ni,ba zan iya ba,akan ki na
rabu da iyaye na,na zaɓi in kasance da ke don kawai ina tsananin son ki, na gaji babu inda za ni",ya kai
zancen ya na mai gyara zaman shi.

Iya ƙololuwar tashin hankali Jadeeda ta shiga ji take ina ma da ta sani ta bi Papa masaukinsa da irin
haka bata faru da ita ba.

Cikin ƙasa da murya gami ,tausasa ta ya ce,"Haba Jadeeda ki ji tausayi na mana,kin sani iyayena sun
daɗe da musulunta na rabu da su na zaɓi da inyi rayuwa da ke,duka Gidan mu Musulmai ne,Ni kaɗai ne
mabiyan addinin Cristian,saboda ina jin tsora gami da tabbacin in na rabu da shi kamar na rabu da ki,
amma ke a kullum ƙara yin nisa da ni ki ke,babu wata halitta da ki ka tsana ta raɓe ki sama da ni,mai na
aikata maki har haka".

Can nesa da shi kaɗan ta samu ta zauna tare da cewa da shi,"Ba wai na tsane ka ne ko bana son ka ba
ne ba a'a,just ba na son maganar Aure ta na shiga tsakanina da kai,zai fi kyau mu cigaba da yin friendship
ɗin mu like yanda mu ka faro tunda farko ",.......ya katse ta da cewa,"Saboda me uhm?, saboda ban kai
matsayin fitacciyar mawaƙiya kamar ki ta so ni ba,ko saboda ba na da kyawun da za ki iya nuna ni a
matsayin Mijinki ? ".
"Oh God Fedrick ka maida hankalin ka jikin ka mana , soyayya fa bata yiwuwa ta ɓangare guda,dole
sai kana ra'ayi nima ina ra'ayi,na ce ba na yi ko dole ne,kabar ni dan Allah ka je ka nemi wata".

A hargitse ya juyo ya na mai bin ta da shanyanyun idanunsa ,ita kanta sai da ta tsorata ,kasa ce mata
komi yai sai da ya janyo bottle ɗin Wane ɗin da ke gefen shi ya ɗaga kai ya sha iya shan shi kafin ya ce da
ita,"Ba ki so na fa ki ka ce ?,in tafi in ba ki wuri,anya kuwa ba akwai wani wanda ki ke so ba da ya sa ki ke
treating ɗina like that ba?",ya kai ƙarshen tambayar yana mai sake ɗaya bottle ɗin wine ɗin sa sai da ya
shanye ta tas sannan ya cire bakin sa a jikinta tare wular da ita a tsakiyar ɗakin gami da miƙewa ya nufe
ta yana mai cewa,"ki ba ni amsa ta shin kina da wani wanda ki ke so ne,ko yaya",ya sake tambayar ta
cike da tsawa,gami da cigaba da kusantowa inda take".

"A'a..... a'a...... Fedrick ka dakata,ka dawo cikin hayyacinta,kar ka aikata abinda za kai da na sani akan
sa","Ba wani danasanin da zan yi ,anya kuwa kin don zafi gami da raɗaɗin da nake ji a cikin Zuciyata a
saboda san da na ke maki, a'a bana tunanin kin sani,amma ina son in tabbatar ma ki da ina maki
mahaukacin so da zan iya aikata komi akan sa,hakan ya sa ba zan taɓa iya jurar ganin ki da wani ba,ba
shakka in haka ta kasance mutuwa zan yi baƙin cikin da takaici sune za su zama silar yankewar
rayuwata,kin san wacce irin rayuwa na ke gudanarwa tun bayan rabuwa da ke da nayi a U.s na sha
wuya ,har jinya na yi kamar zan rasa raina,da ƙyar na samu na farfaɗo da saran zan sake haɗuwa da ke
amma ina hakan bai yiwu ba domin kin toshe duk wata kafa da ki ka san zan iya bibiyarta in iso gare
ki,wai wacce irin tsana ki kai min for the God sake?".

Cikin rawar murya wacce ke bayyanar da asalin tashin hankalin da take a ciki ta ce da shi,"Ba tsanar ka
na yi ba,kawai dai ina son".......ya katse ta da cewa,"Ki na son me kar dai ki ce min sunan wani za ki furta
min a matsayin wanda ki ke so",ya faɗa cikin sigar wine ɗin da ya sha ta fara aiki a jikin sa.

Kafin ta ce wani abu ya ɗora da cewa,"Da in bar hakan ta faru gara in kashe ki , sannan in dawo in
kashe kai na na san wata ƙila in muka je can lahira za ki iya so na,in kin ga ba wani wanda y fi ni a kusa da
ne ,kin ga kenan zamu rayu a matsayin Mata da Miji a rayuwar barzahu da za mu gudanar",ya kai zancen
yana mai rarumo tsagin bottle ɗin da ya sha ya nufe ta da shi sai faman tangaɗi ya ke,alamar ya fara
buguwa.



Jikin Jadeeda tuni ya daskare ta kasa ko motsin in kacire zuciyarta da kanta da ta ke faman girgizawa
dakuma zuciyarta da ta ke faman bugawa da sauri da sauri,in Banda su ba abinda ya rage da ke motsi a
jikinta,haka ya nufeta da tsagin kwalbar ,babu kalar addu'ar da ba ta yi ba,duk dan neman agaji da
taimako a wurin Yesu Almasihu.

Kamar wanda aka sa remote aka dakatar da shi haka ya tsaya ,sai kuma can ya saki tsagin kwalbar da
ke hannunsa,yana mai fashewa da wata irin dariya mai cike da ma'anoni kala daban-daban,sai a lokacin
hankalin Jadeeda ya fara kaiwa ta nemi taimako ko dai daga Hotel ɗin da ta ke ko kuma ta yi amfani da
wayarta,sai dai kash jarkarta na can wajen door ɗin shigowa wacce tai cilli da ita tun da ta yi tozali da shi
da farko,tellophone ɗin hotel ɗin kuma suna da tazara a tsakanin su,ƙasa tazame ta maido da ganin ta
kan shi sakamakon jin abinda ya ke cewa,"O me ma zai sa in kashe ki,in kashe kaina a banza?,me ye zai
sa ba zan yi amfani da wannan damar da na samu ba,ki zama Mata ta tun a duniya ba sai mun kai ga
zuwa barzahu ba",ya ce da ida ita yana mai fara ƙoƙarin cire rigar jikinsa.

"Ban.....gane ba..... Fedrick......mai ka ke shirin aikatawa wannan babban kuskure ne.....a'a .... a'a ka
dakata...ka bar kusanto inda na ke",ta ce da shi tana mai fusgo numfashin ta gami da ƙarfafa
zuciyarta,"Na yarda ina son ka amma na roƙe ka da kar ka cutar da ni","A'a Jadeeda kin makaro,domin a
yanzu ba zan iya dakatar dakai na ba,zan maida ke tawa,mallakina ni ni kaɗai,daga yau ba za ki ƙara
tunanin yin rayuwa da wani ba ni ba,daga yau zuciyar ki zata riƙa bugawa da suna na a kowacce
daƙiƙa,Ni ne zan zama jarumi a cikin labarin rayuwar ki,Ni ne zan zama uba kuma jagora a wurin ƴaƴan
ki,Ni za su kira da mahaifinsu,bayan ni babu wanda za ki kalla matsayin Mijin ki,Ni ɗin nan daki ka raina
ni zan zame me mi ki gata kuma abun alfaharin ki".......duk yana wannan zancen ne yana fidda kayan
dake jikinsa,gami da cigaba da kusantar ta duk data na ja da baya daga gare shi.

Samun sa'ar damƙar ta da yayi yasa ta saki wata ƙara mai ƙarfin gaske,duka ta cigaba dakai mi shi,gami
da kare kanta da duk abinda ya tare ma ta gaba,gami da roƙon shi da duk kalaman da ya zo mata a baki
akan ya ƙyaleta kar yake ta mata haddi,dambe ne ya kaure a tsakaninsu,ita ta na ƙoƙarin kwatar kanta
shi kuma ya na son cika nufinsa a kanta.

Ganin da gaske ya ke haiƙe mata zai yi yasa ta samu wuri Mafi tsoka a cikin fuskar shi ta manna masa
cizo da iyakar ƙarfi ta,kafin ya dawo cikin hayyacinsa ta samu Centre table da ke kusa da ita ta kwaɗa
masa a ka,sai da ya kai ƙasa saboda kwata-kwata bai shirya tsinkayen haka daga gare ta ba,har cikin
kwakwalwar sa zafin ya ratsa shi hakan ya sa ya sake ta batare da ya shirya ma hakan ba,samun wannan
sa'ar da Jadeeda ta yi ne yasa ta fara yunƙurin gudawa daga gare shi,sai dai ko taku biyu lafiyyayu ba ta
yi ba,ya cimmata,ƙafarsa ya sa ya taɗiyeta nan tai wata irin muguwar faɗuwa har kanta na buguwa da
tyle wani Maryan ihu ta saki amma duk da haka ba ya sare ba haka ta cigaba da jan ciki don ta samu ta
ga ta tsira daga gare shi,da iya ƙarfin sa ya fara kai mata duka a saitin cikinta daga ƙarshe ya sa ƙafarsa ya
take hannun ta gami da murzawa da iya kacin iyakar sa, wannan ne dalilin da yasa ta saki ihu da iyakacin
iyawarta tare da fara neman taimako

Wannan ihun da kawar neman taimakon da take yi ne,yai dai-dai da kai kawon tashin hankali da Zeenat
ta ƙunsama Muhammad Jaheed,a razane ya maida hankalin shi saitin inda ya ke juyo ihun nata, nan
zuciyar shi ta rabu gida biyu,wani ɓangaren ya na ya shiga wani kuma ya gargaɗarsa da kar ya je,wata
ƙila ma sharholiyar su ta kai sharholiya su ke zabga ihu,jin yawaitar ihun ne ya sa ya kasa iya riƙe kan shi
har sai da ya banka ƙofar ya shiga, abinda ya ci karo da shi ba ƙaramin tada mashi hankali ya yiba,a
zafafe ya nufi wurin ya na mai yaki ce shi akanta,gami da zabga masa zafafan maruka a kowanne kunci
na fuskarsa,zafin marin ne ya fidda shi daga mayen giyar da ya sha,ya dawo cikin hayyacinsa.

"Kai ****** waye kai da har za ka shiga tsakanin mu,ka san ko ita wace ce to Mata ta ce,don haka jaye
ka bamu wuri",Cikin rawar murya ta ce "....A'a I'm swear ƙarya ya ke,nema ya ke ya keta min
haddi,mutuncina ya ke son ya raba ni dashi", Jadeeda ta faɗa cikin karkarwar baki gami da ɓoyewa a
bayan Jaheed domin duk ya gama yayyaga mata kayan jikinta,kuma bugu da ƙari a matuƙar tsorace take
da shi.
"Kai dabban ina ne,idan matar ka ce haka aka ce ka je mata,wanne irin addini ka ke bi da ya koyar da
kai wannan haukan?".

"Oh ko dai shine wanda ki ke so,wanda a ta dalilin sa ki ka ƙi amsar tayin soyayya ta,to na rantse gara
in kashe ki kowa ya rasa a cikin mu",ya na kaiwa nan ya nufe ta,da tsagin kwalbar da ya wurgar
ɗazu,hannu Jaheed ya sa da iya ƙarfin shi ya riƙe kwalbar,wanda hakan ne ya hana isartar saitin
maƙogwaron Jadeeda,Fedrick da iya ƙarfin sa yake danna kwalbar don ta isa zuwa inda ya ke so,haka
shima Jaheed da iya ƙarfin shi ya hana hakan faruwa,tuni Jadeeda ta fara jiyo ƙamshi mutuwa akusa da
ita,cikin zafin Nana Jaheed ya hankaɗar da shi can gefe ,gami da bin shi ya fara kai mashi duka da mari a
duk inda ya samu a jikinsa, tabbacin da Fedrick ya samu na ba zai iya kwatar kan shi a wurin wannan
baƙon mutumin ba ya sa ya fara neman hanyar gudu,bayan ya ɗauki alƙawarin sai ya sake dawowa ya
cimma ƙudirin shi akanta.

Sosai hakan ya ƙara tada ma Jadeeda hankali amma gani yanda hannun Jaheed ke zubar da jini ya sa ta
nufi shi fuskarta ɗauke da damuwa tare da cewa,"Jesus Christ Kalli hannunka ka ji ciwo fa sosai",takai
zancen ta na mai ƙoƙarin kama hannun na

27 / 37