Author : Cwt Sumiey Category : African Stories & Novels
suna
da rabon rahama Allah zai kar karo da hankalin su,har suma su musulumta, Dan haka ka kwanta da
hankalin ka ji".
"In sha Allah zan dage ba dare ba rana har Allah ya karkato min da hankalin su,Gari ya fara wayewa ina
son zan je Inga Baba Malam kafin lokacin zuwa office yai".
Cikin yanayin murna ta ambaci sunan Baba Malam tare da cewa,"Ka ce in shirya mu tafi tare?".
" A'a yanzu zan dawo ya umarce ni ne da in zo da akwai abubuwan da ya ke son ya koyar da
ni,daganan zai ba ni littafan addinin da zan rik`a amfanin da su tunda ina da malama ta a cikin Gidana".
"Haba dan Allah ta ya za ai ka barni ni kad`ai a cikin Gidannan Allah ina jin tsoro"," I'm so sorry my wify
ba abinda zai faru da ke zan rok`i Allah da ya tsare man ke har inje in dawo ba zan jima ba",kallon shi ya
maida kan prayer mat d`in da ta gama Sallah akanta take, inda k`ur'aninta ya ke aje akai da alama
karatun ta ke,kan prayer mat d`in ya zaunar da ita kafin ya ce da ita.
"Cigabada da reciting d`in sa I will be back soon,ina mai tabbata ma ki yanzu zan dawo",
"Wayo ko shikenan ma hak`ura tunda abun `yar haka ce",murmushi yai mata gami da nufar hanyar
kitchen .
Da d`an d`aga murya ta tambaye shi ina za shi nan," Zan duba ne Inga abubuwan da bamu da su eanda
zamu buk`ata in na fita sai inbiya in taho da su,daganan sai inje in had`a ruwan wanka ".
" Am...to bara na had`a maka ruwan",Hibba ta fad`a ta ma mai nufar hanyar bathroom d`in da wani
irin kallon ya bita wanda har sai da ta tsargu ta waigo ta kamashi yana ma ta irin wannan kallon.
Shagwa`be fuska tai tare da ce mai,"Wannan kallon fa na me,ko ka manta now I'm house wife ?","I
don't say anything, kawai dai ina kallon ki ne kawai",turo baki ta tai gaba gami da nufar hanyar
bathroom d`in ba tare da sake ce masa komi ba,shi kuma sai faman binta da murmushi ya ke.
*JADEEDAH*
(It's a story of two love birds who are so different from each other )
STORY & WRITTEN BY :
(*Cwt~Sumiey*)
Marubuciyar littafin
MENE NE ABIN YI ?
KARAGAR MULKI
And now.....*JADEEDAH*
https://chat.whatsapp.com/CWkZfMqvD4H0mtd7WW6Xbz
https://whatsapp.com/channel/0029VapqU8C002T5Bz8RSQ0a
BOOK 1
PAGE 5 ❤
Tsawar da ya daka itace ta dakatar da Hibba daga tunkarowa inda yake,hannunta rik`e da robar ruwa
mai sanyi da cup,har ruwan dake cikin cup d`in sai da ya zube k`asa alamar ta ji tsoro, dawowar shi
kenan daga office yana k`ok`arin shigowa cikin Gidan.
"Na gaya maki Cecelia zan zo", ya fad`a cikin d`aga murya," Na gaya maki zan zo,ina da aiyuka dayawa
ne anan,nauyi ne ya k`aru a kaina da bazan iya tahowa in barsu ba,that's why ki ka ga na d`au wannan
long time d`in ban shigo ba,amma ba hakan na nufin na manta da ku ba".
"Oh wani abun mai mahimmanci ka ke da shi shine ne har ya tsare ka,kuma har muhimmancin sa ya
kai ka manta da mu,rayuwar ka kawai ka ke kai kad`ai ka manta da mu da dukkanin wani abu da ya shafe
mu in ya wuce ka tura ma na da kud`i,ba ruwanka da mu ,har Grandma ta k`araci ciwonta ta warke ba ka
zo ka ganta ba,ko an gaya maka kud`i sune kawai matsalar mu,muna buk`atar ganin ka a kusa da mu"...
" I said shut up Cecelia are you out of you sense, ba kya cikin hankalin ki ne,ta ya za ki tasa ni gaba kina
fad`ar duk abinda ya zo maki a bakin ki,ko ni sa'an wasan ki ne,don haka ki shiga taitayin ki,ki fita a
harkata kawai ki zuba min ido in kuma ba haka ba".......
"In kuma ba haka ba fa,uhm me za ka aikata,Na ce me za ka aikata Daniel".
" I'm sorry Grandma ba wai wani na ke nufi da hakan ba ne ba,kawai dai jin yanda take magana da ni
ne ta `batan mun rai har na fad`i irin wannan munanan kalam a kanta amma dan Allah ki yi hak`uri ".
" Ka rik`e hak`urin ka ba na so Daniel,ba na son hak`urin na ka,amma ina son ka sani, I swear to the
God idan har ba ka zo Gida mun yi bikin murnar Christmas a tare da kai ba sai na tako k`afata har nan
cikin Garin Kanon in ga abinda ka ke `boyewa da har ya zama katanga ko shamaki a tsakanin mu".
Cikin rawar murya Abbakar ya ce da ita,"Bbbbb.....ba sai kin zo ba Grandma ni da kaina ma zan zo in
sha Allah "," Daniel you said what ?".
Cikin yanayin kama kan shi ya ce da ita,"Ina nufin by the grace of God zan zo har Jos ɗin kafin bikin
Christmas zan zo".
Shiru Grandma tai na wani d`an lokaci kafin ta ce da shi cikin kwantar da murya "Daniel me yake
damun ka,dole akwai wani abu da yake damun ka,ba haka na san ka ba,dole akwai wani abu da ke
damun ka ko kuma ka ke `boye min shi".
" A'a Grandma ni ba abinda ya ke damun kawai pressure d`in office ce yanzu ma haka dawowata daga
office kenan ko cikin Gidan ban shiga ba".
"Shikenan Yarona Na yarda da abinda ka ce,ka kula da kanka ka ji,kuma kayi k`ok`ari ka zo da
Christmas tunda nasan ana bada hutu a lokacin".
" Kar ki damu Grandma zan zo","OK shikenan bye take care of yourself I will call letter yanzu ka samu
ka huta",
A hankali kamar mai yin samd`a haka ta k`araso kusa da shi,hannunta ta kai kan wuyan shi gami da
idasa cire masa neck tie din da ya fara cirewa tun shigowar shi, kujerar da ke kusa da shi ta zaunar da
shi,ta cire mashi takalmi da sock d`in da ke k`afarsa,sannan ta ba shi ruwa mai sanyin da ta zo da shi.
Kan hannun kujerar da yake ta zauna gami da tallafo kan shi ta d`ora a saman k`irjin ta ,tare da cewa
da shi,"I'm so sorry kaji my husband, in sha Allah everything will be ok,kar ka manta muna tare da Allah
ba zai ta`ba bari wani abu mara dad`i ya same mu ba ",haka dai ta cigaba da fad`a masa dad`ad`an
kalmomi har ya saki ranshi ba wai dan ya manta da abinda ya faru ba".
"Na gama had`a abincin tun d`azu ,ka zo kafara watsa ruwa sai mu ci abincin"," Mu watsa ruwa dai
bak`in ya ke I'm tied bazan iya wanka ni kad`ai ba".
"A'a wallahi na fa yi wanka tun d`azu, kuma fa kalli har kwalliya nai maka ko cewa na yi kyau ba kai
ba,kuma sai ace in sake wani wankan a'a gaskiya".
Ta k`asan ido ya fara kallonta tare da cewa," Ai haba ai ni ban gani ba,kuma ma ai kwalliyar mai sanyi
ki kai, Ni kuma kin san nafi son zazzafa,don haka dole a sake min wata sabuwa".
Bakinta ta bud`e gami da fiddo da dara-daran idanunta waje ta tana mai cewa,"Allah wannan wayo ne
nasan na yi kyau na, kuma kwalliyar ta zazzafa ce,kawai dai kawai",ta na maganar ta na ja da baya daga
kusa da shi.
Bai fi taku biyu lafiyayyu ya yi ba ya cimmata,tamkar `yar tsana haka ya rabata da k`asa ya nufi
bathroom da ita,ba tare da ta yi zato ba ya sakar masu ruwan sanyi akan su,k`ara sosai ta saki tana mai
ruk`unk`ume shi,tare da cewa ,"Me ya sa ka aikata haka,kafa san bana son ruwan sanyi",Tai Maganar ta
na mai kai mashi duka a k`irjinsa.
Zuwa lokacin tuni sun gama jik`ewa sharkaf,kayan su sun man-manne a jikin su sai da,ya raba jikinta
da na shi kafin ya bata amsa da cewa,"Ni kuma kin ga ina son ruwan sanyi,kuma da ruwan sanyi ya bige
ki sai kwalliyar ki ta zama zazzafa".
Dubanta ta kai jikin ta ,matsananciyar kuyan ce ta kamata wanda har hakan sai da ya sa ta shige jikin
shi tana mai `boye fuskarta a k`irjinsa.
Hannunsa ya kai yana tattare mata gashin kanta da ya barbazu a saman fuskarta tare shafa gurbin
tsagarta eleven eleven tsagar rumawa,"Da gaske na ke komi na ki birge ni ya ke,duk wani abu da za ki ko
ki ka yi k`arasawa in so ki na ke,ina son ki ina son in k`are rayuwata da ke,ba zan so in rasa ki ba ko da na
dak`ik`a ne domin hakan zai zame min babbar illah da kuma silar cutuwa a gare ni"......
Hannunta ta kai saman bakin sa ta rufe,tare da cewa," Ba abinda zai same ka domin na maka
alk`awari ba zan ta`ba yin wata rayuwa in har ba da kai ba,zan rayu da kai a kowanne irin yanayi na dad`i
ko akasin haka".
Sai da ya rankwafo ya had`a kan shi da na ta kafin ya ce da ita,"Thanks, thanks a lot,Thanks yuo for
being my wife ina farin ciki da samun ki a rayuwata kuma a matsayin matata".
₹₹₹₹₹₹
A k`agauce ya ke shiryawa yana yi yana na cewa,"Yau na makara sosai na yi late,kuma muna da
manyan bak`i da zamu yi meeting da su ban san har Gari ya waye haka ba",ya kai zancen ya na mai
maida hankalin sa akanta,matsawa kusa da ita yai ya zauna har ya zauna ba ta san ya zauna ba,sai da ya
kai hannu ya cire tagumin da tayi da hannu bibbiyu,Wanda hakan ya sa ta firgita ganin shine ya sa ta saki
ajiyar Zuciyar mai k`arfi
"Lafiya me ya same ki,ban saba ganin ki a cikin irin wannan yanayin ba,ko dai kina son komawa
makarantar ki ne ki gama tare da k`awayen ki?",.
Da sauri ta girgiza ma shi kai tare da cewa ," A'a ni bani sha'awar komawa waccan
makarantar,hasalima ta fita a raina,photo na na da naka ba inda ba su karad`e ba a cikin
makarantar,kuma da labari mara dad`i don haka na hak`ura da ita bana da burin sa ke komawa cikinta".
"Ko kin san cewa ba kowanne lokaci ka ke yarda ka bar abinda ka ke so don saboda maganganun wasu
muta ne na daban akan ka ba, a lukutta da dama mutanen mu ba su fiye yayata abun alkairin mu ba,sai
dai su yayata sharrinmu,kuma ma wai me muka aikata,shin son da muka nuna ma juna mu sa`bo ne ko-
ko mun ta`ba aikata wani Zunubi ne?"....
Muryarta na rawa ta dakatar da shi da cewa,"A'a aa ni ba haka na ke nufi ba,saboda ata dalilin sa har
yau iyayena ke fushi da ni,don haka bana son shi,idan harma zan cigaba da karatun to sai dai in sake
wani `bangaren in koma kamar health line haka".
"An gama ranki ya dad`e daga yau ki fara kallon kan ki a matsayin malamar lafiya,mafarkin ki zai cika
wanne `bangarrn ki ke so ki karanta?".
"Ammmm.....Nursing ina son in zama Malamar jinya".
"Daga yau ki fara counting d`in kan ki a cikin jerin Malaman jinyar da mu ke da su a cikin Garinnan, I
promise za ki karanci Nursing za ki Kira kan ki da wannan sunan da izinin Allah".
Cikin yanayin farin ciki ta rungume shi bakinta ya k`i rufuwa,sai faman bin shi da kyawawan Addu'o'i
take,"Kar ki damu responsibility na ne naga na wadata ki da duk wani abu da ki ka buk`ata,tunda har na
iya rabo ki da iyayen ki,bayan shi kuma da akwai abinda ki ke so".
Rau-rau tai da idanun jin ya ambaci iyayenta,", Me kuma ya faru ya Habibaty?",ya tambayeta a
k`agauce.
" Ban san me zan yi masu su yafe min ba,ina son su ina son in rik`a zuwa inda su ke amma ka na ganin
wancan time d`in da mu ka je Baba K`arami ya koroni ko cikin Gidan bai bari na shiga ba,na kasa iya
jurewa ko mantawa da wannan rana".
"Ki shirya mu tafi zan kai ki da kaina ni da kaina zan kai ki cikin Gidan ki ga duk wanda ki ke son gani",
bata san sanda murmushi ya ku`bce ma ta ba alamun taji dad`in abinda ya ce.
" A'a ka tafi wurin aikinka kawai ka makara tuntuni,indai ka bar ni sai in tafi ni kad`ai, idan ka dawo sai
ka biya ka d`auko ni".
"A'a ki dai bari in kai ki da kaina kamar hakan zai fi"," Kar ka damu yau in sha Allah ba abinda zai faru
ka taya ni da addu'a kasan fa yau kana da meeting kuma mai muhimmanci ka ga bai kamata in tsaida ka
ba".....
"Kema kina da muhimmanci mai tarin yawan gaske a gare ni,kin ga kenan bai kamata in bar ki kiyi
tafiya irin wannan ke kad`ai ba".
" Kar ka damu in sha Allah ba abinda zai faru da ni zan je in dawo lafiya, ka ga ni zan iya kai kaina can
Gidan na mu har ma in dawo amma kuma can Companyn ba abinda zai tafi yanda ku ka tsara in har ba
ka,ka ga kenan da buk`atar ka tafi can,kuma ka ga ni ban ma shirya ba balle har mu tafi,kayi tafiyar ka
kawai da zaran na Isa Gidan zan Kira ka in sanar ma ka",da haka dai ta samu har ta shawo kan shi ya
yarda tya tafi ya barta ita kuma ta shirya a tsana ke kafin ta tafi na su Gidan itama.
Cikin shiga ta kamala ta nufi Gidan na su,tun Isar ta k`ofar Gidan fuskarta ta yalwata da mad`aukakin
murmushi,a lokacin su Baba Malam suna majalisi
Da karad`i a muryarta ta shiga cikin Gidan tana kiran sunayen duk wanda ya zo mata a baki,"Ummie
Maryam, Umma Jamila, Umma Hafsat, ku fito ga ni na zo,ina Yarona Jaheed ya ke",Ba iya sunayen
wad`anda ta ambata ba har da su Lami Matar Alaranma Sama'ila da ta zo,hatta da sauran matan `ya`yan
Gidan sai da su ka fiffito,nan fa kowa ya fara murnar ganinta da yai ta dad`e anan tsakar Gida kafin
Ummie Maryam ta ja ta su shiga ciki.
"Yanzu ke Hibba idon ki kenan ace sai yanzu za ki waiwayo Gidannan tun tafiyar ku,kar ki so ki ga
yanda Baba Asabe ke yada maganganu akan rashin zuwan ki".
Rau-rau tai da idanu,hawaye na shirin zubo mata kafin ta ce,", Allah Ummien Jaheed ba laifin na ne
ba,har k`ofar Gidannan na zo amma Baba K`arami ya kora ni,badan na so ba ina ji ina gani na hak`ura na
koma badan na so ba",
Waige-waige Ummie Maryam ta fara yi alamun rashin gaskiya kafin ta fara kwakkwafarta da cewa," To
kar ki yarda ki sanar da Mama wannan labarin don ba zai mata dad`i ba kuma hankalin ta zai ta shi".
Da to ta amsa mata gami da k`ok`arin mai da hawayen da suke son zubowa daga idanun ta.
"Ki yi hak`uri kin ji,kar ki damu da wani abu da ya ke faruwa kin ji wata rana sai labari,ince dai kuna
zaune lafiya da mijin na ki,kuma ya na kula da ke yanda ya kamata?".
Sai da fuskar Hibba ta fad`ad`a kafin ta bata amsa da gyad`awa mata kai.
" Yauwa na ji dad`in jin hakan yanzu maza ki je gurin Mama nasan tana can ta tsumayin ki".
"To Ummie Maryam bari inje,amma ina Yarona ya ke ko yana makaranta ne ?".
"Yayah yau bai je makaranta ba yana can d`akina kwance ba lafiya".
" Ayya bari in je Inga Mama sai inzo in duba shi","To shikenan sai kin biyo".
Da sassarfa ta idasa shiga cikin d`akin Mahaifiyarta,a tsaye a bakin window ta hango ta da alama
jiranta ta ke kamar yanda Ummie Maryam ta ce.
Ambaton sunan ta tai cikin yanayin kewa da kuma rashin ganin ta.
"To me ye haka, daga zuwa kuma sai kuka,ko kin manta yanzu kin girma".
" Mamana na yi kewanki,ban ta`ba d`aukar irin wannan dogon lokacin ba tare da ke ba,Na yi kewanki
ki sosai".
"To ba gashi yanzu kin ganni ba,don haka kukan ya Isa haka,ya mai Gidan na ki yana nan lafiya dai
ko ?",
Sai da Hibba ta duk`ar da kanta k`asa alamun ta ji kunyar tambayar da akai mata kafin ta ba ta amsa da
cewa" Yana nan lafiya ya ce in gaishe ki anjima ma zai zo sai ya ku gaisa".
Haka Mama Hadiza ta cigaba da yi mata `yan tambayoyin,Wanda za su sa ta fahimci wanne irin zama
su ke gudanarwa ita da Mijin na ta,sun d`auki lokaci mai tsawo a tare kafin Hibban ta ce zata je ta gano
jikin Jaheed da aka ce ma ta ba shi da lafiya.
Sosai hankalin Hibba ya tashi ganin yanda jikin Jaheed yai tsamari,kamar tai ma shi kuka,rungume shi
tai sosai a jikinta sai faman lallashin da ban baki ta ke.
Shigowar Baba K`arami ne ya sa ta d`an dakata,cikin ladabi da kwantar da murya ta fara gaishe da
shi,amma ina ko da wasa bai amsa ba,tun kallon farko da tai ma shi ta sha jinin jikin ta Zuciyarta ta fara
kai kawo da tunanin me zai biyo baya.
"Ke waye ya baki izinin sake taka k`afar ki a cikin Gidannan ba na hane ki game da hakan ba?".
"Baba K`arami kayi hak`uri wallahi Allah ba zan iya rayuwa ba tare da ku ba,na tuba dan Allah ka yafe
ni"....
"Yi min shiru mara kunyar banza mara kunyar wofi,ki sani kin riga da Kin `bata rawar ki da tsalle a
wurina tun ba yanzu ba,abu na k`arshe da zan umarce ki da shi kija `yan k`afafuwanki ki bar Gidannan
tun kafin dare yai miki".
Har k`asa ta duk`a tana mai had`e hannayenta wuri guda ta na ba shi hak`uri tare da cewa,"Na rantsa
maka duk abinda ka ji muta ne na fad`a akan mu sharri ne babu wani abu na `batanci ko na rashin
dacewa da ya ta`ba shiga tsakanin mu,sharri ne kawai".
" Ba na son jin komi daga gare ki kawai ki tashi ki ba ni wuri",shine abinda ya ce da ita yana mai nuna
mata hanyar fita daga na shi `bangaren,ko motsin kirki kasawa Hibba tai,wai yau Yayanta da ya ji da ita
acikin kaf ahalin Gidan su yau shine ke kyararta shike korarta ya na fad`in