Author : Cwt Sumiey Category : African Stories & Novels
two love birds who are so different from each other )
STORY & WRITTEN BY :
(*Cwt~Sumiey*)
Marubuciyar littafin
MENE NE ABIN YI ?
KARAGAR MULKI
And now.....*JADEEDAH*
*YOTA*
BOOK 1
PAGE 16❤
After some Months
Zaune take ta rafka tagumi da hannayenta duka biyu,idanunta na kan bed d`in da Abbakar ke kwance
amma a zahiri hankali da tunanin ta ba a nan suke ba,hakan ya sa ko shigowar Mama Hadiza ba ta ji
ba,har sai da ta kai ga dafa kafad`unta sannan tai firgigit ta farka tun kafin tace komi hawaye suka fara
zubowa a saman idonta.
"Hibba me kike yi haka kar dai kice min har yanzu baki d`auki k`addarar da Ubangiji Allah ya saukar
miki ba".
" Mama ba haka bane ba Zuciyata har yanzu da k`una a cikinta kuma na kasa yarda da Cewar wai
Jadeeda ta rasu ta barni,da kaina fa na mik`a ma Cecelia ita ,wannan Gloria ta amsheta,kuma na tuna
komi ko da Accident d`in ya faru banga Gloria ko gawarta ba kenan hakan na nufin duk inda Gloria ta ke
`yata Jadeeda na tare da ita".
Sai da Mama Hadiza ta sauke a jiyar Zuciya sannan ta ce da ita,"Ki yarda da Allah ki d`auki k`addarar da
ta same ki,ki sani har jana'izar Jadeeda an gabatar to me yai saura da ya wuce ki yarda da Allahn ki kar`bi
abinda ya saukar a kan ki,wanda ya baki `yarnan fa yafi ki sonta shine fa ya amsheta to don me za ki tada
hankalin ki,ya kamata ki fara k`ok`arin sake sabuwar rayuwa domin ki samu cigaba a cikin rayuwar ki,ba
wai ki nemi sake jefa kan ki cikin wata sabuwar matsalar ki kalli fa halin da Mijin ki yake yana buk`atar
taimakon ki,idan ki ka cigaba da tafiya a haka ba iya rayuwar ki kad`ai ba harda ta sa rayuwar za ki
lalata".
Tsuru Hibba tai tana mai mai-maita maganganun Mama Hadiza a cikin ranta,"Eh da gaske na ke miki ki
tashi tsaye ki tallafi rayuwar ki da ta Mijin ki,kuma ki dage da addu'a ina mai tabbatar miki indai Jadeeda
na da rai kuma tana taka doran k`asa sai wata rana ta nemeki ta dawo rayuwa da ke",Mama Hadiza na
kaiwa nan ta tashi ta mik`e da niyar barin d`akin,shigowar Ummie Maryam ce ta d`an dakatar da ita.
"Mama ashe ki na ciki,na shiga sashen ki na iske ba kowa"," Eh inanan na zo na iske ta tana yin sana'ar
da ta saba,dan Allah ki rik`a gaya mata gaskiya wala Allah ko ma samu ta dawo cikin hankalin ta ta san
abinda ya kamata ta aikata a cikin wannan lamarin "," To Mama amma wallahi inayin iyakar iyawata
amma har yanzu ba nasara,hatta da Jaheed ya shiga cikin matsanananciyar damuwa saboda yawan
ganinta a cikin irin wannan halin ".
Sai da Mama Hadiza ta mai da kallonta kan Hibba kafin ta ce da ita"To ai shikenan tunda haka ki ka
za`ba ma kan ki",ta na kaiwa nan ta bar masu d`akin.
Wuri Ummie Maryam ta samu ta zauna kusa da ita tana mai d`ora hannunta akan ta ta ce," Kin gani
irin wannan abun nake guje maki tun da farko,Na sani kina cikin damuwa da kuma tashin hankali amma
ki sani ba iyake abun ya shafa ba,duk wani na kusa da ke ko kuma mai k`aunar ki yana jin zafi rad`ad`i da
kuma damuwa kamar yanda ki ke ji,kar ma Mama domin itama d`in uwace ta kan fi kowa jin zafin abu ko
murna idan ya samu d`anta,ina mai tabbatar maki ko ke ba lalle ki kaita shiga cikin tashin hankali da
damuwa ba,ki kalli yanda ta rame ta fita hayyacinta ko barcin kirki fa ba ta iya samu,ga yawan cuttuka da
ke cikin samunta kuma hakan yasamo asaline da sanya damuwar ki a cikin ranta,ya kamata ki ji
tsusayinta,ki rage wannan damuwar,wai ma meye zai sa ba za ki saurari Maganar da ta ke fad`a mi ki ko
sau d`aya ne ba,ki tsamota daga cikin yanayin da take a kai , ko hakan kad`ai ka iya sawa Allah ya
sassauta ko ya yaye maki halin bak`in cikin da ki ke a ciki".
Sai da Hibba ta sharce hawayen da ke fitowa daga cikin idanunta kafin tace,"Shikenan Ummie Maryam
in sha Allahu daga yau ba za ku sake ganina a cikin irin wannan yanayin ba,zan dan ne duk abinda nake ji
in barshi a iya cikin Zuciyata har zuwa sanda Allah zai kar`bi rayuwata in dai har kan ne zai sa ku cikin
farin ciki to zan aikata hakan duk da dai"......
Ta kasa iya k`arasa zancen nata, ita kanta Ummie Maryam hawaye ne ke zuba daga cikin nata idanun
har ta bud`e baki zata sake cewa da ita wani abu ta fasa sakamakon ganin da take in har zasu cigaba da
yin wannan maganar to ba za su ta`ba daina zubar da hawaye ba ko kuma su samu damar kawo
k`arshenta ba,don haka sai ta za`bi yin shirin wala Allah zai zama mafi alkairi a gare su.
"Ammm Hibba kina da bak`i fa", Ummie Maryam ta fad`a ta na mai kauda idanunta gefe.
Cikin sabon yanayin da ya zame ma Hibba jiki ta tambayeta," Bak`i kuma ,a wannan lokacin su
waye?","Daga Companyn su Abbakar ne,sun sake zuwa ne don su duba jikin shi ","To ba matsala ki sa a
shigo da su mana", da to Ummie Maryam ta amsa mata tana mai juyawa har ta kusa fita ta waigo tace
da ita," Ki d`an gyara fuskar ta ki kafin su shigo".
Sai da Ummie Maryam ta sanar da Mama Hadiza zuwan na su,domin ta zo su gaisa ta had`a da saka
Jaheed ya je ya sarna da su Baba Malam sannan ta sa a ka shigo da su,bayan sun shigo an gama
gaggaisawa sun k`ara yi masu ya mai jiki da fatan Allah ya tashi kafad`unsa,sannan Acountern
Companyn Abbas ya ce mu su,"Allah sarki Manager mutumin kirki ne dukkanin mu nan mun shaida
haka,a d`an zaman da mu ka yi da shi tun yana matsayin Crista ba a ta`ba samun sa da wani yana
musayan miyau da shi balle har ta kai su ga yin fad`a ba,ga gaskiya ga kuma rik`on amana gaskiya ba mu
da wani abun fad`a akan shi in har ba yabo da jinjina zamu yi gare shi ba,ba kuma wai a gare mu kad`ai
ba hatta manya da kuma k`ananun ma'aikata ,suna ta kuka gami da jajantawa akan abinda ya yafaru da
shi ne ".
" Tabbas Acounter Maganar ka gaskiya ne wanda hakan ne yasa shi asalin mamallakin Companyn ya
aiko da wad`annan mutanen wasu likitoci ne guda biyu daga can Abuja suke kawai don su dubasa su
bashi kulawar da ta kamata in ta kama a kai ga a fidda shi zuwa k`asar waje ne sai a fidda shi".
"Kai Bayin Allah, Allah ya saka maku da alkairi, mun gode mun gode,ku Isar da sak`on godiyar mu ga shi
Ogan na ku,ni ban ma San da wanne baki ya kamata in nuna muku jin dad`in wannan abun da kuka zo
mana da shi ba,Allah ne kad`ai zai iya biyan ku,ya saka maki da alkairi yai maku tukwuici da Gidan
Aljannah", Cewar Baba K`arami Wanda hatta a muryasa zaka gane yana cikin farin cikin game da abinda
ya saurara.
"Kar ka damu wannan duk can-cantar da shi Abbakar d`in yayi ne,ba sai ka yi wani Godiya ba, suna son
a samu wani yayi masu cikakakken bayanin abinda ya ke faruwa da shi,da kuma irin matakin da ya ke
akai a yanzu".
Nasir ne yai masu cikakakken bayanin asalin da yanda abun ya faru," Ya samu buguwa ne akan shi
sakamakon accident d`in da ya gamu da shi Wanda a turance muna kiran wannan cutar da suna
Neurological disorder the Conditions affecting the brain, spinal cord, and nervous system (e.g., epilepsy,
multiple sclerosis).
Also Neuro developmental disorder Conditions affecting brain development (such as ADHD, autism
spectrum disorder),a ta haka in ka kalle shi zaka iya cewa barci yake ba dan wannan oxygen d`in da aka
sanya mashi ba ,wannan shine matsalar da take damun shi".
"Ammmmm but amma in dai condition d`insa a wannan matakin ya ke bai kamata ace kun na jinyarsa
a cikin Gida ba,zai fi samun Good treatment da samun ingantattun magungu ba da kuma nagartattun
kayan aiki ya akai haka Doctor Nasir ?".d`aya daga cikin Doctors d`in ya tambaya.
"Eh haka ne nasan da hakan amma kasan irin wannan problem d`in yana da matuk`ar hatsari da don
bin taka tsan-tsan gami da lura dalilin ba d`aya ne da ya sa Na dawo da shi,da zaran wurin da yake,yanzu
zai fara shebaring yana shirin fad`owa,yanzu da ace zamu kaure da surutu a cikin wannan d`akin duk da
kasancewar sa baya iya ko motsa d`an yatsan shi to da haka ce zata kasance".
" Okay na fahimci inda matsalar take yanzu za muyi mashi `yan wasu gwaje-gwaje da zamu je muyi
amfanin da su,Amma na so ace zamu iya admitting nasa a Hospital yanda zai samu kulawa da shi
24/7,amma hakan ma ba damuwa zan turo Nurses guda biyu da zasu rik`a taimakawa Madam wajen
kula da shi, har zuwa sanda zamu kammala namu binciken".
Godiya Sosai Mama Hadiza,Baba K`arami, Nasir da kuna Ummie Maryam suka rink`a yi ba, don ita
Hibba ba bakin magana sai faman zubar da hawayen farin ciki ta ke, a tare su duka suka tafi raka su
bayan sun gama duk abinda za suyi har sun kusa fita daga Gidan Abbas Acounter ya dakata yana nai
cewa da su yana zuwa yayi mantuwa,"Madam zan iya shigowa ?",Yace da Hibba bayan yayi sallama ta
amsa.
Tsaye take akan Abbakar tana mai motsa mishi wasu daga cikin sashen jikin saboda gudun kar su mutu
su daina amfanin,"Am kana neman wani abu ne ko kuwa ka yi mantuwa ne ?",Hibba ta ce da shi.
"Madam ba mantuwar da nayi,Na zo ne na Isar da sak`on da aka bayar in baki tun kafin yanzu".
" Sak`o kuma wanne irin sak`o ne wannan haka ?",Hibba ta tambaye shi,bai bata amsa ba sai zura
hannunsa yai a cikin aljihunsa ya fiddo wani Embolof daga aljihunsa ya mik`a mata yana mai
cewa,"Wannan shine sak`on da yalla`bai ya bani akan sai bayan ya dawo bikin k`anwar shi,in ya tafi
seminar d`in da yake shirin tafiya sai in kawo maki,to kafin hakan ta faru wannan tsautsayin ya fad`a
akan sa,shine na yanke shawarar in kawo maki ko da abun ciki ba zai amfani ba,ni dai na sauke
alk`awarin da na d`auka ".
Amsa Hibba tai idanuwanta na fara k`ok`arin zubda hawaye, ta amsa tana mai yi mashi Godiya.
Jikin Hibba na rawa ta fara bud`e Embolof d`in abinda ta gani ne yasa numfashi da kuma jikinta
tsayawa cak,sai da ta d`auki wani dogon lokaci kafin ta dawo cikin hayyacinta,hannunsa guda ta kama ta
rik`e kam tana mai d`ora kanta a saman gadon da yake kwance tare da fashewa da kuka cikin
mad`aukakiyar murya tana mai cewa "Me idanuwana ke gani,wacce irin cutarwa ce na aikata ma
kaina,Na cutar da kai na zama silar salwantar mana da `ya d`aya tilo da muke da ita kai kuma ga ka
kwance cikin halin mutuwa da rayuwa,duk don saboda tsananin fushi da son kaina da ban hassala ka ba
da idanuwanka basu rufe daga ganin motar da ta tunkarowa mu ba,da yanzu ina tare da kai da kuma
ƴata ɗaya tilo da na ke da itanikam wacce irin Mata na zama,wacce irin uwa ce ni mai salwantar ta ran
`yarta da kuma ta Mijin ta,bayan kai ka kasance mutum mafi adalci kyautatawa a gare ni,kullum buri da
fatan ka ka ga na zama abar kwatance,Na cika buri da duk wani fata da nake da shi,da wacce irin fuska
zan kalle ka aduk ranar da ka warke ka tambaye ni ina Jadeeda ta ke, da wanne baki zan iya gode maka
irin tarin alkairan da ka yi min a iya d`an zaman da muka yi tare da kai?"......
Da sauri Ummie Maryam ya k`arasa iso kusa da ita tana mai tambayar," Lafiya me kuma ya k`ara
faruwa ?".kasa iya cewa komi tai sai nuna mata Peppers guda biyu da ke zube a k`asa ,d`auka tayi ta fara
dubawa,d`aya admission na shiga jami'a ne a matsayin d`alibar jinya,sai na biyun kuma dogon bayanin
ne akan yanda yake sonta da kuma murnar samun admission da yake taya ta,daga k`arshe ya ke cema ta
ta kula da kanta da kuma Jadeeda har zuwa ran da zai dawo.
"Mene ne abin tashin hankali a cikin wannan lamarin naga kamar takardar cigaba da karatu a
university ce waye ya samo ta?"," Shine ya samo min tun kafin faruwar wannan a'lamarin ya bari ne yai
surprised d`ina sai kuma hakan ta faru ".
Sai da Ummie Maryam ta samu guri ta zauna tana fuskantar Hibba sosai da sosai kana ta fara cewa da
ita,"Hibba ki natsu wannan babban dama ce kika samu, bai kamata ki yi wasa da ita ba,a da idan kin
d`auki wannan karatun a matsayin buri ko fatan ki,to a yanzu ki canza ki d`auka Cewar za ki yi karatu dan
Mijin ki,za ki rayu dan shi ki yi karatu dan shi,ki manta da komi da ya faru,ki farfad`o da rayuwar ki da
tashi a lokaci guda,kar ki wasa da wannan damar".
Shiru Hibba tayi na wani lokaci kafin ta bud`e baki tace,"Ummie na yi miki alk`awari zan yi amfani da
wannan damar da kuma shawarar da ki ka bani,zan yi karatu ko dan Mijina,zan zama Malamar jinya ko
dan shi ya cigaba da rayuwa ya samu kulawa ta, zan yi iya yi na don ganin haka ta faru".
Sosai Ummie Maryam ta ji dad`in wannan lafazin na Hibba har sai da ta kai ga ta rungumeta.
Wannan kenan
After 5yrs
A guje ta fito tana mai kwalama Ummie Maryam kira ta na mai d`oki da murna,"Mun samu damar
ganin Likitan kwakwalwa a can U.s.a,Ummie muna cikin alkairan Allah ".
Cikin zumud`i Ummie Maryam ta ce," Kai Alhmdllh Masha Allah gaskiya muna cikin alkairi yanzu bayan
Schoolarship d`in da ki ka samu ,kuma sai ga wannan babban alkairin ya zo ?".
"Ke dai bari Ummie ga Mama can ta tafi ta sanar da Baba Malam ,nasan shima zai yi farin ciki, har
Baba K`arami da kuma Yayah Nasir na Kira a waya na sanar da su, yanzu haka na san Baba K`arami ya
kusa isowa domi mu fara tsara yarda zamu yi tafiyar,kin San fa tare da Yarona zamu tafi", ta kai zancen
tana mai fad`ad`a fuskarta da murmushi.
" To ai dama nasan da haka Jaheed ai d`anki ne in ki ka tafi ki ka bar ni da shi, ai ba zan iya ji da rigimar
shi ba,dan haka addu'a ce tsakani na da ku,yanda kuka sanya mashi rai a wannan tafiyar ai in baku tafi da
shi ba ba zaman Lafiya kaf Gidannan don haka Allah ya ba Abbakar lafiya ya sa wannan shine k`arshe
wahalarsa,ku kuma Allah ya sa albarka a cikin karatun da za ku yi".
Haka dai suka cigaba da murnar su har sanda su,Baba Malam, Baba K`arami da kuma Yayah Nasir su ka
zo,suka cigaba da tsara yanda komi zai tafi game da da tafiyar su Hibba, lokacin da mutanen Gidan suka
samu labarin wasu sun yi murna wasu kuma a fili suka rik`a bayyanar da hassadar su a fili,amma a cikin
su ba wanda ya kula su,sai ma k`ara k`aimi da suka yi game da shirin su.
*JADEEDAH*
STORY & WRITTEN BY :
(*Cwt~Sumiey*)
Marubuciyar littafin
MENE NE ABIN YI ?
KARAGAR MULKI
And now.....*JADEEDAH*
BOOK 1
*YOTA*
PAGE 17❤
Gudu ta ke tsalawa na fitar shari'a akan saman titin Tafawa `Balewa Area 8 ,yanayin yanda take tsala
gudun kad`ai ya Isa ya tabbatar maka da ba a cikin natsuwarta take ba,gab da zata hau titin da zai sadata
har zuwa babban gate d`in Garki Hospital Abuja ,ta buga ma motar dake gabanta,runtse idanunta kam
tai tana ambaton suna Jesus da neman agajin gaggawa a wurinsa.
K`arfin bugun ne yasa motar da ta daka kaucewa daga Saman kan titin har sai da ta kai ga bugar wata
bishiya dake gefan su,kafin ta tsaya cak kamar an rik`eta cikin gaggawa da hanzari Dr. Imam Muh'd
Jaheed shi da Driver d`in da ya d`auko shi suka fito daga cikin Motar da har ta fara fidda hayak`i.
Kasa cikakakken motsin kirki Jedeeda ta yi har na wani d`an lokaci,ganin yanda Driver d`in ya nufo ta a
fusace ya sa tai hanzarin fitowa daga cikin tata motar tana mai fuskantar shi da jiran me zai fara fitowa
daga bakin sa.
"Are you out of your sense, ta ya za ki rik`a yin wannan mahaukacin gudun a saman titi,sai ka ce dan ke
kad`ai aka yi titin ko kuma na Gidan ku ne titin?".Saurayin Driven ya ce da ita cikin tsawa da d`aga murya.
"Hey...hey hold on how dare you are da zaka rik`a yi min magana cikin tsawa,Call the mechanic I will
pay the bill".....," Me ne? Maganar kud`I ki ke a irin wannan k`adamin magana fa ake ta tsakanin mutuwa
da rayuwa, wace ce ke me ki ke tak`ama da shi da har ki ke wannan kurin ?".
"Hmmmmmm bana da Lokacin `batawa da kai ina cikin uziri just name the price or you can call your
mechanic I will pay the bill,ka fahimce ni?, ina cikin wani uziri mai muhimmancin gaske".duk wannan
abun da ke faruwaDr. Imam Jaheed ya na gefe nad`e da hannayensa a k`irji yana kallon abinda yake
faruwa a tsakanin su.
"Okay tunda haka ki ka ce let me call the Police ko ba kome za su `bata maki lokacin da ki ke ikirarin
baki son `batawa kin ga inya so sai ki biya bill ta hannunsa".
" Oh Jesus Christ ",Jedeeda ta fad`a can k`asa tana mai dafe kanta da hannunta na dama," Ka ga zan
baka kud`i iya adadin da kake so but don't waste my time, so please accept the money instead of my
apology ".
Sakin baki Drivern yayi yana kallonta da tunanin ina wannan rashin kunyar ta ta zata kai ta,ji yai ba zai
iya kyaleta ba har sai ya kai ga yin reporting d`in ta ko ba komi zai samu sauk`in rashin kunyar da ta yi
masa.
Ganin da gaske kiran Police d`in zai yi yasa ta saurin dakatar da shi ta hanyar cewa," Ammm......I'm
sorry kar ka kira su cause I can not stay,this's my my card you can call me anytime in ya so sai mu kai
k`arshen batun ",ta