Author : Cwt Sumiey Category : African Stories & Novels
ƙarfi. Bai iya ce mata komai ba sai dai numfashi ya dinga ja kamar
mai shirin mutuwa.
“Ina fata Allah ya gafarta maka,” ta ce cikin hawayen da suke ƙona mata fuska.
“Ka ƙaryata tsarkin addininmu. Ka ƙaryata martabar ɗan’uwa. Ka ƙaryata ni.”
Ta juyo da sauri. Bata waiwaya ba. Bata saurari komai ba. Ta bar Edwin a ƙasa, cikin ruɗani da sirrin da
ya shanye zuciyarsa raunana gami da son tarwatsewa a lokacin.
√√√√√√√√√√√√√√√
"Safina kin yada ni ba ki da kirki ko kaɗan","Hmmmmm Zeenat kenan to ba dole in ɗaga ma ki ƙafa ba
kin san ni kin san hali na,in dai maganar gaskiya ta zo dole in faɗa maki ke kuma abinda ki kai hannun
riga da shi kenan".
"Na yi tunanin taren mu ta wuce mu bar wani abu ya shiga cikinta yai tasiri har ya kai ga shiga tsakanin
mu,ki tuna fa tare mu kai yarinta,mu kai wasan ƙasa a tare mu ka yi karatu atare impact komi namu a
tare mu ka yi sa,amma yanzu sai ki kwashe wani tsawon lokaci ba ki ziyarci inda na ke ba,in kuma ni na
zo sai ki fara shamin ƙamshi,na kasa jure hakan abun ya na min zafi,ga shi kuma ban san dalilin faruwar
haka ba".
"Ba na son mu tsawaita zancennan mu bar shi kawai Zeenat","A'a Safina ba zan yi shiru a har sai mun
kawo ƙarshen wannan lamarin,ki sanar dani abinda na yi miki ko kuma wani ne ya ke son shiga tsakanin
mu ban sani ba ?".
"A kan me wani zai shiga tsakanina dake,to idan wannan tunanin ki ke,to ki sauya in ma da akwai
wanda ya shiga tsakanin tarayyar mu to ke ce da kan ki,haba dan Allah Zeenat mai ki ke so,mai ki ka
nema ki ka rasa,da har ki ka maida rayuwar ki haka,kefa matar Aure ce amma kalli shigar da ke jikin ki,ko
kunya ba kya ji ki kazo gidan Surukan ki da irin wannan shigar".
"Ai Safina fuska za ki cimin kan na zo wurin ki domin mu sulhunta tsakanin mu,mu gyara ɓarakar da
ta shiga tsakani tarayyar da mu ka gina tun yarinta,to wallahi na gargaɗe ki domin kin san tun da can
bana ɗaukar raini balle yanzu da girmana har da igiyar Aure a kaina,kin san ko a cikin ƙawayen mu na fi
ƙarfin raini wallahi ."
"A da kenan ban da yanzu ko?,Ni ƴar'uwar ki ce ta haƙiƙa,bawai ina maki wannan zancen da sigar cin
fuskar ba, a'a wallahi har cikin raina ina jin zafin yanda ki ka sauya ki ka mai da kan ki tamkar wata
illitrate,haba Zeenat wallahi kin sauya ina mamaki gami da jin takaicin ssuyawar ki,na kan tuna yanda mu
ka yi rayuwa dake ,komi na ki gwanin ban sha'awa ,kina ɗaya daga cikin ko in ce mace ta farko mai
capacity acikin class mate ɗin mu,amma yanzu du babu,sabo duk kin zubar da shi,shin yaushe rabon da
ki ga ɗaya daga cikin ƴan Click ɗin mu takawo ma ki ziyara,duk sun bari,domin duk wacce ta zo ta yanda
ki ka banzatar da rayuwar ki sai ta ga ta wuce da ajinki sai ta bar ki,a duk sanda wani abu ya faru mu ka yi
taro ko muka haɗu da wasu daga cikin sai an yi hirar ki gami da mamakin sauyawar ki,ina jin zafin haka
domin tamkar ni ake suka in aka soke ki,amma ke kullum sake tsiro da sabbin halaye ki ke,ke ce rashin
tsafta,haukan kishi kin biye ma Baba Asabe to ki sani son tarwatsa maki rayuwar Aure ta ke."
"Safina duk kin san wannan ce-ce ku ce ɗin da ya ke faruwa amma ba ki taɓa zuwa kin sanar da ni
ba,kenan gulmata ma kuka koma yi".
"Na sha yunƙurin hakan amma duk sanda na zo da na fara yi maki maganar sai ki fusata ,ki nuna ma ba
kya buƙatar jin labarin,kuma maganar gaskiya ba gulmar ki ake ba,kin aikata abinda za'a yi magana akan
shi ne,Ni kaina ina baƙin ciki in zo gidan ki in ga yanda ki ke tafiyar da rayuwar Gidan ki,kamar ba Auren
soyayya ku ka yi tsakanin ki da Yah Imam baamma komi a hauka ce cikin fitina da tashin hankali,duk da
na san Auren ku na haɗi ne amma kafin Auren ai kun yi soyayya mai zai sa ba za ki maida wannan
soyayyar ta zama linzamin gina rayuwar Gidan ki,ba ki ƙare kullum cikin baƙin ciki da tashin hankali."
Ta ɗora da cewa,"Wallahi Zeenat ki gode ma Allah,wasu matan Mijin ma su ke nema amma ba su samu
ba,ke kuma Allah ya baki kina wulaƙantawa,ki je ki cigaba watarana in kika zubar da garin ki kya koma
cizon yatsa daga baya
Shiru Ummu Nurain tai kamar Safina ta san ta taɓa mata inda ya fi sosa ma zuciya ta ciga da cewa,"Da
za ki ɗauki shawara da kin gyara kuskuren da ki ka aikata na tsawon shekaru,har yanzu lokaci bai ƙurar
ma ki ba,za ki iya mai faɗa soyayyar ki a cikin Zuciyar Yah Imam gama dana ba daina son ki yai ba halayen
da ki ka tsiro ne ba ya so,kin ganni ko ba aure ne da Ni ba amma akwai abubuwa da dama da ki ke aikata
su wanda ko karan hauka ya biyo ni ba zan iya aikata su ba".
"Ba zaki gane ba Safina domin bana tunani haka za ta yiwu, Gimbiya Ayush ta tsare ko ina ,domin Abu
Nurain ko kallon arziƙiba ya shiga tsakaninmu saboda ita ta shiga ta raba mu."
"Ba wani shiga da tai ta raba ku,in ma ta shiga ke ce ki ka bata fuska,ta hanyar watsar da kan ki da ki ka
yi,eh mana watsar da kan ki da ki ka yi mana,domin duk kin watsar da wasu responsibilities na ki na
matsayin ki na matar Aure kuma Uwar Gida mai Capacity,ke kin zubar da na ki Capacityn ita kuma ta
kwashe,ki farka daga nannauyan barci daki ke kwada ki gani in ba ki kwato Capacity ɗin ki ba,wai wace
ce ma Gimbiya Ayush in ba matar cushe ba,don haka ki manta da ita anan ne za ki dawo da asalin ko ke
wace ce,zamantakewar ki ba ya nufin ki banzatar da duk wasu buƙatu ko ra'ayi na Mijin ki ba."haka
Safina ta cigaba da faɗawa Zeenat gaskiya da kuma hanyoyin da za ta bi don ta magance matsalolin da ta
ke fuskanta a Gidanta,har zuwa sanda yamma ta yi.
"Au ashe kana tafe na sha yau ba zaka shigo Gidan ba", Ummiey Maryam ta ce da shi tana mai gyara
zaman ta,"Ina tafe Ummiey yau tun safe muna Companyn Auduga ne yau zamu fitar da kaya shine fa sai
yanzu na shigo,na taho ne a hanya na haɗu da Nurain sun ta so Islamiyya".
"Tooh ka Nurain maza je ka sashen Momy ka kira Ummanka ta na can".
Da ɗan sauri Jaheed kuma cike da mamaki ya waigo yana son yi tambaya ,shi kuwa Nurain fuskarsa
ɗauke da murmushi ya nufi inda aka aike shi,"Ummiey...Ummu Nurain ta zo nan ne,Ni a tunani na na
baro ta Gida kuma ba ta sanar da ni zata zo nan ba?","Uhmmmm ta zo tananan",ta ba shi amsa a daƙile.
Shigowar Momy Hibba da kuma Ummu Nurain ɗin ya hana shi sake cewa komi sai daman bin ta da ido
da yake,a kallo ɗaya da ya yi mata yasan ba alkairi ne ya kawo ta ba da walakin goro a mita.
Momy Hibba ce ta umarce ta da ta sake maimata duk abinda ta ce da fari,haka ta jero su,sai da
wannan karon muryarta na rawa,ta kuma kasa yarda ta hada ido da wani a cikin su,sai a yanzu take dana
sanin zuwan ta gidan gabaɗaya.
"Mai ka ke son ka zama ne Muh'd,kana da da ilimi fa,shin baka san haramcin abinda ka ke aikatawa
ba,me ye amfanin nuna banbanci ko fifiko tsakanin matan ka",sosai Ummiey Maryam ta ka sa ka shi a
gaba ta inda take shiga ba tanan ta ke fita ba,shi ƙarshe ma rasa laifin me ya yi da har aka gurfanar da shi
a wannan kotun,ga shi ko kusa ko da wasa Ummiey ta hana shi damar da zai yi magana ko ya kare kan
shi, dole ba dan ya so ba ya bar ta ta yi iya yin ta,Duk abinda ake Momy Hibba ba tace komi ba sai bin su
da Idanu ta ke a haka ta fahimci duk zancen da Ummu Nurain ta zo da shi ƙarya ne ba abinda ya faru a
ciki ,ƙarshe Momy Hibba ta yanke hukuncin su ta fi da Nurain in ya so kullum a riƙa tura Driver ya riƙa
ɗauko shi,motsin kirki kasa yi yai,zuciyar shi cike da ƙuna amma ba halin ya bayyanar da hakan ya rasa
me ye a cikin kan Zeenat da ta ke aikata irin wannan aiyuka da duk mai hankali da tunani ba zai aikata
ba,haka ya kwashe su ya su ka nufi Gida,jikin Zeenat kam a sanya ye ko haɗa ido da shi kasawa ta yi..
PAGE 40. ❤
"Wallahi Nurain ka matsa ka bani wuri ,tun kafin in bud`e idanuna in sa ka a cikin su,a yi Yaro sai
fitinanniyar rigama d`an barcin safen ma ba zaka barni in yi ba haba dan Allah....", sautin muryar da ta ji
ne ya sa ta tashi a firgice ba tare da ta shirya ma hakan ba,ta sake fad`awa cikin kogin tunani a lokacin da
tai Arba' da shi zaune a kusa da ita,sake murza idanuwanta ta yi ,ilai kuwa shine zaune a gabanta ba gizo
Zuciyarta ta ke mata ba," Good Morning Ummu,yau Abbunah yai min wanka da wuri kuma ya had`a min
breakfast na ci na k`oshi, ke ma ga naki nan mun taho maki da shi",Nurain ya kai k`arshen zancen ya na
mai kinkimo farantin da breakfast d`in ya ke akai da sauri Imam Jaheed ya tarbo shi don gudun kar ya
zubar,shi ko sai faman washe baki ya ke.
Su duka biyun ta bi da kallo ji ta ke kamar ba wa'inda ta sani kuma ta saba rayuwa da su ba ne a
gabanta,sanya suke su duka da fararan kaya masu taushi,sai raba idanu take a tsakanin su kar ma Nurain
da ta ke ganin fatarsa har wani glowing ta ke,tamkar an musanya ma ta shi,shar da su kamar ba su ba,ko
kad`an bata ga alamar fushi ko damuwar abinda ta aikata ma shi a daren jiya a fuskarsa.
Hankalin ta ya koma akan k`amshin abincin da ya aje mata nan da nan ta ji cikin ta ya fara kuwwa ba
tare da ta jira komi ba ta duma hannu ta fara cin duk abinda ya tare mata gaba,ba ta tsaya ba har sai da
tashi komi da ke jikin farantin, sai a lokacin ta mai da kallonta kan Jaheed da ya zaro idanunsa waje ya na
binta da kallo.
"Kin cinye komi ba tare da Kin tuna Cewar na ci ko ban ci ba, ga shi ko hannu da baki ba wanda ki
wanke ".
Wata irin kunya ce from no way ta ji ta lullu`beta,kafin ta san me ya kamata ta yi ,saurin muryarsa ya
sake ratsa kunnuwanta da kuma gangar jikinta," Yau a Gidannan gasar wanda yafi kowa kyau za ai,ki
tashi ga ruwa can na had`a miki a bathroom,ni da Nurain mun shirya ke mu ke jira",jikinta ta bi da kallo
sai dai tun kafin aje ko ina tai saurin kauda kanta,zani ne d`aurin k`irjin,gashin kanta kuwa ba a ganin
tsagar kitsonta duk ya bi ya susuce.
"Tashi mana kar lokaci ya k`ure mana da", ya kai zancen tana mai sauke tiren da ta ci abinci tare da tai
maka mata don ta mik`e,jikinta duk ya mutu har wani sanyi ta ke jin ya na ratsata ba tare da ta san daga
ina ya ke fitowa ba, bai barta ba har sai da ya tabbatar da ta shiga wankan kafin ya koma wajen Nurain
ya bashi kayan wasa yanda za su d`auke masa hankali.
Tun shigar ta bayin kasa ta`buka komi tai Zuciyarta sai faman kai kawo ta ke gami da sak`a mata wasi-
wasi kala da kala," Duk da kaancewarsa mutum mara rik`o da saurin fushi,Amma abun da ta aikata masa
jiya ya yi wuri a ce har ya manta abinda ya faru a tsakanin su jiya da daddare,me hakan ya ke
nufi,wannan sabuwar kulawar kuma ta me ye,Allah ya sa ba wani tarkon ba ne ya ke yunk`urin d`ana
mata ba", da sauri ta kawar da wannan tunanin tare da cewa,"Aa shi ba haka ya ke ba mutum ne mai
saurin yafiya,sannan baya rama cuta da cuta,eh tabbas haka ne yana yi min wannan kyautatawar duk
dan in gane kuskurena da na aikata",ta kai zancen ta na mai tabbatar ma kan ta game da abin da
Zuciyarta ta ke kitsamata,tun shigarta ba abinda ta aikata ta dai d`auki sponch da soap ta rik`e a
hannunta daga nan fa ta tafi duniyar tunanin.
Baya taja a d`an tsorace sakamakon d`agowa da tai ta ganshi tsaye a gabanta ya yi folding d`in
hannayensa ya zuba mata kaifafan idanunsa ma su sanya mata mutuwar jiki,takowa yai har inda ta ke ya
amshi sponch da soap d`in da ke rik`e a hannunta ba tare da ya ce da ita komi ba,hannu ya sa ya sa`bule
zanin jikinta, da kan shi ya wanke ta tsab,tun tana kauce-kauce har ta gaji ta daina,har shaving cream sai
da yai mata amfani da shi,kitson kanta da bai fi guda shidda ba ya tsefe su ya sa Shampoo mai k`amshi ya
wanke kan,ita kanta jin kanta ta rik`a yi tamkar a wata sabuwar duniyar ko kuma wacce aka sabuntawa
gangar jikinta.
Bayan ya shafe ta da lotion, ya ciro mata wata pich d`in half da da k`adan ta wuce gwuiwarta,kanta
kuma ya sanya mata Vanderner wacce ta bayyanar da gashin kanta daga baya,daga nan kuma yai mata
`barin Brut perfums mai dad`in k`amshi ,cikin jikinta kuwa ya fito rad`au sai ma ya k`ara fitar da kyawun
kwalliyar ta ta, ita kanta sake baki tayi ta na kallon kanta.
"Anya kuwa za ai wannan gasar kuwa,tun yanzu na fara karaya", shine furcin da ya fito daga bakin sa
tun shigowarsa.
Rasa me ma za ta ce da shi tai sai binsa da tarin mamakin da yake bata tun safiyar yau,ba ma a
Maganar tarin kunyar da ta kwasa,rabon ta da irinta tun farkon Auren su.
" Shikenan an gama mataki na farko na gasa,saura na biyu",Zanin gadon da ke kan gadon ya yaye
Wanda yai cud`u-cud`u da daud`a,har ma ba a iya banbance asalin colour d`in sa,sannan ya fara shifid`a
wani,ganin hakan da tayi ne ya sa tai saurin kama ma shi suka shifid`a a tare,nan fa suka zage gyaran
Gidan kowanne lungu da sak`o na Gidan ,wasu kayan ma in ya fitto da su sai ta ji inama k`asa za ta tsage
ta shige cikinta ,hatta da Kitchen, Room d`in Nurain duk sai da suka bi suka gyara shi tsab,duk wani un
use da kuma wanda ba zai wanku ko ya gyarubu sai da suka fitar da shi,tamkar sun sabunta komi,kayan
wanki kuwa guri guda suka tara su da zumar kiran mai yi masu wanki ta zo ta zo ta wanke, sun gama sun
zauna suna maida numfashin tarin aikin da suka sha,Yaron su Nurain sai kara kaina ya ke a tsakanin su
wata magana da ya fad`i duk sai da ta sa su kai shock,"Ummu yau kin yi kyau,kin yi kwalliya ta yi maki
kyau sosai ban ta`ba ganin kin yi kyau irin haka ba, ko dai unguwa za mu ne ?",ya k`are zancen da sigar
tambaya.
Da wayo su ka samu su ka kaudar da batun,ringing d`in wayarsa ne ya katse shi, ya d`auka ya na fara
gaishe ta cikin girmamawa,kafin ya bata amsar abinda ta ce mi shi,"Eh Momynah yanzu na ke son in
shirya na je can babban Gidan,in ga Ummie da kuma su Baba Malam "," Okay daganan sai ka biyo ina
son mu tattaunawa akan wani abu mai muhimmanci ",Hibba ta fad`a daga wancan side d`in,da haka
suka gama wayar ya mai da kallon shi kanta yanda ya ga tana yamutsa fuska gami da dafe bayanta ya sa
ya fara jin tausayina,hanunshi ya kai yana mai tayata har zuwa k`afafunta kafin ya ce," I'm sorry na
wahalar da ke da yawa ko,ki yafe ni ba nufina kenan ba"......hannunta ta kai da sauri ta rufe bakinsa tare
da cewa,"Ba ka wahalar da ni ba ko kad`an,hasalima sai dai in ce ka taimake ni ne na sauke responsibility
na da na kasa saukewa na tsawon wani dogon lokaci,thanks for being by my side,thanks you a lot My
Husband, sannan kuma ina mai baka hak`uri akan abinda ya faru a jiya,ba zan kuma ,kuma na janye
furucin da na yi mara dad`i,kuma ina tuba akan haka".
Murmushi ya sakar mata yace,"Komi ya wuce a gare ni,ko kin manta ke d`in Sarauniyar Imam Jaheed
ce,kuma kin san Sarauniya ba ta laifi,dan haka ki manta da komi,yanzu dai zanje Momynah na Kira
kafinnan zan he wajen Baba Malam,ki kula da Gidan zan tafi da Nurain ko za ki samu ki huta".
"To shikenan Allah ya tsare a dawo lafiya in ka je ka ce duk ina gaishe su".
Nan ya tafi ya sake yin wanka shi da Nurain ya shirya su,su ka fito,saitin ta ya tsaya ya duk`a gami da
kamo hannayenta ya rik`e ya na mai cewa da ita,"Zan tafi dan Allah kafin in dawo ki yi mana lunch domin
na yi kewar abincin ki,zan so in tuna baya,ki sani har gobe har jibi kina nan a raina ina jin son ki a cikin
raina ban ta`ba yunk`urin sauya ki da wata ba,ko wacce mace za ta shiga rayuwata sai dai ta biyo bayan
ki,ke ce ta fari a gare ni,ina yi maki so mai yankan shakku,zan rayu da ke a cikin kowanne lokaci, dan
Allah ki koma kamar Zeenat d`in da na sani bana son cigaba da gudanar da irin wannan rayuwar a
tsakaninmu,ina cutuwa da hakan ,Nurain ma na cutuwa,hatta kan ki kina cutar da kan ki ba tare da kin
farga da hakan ba,zan so mu cigaba da shinfid`a rayuwar mu kamar yanda muka fara tun farko kafin
sauyi ya shigo tsakanin mu".
Daskarewa Zeenat ta yi a zaunen da ta ke,ta riga da ta zama speechless,kafin ta samu damar da zata
ce da shi wani abu ya kama hannun Nurain su bar mata Gidan cike da k`amshin turaensu.
Zuciyar ta ce ta fara gaya mata gaskiya har ta kai ga fara fidda zance zuci a fili, "Wai dama da gaske
har yanzu Abu