Author : Cwt Sumiey Category : African Stories & Novels
trying number na ta amma a kashe ba ta tafiya wani lokacin ma sai ace min not
reacherble".
"To ga Motar can wani ya kawo ya ce,wai a gaya maku tafiyar gaggawa ce ta kamata,da kuma wannan
takardar",ta kai zancen ta na mai miƙa masu Papertun kafin wani ya motsa Papa yace,“Ina ita Jadeedar?
Me yasa wani ya kawo Mota da wannan takardar?!” Papa ya buge da tambaya, yana ƙoƙarin ɗaukar
takardar.
Gidan kowa ya firgita, Zuciyoyinsu sai faman kai komo take da son sani ne takardar ta ƙunsa Granny tana
zaune dafe da ƙirjinta, Papa har ya fara fitar da ɗigon zufa . Momyn Jadeeda kuwa ba ta iya ɗaga kai ba.
Papa ya buɗe takardar cikin sauri, zuciyarsa na dukan bugun tashin hankali. Granny ta daga hannu tana
karanto addu’a a cikin ranta, kamar zata faɗi,Papa ya fara karantawa kamar haka
“Ina roƙon gafararku…
Ba don na tsane ku ba ne na tafi, sai don na rasa inda zan nufa,Zuciyar ta kasa iya ɗaukar abinda ya
tunkaro ni.
Kowane numfashi a cikinsa akwai ruɗani, tsoro da ɓacin rai. Idan ni ce kuskure, sai na zauna kuma na
rayu da shi
Ban san inda nake nufa ba, amma ba zan iya komawa inda ku ke ba.
Ina mai tabbatar maku da zan dawo amma sai Sheɗanin da ya ƙawata Zukatan Ƴan'uwana kuma
makusanta na ya bar gangar jikinsu,to a sannan zan dawo,ina kewan dukkanin kulawa da soyayyar da ku
ke nuna min,zan yi rayuwa a inda na ke cike da kewar ku.
Uncle Miey har yanzu matsayin ka yanan a cikin raina bai sauya ba,haka kaima Bro Edwin,Nora da Martin
zan yi kewar ku,ku kula min da Mommy da kuma Papa har zuwa sanda zan dawo.”
Jadeeda
Uncle Miey ya dafe bango, yana kallon Edwin,“Mun cuce ta...!” Granny ta faɗi da hawaye.
"Kai ne dai ka cuceta,kaine mabuɗi kuma sular faruwar komi,kai ne ka cuceta", Uncle Richal ya faɗa cikin
hargowa yana nuna Edwin da ya yatsa
Papa ya jefar da takardar, ya nufi inda Madam Gloria ta zube ƙasa tana kuka mai cike da raɗaɗi ba kuka
irin na ɓacin rai kawai ba, amma kuka mai tambayar "me ya faru da ƴata Jadee?,ina take a halin yanzu
wacce irin rayuwa za ta riska a duk inda ta ke,shin sake jefa kanta cikin wata rayuwar mai cike da hatsari
tai ko ko hanyar mafita ta samar kanta a sanadin barin Gida"
Amma tabbas barin Jadeeda ya bar ƙura, damuwa, da abin da babu mai iya warwarewa,face sai lokaci
domin shine alƙalin da baya ƙaryata,kuma baya cuta ko kaɗan.
Ina farin cikin sanar da ku cewa an buɗe Paid Group na Littafin JADEEDA domin masu sha’awar ci gaba
da karanta wannan labari mai cike da sirri, ƙauna da ruɗani.
Farashi: ₦300 kacal.
Za ku samu damar karanta Jadeeda har zuwa ƙarshe cikin sirri da tsari.
Account Number: 8102641528
Bank: Opay
Sunan Sumayya Usman
Kai tsaye za ku iya tuntuɓar ta ta wannan Lambar waya 08102641528
Bayan biyan kuɗi, ku tuntuɓe ni kai tsaye domin a saka ku cikin group ɗin.
Mun gode da ƙauna da goyon bayanku kullum. 💕
Cwt~Sumiey ✍️