Author : Cwt Sumiey Category : African Stories & Novels
yi kalaci",da ha suka dakatar da case ɗin.
Part 38
"Ah aha my dear Jadeeda ba dai har kin sallami baƙon ba,naga yayi wuri ace ya tafi tun yanzu,Ni da na
so ace kun ɗauki wani lokaci mai tsawo ko kwa samu ku fahimci juna?","Mom I'm tried,nifa ba ƙaramar
yarinya ba ce ,na rasa gane me ki ke nufi da turomin waɗannan guys ɗin".
"Ina tunanin mun rigada mun yi gama wannan maganar da ke tuntuni ko,nace maki Aure na ke so ki
yi,nan da wani gajeren lokaci".
"Haba Mom Aure kuma?, wanne irin zance ne ki ke yi haka,at how comes zaki yanke ma rayuwata irin
wannan hukunci,na rasa gane dalilin haka,last week kin kawo Johnson a matsayin baƙo kin ce in
sauraren shi,yau kuma kin kawo David shima haka ce ta kasance,shin na yi maki wani laifi ne da ki ke son
hukunta ni ta wannan hanyar ".
"No my dear ba laifin da ki ka aikata min,kawai dai ina son in ga Auren ki shiyasa hankalina ya karkata
akan in ga na samaki Mijin da zai dace da ke,ki yi Aure ki huta ki samu natsuwar hankali "....."Aure kuma
da ni,kuma wai da waɗannan mutanen da ki ka kawo, a'a no Momy ban shirya hakan ba,kalli fa ga Uncle
Miey da kuma Broth Edwin ba suyi Auren ba ,sai kuma ni, a'a idan ma Auren ne ki bari in kawo kalar type
ɗin Mijin da na ke so in Aura mana".
Miƙewa tsaye Momy ta yi gami da ɗaukar Car key nata tare da cewa da ita,"Waye ya gaya maki zaɓin
ki na ke jira a'a zaɓi na za ki bi,ki sa hakan a cikin ranki,daga Johnson har David ɗin ba nayardawa a cikin
su ,dukkanninsu sun fito daga Gidan dattako da kuma girma sannan kuma suna da arziƙin da hatta da
jikokin ki ba zasu taɓa yin talauci ba,dan haka ban ga aibun wani a cikin su ba,ya rage na ki ki zaɓi wanda
yafi kwanta miki a rai a cikin su ko kuma ni in zaɓa da kaina,yanzu ma haka fitar nanda zan yi tana da
alaƙa da wannan maganar da muke,ina son nan da few months in ga na aurar da ke,ko hankalina zai
kwanta in kau da mugun tunanin da ke yawo a cikin rayuwata"...."Momy mugun tunani kuma a
kaina,shin ko kina zargin ko kina zargina akan wani abu ne,ko na sauya daga kan turbar tarbiyyar da ku
ka ɗora ni akan ta ne?", Jadeeda ta tambaya cike da ƙarin mamaki.
"Ko kusa ban taɓa kamaki da wani kuskure makamancin wannan ba,kawai dai zuciyata na faɗa min in
Aurar da ke ,in sama maki Mijin dana yarda da shi gudun kar ko bayan raina wanda ki ka Aura ya cutar
min da ke,ba zan iya lamuntar hakan ba".
"Mom..... Haba nahhh ki bar irin wannan ƙananan tunane-tunanen ba su cika zama gaskiya ba
fa"....."Ko ma mene Jadeeda ba zan fasa wannan maganar ba,ki sa hakan a cikin ranki,Jiya ma munyi
magana da Johnson yace may be tomorrow zai dawo domin ku samu lokaci mai tsawo tare da shi sai ki
shirya ma hakan"...Mom na kaiwa nan tai ficewar ta ba tare da sake bi ta kan Jadeeda da kuma abinda
take son cewa da ita.
Kai tsaye Madam Gloria Gidan ƙawarta da ke Gwarumfa mai suna Sister Tarisa ta nufa,"Ah welcome
my friend Madam Gloria da har na fidda ran ba zaki samu shigowa ba kamar yanda ki ka ce", Sister Tarisa
ta ce bayan sun zauna ta kawowa Momy abin sha.
"Ina tafe My friend Yarinyar ki ta tsaida ni,da alama bore ta ke son yimin akan maganar Aurennan da
na zo mata da shi".
"Na san za a rina fatana ɗaya ace ba dai da itama Zuciyarta ta faɗa da son Richal ɗin ba"..."God for
bid,da na shiga uku in haka ta kasan ce,tonuwar asiri na dai-dai ta ke faruwar wani lamari mai girman
gaske,ban ma san ta ina zan fara fuskantar wannan lamarin ba".
"Ai dalilin da yasa na ce ki dage ki ga kin haɗa Aurenta da ɗaya daga cikin waɗanda na lissafo
miki,shikenan bakin ki alekum,asirin ki a rufe".
"Shiyasa ai na zo wurin ki domin naga yiwuwar hakan kamar da wuya","To bari ki ji riƙe mata wuta za
ki yi ,kar ki kuskura ki ɗaga mata ƙafa,da zaran kin ji tausayin ta ba iya makomarsa ba har da taki kin
ruguza,za ki cigaba da dauwamar da ita a matsayin ƴar ki ta halaliya ne ta hanyar raba alaƙar da ke
tsakanin ta da ɗan'uwanki Richal".
"Ba na fatan zargi da tunanin da muke mi da Momy ya zama gaske akan shi,domin mudun haka ta
kasance sai nasa yayi mugun regret","Kin san me kamata yai ki tare shi ki tuntuɓe shi da maganar idan
har kin tabbatar da hakan sai ki dakatar da shi,ki yi mi shi warning na gaske,ki nusar da shi illar da hakan
zata haifar ,Ni fa a wannan tafiyar banga abun gari a ciki ba,domin in har ya kasance soyayyar gaskiya ya
ke mata bai kamata ya fallasa hakan har mutane ko duniya su sani ba,domin hakan a gare ta tamkar
gurgunta asali da rayuwar ta zai yi ba".
"Ta yani gani wai makaho ya so gulma,akan wannan lamarin na runtse ido ban ji daɗin makanta ba,ba
na tunanin akwai wani amfani da zai samu idan har ya cimma wannan burin na shi".
"Kin ga ƙawats Gloria har yanzu akan wannan lamarin zargin Richal mu ke bamu da wata hujja ko
makama da zamu ƙarar akan shi game da abinda mu ke zargin nasa,don haka kar mu zafafa mu bi komi a
hankali domin gano bakin zaren kar garin gyaran gira a rasa ido kuma".
"Anya kuwa Sister Tarisa zan iya riƙe kaina akan wannan lamarin,ina tsoran kar batun nan ta daɗe in
kasa iya riƙe kaina","Za ki iya Mu Friend tunda har ki ka iya riƙe asalin sirrin da ke binne a ƙasa har kawo
yanzu to wannan ma zaki iya ki bi komi a hankali za ki ga alfanun haka,ya ku ka yi da Mom
Rebecca","Hmmmmm kar ki so ki ga yanda hankalin ta ya tashi kusan komi ya hargitse mata","Allah sarki
ai nasan dole hakan ta kasance,na ga ma ƙoƙarin ta ","Kin san ita ta fara son fahimtar haka har sanar da
ni,in ba dan ita ba da ban san sai zuwa yaushe zan fahimci wannan mummunan lamarin da ke shirun
faruwa a cikin Gidana ba","Ki ƙara kwantar mata hankali by the Grace of God ba abinda zai faru",da haka
su ka cigaba da hirar su gami da neman hanyar da zata zame masu mafita a gare su.
Tun fitar Momy JADEEDA ke faman kai kawo,ta rasa wacce makama ya kamata ta kama ta wacce hanya
za ta fahimtar da ita zuciyarta ba ta yarda da wannan ƙudirin da ta zo mata da shi ba, Uncle Miey da ta
ke taƙama da shi yayi tafiya, Granny kuma ta je Jos ganin Gida,su ne kawai za ta faɗa nawa suyi ma
lamarin tufkar hanci,Papa kam bata maganarsa tunda har Mom ta riga ta yanke wannan hukuncin to da
saninsa da kuma yardar sa,dan a yanda ta san su tun yarintar ta komi bisa yarjejeniyar juna su ke tafi da
shi,"Ko dai in je in sanar da Brox Edwin da abinda ya ke faruwa ko ba zai min maganin abinda,ai zai iya ba
ni shawarar da za ta iya yi min amfani",ta ɗan dakata ta na mai jujjuya maganar a cikin ranta,"Kai bari dai
in je mai yiwuwa ma mu haɗu ni da shi mu fahimtar da Mom haɗarin da ke cikin wannan al'amarin da
take son sanya rayuwata a ciki",da haka ta tashi ta nufi Part ɗin na sa,ta na tafe ta na saƙawa da
kwancewa a cikin ranta.
"Broth Edwin!",ta kira sunan shi a hargitse,"Me na ke gani haka aman jini fa ka ke",Jikin shi na rawa ya
bar gaban sink ɗin ya nufi inda ta ke,"Kin ga ki saurare ni,ba abinda ki ke tunani ne ba na ci wani abu ne
shi ya janyo min faruwar hakan","Kamar ya ka ci wani abu,shine ya sa Jini ya ke fita har ta hancin ka",
Jadeeda ta faɗa ta na mai girgiza kanta alamun ba ta yarda da abinda ya ce ba ba,
Sosai ya matso kusa da ita har tana jin hucin zafin da jikinsa ke fiddawa,ya kama hannun ta tare da
sanyaya muryarsa gami da aro natsuwa yaɗora akan fuskar shi,"Ki fahimce ni jiya mun fita ni da Friend
ɗina ya ja ni mun je wani Club so acan na ci wani abinci da na ke da Algy da shi, so shine ne fa nake ta
faman aman jini,kuma shima yau da safennan na fara yin sa".....
"A'a no Edwin you're liar,ban taɓa jin cewa kana da Algy da wani abinci na daban ba,biside ma fuskar
ka bata gaskata abinda kake cewa ba,ka ga ka faɗa min gaskiyar me ke faruwa da kai,I'm promise ba zan
faɗa ma kowa ba,za mu haɗu mu yi maganin duk matsalar da ta ke damun ka,kalle ni ka gani,Ni ce
jeeyyyy ɗin ka,ƙanwar da ka fara riƙa a matsayin little sister na ka, wacce ka ke tare ma faɗa idan ta
tono,wacce ka ke rago ma duk abinda ka ci a school,wacce ka nuna ma so fiye da kowa ,fiye da kai karan
kan ka,na roƙe ka da ka faɗa min abinda ke damun ka,na daɗe da fahimtar kana rayuwa ne cike da wani
miki ko tabo a cikin zuciyar ka tun kafin ka dawo,ka sani da damuwa na shigo cikin Room ɗin nan naka,na
zo in sanar da kai wani abu da ya ke damuna,amma sai na iske halin da ka ke ciki ya danne damuwar da
na ke a tafe da ita,na ɗauke ka a matsayin ɗan kuwa ɗaya da ɗaya da na ke da shi,wanda zai share min
kuka na yai min maganin damuwar da na ke da ita,mudun ba zaka sanar da ni ainihi kuma gaskiyar
abinda ke damun ka ba,to zan juya da tawa damuwar,na yarda kuma na amince nima tawa damuwar ta
illatani ta saka ni cikin irin yanayin halin da ka ke a ciki".....
"No....No...no Jeeyyyy kar ki yi haka kar ki ce ba za ki sanar da ni damuwar ki ba,a shirye na ke in
tunkari komi in har akan ki ne,ki sani za ki sake jefa ni cikin wata sabuwar damuwar ne muddin ki ka juya
ba tare da kin sanar da ni abinda ki ka zo ki sanar da ni''.
"Broz Edwin!....hawaye....hawaye fa ...kuka ka ke yi fa,hawaye ke zubowa daga cikin idanunka",ta ɗan
dakata ta na mai kai hannunta ta dangwalo hawayen don son tabbatarwa agaresa,kafin ta ɗora da
cewa,"Kenan hakan ya na nufin duk abinda ka faɗa ba gaskiya ba ne ba ko ?",
Buɗe baki yai ya na son cewa da ita wani abu,amma ya kasa bakin sa sai rawa ya ke gami da son
cewa wani abu ba dama,"Ka ga ni ko,bakin ka ya kasa iya cewa komi domin dama bai saba furta ƙarya
ba,don haka ka faɗa ina jin ka kuma ina tare da kai" .
"My Jeeyyyy kar ki damu ko ki matsa akan sai kin san me ke damuna domin hakan sirri ne,zai fi kyau ki
barshi in cigaba da rayuwa da shi ni kaɗai kuma matsayin sirri,na sani a idanuwan ku kuma ganin kamar
ina cutuwa, to a gare ni wannan cutuwar tafi min akan in sanar da ku halin da na ke a ciki,a yanzu ni ke
cutuwa amma da zaran wani ya sani Shikenan za mu koma cutuwa a tare,to me zai sa in cutar da wani
akan wata ƙaramar matsala tawa?,zai fi kyau mu manta da hakan mu fuskanci abinda ki ke tafe da shi".
"Ka juri abubuwa wahalhalu da dama kaina,ka Goya ni a bayan ka ,ka saɓa ni a bayan ka,ka ji da
dukkan wasu ƙananin damuwowina,ka sanya ni farinciki a mabanbanta lokuta,sai yanzu zan kasa
tsayawa a gefanka ,shin wacce irin ƴar'uwa ce ni mai son kanta,mai fifita son ranta a kan wanda ya
saudaukantar da yarintar sa gami da kuruciyar sa a saboda ni ,idan har da gaske har yanzu ina da irin
wannan matsayin a wurin ka,kuma kana ji na a cikin ranka kamar yanda na sani a baya,kuma ka na son
kada in rayuwa a cike da zargin kaina akan ka to ka sanar da ni abinda ke damun ka a yanzu ba sai wani
lokacin ba".
Dafe kan shi Edwin yai gami da fara ja da baya,ya rasa makamar da zai tsaya da ita ,shi ya sanarda ita
damuwar sa ko dan ya ji tata damuwar ko kuma ya bar ta tafi kowa ya riƙe ta sa damuwar,sai dai wani
sashe na zuciyarsa na gargaɗarsa akan kar yai kuskuren sanar da ita domin zai iya yiwuwa,yai biyu
babu,ya samu wata hanyar da zai bi da ita ta sanar da shi damuwarta ba tare da shi ya sanar da ita ta shi
ba,don kar jifan gafiyar ɓaidu,ya zo tsana, gaba gami da distance ya shiga tsakaninsu madadin kusanci da
yake tsakanin su ya ƙara ƙarfi,amma ina ya rasa hanyar ,tunani shi ya cure gami da takurawa guri
guda,baya tunani a yanzu kuma a cikin halin da ya ke a ciki brain ɗin sa na iya tan-tance masa tsakanin
fari da baƙi.....
Part 39
"Ƙarfin zuciya bai zama da sauƙi ba, musamman idan kalmar gaskiya ta tsaya a maƙoshin wanda ya
kamata ya faɗe ta",shine abinda ya fi tsayawa a cikin rai da zuciyar Edwin.
A tsaye Jadeeda ke kallon Edwin, jikin shi na rawa, idanuwansa sun kumbura da hawaye, bakinsa ya kasa
furta komi. Har yanzu bai faɗi komai ba. Sai kawai ya juya ya koma kan kujera, ya dafe kansa kamar
wanda ke gudun tunani ya cinye shi.
Jadeeda ta taka a hankali ta zauna kusa da shi, ta ɗora hannunta kan kafadarsa,tare da cewa,"Bro
Edwin... ka tsorata ni," ta faɗa a hankali, murya cike da laushi.
"Ba komai ne zai sa kai kuka ba, sai abinda ya fi ƙarfin zuciyar ka... kuma duk da haka kana ƙoƙarin ɓoye
shi. Amma me yasa?"
Edwin ya ɗan ɗaga kai, idanuwansa sun cika da wani irin zafin da ba za a iya fassara shi da kalma ba. Sai
dai ya faɗa.
"Na jima da ɓata hanyar da zan iya komawa asalin yanda ne ke,ki bar ni in cigaba da rayuwa a haka
kamar hakan shi yafi dacewa da ni... Na rasa komai Jadeeda, na rasa kai na... kuma bana son ki rasa kan
ki ke ma."
Zuciyar Jadeeda ta buga da ƙarfi. Wani abu na cikin wannan maganar yana nuna cewa ba lafiyar jiki kadai
ke damun Edwin ba... akwai wata annobar sirri da ke cinsa a hankali.
"A'a Edwin, ba zan bari ka ɓace ba.ba zan bari ka sake cilla rayuwar ka cikin ƙaƙanikayi ba, Ka dade kana
riƙe ni lokacin da duniya ta juya min baya. To yanzu sai na tsaya tare da kai har ka tsira, har ka murmure
ka dawo asalin yanda ka ke,na yi alƙawari..."
Ya riƙe hannunta sosai, kamar kar ya saki, kamar wannan ƙananan lamarin ne kadai ke hana shi ruɗewa
gaba ɗaya,ya so ace ƙaramin dalili ne ke cin sa a ransa ,da ya sanar da ita ko ya samu ya kwanciyar
hankali da natsuwa a saman fuskarta,amma ina lamarin ya sha kan shi ya kuma fi ƙarfin zuciyarsa.
Sai kuma ya ce da ita a hankali kamar raɗa,"Jadeeda, idan na faɗa miki gaskiya, rayuwarki zata canza...
wata kila za ki ƙi ni... wata kila za ki ƙi dukkanmu...ki tsane ni ki tsani kan ki da kan ki"
Hawaye suka cika idanun Jadeeda, amma ta daure, ta ce:,"To ka faɗa. Koma me yene, faɗa ɗin kan ka
tsaye. Sai dai ni ka sani ba zan juya maka baya ba na yi alƙawari akan hakan."
Sai dai kafin ya buɗe baki ya ce wani abu zuciyar shi ta sake bugawa har hakan ya sa ya runtse idanunsa
gami da dafa saitin Zuciyarsa, alokacin da Edwin ya dafe hannunta kamar yaro mai jin tsoro, ya rasa ko
ya zauna ko ya miƙe tsaye. Kamar wanda za a yanke wa hukunci ne.
Sai dai wannan karon… ba zai iya gudu ba,Ya buɗe baki da murya mai sanyi amma mai nauyin
gaskiya,"Jadeeda… Ina son ki. Da gaske. Amma ba da irin son da ke da kyau wanda mu ɗauka kamar na
ƴan’uwa ba. Ina son ki da zuciyata amma na san wannan so haramun ne…”,Zuciyar Jadeeda ta tsaya.
Gaban ta ya fadi. Kamar a mafarki. Kamar ruɗanin da ba shi da fassara,ko motsin kirki ta kasa.
“Wannan sirrin na damuna har tun kafin na san ke wacece. Amma tun daga lokacin da na fara jin ki,na
saurare kalamanki, jin kukanki, jin karayarki so ya shiga zuciyata. Na ƙi amsa masa, na yi addu’a, na roƙi
Allah, na karanta Littafi Mai Tsarki… na karanta inda aka ce
“Kada namiji ya auri ‘yar uwarsa.”Na karanta inda aka ce“So da ƙauna su zauna cikin tsarki,amma ina
Zuciyarta ta ƙi ji ,na kurumce gami da makancewa akan haka,na yi tur da halina na tsani kaina,na la'anci
shaiɗanin da yake tare da ni har ya ke son ya cutar da ni amma ina lamarin ya fi ƙarfina ya girmi hankali
da tunani na.”
Sai ya runtse idonsa ya ce, “Amma duk da haka… zuciyata ta ƙi ƙyale ki. Kuma yau, na kasa ɓoyewa. Ban
san yadda zan fuskance ki ba… amma na fi tsoron ƙarya da boye gaskiya.”
Jadeeda ta zare hannunta daga nasa. Ta miƙe tsaye kamar wadda aka zuba wa ruwan sanyi. Hawaye na
gangarowa fuskarta, zuciyarta na ɓari.
Ta ce da karfi, kamar wadda ke magana da kanta,"Ka haukace Edwin,da gaske ka samu matsala a cikin
kan ka,kana buƙatar,a duba lafiyar ka da gaggawa".
Edwin ya durƙusa ƙasa, hawaye ya ƙi daina zuba. Sai dai shiru ne a bakinsa.
Jadeeda ta fashe da kuka. Ta fuskance shi, ta ce da tsawa mai rauni,"Ka daina sona Edwin. Ka manta da
ni! Ka manta da ni gaba ɗaya. Kai ba dan Krista na gari bane idan kana iya soyayya da ƙanwarka!”
"Kin ga ki fahimce ni nasan da hakan haramun ne,shiyasa na zaɓi in rayu a cikin ƙunci da kuma ɗacin
zuciya......ya ɗan dakata numfashinsa yana barazanar rabuwa da gangar ƙirjinsa,kafin ya cigaba da
kokowa da shi.
“Ko kuwa....dai .... ka sauya addini ne domin ka samu damar sona?,Domin Ni na san a cikin Bible, kaf
babu inda aka halatta ɗan'uwa ya auri yar'uwarsa. Ko kuwa kai na na dab ne, Edwin?”,ba na tunani
akwai wani addini a duniya da ya amince da irin wannan kwamacalar da ka zo min da ita".
Edwin ya zube ya fashe da kuka mai