Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Jadeedah Complete Hausa Novel by Cwt Sumiey

Author :  Cwt Sumiey Category :  African Stories & Novels

Chapter   16 / 37

45K to 48K   out of 108.5K words

Suna na
Jedeeda Anderson mahaifina ne wanda d`azu ku kayi da shi zai dawo ka bashi shawarwarin hanyoyin da
za a bi domin kula da mara lafiyar,ya ce min ka buk`aci wasu papers a wurinsa don haka ya tafi Gida
domin ya d`auko daganan yace if possible ka sanar da ni advice d`in".tsura mata ido yai yana son ya gano
wani abu mai muhimmanci daga gare ta wanda yake jin yana jan shi zuwa inda ta ke amma kuma ya kasa
gano komi ye,dole sai haƙura yayi gami da zuba mata ido yana jin me ta ke cewa.

Cikin k`ank`anin lokaci yai mata bayanin irin su kula da shan maganin ta,rashin son hayaniya a inda
take,yawan lura da halin da take a ciki a koda yaushe,samun isasshen barci,aikata abubuwan da ta fi so
da dai sauran su,ya kai k`arshe zancen da wannan.

Jiki a sanyaye Jedeeda ta mik`e ta na mai cewa da shi,"Thanks a lot Doctor na ji dad`in bayanan ka
kuma by the will of God za a yi kamar yanda ka ce kuma za a kiyaye abinda ka ce".Hakanan ya ji
muryarta har a saman kan shi,har sai da takai shi ga kafeta da idanuwansa masu tasiri ga wanda ya ke
kallo.

Sai da ƙyar ya iya cewa da ita bayan ya samu ya mallaki kan shi, "Don't Mind in har da zai ku yi amfani
da duk abinda na ce in sha Allah a hankali a hankali za ta rik`a samun sauk`i,idan ba wani abu da yai
saura za ki iya tafiya".

Rasa me zata ce tai ta so ace ko Yaya ne ya bata damar da za ta yi magana akan abinda ya faru da`zu
amma ko da wasa bai ba ta fuskar hakan ba kamar ma ba da shi abun ya faru ba,har ta kusa k`ofar fita ta
ji ba za ta iya fita ba har sai ta ce da shi wani abu akan abinda ya faru,sai dai tana jiyowa da niyar ko
yunk`urin ta ce wani abu,aka banko k`ofar da k`arfi a ka shigo batire da an ba mai shigowar izinin hakan
ba.

Bakinta na rawa ta fara ambaton sunan shi da cewa," Papa lafiya what wrong with you,ko dai jikin
Momyn ne ya motsa ?".
Ko d`aya bai saurare ta ba domin gabad`aya hankali da tunaninsa ya na kan kan Dr Jaheed, "Dr kalla ka
gani na kasa yarda da abinda na gani a jikin this papers Anya da gaskene Gloria na sane da wannan cutar
sama da shekaru Ashirin,kai I can't believe this".

Amsa Dr Jaheed yai ya na duba paper's d`in na wani d`an lokaci kafin ya ce da shi," I'm sorry to say Sir
domin Maganar gaskiya Madam Gloria ta san da wannan lalurar har ma tana medication d`inta ka ga
wannan takardar shaidar ta ziyarci wani babban Asibiti ne U.s a shekarar 2018 wannan kuma photon
kwakwalwar kanta ne da aka d`auka a Paris in the year 2007 da kuma sauran test-test da ta gudanar
akan hakan".

"What Momy ta san da wannan ciwon at how", Jedeeda ta tambaya fuskarta d`auke da mamakin
abinda ta ji.

" Kun ga bai kamata ku tada hankalin ku ba domin hakan zai iya sake jefa ita patient d`in cikin wani hali
in har ta farka ta gan ku a haka,yanzu ba lokacin maganar ba ne ba,ta lafiyarta mu ke,mu gare mu ma
bayyanar wannan hujjojin wata sabuwar nasara ce domin zamu yi amfani da ita mu cigaba da d`orata
akan medication d`in da ya kamata".

"Kai .....hah....why are you doing that for me,how long mu ke a tare amma ba zaki sanar da ni wani
abu daya ya ke damun ki ba ,wannan wanne irin betraying ne haka shin dama can ba zaman amana mu
ke ba?"....

Dakatar da shi Dr yayi ta hanyar zaunar da shi kan d`aya daga cikin Seater's dake kusa da shi nan ya
cigaba da bashi baki har ya samu ya shawo kan shi hankalin shi ya d`an kwanta kafin ya maida kallonta
akan Jadeeda ya ce da,ita,''Am if possible ki d`auke shi ki mai da shi Gida yai wanka ya d`an huta ya ci
abinci sai zuwa anjima sai ki dawo da shi may be zuwa time d`in ma ta farka amma dan Allah na rok`e ku
Dan Allah kar wanda ya ta da wannan Maganar for now domin ta na buk`atar hutu".

" I promise you ba abinda zai faru ba wanda za sake tada maganar a dai yanzu mun gode da kulawarka
a gare mu,thank for your care, kindness and consent ".

Da murmushi ya amsa ma ta abinda ta ce d`in nan ta kama hannun Revered Anderson Wanda ya zama
kamar sick person su ka fita daga cikin Hospital d`in gabad`aya.




~~~~~~~




"My World da alama dai yau ka yi aiki da yawa domin ga gajiyanan duk ta bayyana akan fuskar ka".
Hannunsa ya kai ya na mai shafa kan shi har zuwa saman fuskarsa kafin ya ce," Ke dai bari Gimbiya ta
tamkar mutanen jirana su ke,ko kusa ban samu wani lokaci da zan huta ba".

"Eyyah I'm so sorry My World na ga hakan kwance akan fuskar ka,ga shi kuma ba kowa a tare da kai
sai kai kad`ai".

" Ayush kar ki damu I will be okay ,yanzu ba ga ki ba,in sha Allah komi zai koma normal ".

" A'a ni ba haka na so ba,iya haka bai wadatar da ni ba".

Murmushin gefan baki ya sakar mata wanda yake k`ara k`awata fuskarsa kafin ya ce da ita,"Ko za ki
taho yanzu ne kin san zan yi farin ciki da hakan ?".

Zaro idanunta waje ta yi tana mai cewa,"Rufa min asiri kar ka sa Ummu Nurain ta zo ta addabe ni da
masifar ta babu gaira babu dalilin".

"Matsoraciya ki taho mana"....sai da Gimbiya Ayush ta `bata fuska kafin ta ce da shi,"Ni wallahi ba
tsoranta na ke ji ba,kawai ba na biye mata ne don kar ajina ya zube,me ye zai sa ma inyi hayaniya ko
fad`a da ita sai ka ce ba Gimbiya Ayush ba,in ma ba dan k`addara da ta had`a ni Auren Miji d`aya da ita
ba ai da ko hanyar da na bi,ba ta isa ta bita ba".

Sosai ta zage sai zuba masifa ta ke,shi kuma ya tsura mata ido tamkar television,ganin kamar ya zuba
ma wuri guda Ido ne ya sa ta ta d`an dakata ,sai a lokacin ta fuskanci ita ya ke kallo.

" Wai har haka ake kishina kuma ake sona ban sani ba ?"ya tambayeta ba tare da ya tsaya ba ya
ce,"Ashe ni Muhammad Jaheed d`an gata ne har haka ban sani ba".

Bata iya ta ce mi shi komi ba sai sake tamke fuskarta da ta yi alamun har yanzu ta na kan k`adamin
fushi akan Maganar da ya yi.

"Ina son ki,ko fushi ki ka yi kyau ya ke k`ara ma ki,komi ki kai burge ni ki ke kuma k`aramin son ki ya
ke,kin can-canci a so ki,daga nan ina iya haikato daddad`an k`amshin da ke fita daga jikin ki,ke d`in ta
daban ce you are so classic woman".

Irin wannan dad`ad`an kalaman ne suka ribaci Gimbiya Ayush wanda tuni ta ma manta da wani batun
Ummu Nurain da yai mata har daga k`arshe take cewa da shi," Ya kamata fa ace ka zauna kayi dogo
tunani cikin jagorantar Al'umma `bangaren Addini ko kuma kula da lafiyar su wanne za kai ,ka ajiye
d`aya,ba na son in rik`a ganin ka cikin irin wannan yanayin, kwata-kwata ba ka samun hutu kullum cikin
aiki ka ke".

"Hmmmm Gimbiyata kenan ba abinda za a fasa walau jagorantar Al'umma ko kuma kula da lafiyar su
domin duka aikin taimako ne ,aikin Allah kuma kin ga bai kamata in janye daga wani `bangaren ba tunda
duka suna da buk`ata ta".

Bud`e baki Gimbiya Ayush ta yi da niyar za ta sake cewa da shi wani abu ya dakatar da ita da cewa,"
Addu'ar ki kawai na ke nema da kuma fatan nasara akan komi,sai dai ban sani ba ko hakan ya na sawa in
shiga hak`ink`i ba?",ya tambaye ta yana mai tsare ta da idanunsa"A'a ni ko d`aya ,kawai dai ba na son in
cigaba da ganin ka a yanayin da na ke ganin ka".

"Kar ki damu ba abinda zai faru da ni ,ina tare da Allah, kawai Addu'ar ki na fi so da kuma kulawar da ki
ke bani", da haka dai su ka kai k`arshe firar ta su da ita.

Gyara zaman laptop d`in da ya ke aiki da ita yai sai dai tun bai yi nisa ba wayar shi da ke gefan shi ta
fara rurin nai man a gaji,sai da yanayin fuskar shi ya sauya kafin ya picking d`in call d`in muryarsa d`auke
da sallama.

" Haba Abu Nurain wannan wane irin rashin adalci ne,me na aikata ma ka har haka da ka za`bi ka
wofintar da ni ka nuna ma duniya ni ba kowan kowa ba ce a wajen ka, kar ka manta nifa `yar'uwar ka
ce,ko ba so akwai zumta a tsakanin da kai ".

" Ya Allah Zeenat mai yai zafi har haka mai ya kawo irin wad`annan k`ananun zancen ?".

"Oh k`ananun zancen ma za ka kira maganar da na zo da ita,yau kwanan ka nawa da tafiya ba Kira ba
sak`o hasalima ban sa ina ka tafi ba kar ka manta ni ma fa Matar ka ce kuma Uwar d`an ka ina da hak`k`i
akan ka".

Cire wayar Jaheed yai daga kunnen shi yai kamar zai yanke kiran sai kuma ya fasa ya san hakan ba
K`arami K`ara rurar wutar rikici zai ba.

Cikin sanyi da kuma gajiyar da ya ke tare da ita ya ce da ita,"Ban san me ki ke so ki mai da ni ba
Zeenat,ke fa na zo part d`in ki ki ka rufe min k`ofa kawai dan kin ga na fara shiga Part d`in Gimbiya Ayush
bayan dawowata daga office,gabad`aya ki ka tashi hankalina,ki ka hanani natsuwar rai, Randa kuma zan
yi tafiya tun da farar safiya na na zo inda ki ke ina maki magana amma ki iya ki bud`e idanun ki ki kalle ni
ki ka kasa , balle har in sa ran za ki saurari abinda na zo ma ki da shi,haka na k`araci zamana na gaji a
haka ki ke iya bayyana ta ki Soyayyar ta hanyar wani mahaukacin kishi na ki marar amfani ?".

" Ni ban wani san ka zo ba,kuma kai ma ai kasan Nurain ba ya wani barina in yi barcin kirki,kullum cikin
fitina da k`iriniya da rashin ji ya ke,da safen kawai ne na ke samu in yi barci mai isata,kuma ai nasan
waccen Matar son ka sanar da ita kafin ka tafi sai ni da ba a bakin komi na ke ba"......

"Kin ga Zeenat ba na son tashin hankali ,in dai kin kirani don ki tada min hankali ne sai da safe".

Tana k`ok`arin sake cewa da shi wani abu ya katse kiran ya barta da wani sabon takaicin a cikin
ranta ,ba shi ya tashi daga nan inda ya ke ba har sai da ya kusa raba dare daga k`arshe ya tashi yai sallolin
sa kafin barcin wahala ya kwashe shi akan prayer mat d`in
*JADEEDAH*



(It's a story of two love birds who are so different from each other )

STORY & WRITTEN BY :

(*Cwt~Sumiey*)

Marubuciyar littafin

MENE NE ABIN YI ?

KARAGAR MULKI

And now.....*JADEEDAH*



https://chat.whatsapp.com/CWkZfMqvD4H0mtd7WW6Xbz.



https://whatsapp.com/channel/0029VapqU8C002T5Bz8RSQ0a




BOOK 1




PAGE 19❤




"Wow Gimbiya Ayush irin wannan Ado haka sai faman k`amshin da walwali ki ke sai ka ce wata sabuwar
Amarya,ko dai Doctor na kan hanyar dawowa ne?", Anisa ta tambaye ta na mai sake bin ta da kallo.
Sai da Gimbiya Ayush ta rausayar da kanta gami da jujjuyawa kafin ta ce da ita, " Ba d`aya k`anwar
biyu,wannan kwalliyar da ki ke gani na yi ta ne domin rad`in kaina ba,babu inda zani Doctor kuma sai nan
da zuwa three days zai dawo".

"Yauwa Gimbiya Fadeelah ina sak`on da Fulani ta bayar ta ce ki kawo min ?".

" Oh ya na motor na baro shi amma in zamu tafi sai in d`auko miki".

"Ina ba ki isa ba salan kuma ki manta ki sake komawa da shi Masarauta".

" Kai Anty Gimbiya yanzu fa muka zo ko ruwa ba ki bamu ba, ki ke Maganar tafiya sai ka ce wad`anda
ki ke kora".

"Na fa san halin ki Fadeelah tsaf za ki iya sake komawa da shi,kad`an ne daga cikin aikin da za ki
iya,kuma Gidan ai ba bak`on ki ba ne ba ba kin san hanyar da fridge d`in ya ke".

" Haba k`awata Fadeelah fa now is a big girl ta ya za ki rik`a mai da ta baya,ita ma fa ta san aikan Fulani
ne ba za ta yarda ta manta ba".

"Yauwa Anty Aneesa fad`a mata dai,kowa yasan yanzu na girma".

" Hmmmm kin girman dai Fulani ta gama sangarta ki ai".....,Anesa ta katseta da cewa,"Wai ke tsaya da
za mu wuto na ga k`ofar Part d`in waccan Matar kamar a rufe kar dai ki ce min da ita yai tafiyar ?".

Sai da Gimbiya Ayush ta zaro idanun ta waje kafin ta ce"Wai wa ki ke nufi kar dai ki ce min Ummu
Nurain, ai ko k`ofar Gida in ba ta zama dole ba ba zai tafi da ita ba balle Gari ya gaarara har Abuja".

"Ki ce har yanzu ta na nan da halin ta na k`azanta" ,"Ai in gaya maki sai abinda yai gaba,yanzu da za ki
shiga Part d`in ta ba lalle ki iya shak`ar iska ba,sai fitinannen kishin tsiya,kamar wacce ke had`iyar wuta".

"Ta`b aiko ta na ruwa,wa ya gaya ma ta yanzu mata na zama da k`azanta ai kai duk ya waye,ba irin
wannan duhun kan"," AI ko ban da ita ita da yanzu za ki fara yi mata complain kan bata yin tsabta sai ta
ce,maki ai Nurain ne ba ya barin ta zauna sakat,kullum cikin sa ta aiki ya ke, idan ki ka matsa sai ta ce
har da laifin Dr. da ya hanata d`aukar me aiki,har ma `yan'uwanta sun kai ga gajiya da yi mata magana
sun kyaleta,ke ni wallahi da ni Imam ya fara Aura na rantse zai yi wuya ya k`ara kallon wata mace bare
har ya kai ga yin sha'awar Aurenta".

"Ikon Allah warnder shall never end wai yau Ayush ke ce ki ke crushing akan d`a Namiji ki ke bayyanar
da mayatar son shi a fili abun akwai d`aure kai da ban mamaki".Cewar Anesa k`awarta ce tun yarinta sai
kuma Gimbiya Fadeelah da take k`anwarta.

" Hmmmm ba za ki gane ba Anesa,dagaske ina son Imam Jaheed so kuma ba irin na wasa ba,Wanda
har ya kai na kan iya mantawa da asalina ko ni wace ce idan ina zaune tare da shi rikid`emin ya ke ya
koma shine Yariman ni kuma a matsayin hadimar sa, duk wani abinda ya ce shi nake yi ,bana son
sa`bawa dokar sa,ki na gani saboda gudun `bata mishi rai ya sa Na sallami duk wata Baiwa da na zo da ita
Gidannan ".
Sake baki Anesa tai tana mai bin Gimbiya Ayush da kallo," Ki gane Anesa Soyayya da Ustaz akwai
dad`i da tsayawa a rai,idan ki ka samu irin wannan dama kar ki yi wasa da ita".....shigowar Hameed ita ce
ta dakatar da zancen na ta.

`Dan dakatawa yai kafin ya ce,"Anty Gimbiya bak`i ki ka yi ashe ?".

"Eh Gimbiya Fadeelah ce da kuma Aneesa,ka shigo ma na ka tsaya daga gefe".

" Au ashema ba baki ba ne `yan Gida ne",ya kai zancen ya na mai wara idanunsa a cikin Parlourn daga
bisa ni ya samu wuri can gefe ya zauna".

"Meet my friend Anesa sai kuma Gimbiya Fadeelah autarmu" cikin mutuntawa su ka gaisa da juna
kafin ya ce,"Ai na san Gimbiya Fadeelah amma a IG ina d`an ganin videos d`in ta haka", da d`an sauri
Gimbiya Fadeelah ta d`ago tana mai sauke idanunta akan shi.

Murmushi ya sakar mata kafin ya ce,"Eh Hameed Abubakar Mai Fata shine suna na har DM na ta`ba yi
maki so d`aya amma ba feedback,daganan ban sake ba ".ya kai ƙarshen ya na mai sakin fara'a a saman
fuskarsa

" Fiye da haka ma za ka gani kai ba a IG ba hatta a Gida cikin Masarauta haka Gimbiya Fadeelah ta
ke,sai ka zo ka ka gama abinda ka ke a Gidan ba tare da ka sa ta a cikin Ido ba"Cewar Gimbiya Ayush.



"A to Na yi shiru tunda abun haka ya ke", rasa me ma Gimbiya Fadeelah tai sai dai bin sa da kallo da
take,shi kuma a lokacin ya maida hankalin sa kacokan wajen Gimbiya Ayush ya na mai cewa da ita," Am
ki yi hak`uri tun jiya Yah Imam ya ki rani ya ce in zo in tambaye ki ko da akwai wani abu da ki ke so ko ya
k`are a cikin Gidan,sai in je in siyo ma ki".

"A'a ha ba yace ya kusa dawo fa?"," Eh haka ya sanar da ni,amma kin sa ko da ya dawo bai fiye zuwa
irin wannan wurin ba","Na sani na yi zaton ko ya d`aga Maganar dawowar shi ne","A'a yananan ko d`azu
da muka yi waya da shi haka ya gaya min".

"Okay akwai kayan abincin wadatattun a store fridge d`ina ne kawai kayan cikin sa su ka fara k`asa sai
kuma Vegetables, kai duk abinda ya kamata ka siyo ka siyo kawai".

Mik`ewa tsaye tare da cewa,"Okay bari in je yanzu in dawo fatan dai ba inda za ku don sauri na ke da
akwai inda za ni in na dawo?".

" A'a ba inda zamu,in ma da inda zamu sai in bar maka sak`o wurin gate keeper","To ba damuwa
hakan ya yi barin in je part d`in Ummu Nurain in ji na ta sak`on ".

"In ka shiga ka gaishe min da ita"..... Da sauri ya katse ta da cewa," Wa!?,Ni a'a ba dai ni ba ai wannan
sai ki ja in na shiga in fito da k`afa d`aya".

"Yo kai ko me zai ja maka fitowa da k`afa d`aya sai ka ce Wanda ya shiga wani bak`on wuri Gidan
yayan ka fa ne".
"Hmmmmmm ko ma

16 / 37