Author : Cwt Sumiey Category : African Stories & Novels
Nora ita
kuma suna kiranta Momys Daughter kasancewar Momy ta fi nuna kula gami da ji da su,Martin kuwa
shine d`an Gidan Papa,ita kuma Jadeeda ita ce `yar Gidan kowa,dukan su suna nuna mata so da iyakar
iyawarsu,ta samu gurbi a Zuciyoyin kowa da ke amsa sunan sa a matsayin ahalin Gidan Rev. Anderson.
~~~~~
Washegari tun gabatowar Asuba ya tashi ya shiriya da nufin zuwa Masallacin da yake jagorantar limanci
a cikinsa,Bai Kai ga fita ba har sai da ya shiga Apartment d`in Gimbiya Ayush,barcinta ta ke cikin
kwanciyar hankali da alama dai babu abinda ya same ta ta samu barci,cikin kwanciyar hankali da
natsuwar Zuciya ya nufi Central Mosque kano Wanda ya ke near Emir Place,duk in yana Gari shi ke
jagorantar su a limanci,bayan gabatar da Sallahr Asuba ya fara karanta masu littafin Buguyatul
Musulimina,inda ya ke karanta masu babin Zina.
"Ku sani Zina bala'i ce,Zina masifa ce, Zina alfasha ce Mai girman gaske,Zina tozartar da Kai ta ke,ba
wai iya kunyar duniya ta ke sawa ba,takan zubar da k`ima daraja ga duk Wanda ya ke yinta Allah
Subahanahu Wata alah ya ce a cikin suratul Israel, ((Wala takrabu zinah inahu kana fahishatan wa sa'a
sabilah,haka ma a suratul an'am yace wala takribul fawahisha ma zahara min ha wa bad`ina)),ku sani
Zina daud`ar Zuciya ce,kar Kai alfahari ko jin kai don ka kasance me wani nasibi da ka ke salwantar da su
ta hanyar aikata alfasha,kar Kai alfahari don yau ka mallaki mota ka na d`aukar `ya`yan mutane a ciki
domin ka lalata ma su rayuwar su,kar kai alfahari don ka kasance cikin jerin mutanen da suke da dukiyar
da za su ita kama ko wanne d`aki a cikin hotel domin yin lalata da `yar wani,ka sani itama d`iyar wani ce
uwar wani,Kuma matar wani,haka kazalika k`anwar wani ce,ya zaka ji in ka wayi gari ka ga wata ta daga
cikin jerin sunayen da na lissafo naka a irin wannan matsayin,shin hauka za Kai ko mutuwa za kai?,ke
kuma na dawo gare ki `yar'uwa,ba abinda ke kai ku Mata ga halaka irin wannan daga kwad`ayi sai son
duniya,son sai kin Kai matsayin da ba ki kai ba,ki zubar da mutunci ahalin da Kuma zuri'ar ku gabad`aya,
wai yanzu lamari har yai tsamari ba ga `yan mata ba ba Kuma zawarawa ba,Mafi k`ololuwar tashin
hankali wai har da Matan Aure wa iya zubillah ki ji tsoran Allah ki zauna a iya matsayin da ki ke,hakan ne
kawai zsi sa ki zauna lafiya har nan gaba ki haifi `ya`yan da za a iya alfahari da su",haka ya cigaba da da
wa'azantar cikin d`acin Zuciya game da abinda ya ke magana akan shi,da su har zuwa sanda su ka tashi.
Kai tsaye part d`in Gimbiya Ayush ya nufa cikin sa'a ya iske har ta farka tana ma kitchen Kai tsaye can ya
nufa cikin murnar ganinsa ta nufo shi da cewa "Good morning my beloved husband fatan ka tashi
lafiya?",sai da ya janyota jikin shi kafin ya ce da ita,"Me yasa za ki fito a irin wannan lokacin bayan kin
san jikin ki ba kwari ne da shi ba,kina buk`atar hutu da kulawa me zai sa ki takura kan ki",sai da ta
shagwa`be fuskarta sannan ta ce da shi,"Ina jin yuwa ne fa,shi yasa na fito,ka ga ma gashinan na d`ora
ruwan zafin na rasa me zan dafa,komi ya fita a Raina bana jin son cin komi",ta kai zancen ta na mai raba
jikinta da na shi,ta koma ta na mai jawo flak's ta fara had`a shayin Coppe,cikin yanayin girmamawa ta
mik`a ma sa.
Hannunsa ya d`ora akan Cup d`in ba tare da ya amsa ba sai Mai maida cup d`in yai saitin bakin ta tare
da cewa,"A yanzu kin fi ni buk`atar shi don haka maza bud`e bakin ki ki amsa","Ba na son Shan shi fa","Ki
daure ko kad`an ne ki sha zai miki amfani",ba dan ta so ba haka ta bud`e baki ta fara kur`bar shayin
Coppe,sai da ta kusa shanye shi duka kafin ta ture bakin ta a jikin Cup d`in gami da cewa
"Yanzu na Sha nawa saura na ka,bari in had`a maka na ka",ta Kai zancen ta na k`ok`arin had`a masa.
"Ki bar k`ok`arin wani girki na sanar da su Ummiey ,sunanan tafe kan hanyar su duba ki,nadan za su zo
maki da abun kakaci don haka ba buk`atar ki wahalar da kan ki","Sai da ta zaro idanunta waje kafin ta
ce,"Haba Sweathert yanzu ashe sai da ka sanar da su abinda ya faru ?","Ya za ai bazan sanar da su
ba,sufa d`in ahalina ne dole zan sanar da su ,su taya ni jimamin rashin gudan jinina da na yi,Kuma ya can-
canta su zo su duba halin da ki ke a ciki ai","Na fa ji sauk`i fa Honey",Tukunna dai ni Banga alama ba".
Tun dawowar sa Gidan Ummu Nurain ke faman Kai kawo ganin ya nufi apartment d`in Gimbiya Ayush
ba k`aramin sake tunzurata yayi ba,tun tana lissafa seconing, minutes har ta kai ta kasa iya rik`e kanta
cikin mak`ura Kuma k`ololuwar fushi da Kuma dokin shed`an da ta hau ta nufi apartment d`in.
Gab da Gimbiya Ayush za ta Kai Cup d`in saitin bakin sa Ummu Nurain ta shigo kamar wacce aka
hankad`ota,har sai da Gimbiya Ayush ta d`an ji tsoro ta ja baya, kafin wani cikin su ya samu damar cewa
komi ta riga su da cewa,"To k`anwar karuwa,mara Zuciya,Mai burin son ta raba ni da mijina ,shed`aniya
kawai,ni har yanzu ban ga ribar da Auren ki ta kawo ma na a cikin Gidannan ba,wai in tambaye ki Dan
Allah har sai yaushe za ki bar ni na zauna lafiya da Mijina?"......"Hold on Zeenat me yake damun ki ta ya
za ki shigo har cikin Part d`in ta kina mai binta da munanan kalamai haka Anya ki na cikin hankalin ki
kuwa?".
Sai da ta rausayar da kanta gefe kafin ta ce"Abu Nurain Kana kashe ni da mamaki,a fili ka ke aikata
rashin Adalcin ka Amma da zaran na yi magana sai ka wayance ka nuna kamar ma ba kasan komi game
da abinda ka ke aikatawa ko yake faruwa ba,ka sani gab ka ke da ka kai ni k`arshe hak`urina ya k`are".ta
Kai zancen ta na mai juyawa ta koma kan Gimbiya Ayush ta na mai tamke fuskarta tare da k`ank`ance
idanunta saboda tsabar masifa,"Ki sani na yi alk`awarin tarwatsa Shirin ki ta kowacce irin hanya sai
aniyarki ta koma kan ki muguwa Mai bak`ar aniya"...."Wai me ya ke damun ki haka ne ko kin fita daga
cikin hayyacin ki ne Zeenat eyeh ?".ya kai zancen ya na mai shan gabanta ya shiga tsakanin su dan ya ga
ba abinda Zeenat take so ko yunk`urin yi da ya wuce ta ga ta Kai inda Gimbiya Ayush ta ke.
"Kin ga Ummu Nurain ki kwantar da hankali ki domin wallahi ba abinda zuciyar ki ke zargi ne ya faru
ba,ya zo duba ni ne ba ni da lafiya ko ba ki samu labarin na samu miscarrage ba?"."Hmmmmmm kar ki
wani yi yunk`urin son fahimtat da ni sabon karatu ko darasi game da munafunci ko Kuma kusisina irin
taki domin kaf na gama biya alon rayuwar ki tas na shanye,Abu d`aya na ke so da ke ki shiga taitayinki
domin kowa ya san karo da kura ba dad`i".
A fusace Jaheed ya Muna Mata hanyar fita ya ce ,"Ki `bace min da ganin tun kafin Zuciyata ta sa na
aikata ba dai-dai ba a kan ki",..."Idan Kuma na k`i fa sai ka Dake ni na ce maka sai ka dake ni?,haba na
gaji wallahi na ga alamun nema ka ke kai da matar ka ku kai ni kushewata tun kafin lokacina ya yi haba
dan Allah,ka ji tsoran Allah fifiko da ka ke nunawa ya Isa haka ma na,ni fa `yar'uwar ka ce ko ka manta da
hakan ne".
"Ke ce dai ki ke manta ko ke wace ce da Kuma matsayin ki a cikin Gidannan,ki sani matsayin ki ya
zarce wanda ki ke ba kan ki,Ina biye ma ki gami da d`aga ma ki k`afa ne saboda wasu dalilai Amma ki sani
kina gab da Kai ni k`arshe Gimbiya Ayush fa mata ta ce kuma ta sunna me ye aibun Dan na zo inda ta ke".
"Eh ai na sani Kuma na gani,hakan ne ma yasa ka ke d`aukar hak`k`ina kana kawowa wurin ta kana cin
amanata ko",ta Kai zancen fuskarta na k`ara bayyana d`aci da zafin abinda ta ke ji a Zuciyar ta.
Cikin rawar jikin Gimbiya Ayush ta matso kusa da ita tana Mai cewa,"Aa Ummu Nurain na rantse maki
ba abinda ki ke tunani ba ne ya faru ba,ya zo duba ni ne ya ga ya na tashi saboda rashin lafiyar da na
kwana da ita Amma bayan haka ba wani abu a tsakanin mu".
"Kin ga Gimbiya Ayush bar ta ta yi duk tunani da zata yi,ita ya shafa,in ta so ma ta d`auka akan
shimfid`a ta zo ta iske mu,duk matsalar ta ce wannan Ina da damar aikata fiye da haka,ita d`in mata ta ce
ta sunna,ki sani ko jiya na bar ki da abinda ki ke so ne don son dakatar da fitinar da ki ke son haifar da ita
a wannan lokacin,shin hankali ki bai kai kan za ta iya shiga cikin wani Hali ba a wannan Daren,in ta samu
wata matsalar da wanne baki zan iya kare kaina,ya ya ki ke ganin idan abun ya zo da k`arar kwana da
wacce fuska zan kalli iyaye da ahalinta,shin kina tunanin zan iya yafe ma kaina akan haka,Kuma da wacce
fuska zan cigaba da kallon ki da ita,ke kullum hak`k`in ki ki ka sani ba ki duba da hak`k`in Wanda ki ke
tare da shi,ta ya za ki zauna lafiya da irin wannan halin,a taya za ki haka za ta faru",Ya Kai zancen a
tsawace,tabbas ta fara kai shi bango har ta kai ga fusata shi.
Ganin haka da Gimbiya Ayush ta yi yasa tai saurin kama hannunta tare da cewa,"Kinga zo mu je zan
maki bayani yanda yanda za ki fahimta kin ga ranshi ya fara ɓaci akan wannan maganar".
"Dallah Malama rufa min baki duk ba ke ki ka haddasa komi ba Munafukar banza munafukar wofi",ta
kai zancen tana Mai hankad`ata baya cikin tsautsayi ta tafi zata fad`i Bata Kai ga fad`uwar ba Amma
ruwan zafin da ta d`ora hannunta ya bugo shi ruwan ya kifo mata a saman k`afarta,a gigice ta saki k`ara
gami da sallallami d`auke a bakinta tana mai cewa,"Honey shikenan na k`one ,ta k`ona ni,k`afata
zafin,zafin ko ina".
A rikice a rude ya nufeta yana Mai kama k`afar domin ganin abinda ya same ta,sakin k`afarta yai ya
koma kan Zeenat da jikinta ya fara rawar,kafin ta yi wani yunk`uri ya sauke mata mari hagu da dama,rasa
ma me zai ce da ita yai sai daga baya ya koma kan Gimbiya Ayush ya sunkuce ta ya bar kitchen d`in da
ita.
Wasu zafafan hawaye ne suka fara zubowa daga cikin idanun Ummu Nurain,wannan wacce irin fitinar
da bala'i ne ya sauka a cikin Gidanta,idanuwanta a rufe ta nufi part d`in ta ko gabanta ba ta gani.
A parlour ya sauke ta ya nufi sashen shi cikin hanzari ya d`auko first aid box ya fara bata taimakon
gaggawa.
"Kin ga bari in d`auko maki kaya ki sauya mu tafi Asibiti da buk`atar a duba ki da kyau",Cikin yanayin
wacce ta ke cikin jin zogi ta dakatar da shi da cewa,"Aa ba sai mun je ko ina ba ban wani k`one sosai
ba,zan ma iya taka k`afar bari ma ka gani".
Shigowar su Umma Jamila Mama Hadiza,Safina da kuma Biba domin dubiyar jikin Gimbiya Ayush ɗin ce
ta ɗan ja hankailinsu.
"Aa Jaheed me yake faruwa,na ga Zeenat ta fita daganan a cikin wani yanayin Kuma mun shigo mun
ga Gimbiya Ayush a irin wannan yanayin",Mama Hadiza ta tambaye shi.
Cikin d`acin Zuciya ya ce da ita,", Zeenat ce to k`onata saboda tsabar rashin hankali da bak`in
kishinta","Subahanallahi garinya ya haka ta faru,wannan ai hauka ne,Asibiti ai ya kamata mu tafi ba wai a
tsaya a gida ba ",
"Haka na ce Amma ta ce wai ba sai anje ba","A'a wannan ba Mai yiwuwa ba ne,tashi maza mu tafi tun
kafin abun yai tsamari",cewar Momy Hibba.
Hankali a tashe Gimbiya Ayush ta so hana tafiyan Asibitin don gudun kar abinda take k`ok`arin
`boyewa ya tuni nu,kar k`ilu ya jawo bau,Amma Ina hakan Bata samu ba domin ba tayi nasara ba,ba dan
ta so ba haka suka tafi Asibitin.
*JADEEDAH*
STORY & WRITTEN BY :
(*Cwt~Sumiey*)
Marubuciyar littafin
MENE NE ABIN YI ?
KARAGAR MULKI
And now.....*JADEEDAH*
*YOTA*
BOOK 1
https://whatsapp.com/channel/0029VapqU8C002T5Bz8RSQ0a
PAGE 27 ❤
"Anya Gloria ba akwai wani ɓoyayyen sirri da ke wanzu tsakanin Richal da Jadeeda ba ?",Mom
Rebecca ta faɗa bayan sun gama yin dinner.
Shiru Momy ta yi ta kasa iya cewa komi sai can daga ƙarshe ta sarƙe da miyau, saurin ɗaukar Cup ɗin
ruwa ta sha sakamakon ƙwarewar da ta yi,ko ta samu ya lafa.
"Mom wannan wacce irin magana ce,me ya kawo ta,kamar ba ta da muhalli a irin wannan wurin
","Hmmmmm Gloria kenanan dama na san irin haka ce zata faru,ba lalle ki yarda da duk abinda zan faɗa
ma ki ba a yanzu ba,amma ki sani tuni zuciya ta daɗe da fara kawo zargi kala daban-daban a cikin
tarayyar Richal da kuma Jadeeda"...."Mom zargi fa haramun ne,kuma ke fa tamkar Uwaki ke a gare su
wannan bai kamata ya fito daga bakin ki ba",Girgiza kai Mom Rebecca tayi kafin ta ce,"To Shikenan
tunda haka ki ka ce na bar maganar ba zan sake danganta su da irin wannan magana ba tunda baki yarda
ba",tana kaiwa nan a zancenta ta tashi ta bar mata dinning ɗin gaba ɗaya.
Tun bayan fitar Granny da ga dinning room ,Momy ta shiga cikin ƙololuwar tashin hankali, Zuciyar ta sai
faman saƙa mata munanan tunanin ta ke, kwakwalwar ta cushe,ta kasa samun natsuwa balle har ta
samu damar da zata samu makama a cikin zancen,tun tasowar Jadeeda ta san akwai kyakkyawar alaƙa a
tsakanin su,ya kan ɗauki dukkanin wani lamarin ta da muhimmanci baya taɓa manta wani abu da ya
shafeta,duk da kasancewar ba a ƙasa ɗaya suke zaune ba hakan bai hana shi halartar duk wani abun da
zai sa ta farin ciki,shaƙuwar su takai matuƙa har ta kai ya fi kowa sanin sirrikanta da kuma abinda take
so,sai dai ko ɗaya bata taɓa kawowa a ranta cewa da akwai manufar hakan ba,sai yanzu zuciyar ta ta
fara kawo mata hakan a matsayin zargi.
"Kai a'a hakan ma ba zai yiwu ba,Richal ba zai taɓa aikata min irin haka ba,ya na da hankali ya san
girman sirrin da ke lulluɓe acikin wannan lamarin ba zai aikata haka ba",Gloria ta faɗi hakan ta na mai
cigaba da kaiwa da komowar da ta ke.
"Idan kuma hakan ta kasance fa yake nan ?",wani sashe daga cikin zuciyar ta ya sanar da ita haka,sai
da bugun zuciyar ta ya ƙaru kafin ta dafe saitin wurin tare da cewa,"Shakka babu kuwa da ya aikata
babban kuskuren da bai taɓa aikata shi a rayuwarsa ba,zai yi dana sani mai girma,har sai takai shi ga jin
dama bai bari sakarar kuma mayaudariyar zuciyar sa ta rinjaye shi ga aikata abinda ya aikata ba".
Tunani ne ya cinkushe mata kai har ta kai ga ta fara iya daina gane komi ji da ganin ta sun fara gushewa
,kanta kuma na tsananta mata wajen sarawa.
Amma duk da hakan ta kasa iya dakatar da kanta game da tunanin da take, abubuwa masu yawa sai
yanzu suke zuwan mata,misali irin yanda suke ba junan su kulawa da kuma yanda shaƙuwar su take,kafin
ka ce me tuni ta fara ganin duhu a cikin idanunta da ƙyar ta samu ta daga bango ta isa bedroom ɗin ta ta
zube a kan shi wasu zafafan hawaye na son zubo mata amma zuciyarta ta ƙeƙashe kwata-kwata ba ta
son ta yarda da zarge-zargen da suke kai kawo mata a cikin ranta,balle har ta yarda da su.
"Anty Jee wai ina za ki ne dare fa ya fara yi na ga sai faman kwalliya ki ke,is there anything special da
ki ke expecting ɗin sa ne?","Yeah off course ko kin manta Uncle Miey ya na can yana jirana,zai yi Surprise
ɗina da wani abu mai matuƙar muhimmanci,so ya ki ga fitar tawa ta fita ko in sake wata",ta kai zancen
tana mai jujjuya jikinta yanda zata ganta sosai,sanye ta ke da mini skect sai wata half ɗin riga mai hannu
guda,wacce ko cibiyarta ba ta rufe ba,ƙafarta sanye da high heel shoe,gashin kanta ya sauka har saman
shoulder ɗin ta,komi nata shigar red and black, skect da bag ɗin ta black sai rigar jikinta da shoe ɗin ta
red.
Da yatsun hannunta ta yi mata alamar ta kai maƙura,"Am bari in ƙara fiddo da Anty Jeee ɗina",ta kai
zancen tana mai saukowa daga kan bed ɗin da take ta ɗauko eye glass black ta sanya mata,gami da tsara
mata simple make up a saman fuskarta,sai da ta ƙara yi mata ɓarin mabanbanta tauraruwa a jikinta kafin
ta juyar da ita saitin mirrorn dake ɗakin gami da cewa da ita,"Ya ki ka ganki yanzu nasan in ku ka haɗu
da Uncle R ba zai iya noticing ɗin ki da sauri ba".
Dariya Jadeeda ta saki gami da kai ma Nora bugu ta goce tare da cewa,"Ba kyau zan yi ba ko da suffa za
a sauya min in har Uncle Miey zai iso gare ni da bugun zuciya kaɗai ya isa ya gane ni,balle kuma wata
kwalliya da ko matakin Princess ban kai a kira ni da ita ba","Wa ya gaya maki haka ai Auntyna ta wuce da
wannan matsayin ,sai dai a kira ki da Queen ba Princess ba","Ma za ki cigaba har wani ya jiki,da anzo zan
tsere jikinsa in ce ba ruwana","A haba ai nasan ba za ki aikata hakan ba,ke ɗin ta dabance,za ma ki iya
ɗaukar laifin akan ki,saboda tsabar ji da ni da ki ke kin san wani time ɗin ina mamakin yanda wasu
abubuwa na mu suka sha ban-ban da na ki,misali yanayin hasken fatar ki,ɗan ƙaramin jiki da ki ke da shi
babu wani abu guda ɗaya wanda ku ke kamanceceniya da shi da wani a Gidannan komi na ki so special
ke ka ɗai ke da irin sa".
Ta buɗe baki za tabata amsa Martin ya shigo a hargitse kamar wanda aka watso shi , Muryar sa na
rawa yace da su,"Momy....Momy ....jikinta ya motsa tana can bata iya gane komi da alama ta na