Author : Cwt Sumiey Category : African Stories & Novels
gani ba sai yanzu da aka nuna ta ta ganta,da
hanzarin ta ta isa gurin ta na mai haɗa ta da jikinta tana mai lallashinta".
Biba ce ta ɗan matso kusa tare da cewa"Mama ko dai za a sa ta tafi Gidan su ne,ko hakan zai sa Yayah
Jaheed ya samu sauƙin abinda ya ke ji game da ita,in kuma ba haka ba bamu san ta inda za mu shawo
kan matsalar ba".
"A'a babu inda za ta har sai ta faɗa mana duk abinda ya faru in kuma ta ƙi sai mu danganta lamarin da
iyayenta,domin a yanzu ita kaɗai ce za ta iya sanar da mu asalin gaskiyar abinda ya faru,shi dai a wancan
halin da ya ke ba mai iya sauko da shi dan yanzu".
Cikin ɗacin zuciyar da ya fara ziyar Gimbiya Fadeelah ta tambaye ta da cewa,"Aunty Gimbiya me ki ka
aikata, wanne irin laifi ko zunubi ne ki ka aikata da har ki ka cancanci a yi maki wannan taron
gangamin ?","Fadeela dan Allah ki dakatar da su kar ki bari su kira Fulani ko Me martaba su sanar da shi
abinda ya ke faruwa,dan wallahi nasan ba za su hukunta ni ta daɗin rai ba".
"To in har ba ki son haka ta faru to ki sanar da mu abinda ki ka aikata ma ɗan mu duk yabi ya fita a cikin
hankali da tunanin sa"..
Sai da Gimbiya Ayush ta runtse idanunta kam jikinta ya ƙara rawa kafin ta fara magana muryarta na
rawa,"Asiri na da na daɗe ina binnewa a cikin Gidannan ne ya tuni...","Asiri...asiri kuma wanne irin
asiri ?","Ya kamani dumu-dumu muna fira da ƙawata akan yanda zan ...zan zubar da Cikin da ke
jikina,bayan na yi niyar zubar da shi tunda farko Allah bai yi ba,duk yawan missacarage da na ke ba na
Allah da Annabi ba ne ba ni da kaina na ke shan magani ko allura cikin ya zube,ba yau na fara aikata
hakan ba,amma Allah na rantse maku sharrin sheɗan ne,haka ba za ta sa ke faruwa ba,ina son Mijina,Ina
son zama da shi dan Allah ku ba shi haƙuri kar ya kore ni".
Sallallami sosai Yayah Hanne ta saki kafin ta ɗora da cewa,"Ai lalle dole ne ki ke kuka,ke ko wacce irin
Mace ce ke haka,me ki ke nema a duniya da har ya ja ki ki ka aikata wannan ɗanyan aikin,gaskiya kin ba
ni kunya,dole ma yake cewa ki tafi Gidan ku baya ma ko son ganin ki balle ya ji Muryar ki,wace ce ke me
ki ke taƙama da shi,da har za ki riƙa watsar nasa da jinin sa a rariya,ba sau ɗaya ba sau biyu va sai ka ce
ƴaƴan shegu,dan haka tun da wuri ɗau hanya maza a tafi a je a sanar da iyaye abinda aka aikata"..."A'a
Yayah Hanne abun bai kai haka ba,ba sai ta kai ga tafiya Gidan su ba maganar za ta yi tsawo da yawa,mu
bi komi a hankali,mu tafi da ita zan zuwa gidanmu in yaso ko zuwa gobe ne sai mu zauna mu tattaunawa
akan batun kamar hakan sai ya fi",","A'a ko da wasa ban aminta ba,ta tafi Gidansu itama Iyayenta su san
irin kuskuren da ta aikata,ai wannan magana ba ta wasa ba ce, Allah kaɗai yasan iya adadin yaran da ta
murƙushe ta niƙe su gami da watsar da su a rariya dan haka ta tafi Gidan su,ko ma meye ma biyo
sawunta nan",Nan fa hankalin Gimbiya Ayush yai ƙololuar tashi iya tashin hankali ta gani,babban abinda
ta fi tsoro Maganar ta koma kunnen Me martaba don ta Fulani mai sauƙi ce,haka dai tai ta ƙoƙarin ganin
sun barta a ɗakinta amma fafur Yayah Hanne ta hana,in Momyn Hibba ta bude baki za tai magana sai ta
dakatar da ita, ƙarshe Fadeela ce ta tasa ta don dole su ka tafi ba dan ta so ba,
Haka su ka ɗunguma su duka su ka tafi can main house ɗin nasu aka bar Ummu Nurain cike da tarin
mamaki,a ka barta daga ita sai Jaheed da bai da buƙatar kowa a kusa da shi.
Part 45
Jiki a sanyaye Ummu Nurain ta iso kusa da inda ya ke zaune ta aje masa Abincin da ta kawo masa tana yi
tana satar kallon shi,har ta miƙe za ta bar wurin ta dawo ta zauna ta fuskance shi da cewa,"Dan Allah ba
dan halina ba ko yaya ne ka ci wani abu daga cikin abinda na kawo maka,ba zan iya jure ganin ka a cikin
irin wannan yanayin,kuma ga shi tafiya za kai mai nisa ya kamata ka ci wani abun,dan Allah".
Shima gyara zaman shi yai tare da cewa da ita,"Ki yi haƙuri,na yi maki tsawa,na horar da ke ba bisa
laifin ki ba,ki yafe ni kinji Mata ta".
Wata ajiyar Zuciya Ummu Nurain ta saki mai ƙarfi,kafin hawaye su biyo bayan ta,ba ta ce komi ba kan
abinda ya ce sai cewa tai,"Me zan zuba ma ka,ko Black bhazar Coffee zan fara haɗa maka",ta kai zancen
tana mai ƙoƙarin buɗe plaks ɗin,hannunsa yasa ya riƙe na ta tare da cewa,"Ba abinda zan sha matuƙar
ba ki furta kalmar yafiya a gare ni ba,zan zauna da da yunwa har in tafi Bazan ci komi ba".
"Ka bari in haɗa maka,domin Ni ban ji zafin ka ba,kawai dai na ji ba daɗi da dana ga laifin wata ya
shafe ni,kuma nasan kaima hakan ya faru ba don son ranka ba","Na gode da wannan karamcin na
ki,amma ina gani kamar Babban Gida ya kamata ki koma har zuwa san da zan dawo bai kamata kina
ɗauke da irin wannan Cikin a ce ,ki zauna ke kaɗai duk faɗin shi","Hmmmmm in ka ce in tafi zan tafi,haka
ma in ka ce in zauna zan zauna domin ni gareni wannan Gidan ya fiye min ko'ina,na fi son in zauna a cikin
sa kamar Sarauniya","Haka ne amma saboda tsaran lafiyar ki zai fi kyau ki tafi can","To zan tafi Abu
Nurain amma dan Allah in ka dawo ka rage wannan yawan tafiye-tafiye mu Ahalin ka muna buƙatar
ka,mu na san ganin muna samun lokacin ka ko yaya ya ke",.
"Zan duba hakan Ummu Nurain amma ban miki alƙawarin a kan hakan ba,domin duk ɓangarorin guda
biyu duk sun zame min kusan dan dole,daga ɓangaren yaɗa Addini sai kuma ɓangaren Ceton rayukan
muta ne,to kin ga a cikin su ba wani na bari","Ya kamata ko yaya ne a duba magabana,ko ba yanzu
ba","To shikenan zan duba in Sha Allah","Yauwa Abu Nurain bari in je in haɗa maka sauran kayan da za
ka tafi da su,domin na fara ɗazu na aje gaba ɗaya hankalina na kan ka saboda ba ka ci komi ba","To bari
in zo in taya ki ,in muka gama da nawa sai mu haɗa naki ke da Nurain","A'a zauna ka ci Abinci ka na
hutashshe ka yanzu zan gama".
√√√√√√√√√√
“Sister Zahara Komi ya kammala ko?", Jadeeda ta tambaye ta a hankali.
"Komi ya kammala Jadeeda kamar yanda ki ka so,amma dai...",ta ɗan dakata ta na maida hankalin ta
akan Jadeedar.
"Kai na gode Allah,na samu natsuwar ruhi da jin haka"."Amma Jadeeda ba ki ganin hakan a matsayin
babban kuskure ta ya za ki ce za ki bar gida, Revered Anderson ya dawo ya tsawatar game da
lamarinnan,kuma jikin Madan Gloria yayi sauƙi komi fa a hankali ake samun sa" .
"Sister Zarah kiyi haƙuri amma ba zan iya janyewa daga wannan tafiyar ba,nasan kin girme ni,mun zauna
a tare cike da amana da kuma mutunta juna,ba za ki bani shawara wacce za ta cutar da ni ba,ina baki
haƙuri akan ƙin ɗaukar shawarar ki a wannan karon".
Sister Zahara ta kalle ta na ɗan lokaci kafin ta ce da ita da cikin taushin murya da son shawo kanta, "Ke
kin san, akwai bambanci tsakanin guje wa matsala da kuma fuskantar ta da zuciyar da ba ta jin tsoro,shin
dan me zai sa ki yanke wannan hukuncin?,wanda zai iya jefa ki a cikin halaka".
Jadeeda ta yi shiru. Idonta ya cika da hawaye, zuciyarta kuma na bugawa.ta dubi Sister Zahara tare da
cewa,"Bazan iya ba....ba zan iya janyewa daga wannan tafiyar ba,ina jin acan ne kawai zan samu salama
da kwanciyar hankali,komi zai koma Normal idan ya kasance bani nan,domin kumi ya faru a sanadina
ne,Ni ce silar komi,domin Ni sheɗan ya samu mafaka a cikin Zuciyoyinsu,za su dawo cikin hankalinsu,
natsuwa da kuma tunanin su,idan komi ya lafa zan dawo".
Sister Zahara ta bude Jakar da ta zo da ita ta ciro,Biza ta miƙa mata tana yi tana waige-waige don kar
wani ya ganta kafin ta ce da ita,"Kafin ki tashi, ki tabbatar kin gama da dukan sirrin zuciyarki. Kasar da za
ki je ba za ta share maki hawaye ba sai zuciyar ki ta yarda da ita ce take da ikon yin hakan."
Jadeeda ta kalle ta da idanunta a waje da son fahimtar me ta ke son cewa,ganin kamar abun zai ja ta ta
da nisa yasa ta amsa kawai gami da yi mata godiya tare da cewa,"Na roƙe ki ki riƙe min wannan a
matsayin sirri kar wanda ya sani,ba na son kowa yasan ina zani komi rintsi ko wuya zan dawo da lokacin
hakan yayi,na roƙe ki kin ji Sister Zahara"."Indai don ta ni ne kar ki damu,babu wanda zai ji,amma na
roƙe ki da ki sake duba wannan lamari Jirgin Ak Peace shi za ki bi zai tashi ƙarfe 4pm amma sai dai ki yi
haƙuri domin Jirgin ki Transcit Flight ne za ki iya samun delay na wucin gadi,amma dai by the grace of
God za ki isa lafiya , sannan zai fi miki ki sauka a garin Quebec ko kuma Montreal zai fi miki daɗin zama,
sannan ki kula da matakin lafiyar ki".
"For the sake of father lord ba abinda zai same ni,tamkar zan yi hijira ne, Jesus Christ zai bani kariya,ya
sani zan aikata hakan domin guje ma faɗawa daga halaka ko kuma sauka daga kan littafin shi littafin tsira
Bible","Amen Jadeeda zan taya ki da addu'a kin ji",ta kai zancen ta na mai dafa kafaɗar ta haka dai su kai
bankwana kafin Sister Zahara ta tafi da sauri ta na yi tana waige-waige,sai da Jadeeda ta tabbatar da
wucewar Sister Zahara kafin ita tama ta tafi bayan tabbata babu wanda ya gan su.
"Aunty Jeeyyyy lafiya me ya faru daga ina ki ke tunda safiyar nan,na shiga Bedroom ɗin ki na iske ba ki
nan ?",Nora ta tambaye ta"Ba ko ina na ɗan fita waje ne na shawo iska",ta ba ta amsa ba tare da ta
yarda sun haɗa ido ba kuma ta na magana ta na tafiya.
Da kallo Nora ta bi bayanta da shi,kafin ta gyaɗa kai ta cigaba da tafiya zuwa inda ta nufa.
Jadeeda tunda ta shiga ɗakin ta ke daman kai kawo,"Yanzu ya zan yi, Flight ɗina zai tashi around Four ya
kamata ace before time ɗin na bar Gida,kuma in bar Gida ba tare da wani ya farga ba ,domin in hakan ya
faru zai iya zama tsaiko ko dalilin da zai hana ni tafiya,to yanzu ya zan yi,gashi yanzu Past Eleven ya zan
yi,dole ina buƙatar tafiya da wasu kayan tunda ban san kowa a can ba,to ya zan yi?", shiru ta yi na wani
lokaci kafin ta ce," Yes na samo mafita".
Wurin Momy ta nufa ta iske ta kishin giɗe tamkar wacce ta lula wata sabuwar duniyar ta
tunani,"Mommy kina lafiya kuwa?", Murmushin yaƙe ta yi mata kafin ta gyara zama ta ce da ita ,"Me ki
ka gani ne Sweathert?","Mommy duk wanda ya kalle ki yasan You are not in the mood ba haka ki ka
saba zama ba ,komi na ki ya sauya kuma duk a saboda ni....","A'a Jadeeda ba laifin ki bane wadancan
shashan ne da su ka ja komi sune ke da laifi ba ke ba".
Rausayar da kanta gefe tai gami da saurin kawo maganar da ta kawowa kar ta bari damar ta suɓuce
mata,"Am Mommy wai Ezekeal ne ya kira wai da buƙatar in zo yana son gani na,wai wani case ya taso a
ɗaya daga cikin ƙauyukan da mu ke zuwa Bushara ,to na ce masa ba zan sami damar zuwa ba shine ya
matsa na ce bari in zo in sanar da ke".
"To mene ne a ciki Dear ki tafi mana ko ba komi za ki ɗan rage abinda ki ke ji in ki ka shiga cikin
mutane biside ma aikin lada zaki don haka ba ni da ja ki tafi sai kin dawo ,Yesu Almasihu ya albarkace ki a
tafiyar da za ki ki je ki dawo lafiya",sai da fuskar Jadeeda ta faɗa ta rungume ta gami da cewa,"That's My
Sweat Mom na Gode da samun ki da nai a ciki rayuwata".
"Nima na Gode ma Jesus da ya sanya ki ka kasance ɗaya daga cikin tsatsona,amma dakata ba zaki kai
4pm a waje ba ko".
Sai da Jadeeda ta yi jim kafin ta ce"Ehhhhh to ba lalle ba,domin case ɗin na wata ƙaramar yarinya da
ke fama da ciwon zuciya to muna son foundation ɗin mu yaɗauki nauyin aikin da za ai mata ne, da zaran
mun yi solving ɗin sa zan dawo buy the grace of God".
"Okay ki kula ki kira ni ki sanar da ni komi ke faruwa kin ji,in ma da buƙatar mu sa hannu a cikin
lamarin sai ki sanar da ni","Wai da na ce ina Martin ya ke ko shine sai mu tafi tare ban san tafiyar ni
kaɗai",ta ƙare maganar zuciyar ta na bugawa da ƙarfi da addu'ar Allah ya sa baya Gidan,"Sun fita shi da
Papa ɗin ku,ita kuma Nora Unexpected test ce ta taso ma ta tafi school sai dai ko kusa Driver ya kai
ki","A indai haka ne Gara in tafi ni kaɗai ,na yi driving ɗin da kaina amma kafinnan in wuce zan shiga
Church ɗin Our Lady Queen of Nigeria Pro-Cathedral","Kina ganin ba zaki sanya su ta jiran ki ba","A'a
Bazan jima ba zan wuce,ina so in ɗan yi addu'o'in ne kafinnan","okay ba matsala ina maki fatan alkairi sai
kin dawo".
Da wannan damar ta samu ta haɗa duk abinda zata buƙata tasa a cikin troly ta saɓa ta fitowa ta ci karo
da Ester wanda har sai da gabanta ya faɗi,"Aunty ina za ki haka na ga kin fito da sauri irin haka?",sai da
Jadeeda ta haɗiye yawun da ya tarar mata a baki kafin ta ce da ita,"Wanki zan bada na","Wanki kuma
Aunty ba akwai Machine ba?",Cigaba da tafiya tai kafin ta ce da ita,"Bana da buƙatar shi ",idanu Ester ta
zaro waje ta na mai cewa a cikin Zuciyar ta,"Anya kuwa lafiya,Aunty Jadeeda ba haka ta ke ba,ba ta
magana da mutun a irin wannan yanayin kuma na ga kamar unguwa za ta ,Uhmmmm ba ruwana",ta
ƙare zancen ta na mai tafiyarta abinta.
Kai tsaye Church ɗin ta nufa acan ta kwashe tsawon lokaci acan sai da taga gabatowar 4pm sannan ta
baro cikin Church ɗin ta samu wani ɗaya daga cikin masu aikin Cleaning a cikin Church ɗin ta kira shi gefe
guda ta ce da shi,"Ina son za ka yi min wani aiki zan biya anan take shin kana da interest akan shi?,zan
biya ka 50k anan take just delevering ɗin saƙo za kai min zuwa wani address da zan baka",zaro idanu
waje yai alamun zuciyar shi na son kuɗin kafin ya ce,"Anya ba akwai wani abu a cikin wannan aikin da ki
ke son sanya Ni acikin da ba,ma'ana akwai lauje cikin naɗi akan shi ba","Ba wata manufa a bayan
haka,tafiya ce ta gaggawa ta ka mani zan baka keyn Mota ta ka kai min ita,zuwa Gidan mu,da takarda da
zaka ba su in ka isa, simple shine kawai,na faɗa maka haka da iya gaskiyata ba zan cutar da kai ba,nan
guri mai tsarki mu ke,ba zan faɗa maka akasin gaskiya".
"To shikenan na yarda da ke","Amma ina so sai nan da 6pm za ka kai sauƙin",da to kawai ya amsa
mata ta je farking space ta nuna masa Motar tafidda trolynta ta ba shi keyn sannan ta tafi ta tari tacxi ta
nufi Airport kai tsaye.
Bayan awannin biyu da tafiyar Jadeeda a kai sallama a bakin gare ɗin Gare Akan ɗin Gidan ya leƙa ya ga
wani Magidanci tsaye da takarda a hannunsa ga kuma Motar Jadeeda tare da shi,"Lafiya Malam na gan
ka anan ko wani ka ke nema ne?",Gate Man ɗin ya tambaya.
"Eh wani daga cikin Halin Gidan na ke nema domin in isar da saƙon da na zo da shi","Kamarya wani
daga cikin Gidan kana da alaƙa da su ne","A'a kawai dai an bani saƙo ne,wanda zan fi son in ba wani ahali
na Gidan",Shiru Gate Man ɗin yayi kafin kuma ya ce da shi,"A'a ka dai fara sanar da ni abinda ke tafe da
kai sai in ji daɗin sanar da mutanen Gidan abinda ya kawo ka ba hakanan in tunkare su da labarin da ba
ni da wata masaniya akan sa ba","Zan dai fi son ka kiramin wani a Gidan sai a yi komi a gaban ja domin
Ni ban zo da wata cuta ba".....Isowar Nora wurin ya dakatar da musayar yawun da suke ,ta dakatar da
gami da tambayar Gate Man ɗin da cewa,"Baba Joshua lafiya na ga Motar Aunty Jeeyyyy a
waje ?","Nima yanzu na fito na iske ta anan da alama dai wannan mutumin ne ya zo da ita",da sauri Nora
ta maida hankalin ta akan mutumin da aka nuna da sunan shine ya zo da Motar,"Ina ka sami wannan
Motar,Ina mai Motar ta ke,meye haɗin ka da ita", wannan sune jerin tambayoyin da Nora tai mi shi a
ƙagauce da son jin amsar su.
"Kwantar da hankalin ki me motar da kanta ta bani ita gami da bani address ɗin wannan Gidan ta ce in
kawo ,in sanar maku tafiyar gaggawa ce ta risketa,ga wannan takardar da ta bani don ku tabbatar da
abinda na ce da gaske na ke",ya kai zancen ya na mai miƙa mata ,tana amsa ya juya yai tafiyarsa ba tare
da ya tsaya ba.
Ita kuwa Nora a hargitse ta shiga cikin Gidan kamar wacce aka biyo,tun kafin ta shiga ta ke kwalama
Momy kira,"Lafiya Nora me yake damun ki za ki shigo Gida a cikin irin wannan yanayin,sai kace
makauniya".
"Momy ina Aunty Jadeeda,ina ta tafi?","Nima abinda na ke tambaya kenan ki ka shigo",cewar Papa da
ke zaune a kan dinning suna cin abinci".
"Ohhh,ta tafi duba wata Yarinya mai ciwon zuciya ƙarƙashin Foundation ɗin su, Shikenan ko sai ki
samu wuri ki zauna kin shigo kina ƙoƙarin tada ma mutanen Gida hankali".....,"Kin kirata ko kuma ita ta
Kirani tun bayan tafiyar ta?",Papa ya tambaya.
"A'a na yi ta