Author : Cwt Sumiey Category : African Stories & Novels
ki ko,za ki shiga hannuna ne"...."Oh sorry ba haka nake nufi
ba,biside ma ai ni banga laifin ki ba you can fight for you love,but I beg you kar ki tada mana wata fitina
ki bari mu gama wannan bikin lafiya lafiya daga baya sai musan me zamu yi".
"Okay I promise you babu abinda zai faru,har mu gama wannan bikin lafiya, dama babban burina ki
bani goyan baya a cikin wannan tafiyar nasan in har hakan ta faru zanyi nasara",sai da Cecelia ta dafa
kafad`arta kafin ta ce," Don't worry I'm with you always, I will support you hundred percent, zamu shirya
komi yanda ya kamata,sai mun dawo da Broth Daniel kan hayar da ta dace,ko kin manta shi kad`ai ke
gare ni da zan iya Kira da sunan family taya zan barshi ya su`buce min,sai dai ki sani a can k`asan Zuciyata
ina jin tsoro kar Garin ean in dawo da shi cikin rayuwata ya su`buce min gabad`aya ".
"In Jesus name haka ba zata faru ba,komai zai tafi smoothly yanda muka tsara".
Shigowar Hibba sa`be da Jadeeda da ta koma barci ta dakatar da su daga zancen da suke yi," Am kuyi
hak`uri Na shigo muku without a knocking ba na son in yi knocking k`aryar ta tashi Jadeeda daga
barci,domin barcin bai nisa ba,ku fi to muyi breakfast d`in Abban Jadeeda ya dawo yana jiran mu".ta kai
zancen Zuciyarta na son hasko mata wani gi`bi da ta hango a cikin zancen na su,A'uxiyya tai gami da
watsar da zancen da Zuciyar ta ta take tsamata don son kyautata masu zato,kamar yanda Addini ya
koyar.
"Am sorry Sis mun tsaya firar yaushe gamo ne,kin San an kwana biyu ba a had`u ba", murmushi Hibba
tai tana mai juyawa tayi gaba a tare su ka nufi hanyar zuwa dining d`in,tunda idanun Gloria suka sauka
akan fuskar Abbakar k`afafuwanta su kai mata wani irin sanyi,kwarjini,kamala da haibar da ta gani
kwance akan fuskar suka sa Zuciyarta ta fara bugawa da sauri da sauri,a d`arare ta iya zama kan d`aya
daga cikin kujerun wurin,muryarta hard`ewa ta ce da shi," Brother Daniel Good morning "
"Morning Gloria how are you and how about you journey ?".
"Bro everything are okoy,kasan flight Na biyo so that's why tafiyan bai wani wahalar da ni ba"," That's
good Na ji dad`in hakan,what about Pastor Emeka,Momy Rebecca and your brother Richal ?",'Ahhh
they're fine duk suna lafiya,kasan Dad ya samu k`arin girma tun da dad`ewa, Momy ta zama woman
leader a Church d`in da Dad ke jagorantar,My Brox kuma ya na Canada karatu".
"Masha Allah labarin yayi min dad`i komi na tafiya yanda ya kamata,what about you,wanne mataki ki
ke, je a yanzu?".
Wannan tambayar ba k`aramin dad`i tai ma Gloria ba har wani blushing tafara yi gami da k`ara gyara
zaman rigar jikin ta kafin ta bashi amsa da cewa," Na fara masters anan Herbal institution dake nan
Lagos "....
" Haba mana my Brox,ya isa haka mana ,ku dakatar da wannan hirar mana ko kun manta muna da
tafiya mai nisa a gaban?","Hehhh Cecelia mene ne haka,shin kina son raba hirar zumunta ne komi ?,mu
fa d`au long time ba mu had`u ba".
Dariya Abbakar yai kafin ya shiga tsakanin su da cewa,"Bar ta zumud`i take ta na son zata ga groom to
be d`inta kin san ta yi spending almost a ten days ba tare da ta gan shi ba".
Baki sake Cecelia ta bisau da kallo ita kanta mamakin jin zancen da ya fita daga bakin sa tai,sosai suka
zage shi da Gloria suna tsokanar ta,duk abinda ke faruwa Hibba na can tana son barcin Jadeeda yai k`arfi
bata san abinda ke faruwa anan Parlour ba.
Abbakar ne ya cire baki ya na nai kiranta da cewa,"Madam a zo a bamu abinci we are felling hungry
",sai da Hibba tai k`asa da muryarta kafin ta mai do mashi da amsa da cewa," Please I'm sorry ina so
barci Jadeeda yai k`arfi ne,but please Cecelia ki yi sarving d`in ku kafin in zo ".
Zaraf Gloria ta mik`e tana mai cewa,"A zauna bari in Sarving d`in ,Na hutashshe ki", Jiki a sanyaye
Cecelia ta koma ta zauna ta bar Gloria da sarving d`in su domin ba zata so suyi jayayya a gaban Broth
Daniel ba,don gudun kar ya fahimci da akwai wata a k`asa,tunda yasan ba hakan a tsakanin su a can
baya.
Gab da Hibba za ta isa dinning wayar hannunta ta fara ringing, ganin kiran Mama Hadiza ya sa ta
fad`ad`a murmushinta kafin ta d`aga ta fara gaishe ta," Ina lafiya Auta ashe har yanzu baku tafi ba ?","Eh
Mama yanzu dai muke shiri zamu tafi ya mutanen Gidan ?","Duk suna lafiya yanzu ma Babanku ne ya ce
in sanar da ke ranar bikin Ummien Jaheed, Yayar ku (Yayah Hanne ta ke nufi bata fad`in sunan ta),da
kuna Umma Jamila za su zo nan Jos d`in su taya ku murnar gami da Allah sa alkairin ".
" Kai Mama na ji dad`in haka sosai Allah ya saka maku da alkairi ya biya buk`ata ya kuma baku aljanar
fiddausi","Amen Allah ya kai ku lafiya ya dawo da ku lafiya","Amen Mama,kin ga kuwa da na sani ai da
na kawo Jadeeda nan in su Ummie Maryam zasu taho sai su taho min da ita"......"Ahir d`in ki Hibba, ba ki
da hankali ne Yarinyar `yar shekara d`ayar za ki aje ki tafi wani waje har na tsawon kwanaki ba tare da ta
Isa yaye ba".
Cikin rawar murya Hibba ta fara bata hak`uri,"Mama Dan Allah ki yi hak`uri,wallahi haka nan na ji bana
son in tafi da ita,kamar wani abun zai iya samunta,gabana sai fad`uwa yake ".
"Addu'a za ki yi tayi,in sha Allahu ba abinda zai faru da ke,dole za ki hak`uri ku tafi tare can ma inda za
ku ahalinta ne danginta ne,suna da hak`k`i ki kai ma su ita su ganta suma,su Santa su Saba da ita".
" To shikenan Mama zan yi ta yin Addu'ar kamar yanda ki ka ce,da zaran mun Isa zan kiraki","Yauwa
`yar Albarka ki shafa min kan `yar rigima mai kukan banza,au na manta yau Jaheed da zazza`bi ya tashi
shiyasa bai zo maki sallama ba ",
"Ayyah Allah ya bashi lafiya zan kira Ummie Maryam sai in yi mashi ya jiki","To hakan yayi kyau amma
ki bari sai kun isa don da yaji ba ku tafi ba zai sanya rigima", To Mamma", da haka suka yi sallama ta
k`arasa zuwa dinning d`in.
Zuwan Hibba dining d`in ne ya rage ma Gloria rawar kan da take,cikin k`ank`anin lokaci suka gama
breakfast d`in suka sake had`a `yan sauran kayan da zasu had`a,Hibba ta goya Jadeeda, wacce har yanzu
take barcinta kana suka d`au hanyar zuwa Jos daga Kano
Sai da su kai tafiya mai nisa kafin Jadeeda ta tashi daga dogon barcin da ta sha,minti kad`an bayan
Hibba ta yi feeding d`inta ta fara kai hank`oran zuwa Inda mahaifin ta yake,"A'a Jadeeda yi zaman ki nan
wurin Momynki,ba zan iya d`aukar ki ba alhalin ina driving".
Duk yanda Abbakar ya so dakatar da Jadeeda k`i tai,babban burinta ta isa gare shi,ganin an hanata ya
ta fara kuka gami da ƙara son sai ta isa inda ya ke.
" Dama Na sani abinda nai ta gudu kenan ke ko kusa ba ki iya zama wuri guda tsaf",Ai ko kamar ta san
fad`a ta K`ara tsandarewa da wani sabon kukan.
Cecelia ce ta fara cewa,"Kai³ Momy ce tai miki fad`a to yi hak`uri kyaleta ba zata sa ashoben bikinnan
ba,kyauta za mu yi da nata",ta kai zancen ta na mai mik`a mata hannu,ba musu ta tafi wurinta
kasancewar ta Yarinya mara k`iwa.
"Wawooooo beautiful girl, ai sai yanzu naga fuskarta sosai,kai she's so beautiful,Babyn tamu
kyakykyawa ce ta zarcewa sa'a", cewar Gloria,da ita sai yanzu ta gamda dominsanda ta zo ta yi barci.
Murmushi kawai Hibba tai ba tare da tace da ita komi ba," Ai tukunna ma sai ma nan da wasu shekaru
za ki ga asalin kyau a wurin my daughter "," Maganar ki gaskiya ce Our Father Lord ya bamu Ikon ganin
wannan lokacin","Amen...Amen Gloria zan yi farin ciki in na riski wannan ranar kar ma ace in ga ranar
bikinta hohoho",Cecelia ta kai zancen ta na mai d`aga Jadeeda sama wacce sai faman wasa da gashin
attache da ke kanta ta ke.
"Yama sunan ta ?",Gloria ta tambaya ta,na mai amsar ta d`auke ta,Cecelia da take kusa da ita ta bata
amsa da cewa" Am sunan ta Jadeeda ",duk yanda Gloria ta so ta mai-maita suna kamar yanda Cecelia ta
fad`a amma ta kasa,madadin ta ce Jadeeda sai ta ta ce Jedeeda.
Sai a lokacin Hibba ta waigo tace da ita," Ba Jedeeda sunan yake ba Jadeeda ne, J d`in harafin a ne da
ita ba e ba".
"Oh Jedeeda, Na gane thanks for your correction", Gloria ta ce tana mai sakin fara'a akan fuskarta da
tunanin ta faɗa dai-dai.
"Ba Jedeeda ba fa Jadeeda", Hibba ta sake gyara mata a karo na biyu.
Duk yanda Hibba ta so ta gyara ma Gloria sunan ta fad`a dai-dai amma hakan ya faskara,kuma wani
abun Allah ita kuma ta kasa hak`uri ta barta ta kirata da Jedeedan,ita kuna sai faman mai-maitawa take.
A karo na ba adadi ta sake bud`baki ta gyara mata.
"Please Hibba ki barta ta kira da iya yanda bakin ta ya iya mana, tun d`azu sai faman abu d`aya ake
yak`i ci yak`i cinyewa"....
" Kamar ya in barta,kana nufin in barta ta cigabada da kiran sunanta da duk sunan da ya zo mata
komin munin ma'anarsa".Hibba ta katse shi k`asa Zuciyarta Na yi mata zafi from no way,ba tare da ta san
daga inda ya zo ko kuma dalilin zuwansa ba.
"No no no I don't mean that, but she try,she can't pronounced it very well, sai ki barta haka".
Sororo Hibba tatana kallon sa ba tare da ta iya cewa da shi komi ba,ba wai don ba ta da abin cewa ba
ne ba,a'a mamakin furcinsa take.
"Kin ga ba wai ina nufin wani abu na daban ba be ba,a'a just bana son abun yai nisa ne,but I'm sorry
naga ranki ya `baci I don't mean that, kuma ke ma ai kin san ina son a kirata da sunan ko,son sunan da
kuma ma'anarsa yasa na yarda har aka sa mata sunan".
" Hmmmmmm si shiyasa ka bada damar da za a rink`a kiranta da kowanne suna ba tare da la'akari da
kyawu ko munin sa ba,`yata fa muslmace ta ya zata rik`a kiranta da sunan kafu".....ta kasa k`arasawa
sakamakon zazzafan kallon da ya jefe ta da shi.
Ita kanta nan take danasani ta rufe ta, gabad`aya ta diriri ce ta rasa me ma zata ce.
"Kiyi hak`uri sister it's my mistake I'm regret ba zan k`ara furta sunan ba, har sai na iya,please I'm so
sorry".
Ko ta,kanta Hibba ba ta bi ba,babban burinta taga ta samu hanyar da zata bashi hak`uri amma ina ko
kallon inda ta ke bai sa ke ba,ranshi a `bace ya cigaba da driving d`in.
Kamar a mafarki wata babbar mota ta nufi kansu,damuwa,firgice da kuma rud`u duk sune suka
rufesa,gashi yana k`ok`arin sauke ko danne damuwar da yake a ciki,ga kuma firgicin abinda take
tunkararsa,amma ina duk yanda ya so ya hana hakan faru bai yiwu ba,sai fa gani yai su suna yawo a
sararin samaniya.
*JADEEDAH*
(It's a story of two love birds who are so different from each other )
STORY & WRITTEN BY :
(*Cwt~Sumiey*)
Marubuciyar littafin
MENE NE ABIN YI ?
KARAGAR MULKI
And now.....*JADEEDAH*
*YOTA*
https://chat.whatsapp.com/CWkZfMqvD4H0mtd7WW6Xbz
https://whatsapp.com/channel/0029VapqU8C002T5Bz8RSQ0a
BOOK 1
PAGE 13 ❤
Da k`yar mai motar da ke bayansu ya iya dakatar da tashi motorn,a gaban idon shi komi ya faru,rud`u
da tashin hankali duk sun baibaye shi,abun tashin hankalin shi kad`ai ne a cikin tashi motar,iya tashin
hankali ya ga tashin hankali, sai da motar ta tsaya dan kanta sannan ya nufi inda take, a yashe a k`asa ya
iske Hibba sai Cecelia da Abbakar da ke kwance cikin motar face-face da jini,da k`yar ya iya matsawa
kusa da su saboda hayak`in da ke tashi a cikin motar yana haki yana tari ya samu ya fiddo su daga cikin
motar,babbar motar da ta haddasa had`arin ya nufa shima da k`yar ya samu ya fiddo Wanda ya ke a
cikinta ya bugu sosai shima, ya gigita matuk`a Ainu da ganin yanda cikin k`ank`anin lokaci komi nasu ya
sauya karma Cecelia da ko fuskarta ba ka iya ganewa,a gabansa ya zube su sai faman salati da naiman
d`auki ya ke,ganin kamar Hibba na motsine ya sa ya garzaya da gudu cikin motar shi ya d`auki ruwa ya
watsa mata ,cikin Ikon Allah sai ga shi tana jan numfashinta da sauri da sauri.
Lokacin da idanuwanta su ka bud`e ta ga abinda ya faru da su ,kusan k`ara sumewa tai.
"Innalillahi wa'inna ilaihir raju'un Abbakar Abbakar,Na shiga uku baya motsi", saitin inda Cecelia take
yashe a k`asa ta nufa,tana mai jan k`afarta da k`yar wacce ta bugu a jikinta, sai dai tana kusantar wurin
tai baya a kid`ime,kuma a firgice,ko shakka babu ba rai a jikinta.
Kamar anyi ma hanyar baki tunda had`arin ya faru ,sai mutane suka d`auke daga bin hanyar babu
wanda ya zo wucewa,sai da aka d`au lokaci mai tsawo sai ga wata motor da mutum biyu ne a cikinta da
alama ma mata da Miji ne.
"Hubby da alama can accident akayi naga kamar hayak`i ne ke tashi a wurin"," Subbahanallah bari mu
matsa mu gani",nan ya Isa wurin da hanzarinsa suka fito suna mai nufar inda Hibba da wannan mutumin
suke tamkar mahaukaciya suka ga tana behaving,hankalin su ba k`aramin tashi yai ba sakamakon abinda
su ka ci karo da shi.
"Innalillahi wa'inna ilaihir raju'un ",shine kalmar da Hibba tai ta mai-maitawa," Cecelia me zan gani
haka ,wannan wacce irin munmunar k`addarar ce ta fito da mu".
Munmunar mutuwa Cecelia tai wacce in badan tare da ita suka fito tun daga Gida ba to da bayanda za
ai ta iya ganeta,da zaran Hibba ta matsa kusa da inda gawar Cecelia take sai wannan baiwar Allah ta
rik`ata ta tana mai son kwantar mata da hankaki gami da bata haƙuri
Hannunta na hagu wanda take tabbatar ma kanta ta samu karaya ko tsagewar k`ashi a jikin sa,a ka ta
d`ora shi ta na mai cigaba da salati.
Mutane ne suka fara taruwa wurin wasu har sun fara rik`eta,ganin yanayin firgicin da kuma rud`u da
take ciki.
Cak ta tsaya sakamakon tuna wani abu da ya fad`o mata a cikin ranta, "Jadeeda!......
Jadeeda!! .....Jadeeda!!! `yata kina ina ?,ban ganta ba kina ina,ban ga `yata ba,ku tai maka min ku nemo
min ko ku sake ni in nemo ,ƴata".
Jin wannan Maganar tata ne ya sa mutanen da suke wurin fara rarrabuwa domin su dubo ko dagaske
tana tare da d`iyar tata ne kamar yanda ce.
Har suka gama bulayin Neman su nan kusa da inda akai accident d`in ba su ga Yarinyar da ta ke kira da
`yarta ba,kai har inda babbar motar da ta kad`e su ta gangara sai da suka je nemanta amma bata,basu
ganta ba,ganin kamar dai firgicin ne yasa ta ke ikirarin ta taho da d`iyar ta ya sa suka dawo wajen da
accident d`in ya faru.
" Kun ga mutane bai kamata mu zuba ma bayin Allahnnan Ido a haka muna kallon su ba, kamata yai
mu kai su asibiti ko mu Kira motar ujila ta kawo masu d`auki",Cewar wani daga cikin mutanen da suke a
wurin.
Mijin wannan Matar da suka fara tsayawa wurin ne ya bashi ansa,"Tun zuwan mu nan wurin Na Kira
police sun ce suna zuwa,domin kasan ko mun kai su Hospital ba za a amshe su ba sai tare da police ".
" Wannan ai Maganar banza ce ta ya za ai ace mutane na cikin irin wannan halin,Na mutuwa da
rayuwa ace sai an jira wasu police ai wannan dokar banza ce dokar wofi, rayuwar su fa na cikin
hatsari,komi zai iya faruwa da su a wannan d`an tak`in lokacin ".
" To ya za muyi wannan dokar k`asa ce,dole zamu bita",...Dokar banza dokar da ake fakewa da ita ana
kashemana `yan'uwa ba zamu yarda ba ku d`auke su mu nufi asibiti da su ko zasu San wani taimakon da
za su yi ma su,ko da wannan da take Raye ce ,tunda ta ji ciwo sosai tana buk`atar taimakon gaggawa,ga
alamanan har a kanta ta bugu ban da sauran ciwukan da suke jikinta"........
K`arar da Hibba ta saki ce gami da kwacewa daga rik`on da wannan Matar tai mata ne ya dakatar da
shi tana mai cewa,"Wallahi Na zo da `yata,tare muke da ita,ga zanan goyantanan ga kuma feeder d`inta
harma da jakar kayanta kun gansu",ta kai k`arshen zancen ta na mai tarwatsa kayan a k`asa yanda zasu
gansu.
"Kai Matarnan tana da gaskiya ga alamanan da ke tabbatar da tare take da `yarta don haka bayin Allah
muk`ara hak`uri a sake dubata ko Allah zaisa mu dace a ganta ceton rai muke".
Duk abinda ke faruwa Gloria na wani k`aton rami da yake nesa kad`an da wurin da accident d`in ya
faru,yanayin yanda motar ta jujjuya a sama ne yasa ta watsar da ita can gefe,sautin hayaniyar da mutane
ke yi ce ta dawo da ita daga cikin hayyacinta, sai dai bishi-bushi take gani sakamakon buguwar da kanta
yai mata sosai.
Hannunta ta kai kan idanunta sai faman murzawa don son ta gano a ina take me kuma yake faruwa da
ita.
Da k`yar ta samu ta fara gani bishi-bishi,idanuwanta ne suka sauka akan Jadeeda da ke fidda
numfashinta sama-sama ko kuka bata iya yi,da sauri ta janyo ta jikinta tana mai jijjigata domin son ta
dawo dai-dai.
Jin motsin kusantowar mutane inda take ya sa ta sake lafewa yanda ba za su ganta ba,ta na mai kasa
kunne domin jin abinda suke cewa.
A bakin ramin su ka ja suka tsaya Wanda da wani a cikin su zai lek`a zai wuya bai ganta ba, Allah ne
kawai ya rufe idanunsu gami da hana su lek`awa cikin ramin, "Kai abokina na ga tashin hankali, gabaki
d`ayansu duk sun mutu in banda wannan Matar da ta ke faman neman `yarta ita kad`ai ce bata mutu
ba".
"Ikon Allah, k`addara ce ta kawo su da kuma kiran ajali