Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Jadeedah Complete Hausa Novel by Cwt Sumiey

Author :  Cwt Sumiey Category :  African Stories & Novels

Chapter   3 / 37

6K to 9K   out of 108.5K words

Hanne gami da cewa,"Ahir d`in ki Hanne anan a tafin hannunna a ka
haife ki,don haka ba ki isa ki goranta mata akan abinda ba ta ji ba bata gani ba".

"Au ashe babu dad`i Baba Asabe mai yasa ba ki dakatar da ita ba a lokacin da ta ke k`ok`arin cin zarafin
Mahaifiyata"....

Shigowar Baba K`arami ne ya dakatar da ita ran shi a `bace ya ce da ita,"Au dama abinda Baba Malam ya
turo ki ki yi kenan,me ya sa ki ka zo in kinsan tada ma mutanen Gidan hankali za ki yi ?".

" Yayah ta ya inaji ina gani zan barsu su ci zarafin Mahaifiyata a gabana kuma in kyale su,wallahi ba ta Isa
ba in yanzu ta sake cewa wani abu sai na maida mata da martani ".....

" Ba ki da hankali ne Hanne Baba Asabe k`anwar Mahaifin ki ce ta ya za ki tsaya ki na sa'insa da ita".

"Na san da haka K`arami,amma me ya sa kaf cikin Gidannan ba su da abokin rikici sai Mahaifiyata, na riga
da na dad`e da fahimtar su daga ita har Baba Asabe ba wani son mu su ke ba"....

Cikin matsananancin fushi Baba K`arami ya daka mata tsawa" Ki `bace min da gani tun kafin in sauke
fushina akan ki,ko dai ki koma Gidan ki in kinsan fitinar za ki tada mana ko kuma kije ki aikata abinda aka
Kira ki domin shi,ku kuma lokacin Sallahr magariba yayi kuna iya tashi ",duk yana magabar ne cikin fushi.
Kowa tashi yai ya nufi d`akina sa,ba tare da wani ya ce uffan ba,kowa ya san halin Baba K`arami yana da
hak`uri da kawaici,amma idan ran shi ya `baci bai iya fad`a ko fushi ba, sanin hakan ne ya sa ba Wanda ya
sa ke cewa komi su ka tashi.

Shima d`akin da Hibba ta ke a ciki ya nufa ran shi na jin suyar abinda ta aikata.

"Haba Hibba mai ya shiga cikin kan ki ta ya za ki zo da irin wannan batun ba ki zauna kin yi tunanin
abinda ka iya biyo baya ba,wai me ya sa baki ta`ba zuwa kin sanar dani abinda ya ke faruwa ba har sai da
komi ya lalace ?".

" Yaya Hanne mutumin kirki ne fa ya na da dad`in zama da kuma kyawawan d`abi'u "....

" Au abinda za ki fara kafa hujja da shi kenan,shin ba ki san kaf ahalin Gidannan ba wanda ke son
wannan Auren ba,hatta da Baba Malam ya biye ma ra'ayin ki ne kawai,amma ba wai yana son Auren ba
kafin in shigo nan na biya d`akin Mama na iske ta na zubar da hawaye kuma duk akan wannan maganar
Auren ne,shin ba ki tunanin wani abun ka iya biyo baya sakamakon rashin amincewar da su ka nuna?".

Hankalin Hibba sosai ya tashi da jin batun Yaya Hannenta ,cikin muryar kuka ta ce,"Kuka....Kuka
kuma..Mama ke kuka akai na,na shiga uku,ina zan sa kaina inji dad`i,wallahi indai haka ne na fasa Auren
ina son Mamata tai alfari da ni ba zan so zubar hawayenta akaina ba ".

" Haba Yaya Hanne ya za ki fad`a ma ta haka kin ga fa hankalin ta ya tashi,da kin sa ni ba ki sanar da ita
ba",Cewar Ummie Maryam.

"A'a Ummien Jaheed gara ta sani tun yanzu ta san irin kuskuren da ta aikata tun kafin lokaci ya kure
mata"....

" Wallahi indai haka ne na fasa Auren,zan zauna a Gida ko ganinsa ma ba na so,ku sallame shi ya tafi ya
bani wuri".

"Hmmmmmm kin makaro domin kin fi kowa sanin Baba Malam ba zai ta`ba sauya maganar sa ba,Aure
ba fashi kamar anyi an gama".

Hannu Hibba ta d`ora aka gami da sakin salati ta na mai cewa," Na shiga uku na bani ni kuma yanzu ya
zan yi Allah ba na son sa na daina son sa ina son in zauna da ku ba na son Auren gabad`aya "...

Shigowar Baba K`arami ya sa ta dakata,Hawaye sha`be-sha`be a idonta ya iske ta, ta na hango shi ta nufi
wajen da ya ke,ta na mai cewa," Yayah dan Allah ka yi hak`uri ka dakatar da wannan Auren,Na hak`ura
na fasa Auren ba na Son shi,ka dakatar da Baba Malam Dan Allah, Na fahimci kaf ahalin Gidannan ba
wanda ya ke son wannan Auren na rok`e ka kaji Dan Allah".ta kai zance ta na mai had`a hannayenta wuri
guda.

"Ai kin makaro Hibba domin yanzu haka an d`aura Auren ki da Abubakar,ni da kaina Na ba da Auren
ki,shi kuma Baba Malam ya zama waliyinsa,yanzu haka ya na waje ya na jiran ki ki fito ku tafi Gidan ku".
" Innalillahi wa'inna ilaihir raju'un,Yayah wallahi na tuba ka sa shi ya warware Auren ba na son bin shi ni
anan zan zauna na fasa Auren ".

Wata tsawa ya daka ma ta gami da nuna mata hanyar fita daga d`akin ya ce da ita," Ta shi ki fita ki bani
wuri ki tafi can Mijin ki na can na jiran ki,shin da ba ki san da zuwan ranar da za ki bar Gidan ba sai
yanzu,don haka tun kafin in sa`ba maki ki `bace min da gani".

"Allah na hak`ura na fasa ba inda zani,ba na ma son shi yanzu ka bashi hak`uri Dan Allah,kasa shi ya
warware Auren, ka sa ya sake ni"....

Ranshi a matuk`ar `bace ya nufi ta,sandar Covebing ya ci karo da ita ya d`auke ta ya nufe ta da ita,ganin
yanda ya nufota yasa ta kasa da gudu ta nufi waje hannunta rik`e da mayafinta.

Ko da isarta wajen,Jan tunga tai ta tsaya tana mai kai hannayenta saman fuskarta gami da murza
idanunta,Anya kuwa idanunta gaskiya suke gane mata kuwa,duk da kasancewar duhun Magariba ya fara
amma hakan bai hanata iya gane shi ba

Tsaye ya ke jingine jikin motar sa sanye cikin jamfa riga da wando,an dai-daita sumar kansa ya kawo hula
jaddara wacce tai dai-dai da kayan da ya sa,hannunsa rik`e da casbaha ya na ja,fuskarta shi sai faman
fad`ad`a murmushi ta ke,hasken muslunci ya baibaye shi,da ka yi ma sa kallon guda za ka fahimci ya na
cikin,farin cikin natsuwa da kwanciyar hankali.




*JADEEDAH*



(It's a story of two love birds who are so different from each other )

STORY & WRITTEN BY :

(*Cwt~Sumiey*)

Marubuciyar littafin

MENE NE ABIN YI ?

KARAGAR MULKI

And now.....*JADEEDAH*
https://chat.whatsapp.com/CWkZfMqvD4H0mtd7WW6Xbz

https://whatsapp.com/channel/0029VapqU8C002T5Bz8RSQ0a



Wannan page naku ne massoya na Allah ya bar mu tare forever and ever



BOOK 1

♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡




PAGE 4 ❤




Duk ta tada ma shi hankali da kukan da ta ke,kwata-kwata hankalin shi baya kan driving d`in da ya ke,ji
ya ke kamar ya janyo ta jikin sa ya lallasheta ya tambaye ta abinda ya ke damun ta amma ina hakan ba
mai yiwu ba ne ba.

"Why are you crying, me ya sa hawaye ke zuba daga cikin idanunki ko na yi ma ki wani laifin ne ban sa
ni ba?", ya tambaye ta cikin hausar shi mara fita sosai.

`Dago kanta tai tana kallon shi da sauri tai k`asa da idanunta tana mai kasa cigabada da kallon shi
tai,muryarta cikin alamun wacce taci kuka ta ce da shi," Ni bana son Auren ka maida ni Gida na fasa bin
ka".



Sosai Maganar Hibba ta daki k`irjin Abubakar har sai da ya samun wuri yai parking gami da mai da
kallon shi kacokan akan ta ba tare da ya iya cewa da ita kumi ba,sai tsura ma ta idanu da yai.

"Why....why...Hibba me ya sa za ki ce haka,ko kin manta we are married now,mun yi Aure ni da ke,mu
d`in ma'aurata ne,mun zama Mata da Miji,ta ya za ki ce kina son ki koma Gida,yaune fa aka d`aura Auren
mu,kuma ki ce za ki koma Gida a yanzu,to ki ce da su me in kin koma ?".

Rau-rau tai da idanu,hawaye na sake zubo ma ta daga idaniyarta," To ai duk basa san Auren na mu da
kai,fushi su ke da ni,Mamana ma kuka ta ke,hawaye zuba su ke da ga idanunta akaina".
Shiru Abbakar yai na wani lokaci,Kafin ya cire baki ya ce da ita,"Ban ji dad`in jin Mama na zubar da
hawayenta akan Auren mu ba,amma ki sani na maki alk`awari zan zauna da ke cikin Soyayya da kuma
amana,zan kyautata ma ki in baki farin ciki fiye da yanda za ki yi zato da tsanmani,zan zame mi ki Mijin
kwatan ce,Mijin nunawa sa'a,ba zan ta`ba bari ki sake kuka ba,zan maye ma ki duk gurbin da ki ka rasa a
sanadin Aure na,kuma a sannu in mu ka yi haƙora,wata rana za su yafe mu su amshi Aurenmu da hannu
bibbiyu".

Kai ta fara girgiza ma shi alamun ba ta amince da duk abinda ya ce a yanzu ba.

Marairai ce mata shima ya yi cikin fuskar tausayi ya ce da ita,"Dan Allah kiyi hak`uri kar ki bar ni,ina
son in rayu da ke,kar ki bar ni,ban san wacce irin rayuwa zan shiga ba in ki ka bar ni,zan cika mi ki
dukkanin alk`awarin da nai ma ki,domin yanzu ba zai yiwu in maida ke Gida a wannan lokacin ba,ran
Baba Malam zai `baci sosai fiye da yanda da ki ke tunani,in Mama ce zuwa nan gaba sai mu je mu bata
hak`uri, hatta da sauran mutanen Gidan duk za su yafe mana zasu so Auren mu da ke,ki bani wani d`an
lokaci kad`an ba zan kunyatar da ke ba, ba zan bari wani abu guda d`aya da ahalin ki su ke tsoran ya faru
da ke,ya same ki ba,ba zan ta`ba cin amanar ki ba ko in juya ma ki baya,zan kasan ce da ke a kowanne
irin yanayin na dad`i ko akasin haka,ki amince da ni mu tafi tare dan Allah Hibba, you are one and only
that I have in my life so please don't live me",ya kai zancen cikin raunanniyar murya.

Kalaman sa sun yi tasiri a cikin Zuciyarta har hakan ya sa Zuciyarta ta fara yin sanyi,kukanta ya tsaya
amma duk da hakan ba ta iya ta ce da shi komi ba.

Cikin muryar shi mai sanyi ya ce mata,"My Wife please shall we go,dare na k`ara yi dan Allah, dan
Soyayyar da mu ka nuna ma juna kafin Auren mu ?".

Da idanu kawai ta ke binsa,gani ta ke kamar duk abinda ya faru ba gaskiya ba ne ba kamar duk mafarki
ne,sai dai ko kusa ko da wasa ba mafarki ta ke ba gaskiya ne,a zahiri komi ya faru cikin d`an k`ank`anin
lokaci.

"Shall we go,please dan Allah ?", ya sake tambayarta a karo na ba adadi,da kai ta bashi amsa ya ja
motar cikin farin ciki da annashuwa.

Cikin some minutes ya isa zuwa Gidan shi da ke Jan Bulo,ba wani babban Gida ba ne,two bedroom ne
sai kitchen,main parlour da`yar farfajiyar tsakar Gidan daga gefe kuma sai parkin space wurin da ya ke
aje motar sa.

Tamkar bak`uwa haka take raba idanunta a cikin Gidan duk da kasancewar yau ne zuwan ta na farko
cikin Gidan,da kan shi ya shigar da trolleys d`in kayanta da suka taho da su ita kuma sai bin bayan shi
take.

Har ya Gama shigar da kayan tana biye da shi,kai tsaye ta ke nuna rashin sakewarta,da amincewar a
cikin Gidan,sai a sannan ya nuna mata wuri ta zauna,idanu ya zuba mata yana kallon ta kafin ya
tambayeta,"Amm nasan kin gaji da yawa kamata yai ki fara yin fresh up kafin nan me ki ke son ki ci in
sama maki kafin ki fito?".
"Ni ba wani wanka da zan yi,kuma ba na son cin komi".

" Seriously ya kamata ki ci wani abu ko da ba zaki yi wankan ba,bazan iya barin ki ki kwana a haka
ba,domin ma san ba makawa za ki cutu,ni kuma ba zan ta`ba iya barin wani abu ya cutar da ke ba
madamar ina da hanyar da zan iya dakatar da hakan ta faru,don haka ki fad`a min me ki ke son ki ci
yanzu in gabatar ma ki da shi ?".

"To...to..Just I need a one cup of tea".

" Nop ban yarda ba,abincin za ki ci,kin san fa na iya cooking",idanu ta zaro alamun bata yarda da
abinda ya ce ba.

"Sincerely da gaske na ke,in ma badan kar ki ce na cika baki ba da sai ince I'm the one of the great
chief a garin kano", sosai maganarsa ta ba ta dariya,har ya ga alamun ta fara sakewa a cikin Gidan.

Gyara zaman shi yai sakamakon nasarar da ya ga ya fara samu,hankalin ta ya fara dawowa kan shi,"
Ina gaya maki lokacin da ina Jos a time d`in da inada 13 to 14yrs muna tare da Grandma d`ita ni ke mana
girgi,a lokacin my Sister Cecelia shi's 5yrs,Grandma na can kasuwa tana kasuwancinta ni ke mana
girki,some time's in cika gishiri,Magi ko yaji,wani lokacin har ruwa na ke cikawa,but fa yana yin dad`in in
ki ka ci sai kin kusa tsinka yatsan ki kan dad`i ".

Dariya sosai Hibba ta ke har ma ta saki jikinta yadda kasan ba abinda ya faru da su .

Ya cigabada da cewa,"Ina da kyankyami shiyasa bana cin abincin waje fad`a min me ki ke son ci just
mention it yanzunan ki gan shi a gaban ki".

Cikin yanayin jin dad`in hirar da suke tace da shi,"Amm to in haka ne ina son zanci tuwo ko d`an
wake,waina ko danbu,a cikin su duk wanda na samu zanci".

" No...no...no...banda wannan i can't,ban iya girka Hausa food ba,ki choosing wani na daban except
wanda ki kai mentioned at the first".

"OK kai dai kawai ka ce baka iya girki ba".....

" No I swear na iya girki,kawai ki ba ni dama ki gani,sai kin tsotse yatsun hannun ki".

"OK to muje kitchen d`in mu gani amma fa da sharad`i"," Oh sharad`i kuma to inajin ki","Da ni za a tafi
kitchen d`in ayi komi a tare","Na yarda mu je",haka su ka tafi a tare zuwa kitchen suka yi komi a tare.

Cikin k`ank`anin lokaci suka kammala daga jellof spaghatti da Stew,suka ci cikin farin ciki da
annashuwa tamkar komi bai ta`ba faruwa a cikin rayuwar su ba,har dare ya raba, suka nufi d`akin da
suka baro.

"Ka ga yau ba sai na farka cikin dare ba neman wani abu ba",

"Farkawa cikin dare kamarya ?"," Ina farkawa cikin dare a kowanne dare inci wani abun kamar cup of
tea ko Coffee something abu mara nauyi ko noodles haka dai haka".ta ba shi amsa
"Ikon Allah Babba da ke?", Ya tambaye ta kai tsaye cikin sigar tsokana.

" Uhmmmmm zan dai iya cewa halitta ce, don da nima ina tunanin zan daina a lokacin da ina Yarinya
amma kuma daga baya na gane halitta ne kawai,Kai dare yayi 20minutes to 12", zaro Ido waje Abbakar
yai ya ce da ita ,"Zo ki kwanta kar gobe mu makara wurin tashi", ya kai zancen ya na mai nuna mata bed
ta je ta kwanta,shi kuma ya zauna kan bed side drawer yana mai cewa da ita," Zo ki kwanta kin san ma
iya tarairayar mutum har yai barci domin a dacan ni ke tarairayar Cecelia har tai barci,kin san itama `yar
rigima ce".

Murmushi Hibba ta saki tana mai gyara kwanciyar ta ta ce Cecelia na ina yanzu?","Tana can gaban
Grandma ta girma fa yanzu, but har yanzu `yar rigima ce",nan fa ya fara bata labarin Cecelia da
halayenta na ban dariya da kuma shiririta har barci `barawo yai gaba da ita.

Binta yai da irin sanyayyan kallonnan mai cike da shauk`in so da k`auna,ya na mai k`ara gode ma Allah
da yasa ya had`u da ita har ta zama sila ko kuma tsanin shigar shi cikin Addinin muslunci, bai yarda ya
kwanta ba har sai da ya shirya dukkanin kayanta a cikin wardrobe, kan carpet ya yasar da Philo ya
kwanta a k`asa ba tare da ya kula da ita Hibban ba.

Sanyin Asuba da ya fara saukowa yasa Hibba farkawa,waige-waige ta farayi taga ina za ta hangoshi
kwance a k`asa a hankali ta sauko ta nufi inda ya ke motsin tafiyar ta ne ya farkar da shi ya tashi zaune.

"Me ye haka dan Allah,taya za ka zo nan ka kwanta a k`asa, idan sanyi ya kama ka fa?", had`a
hannayensa yai guri guda alamun ban hak`uri tare da cewa da ita," Ki gafar ce ni,yau ce ranar ki ta farko
a cikin Gidannan ba zan so in takura ki ba,haka kuma ba zan iya tafiya in bar ki ke kad`ai ba,shiyasa Na
aikata abinda ki ka gani amma ki gafarce ni kin ji".

"OK badamuwa amma dan Allah kar hakan ta sa ke faruwa ka ji,yanda ba ka son wani abu ya same ni
haka nima ba na son in gan ka cikin wani yanayi mara kyau".

" Tuba na ke my princess hakan ba zata sake faruwa ba i promise ".

Clock d`in dake manne jikin bango ta kalla kana ta ce da shi,"Lokacin Sallah Asuba ya kusa da buk`atar
ka shirya da wuri",

Bathroom ya shiga cikin k`ank`anin lokaci ya d`aura Alwala kamar yanda aka koyar da shi,bayan ya fito
ya ke cewa da ita," Da akwai wani Mosque anan kusa zan je in yi sallah a cikin sa".

Itama tana k`ok`arin d`aura ta ta Alwalar ta ce da shi,"To sai ka dawo Allah ya tsare amma dan Allah
kar ka dad`e",da murmushi d`auke a fuskarshi ya bata amsa.

Bayan wajen mintuna Ashirin da biyar sai ga shi ya dawo,jikin shi a sanyaye,da d`an sauri Hibba ta je ta
tarbo shi,fuskarta na nuna rashin jin dad`in halin da ta gan shi a cikin.

"Lafiya mai ya faru ,na ga ka dawo cikin irin wannan yanayin ko dai wani abun ya faru da kai ne ?".
" Hibba ki gode ma Allah da ya hallice ki da ke da ahalin ki a cikin muslunci,a yau na shaida Cewar ba
k`aramar rahama Ubangiji ya so ni da ita ba da har na gane gaskiya na bita kuma na amsheta da hannu
bibbiyu,ina ma da `yan'uwana da su kai saura za su fahimci irin gaskiya da na fahimta su tuba su dawo
kan hanya madaidsiciya ,da sun samu tsira tunda ga nan duniya har lahira,mutanen wannan masalacin
sun mutuntani sun karramani a tsakanin jiya da yau na ga asali kuma zahirin Soyayya da ke fitowa daga
cikin zukatan muta ne,ina ma da zan iya janyo `yan'uwana su musulumta, ina ma da zan iya fad`a masu
gaskiya su yarda ina ma......ina ma"....

"Ka ga ya isa haka ba kuka ko tashin hankali ya kamata mu nuna ba,addu'a zamu yi ta yi mu,idan

3 / 37