Author : Cwt Sumiey Category : African Stories & Novels
ya zuwa yanzu ma ace result d`in ya fito,tun fa safe
gashi 5pm na shirin yi".
"Uhm gaskiya kam nima tun d`azu abun na raina", Cewar Martin.
"Ko dai zan je in gano ,halin da ake ciki wata k`ila aiki ya yi masu yawa ne shiyasa ba su dawo ta kan
mun ba".
" Yauwa Aunty Jee ki je ki jiyo mana ko ma samu mu fita daga bakin tunane-tunanen da mu ke a
ciki",Cewar Nora da ke haɗa kayan da za su koma da su Gida.
"Okay bari in je Allah ya sa mu ji abinda zai kwantar mana da hankali ba ya k`ara tashi ba"," Ameen",Su
ka had`a baki su duka.
K`arar knocking d`in da ake ne ta sa yad`an d`ago ya kalli Door d`in ba tare da ya bar abinda ya ke ba
ya bada izinin shigowa.
"Good Evening Doctor", ta fad`a a d`an d`arare ,a hankali ya d`ago da kan shi ," Oh ke ce come in, ina
fatan lafiya dai?".ya tambayeta ya na mai cigaba da aikin da ya ke.
"Amm.....muna cikin jimami ne,muna ta dakon jin sakamakon test d`in da akayi ko zamu fita daga
cikin tunani da damuwa".
"Oh Sorry aiki ya d`an rik`e ni,test d`in are yet to be out amma zo zauna have a seat,akwai Maganar da
na ke son yi dake", ya kai zancen ya na mai nuna mata wurin zama.
Zaunawa yai ya na mai tattara hankalin shi wuri guda ya na kallonta," Ammm Mahaifiyar ki ta na
samun sauk`i sosai sai dai da akwai buk`atar taimakon ku a cikin lamarinta in har kuna son lafiyarta ta
d`ore,da akwai shawarwarin da na ke son baku ko Allah zai sa a dace".
"Doctor ina sauraron ka I'll do everything in har akan samun lafiyar Momynah ne",ta ce da shi a
ƙagauce.
"Yana da kyau a ce ta rik`a yawaitar yin exercise domin motsawar ga`bo`binta,sannan a rik`a kula da
abincinta ta rik`a samun wadataccen barci, a hanata yawaitar tunani ko barinta ta zauna ita kad`ai,
banda shan wani abu wanda ya danganci Alcohol da sauran su"....haka dai ya cigaba da jero mata
dokokin da ya kamata mai irin wannan ciwon ya kiyaye
" Thanks alot Doctor, ban san da wanne irin baki zan iya Gode ma ka akan irin kulawa da kuma
sadaukantar da lokacin ka daka yi akan Mahaifiyata ina maka fatan alkairi ".
" Don't Mind cause it's my duty kin ga kenan ya zame min dole in aikata abinda ya kamata".
"Duk da haka I'm really appreciate ba zan manta da hakan ba", ta kai zancen ta na mai mik`ewa za ta
fita,har ta fara tafiya ta dawo,gami da komawa ta zauna ta na mai fuskantar shi da cewa ta ce da
shi,"I'm sorry about the last day, I'm swear to the Jesus Name ba halina ba ne,a that day ina cikin tashin
hankali da firgicin rashin lafiyar Momynah,ina mai baka hak`uri akan hakan,ba ni da wani za`bi ne I know
Abuja Boys ba yaren da suke ji sai na kud`i hakan ya sa nai amfani da wannan policy d`in dan tak`aita
zancen amma har cikin raina nasan ban kyauta ba abinda na yi ".
" Kar ki damu na fahimce ki ,tun kafin ma ki yi bayani, Allah ya bata lafiya ".
Wayar shi ce tai k`ara ya d`aga na wani d`an lokaci kafin ya aje wayar ya na mai cewa," I'm sorry for
interruption da akwai wata Doctor ya na da muhimmanci idan zai yiwu ku ganta she is expert about
Neurogical disorder zai kyautu a ce kun kai mata ziyara ,idan har kuka aikata hakan za ku fahimci abinda
Na ke son sanar da ke".
Cikin zumud`i Jedeeda ta ce,"Why not me zai sa ba za mu iya zuwa inda ta ke ba,ai komin nisan inda
ta ke za mu je ,mu ke da riba akan hakan fa,mu ke Neman inda Momy za ta samu lafiya ta warke daga
lalurar da ta ke damunta,don haka a kowacce k`asa ta ke a shirye mu ke da mu je can,kai ko nawane za
mu kashe in har zamu samu damar ganinta".kasaƙe yai yana kallonta ya rasa me yake faruwa da shi,komi
nata neman rikita shi yake, murmushinta maganarta,tafiyarta hatta da motsi in tai sai ya riƙa ganin
kamar yasan wani ko wata da irin wannan ɗabi'ar, yanayin yanda ta ke juya idanunta tare da yanayin
yanda ta ke sarrafa bakinta wajen yin magana,sukan su na ɗaya daga cikin abinda ya ke sake jefa shi
cikin kokonto a cikin Zuciyarsa
"Ba wani Gari ko wata k`asa ta ke ba anan nan Kano ta ke da zama,sai dai ta na da k`a'ida guda d`aya
duk wani patient da za ta duba sai dai ya same ta a Gidanta ,ko kuma mutum ya bi ta Asibitin AKTH
Wanda ta ke aiki a cikin sa sau d`aya ko sau biyu a wata".ya ce da ita yana mai son gano wani abu daga
gare ta.
" Kano kuma ?",ta tambaya fuskarta na nuna rashin jin dad`in abinda kunnuwanta su ka ji mata.
"Eh haka na ke nufi ,amma ki bi komi a hankali lamarin it's about a choice sai fa kuna buk`atar ta,idan
kun ji ba kwaso ba dole ba ne ba, shi has experience about the case Neurogical disorder, yanzu haka ta
na da patient d`in da take kula da shi sama da shekaru Ashirin, kin ga kenan ta san hanyoyin da za a
samu sauk`in cutar".
" Na fahimce ka amma wani hanzari ba gudu ba,zuwan Momy Garin Kano kai tsaye zan iya ce maka
abu ne da ba zai yiwu ba,ba ma ita da kanta ba ko mu ba mu da damar zuwa wannan Garin, baza ta ta`ba
yarda da hakan ba,ka sani za mu iya kashe ko nawa ne in dai zata yarda ta zo ta dubata anan".
"Warnder shall never end me ye a cikin Garin Kanon da har za ku gitta irin wannan lafazin akan
shi,shin wani abu ya faru ne da ita a Garin wanda ba ta son tuna shi ko sake faruwar shi?".
" Ba ni da wannan masaniya gaskiya nasan hakan dai a matsayin dokar cikin Gidan mu,...amma ka
manta kawai mu koma kan Maganar yanda za mu shawo kan wannan Doctorn ta amince da buk`atar
mu".
"Hmmmmmm ki yi hak`uri amma dagaske ina mai sanar da ke ba zaki ta`ba iya sanyata ta zo Garinnan
ba,idan har kuna buk`atar taimakonta to ku kai mata ziyara ta na da dalilin mai matuk`ar muhimmanci
da ba za ta iya bari ta zo nan ba,abu d`aya na sani zan iya had`a ku da ita domin ta rik`a baku
shawarwarin da za su amfanar da ku".
" Ba wani taimako da zaka iyai mana akan haka,zan so in ga na samu wata hanya da zan taimakawa
Mahaifiyata na ga ta warke daga wannan lalurar da ta ke fama da ita,ciwon kan da take fama da shi yai
tsanani ba na son in ga ta na yanke jiki ta fad`i ko kuma ta fita a cikin hayyacinta, ba na son haka".
"Gaskiya babu", ya bata amsa a tak`aice, shiru Jedeeda ta yi na wani d`an lokaci, kafin ta d`ago ta kalle
shi ta ce," I'll do my best, zan yi iya me yiwuwa na ga nayi convince d`inta ta amince mu je ta had`u da
Doctor d`in, idan har kana da tabbacin samun sauk`in na ta","Allah shi ke da iko akan komi muna sa ran
faruwan haka","Hakan ya yi kyau ga wannan card d`in ta ne,za ki iya yin contacting d`in ta da zaran kun
shirya ma hakan,bata da wata matsala zan yi mata bayani",ya kai zancen ya na mai mik`a mata ta
amsa,tare da yi mashi godiya
"Lokacin tashina ya yi zan wuce,zuwa gobe in na shigo zan duba Test d`in na ta daganan sai in duba
yiwuwar discharging na tan".sannan su ka yi sallama ta tafi,shi kuma ya cigaba da had`a abinda zai tafi
da shi.
Tafe take ta na tunani hanyar da za ta iya shawo kan Momynta,da kuma tunanin dalilin da ya sa ta
hana su zuwa garin Kano bayan kuma suna da damar kai ziyara a ko'ina na fad`in k`asarnan kai ba cikin
k`asarnan ba har da k`etare suna da damar zuwa,ta kan nuna `bacin ranta matuk`a in taji ko firar Garin
Kano su na yi ,kai ko k`awa bata son ta ji sunyi in har `yar Kano ce,to meye ya jawo hakan,tabbas ta d`au
aniya binciko ko ma me ye ya ke binne a k`asa, ta yi maganin matsalar in har hakan zai zama sanadin da
Momynta zata samu lafiya ,da wannan tunanin ta isa Room d`in da su ke.
√√√√√√√√√
"Amm..... Ya ma ki ke da suna,Bibah ki ke ko wa ma ?,ki tattara inaki-inaki ki bar min Gida,tun muna
shaida juna ,ki je ki ce wa wanda ya turo ki na kore ki,ba na buk`atar taimakon na ki, shashashar banza,
munafuka kawai".
" Subahanallahi Aunty Zeenat me ya faru ,mai yai zafi har ka?".
"Ban sa ni ba,kawai abinda na ke da buk`ata ki fita ki barmin Gida,ki je ki sanar da munafukai da kuma
`yan gulmar da su ka turo ki,lafiyata lau ba abinda ya same ni".
" Amma Aunty Zeenat ".....kar ki kuskura ki k`ara cewa da ni komi,salin alin ki d`auki mayafin ki ki fice
min a Gida".
Ganin kamar ba za ta tafi ba yasa ta daka mata tsawa tare da fara fatali da duk kayan wanke-wanken da
ta fara had`awa ta re d`aga sautin muryarta ta na cewa," Za ki fitar min a Gida ta daɗin rai ko ko sai na
raunata ki?"
Bibah a firgice ta ɗago tana kallon ta gami da rasa me za ta yi, duk ta firgice domin ba ta ta`ba ganinta a
cikin irin wannan yanayin ba,sai ta kalli tarin wanke-wanken da ke gabanta wanda ta had`a za tayi da ita
Ummu Nurain ta warwatsar da su sai ta kalli Zeenat da ke tsaye a saman kanta sai faman huci da ta ke
tamkar wacce tai tsere,ganin cigaba da zamanta ba lalle ya haifar da d`a mai ido ba ya sa ta d`auraye
hannunta gami da d`aukar mayafinta ta bar mata Gidanta.
"Duk dai-dai na ke da ku munafukan banza da na wofi,ku ne fa kuka zuga shi ya Auro waccen mai
kama da karuwan,wacce ta dalilin ta na zama tamkar bola a wajen shi ,Na rantse da Allah ba zan bar ku
ba,ku dai jira lokacin da zan sauke abinda ke cikina ku ga irin matakin da zan d`auka ba shi ba hatta da ku
sai kun gane asalin wace ce ni".haka dai ta cigaba da maganganun ta har Nurain ya farka da daga barcin
wuyar da ta kora shi ya je ya yi,kan ta ya nufa sai faman murza idanun shi ya ke da hannayensa,ya ce da
ita," Umma yunwa Na ke ji ki bani abinci in ci".....tun kafin ya kai k`arshen Maganar tasa ta kai masa duka
tare da cewa,"Dan Ubanka wuce ka bani wuri ,in yunwar ta tashi ta kashe ka duk ba ta sanadiyar ka ake
yimin duk kalar wulak`ancin da ake so ba".
Ihu ya sakanmata da iyakacin k`arfin sa ya na kuwwa yana cewa shi yunwa ya ke ji ta bashi abinci,ta
tashi ta dafa mai ba zai ci biscuit ba ba zaici Noodels ba,dole ba dan ta so ba ta tashi ta d`ebi wasu daga
cikin kayan da za tai amfani da su ta wanke kafin ta d`ora masu girkin.
*JADEEDAH*
STORY & WRITTEN BY :
(*Cwt~Sumiey*)
Marubuciyar littafin
MENE NE ABIN YI ?
KARAGAR MULKI
And now.....*JADEEDAH*
*YOTA*
BOOK 1
PAGE 23❤
"Kar dai kace min nan ka fara sauka ba ka Isa Gidan ka ba,wai sai yaushe za ka girma ne,iyali ne fa da
kai ,Anya kuwa Jaheed ?".....
"Momynah Haba dan Allah,welcoming d`ina ya kamata ki yi ba ki tare ni da tarin tambayoyin ki irin haka
ba".
" Au nufinka in zuba ma ka Ido kawai ka dinga aikata duk abinda ka ke so ka ke ganin dai-dai ne,to
hakan ba zai yiwu ba,dole ne in nusar da kai gaskiyar kuskuren da ka ke aikatawa ".
Sai da ya maida fuskarsa kalar ban tausayi kafin ya ce," Momynah na yi kewar daddad`an abincin ki ne
me sa mutum ya ji ya kusa k`oshi,shiyasa na biyo in d`an d`ana kafin in wuce".
"Au tunda k`amshin abincin nawa ya isa mutum ya k`oshi to zo ka tafi ai nasan ka ji k`amshin don haka
ga hanyanan ma za zo ka tafi Gidan ka Matanka na can na jiranka".
"Momy ki bar ni in k`arasa cin abincin sai in zo in tafi,Allah ban k`oshi ba".zuba mi shi Ido ta cigaba da
kallon shi har ya kammala cin abincin.
" Ya jikin Uncle, komi na tafiya lafiya lau dai ko?","Jikinsa da sauk`i kamar dai ko yaushe",sai da ya
gyara zaman sa kafin ya ce,"To Allah ya k`aro sauk`in ya maganar taron k`arama juna sanin da za'ayi a
Canada, shin har yanzu Maganar ta na nan?","Eh tana nan ,ina bibiyar su mai yiwuwa za su iya Kira a
kowanne lokaci"
"Amma....Momy".....ta katse shi da cewa,"Ya isa haka tashi ka tafi Gidan ka koma meye ma k`arasa shi
nan gaba amma banda yanzu,sannan maganar Patient d`in ka da muka fara kabar min sauran aikin,in sha
Allah I'll do my best,ka je ka huta idan ka isa ka gaishe mi da `yata Ummu Nurain da kuma Gimbiya Ayush
banda wannan d`an mai surutun tsiya", murmushi kawai yai ba tare da ya ce komi ba ya nufi hanyar fita.
Tun shigar shi mota ya fara tunani in ya Isa Gidan me zai tadda ,fatan shi d`aya Allah ya sa ya koma me
ye zai zo ya zo da sauk`i,Dan bai ta`ba yin tafiya da ta kai sati ba tare da ya iske tashin hankali a cikin
Gidan na sa ba,tun shigar shi farfajiyar ya fara ganin sauye-sauye a idanunsa,muryarsa ya bud`e da d`an
k`arfi ya kira gate keeper yana mai cewa da shi," Lafiya me yake faruwa na ga Part d`in Gimbiya Ayush a
rufe,haka ma na Ummu Nurain,ko wani abun ya faru ne?".
"Allah ya gafarta Malam bani da masaniya akan faruwar wani abu gaskiya sai dai d`azu bayan fitowa
Sallahr Azahar na ga k`anwar Madam ta Gidan Sarauta ta shigo Gidannan, sun fita tare da Gimbiya a guje
ba tare da sun kula kowa ba, da alama dai Gimbiya ba ta da lafiya kamar hakan na fahimta daga gare
su,bayan ganin wannan lamarin, Na tafi k`ofar Uwar Gida,Na sanar da ita,amma cikin rashin sa'a ta koro
ni ba tare da ma ta saurare ni ba,ta maida ƙofarta ta rufe".
" Subahanallahi me ya same ta to, ta na wanne Asibitin yanzu ?",ya jero mashi tambayoyin ba tare da
ya yi la'akari ba yanda zai si ya san amsoshin su ba,"Wallahi Allah yalla`bai ban sani ba,kawai dai na ga
fitarsu cikin matsananancin tashin hankali bayan haka ban san komi ba"....
K`arar Horn da Me gadin ya ji ce ta dakatar da shi yana mai nufar gate d`in da d`an gudun sa,sai da ya
fara lek`awa ya ga waye sannan ya bud`e fuskar shi d`auke da hamdala.
Motar Na tsayawa Gimbiya Fadeelah ta fito tana mai tallafo Gimbiya Ayush jikinta ,wacce ko tsayiwar
kirki ba ta iya yi,da taimakon Gimbiya Fadeelah su ka Isa Cikin Part d`in har bedroom ta kaita ta kwantar
da ita,duk wannan abun da yake faruwa Jaheed na biye a bayan su sai faman jera mata sannu ya
ke,hannunsa ya kai saman kanta tare da yi mata sannu,hankalin shi ya maida kan Gimbiya Fadeelah tare
da tambayar ta,"Me yake faruwa me ya same ta,Allah ya sa koma meye ba mai tsanani ba ne ba ?",ya
tambaya a d`an rikice,inda-inda Gimbiya Fadeelah ta fara ta rasa me ma za ta ce da shi,Gimbiya Ayush ta
fara kici-kicin tashi zaune Zuciyarta sai faman dukan uku-uku ta ke mata,"A kin ga koma ki kwanta jikin ki
ba shi da k`arfin,ki na buk`atar hutu",muryarta cike da rauni irin na marasa lafiya wanda ya ji jiki ta ce da
shi, "Zan iya tashi ai,kuma so na ke in yi maka bayanin abinda ya faru,yanda za ka fahimta", gyara mata
kwanciyar yai gami da janyo blanket ya sake rufa mata," Ba buk`atar ki wahalar da kan ki ga Gimbiya
Fadeelah sai tai min ba yani",ya fad`a a hankali cikin muryarsa mai sanyi.
Kam Gimbiya Ayush ta runtse idanunta a cikin ranta sai faman Addu'a da fatan Allah ya sa kar Gimbiya
Fadeelah ta kwafsa mata ba k`aramin aikinta ba ne ta kwashe komi da ya faru ta sanar ma sa,da sauri ta
bud`e idanun na ta sakamakon jin abinda ke fita daga bakin Gimbiya Fadeelahn take bugun Zuciyarta ya
tsananta hankalinta yai mugun tashi sai faman jujjuya kanta ta ke da bin Gimbiya Fadeelah da kallon da
zai iya dakatar da ita.
"Ina mai baka hak`uri ta sake miscarriage ne ma a wannan karan", Idanuwan shi ya runtse kam ya na mai
k`ara k`arfin ruk`on hannunta da yake a cikin nasa,k`arar da ta saki ce ta dawo da shi cikin
natsuwarta,tuni idanuwansa sun rine sun sauya kala,duban shi ya maida kan Gimbiya Fadeelah tare da
sake jefo mata wata tambayar da cewa,"Shi kuma wannan mene ne silar faruwar shi, me bincike ya
nuna, kuma ita ya matakin lafiyar ta ya ke?", tuni idanuwansa Gimbiya Ayush sun fara zubda ruwa,irin
haka bata ta`ba faruwa ba,salin alin cikin duk da ta ke zubarwa ya ke fita ba a ta`ba dangana ta da Asibiti
ba iya ita kad`ai da shi ne,wani time d`in ma bayanan hakan ya sa ta ke amfani da wannan damar ta tsara
masa k`arya da gaskiyar da zai yarda da ita,yau kuma an samu kuskuren da jini ya `balle mata wanda har
sai da ta kai ga neman taimakon Gimbiya Fadeelah, Wanda da k`yar ma ta samu ta zo,Addu'ar ta d`aya
Allah ya sa kar ta tona mata asiri in hakan ta kasance bata san zai biyo baya ba, hankali da tunanin ba za
su iya haikato mata ko mi zai faru ba.
"Last two days ta kirani ta ke cemin tana fuskantar Abdominal pain,ta ce min bata son ta sanar da kai kar
ka raba hankalin ka Gida biyu ,hakan tasa nai prescribing d`in medication na aiko mata da su, but amma
still ciwon bai daina ba,yau da sassafe ta kirani ta sanar min,sai dai kafin in zo har ta fara bleeding, haka
na kwashe ta mu ka nufi Hospital, kafin mu kai cikin ma