Author : Cwt Sumiey Category : African Stories & Novels
da aro natsuwa su ka ɗaura akan fuskokin su.
Yanayin yanda Daniel ya shigo da kuma suturar da ke jikin sa ya k`ara harzuk`a Zuciyoyin su Baba K`arami
ta yi ba,ya tara gashi himili guda an saisaye gefe da gefe ga gashin duk a wani mur-murd`e shi tamkar
wanda akayi ma kitso,wandon shi kam duk a yaiyage ya ke wanda matasa ke yayin sa crazy trouser ,sai
chain d`in da ke wuyan shi kuwa k`atuwar ce da hoton cross a jiki.
Maganar Baba Malam itace ta d`an ja hankalin su da yake cewa,"Ku gafar ce ni,bayan mun fito daga
sallahr Asar na tsaya ganawa ta musanman ne shiyasa ku ka ji na d`anyi jikirin kafin na shigo,wasu baƙin
da ban tsanmace su ba ne suka kawo min ziyara ".
" Ba damuwa ai tunda mu ka ji shiru mun san wani lamarin ne mai girma ya taso",Alaranma Sama'ila ya
fad`a cikin girmamawa.
"Masha Allah kusan dukkanin mu nan, mun san abinda ya tara mu anan ,k`anwar ku ta zo mana da wani
babban lamari ta zo mana da k`aruwa a cikin addinin mu na muslunci,sai dai bayan haka da akwai wani
babban lamarin da ke biya da wannan batu,kai tsaye dai zamu ce wannan d`an uwanmu",ya nuna
Daniel,tare da cigaba da cewa" Ya yi niyar shiga cikin muslunci tare kuma da rok`on alfamar a bashi
Auren Hibba,sai dai kuma tun da dad`ewa mun yi alk`awarin Aurar da ita ga d`an'uwanta
Alk`asim,wannan shine abinda ya tara mu anan gaba d`aya",Ya kai k`arshe batun yana mai sauke
idanunsa akan Yaran na shi domin fahimtar halin da su ke a ciki.
"Allah ya gafarta Malam ai mu wannan abun murna da farin ciki ne a gare mu in a kai duba da irin tarin
ladan musulumtar da wani ta ke da shi,kuma bugu da k`ari ya nuna ya na son ahalin mu ai wannan abun
alfahari ne a gare mu ba ki d`aya".
" Ka yi gaskiya Yaya Sama'ila domin wannan cigaba ne mu ka samu a cikin Zuri'ah mu,Na san mun
musulumtar da mutanen da yawa a cikin wannan tsangayar ta mu amma ba mu ta`ba samun wanda mu
ka had`a alak`ar Auratayya da su ba, domin ya na da kyau duk Wanda ya musulumta a bashi duk wani
abu da aka san zai iya buk`ata ko ya nema ya rasa,a wadata shi da komi don gudun komawa waccan
munmunar rayuwar da ya baro,hatta da Sana'a,Gidan zama ko makamancin haka"....
"Yayah Kabir ba wai na tari numfashin ka ba ne ba,a'a ina so ka sani ba dole sai an had`a ma shi da Aureb
Hibba ba, zai musulumta in har da gaske ya yi niyar musulumta zai musulumta, shin ko kun manta mun
dad`e da yin alk`awarin akan ita Hibban,ya zamu yi da girman ko nauyin alk`awarin da mu ka d`auka",
Cewar Baba K`arami.
Baba Malam bai dakatar da su ba sai da ya saurare kowa daga cikin su ,ɗaya bayan ɗaya da kuma irin
dalilin da ya sa ya fad`i ra'ayin da ya ke a cikin Zuciyar sa.
Sai da yai gyaran murya ya kuma gyara zaman shi kafin ya ce da su," Duk na saurari duk kanin ra'ayoyin
ku da kuma dalilin da ya sa ku ka fad`e su sai dai ina so ku sani gabad`ayan ku ni ke da ahak`k`u akan in
yankar da hukunci akan kowanne d`ayan ku ko wanne iri ne,Na ba ku wannan damar ne domin sauke
hak`in ku domin in bayan babu ni ku ne za ku cigaba da Jan ragamar wannan Gida na mu da duk abinda
ya biyo bayan shi,ina so ku sani mu kan tauye kan mu madamar mu ka ga wani abu da zai amfanar da
addinin mu ko ya kawo masa cigaba,to shi zamu d`auka mu kawar da son Zuciyar ko buk`atar mu,Dan
haka ku mai do hankalin ku a kaina".
Kallon shi ya mai da kan Daniel da ke zaune sai faman rarraba idanu ya ke ,baya gane wata maganar ma
da su ke cewa,ya ce da shi,"Yaro da gaske ka shirya musulumta,ka shirya barin addinin Crista,ka yarda
cewa Annabi Isa ba d`an Allah ba ne ba kuma ba Allah ba ne ba,Allah bai Haifa ba kuma ba a haife shi,Da
Maryam da shi Annabi Isa dukkanin su bayi Allah ne,shin ka amince da hakan ?".
Cikin muryasa da ba ta ji Hausa sosai ba ya ce da shi,"Na yarda Annabi Isa bawan Allah ne,haka ma His
Mother Maryama itama baiwar Allah ce,babu Allah uku Allah d`aya ne,bai haifa ba ba a haife shi ba,shi
ka d`ai yai deserving a bautawa ba tare da an had`a shi da wani ba"..
"Masha Allah na ji dad`in jin wannan lafazin da ya fito da ga bakin ka,shin yanzu idan na ce ba zan baka
Auren `yata Hibba ba shin za ka yadda ka musulumta ko kuwa za ka fasa ne ?".
Sai da Daniel ya runtse idanun sa kam tare da datse bakin sa da hak`oran shi na sama sakamakon jin
furucin Baba Malam a kunnensa sanda zai bud`e idanunsa har sun sauya kala kafin ya saita kan shi ya ba
shi amsa da cewa," Ba wai don a bani Auren Hibba ba na ce zan musulumta ba a'a kawai dai na fahimci
kyawawan halayya da d`abi'u wannan addinin a dalilin ta,shi yasa Zuciyarta ta kwad`aitu da son yin
rayuwa da ita,ba zan fasa kar`bar tuba ba wai fan na rasa ta,ina da comrfing Ubangiji zai dube ni da idon
rahama ya ba ni wata kamar ta,ya hak`urk`urta da Zuciyata akanta ban ta shi musulumta domin wani
dalilin ba,in badan fahimta gaskiya da nai ba".
Nan take wurin ya d`auki kabbara,alamun sun ji dad`in abinda ya fad`a.
"Tambaya ta gaba,ka tabbata ba wani nai yai maka barazana ko ya tursasa ka akan ka amshi addinin
muslunci ba?".
" A'a ko d`aya babu wani wanda ya tursasa ni ko yai min barazana,hasalima don rad`in kaina na ji ina
son in musulumta domin kyawawan d`abi'u da halayen addinin ne ya ja ra'ayina na amince zan kar`bi
tuba".
Baba Malam kan shi ya fara gyad`awa alamun ya aminta da zancen da ya ke fitowa daga bakin Daniel
kana ya mai da kallon shi kan Hibba ya na mai cewa,"Kin ji abinda ya ce Hibba don haka yanzu kina da
damar da za ki za`bi d`aya daga cikin su,Daniel ko Alk`asim da ki kai rayuwa da shi tun k`uruciyarki wanda
ya ke da tarin Illimi na addini da na zamani?".
Sosai wannan tambayar ta girgiza ta,har ta rasa me ma za ta ce sai faman kame-kame ta ke,har sai da
Yah Mustapha ya ce da ita,''Kinga ki natsu ki fad`i abinda ke a cikin Zuciyar ki bawanda zai maki dole
za`bi a ka ba ki".
Muryarta na rawa ta samu ta saita kan ta kafin ta ce "Abbanmu shima fa ya ce ya na son yai ilimi,ba shi
da wani buri da ya wuce ya zama tamkar kai ya gan shi yana koyarwa kamar kai,yai koyi da duk
kyawawan d`abi'un ka".
Wani murmushi mai cike da kamala Baba Malam ya saki tare da cewa da ita,"Allah yai maki albarka ta
shi ki shiga cikin Gida ki turo min Uwar d`akin ta ki".
Har ta kusa fita daga cikin d`akin ta waigo ta sauke idanunta akan Daniel idanuwanta sun yi rau-rau
kafin ka ce me tuni hawaye sun fara zuba daga idanunta,shi dama tun d`azu ya kasa iya d`auke idanunsa
akanta,haka ta na ji tana gani ta sa kanta tai waje ,Zuciyar ta sai k`ara raunana ta ke ,game da tunanin
wanne irin mataki ne Baba Malam zai d`auka akan ta da kuma rayuwar ta.
Gyaran murya Malam Babba yai kafin ya Kira sunan Alk`asim ya ce da shi,"Alk`asim kasan matsayin ka a
gare ni,tamkar d`ana da na haifa ka ke,kusan a hannu na ka girma na san halayenka,Wanda su ne suka
kwad`aitar da ni akan had`a Auren ka da Hibba, to sai dai zuwan wannan lamarin ya kawo mana
tsaiko,Na yanke hukuncin bada Aurenta a ga wannan bawan Allah,ba wai don wata gazawa ta ka ba, a'a
sai dan kwaikwayon kyawawan d`abi'u na magabatan mu,idan mu kai duba da yanda mutanen Madina
suka kasance a lokacin da Annabin mu,Annabin da muke koyi da shi Annabi Muhammad (S.A.W) yai
hijira tare da muhajiran shi zuwa Madina,a wannan lokacin mutanen Madina matayen su na Aure su ka
rik`a saki suna bawa muhajiran su aure,duk dan nuna karamaci,d`abi'u da kuma halayen su ma su kyau a
gare su,kun ga kenan ba laifi in mun yi koyi da hakan,ina fatan hakan ba zai zama wani abu na daban a
gare ka ba?,idan har haka ta kasance ina mai Neman afuwar ks ,ka yafe ni dan Allah".
Sai da Alk`asim ya matsa kusa da Baba Malam ya kama mayafin da ke jikin sa kafin cikin girmamawa ya
ce da shi,"Haba Malam kai fa Uba ne a gare ni ka can-canci ka yanke min ko wanne irin hukunci,balle
kuma irin wannan lamarin mai girman gaske, ba wai sadaukar da Soyayya Hibba ba ko da fiye da wannan
buk`atar za ka zomin da ita zan kasance mai yi maka biyayya akai".
"Na gode sosai da jin wannan kalami daga bakin ka,shakka babu Allah zai musanya maka da wacce ta
fita".
Kallon sa ya maida kan Alaranma Sama'ila ya ce,"Ana son a gaggauta wasu abubuwa ciki harda
musulumtar da Wanda ya zo musulumta, don haka zamu lak`anta ma shi kalmar shahada a yanzu,dan
haka ka jagoranci lamarin".
Nan Alaranma Sama'ila ya fara lak`anta ma shi kalmar shahadar,"*Ashshahadu Allah ilaha illallah,wa
Ashshahadu Ana Muhammad rasulullahi,wa Ashshahadu Ana Isa Abdullah wa rasuluhu*",yana fad`a
Daniel na maimaitawa harshen shi a rarrabe.
Nan fa suka d`auki kabbara baki d`ayansu kowa a cikin su na farin ciki shigar shi muslunci gami da samun
k`aruwa da su kai.
Alaranma Sama'ila ne ya tambaye shi da cewa,shin kana da wani suna da ka ke sha'awar a maida maka
madadin Daniel da ake kiranka?".
Shiru na wani d`an lokaci Daniel yai,ya na mai tunanin wanne sunan ne ya dace da shi da ," Am am ina
son Abubakar zan so a kira ni da Abubakar saboda na samu labarin irin gudunmuwar da ya baiwa addinin
muslunci ".
"Tabbas ka yi dacen suna ina fatan kayi koyi da mai sunan,Allah ya albarkaci rayuwar ka ya baka ikon
zamowa cikin salihan bayin sa".
" Shin yanzu idan Na ce zan baka Auren Hibba, kana da wanda za ka gabatar a matsayin iyayen ka ko da
acan asalin Garin ku ne?",
Duk`ar da kan shi k`asa Daniel yai kafin ya ce da shi"I don't have any relative in this town, Na zo Garinnan
a matsayin bak`o aiki ne ya kawo ne,Ni d`an asalin Garin Jos ne,iyayena sun rasu a wani rikici da akayi su
duka biyun,sai dai muna zaune tare da Grandmother d`in mu da kuma Sister na".
"Eyyah Allah sarki na jajanta ma ka akan haka,amma ku na da wasu dangi haka bayan su ko?".
" Eh to ba na ce babu ba amma na san akwai wani Uncle d`inmu guda d`aya,ya na can Benin da zama ,ya
ta`ba zuwa inda mu ke sau biyu bayan rayuwar Parents d`inmu,in fact dai muna rayuwa ne mu biyu da
Grandmother d`in mu da ta tsufa sosai,bayan ita kuma bamu da kowa gaskiya ".
Shiru duk mutanen wurin su kai kowa na mamakin labarin da ke fitowa daga bakin sa,Sallamar da
Ummie Maryam ta yi ce ta ja hankalin su, Baba Malam ne ya bata umarnin shigowa gami da samun guri
ta ja ta tsaya tare da cewa cikin mutuntawa da girmamawa matsayin ss na sirikinta," Hibba ta ce in zo ka
na son ganina Baba","Eh haka ne ina son ki je ki sanar da mutanen Gidan cewa a yau zan d`aura ma
Hibba Aure dan haka da buk`atar ku san da hakan ku shirys mata `yan kayayyakin ta dan da an fito
sallahr magariba za ta bi mijin ta".
Ba Ummie Maryam ba hatta da su Malam K`arami da ke zazzaune da ya ja bakin sa yai shiru tun fara
fahimtar abinda Baba Malam ke shirin aiwatar wa,sai da yai saurin ɗago kansa bakin sa na rawa,saba
damar furta komi.....
*JADEEDAH*
(It's a story of two love birds who are so different from each other )
STORY & WRITTEN BY :
(*Cwt~Sumiey*)
Marubuciyar littafin
MENE NE ABIN YI ?
KARAGAR MULKI
And now.....*JADEEDAH*
https://chat.whatsapp.com/CWkZfMqvD4H0mtd7WW6Xbz
https://whatsapp.com/channel/0029VapqU8C002T5Bz8RSQ0a
BOOK 1
♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡
PAGE 3 ❤
Cikin rawar murya Ummie Maryam ta sake mai-maita abinda kunnuwanta su ka jiye mata amma ta sigar
tambaya.
"Eh abinda ki ka ji shi na fad`a zan d`aura Auren Hibba da d`an'uwanmu Abubakar", ya na mai nuna inda
Daniel ya ke zaune ba tare da ya tsaya ba ya cigabada da cewa,"kuma a yau yanzu ma bayan sallahr
magariba, kuma zata bi mijin ta a yau d`in ba sai gobe ba, don haka ki je ki aiwatar umarnin da na sa ki",
ya kai k`arshe zancen yana mai kaurara muryarsa.
Ummie Maryam na tafe na waigen inda Daniel ya ke zaune wanda ya sauya sunan shi daga Daniel zuwa
Abubakar .
" Amm K`arami shiga da shi sashen bak`i ka nusar da shi duk abinda addinin ya tsara, ya gudanar ya
tsarkake jikin shi,sannan ya sauya suturar shi izuwa wacce addinin mu ya koyar da mu musan ya".
Jikin Baba K`arami a sanyaye ba tare da ya so ba ya mik`e gami da nuna ma Abubakar hanyar da ta da ce
su bi,Alk`asim ne ya dakatar da shi ta hanyar cewa, "Baba K`arami ina so zan bika domin mu aiwatar da
wannan aikin ladan a tare".
" Ba damuwa mu je",ya bashi amsa a tak`aice,su kuma sauran duk su ka mik`e su ka nufi hanyar da zata
sada su da babban masalacin anguwa da suke gudanar da sallah a cikin sa kuma su ke jagorantar duk
wani abu da ya ta so a cikin sa.
"Ummien Jaheed lafiya na gan ki haka kin shigo jikin ki ba k`awari?", Anty Zulai Matar Yah Mustapha ta
tambaye ta .
Sai da ta sauke idanunta akan Mama Hadiza,gami da duk`ar da kanta k`asa kafin ta ce da su," Baba
Malam ne ya umarce ni da in had`a ma Hibba kayanta domin zai d`aura ma ta Aure yanzu bayan sallahr
magariba kuma za ta bi mijinta ".
Zumbur Umma Jamila tai ta mik`e bakin ta d`auke da salati ta na cewa," Auren kuma wacce irin magana
ce haka mai ya sa Malam zai yanke irin wannan hakunci cikin k`ank`anin lokaci sai ka ce wata mara
gata,to wai ma da wa za'a d`aura Auren? ".
Sai da Ummie Maryam tai k`asa da muryarta kafin ya ce," Da wanda ta kawo managern da ta ke IT a
Company d`in sa".
Mama Hadiza runtse idanunta da k`arfi tai alamun maganar da ta ji ta bugi Zuciyarta, Umma Hafsat ce ta
amshi zancen muryarta na bayyanar da rashin yarda da hukuncin da Baba Malam ya zarta,gami da
cewa"Ba zai yiwu ba,ta ya zai amince da abinda k`aramar Yarinya za ta zo mishi da shi,ba tare da yai
duba da zata iya cutuwa ba,bai fa san komi game da shi ba,ta ya zai ɗauki ƴa ya ba shi sai ka ce wacce ya
tsinto",d`an tsagaitawa tai gami da maida akalar zancenta akan Mama Hadiza, "Ya kamata ki sa baki a
wannan zancen ki dakatar da Malam Babba in kuwa ba haka ba ke ce wacce za tafi kowa zubar da
hawaye a cikin Gidannan,ba fa a san asalin wannan Yaron ba ahalin sa gabad`aya duk ba sa Sallahr,a
haka za ki bari ya zama Sirikin ki Mihaifin wurin jikokin da za a haifa ma ki anan gaba?".
Umma Hafsat ce ta amshi zancen da cewa," Kin fad`i gaskiya Yaya bai kamata mu zuba Ido mu bar
wannan lamarin ya tafi a haka ba,an sha yi ma na irin wannan yankan k`aunar a cikin Gidannan a d`auki
`ya`yan mu mata a bayar da su ga wanda aka ga dama ba tare da anyi duba da suna son mijin ko a'a
ba,ba tare da anyi shawara da wani daga cikin mu ba,amma duk da haka ba a ta`ba kawo mana mutum
irin wannan ba,don haka dole zamu had`a k`arfi a tare mu dakatar da wannan k`udirin na su".
Kauda kai gefe Mama Hadiza tai gami da saurin d`auke d`igon kwallahr da ta ke k`ok`arin zubowa daga
idon ta gami da cewa,"Hmmmm kun manta shima `yar shi ce ya ma fi ni iko da zartar da hukunci akan ta
kuma ma dad`in gushi ai ita gata a kai mata,wacce `ya ce a Gidannan ta kawo wanda ta ke so a ka bata
shi,sai fa ita,ko kun manta za`bin ta ne,don haka kar ku tada hankalin ku akan d`an wannan k`aramin
abun".ta d`an dakata gami da cewa da Ummie Maryam, "Yauwa Matar K`arami(da ya ke ba ta fad`in
sunan ta),bari in je in kwaso maki kayanta na cikin d`akina ki had`a da na wajen ki kar lokaci ya k`ure". Ta
na kaiwa nan ta wuce ta tafi d`akin ta hannayenta saman fuskarta.
Umma Maimuna ce ta niyar dakatar da ita Baba Asabe ta saurin dakatar da ita gami da girgiza mata kai
tare da cewa," A'a kar ki je ba za ku iya can za komi ba,domin ba ku Isa ku can ja wannan hakuncin
ba,kun san halin Baba Malam ciki ba hatsi ba, ba zai ta`ba can ja maganar sa ba, don haka ku ja bakin ku
kuyi shiru kar da kuma ku ta da wata fitinar".
Kamar wacce aka hankad`o haka Yaya Zaliha ta shigo cikin Parlourn sai faman haki ta ke ita ce d`iya d`aya
da Baba Asabe ke da ita sai kuma Alk`asim shi d`in k`anin ta ne
"Inna Hibban ta ke mayaudariya macuciya ki fito inji dalilin da ya sa ki ka fasa Auren k`anina,ki fito gani
tsaye ina jiran ki,sai da ki ka bari Yaro yai nisa akan son ki sannan ki zo ki ce kin fasa Auren sa akan
me,me ya aikata ma ki", cikin d`aga murya ta ke magana.
Saida gaban Hibba ya yanke ya fad`i sakamakon jin wannan kiran da Yaya Zaliha ta ke mata.
"Ko da ya ke ai barewa bata yi gudu d`anta ya rarrafe ba daga dukkan alamu d`aki aka sa ki aka hure ma
ki kunne akan ki guji d`an'uwanki na jini akan wani banzan bare kafirin banza wanda kaf ahalin sa ba mai
yin Sallah,to ki sani za kiyi danasani mai girma wacce ba za ki ta`ba iya gyara kuskuren da ki ka aikata
ba,za ki gani a k`ok`on shan ki ki jira lokaci"........
" Kar ki kuskura ki yi mata mugun baki,domin ita ba `yar da ki ka haifa ba ce ba,wannan ina son ki sa ni
ko kuma ince ina son ki tuna ita a kaf ahalin ta ba ta ta`ba aikata wani abun kunya ba balle har ki goranta
ma ta da shi,bugu da k`ari ita ai alfamar ta yi ma Alk`asim da ta amince za ta Aure shi",Cewar Yayah
Hanne da shigowarta kenan itama goye da `yar ta a bayanta, itace babba `ya mace a d`akin su Hibba.
Wata tsawa Baba Asabe ta dakawa