Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Jadeedah Complete Hausa Novel by Cwt Sumiey

Author :  Cwt Sumiey Category :  African Stories & Novels

Chapter   6 / 37

15K to 18K   out of 108.5K words

Oh kayi tunanin marainiyar wayon taka ce ko, to ba ita ba ce nice,Anya Daniel, ba akwai wani abu da
kake `boyemin ba wannan sauyin naka ya fara bani tsoro,let me ask you kana ma zuwa Church kuwa?".

Wani zazzafan gumi ne ya fara keto mi shi tare da sanyi a lokaci guda,har sai da Grandma ta sake
tambayarsa tare da cewa,"Wai ko ba ka jin abinda nake cewa ne?".

Shiru Abubakar yai hankalin shi yai matuk`ar tashi hakan ya sa ya kasa iya sarrafa harshen shi.

"Na shiga uku ni Deborah, me nake shirin ji haka daga gare ka,Yesu Almasihu ka kawo min
d`auki,yanzu Daniel so kake kace min ka daina zuwa Church wanne rud`un duniya ne ya same ka,ko so
kake ka ta`bewa ta samu wurin zama a cikin rayuwar ka,me kake so ka zama ?", ta tambaye shi cikin
tsananin tashin hankali.

"Amm mmm...uhmmm.....Grandma ki yi hak`uri ki saurare ni,you know ranar Sunday ita kad`aice ranar
da nake samun hutu,shiyasa nake yawan tashi a makare", muryar shi ta raunana sakamakon k`aryar da
zai mata ya ciga da cewa," Amm...ammm...amma fa ina zuwa time to time ".

" k`aryar ka ke Daniel, you are a liar ba ka zuwa Church muryarka ta tona maka asiri,Na shiga uku na ni
Deborah, Anya ba sauya min kai a kai ba,haka fa nai ta fama da kai ka zo muyi Merry Christmas tare da
kai k`iri-k`iri ka k`i zuwa,har happy new year mu kad`ai muka gudanar da shagulgulan bikinta,,wai meke
damunka mene ne ya sa kasauya,me kake son kazama da har ya sauya d`abi'un ka har haka,Daniel ka
gayamin asalin gaskiyar da ke faruwa anan ?",ta kai k`arshen Maganar da sigar tambaya cikin nuna
tashin hankali da kuma fushin da ta ke a ciki.

Sai da Abubakar yai da gaske kafin gwarin gwuiwa gami da dakiyar Zuciya ya ce da ita,"I swear ni ba
abinda ya canza ni,inayin bauta iyakar iyawata ina zuwa wurin bauta gami da tsarkake ko neman kariyar
kaina daga dukkanin wani abun k`i ba lalle sai ranar Sunday ba duk ranar da na samu sassaucin aiki ina
kai ziyara zuwa Church ".

" Hah Daniel ban yarda da kai ba I'm not believing you,you are a big liar,ka kawo min wata hujja guda
ɗaya da za ta iya sawa in amince da kai ".

"Grandma i swear ina zuwa Church, mai zai sa in bar asalina,in bar koyarwa da tarbiyar da ki ka bani
ba".

" To in har haka ne ka tashi a yanzu ka nufi Church d`in da kake attainding ka had`a ni da wani Pastor
ko Reberal to fa sannana ne zan gasgata abinda kake cewa".

"Innalillahi wa'inna ilaihir raju'un",shine abinda Abubakar ke ta yawan mai-maitawa,yau ya tabbata
sharri ko illah da k`aryar ke dashi,a yau ya k`ara tsanar k`aryar da yake mata tun bayyan musulumtar
shi,bai san dalilin da yasa yake tsoro da shakar gaya masu ya musulumta ba,ko dan tsoran kar yarasa su
amatsayin su na dangi kuma ahalin da yake da da su akaf fad`in rayuwar sa.

Idanuwansa da suka rine sukai jajajur ya sauke akan Hibba da tun farkawar ta a barci taga bashi a cikin
bedroom d`in ta biyo sa Parlourn, yanayin da ya gani akan fuskarta yasa shi yai saurin d`auke idanunsa
akanta.

Ammon muryar Grandma da ya sake karad`e masa kunnensa ya fargar da shi gami da dawowa
hankalin shi akanta," I repeat it ka tashi ka je ka had`a ni da Pastor d`in Church d`in da ka ke zuwa ko
wani wanda zai gamsar da ni in yarda".

"Shikenan Grandma......shikenan zan je yanzu amma ki sani duk abinda ya faru da ni it's your fault,
because i'm felling sick, na dad`e kwance bana da lafiya,I spend almost two weeks bana da lafiya,sai jiya
aka sallame ni, na dawo Gida".

"Jesus Christ amma kuma Daniel shine baka gaya min ba,me yasa kake haka,mai yasa zurfin cikinka
yayi yawa,ka ga fad`a min mene ne matakin lafiyar taka a yanzu,ina fatan dai kana samun sauk`i,ka Na
dai taking medicine naka akan lokaci ko ?".ta fad`a cikin rud`u

" Ina samun lafiya in sha Allah tomorrow zan yi resuming a bakin aikina"....

"In sha Allah kuma Daniel, Na ji kamar haka ka ce ko dai kunne na ne ke jiye min ba dai-dai ba ?".

A diririce ya ce da ita"I'm sorry ba haka na ke nufi ba,I mean by the grace of God".

."A'a Daniel there are something wrong don haka,....hello.... hello".....ta kasa k`arasawa sakamakon
mutuwa da wayarta ta yi a dalilin rashin charge.

Innalillahi wa'inna ilaihir raju'un Abbakar ya fad`a gami da kai hannunsa saman kan shi ya rik`e alamun
alamun jin zafi ko ciwon da yake ji,cikin sauri ya sake bin layin nata amma kuma yaji wayar a kashe.

" Ya Salam Allah ka sa ba wani abun sabo Grandma ta ke shirin aikatawa ba da har ya sa ta kashe wayar
gabad`aya",shine abinda ya fara fad`a bayan gama kirannata.
"Me ye zai sa ba zaka fad`a ma su ba,ka sanar ma su da Cewar ka Musulumta a bar wannan `boye-
`boyen da kuma shiga cikin irin wannan tashin hankalin".Cewar Hibba bayan ta k`araso kusa da shi game
da mik`a mi shi Glass Cup na ruwa mai sanyi.

Bayan ya sha ruwan ne ya bata amsa da cewa," Ina jin tsoro Hibba, ina jin tsoran abinda zai biyo baya,
idan har suka san gaskiya zan iya rasa su su duka ban san dalilin da yasa na ke jin bugun Zuciya a duk
lokacin da nai tunanin ko yunk`urin aikata hakan ba,Cecelia k`aramar Yarinya ce,ita kuma Grandma ta
tsufa ga shi ba wata isasshiyar lafiya ce da ita ba,ina jin tsoran halin da za su shiga idan suka samu
wannan labarin".

"Abu mafi a'ala ka sanar da su sai ka fi samun kwanciyar hankali fiye da ka cigabada da `boye wannan
lamarin mai girma a cikin Zuciyarka,ka sani kana tare da Allah, ka Sani dogaro da shi kad`ai ya Isar ma
akan komi".

" Kar ki damu in sha Allah zan yi k`ok`arin aikata hakan,amma yanzu ya jikin naki,ko dai zamu je
hospital ne a sake duba jikin ki da na Babyn gudun faruwar wata matsalar ?".

"A'a kar ka damu na samu lafiya,Doctorn da ya duba ni jiya ma ya isa I'm feeling better now".

"Anya kuwa na yarda,karda fa unborn d`ina ya samu matsala ",ya kai zancen yana mai d`ora hannunsa
a saman cikinta d`an kimanin watannin biyar.

Yalwataccen murmushi ta saki gami da cewa," Au ta Unborn d`inka kawai ka ke bayan kuma jiya shine
ya hana mu samun wadataccen barci ".

"Shikenan tunda na ga abun naka akwai selfish a ciki,tashi mu je in had`a maka ruwan wanka kafin ka
fito na gama had`a mana breakfast tunda Garin ya riga da ya waye"," okay to mu je ".

Acan `bangaren Grandma hankalin ta a tashe ta kai dubanta kan Cecelia da ke zaune ,ta ca`ba adonta
da k`ananan kaya as usual, ta jawo attached d`inta ta d`ora asaman kanta .

"Cecelia akwai matsala there is a problem, something happened","Matsala kuma Grandma,which kind
of problem, shin ko wani abu ya samu Brox Daniel d`in ne ban sani ba ?".

"Ban sani ba Ceceliar, Something wrong ya faru,gabad`aya Daniel ya janca na rasa gane kan shi ko ku
ma a abinda ya ke cikin Zuciyarsa".ta kai zancen muryarta na raunana.

Kusa da ita Cecelia ta matsa gami da jawota jikinta ta fara lallashin ta da cewa,", It's okay mana,ki bar
tashin hankalin ki haka,kin ga ba wata isasshiyar lafiya ce da ke ba kar ciwon ki ya motsa, in Jesus name
komi zai dai-daita kin ji".

" Ameen Cecelia, ta shi mu je Church d`in nan domin so nake in sa ayimin dogon Addu'o'i akan Daniel
lamarin sa ya fara bani tsoro,amma ina mai tabbata maki in har bikin Easter ya zo Daniel bai shigo
Garinnan ba ni da kaina zan shirya in je har can Kanon Inga halin da yake a ciki,domin ba na tare da
natsuwa ko kwanciyar hankali a game da shi".
"Hakan ma yayi dai-dai, da zaran anfara yi mashi addu'a komi zai dawo Normal.

Tunda ga wannan lokacin Grandma ba ta sake zama ba kullum cikin yawaita bauta da yin sadaka take
akan Jesus Christ ya sa hankalin Daniel ya dawo gare su tayi addu'ar da kanta sannan tasa Pastor ko
Reberal yayi,Cecelia ma na iyakar iyawarta.

Yau Sunday Cecelia ce zaune a k`ark`ashin wata bishi sun fito cin abinci,ta rafka tagumi da duka
hannayenta,,k`arasowar Gloria k`awarta ta sa hannunta ta cire mata tagumin kafin ta fara yi mata fad`a
da cewa " Haba Cecelia me yake damun ki,what happen,ko kina son ki cutar da kan ki ne ta ya tun kina
`yar Yarinyar za ki rik`a jefa kan ki cikin irin wannan dogon tunanin,kin San how long nake tsaye anan ina
maki magana amma ko motsin kirki ba ki ba ?".

Sai da Cecelia ta kamo hannunta ta zaunar da ita kusa da ita kafin ta fara ce da ita,"Ki yi hak`uri Besty
ina cikin damuwane lamarin Brox Daniel kullum k`ara worth yake,kullum K`ara yin nisa daga gare mu
yake,yanda kika san Wanda akai masa asiri haka ya koma,ga Maganar Aurena da Samuel sai matsowa
take yanzu haka ya kusa six months bai zo inda muke ba".

A firgice Gloria ta mik`e tsaye kafin ta ce,"what kina nufin Brox Daniel Wanda na sani ko kuma wani
daban ki ke nufi".

"My friend I'm sorry, da `boye miki wannan lamarin da na yi,Na san halin ki ne za ki tashi hankalinmu,
saboda tsananin son da ki ke mashi,Na bari komi ya dai-daita sai in sanar da ke"....

" It can not be possible, ba zai yiwu ba, I will find him,zan nemo shi a duk inda yake,kawai ki bani
address nasa zan je in ga halin da yake a ciki".

"Kin gani ko dama abinda na guda kenan shiyasa tun da faru ban sanar da ke abinda ke faruwa ba,but
please ina so ki kwantar da hankalin ki domin da akwai shirin da muke shiryawa ni da Grandma,by the
grace of God komi zai dawo Normal".

" No no Cecelia bazan iya hak`uri ba kawai ki bani address d`in in je in gani halin da yake a ciki".....

K`arasowar Grandma cikin hanzari da kuma fushi shine ya dakatar da Gloria game da san amsar
address d`in Daniel a gurin Cecelia da ta ke, hannun Cecelia kawai Grandma ta fara ja tana mai bin
hanyar da zata kai su Gida, a firgice Cecelia ke binta sai faman tambayarta me ke faruwa take amma ta
kasa sanar mata har sai da su ka isa Gida.

"Wai Grandma me yake faruwa haka naga duk kin tashi hankalin ki, nima kuma kin tashi nawa?".

Sai da ta fitar da isaka daga bakinta kafin ta sanar da ita abinda ke faruwa da cewa," Yau Pastor ya
sanar da ni wani abu game da Daniel wanda ya tashi hankalina,don haka yau ba zan iya rintsawa ba har
sai na sa Daniel a cikin idanuna,ba zan runtsaba har sai nayi tozali da shi in my own eyes ".

" A'a Grandma ma haka ma ba zai yiwu ba, kin san ko k`arfe nawa kuwa yanzu,zamu yi tafiya dare fa
kenan? ".
" Yo meye matsalan a cikin ba dai zamu ruski Garin da ya ke a ciki ba komi dare,mu tafi kawai".

"A'a ba za ai haka ba gaskiya kin manta k`asarnan yanzu bata da tsaro,taya zamu jajibi tafiya cikin dare
alhakin ko inda zamu ba mu sani ba kuma ba mu ta`ba zuwa ba,ga ra dai mu bari sai zuwa gobe early in
the morning sai mu tafi".

" Ina ni ban aminta da wannan tsarin na ki ba a yau zamu tafi ba sai gobe ba","Haba Grandma taya
idon ki zai rufe ga gaskiya ina fad`a maki amma kin k`i amincewa,taya garin gyaran wata `barnar zamu
jefa kan mu cikin wani halin na had`ari,Na roƙe ki da suansn Yesu mai cetonmu ki bar tafiyatnan sai
gobe,in har ba so ki ke wani abun kuma na daban ya same mu ba",da k`yar Cecelia ta samu tai
convincing d`in Grandma ta bar tafiyar sai da safe amma ba ta barta ta huta ba har sai da ta had`a masu
duk wani abu da ta san zasu buk`ata kafin ya kyaleta,Ai ko Gari na wayewa ko breakfast bata,bar su sunyi
ba su ka d`auki hanya sar Garin Kano don sugano me ya ke faruwa da Daniel d`in su.




*JADEEDAH*



(It's a story of two love birds who are so different from each other )

STORY & WRITTEN BY :

(*Cwt~Sumiey*)

Marubuciyar littafin

MENE NE ABIN YI ?

KARAGAR MULKI

And now.....*JADEEDAH*



https://chat.whatsapp.com/CWkZfMqvD4H0mtd7WW6Xbz

https://whatsapp.com/channel/0029VapqU8C002T5Bz8RSQ0a
BOOK 1




PAGE 8 ❤

FREE PAGE



"To fa wai wake ta faman kiran wannan wayar ne haka ?,in ka kira d`aya biyu ba a d`aga ba sai ka
hak`ura alamun mai wayar ba ya kusa ne ko kuma yana wani abun mai muhimmanci da ya hana shi
d`aga kiran", Cewar Hibba wacce sallame Sallahr Isha'in take nan tun tana Sallah ake faman kiran wayar
Abubakar da ya barta a charge ya tafi masalaci domin gabatar da tashi Sallahr.

Har ta mik`e za ta je taga waye yake ta faman kiran wayar,sai wayar ta katse,sai da Hibba ta ja tsaki
kafin ta koma ta zauna.

"Grandma ya k`i d`aga kiran ko dai yasan muna cikin Garinnan ne shiyasa ya k`i d`aga kiran wayar ? ".

" In ko haka ne da Daniel ya bani kunya,da ya aikata abinda ban ta`ba expecting daga gare shi ba".

"To yanzu ya zamu yi Grandma, ko dai komawa Gida zamu yi ?".

" God for bid, Cecelia ba inda za ni har sai na sanya Daniel a cikin idanuna "....

Cecelia ta katseta da cewa," Kenan haka Na nufin zamu kwana a saman Street ? "," No my dear ba
zamu kwana a saman titi ba,dole wata dabarar zamu sake wata k`ila muyi nasarar samun sa".

"To ko dai wata wayar zamu ara sai mu Kira shi da ita in anyi sa'a ya d`aga shikenan","To shikenan
Cecelia gwada mu gani",wara idanu Cecelia ta fara yi a cikin tashar da suke,can ta hango wani shop,ta
kalli Grandma tace ko can zamu je ga wani shop can sai mu rok`e shi ya ara mana wayar ?"," To mu je
mu gani ko zamu da ce".

A tare suka isa cikin Shagon,bayan sun gaisa Cecelia tace da shi,"Please ka ara mana wayar ka,muna
so zamu yi kira tamu wayar ta mutu ne saboda rashin charge, gashi munyi tafiya mai nisa".

Wani irin kallon mai Shagon ya bisu da shi alamun kamar bai yarda da su ba.

"Haba Yarona ka taimaka ka ara mana,ba cutar da kai zamu yi ba, idan baka taimake mu ba,ba mu san
ina zamu kwana ba,gashi ba mu san kowa a cikin Garinnan ba,please ka tai maka mana".
Haka ba dan ya so ba ya basu aron wayar,Cecelia ta sa number,tana fara shiga ta mik`awa Grandma
wayar.

Sai da Hibba ta ja dogon tsaki kafin ta yunk`ura da k`yar ta nufi inda wayar take,ganin bak`uwar
number ne ya sa ta d`aga kiran tare da yin Sallamar tare da cewa," Mai wayar baya kusa a sake Kira
zuwa anjima ".

Cikin d`aga murya Grandma ta ce, "Who the hell are you, wace ce ke da har zaki d`aga min wayar Yaro
ina Daniel d`in yake ?".

Ba Hibba kad`ai ba hatta Unborn d`in da ke cikinta sai da ya motsa sakamakon tsawar da kuma murya
Grandma da ta ji".

" Na ce maki ina Daniel d`in ya tafi a cikin irin wannan daren,kuma ke kuma wace ce da har aka samu
wayarsa a hannunki?".

Diriricewa Hibba tai Zufa sai faman tsa-tsafo mata take,ta rasa me zata ce da ita,shigowar Abbakar ya
d`an saisaita mata tunanin da hanzarinta ta nufi inda yake ta na mai mik`a mashi wayar amma ta kasa iya
cewa da shi komi.

"Lafiya me yake faruwa ya na ganki a cikin irin wannan yanayin, ko dai jikin ne har yanzu ?"......

" Grandma ce akan line"...shine abinda ta iya cewa kawai

"Grandma kuma ina fatan dai baki d`aga ba ko ?","Yanzu haka tana kan layi tana jinka", sosai tsoro da
fargaba suka bayyana akan fuskar shi,jikin shi a matuk`ar sanyaye ya kai wayar a kunnensa shi tare da
kiran sunanta yanda zai samu tabbacin ita d`ince.

" Eh ni d`in ce dai wace kake gudu, kenan saboda mace ka ne aikata mana duk abinda ka ga
dama"...muryar shi na rawa ya fara k`ok`arin dakatar da ita,hanashi cewa komi tai sai itace ta cigaba da
cewa,"Ka bar komi kake ka zo nan Tasha muna jiranka".

"Tasha kuma wacce irin Tasha,to wai ma wacce tashar ki ke nufi".ya faɗa a firgice

" Tashar Ubanka na ke nufi,ina nan cikin Garin Kano ka zo ka d`auke mu ,kana da za`bi ko dai ka zo ka
d`auke mu ko kuma mu juya mu koma inda muka fito ko kuma mu kwana a Street ya rage ruwanka".

"A'a Grandma ba ayi haka ba,ku jirani ganinan zuwa".



Haka ya kashe wayar ya nufi inda ya ke aje keys d`in motarsa,rasa ma Ina ya aje su yai sai yai gaba sai
kuma ya dawo yai baya,ya ma rasa ne ya kamata yai sai Hibba ce ta d`auko mashi key d`in ya fita,ko da
ya fita yawo kawai ya kama yi akan titi,sai daga baya tunanin shi ya fara dawowa jikinsa,sannan ya fiddo
wayarsa ya Kira layin da su ka kirashi da shi ya Kira shi ya gayama sa Tashar da suke ya nufi can d`in.
"Kin ji tashin hankali Cecelia, wai mace kuma ce ta d`aga wayar Daniel da farko","Mace kuma to wace
ce ita,wanne matsayin ne da ita har haka ?"," Ban sani ba,a iya sani na Mace ba ta cikin d`abi'u ko
halayyar Daniel ".

" Ko dai yana tare da fiance d`in sa ne ?","To in haka ne mai zai sa tun farko ba zai sanar da ni ba,sai ya
rik`a gudunmu",

"Tom ,ni dai bana ce komi ba ,sai dai mu bari ya zo sai mu ji gaskiya daga bakin sa".haka dai suka
cigaba da wannan zancen har zuwa sanda ya iso tashar.

Ko da isar shi tashar da hayaniya

6 / 37