Author : Cwt Sumiey Category : African Stories & Novels
ki ke aikatawa ba sa
tabbatar da hakan,ina jiye maki tsoran randa zai fahimci mummunar fuskar ki dake ɓoye a bayan
hijabi,idan hakan ta kasance kar ki yi kuka da kowa ki yi kuka da kan ki"..."Riƙe mugun fatan ki domin ba
abinda zai same ni da zaran na ida nufi na zan kira ki ki tayani celebration", Gimbiya Ayush na kaiwa nan
ta zari jakarta ta nufi hanyar fita tana tafe tana mai dafe kanta dake faman sara mata,"Ki tsaya in mai da
ki Gida", Gimbiya Fadeela ta ce da ita,"Kar ki damu zan iya kai kana Gida",da haka ta bar Office ɗin.
Ko da isar Gimbiya Ayush kai kawo ta cigaba da yi, mabanbanta tunanin nika na ta zuwan mata a cikin
Zuciyarta,ta na jin ba makawa sai ta fitar da cikin ba za ta iya barinsa ba.
A firgice ta juya sakamakon jin an dafata ta baya,"Honey ka tsorata ni kwata-kwata ban ji shigowar ka
ba,ban ma tsanmaci dawowar ka yanzu ba",ta faɗa ma shi muryarta a diririce,"Ba dole na in dawo Gida
ba kin turo min irin wannan saƙon kuma kina kashe waya,Me yake faruwa,kina lafiya kuwa .".
Murmushi ƙarfin hali ta saki game da fara waige-waige,tarasa da wacce kalma za ta yi amfani wurin yi
masa bayanin yanda zai fahimta,''Kin ga ki natsu faɗa min ina ki ka je,kin ce in kin dawo za ki sanar da ni
komi,yanzu ina sauran ki,Doctor Faisal Abokina ya kira ni ya sanar da ni ya ganki a Hospital ɗin da ya
yake, me faruwa wani abun ya na samun ki ne?"....."A'a...a'a ni ba abinda ke damuna ina lafiya","Ban
yarda ba gaskiya idanuwanki ba su tabbatar da hakan ba,faɗa min me yake damun ki","Tooooo Na je
dubiya ne a Hospital ɗin wata ƙawata Mubaraka to ita a kwantar na je dubawa","Mubaraka kuma wace
ce haka ,Ni ban san wannan sunan a cikin ƙasashen ki ba","Ayya ko dai ka manta dai amma Aminiyata ce
ta gaba-gaba","Okay na ji ,ina tunanin na manta ta yanzu gaya min ina ki ka je,wacce matsala ce da har
tai tsamari ki ka fit ba tare da kin iya jira na dawo ba,ko dai Dubiyar ki ka je ne kawai?",.
"Ai jikin Bara'atun ne aka kirani ake sanar tana jin jiki,shine fa hankalina ya tashi har na tafi na ga halin
da ta ke ciki kar rabon ganawa ya ƙare","Bara'atu kuma ba Mubaraka ki ka ce ba?"......."Yauwa Eh
Mubarakar na ke nufi",tsuru yai mata yana kallonta kafin ya ce da ita wani abu wayar shi tafa ringing
hakan ya dakatar da abinda ya ke son cewa da ita,",Ina ka tafi ne ka barmu da aiki mutane sai faman
tambayar ka su ke",Kawu Salihi ya faɗa daga can ɓangaren,"Kawai ayi haƙuri ganinan dawowa wani ɗan
uzuri ne ya taso na zo Gida amma ganinan zan dawo","To Shikenan ka yi sauri domin so na ke a yau a
gama cinikin filayen nan,ko mun samu mu sallame masu su mu huta","Ayi haƙuri ganinan dawowa".
"Ki kula zan koma in na dawo ma cigaba daga inda muka tsaya,na fara fahimtar da akwai abinda ki ke
ɓoye min tun dawowa ta da ga Abuja",......sororo Gimbiya Ayush ta yi tana mai bin bayan shi da kallo
ƙirjinta na tsananta bugu,"Bai dai Habibi ya daɗe da fahimtar Cikinnan na nan bai fita ba in haka ta
kasance ina cikin halaka ban san kuma ta ina zan fidda kai na ba",haka dai ta cigaba da tunaninnika a
cikin ranta zuciyarta sai aiyana mata abubuwan da za su iya faruwa ta ke masu kyau da kuma akasin
haka.
✓✓✓✓✓✓✓✓✓
"Abban Jadeeda ba zan gaji da baka haƙuri ba,domin gazawa ta ta bayyana ƙarara,na kasa iya taimaka
maka da wani abu dangane da wannan rashin lafiyar da ka ke fama da ita tsawon shekaru Ashirin da
biyar,duk da Alhmdllh akwai nasara a tattare da samun lafiyar ka amma,ina ɗaura laifin faruwar hakan a
kaina,ba zan huta ba har sai na ga sanda bakin ka zai buɗe ka yi min magana da kan ka,ka kira suna na da
daddaɗar muryar ka,zan so in ga ranar da zaka taka ƙafarka kamar yanda kowa ya ke takawa zan so mu
zaga gari a tare ba tare da tunanin wani abu zai iya faruwa da kai ba,in rayu da kai kamar yanda kowacce
Mace ke rayuwa da Mijinta,in dafa maka Abincin,in yi maka kwalliya don ka yaba,wata ƙila ma in da rabo
in haifa Maka kyawawan yara kamar irin Jadeedar mu da muka rasa a baya".....ta kasa iya cigaba
sakamakon kukan da ya ci ƙarfin ta,ba tai nisa a cikin kukan ba ta dakatar da kanta ,da murmushi ta
maye gurbin kukan tare da cewa,"Oh baka son ka ga ina kuka ko?,to na daina ka ga ma na share
hawayen",ta kai zancen ta na mai goge hawayen da hannayenta tare da cigaba da cewa,","In sha Allah
komi ya kusa zuwa ƙarshe da akwai wani program da zamu gudanar da zaran mun halarci shi da izinin
mahalicci za ka warke,komi zai wuce,ka cigaba da sani a addu kasan Allah na saurin karɓa Addu'ar Miji ga
Matar sa",ta kai zancen ta na mai gyara masa rigar shan iskar da kejikin sa gami da ɗaukar allurar sa ta yi
masa",bayan ta sanya masa kaya marasa nauyi a jikinsa,duk ta na waɗannan zantuttukan da kanta ne
amma shi ko motsi ba ya yi iya kacin ta kwantar ta tayar in buƙatar hakan ta taso , .
Page 37
"Ah aha,ya na ga abincin haka ba dai har ka ƙoshi ba,domin na ga kamar baka ci wani abin kirki ba",
Ummu Nurain ta ce ta na mai bubbuɗe Food flask ɗin,ba tare da ya bar abinda ya ke ba ya ce da ita,"Na
ƙoshi ne,ki haɗo min shayin Coffee na fi buƙatar shi a yanzu","Haba Abu Nurain duka-duka me kaci a
cikin wannan abincin ,kuma tun ɗazu ina kula da kai gaba ɗaya hankalin ka ba ya kan cin abinci kafi
karkata akan aikin da tun da ka shigo ka ke yinsa,na rasa wanne irin aiki ne da tunda ka shigo ka
rungume system ɗin ka ko san ajewa ba kayi".
"Ki yi haƙuri Ummu Nurain aikin ne ya zomin a ƙurarren lokaci,kin san gobe 28 to ina son in sallami duk
wani ma'aikaci dake ƙarƙashi na ya ke kuma saran zai sami Albashin sa a Goben,kuma maganar abinci da
ki ke,na ɗan ci wani abun ne kafin in shigo nan,zan fi son Shayin Coffeen a yanzu".
Turo baki gaba Ummu Nurain ta yi gami da fara tattara kayan wuri guda,"Ka je can ka ci gurin wata
ko,Hmmmmmm na rasa har sai yaushe komi na Gidannan zai dawo dai-dai,ita gata matar so ko",...."A'a
Ummu kar ki ɗauki alhakin ta domin ba ki san gaskiyar abinda ya faru ba kuma abinda na ci ba daga gare
ta ya fito ba","Ko ma daga wurin waye mi ba ruwa na domin kasan zan girka ma ka abinci ai,da wannan
tirtsetsen cikin in tashi in ta fangan-fangan wajen ganin na girka maka abinci da za ka ci,sai ka ɗan yi
Spoon da bai fi uku ba ka ce wai wani ka ƙoshi,ai ba adalci a ciki ,ai ko ba komi ko dan halin da na ke ciki
ka ji tausayi na ka ci abinci ko ba dan in ji daɗi ba".
Zazzaro idanu waje Jaheed yai ya na mai binta da kallo mai tarin mamaki,sai ya kalleta sai ya kalli flate
ɗin da ya ci abinci ,shi dai a zahirin abinda ya ke gani a cikin plate ɗin ya ci kaso mafi yawa daga cikin
abincin amma ga shi tana cewa wanda ya ci bai fi Spoon uku ba,ta na ankare da shi,har a cikin ranta tana
cewa,ai baka ga komi ba sai na haɗa plan ɗin da zan dawo da ɗana gaba na ba tare da ka so ba,kana ji
kana gani dole ka haƙura, "Allah ya baki haƙuri ba zan kuma aikata hakan ba",ya faɗa yana mai kama
kunnensa",Af nasan haka za ka ce dama ai da Matar so ɗin ka ce ai ba za kai kuskuren aikata hakan ba
balle" ......"Ya Salam Zeenat wai me yasa ba za mu taɓa zama mu tashi tsakanin ni da ke ba tare da kin
ambaci sunan Gimbiya Ayush a cikin zancen ki ba,shin me ye alfanun da ki ke samu a ciki in kin ambaci
sunan ta,alhalin ita in har ba ta yi dalili ba hakan ba zata faru daga gare ta ba?".
"Ai dama na san in har za ka danganta ni da ita to ni ce zan kasance mai laifi a ciki ,kuma ai abun a
bayyane ya ke ni ta shigarma cikin rayuwata ta yi bake-bake,ta hana ni gaba ta hana ni baya,ka ga kenan
dole in sata a cikin raina gami da ambaton ta a kowane batu nawa,Ni da ban shiga rayuwar ta ba ai
shiyasa ba ta yawon ambatona a zancenta,ita kuwa kullum shiga ta ke cikin rayuwa ta na yi min mulkin
kama karya a cikinta".
Ɗaga hannun Jaheed sama yai tare da fara addu'a ya na cewa,"Yah Allah ka kawo min ɗauki a cikin
Gidana,ka shiryar min da wannan Matar ta wa,ka rage mata zafin kishin nan da ya ke damu ta gami da
ɗawainiya da ita",kasa iya cewa komi Ummu Nurain tayi sai faman bin shi da idanu da ta ke,domin
lamarin na shi ya kai ta ƙarshe har ta zama speechless akan sa.
"Ni fa ba wani abu na ce ba naga kin zuba min ido,kar ki sauya min manufa, Addu'a na yi ,kin san ba ni da
wani buri a yanzu da ya wuce ace na ga Gidana ya zauna lafiya, sannan kuma in ga kin sauka lafiya,na
tabbata da zaran kin sauka lafiya duk wannan tsiwar da neman fitinar da ke damun ki za ki bar su"...."Au
dama kana fatan irin wannan abun alkairin a gare ni,ai na so ace itama ya zuwa yanzu itama na ta cikin
yananan ,in yaso itama ta haifu ta ji irin wahalar da ake ji,in ya so itama ka fara fuskantar canji daga gare
ta ,zama uwa ba wasan ne ba,raino da kula da yara ba na sangartacciyar mace ba ne ba".
"Kin ga dan Allah mu kawo ƙarshen wannan lamarin domin na ga ya fara tsanani,don ban shirya
kwana cikin tashin hankali a yau ba so Please mu kawo ƙarshen sa haka,zan iya samun Shayin
Coffeen ?",tutturo baki ta fara yi gami da ɗaukar kayan da ta haɗa ta bar Parlon har ta dawo da Shayin
Coffeen a hannunta ba ta saki fuskarta ba,yanayin yanda ya ga tana tururi bakin ne ya sa ya saki
murmushi gami da ture System ɗin da ya ke amfani da ita gefe tare da cewa,"Allah dai yasa Babyn da za
a haifo min ba zai biyo wannan neman rikici da wannan tsiwar ta ki ba".
"Ai kai ma kasan duk abinda ka ga ina rikici a kansa to an taɓo ni ne,ko kuma an dainne min haƙƙina
shiyasa zan tanka","Wannan Zeenat ɗin da na sani a baya ce ke da irin wannan halin amma ba ta yanzu
ba",ya faɗa yana mai karɓar Black bhazar Coffeen da ta kawo mashi.
"Me ka ke nufi da wannan maganar da ka yi yanzu,shin kana nufin da akwai ban-banci Zeenat ɗin
yanzu da ta baya?",Sai da Muh'd Jaheed ya gyara zaman shi kafin ya bata amsa da cewa,", Banbanci mai
yawa ma kuwa, Zeenat ɗin da na sani ƴar gayu ƴar kwalisa ce,mai aji mai natsuwa ga tsabta,komi nata
cikin takatsantsan ta ke yin shi, ba ta da hayaniya,bata gardama bare a kai kan jayayya,ga girmama na
gaba da ita,uwa uba ta iya tsantsara kwalliya da duk kalan nau'ikan suturu karma in tai shigarnan ta
ƙananan ƙaya sai in ji kamar in ɗauke abata in Goya don burgewa",ya kai zancen fuskar shi ɗauke da
shauƙin abinda ya faɗa,kafin ya ɗora da cewa,"Ban san ya a kai ba wannan Zeenat ɗin duk ta bar
waɗancan kyawawan halayen da na santa da su,tun farkon cikin Nurain komi ta sauya ban san dalili
ba,ko ƴar kwalliyar ma bana samu,ya kamata ki koma yin gayun ki,ko in siyo maki wasu sabbin ƙananan
kayan domin kina Min kyau a cikin su,don har na tuna wata shiga da kika taɓa yi na wani ƙaramin skirt da
kuma wata half ɗin riga,kin kusa tashin kaina da wannan wanka,har yau na kasa mantawa da shi .
Da wata irin dariya Ummu Nurain ta kwashe,ta na yi tana kallon fuskar Jaheed,shima sai bin ta da
idanunta yai,har sai data yi mai isarta kafin ta ce,"Amma Abu Nurain ka bani dariya taya da wannan
ƙaton cikin zan yi Irin wannan shigar,ai yanzu ta fi ƙarfina baka ga muna da ɗa saurayi kamar Nurain
ba,ta ya zan iya irin wannan shigar a gaban shi?","A'a Zeenat ba haka na ke nufi ,ina nufin in mun
kasance daga ni sai ke,ai ba wai at random za ki riƙa sa su ba".
"A'a Ni yanzu irin wannan shigar ba ta wani burge ni,taya zan sa kayan da za su bi duk su yi fitting ɗina
ko motsin kirki in kasa ba wannan maganar,mu munci na mu zamanin mun bar ma ƴan baya,taya ina da
wannan tirtsetsen cikin zan ƙarawa kaina wata sabuwar,in ma ji da wannan nauyin da na ke tare da
shi","Akwai fa wasu na daban irin na ku na masu juna biyu,irin rigunan nan da su ka zarce gwuiwa ko
wanda ba su kai su ba",......ta katse shi, da cewa,"Ni fa bana ra'ayin su,sai dai kayi haƙuri Allah Zuciyata
ta fara raya min don cikin nan ba a jikin ka ya ke ba shiyasa ka ke faɗin haka da kasan nauyin da mu ke ji
da ba za ka ma fara irin wannan zancen ba".
Rasa me ma zai ce da ita yai sa bin ta da idanu da ya cigaba,",Hmmmmm Ni ka ga tafiyata na fara jin
barci,sai ka taho",da wannan ta yi shigewarta ta bar shi ya na bin ta da idanu
√√√√√√√√√√√√
"Hibba kallo ake kenan,na ga na shigo sai sallama na ke shiru ba ki amsa ba hankalin ki nakan
television",Ummiey Maryam ta ce ta na mai shigowa ta samu wuri ta zauna a cikin Parlon.
"Wallahi Ummiey Maryam idanuwana ne kawai akai amma kwata-kwata ba na gane me su ke
cewa","Ah aha wai wannan taronnan meye ne,kusan sau biyu ina zuwa in iske kina kallon shi ?","Taron
Ester ne da ya gudana a wata Church dake Lagos,shine fa wannan tashar su ke ta yawan haskaka shi,Ni
kuma kin san da kallon ba cika damuna yai ba shine ban damu da in sauya tasha ba".
"Ikon Allah yanzu wannan kyakkyawar Yarinyar da ke tsaye Crista ce ba musulma ba?","Sosai ma da
alama ta yi zurfi a cikinta irin ƴan na gada ɗinnan ne a cikinta,ina ma zaton kamar zabayar su ce","Kaico
Kaico na kusa ince anyi asarar kyau anan dubeta kamar ki taɓa jini ya fito ni gani na ke ma kamar na taɓa
ganin wani ko wata mai kama da ita","Ni ma kusan haka na ke ji akanta,tun ɗazu na ke kallon ta dalilin
da yasa na kafe tvn da ido kenan amma na kasa gane asalin abinda na ke ji akan ta".
"Kin ga watsar da wannan lamarin ga ƴar ki can ta zo sai faman rusa kuka ta ke,nayi nayi da ita ta faɗa
min me ke faruwa ta ƙi","Ƴata kuma wacce wa ki ke nufi?", Momy Hibba ta tambaya a mamakance.
"Zeenat mana yanda ki kasan wacce aka yi ma mutuwa haka ta shigo cikin Gidannan,inda Allah ya
taimake ni ma ba wani wanda ta haɗu da shi daga cikin Mazan Gidan","To fa Allah ya sa lafiya,ko
wannan karan me ya faru Allahu a'alamu","Ke dai bari tashi mu je ke ki tambaye ta wata ƙila ke ta sanar
da ke abinda ke faruwa".
A tare su ka bar Part ɗin da a yanzu Momy Hibba ke rayuwa da ita da Majinyacin Mijinta su ka nufi
Part ɗin Ummiey Maryam,har suka isa gursheƙan kukan ta ke,da ƙyar Momy Hibba ta samu ta lalleshe ta
kafin ta yi shiru ta fara sanar da su abinda take son sanar da su,kuma dalilin zuwan ta,"Ummiey ku ya fe
ni,ban yi niyar zuwa in sanar da ku abinda ya ke faruwa dan in tadar maku da hankali ba, a'a sai dan kar
nan gaba wani abun ya ɓullo ace laifi na ne tunda ni ce babba, wallahi Momy Hibba na gaji da irin
rayuwar da na ke a cikin Gidan Abu Nurain kwata-kwata baya ganin ƙima balle mutuncina,ba ruwan shi
da ni balle kuma haƙƙina da ya rataya akan shi,ko kwana na ne Part ɗin Gimbiya Ayush ya ke kwana,ba
ruwan shi da ni,baya cin abinci na balle ai maganar kwana Part ɗina,idan nai magana ya ce na cika ƙorafi
ba ni da haƙuri,ba yanda za ai magana mai daɗi ta shiga tsakani na da shi",ta ɗan tsagaita
Kafin ta ɗora da cewa,Jiya mun samu saɓani ni da Matar shi,anan take yada min maganganu,ciki har
da wacce tai mugun tada min hankali,wai ni sakara ce ba ni da zuciya,na yadda kare ya ɗauka,an nuna ba
a sona amma na nace,anmin kora da halin na ƙi ganewa,to in jira har sai an yi min korar kare tunda ita
nafi ganewa,kuma wai ko dawo da Nurain nan Gidan ba hakanan ta faru ba, anyi hakan ne da wata
manufa,Ni babban tashin hankali na anan ko dai Abu Nurain ya sake ni ban sani ba na ke rayuwa a cikin
Gidansa ban tafi namu ba?".ta na kaiwa nan ta sake fashewa da wani sabon kukan da iya ƙarfin ta.
"Innalillahi wa'ina ilaihir raju'una wai duk Muhammad Jaheed ɗin ne ke aikata hakan ,ko dai ya samu
matsala ne akan shi bai san illar da hakan zai haifar masa babbar gobe alƙiyama",Zaraf Ummu Nurain ta
yi ta anshe zan ce da cewa,",Nima Ummiey abinda na ke gudun ma shi kenan, rayuwar gobe inda ba
wani mutum da ya isa ya guje ma laifinsa da makomarsa", Cikin fushin Ummiey Maryam ta da ce ita,"Bar
ni dashi zai gane kuren shi,tabbas sai na bi maki kadin haƙƙin ki da suka danne barima in kirasa"...."A'a
Ummiey Maryam kar ki gaggawar yanke hukuncin,ki bar shi ba sai kin kira shi ba ba dai duk inda yake
anjima zai zo ba,kin ga in kina kira shi yanzu ya san da maganar amma anjima sai dai kawai mu rutsa shi
kun ga kenan dole ya faɗi gaskiya,to mu jira shi har zuwa sanda zai zo,tabbas sai ya yi dana sanin abinda
ya aika","Kuma fa kin kawo shawara bari mu jira shi,ke kuma ta shi ki shiga wajen ƴan'uwanki Mata ki yi
wanka ki shirya sai ki zo ki