Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Jadeedah Complete Hausa Novel by Cwt Sumiey

Author :  Cwt Sumiey Category :  African Stories & Novels

Chapter   35 / 37

102K to 105K   out of 108.5K words

ɗin sai da wani friend nasa ya kira sa ya ce
masa ya ganni,hakan ya sa na kasa iya zuwa wani Hospital ɗin"...."Caɓ akwai babbar matsala bai kamata
ki bar Cikinan ba ya kamata mu bi duk hanyar da zamu bi mu zubar da shi kafin wani ya sake farga da
shi,shin ko wani ɓoyayyen Chemist za mu je inda ba a sanmu ba,a zubar da shi kawai kowa ma ya
huta,na yi matuƙar mamakin rashin aikin wannan maganin ko dan kin saba da shan ire-iren magunguna
na zubar da Ciki shiyasa wannan bai yi ma ki aiki ba".....



“Wallahi Anesa da kin gan ni lokacin zubar da cikinnan, da kin tausaya min, Na sha wahala sosai…...na
kasa yarda duk wahalar da na sha ta tashi a banza,amma ina cikin firgici da tsoro,ina jin kar garin son
kaina da kuma cikar wani buri nawa in gurgunta igiyar Aurena,Ina tsoran kar Imam Jaheed ya fahimci
halin da na ke a ciki,ban san kuma ta wacce hanya zan iya fidda kaina a wurin sa ba".

“Ke dai kin fi kowa tsoro. Amma wallahi karki fa taɓa barin wannan cikin . Maza ba su da hakuri
fa,kuma ba su da kawaici ko kara,in dai a kan mata ne,da zaran ki saki jiki kin fara kwatsa ƴaƴa a Gidansa
sai ya fara sauya maki,gami da tsiro da sabbin halaye,ko yana ƙaunar ki sai kin ga wani ɓangaren sa na
daban.”

Imam Jaheed da shigowar shi kenan ya kasa motsi. Fuskar sa ta sauya launi,bugun zuciyarsa ya
tsananta idanunsa suka ciko da hawaye. Ƙirjinsa ya fara bugu da sauri kamar ana dukan ganga. "Gimbiya
Ayush? Ita? Zubar da ciki, Abortion kenan fa? Kuma da Aurena akan ta,ba sau ɗaya ba sau biyu ba?..."

Ya ɗaga idanunsa masu cike da tambayoyi,kafin ya iya cire ƙafarsa ya tura zuwa cikin Parlon,ba wai iya
Gimbiya Ayush ba,hatta da Anesa sai da ta firgita da ganin sa,ita kuwa Gimbiya Ayush sai da numfashin
ta ya tsaya na wucin gadi,komi na ta a tsaya,zuciyarta ta fara kai kawo shin ya tsinkayi tattaunawar da su
ke,ko kuma bai ji komi ba.

Da ɗan saurinta ta yi kan shi don son ta fahimci gaskiyar abinda ta ke zargi,duk da ta kasa karantar komi
daga gare shi,"Habibi lafiya na ga ka dawo ko ka yi wata mantuwa ne?".

“Kamar dai akwai abubuwa da dama da nake tunanin ban sani ba… Wanda suke faruwa a cikin Gidan
ko ?”ya faɗa cike da ɗacin zuciyar da ya ke ta so ma shi.

A rikice ta ɗago idanunta ta zuba su akan shi zuciyarta ta buga,kafin ta gama saita natsuwar jikinta ya
cigaba da magana, “Idan mace ta ɓoye gaskiya mai girma ga mijinta… me hakan ke nufi? Ƙarya? Kiyaya?
Ko kuma tsoro?”, Gimbiya Ayush ta sunkuyar da kanta ƙasa, ta kasa cewa komai. Zuciyarta ta shiga
rawar tsoro. Ashe ya ji? Ashe sirrin ya ƙare?,ya bayyana yau ƙaryata ta ƙare,ya riga da yasan ɓoyayyar
fuskata da na jima ina ɓoye masa,

Cike da mamaki da ciwon zuciya, ya ce da ita, “Kin sani ina kallon ki a matsayin mace mai kamala da
amana, Gimbiya Ayush,na ɗau so,ƙauna gami da amana na damƙa ma ki ina kallon ki a matsayin wata
babbar kyauta da Allah ya bani,ashe shirmen na ke,ashe ni ki bari ina ta hauka akan son ki,da tunanin na
yi dacen Mata ta kwarai,ashe kallon sakarai ki ke min",Yayi shiru.kafin ya ce da karfi, kamar wanda ya
kamu da kunya da tsana,"Zubar da ciki bayan kina da yaure? Kuma ba so ɗaya ba? Gimbiya Ayush??!”.

Gimbiya Ayush ta fashe da kuka. Ta durƙusa gaban mijinta, tana fadin,“Na ji tsoro ne Habibi… Na ji
kamar idan na haihu za ka guje ni,za ka bar ni,na koma ba wani amfani da zan maka illah in zama mai
renon Yara a gare ka".

Da wani mugun kallo ya bita gami da ja da baya, ya ɗan kalli ƙasa,kafin ya ce “To me kike tunani yanzu da
na sani?,Gudan jini na su ki ka zubar,Jini na ɗana shi ki ka zubar a cikin bola da kwatoci Kin san me kika
zubar da shi kuwa?",wahalata,Jiɓi na da kuma ƙarfina,kin san kuwa irin wahalar da Uba mahaifi ke sha
kafin ya fitar da ɗa daga jikinsa,amma a haka ki ka riƙa zubar mun da su a rariya,tamkar wanda ki ka
maida wani ɗan iska,yau ko a waje mu kai wannan cikin ai ya kamata ki shawarce ni kafin ki zubar da
shi,kai!..... Abortion a gidana abun da mamaki,gaskiya kin shammace ni,ban san haka ki ka ɗauke ni
ba,ashe ni wulaƙantacce kuma abun ƙyama ki ka ɗauke ni ba",ya ɗan tsagaita yana mai cije leɓen shi na
ƙasa,zuciyar shi na ƙuna .

Gimbiya Ayush ta sunkuyar da kai, hawaye na gudu a fuska,Yayi shiru,kafin ya juya wurin Anesa wacce
tuni hantar cikinta ta kaɗa.

"Wa ma ki ke da suna,Anesa ki ke ko wa?,ke ce wacce ki ke ba Mata ta shawara akan zubar da Ciki
bayan ke ko Auren kin kasa,amma a haka ki ke bata gurguwar shawara,da ya ke ita kuma bata da hankali
ta biye miki ba tare da ta san rijiya gaba dubu ki ƙoƙarin jefa ta a ciki ba".

"Me na aikata maki da har na can-canci ki bada shawarar da a cutar da ni haka!?",ya kai zancen a
tsawace,kafin ta dawo daga razanin da tashiga ta ji saukar mari a duka kuncinta,wanda ba ƙaramin jin
marin tai ba,har sai da ta kai ga fasa wata irin razananniyar ƙara gami da yin hanyar fita a guje shi kuma
ya rufa mata baya yana cewa sai ta faɗa mi shi gaskiyar dalilin da ya kawo ta har cikin Gidan shi kuma
aka haɗa baki ita ana cutar da shi.

"A'a.... a'a...kai ya akai me ke faruwa ya na ga kun fito a cikin irin wannan yanayin kamar waɗanda wani
abun ya biyo daga ciki ?",Yayah Hanne Mamar Biba,wacce ta ke ƙanwa a wurin Mahaifin shi ta ce wacce
shigowarta kenan.

Kasa iya magana yai sai faman nuni da hannu ya ke,ya nuna saitin inda Gimbiya Ayush ta ke da kuma
Anesa da ke ƙoƙarin wajen ganin ta samu hanyar barin Gidan.

"Lafiya me ya ke faruwa ya na gan ka a cikin irin wannan yanayin shin ko akwai wata matsala ne a Gidan
na ku?",cikin rawar murya bayan ya samu ya kwato numfashinsa ya ce da ita,"Mama ki ce ta fita...ta tafi
ta bani wuri bana son ganinta",ya kai zancen ya na mai nuna inda Gimbiya Ayush take,tun kafin ya kai
ƙarshe Gimbiya Ayush ta zube ƙasa tana mai ɗora hannayenta a saman kanta gami da fashewa da kuka
tana furta kalamai daban-daban.

"Subahanallah me yai zafi haka ta ya zaka yanke irin wannan ɗanyen hukuncin,ai bai kamata ba,idan rai
ya ɓaci hankali ake sawa a dawo da shi".

"Mama Hanne dan Allah ki fitar min da ita,ta tafi Gidan su,ina jin zuciyata na sake tafarfasa gami da shiga
cikin wani ƙunci a duk lokacin da na kalli inda ta ke,dan Allah ki fitar min da ita daka Gidana,ko kuma ni
in bar mata Gidan",ya kai zancen hawaye na fara zubowa daga cikin idanunsa.

"Kai...kai lamarin nan yai tsamari,ku zo mu shiga daga ciki",fafur Jaheed ya ƙi shiga in har tare da
Gimbiya Ayush ne ba inda zai motsa,ganin hakan yasa Yayah Hanne tasa Bibah ta ɗauko Mayafin
Gimbiya Ayush su ka bar Gidan shima da ƙyar ta yarda za ta bi su, kafinnan Yayah Hanne ta tafi da shi
Part ɗin shi gami da fara lallahinsa.

Page 44
"Yau ni Hannatu na gode ma Allah na ga abinda ya fi ƙarfina, wannan wanne irin rikitacen al'amari ne ya
kunno kai a cikin Gidannan,ta ya za ai ace nayi-nayi ka sanar da ni me ya ke faruwa amma hakan ya
gagara,sai hawaye ne ke faman fita daga idanunka,ka kasa ce min komi".

Motsin da ta ji a bayanta ne ya sa tai saurin waigawa,Bibah ce tare Zeenat da ke ta faman raba idanu
alamun ba ta san abinda ke faruwa a cikin Gidan ba,sai daga can baya Gimbiya Ayush ce,sai faman rusa
kuka ta ke ba ƙaƙautawa,"Umma Hanne me ya ke faruwa na ji Gidan ya cika da hayaniya ?", Ummu
Nurain ta tambaya.

"Ni ma abinda na ke son in sani kenan,na shigo Gida na ga ƙawar Gimbiya Ayush ta fito a kiɗime in
taƙaice maki labari, Muhammad ya wan-wanke Yarinyarnan da mari ta fita Gidannan a gigice,Da bakin
shi ya kori Gimbiya Ayush ya ce ta bar mashi Gida,tun daga nan ya shige cikin ɗaki,har yanzu na ya ƙi
fitowa kuma nayi-nayi ya sanar da ni abinda ke faruwa wallahi Yaronnan fafur ya ƙi sanar da ni abinda ya
faru".

Subahanallah yanzu Abu Nurain ɗin yana ciki?", Zeenat tai tambayar a kiɗime ta na mai ƙarasawa
wajen Door ɗin ta fara bugu gami da yi masa magiyar ya buɗe.

"A'aha Bibah ya na gan ki tsaye a nan wai ko har kin dawo Kaita ki kai ki ka jiyo?","Wallahi Mama ba
inda mu ka je,tun fitar mu muna tsaye a waje sai faman kuka ta ke,nayi duk yanda zan yi amma ta ce ita
ba inda zata".

Sai a lokacin Yayah Hanne ta ga Gimbiya Ayush da ke rakuɓe a can gefe sai faman kuka ta ke da iya
ƙarfin ta.

Ta backyard Ummu Nurain ta samu ta shiga cikin Part ɗin na shi,da hanzarin ta ta samu ta isa gare shi
muryarta na rawa ta ce da shi,"Abu Nurain lafiya me ya ke damun ka,waye yai silar jefa min kai cikin irin
wannan damuwar da har yai nasara zubar da hawaye daga cikin idanunka,faɗa min ko shi waye,na
rantse ba zan bar hawayen ka su zuba a banza ba",kamar yanda ta zo ta iske shin ,ko motsin kirki bai yi
ba balle kuma ta sa ran zai ce da ita wani abu,haka ta cigaba da jero masa tarin tambayoyi ba tare da ta
samu amsar ko ɗaya daga cikin su ba,daga ƙarshe cikin fushi ya ɗago yana mai sauke idanunsa da su ka
sauya launi ya ce da ita,Cikin kakkausar murya,"Ki bar wurin nan kar ki nemi ki ƙara hassala ni,in kuwa
ma ba haka ba kema za ki bita zuwa na ku Gidan".

Wannan furuci na shi ba ƙaramin hargitsa ma Ummu Nurain hankali yai ba dan a rikice ta ɗago ta na
mai sauke idanuwanta akan shi cike da mamaki.

"Eh haka na ke nufi kuma ba da wasa na ke ba fita ki bani wuri domin a yanzu na fi buƙatar kaɗai ci".

Hawaye ne suka fara sauka a saman tata fuskar itama,kafin ta ce da shi,"Saboda laifin wani,saboda na
yi yunƙurin shawo kan matsala,saboda na yi niyar cire ka a cikin wannan lamarin,saboda na nuna
damuwar ka damuwa ta ce,shine za ka furta irin wannan munanan zancen a gare ni?"...ya katse ta da
gaggawa,"An gaya maki a irin haka ake raba Miji da damuwar da ya ke a ciki,kin zo kin tasa ni a gaba
akan lalle sai na sanar da ke abinda ya faru,kin ga dan Allah ki tashi ki fita I need a privacy",ya Kai zancen
ya na mai nuna mata hanyar fita.
Jiki a sanyaye ta fito idanuwanta na zubar da kwala,"Ke lafiya ya na ga kin fito a cikin irin wannan
yanayin,"Mama nima ya ce in tafi Gidan mu in har zan takura ma shi da tambaya

"Kai A'a da sake ni wannan lamarin ya fi ƙarfina,ke Bibah sa waya ki ramin Mahaifiyarsa in sanar da ita
abinda ya ke faruwa",da to ta amsa mata kafin ta fara kiran layin cikin Sa'a bugu ɗaya ana biyu ta ɗaga
bakinta ɗauke da sallama gami da gaisuwa.

"Kin ga ki riƙe gaisuwar ki ganinan Gidan Jaheed na zo na iske su ba a dai-dai ba yanzu haka ma yace
duk matan su tafi Gidan su dan haka ki zo kar ai ɓatatta".

"Subahanallahi shi Jaheed ɗin ne ya aikata hakan to yayi hauka ne ?","Ba na ce ba na dai san nayi
iyakar iyawa ta ganin na shawo kan lamarin amma hakan ya gagareni,ƙarshe ma cewa yai in tafi komi ya
wuce amma sai ya koma ya rufe kan shi a cikin ɗaki, nayi-nayi ya fito ya ƙi,don haka ki zo ki gane ma idon
ki".

"Yayah Hanne ki yi haƙuri amma ba zan iya zuwa wannan Gidan ba,ki kira Momynsa inda hali sai ta zo
taga me yake faruwa"...."Amma ke dai kam Allah ya kyauta miki ɗan na ki,in kira in sanar da ke wani abu
mara daɗi na faruwa da shi sai ki ce wai a kira wani"."Yayah ai da ni da ita duk ɗaya ne za ta yi fiye da
abinda zan yi"...."Ke tafi bani wuri",ta faɗi haka ta na mai katse kiran gami da miƙa ma Biba wayar ta ce
ta da ita,"Kira min Auntyn ku Hibba ki ce mata ta zo nan gidan yanzu da gaggawa".

Haka kuwa a ka yi cikin ƴan mintinan sai ga Momy Hibba tamkar za ta tashi sama, Allah ya taimake ta
tana kan hanyar dawowa daga Hospital wurin aikin ta ta juya alamar Stearing Motar ta nufo Gidan.

"Lafiya me yake faruwa wani ne ba shi da lafiya a Gidan,ya na gan ku a haka,ina Jaheed ya ke me ya
same ku,na ga Gidan kowa a firgice ya ke?","Ni ma abinda na ke ta faman son in sani kenan,na fi ƙarfin
awa ɗaya a Gidan amma har yanzu ba wanda ya iya buɗe baki ya sanar da ni abinda ya ke faruwa,abu
guda da na fahimta rikicin tsakanin Gimbiya Ayush ne da kuma ɗan ki Jaheed dan na iske wata ƙawarta
da alama ma sai da ya wanwake ta mafi kafin ta bar Gidan".

"Mari kuma shi Jaheed ɗin?,to garin ya aika hakan ta faru,Ni a tunanina rikici ko makamancin irin haka
ba,in dama da Zeenat ne sai ince sun saba ai",", Wallahi Momy Hibba ba ruwana nima hayaniya su kawai
na ji na fito na ke tambayar me ya faru,cikin rashin sa'ah reshe ke niyar juyewar da ni,duk abinda ya faru
wannan algungumar ce ta haddasa shi dama shigowarta Gidann ba alkairi ba ce ba abinda ta tsinana
mana sai ƙoƙarin rusa kan Gidan da ta ke,munafuka,annamimiya....","Ke!!! yi mana shiru ai ke ce babbar
banza a Gidan komi ya faru ke ki ka buɗe ƙofar fara faruwar sa,ki kiyaye kan ki in har na gano da sa
hannun ki akan duk abinda ya faru",Momy Hibba na kaiwa nan a zancen ta nufi Door ɗin Jaheed ta fara
bugawa cikin tsanaki tana yi tana kiran sunan shi gami da cewa ya buɗe ita ce.

Jiki ba kwari ya zo ya buɗe mata ƙofar ya na buɗe mata ya juya nan fa ta bi shi ciki ta na mai dakatar
da shi da cewa,"Me ya ke faruwa,garin ya ka ke son aikata wannan shirmen,kana cikin hankalin ka,ina
ilimi da hankalin ka su ka tafi,ko ka fara shan wani abu ne?",da wani irin sauri ya ɗago idanunsa cikin
rawar baki ya ce da ita,"Momy ke ma har da ke,kin san kuwa me ta aikata min,dan Allah ki ce Gimbiya
Ayush ta tafi bana son ganinta,ina tuna ko sunan ta sai in ji Zuciya tana barazanar tashi ƙirjina ya ƙoƙarin
fitowa waje",ya kai zancen ya na mai matsowa kusa da ita ya ɗora kansa a kan kafaɗarta,nan da nan
hawayen da ya ke son dakatawa su ka fara sauka a jiki ta,ɗimin na ratsa jikinta,ba ƙaramin tashi hankalin
ta yai ba,kuka yau Jaheed ne ke zubar da hawaye daga cikin idanunsa akan wani lamari shakka babu
wannan lamarin ba ƙaramin ne ba,da kanta ta ja shi zuwa Bathroom ta sashi ya ɗaura Alwala ya fito ta
shimfiɗa masa prayer mat,ta ce da shi,"Zauna karanta abinda ya sauwaƙa ko yayah ya ke, zaka samu
sauƙin abinda ka ke ji a cikin ranka.

Sai da ta ga yafara karatun kafin ta fito gurin da su Yayah Hanne su ke tsaitsaye suna jiran su ga
fitowar ta.

"Yayah Hanne akwai matsala,koma me ya faru a Gidann ba ƙaramin ba ne,rabon da in ga Jaheed a
cikin irin wannan halin har na manta,ina mai tabbatar maki duk yanda za ai ba zai iya fadar abinda ya
faru a yanzu ba".

"Yau Ni kam na ga abinda ya girme ni,to mu Shikenan yau a nan a tsakar Gida zamu ƙare sai ka ce
marasa magayi?",ta mai da kallonta inda Gimbiya Ayush ta ke sai faman rusar kukan ta take,"Ke ƴarnan
ki dubi Girman Allah da na Annabi sa ki sanar da mu me ki ka aikata ma wannan yaron da har ki ka jefa
shi cikin irin wannan mummunan yanayin,kin ga gaba ɗaya kin tashi hankalin mu,ko iya wannan aka bar
ki da shi kin kwashi alhaki mai tarin yawa".

Ka sa cewa komi Gimbiya Ayush tai sai ƙara fashewa da kukan da ta yi da iya kacin muryarta,"Ahaf kin
gani ko Hibba,da ma abinda na zata kenan ba zata ce komi ba,da ga gani ke ce ba ki da gaskiya tunda na
ga irin kukan da ki ke nasan na dana msani ne".

Shigowar Motar Hameed ce ta ɗan ɗauki hankalin su,shida Fadeela da suka haɗu a hanya tana ƙoƙarin
zuwa Gidan Motar ta talalace shi kuma ya biyu sahun Jaheed,ma su sayar da da filin sun zo shi ake
jira,dama ya je ne yana faman jiran su ba su zo ba shine ya gaji ya dawo Gida ashe rabon ya ji ma kan shi
abinda zai hana shi zama lafiya ne,ya sauya masa sunan rayuwar farin cikin da ya daɗe ya na yi,wacce ya
rada mata suna mafi soyuwa a gare shi.

"Momy lafiya ya na gan ku duk a waje Gidan lafiya,ina Yayah Jaheed ɗin ya ke,ko bayanan ne?, shi na
zo nema na masu sayar da Filin sun zo".

"Yana ciki sai dai amma ba ya cikin yanayin da zai iya haɗuwa da wasu masu sai da fili",Yayah Hanne ta
ce da shi.

A ɗan rikice ya jero mata tambayoyin da suka zo mashi a cikin rai,"Lafiya me ya same shi,ko bai da
lafiya ne,in be lafiya ai Hospital ya kamata a ce an kai shi ba ku bar shi a Gida ba".

"Tambayi waccan itace tsunma maƙunshin cutar da ta cutar da shi,saboda tsabar rashin imani da
rashin jin tausayin ɗan Adam ta ƙi faɗin me ta yi masa bale a samu a sami bakin zaren",cewar Ummu
Nurain da ta kasa iya cigaba da riƙe kanta.
A ɗan firgice Fadeela ta iso gurin gami da tunkarar Inda Gimbiya Ayush ta ke,ita da tun da farko bata
fahimci abinda ke faruwa ba,ko Gimbiya Ayush ɗin ma ba ta

35 / 37