Author : Cwt Sumiey Category : African Stories & Novels
son
gano asalin gaskiyar da take akan fuskarta".
" I swear iyah gaskiya ta,Na fad`a miki kin ga ma wayar Cecelia da ita,ma taho tayi daga-daga hakan
yasa ba za su ta`ba samunta ba", ta tashi ta bi bayan ta,kwantar da Jadeeda akan kujera da tuni ta koma
barcinta ta d`auko mata wayoyin nasu Wanda Allah ya taimake ta suna cikin bag d`inta tun kafin
had`arin ya faru,sai a sannan Mom ta sake yarda da ita.
"To amma wani hanzari ba gudu,barin wannan wayoyin a hannunki zai iya janyo wata matsalar zai fi
kyau ki salwantar da su", da sauri Gloria ta fita hannunta d`auke da su a hannunta da kanta ta sa k`aton
dutse ta yi ma,wayoyin ratsa-ratsa yanda ba za su sake amfanuwa ba bayan ta kakkarya sim's d`in ,kai
tsaye dustbin ta watsa wayoyin sannan ta nufi bathroom tai fuloshing d`in sim's d`in.
Ita kuma Mom Rebecca tana can suna waya da Anderson"Hello the most lovely Mom in the world
ykk"," Ina lafiya,my son fatan dai ba ni na tashe ka a barci ba ?".
Murmushi yai ba tare da ya,bata amsar tambayar da tai ba,kasancewar sa matashi mai natsuwa da
hankali sai cewa yai,"Mom what is the problem mene ne yasa ki ka kira yanzu ko da akwai abinda ki ke
son inyi ma ki ne?".
Dariya tayi kafin ta ce da shi,"Ba wata Matsala my Son just it's a surprise but gest what ?".
Sai da Anderson ya tashi daga kwancen da yake fuskar shi d`auke da murmushi kafin
yace,"Ammmm......Dad will be back",ya fad`a bayan ya d`an d`au lokaci,"Nop baka canka ba",Mom ta
fad`a tana dariya.
Haka ya cigaba da gesing har wajen sau uku amma bai dace ba sai can ta ce yana mai rarraba
zancen,"Gloria..... Accept"......,k`arar ihun da Mom ta saki ne yasa ya gane ya canki abinda yake
faruwa,shima k`arar ya saki har yana mik`ewa tsaye saman bed d`in da yake ya na rawa.
"Mom I'm coming ganinan zuwa in a no time I will be there", Okay see you soon my son muna Gidan
Gloria".
Kamar yanda ya ce cikin k`ank`anin lokaci zai Isa hakata kasance,bayan isar ne Mom da kanta tai mashi
bayanin komi.
Sosai fuskarsa ta bayyanar da tausayin Jadeeda har sai da ya matsa kusa da ita ya na shafa kanta,d`an
motsawa tayi gami da turo bakinta gaba alamun cikin rigima take har sauke ajiyar Zuciya ta yi, bai San
sanda ya saki murmushi ba gami da cewa,", She is so cute", wannan magana tashi ba K`aramin sanya
Gloria farin ciki tai ba don sai da tai dariya har haƙoranta na bayyana, shi kan shi tsayawa yai yana
kallonta rabon da ya ga irin wannan yanayin a tare da ita,har ya manta ya sota tunda dad`ewa so mai
tsansni da zafi amma sanda ya bayyanar mata da shi sai ta rufe idonta tace masa tana da wanda ta ke
so,da kyar ya samu ya hak`ura da ita bayan an sha gwagwarmaya ya fara Dating da wata Yarinya mai
suna Juliet bayan tayi getting pregnancy ta ce ba ta son shi ta fasa Auren sa, kuma tace sai tayi abortion
ta zubar da cikin jikinta sune rigima har Court, dole ta hak`ura ta haifi cikin ,shima ba da kanta ta haife
shi ba,C,s akai mata don tace ba zata yarda ta haihu da kanta ba ,Ana cire Yaron ta basu abinsu ta
cigabada da sabuwar rayuwar ta ba tare da ta,k`ara bi ta kansu ba,yanzu haka Yaron mai suna Edwin
d`an 5yrs yana hannun iyayensa suke rainon sa.
"Mom Na amince zan Aureta kuma,in raini d`iyarta in Kira kaina da sunan Dad d`inta domin Yaro na
kowa ne,sai dai wani hanzari ba gudu nima ina da nawa d`an Edwin ina son bayan Aure in dawo da shi
gabana in cigabada da rainon sa".
" Kar ka wani damu wannan ba wata Matsala bace ba,duka zan haɗa in raine su kaga ko iya su biyu
sun ishe mu".Gloria ta bashi ansa cikin zumud`i.
"No...no ba su ishe mu ba,ke ma za,ki haifi naki we need to build a big family", ya kai zance yana dariya
gami da rungume ta, sosai Mom taji dad`in faruwar wannan lamarin nan da,nan Jadeeda ta samu wani
k`arin matsayin a wurinta domin gani take kamar dalikinta ne yasa burin da ta dad`e da shi a cikin ranta
zai cika.
" Ammmmm....ina son in in rok`i alfarma akan bana son kowa yasan da labarinta har a gama biki,
hasalima so nake da zaran an d`aura Auren mu bar k`asarnan, sannan ko da zamu dawo bana son cigaba
da zama a Garin Lagos mu sake wani Garin ko da kuwa k`auye ne".
"I'll do kamar yanda ki ka ce duk abinda ki ka so shi za a yi,hatta da k`asa ko Garin da zamu zauna ke
zaki za`ba wannan shine reward d`ina na farko na jin daɗin amsar Soyayyar da ki kai, but Mom Na
manta,ban zo da ring d`in da zan yi proposal d`in ta ba".
" Oh to yanzu ya za ai"?",Mom ta tambaye shi like Seriously d`inan.
Duk`awa,yai yana mai `boye hannunsa a baya gami da kiran sunanta cikin sanyin murya,"Gloria I know
you are the most beautiful woman in the world, Na San kyawawan d`abi'u da kuma halayenki,nasan ke
d`in mace ce nagartacciya mai amana please can you married me".
Tsalle Gloria take tana mai rufe fuskarta har ya,kai k`arshe zancen yana,kaiwa ta amsa da Yes Yes, da
saurin sa ya janyota ya rungume ta,haka yake shi mutum ne mai barkwanci da son ayi dariya,duka Mom
ta had`a su ta rungume ta ta mai sake gode ma Allah a cikin ran ta.
Cikin d`an lojaci aka d`aura Auren su bayan dawowar Dad d`in Gloria, shi kan shi ya ji dad`in hukunci
da ya ga sun yanke ma kan su ko ba komi zasu yi farin ciki tunda su uaka za`bi hakan ,hatta da Visa d`in
su ta,kammala bayan gama biki su ka d`auki hanya sai U.K.....
*JADEEDAH*
(It's a story of two love birds who are so different from each other )
STORY & WRITTEN BY :
(*Cwt~Sumiey*)
Marubuciyar littafin
MENE NE ABIN YI ?
KARAGAR MULKI
And now.....*JADEEDAH*
BOOK 1
*YOTA*
PAGE 15 ❤
"Dan Allah ku kyale ni,ku barni ina so in je in ga `yata da kaina,Zuciyata ta kasa hak`uri, ban san a
wanne irin hali take a ciki ba,ina buk`atar in ji d`uminta a kusa da ni", Hibba ta kai zancen cikin yanayin
jinya da,kuma marairaicewa.
" Kin ga Hibba dan Allah ki kwantar da hankalin ki,Jadeeda na can ita ma ana dubata kuma ta na
samun kulawa ta musanman,don haka ki natsu ki kwantar da hankalin ki,Yarinyar ki zata dawo hannun
ki,da izinin Allah.Cewar Ummie Maryam cikin lallashi da ban baki.
Hawaye ne suka fara zubowa daga cikin idanunta, tana mai girgiza kanta alamun bata amince da
hakan ba,cikin k`ank`anin lokaci ta birkice musu,"A'a ni ba abinda za ku fad`a min a yanzu in sake yarda
da ku,yau kwana nawa wajen kwanana uku da farkawa amma kun hana ni ganin Jadeeda, idan ba za ku
bar ni in je inda take ba ku kawota nan in ganta mana, Haba dan Allah",ta kai zancen ta na mai fincike
drip d`in dake hannunta har ma da yunk`urin sauke k`afarta da aka d`ageta sama wacce ta samu karaya.
"Hibbah!!!! Ki dakata nace ya isah haka,ko baki da hankali ne,ko kin manta cewa ke muslmace,ya ki ke
abu kamar wacce kwakwalwarta ta juye ?"...ya d`an dakata ba tare da ya kai k`arshen abinda yake son
cewa ba.
Jikin duk wanda ke wurin sai da yai sanyi,ganin yanda yake mata tsawar kuma hawaye na zuba daga
cikin idanunsa,Lura Mama Hadiza tai ya na shirin cewa wani abu tai saurin shan gaban shi gami da fara
girgiza masa kai,runtse idanun sa yai Wanda hakan ke tabbatar ma Mama Hadiza ba zai fasa fad`ar
abinda yai niya ba.
Tarar numfashin sa tai da cewa," A'a Nasir a kull d`in ka kar ka soma wannan ba shine lokacin da ya
dace ba,ka bar komi ya lafa in ba haka ba kuma"......"In ba haka ba kuma me Mama, tsoran me kike ji,me
ye ku ke gudun kar ya faru,ita fa Muslmace yarda da k`addara ya zame mata dole, don haka ku gaya
mata gaskiya ku fad`a mata cewa Allah ya zartar da hukuncin da yafi dacewa akan ta"....
Duk tsansni da tsafin da take ji a k`afartata,haka ta takata,ba tare da ta yi tunani me hakan zai iya
haifar mata da wani abu ba,sai ganin ta su kai a tsaye a gaban su tana mai kama hannun Naseer
d`an'uwanta ta na mai cewa,"Dan Allah me ke faruwa shin wani abu ya same ta ne, kar ka ce min da
gaske abinda na gani a mafarkina shine ya faru da ita,wai tsaya ina Abbanta yake ban yarda da kuka ce
min yana can office aiki ya rik`e shi ba".
Sai da ya kama kafad`arta ya rik`e har da hannun da ta samu tsagewar k`ashi kana ya ce da ita,"Eh ba
gaskiya su ka gaya maki ba, Mijin ki na can kwance rai hannun Allah a sanadin hatsarin da kuka samu har
k`anwar Mijin ki Cecelia ta mutu"...bige hannun sa da sauri tana mai fara ja da baya daga kusa da shi
tana mai cewa, "A'a Yah Naseer kar ka ce min itama Jadeeda ta mutu,kar ka ce min itama na rasata?".
Sai da yak`ara matsawa kusa da ita ,sannan ya bata amsa da cewa,"Ki saurare ni ki kuma natsu Allahn
da ya baki ita ya fiki son ta,don haka ya amshi abarsa"....Sai da ta sa hannunta mai lafiya ta hankad`ola
shi kafin ta ce "k`arya ka ke Naseer `yata Jadeeda ta na da ranta ba ta mutu ba, domin,ruhina Zuciyata da
kuma gangar jikinta suna gaya min ta na raye,kuma bari ka ji yanzu zan fita da kaina in dawo da ita", ta
kai zancen ta na mai dosar hanyar da za ta bar room d`in, tangal-tangal ta fara za ta fad`i sakamakon
duhun da ya mamaye mata idanunta da sauri su duka Ukun Mama Hadiza, Ummie Maryam da shi kan
shi Naseer d`in su kai kanta,jiki na rawa Ummie Maryam ta tafi kiran Doctor bayan sun kwantar da ita .
Ta ma fita Baba Malam da kuma Baba K`arami suka shigo cikin d`akin ganin halin da suke ciki ne ya sa
ba su sami zarafin tambayar su me ke faruwa ba.
"Garin ya akai haka ta faru, wannan wanne irin sakaki ne ?",Doctorn ya fad`a a zafafe bayan ya ji
abinda ya faru,sosai Doctorn yai fad`a tana mai nuna nasu muhimmancin kulawar da zasu yi da
ita,hak`uri suka ba shi har ya gama yi mata duk abinda ya dace yai mata .
A fusace Baba K`arami ya fuskanci shi yana mai cewa," ba ka da hankali ne,ta ya za ka aikata irin
wannan d`anyen aikin ko kana hauka ne ?".
"Eh Baba K`arami hauka na ke bani da hankali,idan har gajiya da kallonta a cikin irin wannan yanayin
shine hauka to ba shakka na hauka ce,da gaske na haukace,shin ba kwa tunani ko jin tsoran kar yawan
sanya ta barcin dole da kuma `boye mata asalin gaskiyar da kuke ya jefata cikin wani mawuyacin halin,
shin ko so kuke ta koma sai an kwantar an tayar har k`arsheb rayuwarta,ko kuma so kuke ta koma
rayuwar kamar irin wacce Mijin ta ya ke yi a yanzu, na rasa gane wannan tausai ne ko kuma wata
sabuwar hanyar cutarwa,ya ci a ce ya zuwa yanzu kun gaya mata gaskiya yau wajen kwana biyar kenan
da farkawarta da zaran ta tambaye ku game da Mijinta ko `yarta sai ku `boye mata gaskiya a haka ku ke
so ta cigaba da rayuwa,don haka ni dai ma gaji ,Na gaji da ganin `yar'uwata a kwance shar`be kamar
gawa ina son in ganta kamar yanda na saba ganinta tun muna yara"... Ya kasa kai k`arshen maganarsa
sakamakon rungumar da Baba K`arami ya kai masa,sai da ya tabbatar da ya lallashe shi yanda ya kamata
kafin ya raba jikin su ya fuskanci Baba Malam da cewa.
"Maganar Naseer gaskiya ce,ya kamata mu kawo k`arshe komi,mu bar Garin Jingir d`inan haka mu
koma can Kano ,za su fi samu kulawa fiye da wacce suke samu anan".
" A'a ni dai ina jin tsoro ta ya zamu bar da su daga cikin Asibiti a irin wannan halin ",Cewar Mama
Hadiza.
"Mama ki kwantar da hankalin ku ba gani ba,zan iya ba su duka kulawar da ake so,nima fa Doctor ne,a
dukaninsu sun fi buk`atar kulawa ta cikin Gida fiye da ta asibiti, domin ya zuwa yanzu sun d`an samu
sauk`i da ciwukan da suka samu na external saura na internal
" To ba matsala amma ya kike gainin za muyi doguwar tafiya irin wannan da marasa lafiya har guda
biyu?","Lafiya lau zamu tafi da su ai referring d`in su zuwa wani Hospital d`in zamuyi don haka za su
bamu motar mara lafiya a sanya su a ciki har zuwa can Kanon".
"To shikenan sai mu fara Neman Sallamar amma,kafinnan kai K`arami ya ka yi da gawar ita k`anwar
Abbakar d`in ?".
" Daganan Asibitin suka had`a ni da wani Pastor nai mishi duk bayanin yanda komi ya faru, ya jimanta
mana bayan ya saurari duk abinda ya faru sannan ya amshe ta ban bar wurin ba har sai da su kai mata
duk abinda suke yiwa `yan'uwansu in sun mutu sannan suka buzne ta,sun bani tabbacin ko nan da
shekara nawa zan zo zasu nuna min kabarinta domin har rubutu a takardar sai da muka yi sannan na
taho".
"Masha Allah hakan yayi domin adalcin da zamu yi mata kenan mu sadata da `yan'uwanta su binneta
kamar yanda suke ma `yan'uwansu,kun san zamu iya kiran haka a matsayin hak`k`in ta ne a kan mu ,don
haka zamu iya tafiyar mu tunda ba wani nauyin ta akan mu".
"Tukunna dai wani hanzari ba gudu ba,shin kun manta a sanda Hibba tai farkawarta ta farko ta ambaci
sunan wata ta na mai cewa `yarta na hannunta,to ta ya ke nan idan har hakan ya zama gaskiya, gani na
je kamar bai kamata mu bar Garinnan ba har sai mun nemo ta idan mun tabbata ba ta tare da Jadeedan
sai my yi tafiyar mu".Cewar Mama Hadiza.
Sai da Baba Malam ya fuskance ta kafin ya ce"Ki natsu ki saurare ni,yanzu haka daga police station d`in
da suke gudanar da wannan binciken na ke akwai rikitarwa mai tarin yawa a cikin binciken,sun ce min
sun yi iya binciken su su basu ga kowa a wurin ba,kai ko wayar mamaciyar ba a gani ba balle ai amfanin
da ita a gano shin da gaske da akwai wata Mace wacce suke tare da ita ko babu,to babu wata takardar
ko guda d`aya dake nuni da Cewar akwai wata bayan su uku da kuma `yarsu iya ita Hibban Mijinta da
kuma k`anwarsa su ka tarar,babu wata shaida da ka iya tabbatar da wanzuwar ita wannan mai sunan da
take ambata,saman wani Mutum Wanda a gaban shi hatsarin ya faru,ya tabbatar mana da cewa ya fi
zargin buguwar da tayi ne yasa take ambaton wanna sunan ,kai tsaye dai binciken ya fi tabbatar mana da
Jadeeda ta rasu ta k`one a cikin wannan motar".
"Innalillahi wa'inna ilaihir raju'un yanzu Malam kana nufin Yarinyarnan ta rasu ta riga mu Gidan
gaskiya da wacce fuska zamu itta tarar Hibba da zancen mutuwar `yarta bayan ga munmuna hademarin
da ya fad`a ma Mijinta na juyewar kwakwalwa".Ummie Maryam ce ta matsa kusa da ita tana lallashin ta
duk da itama tana zubar da nata hawayen ne.
" Sai hak`uri k`addarar Allah ce,haka ya tsaro mana ita,don haka dole zamu d`auke ta, domin a yanzu
in munce zamu nemo me irin wannan sunan nata,ya ma sunan ya ke ?",ya na mai tambayarta su sunan
da Hibban take yawan ambata bayan farkawarta.
"Gloria sunan ta",Naseer ya ba shi amsa.
" Yauwa Gloria idan mun tashi nemanta a yanzu ina zamu fara,domin mu ba musan daga ina ta zo
ba,ya kamanninta su ke bamu san komi daga gare ta ba,iya Abbakar da k`anwar shi su ne suka santa da
kuma inda ta fito, ita waccan Allah yai mata rasuwa,shi kuma wannan ya na kan matakin da shi kan shi
bai san ko shi waye ba,kai ko ahalinsu bamu sani ba,in kuma munce muje Jos neman ahalin nasu to ta
ina zamu fara da wacce hujja zamu yi amfani ,don haka bamu da wata makama wacce ta wuce muyi
hak`uri".
Naseer ne yace,"Ni da cewa nai ko a d`auki hoton ita Ceceliar a sanya a kafafen television ko Allah
zaisa ahalin su su gani kun ga shikenan daganan sai mu fara Neman Gloria "," Hmmmmmm Naseer
kenan baka ga yanda Allah ya sauyawa Yarinyar nan kamanninta ba, shiyasa har kake fad`in wannan
Maganar,zai wahala ko `yan'uwanta su iya gane ta".
"Allah gare ka mu ka zo gare ka muke neman taimako,Allah ka kawo mana mafita a cikin wannan
lamarin", Mama Hadiza ta fad`a tana mai share hawayen fuskarta.
" Shikenan kin gama magana Mama Addu'ar mu kawai take so,in sha Allahu indai Jadeeda na da rai a
doran duniyarnan to zata kawo kanta gare mu har inda muke duk min daren dad`ewa bi izzatillah,zamu
duk`ufa wajen gayama Allah kukan mu,ba zamu gajiya ko min daren daɗewa ba".nan fa suka had`a me
kansu kowana k`unshe hawaye da kuma bak`in cikin halin da suke a ciki.
"Masha Allah, Allah yai maku albarka ya zama gatan ku gabad`aya sai abu guda da zan so daga gare
ku,daga yau ko da wasa kar wandaya k`ara tada zancen wata Gloria kai hatta ita Jadeedan mu d`auka a
ta rasu bata Raye,ko da ita Hibban ta farka kar wani ya bata goyan bayan akan duk abinda zata zo mashi
da shi,karma in na son tada wancan zancene,don haka da zaran mun Isa Gida zamu gabatar da Sallahtul
ga'ib (Sallahr da ba gawa),da sunan Jadeeda da fatan Allah ya kai rahama da jink`ai cikin kabarinta".
Jikin kowa sai dai ya ƙara sanyi sai dai ba su da yanda zasu yi dole abinda ya kamata suyi kenan su
d`au k`addara ta fuskar da ta zo masu,nan Naseer ya fara cuku-cukun sama masu referral zuwa Kano bai
huta ba har sai da ya samu a wannan ranar su ka bar Garin Jingir badan sun so ba,Zuciyoyin su d`auke da
wani miki ko gyambon da ba zai ta`ba warkewa ba.
*JADEEDAH*
(It's a story of