Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Jadeedah Complete Hausa Novel by Cwt Sumiey

Author :  Cwt Sumiey Category :  African Stories & Novels

Chapter   10 / 37

27K to 30K   out of 108.5K words

yanayin mamakin ta ce da
ita,"Auntynah biki fa sauran sati guda fa kenan ?","Eh mana na sani Cecelia, ko kin manta we are family
now,ba ki da wasu ahalin da suka kaimu kamar yanda a gare mu ki ke ta musanman,don haka dole ne
mu tsaya tsayain da ka akan duk wani lamari naki da ya taso mu yi iyakar iyawar mu domin mu fidda ki
kunya akan shi".

"Sai fa bayan Christmas da kwana d`aya sannan za a yi bikin fa"," Na San da haka Cecelia, to wai mene
ne abun mamaki a ciki,lafiya lau zamu gudanar da shagalin bikin har a gama a tare da ku".

"I'm so surprised sister Hibba ban ta`ba expecting d`in haka daga gare ku ba,ni duk anawa tunanin ba
za ku samu halatar bikin ba tunda mun kasance masu mabanbanta Addini,a tunani na addinin ku ba zai
bar ku ku halacci bikin ba".

" A'a Cecelia si Addinin Muslunci baya raba kan `yan'uwa ko kuma ya `bata zumunta,hasalima shike
k`ara k`arfafa su,ina mai tabbatar maki tare da Yayanki za a d`aura Auren ki,ba za ki rasa shi a matsayin
dangi ko ahalin da ki ke tak`ama da shi ba, har yau har gobe yana tare da ku".

Da gudu Cecelia ta k`arasa kusa da Hibba ta rungume ta ta mai kasa iya cewa da ita komi har sai daga
k`arshe ta fara yi mata godiya, "Thanks a lot ina Godiya sosai godiya mai tarin yawa,ita kanta Grandma
za ta ji ddad`i gami da farin cikin jin wannan labarin".



" Ki ce da na sani ban fad`a maki ba kawai sai dai ki ga mun fara shiri","A'a gara da kika fad`a min
yanzu don da ban san wanne irin abu ne zai same ni ba kan murna da farin ciki ".
" Kin ga bari in tashi in d`ora girkinan tun kafin `yar rigimata ta farka",da haka su ka canza akalar firar
bayan sun shiga kitchen d`in a tare don girka abinda za su ci.




₹₹₹₹₹₹₹₹₹₹₹




"Haba Ummie Maryam wannan fad`an ya yi yawa,Yaro ne fa har yanzu"," Hibba Na ga ji wallahi,wannan
bak`in ran har ina,tun jiya ya sa maganar tafiyar ku Jos shikenan ya rasa sukuni,kuma ya sani Abbansa ba
zai bar shi ayi tafiyatnan da shi ba saboda School, suna k`arshe term ne kuma gashi in kuka tafi zaku
dad`e amma ya k`i hak`ura nayi lallashin na yi ban bakin amma duk a ban za".

"Haba Jaheed tun yaushe muka gama wannan maganar da kai ba na ce kar ka damu ba,everything will
be OK zamu dawo da wuri,ko dai so kake in fasa tafiyar ne ?",

Da kai ya bata amsa ba tare da ya bud`e baki ya ce wani abu ba,"Kin ga ni ko hatta miskilancin nasa
yau ya motsa,ina ganin wata k`ila sai dai ki bar mashi Jadeeda anan ke ki tafi ke kad`ai".

Cecelia ce ta matso kusa da shi ta na mai dafa kafad`arsa tare da cewa," Haba my friend don me za ka
sa kan ka a cikin damuwa,hakan bai kamata ba,I promise da zaran an gama biki za su dawo,they will be
back soon".

"Kin tabbata dagaske ki ke ?", ya tambayeta yana mai tsareta da idanuwansa,"I'm sure Hundred
percent zasu dawo da zaran an gama biki,ba zan barsu su k`ara zama ba,Crying Baby d`in ka kuma ba zan
bari wani abu ya same ta ba,ko kuka ba zan bari ta yi ba"

Sai a lokacin ya d`an saki fuskarsa,"Ikon Allah ni narasa wacce irin shak`uwa ce tsakanin Jaheed da
kuma Jadeeda ko da yake shak`uwar da ke tsakanin ki da shi ne ta koma kanta".

''Yamma na k`ara yi bari mu zo mu tafi,sai kuma Allah yai mana dawowa,My Boy ka kula min da kan ka
ka ji,in sha Allah zamu dawo lafiya".

"Momynah mu je in raka ku,sai driver ya dawo da ni", Jaheed ya kai maganar ya na mai kama hannun
Jadeeda su kai hanyar fita,kasancewar ta Na cika Shekara d`aya ta fara tafiya, saboda k`iriniyarta, sai
faman zuba mashi gwaranci da ba a ganewa ta ke,sai da suka koma sashen Mama Hadiza suka zauna
gami da sake yi mata ban kwana kafin su fito su tafi.

Har farfajiyar Gidan Mama Hadiza ta rako su,gami da yi masu tarin Addu'o'i.

"Ikon Allah Hibba, yanzu ke ko kunya ba ki ji ace da wannan arniyar ki ke jerawa kuna tafiya har ma
kina bata `yar ki ta d`auka,gaskiya na yarda baki da hankali da ace kina da hankali da ko bangon
Gidannan ba zaki bari ta shafa ba balle har ki shigo da ita cikin Gidan ko kuma ta samu hanyar ko damar
da zata ta`ba miki d`iya ba", Cewar Zaliha da ita ma ta fito da shirin tafiya Na ta Gidan.

" Ahaf ai ke kya fad`a a zauna lafiya da nice na fad`i wannan zancen da yanzu an taso min kamar za a
cinye ni d`anya ba gasassa ba,wani dan jin dad`i sai yace k`azafi nai masu ko kuma neman fitina nake".

"Omg da wa wannan Matar ta ke,kar dai ace da ni take,kar a ce ni take Kira da Arniya?".

" Kin ga Cecelia na rok`e ki ki zo mu tafi,kar ki biye mata ki zo mu tafi".

"Gaskiya babu inda za ni har sai ta gaya min dalilin da yasa ta kirani da Arniya kuma a saboda wanne
dalilin ne zai sa a hana ni d`aukar d`iyar d`an'uwana ,sai naji dalilin".

" A'a dan Allah ki barta ki zo mu tafi,kar ki biye mata"....

"A'a Hibba ki barta dan Allah, ai mu yau abun murna ne ace yau an samu wanda zai maida masu da
murtani ki barta".

"Ke Yarinya kar ki min rashin kunya,dama Na sha jin ance ba kunya ce ta ishe ku ba,balle a kai ga kan
tarbiya"....

"Haba dan Allah Yayah Zaliha me ki ke aikatawa haka sai kace wata mara hankali ko mara ilimi".

Baki bud`e Yayah Zaliha ke bin Alk`asim da Ido gami da rasa abinda zata ce da shi," Alk`asim ni kake kalla
ka danganta da kalmar hauka da kuma rashin ilimi, Anya kuwa kai ne ?".

"Na fad`a fiye da haka ma zan kira ki da shi,in ba haukan ba mai zai sa ki furta duk abinda ki ka furta ko
so ki ke ki zama silar tashin wata sabuwa fitina a cikin Gidannan wacce ba zamu iya kashe ta ba,in kuma
rikicin Addini ki ke son tadawa sai ki sanar da mu mu sani tunda wuri".

''Au Alk`asim me nake gani haka,ashe kai ma an shanye ka ban sani ba?"Baba Asabe ta tambaya cike da
mamakin abinda ta ga yayi.

" Ka ga Alk`asim ka fita a cikin wannan maganar kar abun ya girmama,don wallahi hak`uri na yafa
k`arewa".cewar Hibba

"A'a Hibba Dan Allah kar kice haka, kiyi hak`uri kin ji", kallon shi ya maida hankalin shi kan Cecelia da ke
ta faman `bata rai,da son barinta ta bi kadin laifin kofin zarafin da akai mata.

"Kin ga please and please Sis kiyi hak`uri,don't mind her shi's out of her senses,please Dan Allah", sai a
lokacin Zuciyar Cecelia ta fara yin sanyi ,kallonta ta maida kan Yayah Zaliha yanda taga tana ta `ba`batu
da hayaniya yasa ta yarda da Maganar Alk`asim cewar bata da hankali, bai bar su ba sai da ya tasa
k`eyarsu ya fitar da su daga Gidan daga ita har Hibban,daga k`arshe ma har cikin motar shi yasa su ,shi sa
kan shi ta maida su Gida,bai bar Cecelia ba har sai da ya ga ta yarda gami da sakankancewa Yaya Zaliha
ba ta da isasshiyar lafiya sannan ya tafi,gami da gargad`ar Hibba akan kar ta kuskura ta sake tada batun
ta bar shi su tafi a haka,.
Ko bayan tafiyar Hibba ta je da niyar ta bata hak`uri, dakatar da ita tayi gami da nuna mata ta riga da ta
fahimci daga inda matsalar ta ke,komi ya riga da ya wuce a wurinta.

Sosai Hibba ta ji daɗin hakan nan ta barta domin ta je ta sauke Sallahr da ke kanta,ita kuma ta fad`a
bathroom don tai wanka,tun kafin ta fito ta fara jiyo wayarta Na faman ringing a gurguje-a gurguje ta fito
ta nufi inda wayar ta ke.

"Oh my friend Gloria how fa now ya ki ke,I miss you".

"Ina lafiya k`awana gobe nake son in taso saboda ina son ayi komi na bikin ki tare da ni"," Yeehhh Na ji
dad`in haka sosai shi yasa na ke k`ara sonki".

"Hmmmm ai dole ne in yi ina Broth Daniel yake fatan dai yana lafiya, kin san har da son sanya shi a Idona
da nake ya sa nake son halartar bikinnan da wuri,bana so a ce ya zo bamu had`u da shi ba,kin san har
yanzu ina jin sa a cikin raina na kasa iya mantawa da shi"...." Gloria Anya kuwa...,wai me ya ke damun
ki,kin fa san Broth Daniel yayi Aure yanzu ma haka yana d`iyarsa ba za ki kyale shi ki huta ba,ki samawa
kan ki lafiya Kema ki fiddo Miji mai sanki ki aura ba,kar fa ki manta ba addinin mu d`aya da shi yanzu ba
".

" Cecelia ba zan iya ba,ba zan iya cire son Daniel daga cikin Zuciyata ba kuma ni Addinin shi bai dame ni
ba,in har zai Aure ni,kuma wai tsaya ba Mace ce ta yaudare shi har ya bar Addinin sa na gaskiya ba,to ba
kya tunanin haka nima zata kasance ta nawa `bangaren ba".

"Hehhh Gloria I'm swear ba ruwana ,kin san yanda yake Son Matarsa da `yarsa kuwa,domin yanzu haka
ina Gidan su Gobe za mu tafi Jos d`in tare".

Zumbur Gloria ta mik`e zaune daga kwancen da ta ke,tace," Seriously da gaske ki ke Cecelia ",sai da
Cecelia ta d`an `bata fuskarta kafin ta bata amsa da cewa," Eh mana da gaske nake kin san ai ba zan maki
irin wannan wasa ba".

"Na sani....na sani Cecelia, but ina neman alfarma a wurin ki na had`a ki da Allah kar ki cemin a'a, ban
san mai zai faru ba in baki amince ba".ta kai zancen muryarta na marairaicewa.

" Shikenan shikenan faɗamin me ki ke so a garuni,amma ki sani idan har abun akwai cutarwa a cikin sa
ba zan yi ba".

"No...no there are no any harm in it,kawai dai ina son zan biyo flight gobe ya sauke ni nan Kano, ke kuma
sai ki san yarda za ki sa Broth Daniel ya yarda ya amince mu tafi tare da shi zuwa Jos a motar sa"....

" Wait.. Wait.. Kina nufin gobe tare da ke zamu yi tafiya tundaga nan Kano har zuwa Jos ?".

"That's my friend haka nake nufi",shiru na wani d`an lokaci kafin tace," Anya Gloria ba wani abun a `boye
ki ke shiryawa ba da har ki kai saurin yanke wannan hukunci a wannan short time d`in ba".
"Oh Jesus na rantse maki ba abinda nake shiryawa kin san ni fa you know me,duk abinda zan iya aikata
kin sani,just one thing I know ina son ganin sa,ina son in ganni a kusa da shi kin san mun yi taking d`in
long time ban gan shi ba".

Shiru Cecelia tai tana,mai son gasgata abinda Gloria tace da ita,horns d`in motar sa da ta ji ne ya sa ta
yanke hukunci cewa da ita," let me try but amma ki sani ba zan wani zafafa duk hukuncin da ya yanke ya
yanku,zamu d`auke shi a haka kawai ".

" Eh I'm agree Na yarda",Gloria tace ta na mai saurin a je wayar tana mai rufe idanunta gami da had`e
hannayenta wuri guda ta fara addu'ar samun nasara.

"My Broth har ka dawo?",ta tambaye shi tana mai kama kanta alamun tana da abinda take son cewa,"
Are you OK Cecelia, ko da akwai wani abun da ki ke so ne?".

In'ina da kame-kame ta fara Wanda har sai da ya sa gaban Hibba fad`uwa don ita a tunanin ta ko abinda
ya faru a Gidan su zata sanar ma sa da shi,kafin ta bud`e baki ta samu damar dakatar da ita har ta riga da
da cewa.

"You know my friend Gloria wannan neighbor d`in nan ta mu,...wacce na baka labarin sun koma Lagos
da zama?"ta,kai zance a d`an d`arare.

" Oh Gloria your best friend ?","Yauwa ita mun yi waya da ita ne d`azu take cemin gobe zata bi flight
daga can Lagos d`in zuwa Jos don tai attainding my wedding ceremony ,amma yanzu cikin rashin sa'a ta
kirani ta ce bata samu ba sai flight d`in zuwa nan Kanon,ta ce min tana son zuwa amma ba ta da wata
hanyar,da zaran ba ta samu wannan damar ba shikenan ba za ta attainding ɗin bikin ba, shine na ce in ba
damu in tambaye ka ta biyo flight d`in zuwa nan Kanon in yaso sai mu tafi can Jos d`in tare da ita,idan ba
damuwa,domin na dakatar da ita na ce sai na tambaye ka".

"Oh Cecelia me ye abun damuwa a cikin wannan, bikin ki fa zata zo,AI ko daga Lagos d`in tace inje in
d`aukota ai zan je in d`aukota balle kuma daganan zuwa Jos, kar ki wani damu ki ce mata ta shirya ta
taho kawai abinta zamu jirata", wani tsalle Cecelia ta daka tana mai fad`awa jikin sa gami da jero nasa
godiya kala-kala.

" Kin ga sake min Miji kar ki je ki karya min shi",Hibba tace tana mai k`ok`arin rabata da jikin sa,"Kai Sis
duka ni d`in nawa na je da zaki ce zan karya shi ?","A'a ba anan take ba,yanzu sai ki ga tsautsai ya gifta ki
bar ni da Allah yai abun,bayan ke kuma fa naki Ango na can sabo dal yana jiran ki".

Rufe fuska Cecelia tai ta nufi d`akinta tana mai had`awa da gudu ,wayarta ta d`auka gami da kiran Gloria
kamar jira taje ta d`aga tare da cewa,"My friend what is the feed back fatan dai anyi nasara ?","Yeeee
we succeed mun yi nasara",wata k`ara mai k`arfi Gloria ta saki gami da mik`ewa tsaye ta fara tsalle akan
gadonta,Wanda wannan k`arar ce tasa Cecelia saurin kashe wayar ta.
*JADEEDAH*



(It's a story of two love birds who are so different from each other )

STORY & WRITTEN BY :

(*Cwt~Sumiey*)

Marubuciyar littafin

MENE NE ABIN YI ?

KARAGAR MULKI

And now.....*JADEEDAH*



https://chat.whatsapp.com/CWkZfMqvD4H0mtd7WW6Xbz

https://whatsapp.com/channel/0029VapqU8C002T5Bz8RSQ0a




BOOK 1




PAGE 12 ❤

"Wawooooo my friend you look so awesome, kin ga yadda skin d`in ki ke shining and glowing wai
mene ne sirrin ?".

"Yeehh Thanks my dear it's a God luck,bayan haka ba wani abu,amma na gode da yabon ki", ta kai
zancen ta na nai jujjuya jikin ta,ta d`an dakata ta na mai cewa," Ina my love yake na ji ban ji motsin kowa
a Gidan ba".
`Bata fuska Cecelia ta yi kafin ta ce da ita,"Za ki fara ko,kin san na fad`a maki bana son irin haka tunda
farko,Na gaya maki Broth Daniel yana san Matar shi,kuma ma Matarsa na son shi,Matanan fa
bahaushiya ce kuma kin san halin Hausawa ba sa da kirki ko mutunci in dai akan Mazajensu ne".

Yamutsa fuska Gloria tai kafin tace,"I swear bata gabana,haka kuma duk abinda za tai ba zai tsorata ni
ba ko da ko kan bala'i da masifa zata rik`a cizon sama ne,muddin Daniel zai nuna yana sona ta nayi
alk`awari sai na Aure shi ba tare da duba da ita ba,Matsala d`aya ace bai nuna interest d`in sa a kaina
ba"..

"God for bid in dai Broth Daniel ne ma ba zai nuna ba domin kin san ni bana son tashin hankali, ba zan
so ki zama silar tarwatsa farin cikin da yake samu a Gidan shi ba".

Cikin mamakin jin abinda ya fito daga bakin,ta ce" Cecelia me wannan maganar taki take nufi ,kaddai
ace kina nufin kin fifita wannan baren kaina,kamar fa haka maganganun ki su ke nunawa,in ko haka
ne".....ta dakata sakamakon jin nuryar Hibba na cewa, "Ba dai har bak`uwar tamu ta iso ba,a sannu da
zuwa your highly welcome".

"Yauwa sannu Aunty ya Gida mun same ku lafiya,ya kuma shirye-shiryen biki ?".

" Alhmdllh kumi na tafiya yanda ya kamata, ki samu wuri ki zauna Cecelia ya akai ki ka barta a
tsaye ,yauwa gama breakfast can ki had`o mata may be ko tana jin yunwa kinsa ba kowa ke son ya ci
abinci a yayin da zai tafiya ba",ta kai zancen tana nai maida kallonta akan Cecelia.

"Muna gaisuwar yaushe gamo ne shiyasa, amma bari in had`o mata", tayi hanyar derning d`in har ta
fara bud`e wermars d`in abincin ta dakata ta na mai cewa," Amma dai Broth fita yai naga kamar ban ga
motorn sa a waje ba?".

"Eh fita yai ya samu urgent call ne a office shiyasa ya tafi can ko breakfast bai yi ba".

"Eyyah nasan hankalinsa nanan domin ya ce min baya san mu yi dare a tafiyarnan"....

Cikin rarraba zance Gloria ta dakatar da ita da cewa," Am...uhmm...ki bar zuba abincin ina so zan yi
using resting room,in..Na fito sai ki zuba min".

"OK badamuwa muje na raka ki",koda shiga Gloria bathroom kai kawo ta farayi tana mai cewa," Ya
zanyi,ta ya zan iya dakatar da Cecelia daga zuba abincin nan I need to eat with Daniel, Na kwashe almost
a year ban had`u da shi ba,yau na samu damar da zanci abinci tare da shi ya za ai in wasa da ita,No haka
ba zata faru ba I will use this opportunity I can't not lost it ".

Shiru-shurun da Cecelia ta ji ne yasa ta fara knocking bathroom d`in ta Na mai kiran sunan
Gloria,"Are you ok,Na ji shiru har yanzu ba ki fito ba ?"," I'm coming" ta bata amsa a tak`aice.

"Dem it,wai me yake damun Cecelia ne,Anya kuwa zata Goya min baya in samu hanyar da zan mallaki
Daniel kuwa I don't think so,bana tunanin haka,amma ko in har ta juya min baya ta biye ma wannan
Hausa girl d`in nan ta ci amanar zaman tare,dan haka ba zan barta ba,dole zan bi komi har in gano
abinda ke cikin Zuciyarta sannan in yi maganin su gabad`aya", wannan duk maganganun da Gloria ke yi
ne a cikin Zuciyarta.

K`arar bud`e Gate da shigowar Motar shi cikin farfajiyar Gidan ne yasa Gloria saurin nufar hanyar fita
daga bathroom d`in bayan murmushin cin nasara ya bayyana a kan fuskarta.

"I'm sorry Beb I keep you wait cikina ne ya d`an `baci that's why", Gloria ta kai zancenta tana mai sosa
k`eyar ta.

"Hhhhhhhhh my friend kenan k`ya gama `boye-`boyen ki I know you,I kno everything, ke dai kawai ki
ce kina son ki yi breakfast da my Broth,ba sai kin shiga bathroom kin rufe kan ki ba".ta kai zance cikin
yanayin tsokana.

" Au Abar tsokana ma Na zama wurin

10 / 37