Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Jadeedah Complete Hausa Novel by Cwt Sumiey

Author :  Cwt Sumiey Category :  African Stories & Novels

Chapter   21 / 37

60K to 63K   out of 108.5K words

shi a jikinsa,a hankali ya d`ago ya Na kallon shi ya ce da
shi,"Abbu barci na ke ji gashi kuma ina jin yunwa",runtse idanuwan shi yai ya na mai sake jin zafin irin
rayuwar da ta ke gudanarwa tsakanin sa da Ummu Nurain, da kan shi ya tashi ya had`a mi shi abinda zai
ci d`an simple yana jin ya k`oshi anan take barci ya kwashe shi.

Zaman shi ya gyara akan gadon bayan ya d`auko System d`insa da wayoyinsa,kamar jira ake sai ga video
call d`in Gimbiya Ayush ya shigo wayarsa,sai da ya ji wata natsuwa ta zo ma shi kafin ya picking call d`in,
duk yanda ya so ya kauda damuwar dake kwance a saman fuskarsa kasawa yayi don a kallo d`aya da tai
mashi ta fahimci hakan,duk da tun bayan da yafito daga Part d`in yake fad`a da Zuciyarsa akan kar ta
sake kawo mashi abinda ya faru a cikin ransa,amma ina hakan ya faskara.

"I'm sorry Mijin Gimbiya ban so ta dalili na ranka ya `baci ba ,ban so ace saboda damuwata za ka ga
tsawon darennan cikin damuwa da `bacin rai ba",Kauda zancen yai ba tare da ya ce komi akan abinda ta
ce ba sai tambayarta yai da cewa,"Ya jikin na ki I hope ba wata damuwa,ba wani sauyin yanayi da ki ke ji
a jikin na ki?"," I'm feeling much much better, ba na jin komi","Are you sure?,kin san siled mistake ya ke
coursing big problem, ko cikin dare da zaran kin ji sauyin yanayi ki sanar da ni,komin k`ank`antar ciwon
da ki ka ji,kin ji".

"Okay Mijin Gimbiya I'll inform you", ta amsa mi shi cikin respect gami da d`orawa da cewa,"Da zaran
ciwon ya zo zan zaro masa Ido gami da daka ma shi tsawa in sanar da shi koni Matar waye,nasan da
zaran ya ji hakan zai ruga ya bani wuri".

Murmushin ya saki wanda dama shi ta so ya kafin ya ce da ita,"Ina maki fatan ki kasance cikin amincin
Allah har zuwa safiyar gobe daga k`arshe kuma ina mai baki haƙora akan rashin kasancewa da nai tare da
ke a lokacin da ki ka fi buk`ata ta", ya na kaiwa nan ya ending d`in Call d`in, gami da gyara kwanciyar
yaronsa a Jikinsa da haka barci sarkin ita sata ya sace shi bayan ya gama shan gwagwarmaya da
Zuciyarsa kan ta manta da abinda ya faru.




*JADEEDAH*



STORY & WRITTEN BY :

(*Cwt~Sumiey*)



Marubuciyar littafin

MENE NE ABIN YI ?

KARAGAR MULKI
And now.....*JADEEDAH*



*YOTA*

BOOK 1




PAGE 25❤



"Yauwa Momy bari in k`ara maki da wannan so nake ki cinye komi dake soman table d`innan",
Jedeeda ta fad`a ta na mai k`arama Momynta Plantains ɗin dake gabanta.

" Jedeeda na k`oshi tun d`azu kin san ko lafiya na lau ban cika son cin abincin mai nauyi ba,Na ci
omelette,Na sha Oat,kuma yanzu ki ce za ki k`ara min da plantaint,Haba ya isa haka".

Turo baki gaba Jadeeda tayi kafin ta ce,"Momy so na ke fa na ga kin maida jikin ki,kalli fa duk kin
rame,ba na son ganin ki a haka".

"In banda abun ki Jadeeda,Ai sai da muce mun gode ma Allah, Matar da ko Tea bata son sha ,yanzu ta
zage ta ci wad`annan,ai lamari yayi kyau", Cewar Granny da ke zaune a gefe.

" Mom ai haka Jadeeda ta ke bata da natsuwa ko kwanciyar hankali indai akace maki Momynta ba
lafiya,in kin ga ta huta to ta samu lafiya ne,duk wata d`awainiyar da kulawa ita ke yi mata ita".

Uncle R ne ya sauke Cup d`in da ke hanunshi shi kafin ya ce,"My Angle ta musanman ce hakan ya sa na
ke ji da ita,Ko ba komi tana da kyawawan halaye da za ai koyi da su"Ya ɗan dakata kafin ya cigaba da
cewa,"Wai ya Maganar Voice of Convenant, ɗin da ki ke gudanarwa ya yanayin program d`in yake tafiya
fatan kuna Succeeding yanda ya kamata?",ya kai zancen da sigar tambaya tare da maida akalar zancensa
kacokan kan Jadeeda.

Yanayin yanda ta fara raba idanunta ya sa Gloria ta fahimci akwai wani abu da ke faruwa ko ma ya riga
da ya faru,a jiye Spoon d`in hannunta ta yi kafin ta ce da ita,"My Daughter ya dai,ko dai kun fara
fuskantar wasu matsaloli ne akan program d`in na ku,shin wani abu ya faru ne?".

"No Momy ba abinda ya faru,kawai dai bana attainding d`in komi,I'm focus on you ,hankalina baya
kan komi ,tun ranar da aka kirani akasanar dani halin da ki ke a ciki ban sake zuwa wani Hall,meeting ko
kuma Church ba,in har da sunan gudanar da program d`in da na saba ne".....,"Hah...Jadeeda....
Halalujah..wannan wanne irin hukunci ne ki ka yanke, ai bai kamata ba,aikin da ki ke yana da matuk`ar
girma da lada kina fa kiran mutane ne to the word of God, so akan me za ki dakata,shin kin san iya
adadin mutanen da suke amfana da abinda ku ke,ina Sister Zarah da kuma Madam Alena suke akan me
suka bar ki,ki ka yanke wannan hukuncin?".

Fuskar Jadeeda tamkar zata zubar da hawaye kafin ta ce,"Momy ke ce fa baki da lafiya,ta ya Zan iya
maida hankalina akan wani lamari bayan ga ki kwance ba ki san inda kan ki ya ke ba"...."Ciwona bai kai
yad`a bushara da ki ke yi ba Jadeeda ,haka kuma Ciwona bai kai rera wak`ok`in ban gaskiya da yabo ga
Yesu Almasihu ba,ta ya ma za a had`a su ?".

" Anty please kiyi hak`uri ban san wannan Maganar tawa za tai coursing d`in wata hayaniya ba,biside
ma ta na da gaskiya bata da natsuwa taya za ta iya gudanar da wad`annan muhiman aiyuka za a iya
samun Matsala so please ki yi mata hak`uri za ta koma kan aikinta idan komi ya natsa".Cewar Uncle R.

"Ko ni ma mun yi wanna Maganar da ita,tunda fari uzirin da ta bani mai girma ne shiyasa na amince
ma ta har da sake bata goyan bayan,ta na iya k`ok`ari ta yanzu haka Synagogue, Church of All Nations
(SCOAN) da ke Lagos sun za`beta a matsayin wacce zata bud`e masu taro da dad`ad`an wak`ok`inta a
ranar Easter".

Gaba ki d`ansu murna su ke da jin wannan labarin dan ita kanta Jadeeda bata san da zancen ba,ba ta
san san da ta je ta rungume Papa ta na ta zuba masa Godiya ba,"Kai wanna abun farin ciki ne,Anty J za ki
tafi Lagos kuma wannan katafariyar Church d`in gaskiya da ni za ki tafi", Cewar Martin,Cikin murna
Jadeeda ta ce da shi," Kar ka wani damu gamu can mun tafi tare,Nora Kema za ka biyo mu mu tafi
tare ?", sai da ta ya mutsa fuska kafin ta ce,"No Anty J I'll Stay with Mom zan kalli komi a TV or through
the Phone".

Granny ce tace,"Abun murna ya same mu sai na ke ji kamar in tashi in taka rawa my Granddaughter
zata je SCOAN",ta fara girgiza jikinta ta na daga zaune,nan fa suka dunga nuna murnar su a fili,har Uncle
R na cewa nan gaba shine zai zamo Bodyguard na ta.

"My Daughter matso kusa da ni in rungume ki,Na ji dad`i ban ta`ba tunanin zan wayi Gari in ga irin
wannan ranar ba,sai ga shi Allah ya nuna min na rasa ta wacce hanya ma zan bayyanar da farin ciki
na,tafiyar ma ta kusa nan da one weeks ne ko ?", "Eh haka ne haka suka sanar da ni so ya kamata ku fara
preparing, in ya so sai mu tafi gabad`aya kamar hakan zai fi"..... Cewar Papa,da sauri Granny ta katse shi
da cewa," Jikin Gloria har yanzu da sauran shi zai fi kyau ace ta na zaune wuri d`aya ko da na d`an wani
lokaci ne,in ya so kai za ku iya zuwa ni sai in zauna tare da ita".

"Okay Mom yanda ki ka ce haka za ai,kai lokaci ya ja yau ne fa Edwin zai dawo Na so in shafa'a,har
zuwa yanzu ban tura Wanda zai d`auko shi ba".

" What!! Yau Broz Edwin zai dawo amma ban sa ni ba ?","Kamarya ba ki sani ba Jiya jiyannan fa muka
gama Video Call da shi,ni da na gaji ma nan na barshi shi da Nora, Martin da Granny yana ta faman
tsokanar su,kin san shi da barkwanci har ma yana cewa da ya yanke zai Kira ki".
Cikin rashin jin dad`i Jadeeda ta ce,"Mom I swear to the God bai kirani ba,ko na kira shi ma baya
d`auka mun d`au lokaci mai tsawo a haka,baya picking call d`ina na rasa me na yi masa,kuma a baya ba
haka ya ke min ba,muna da fahimta a tsakanin mu".

"I'm sorry kin ji ban San haka na faruwa a tsakanin ku ba,da ni da kaina zan kira shi in ji ba'asi amma
koma me ye I promise to you ya zo k`arshe tunda ga shi yau zai dawo Gida", Cewar Papa ya kai zancen ya
Na mai bubbuga mata baya alamun lallashi.

" Papa ka barni in je in picking d`in sha a Airport zan so in fara had`uwa da shi","Ba damuwa sai ku tafi
tare da Uncle R da Martin nasan Nora ba lalle ta je ba,ta fi son ta kasance jikin Momyn ta a koda
yaushe".Nan ya basu details d`in Flight d`in da kuma lokacin saukarsa,kana ya shirya ya fita dama yana
da inda yake son zuwa tare da su Nora ya tafi ya aje su inda suke part time d`in su na koyan Computer
kafin fitiwar Jamb d`in su.

Haka suka cigaba da hirarrakin su har time d`in ya gabato

"Uncle Miey let me take a shower before the flight arive","Take your time I'll Wait you in the car,but
please kar ki dad`e ina so mu yi sauri mu dawo,akwai inda na ke son in kai ki I need to surprise you".

Sai da tai hugging na sa kafin ta ce," I'll be right back ba zan jima ba,domin kasan ina son surprise d`in
ka, dad`i na kusan kashe ni","To ki shirya ma wannan domin kusan ya fi na koyaushe",idanuwanta ta
fiddo waje irin da sigar tambaya d`in nan,"Yes I'm sure ke dai don't waste my time ki yi sauri ki fito ",ya
kai zancen ya na mai binta da wani kallo mai cike da tarin ma'anoni,ita ko ko a jikin ta sai mik`ewa tayi ta
upstairs da saurinta domin ta shirya.

Wani dogon tsaki Granny ta saki tare da cewa,"Haka za ka k`are kullum ba ka da aiki sai d`aukar your
Niece kana yawo da ita lungu da sak`o amma ba za ka iya fitar da mata kai Aure ba".

"Mom Haba mana na ce fa zan yi Aurennan to meye na irin wad`annan k`ananun zancen"," Oh
k`ananun zancen ne ma to idan baka son k`ananun zancen ka bari ni in nemo maka Matar Auren ai ni
hakan ba abu mai wuya ba ne a gare ni".

"Ah no Mom ina da kalar type d`in Macen da na ke so ki bar ni zan nemo da kaina ,in dai Aure ne a bar
Ni zan yi,zan za`bi wacce ta yi min", ya kai zancen ya na mai barin wurin gabad`aya.

Cikin karyayyiyar murya Granny ta dubi Mom ta na mai cewa," Kalli Gloria ya tashi ya tafi ,ban san har
sai yaushe Rechal zai ji ya kuma saurari Maganata ba,har Mahaifinku ya mutu ba shi da wani buri da ya
wuce ya ga Aurensa amma Yaronnan ya k`ek`ashe idanunsa ya ce mi shi bai ga Matar da zai Aura ba har
ya mutu ya na tuna hakan, yanzuma gashinan sai fama na ke da shi ya k`i ji,wata k`ila nima ba ni da
rabon gani Auran na shi ".

" God for bid Momy za ki ga Auran shi,by the grace of God, bari ya dawo ni nasan ta inda zan `bullo
masa",haka ta ciga da lallashin ta har zuwa wani lokaci.
Sanye da gowm wacce bata kai gwuiwarta ba ta fito gashin kannan nata ya sha gyara ta sake shi har
gadon bayanta,kafarta kuwa sanye take da high heel shoe, sai k`amshin Oud da ke faman tashi a
jikinta,yadda kasan yar bebyn roba haka ta ke taka k`asa,ta yi kyau matuƙa kamar ka sace.

"Oh my Goodness Anya kuwa zan yarda mu fita tare da ke a haka,kar fa ki sa in rik`a had`a goslwo ko
accident a saman hanya,irin wanna kyau haka,na ga alama da gaske so ki ke, ki samu wanda zai huf ya
raba ni da ke".

Ah Uncle Miey ba wanda ya Isa ya raba ni da kai,domin duk wanda zan rayu da shi zai so ni bayan son
da ka yi mi ni ne,haka kuma zai kuka da ni akan kulawar da ka ba tun ina `yar karamata,har kawo
girmaba".

" Har yanzu ke Baby ce a gare ni,ban k`i in d`auke ki in goye a bayana in zagaye Gidannan da ke ba,ki sa
ni kina da matsayin mai girma da muhimmanci a wuri na duk da kullum a cikin zullumi da fargaba na
ke",ya kare zancen ya na mai matsowa kusa da ita.

Cikin yanayin Maganar da ya yi ta shiga ranta ta ce da shi,"Uncle miey me ye yake sa ka cikin Zullumi
da fargaba a kaina ba tare da na san shi ba?",sai da ya kamo hannunta ya rik`e a cikin nasa kafin ya ce da
ita,"Ina tsoran ranar da za ki bar ni ranar da za ki za`bi wani sama da ni ranar da za ki fifita Soyayyar wani
akan tawa ban San ya Zuciyata za ta kasance ba ,tabbas zan iya rasa rayuwata akan haka",da sauri ta kai
hannunta saman bakin sa ta rufe tare da cewa,"Uncle Miey haka ma ba zata faru ba,kai jini na ne kuma
rayuwata babu ta yanda za ai wani ya shigo rayuwata jiya ko yau ya ce zai maye gurbi ko matsayin ka a
wurina ka sani ba zan ta`ba barin ka ba a koda yaushe zan rayu da kai ,a duk inda na ke ba abinda na ke
tunawa indai har za a ambaci ko me irin sunan ka ne face na tuna,kulawa,Soyayya karamci da halacin da
ka ke min".

"Da gaske ba za ki barni ba,ko da kuwa nan gaba,ba za ki ce nayi ma ki tsufa ba", ya fad`a ya na mai
damtse hannunta dake cikin na sa.Dariya sosai Jadeeda ta saki jin ya ambaci tsufa,`bata fuska ya yi,tare
da cewa,"Au dariya ma na baki to shikenan sai ki cigaba tunda na zama abun dariya".

" Oh sorry Uncle Miey ba haka na ke nufi ba,just kawai na hasaso fuskarka da furfura ne shiyasa Na ke
dariya",shima dariyar ya yi gami da sa hannu ya bud`e mata front seat wurin zaman banza kafin ya shiga
ya tada motar su tafi,suna tafe ta na tsokanar shi.




*JADEEDAH*



STORY & WRITTEN BY :
(*Cwt~Sumiey*)




Marubuciyar littafin

MENE NE ABIN YI ?

KARAGAR MULKI



And now.....*JADEEDAH*



*YOTA*

BOOK 1

PAGE 26❤



Saukar Jirgin yai dai-dai da bugawar k`arfe 5pm janye da trolleynsa ya fito sai faman kai hannu ya ke
na rik`e kan shi alamar yana sara ma sa ne ko kuma ya na ciwo.

"Momy", shine abinda ya furta daga can k`asan bakin shi bayan ya cikaro da abinda ya ke a gaban
shi,"Irin wannan ai sai kisa in fita da gudu taya za ki ba Security welcoming card d`auke da suna a jiki ai
sai wani ya yi tunanin mai laifi ne ni", shine abinda ya fad`a har ya idasa kusa da shi ya ce mishi," Hii I'am
Edwin Anderson "," Hy nice to meet you, how was the trip I hope you enjoy it",ya kai zancen ya na mai
mik`a masa wata flowers da ke gefan shi wacce ta ke d`auke da wata Paper,amsa yai gami da yi masa
Godiya kafin ya fara warware Paper.

Sannu-sannu ya kai kan shi inda su Jadeeda su kai parking, ta hanyar wanna Paper,gabad`aya ya zak`u
hankalin shi na kan motar ya k`osa ya isa ya rugumi Momynsa a jikin sa

"Momynah sai kin gama wahalar da ni sannan za ki bari in ganki,kin san fa na yi kewar ki,", shine
abinda ya ce bayan ya Isa gurin Motar, yanayin yanda aka saukar da glass d`in Motar da fara k`ok`arin
fitowar da akai sai da ya sa gaban sa ya fara bugu da sauri da sauri,har sai da ta kai ya fara kai hannunsa
ya na dafe kan shi da Ya tsananta ma shi da ciwo.

Da gudu Jadeeda ta fito ta yi kansa ,da hannayenta bibiyu ta rik`a kai masa duka a duk inda ta samu a
jikin sa,shi kuma kasa dakatar da ita yai har sai da ta yi mai isata kafin kuma ta koma ta rungume shi a
jikinta ta Na mai cewa," Me na aikata ma ka, wanne laifi ne na yi maka da har na yi diserving irin wannan
punishment d`in,Na zama wararriya a cikin ahalin ka bayan kuma a da,Na fi kusanci da kai akan kowa,
me na aikata maka ka sanar da ni?".

"Ki yi hak`uri na amshi laifina,kuma a shirye na ke da in amshi wani sabon hukunci fiye da wannan da
na amsa a yanzu,amma kafin nan ina so ki sani ba ki aikata min komi ba"....ta katse shi da cewa,"
What?!,Shut up ka na nufin hakanan ba tare da na yi maka komi ba ka sauya min,no wannan ba abu mai
yiwuwa ba ne".

"Please and please na rok`e ki da ki bar wannan maganar mu je Gida ,zan ma ki bayanin komi yanda za
ki fahimta,ki sa ni nima kaina ina cutuwa da rashin ki a tare da ni".

K`arasowar Uncle R wanda ya tafi samoma Jadeeda ruwa sakamakon sark`ewa da ta yi da miyau itace
ta sa shi ya d`an dakata ya nufi wurin shi da sassarfa ya na mai murnar ganin sa," My son Edwin kai ne ka
zama haka gaskiya ba k`aramin amsar ka Gidan Sojannan yai ba,see you yanda ka kere ni a tsawo",ya kai
zancen ya na mai janyo shi Jikinsa ,nan fa suka shiga mota cike da farincikin a fuskokin su,Jadeeda k`in
zama front seat d`in tai ta koma can baya wajen Edwin sai faman cika shi da surutu ta ke ba tare da ta
fahimci halin da ya ke a ciki ba.

Tarba ta musanman ya iske lokacin da su ka Isa , tarbar da bai yi zato da tsanmani ba,kar ma Momy
yanda ta zage ta na kula da shi da kuma Jan shi a jiki dama can Momys Son suke kiran shi,shi da

21 / 37