Author : MEELAT MUSA Category : African Stories & Novels
wani tunani ya faɗo mata, ita kaɗai tasan ko miye ta , dan haka fita tayi daga gida, haka ta shiga fafutukar neman kuɗi, daƙel ta samo su, ba gida ta dawo ba, haka ta shiga gari ta nemi wurin da ake siyar da kayan ɗaki masu kyau, kujeru ta siyo na alfama babu kuɗin gado don haka katifa ta siyo da tv, dadai abinda ya sawwaƙa, haka aka tsauno kaya suka yo gida,
Bayan sunxo gida wanda suka kawo kayan su suka saka mata a ɗaki, aka saka mata labule komai dai aka haɗa ma jawwahir,
Bayan an gama komai ta zauna saman kujera tace Alhamdulillah, na gama ɗaya sauran na biyu,
*Muje zuwa danjin ya zasu ƙare?"" dan wanda dai baiji bari ba, hausawa sunce bazaiƙi jin hoho ba,*
*wai wace ce jawwahir?"" sannan waye sadiq?"" waye innasco?"" waye kuma baba??""" wai duk ya jawwahir take dasu?"" kuma su waye iyayenta?"" sannan kuma mi tazo yi a gidansu sadiq?"" yaushe tazo?"" wanda har take ganin sune iyayenta?""*
*ya honey j yake a wurin jawwahir?"" ya kuma zasu ƙare da alhaji?"" ina mutane da take ta danfarewa tare da wanda take cin bashinsu bata biya?"" nidai nace duk wanda baiji bari ba,*
sai mun sake haɗuwa, meelat musa nake maku fatan alkairi,
[1/17, 7:38 PM] Jamila Musa Ws: ☄
☄☄
☄☄☄
🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥
*WANDA BAIJI BARI BA*
🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥
☄
☄☄
☄☄☄
*AMEENCI WRITER'S ASSOCIATION* 📚✍🏻
*MEELAT MUSA* 🌹
*PAGE* *14*
****
*M*alam Umar Azuba, da *Hauwa'u* wato inna sune mahaifan sadiq sadiq , ɗa ɗaya kwal wanda daga shi basu sake aihuwa ba, malam umar azuba da hauwa,u ko ince maku inna auren zuminci ne kuma tunda ya aureta har yau ɗin nan bai sake aure ba,
Malam umar ya riƙe ɗan kuɗaɗe daga baya kuma Allah ya kawo mashi ƙarayar arziƙi, wanda ya koma abinda za"aci a gidanshi yana wahalar samu, dama ita rayuwa haka take,
Sadiq koda ya taso ya taso cikin hazaƙa da ƙoƙari kuma Allah yasa mashi haƙuri a rayuwarshi dan yasan lokacin da mahaifinshi yake da "yan canji kuma da "akazo babu yasa ma rayuwarshi haƙuri,
Wannan halin yasa sadiq ya fara "yar sana"ar shi, yana neman kuɗinsa kuma Allah yasa ma neman albarka, wannan kenan,
*jawwahir* hmmm jawwahir kenan, jawwahir ba ɗiyar inna bace kuma haka ba ɗiyar baba bace, jawwahir maman ta rasu tun tana shekara biyu, da maman jawwahir da maman sadiq wato inna uwa ɗaya uba ɗaya suke, haka kuma suna da zuminci da baba,
Jawwahir lokacin da mahaifiyarta ta rasu ta barta ta taso cikin wahala da ƙuncin rayuwa, shekaratar biyu amma idan kaga yanda take ɗaukar nau"in azaba kai kace "yar shekar goma ce, dan matar babanta bata tausaya mata idan tayi abu, dan ko fitsarin kwance tayi duka take mata bana wasa ba, ganin halin da jawwahir take ciki yasa maganganun suka fara yaɗuwa a cikin dangin,
Idan aka je aka ɗauki jawwahir wani ya tafi da ita gidanshi sai tabi taje ta ɗaukota, wai an rabata da ɗiyarta, dalilin dawowar jawwahir gidan inna sadiq ne yaje kauyensu yaga halin da take ciki, shine ya sato ta , ba tare da kowa ya sani ba, dan duk "yan uwa basu san jawwahir tana wurin inna ba saida takai shekara 7 dan lokacin da sadiq ya ɗauko ta tana da shekara 3 ne,
Sadiq yana tausayawa jawwahir sosai dan idan ka bayan ta yanda sahun bulali yake a jikinta sai kaji imani yaxo maka da tausayin jawwahir, wannan dalilin yasa sadiq yake ƙoƙarin kyautata mata duk abinda take so zai mata, ta taso bata san kosa ba, sai inna da baba da sadiq da take ganin ciki ɗaya suka fita,
Lokacin da sadiq kasuwa tayi mashi tsaye ya daina samun "yan kudaɗe jawwahir ganin yanda aka sakata ne, yasa ta shiga damuwa, dan ita kullum mai daɗi ta sani, rashin cin abincin gidansu dama ya taso ne daga sadiq don baya barin taci abinci idan dai baiga wani abinci mai daɗi bane,
wannan rayuwar yasa jawwahir ta ɗauka wata rayuwar kirki ce, wannan abun yasa ta taso da rayuwar bata san babu ba, tana jss3 ne, ta boɗare sai ta koma makarantar kuɗi, daga sadiq har baba babu wanda yake da kuɗin biya mata makarantar da take so, wannan shine dalilin da yasa jawwahir ta shiga cikin harƙalar duniya, wannan kenan, tunda kunsan komai,
*Ja"afar* wato *honey j* yana san jawwahir sosai, amma kasancewar halinta iyayenshi suka ce bazai aureta ba, amma saboda san da yake ma jawwahir ya hanashi rabuwa da ita, amma duk halin jawwahir ya sani , bata da hali ɗaya na zaɓe, shi kanshi idan tayi abu mara kyau yana nuna mata ta bari, amma wanda yayi nisa bayajin kira,
mu dawo labarinmu,
*I*nna ce take tama jawwahir magana ta rage ƙarar waƙar data kunna a motarta amma idan bango yayi magana jawwahir tayi magana, babane ya fito daga ɗaki yace ke dan gidanku bakiji ana maki magana ne?"" jawwahir dake duƙe tana goge takalmi ta ɗago ta kalli baba, zufar goshin ta , ta goge sannan tace nidai gidan nan naga ansa man ido, naga kowa abinda yaga dama shi yakeyi,
yanxun nan sadiq so yayi ya kasheni Allah ya ƙautar man rayuwata, amma naga babu wanda ya kirashi a waya yace bai kyauta ba, saini dan na kunna waƙa za"aga laifina,?"" to wanda baya iya ji koya fita yabar gidan ko kuma yasa kaɗa ya toshe kunnenshi,
baba yace babu ɗaya wanda wani zaiyi, kuma dole koki rage ko ki kashe, sai kin zaɓi ɗaya, jawwahir tace duka babu wanda zanyi, inna tace wai miyasa bakijin magana ne?"" murmushi jawwahir tayi da gefen bakinta sannan tace innas kenan?"" nidai naga duk gidan duniya duk inda naga autares ji ake da ita, amma ni gani nazo a autar amma kinfi san ɗan farko, wallahi da zaman dane surutu za"ayi ta maki ace baki da kara, wannan maganar da jawwahir tayi yasa inna ta shige ɗaki,
baba yace sai kin kashe waƙar nan dan uwariyanki, dariya jawwahir tayi sannan take naga daga bakin hanya kake, acan akwai ƙarar motoci akwai masu kunna waƙoƙi, akwai "yan iskan da duk sunfi jawwahir iskanci miyasa duk bakai masu magana ba?"" saink daka ga muna kwana gida ɗaya?"" girgiza kanta tayi sannan tace shi yasa nake ƙoƙarin zama ƙauranya, da an faɗa man ba daidai ba wallahi saidai in saƙa sara, baba yace waye zaki rasa ne?"" sadiq shi zan fara cire ma kai, dan ina san labarin rayuwarshi ya shafe daga duniya baki ɗaya,
baba yace idan yaxo sai ki faɗa mashi, ya juya zai shiga ɗaki jawwahir tace ya maganar rabon gidan?"" nidai a raba a bani haƙƙina, baba yace ai gidan yanxun ba nawa bane, na sadiq ne ki bari idan ya dawo sai ya raba ya baki naki kason,
jawwahir tace kaji banbancin ko?"" mu duk "ya"yanka ne, amma dan san kai sai ka ɗauki gida ka bawa namiji don Allah?"" aini ya kamata ka bawa, idan nayi aure aka sakeni basai in samu wurin zama ba?"" baba ya kalli jawwahir sannan yace ke yanxun har fata kike kiyi aure ki rabu da mijinki?"" jawwahir tace to baba idan naji zaman babu daɗi ai dole inyi haƙuri in dawo gida, baba yace Allah ya sawaƙe, jawwahir tace amin inda gaske kake?"", tsaki baba yayi sannan ya koma ɗaki,
bayan ta gama goge takalmin cikin motar ta shiga ta kunna ta , tayi ta cewa buuuuuu buuuuuu bummmm bummm, baba ya sake fitowa yace wai miye haka ne?"" jawwahir tace motace ke sararawa a cikin gidan su, haka dai tayi ta iskancin ta, baba ya gaji ya fita yabar gidan dan dama bacci ya dawo dashi amma dole yanxun ya haƙura,
haka jawwahir tayi ta iskancin ta, daga baya ta nufi ɗakinta danyi wanka,
saida ta gama shirin ta tsaff sannan ta fito ta ɗauki motar ta tabar gidan, ƙawalu baƙe gareka alhaji,
tun daga waje alhaji ya hango jawwahir, da sauri yace ma masinjan shi idan taxo yace baya nan, yace to, jawwahir kuwa tana fitowa office ɗin Alhaji ta tun karo, koda akace mata alhaji baya nan, tace ma masinjan kai da Allah matsa bani wurin kafin inci ɗammara kn fara ci maka mutumci a wurin nan, ƙin matsawa yayi dan haka tureshi jawwahir tayi ta shige office ɗin,
Gaban alhaji sai faɗuwa yake, amma dole ya dake, jawwahir ta samu wuri ta zauna, Alhaji ya kalli jawwahir sannan yace mi kuma akayi ne?"" jawwahir tace ban sani ba, dan ka ganni zaka ace man baka nan ko?"" to ai naxo sai kayi yanda zakayi dank?"" kuma kaje ka faɗa a gidanmu ni karuwa ce ko?"" ka faɗa ma sadiq kayi man kiss ka shashshafa ni ko?"" to da kyau amma inaso ka sani yanda kayi man nima sai nayi maka, kuma nice zan zama ajalinka, idanuwa alhaji ya zaro da niyar yin magana, amma ina tuni jawwahir ta fice daga office ɗin,
Hankalin Alhaji ya tashi zufa sai keto mashi take, hankalin shi ya kasa kwanciya, dan haka ya fito daga office cikin tashin hankali, ya fara faɗa ma mutane jawwahiri tace itace ajalinshi sai kuka alhaji yake kamar ƙaramin yaro,
wasu na cewa Alhaji yaje wurin "yan sanda yayi reporting amma yace yayanta zai kira ya faɗa mashi, wasu suce kada ya tsaya kiran sadiq wasu kuma suce ya kirashi,
Alhaji ya shiga cikin tashin hankali, sosai, tunanin jawwahir da kallamar data faɗa yake tunawa, wai itace *AJALINSHI* cafff kaji wani shirme, Wanda dai baiji bari ba,🤣,
jawwahir tana fita dariya tayi sosai, harda hawaye, tana tuna yanda alhaji ya zaro ido da yanda ya fara zufa lokaci ɗaya, dariya tayi sosai sannan tace shege ai yanxun ka kiyayeni, niko nace keda zaki kiya duniya, tunda dai baki jin bari,
itadai jawwahir batayi wannan abun dan wani abu ba, sannan kuma batayi dan niyar ta kashe alhaji ba, tayi ne kawai dan yaji tsoronta, kuma ya kiyayi haɗata da sadiq, amma furuci marar amfani baya da kyau, sai mu kiyayi harshenmu, duk yanda muke cikin ɓacin rai musan abinda muke faɗi kada mu bari zuciya da sheɗan sukaimu su baro mu,
Daga office ɗin alhaji jawwahir gidansu hafsat ta nufa, tace maganar party a bari ba yanxun ba, dan tana so sai yayanta ya dawo, tana so ta ɓata mashi rai, hafsat tace babu damuwa, bayan sun gama firarsu ne jawwahir tayi ma hafsa ban kwana ta nufi gida,
***
*K*wana ukku da faruwar matsala tsakanin jawwahir da Alhaji, saboda haka Alhaji ya samu number sadiq , ya kirashi ya faɗa mashi yanda sukai da jawwahir, kuma ya ƙara mashi da cewa wasu sunce yakai ƙararta amma baiyi hakan ba, saboda haka sadiq ya shiga tsakanin su, sadiq yace to ya gode sosai kuma yayi haƙuri, zaizo zo kwanan nan, kuma insha Allah zaiyi maganin matsalar , sannan sadiq yace ya turo mashi number jawwahir danshi baya da number ta ma, alhaji yace to, niko nace mi zai dawo da sadiq bayan yace idan ya tafi sai bayan shekara ɗaya zai dawo?""", suna gama wayar Alhaji ya tura mashi number jawwahir,
saƙon na shiga sadiq ya fara kiran jawwahir, amma jawwahir bata ɗauka ba, haka yayi ta kira harya gaji, dole ya haƙura ya daina kiranta, ya tura mata saƙo,
```Ki ɗauki waya zanyi magana dake sadiq umar azuba```
lokacin da jawwahir taga saƙon ta karanta, ita tura mashi tayi kamar haka:•
``` anƙi a ɗauka , kaji hada wani in ɗauki waya sai kace kaine ka siya man,?"" kuma saboda wayana ma daka saka a rijiya, sai naja maka, la"uƙusumi biyaumil ƙiyama, dan ban yafe maka ba, har lahira nake nufi```
Lokacin da sadiq yaga saƙon abun dariya ma ya bashi, lallai jawwahir mahaukaci yace.,, wato la"uƙusimi biyamul ƙiyama, kam amma wannan yarinyar Allah ya sawaƙe,
sake tura mata saƙo yayi,
```banza ki bari sai kin fara sallah, jahila kawai dake```,
kam babbar biredinda boter"" jawwahir tace lokacin da ta gama karanta saƙon sadiq, tsakar gida tayo da gudu tace ma inna wallahi innas nidai sadiq ya wulaƙanta ko?"" nice jahila?"" kuma wai bana sallah, inna tace ai ba ƙarya ya faɗa ba, babu sallah babj salati, baki ajiye komai ba sai zalinci da cuta a ranki, daga danfara sai yaudara, amma ita yaudarar kanki kikai mawa, Allah zai huƙunta ki da wannan halin naki jawwahir ,
ganin inna bata goyi bayan ba, jawwahir ta koma ɗaki tana kuka, saida ta gama kukan wanda taji ta gaji, agogon hannunta ta duba, taga 3:38,pm tsaki tayi sannan tace bari inje inyi sallahr, niko nace daga baya kenan,
***,
*K*wanaki biyar da faruwar hakan sadiq ya dawo, lokacin da yaxo gida jawwahir bata nan, daga inna sai baba, duk da yau ya dawo bai hana inna da baba yi mashi faɗan abinda yayi ma jawwahir ba, su duka biyun sun nuna damuwarsu, kuma sun nuna mashi bai kyauta ba, faɗa sosai sukai mashi , inna tace ban hanaka hukunta ta ba, amma kasan irin dukan zmda zaka mata, yace to, bayan ya gama abinda yake , zai fita ne, inna tace mashi gobe zataje kauye ganin hajiya ko zaije ne?"" sadiq yace ah ah, zaije daga baya, sallama yayi masu sannan ya fita daga gidan,
Tun a hanya yake cewa wato yarinyar nan ta gina ɗaki wato duk abinda zanyi inyi?"" wata zuciyar tace mashi abinda take nufi kenan mana, sadiq yayi magana a bayyane yace aiko zataci ubanta wallahi,
Koda jawwahir ta dawo babu wanda ya gaya mata sadiq ya dawo, itama kuma batayi ma kowa magana ba, ta shige ɗakinta,
***
da safe inna tayi shirin ta tsaff dan tafiya kauye, don haka batayi ma jawwahir ma bankwana ba, shima baba yayi tafiyarshi wurin neman abinci shi,ita kuma jawwahir tana ɗaki tana bacci cikin jin daɗi da kwanciyar hankali,
sadiq kuma kamar yanda yasa kalilu idan yaga fitar inna da baba ya faɗa mashi haka kuwa akayi, yana ganin duk sun fice ya kirashi ya sanar dashi, shima waya yayi yace ma wanda sukai wayar su sameshi gidansu,
yana gama wayar wanka ya shiga yayi ya shirya cikin ƙananan kaya, ya fito fess yayi kyau sosai ba mace ba, ko namiji yaga sadiq sai ya burge shi, yana gama shirin shi, ya nufi gida,
Sallama yayi ya shiga, wuri ya samu ya zauna, yana jiran zuwansu,
jawwahir kuma ƙarar wayarta ne ya tasheta, lokacin data farka ma har wayar ta tsinke, tsaki tayi sannan ta tashi ta shiga toilet tayi wanka da brush ta fito, riga da zani na atamfa ta saka,bata ɗaura kallabi ba, saidai ta ɗauki hijabi ta saka, makullin motar ta ta ɗauka ta fito tsakar gida,
Tana fitowa gabanta ya faɗi, innalillahi wa"inna ilaihiri raj"un tace, a ranta tace waccan jarabar kuma yaushe ta sauka?"" wato innas ta fara sake hali fa?"" yanzun tasan wannan munafikin zai dawo amma shine bafa faɗa ba,?"" a lokacin da yake cewa ku shigo mana,
Jawwahir maidai dubanta take haryar shigo dan ganin wanda zasu shigo cikin gidan, miƙewa sadiq yayi a lokacin da suke isowa kusa dashi, hannu ya basu suna gaisawa,
Kallo jawwahir tabi su dashi ɗaya bayan ɗaya amma idon ta ya kasa sauka wurin sadiq, shi kuma yace yawwa bismillan ku, a lokacin da yake nuna ɗakin da jawwahir ta gina, idanuwa ta zaro tayi ƙarfin halin tace yaya m za"ayi ne?"" kallonta sadiq yayi sannan yace anan gidan babana ne, kuma babu wanda ya isa yayi mana gini a gidanmu saini ɗan gidan, gaban jawwahir ya faɗi ta kalli sadiq tace wannan wace irin magana ce kake yi?"" sadiq ya matsa kusa da ita sosai sannan ya kallo fuskarta dan ya fita tsayi sosai, yace nasan kinji abinda nace bana magana biyu amma da yake kece zan sake faɗa maki, nace anan gidan babana babu wanda ya isa yayi gini a ciki saini kaɗai ni *Sadiq Umar Azuba* kinji ko saina sake faɗa?""" shiru jawwahir tayi sadiq yayi dariya sannan yace ko shima za"a danfare mane?"" kamar yanda kika saba kwace ma mutane motoci da kudaɗe?""" Jawwahir tayinshiru yace shirmen banza kai,
jin maganar sadiq yasa jawwahir taga duniya tana juya mata, mi sadiq yake nufi da nan gidan babanshi ne?"" kallon sadiq tayi sannan tayi magana cikin sanyi murya tace yaya kallonta yayi baiyi magana ba, saida ya ɗaga gira ɗaya alamar kina da magana?"" jawwahir tace ai nima babas da innas sune suka haifeni, kuma duk su gwaggos ɗin kauye ai duk sune gwaggo ɗina, dariya sadiq yayi a ranshi yace wato mai hali baya barin halinshi wai gwaggos kaji iskanci, ita baza tace gwaggo ba, a,a dole sai ta kara masu s , sadiq yace kai wurin nan anyi tantiriyar yarinya,
Baiyi ma jawwahir magana ba, ya kalli masu aiki yace su ci gaba da aikin su, wani yace ranka ya daɗe kayan ciki fa?"" sadiq yace idan kuna iyawa ku foto dasu,
jawwahir tanaji tana gani haka sadiq yasa aka watso kayanta waje, kuma cikin wulaƙanci ake abun, hawaye ya taru a idon jawwahir tayi kalar ban tausayi lallai maganar sadiq gaskiya ce, yau ta yadda ita ba diyar gidan nan bace, dan da a gidan nan take da sadiq baisai aka wulaƙanta ta ba,
[1/17, 7:40 PM] Jamila Musa Ws: ☄
☄☄
☄☄☄
🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥
*WANDA BAIJI BARI BA*
🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥
☄
☄☄
☄☄☄
*AMEENCI WRITER"S ASSOCIATION* 📚✍🏻
*MEELAT MUSA* 🌹
*PAGE* *16*
****
*Asmeenat xeeyan muna ma momy barka Allah ubangiji ya raya mana ɗan ƙaninmu Allah ya shirye shi ubangiji yasa makaranci Alkur"an ne, muna ma momsy barka , masu juna biyu Allah ya rabasu dashi lafiya, Allah kasa aihu ta zamar mana Alkairi ka shirya mana ziri'a, dan matsayin manzan rahama *S. A. W*
***
*J*awwahir dai har yanxun bata saduda da rayuwa ba, bashi bata daina ci ba saima abinda yayi gaba, idan taci bashinka zataje kawai ta ajiye kuɗi a bank ne, komi zatayi dasu Ohor mata,
Malama don Allah zuba mana abincin tun ɗaxu muna magana kin wani basar damu, wani mutumne yake ma jawwahir magana, tsaki tayi sannan tace da Allah gafara kada ka damenk saboda cinikin 1k idanma ka tafi ai wasu zasu xo, mtswwwww
Mutumin yace ke yarinya kada kiman rashin kunya fa, jawwahir tace idan anyi kana da magani?"" tana magana tana murguɗa baki, ga ɗamara tasha da gyale a kugunta , yanda ta mayar da rayuwarta kana kallon ta zaka ƙadda ita "yar bariki ce ta hannu,
Mutumin yace to bani kuɗina mana, jawwahir tace bazan