Author : MEELAT MUSA Category : African Stories & Novels
da kuɗi ta ɗauka, sannan ta sake gargaɗin shago da su kula kuma kada ayi mata ganganci da dukiya,
Auwal ne ya ɗauketa a mota, hada hajiya zarto itama zataje rakiyar jawahir, haka suka ƙunduma, sai filin jirgi, Auwal saiso yake yama jawahir nasiha amma bata tanko dole ya haƙura,
bayan sun ajiyeta sukai mata sallama suka tafi, ita kuwa jiki sai karma yake, za"ahau jirgi, don haka tana shiga cikin jirgi abinda ta fara sai hotuna, saida ta ɗauki masu isarta, sannan tayi ma hafsat magana a whatsapp dan basa chat kuma idan zata kirata a waya prevet no, take sakawa, amma yau da yake ƙaryace zatayi ta mata magana,
hotunan ta tura mata, sannan tace kawata naje *London* a sakani a addu"a, tana faɗin haka ta kashe wayarta baki ɗaya, saida kowa ya gama shiga matafiya lagos sannan aka rufe jirgi, su jawahir an ɗaga binne lagos,
Auwal bayan ya ajiye zarto, wayar hafsat ya kira, ya mata kira babu adadi sannan ta ɗauka, bayan ta ɗauka suka gaisa, Auwal yace don Allah ni aminin jawahir ne , ko zan samu number wani ɗan gidansu don Allah?"" hafsat tace lafiya dai?""",,,, Auwal yace inaso inyi magana dasu ne, kuma in sheda masu cewa insha Allah idan ta dawo daga tafiya, nine zan sanar dasu dan suxo su tafi da ita,
Hafsat tace to bara in turo maka number yayanta, godiya Auwal yayi sannan ya kashe wayar, suna gama wayar kamar yanda hafsat tayi alƙawari haka ta sanbaɗa mashi number sadiq,
Auwal yaji daɗi ganin number don haka da sauri ya saka ya fara kira, sadiq bai ɗauka ba, ya sake kiranshi, bai ɗauka ba, dan sadiq shima yanxun ya fara zama busy dan ya fara aiki ne, amma har yanxun bai dawo ba, yana london, a na ukkun ne, ya ɗauka, yanda yayi magana ne yasa gaban Auwal faɗuwa, lallai wannan ko waye dole lamarinsa akwai firgice, haƙiƙa akwai wani abu na daban tattare dashi,
Sadiq yace inaji waye?"" cikin in ina Auwal yace ni , nine, Sadiq yace ai nasan kaine, miye?""" yace dama , wai dama , sadiq yace dama miye?""",,,, Auwal yace jawahir ce, Sadiq yace kaima ta kwamashe maka dukiya ne?""",,,, Auwal yace a, a, nasan inda take ne, Sadiq yace tana inane?"",,, Auwal cikin tsoro yace tana kano, amma yau ɗin nan ta tafi lagos, Sadiq yace to ya kake so ayine?""",,,, Auwal yace idan ta dawo zan sanar dakai,
Sadiq yace saina jika, ya kashe wayarshi, ajiyar zuciya Auwal yayi sannan yace wai wannan duk da banganshi ba, abun tsoro ne, niko nace a tambayi jawahir,
Saduq kuwa bayan Auwal ya kashe wayarshi tsaki yayi sannan yace kai wannan yarinya Allah ya sawaƙe halinta , tsaki yayi sannan yace Allah ya haɗaki dani zaki gane kurenki, da kuɗi akace ma kije wani iskancin yawo bazaki ba, tsaki yayi sannan yace ƙafar zan ƙare ma inga da wacce zata fita,
Ko kuma in mayar da banza can kauye gidansu , dariya yayi yace sosai kauye zaki koma muguwa, ko yunwa saita ladabtar dake, dariya ya sakeyi sannan yace ga shegen bakin ya iya cin daɗi, acan fura babu nono za,a baki ,
Yana cikin haka ne, yaji wayarsa tana ƙara, dubawa yayi yaga hafsa ce, kashe kiran yayi ya kirata, tana ɗauka gaisheshi tayi, bayan sun gaisa ne, take mashu maganar Auwal yace sunyi magana da shi, hafsat tace to yanxun tace man zataje london ne, dariya sadiq yayi sannan ya kashe wayar, lallai wato london ma zata zo, hmm tsaki yayi sannan yace dama Allah ya kawoki london ɗin da kin zama swry,
kiran hafsat ya sake shigowa, kashewa ya sakeyi ya kirata, tace na tura maka hotunan data tura man, sadiq ba damuwa zan duba, sannan ya kashe wayar,
Saida yayi wanka, sannan ya ɗauki wayarshi dan duba, hotunan da hafsat ta tura mashi, kallon hotunan yayi ya ƙara kallon su, gaba ɗaya jawahir ba haka yayi tunanin ganinta ba, duk ta rame tayi baƙi, tsaki yayi sannan yace to ina mafanin irin wannan rayuwar don Allah?"",,,, haka nannsai yaji tausayinta yace kai Allah ya shiryar dake,
jawahir ga ƙarya, yace wallahi kilama babu wani inda taje , tsaki yayi sannan yace Allah ya sawaƙe,
Su jawahir an iso lagos lafiya, don haka an wani sauko daga saman jirgi, jin kanta take kamar ba ita ba, saidai a kwashi fili a ɗauki hoto cutt, sai iskanci take , saida ta gama hotunanta , sannan ta tafi,
Tafiyarta kawai take abunta tana jin wani ƙarfi lallai shiga jirgi akwai daɗi, duk inda ta wuce taga yayi mata kyau sai ta ɗauki kanta hoto, saida tayi "yar tafiya sannan ta samu wani tace mashi malams don Allah ni baƙuwa ce, ina ne anguwar baƙi?""",,,,,
Cewa yayi hajiya ai bansan ina zance maki ba, jawahir tace jeka baka da amfani, dariya yayi sannan ya wuce dan ya lura wannan "yar shan iskace, yana tafiya bada daɗewa ba, ita kuma tana tafiya tana shegantaka, mutane ta gani suna rugawa da gudu, maimakon ita ta ruga sai ta tsaya tana tambayar lafiya,
babu mai lokacinta bare ya bata amsa, wata mace ce, ta sharto cikin 360, ta wuce jawahir fuuuuu, dariya jawahir tayi tana cewa kai wancan da gani dai ba saiti, niko nace kece baki da seti yarinya,
watace ta ƙara rugowa a guje, ganin jawahir yasa tace anshin anshi nan, ta miƙama jawahir wata jaka, kundai san, jawahir da san banza, da sauri ta miƙa hannu ta ansa, ita kuna ta ruga, da sauri jawahir ta fara buɗe jakar tana duba abinda yake ciki,
kuɗine a ciki na ƙasar waje, tsalle jawahir tayi tana rawa, tana faɗin lallai na shigo lagos a sa,a, na ƙara samun wannan biyu ai na haye, bata gama murna ba, taji an rufeta da duka ta ko ina , ihu take tana tambayar lafiya?""",,,, babu wanda ya saurara bare ya bata amsa saida sukai ma jawahir lilis sannan suka jefa ta a mota suka bar wurin.....................
[1/17, 7:43 PM] Jamila Musa Ws: ☄
☄☄
☄☄☄
🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥
*WANDA BAIJI BARI BA*
🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥
*AMEENCI WRITER"S ASSOCIATION* 📚✍🏻
*MEELAT MUSA* 🌹
*PAGE 19*
****
*J*awahir sai ihu take tana neman agaji ganin babu wanda yasan tanayi ne yasa jawahir cewa bayin Allah ina zaku kaine don Allah?"""",,,,,,
Babu wanda yayi mata magana, sai ihu take su kuma sai zuƙa gudu suke da motar har suka isa police station, bayan sunje ne, aka ciro jawahir daga mota aka jefeta magarƙama,
Jawahir kuka take tana tambayar abinda tayi?"""",,,,,,, wani ne yace rufe ma mutane baki dan ubanki sai ɓare ma mutane baki kike kina kuka kamar wanda mijinta ya mutu, jawahir tsoronta yayi yawa, kafin ya gama rufe bakinshi tuni ta ɗauke nunfashinta,
Ƙarfe cell ɗin ta riƙe tana leƙo kanta waje kamar wata biranya, hawaye kaɗai ke zubo mata daga idonta, amma babu damar kuka, sai kallon mutane takeyi, duk tayi wata kalar ban tausayi,
Waya yake yana cewa Oga bamu samesu su duka ba, ita kaɗai muka kama amma ta fito da sauran, okey sir, yana kashe wayar ya kalli wasu ƙattin "yan sanda yace su buɗe jawahir Oga yace sai anji bata lumfashi,
Jin han faɗi haka ai kafin su buɗe ƙofar tuni jawahir ta faɗi ƙasa somammiya, ganin ta suma ne, yasa basu daketa ba, haka suka barta kowa ya kama aikin gabansa,
***
*J*awahir bata farko ba sai 8:06am, tana kwance a ƙasa sai kuka take duk wutar jikinta gaba ɗaya ta ɗauke, tashi tayi a hankali ta matso kusa da ƙarfen da aka sakata ciki aka kulle ta riƙe tana leƙowa, sai kuka take, tana kallon mutane,
Ganin duk "yan sanda dake wurin sun miƙene suna kallon wuri ɗaya dukansu, yasa jawahir kallon wurin itama taga abinda ake kallo, itama da sauri ta miƙe tsaye taci gaba da kallon mutumin, tsayawa haka yasa duk wanda suke take masa baya suma suka tsaya, yace wannan ce ko?""",,,,, gaba ɗaya sukace Eh ranka ya daɗe, yace ku kawota office, yana faɗin haka yayi gaba,
Buɗe inda jawahir take ciki akayi sannan aka tasa ƙeyar ta gaba har zuwa Office ɗin Oga, shiga sukayi dukansu, "yan sanda suna sara mashi alamar girmamawa, shi kuma yana saman kujera ya hakime saida yaɗan juya dama ya juya haggu, sai isa yake yana zuba mulki,
Kallonsu yayi sannan yayi masu nuni da hannu alamar su tafi, saida suka sake girmamawa sannan suka fita daga Office ɗin, bayan sun fitane, ya kalli jawahir yace ina sauran kudaɗen ne?""",,,,, jawahir tace wane irin kuɗi kuma ranka ya daɗe?"",,, cikin fusata yace ina tambayarki kina tambayata?"""",,,,,,
Wayarshi ya ɗauka yayi magana, babu ɓata lokaci wasu "yan sanda masu kalar bada tsoro suka shigo, miƙewa Oga yayi daga inda yake zaune , inda "yan sanda suke yaje yana zuwa ya ɗaga hannunsa ya wanka ma wani mari, sannan yace kunce kunyi mata duka, yace Eh , yace to bata hukuntu ba,
Kan jawahir suka nufa, sukaci gava da dukanta saida suka farfasa mata baki da fata, sannan yace su barta haka, sai kuka take , tana sosa jikinta, Ogan da gani baya da imani yace aje a kawo mashi gishiri, jawahir ta miƙa d asauri tace don girman Allah kayi haƙuri wallahi ni baƙuwa ce jiya na shigo garin nan,
Yace to keda su waye kukayi satar?""",,,,,, jawahir tace nidai wallahi ina tafiya suka bani jaka bayan haka bansan komai ba, tsaki yayi sannan yace su sake zane jawahir, kafin su fara dukanta da gudu ta miƙe ta nufi inda yake tsaye ta riƙe ƙafarshi tana kuka, ka rufa man asiri wallahi tashar mota nake nema, bama zan hau jirgi ba, yau ɗin nan zan bar garin nan don Allah kace kada su dakeni ka tausaya man, ta ƙarasa maganar tana ɓarke wa da wani irin kuka,
Duƙawa yayi inda jawahir take kwance ta riƙe ƙafarsa, gashin kanta ya riƙe gam harya miƙar da ita tsaye, har yanxun yana riƙe da gashin kanta ya hanƙare mata kai sama yana kallon idon ta, ita kuma sai kuka take ,
sakinta yayi ta tafi tangal tangal zata faɗi ƙasa amma bata faɗi ba, ta dafa kujera ta sulale ƙasa, taci gaba da kuka, kallon "yan sanda yayi sannan yace suje, fita sukayi daga Office ɗin, saida yayi "yan rubuce rubucen sa, sannan yace mata yau kuma ina zakuyi sata ne?""",,, jawahir tace don girman Allah ka daina man maganar sata niba ɓarauniya bace,
tsawa ya dakawa jawahir sannan yace nace a ina kuke harin yin sata yau kuma?""",,,, jawahir tace innalillahi wa"inna ilaihir raji"un, don girman Allah ka rufa man asiri nidai bana cikin ɓarayin da kake magana, yace okey to ke wace ƙungiya kike?"""",,,,,,,, jawahir cikin kuka tace ina ƙungiyarka,
Ance maki nima ɓarawo ne?""",,,, jawahir tace saboda ba ɓarawo bane kai shi yasa na shiga cikin tafiyarka, kayi haƙuri ka tafi dani bana sata kwata kwata, ba sana"ata bace, yace to miye sana"arki?""",,,, jawahir tace idan na faɗa maka zaka barni in tafi?""",,,,, yace idan na gamsu da abinda kika faɗa ba?""",,,,,,
jawahir tace ɗan sanda sahun keke ne, ba"a gane gabansa ba"a gane bayansa, amma ni zan faɗa maka bisa yadda da amana, kallon jawahir yake har yanxun baiyi magana ba, goge hawayen fuskarta tayi sannan ta fyace majina da gefen zaninta, ta faɗa mashi yanda jikka taxo hannunta, da kuma zuwanta wurinsu,
Bayan ta gama ne, yace to miye sana"arki tunda kince bakya sata ne?""",,, jawahir tace bana sata, amma ina cin bashi, sai kuma *4 1 9* yace kice kece abin hukuntawa, miƙewa yayi yayo kanta da sauri ta duƙunƙune kanta kamar wata dodon koɗi, fita yayi daga Office ɗin , ita kuma jawahir jin ba"a fara dukanta ba yasa ta ɗago kanta don ganin abinda ya hana a daketa, ganin bata ganshi Office ɗinba, yasa ta fara zullimi lallai takai babbar sakara data faɗa mashi kila ma kasheta zaiyi, tace w......a.....y......y.....o na bani, na kashe kaina,
Da sauri ya shigo Office ɗin dan ganin abinda yake faruwa jawahir take ihu, jawahir tana ganinshi da sauri ta miƙe ta nufi wurinshi tana cewa don girman Allah ka barni inje, yace ina zan bari ki tafi , ƙafa ɗaya kawai zan cire maki sai hannu ɗaya, idanuwa jawahir ta zaro, yace yawwa hada wannan idon zan zare ɗaya shima, ina wuƙar nan take, jin an faɗi wuƙa yasa jawahir ta tafi ƙasa luuuuuuuu,
kafin ya riƙota harta kai ƙasa ta faɗi somammiya, dariya yayi yace lallai baki kai kangararra ba, inda take kwance ƙasa ya matsa kusa da ita, yana kallonta, a bayyane yayi magana , yarinya ƙarama kamarki take faɗi da bakinta tanayi danfara, lallai dole yana san sanin labarin jawahir, towai miyasa ma kika zo lagos?""",,,,,,,,,,,
Ya tsugunne a gaban jawahir ne, yaji an shigo Office ɗin, tare da sallama, bai juyowa ba, yace uhum , ranka ya daɗe an samu wata a cikin mutanen da sukai sata, jiya, je kaxo da ita,
babu ɓata lokaci suka dwo tare da ita an wani rirriƙota sai wani iskanci take kana ganinta kasan gwanjon "yar iskace, bayan sun shigo ne, ya miƙe tsaye daga inda yake sannan ya juyo yana fuskantar su, sai wani ciccijewa take, kamar zata buge mutane, kallon da yayi matane yasa ta natsuwa,
yace kuje da ita, kuma a bata hukunci ta faɗo idan sauran suke, haka suka sake janta suka tafi, bayan sun fita ne, ya koma inda jawahir take ya sake kallonta, tsaki yayi sannan ya miƙe ya fita daga Office ɗin,
Sadiq ne yake kiran wayar Auwal, bayan Auwal ya ɗauka suka gaisa, sannan Sadiq yace ma Auwal insha Allah zai shigo nigeria jibi, idan kuma yaxo zai sauka kano saboda yana san ganin shi, Auwal yace to Allah ya kawoka lafiya, ba tare da yace komai ba ya kashe wayar, ajiyar zuciya Auwal yayi sannan ya kalli wayar yace kai gaskiya anya ina iya haɗuwa dakai?""",,,,,,,,,,, daga ji zakai zafi ra"ayinka yayi yawa,
Yana shigowa Office ɗin yace su ɗauketa suka kaita asibiti, wani yace ranka ya daɗe kada a kaita asibiti zata iya guduwa ne, yace duk kuna aikin mi zata gudu ne?""",,,,,,,,,,, ɗan gajeran tsaki yayi tare da cewa kuje da ita , wani ne yace ranka ya daɗe suma tayi zata dawo, a zuba mata ruwa, shidai bai sake magana ba, don haka wani ne ya tafi wurin firij ya ɗauko ruwa yaxo ya yayyafawa jawahir, tace himmmm , ta ɗaga numfashin ta sake saukewa cikin yanayin wahalatuwa,
Haka tayi tayi har ta gama dawowa daidai, kallonshi tayi tana kallonshi ta fashe da kuka, tana cewa don Allah kada ka cire man ƙafa ka rufa man asiri, baiyi magana ba, ya miƙe ya fita daga Office ɗin "yan sanda suma suka bi bayanshi,
Itama cikin sanɗa tabi bayansu a hankali babu kowa don haka anan ta samu damar fecewa da gudu, saida ta wuce da gudu sannan wani ɗan sanda ya ganta, yace kai kubita ku kamota, wani ɗan sanda ne ya hau mashi irin mai gudun nan yabi jawahir,
ita kuma gudu take ba tare data san inda zataje ba, haka taci gaba da kutsawa cikin santoci, shima a bindige yake binta saman mashin, Oga yanajin ance jawahir ta gudu yasa aka haɗa motoci don binta a kamo ta,
wata unguwar arna ta kusa ta shiga, aikokamar jiran zuwanta suke , wata inyamura tace yawwa gata nan itace ta kwace man waya, da gudu sukayi kan jawahir suka riƙota, babu ɓata lokaci suka fara dukanta, suna takata, jawahir sai ihu take tana cewa ba itace ba, nunawa sukai bama susan abinda take cewa ba,
shi kuma lokacin ya iso saman mashin ɗin, don haka bindigarshi ya fiddo ya ɗaga sama ya fara harbawa, da sauri suka matsa, jawahir jiki na ƙarma ta miƙe tayo wurinshi a daidai lokacin da Oga ya iso , motar tana tsayawa ya fito,
Da sauri ya isa inda jawahir take yana zuwa ya ɗaga hannunsa ya wanka mata mari, ya ƙara sauke mata wani marin, jawahir tayi shiru dan kukanma ya zamar mata aiki don haka tsaye tayi sai yanxun tayi da na sanin zuwanta lagos, da taji bari da bata zo ba,
hannunta Oga yaja ya jefata mota, shima shiga yayi sannan akaja suka bar wurin, saida suka dawo Office ya fara faɗa da sun kasheki kuma zasu kashe banza ne, idan sun matar dake zasu je su jefar dake can a ruwa, ko kuma sun babbaka maki taya ki kama da wuta, jawahir dai sai kuka take, haka yayi ta faɗa yana ƙarawa, amma jawahir tayi ɗaukewar wutar nepa,
Saida ya gama faɗan sannan yace a mayar da ita cell, kuka jawahir ta fara tana cewa don Allah ka rufa man asiri kasa a mayar dani garinmu, tsawa ya daka mata tare da cewa nine na kawo ki ne?""",,,, jawahir tanaji tana gani akaja ta, aka fita da ita, sai juyowa take tana kallonshi hawaye sai fita suke daga idonta,
Tanaji tana gani akaje aka dannanta magarƙama, sai kuka take tana ƙarawa, ina zata samu sa"a ta koma kano, suna can zaman lafiya babu faɗa babu hayani, kuma ga yunwa tanaji kamar zata kasheta bata da mai bata abinci,
wani ɗan sanda dayazo wucewa tace "yar laɓai don Allah a cikin jakana ina da kuɗi ka cire ka siyo man abinci, kallonta yayi sama da ƙasa ya wuce, haka jawahir tayi ta kuka tana ƙarawa babu mai bata haƙuri,,,,
***
*D*a safe oga yana zuwa Office bayan ya gama abinda yake yasa aka ciro mashi jawahir , bayan an kawo ta ne, yace su tafi, bayan sun tafi ne, yace ma jawahir ta zauna wuri ta samu ƙasa ta zauna ciki da ladabi kamar wata ta kirki, cikin sanyi yayi magana yace zauna saman kujera, jawahir ta miƙe a hankali sannan tahau saman kujerar , tasowa yayi daga inda yake zaune, yazo ya zauna kusa da jawahir, sannan yace mata ya sunan ki?""",,,,, kallonshi tayi sannan tace suna na jawahir, yace ni suna na, Ahmad, jawahir tace to don Allah kayi haƙuri,
Yace nayi yanxun ya kike so ayine?""",,, cikin sanyin murya jawahir tace don Allah so nike in tafi ne, yace ina zakije?"" tace zan koma garinmu ne, yace to baki bani labarinki ba, jawahir tace ai yunwa nakeji, yace to bara a kawo maki abinci kici, tace to,
Fita yayi bai daɗe ba ya dawo da