Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

WANDA BAIJI BARI BA Rayuwar Ƙarya da Nadama by MEELAT MUSA

Author :  MEELAT MUSA Category :  African Stories & Novels

Chapter   14 / 28

39K to 42K   out of 83K words

abinci , ya bata bayan ta gama cine, tayi mashi godiya, sannan tace zata wuce, yace ta bari sai Allah ya kaimu kamar yanda taxo a jirgi to a jirgi zata koma kano insha Allah,

Tana nan Office har lokacin tashin shi yayi , kayanta yasa aka kawo mata yace akai a motarshi, bayan ankaine yace mata ta tashi suje, babu garma ko tsoro jawahir ta tashi simimi ta bishi,

dukansu a bayan mota suka shiga, aka jasu, sai gidansu Ahmad, bayan sunje ne, shi ya fita daga motar amma jawahir bata fito ba, da ɗan sauri ya shige cikin gidan, saida ya daɗe sannan ya dawo yace ma jawahir ta fito, fita tayi tabi bayanshi har cikin gida,

a farlo yace ta zauna yana zuwa, bayan wani lokaci suka fito dashi da wata "yar tsohuwa, bayan ta zauna jawahir ta gaisheta, cikin girmamawa, ta ansa, Ahmad yace itace wanan gobe da safe insha Allah zata wuce, tace to Allah yasa rayuwarmu takai,

Daga haka bata sake cewa komai ba , tashi tayi ta koma ta hanyar data fito, Ahmad da kanshi yaje ya kawo ma jawahir abinci taci , bayan ta gama ya kwashe kayan ya mayar, zuwa yayi kusa da ita ya zauna, sannan yace ta ɗan bashi labarinta, murmushi jawahir tayi sannan ta lallaɓa ta zunkuɗa mashi ƙarya kundai san hali, haka dai taci gaba da zazzaga mashi ƙarya shi kuma sai dariya yake,

jawahir sai kallonshi take, a ranta kuma tace kaima mai kama da azzalimi sadiq jiyan nan kasa aka gama cima man uwa amma hada wani yashe baki kana dariya kamar yaro yaga abin wasa,

Sun ɗan daɗe suna fira sannan Ahmad yace taje ta kwanta, tashi yayi itama ta tashi tabishi har inda zata kwanta, ɗaki ɗaya da tsohuwar ya kaita, sannan yayi masu saida safe,

jawahir sai yanxun ta samu natsuwa, ta fara tuno maganar Alƙali ki daina damfara dan duk haƙƙin wanda kaci babu kai babu zaman lafiya a rayuwa, hawaye suka zubo mata daga idon ta, a bayyane tace insha Allah duk abinda ba nawa ba, har abadan duniya na kauda idona akan shi, niko nace anya?""" kodai don kinsha wahala ne?"""",,,,,,,,

Haka tayi ta juye juye har bacci ya ɗauketa, Ahmad kuma yana fita ɗakinshi ya tafi shima ya kwanta bacci,

***

*A*suba nayi "yar tsohuwa ta tashi jawahir tayi sallah , amma sai jawahir tace mata period take, tace to, ƙarya take tana sallah fa, kawai dai batayi, saida "yar tsohuwar ta fita jawahir tayi tsaki tace ko ina ruwanki da sallah ta, wannan da gani irin halinki ɗaya da innasco, tsaki tayi ta sake jan bargo ta lulluɓe, taci gaba da bacci, bata farka ba, sai 12:31pm, tana tashi wanka ta shiga tayi, sannan ta shirya bayan ta gama shirinta ta , ta fito,

A farlo ta samu "yar tsohuwar da bata san sunan ta ba, suka gaisa sannan tace taje tayi kalaci, Ahmad yaje wurin aiki saiya dawo, jawahir tace to ai yace da wuri zan tafi ne, tace A, a, saida ƙarfe 4:00 jawahir tace to , bayan ta gama kalancin ne, ta dawo ta zauna, wayarta ta ɗauko ta fara dubawa,

Miss call 30 da wani abu, dana hafsat da Auwal zarto da Alƙali da number's in da bata sani ba, tsaki tayi sannan ta kira Auwal , bai ɗauka ba, itama bata sake kiranshi ba,

1:30pm jirginsu Sadiq ya sauka a filin jirgin malam aminu dake kano, jirginsu yana sauka ya kira Auwal, yace mashi ya iso, Auwal yace yana zuwa yanxun in Allah ya yadda, dan unguwar da yake katsina road babu wani nisa zuwa airport, bayan sun gama Auwal gabanhi sai faɗuwa yake dan tun kafin yaga Sadiq yakejin tsoro, niko nace saima kun haɗe,

Yana gama waya sadiq ya kira jawahir, bayan ta ɗauka suka gaisa yace tun ranar da kika tafi nake nemanki baki ɗauki waya ba, tace E ai ina zuwa coutnour na wuce ne, yau na dawo insha Allah yau zan shigo kano, Auwal to Allah ya dawo mana dake lafiya, jawahir tace Amin,

Yana gama waya da ita, ya wuce filim jirgi dan ɗauko Sadiq, bayan yajene yace ma sadiq ya iso, sadiq yace to yaɗan jirashi kaɗan ya kusa gama zai fito, Auwal yace tom,

Bayan sadiq ya gama abinda yake ya kira Auwal , yace ina ka tsaya ya faɗa mashi,tare da faɗa mashi cikin motar da yake da number motar, sadiq tam, bayan ya fito ya duba, Auwal yana hangoshi gabanshi yaci gaba da faɗuwa, zufa ta keto mashi lallai idan baiga jawahir ba, akwai matsala, haka yayi ta tunani har sadiq ya ƙaraso wurin,

Fita daga motar Auwal yayi , sannan yayi ma Sadiq sallama, hannu ya miƙa mashi su gaisa amma Auwal saida ya ɗan duƙa amma yama kasa kallonshi bare ya iya haɗa hannunshi da nashi, Sadiq yace to muje dan a agiye nake, Auwal yace to ranka ya daɗe muje ɗakina, dariya yayi sannan yace,

ka sama man hotel mai kyau inje in huta, Auwal yace to ranka ya daɗe, da kanshi ya buɗewa Sadiq motar ya shiga, sannan ya rufe, shima shiga yayi sannan yaja suka tafi,

Saida yakai Sadiq masauki, Auwal yace zai tafi, sadiq yace ina labarin jawahir ne?""",,, gaban Auwal ya faɗi amma ya dake yace ranka ya daɗe itama tana hanya, yau zata shigo kano, Sadiq yace dakyau, zauna dani dakai mu jira zuwanta, Auwal yace to , haka nan ya zauna badan san ranshi ba, da ko ido baya iya haɗawa da sadiq wani iri yake mashi,

Jawahir kuwa Ahmad sai 3:45pm ya shigo, da sauri ya shigo yace ma jawahir ta fito, da kanshi ya ɗauki kayan ta yana fitar dasu, cewa yake kiyi sauri, jawahir tayi ma "yar tsohuwa ban kwana, itama tayi mata fatan alkairi, sannan tabi bayan Ahmad, suna fita, mota suka shige, tana shiga yaja suka tafi,.......,,,

A mota ne yace kisa kisa number na, muna gaisawa kuma insha Allah duk ranar danazo kano zanzo wurinki!""",,,, jawahir tace to, faɗa man ya faɗa mata ta rubuta, haka sukaci gaba da tafiya har suka isa filin jirgi,

Ya sauke ta, tare da kayanta, ta ɗauki jakarta ta wuce tana ɗagawa Ahmad hannu, bai tafi ba, sada jirginsu ya tashi, sannan ya juya ya tafi,

To jirginsu jawahir yana isowa jikinta har ƙarma yake, ta ɗauki wayarta ta kirawo Auwal, ta shida masa cewa ta iso yanxun, Auwal yayi mata sannu da zuwa, sannan yace zaizo ɗaukarta, tace A, a, kawai zataxo su haɗu a gida, yace to sai kinxo,

Bayan ta gama abinda take , ta fito adedeta tahau , har ƙofar gida aka kawota, ta fita ta sallami mai napep ɗin, sannan ta ɗauki kayanta ta shige cikin gida, tana shiga ta buɗe ɗakinta ta shiga, bayan ta ajiye kayanta wanka ta shiga..................
[1/17, 7:43 PM] Jamila Musa Ws: ☄
☄☄
☄☄☄
🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥
*WANDA BAIJI BARI BA*
🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥

☄☄
☄☄☄

*AMEENCI WRITER"S ASSOCIATIO* 📚✍🏻

*MEELAT MUSA* 🌹

*PAGE 20*

***

*T*ana fitowa daga wanka wayarta ta ɗauko ta kira shagon da ake siyar mata da abinci tace akwai abinci?"",,,,, sukace E, tace Auwal zaizo ya ansar mata, sukace to,

Tana gama waya dasu ta kira Auwal, lokacin data kirashi Sadiq yace yasa speaker phone, bayan ya ɗauka ya sakane, jawahir tace kana ta ina ne?""",,,,yace yana nan, nan ina ne?"",,,, yace mi kike so ne?"",,,, kaje shago ka anso man abinci yunwa nakeji don Allah kayi sauri, yace to gani nan zuwa, tace aha,

Bayan ta gama waya da Auwal , ta kira Ahmad, suka gaisa ta sheda mashi ta dawo gda lafiya, yace to yyi sai sunyi waya, jawahir tace ta gode,

Tana gama wayar ta shafa mai da "yar powder, man baki kaɗai ta shafa, sannan ta saka doguwar rigar atamfa, ta ɗan coga kallabi , wayarta ta ɗauka ta kira Auwal idan bazaizo ba ya faɗa mata, yace kiyi haƙuri ina hanya,

Sadiq da Auwal suke tafiya a mota, don haka lokacin da suka iso ƙofar gidan da jawahir ta kama haya, anan Auwal yayi parking, sannan ya fita, yana fita, sadiq shima fita yayi don haka Auwal ne a gaba sadiq yana bayanshi,

Jawahir dake ɗaki zaune jin anyi sallama ta ansa amma bata fito ba, take cewa yawwa Auwal ajiye man a ƙofar ɗaki, Auwal yace to , Sadiq shi kuma wucewa yayi ya nufi ɗakin, jin ana taɓa ƙofa yasa jawahir ta fara cewa haba nace ka ajiye a ƙofar ɗaki mana, shi kuma sadiq a daidai lokacin daya tura ɗakin ya shiga, jawahir dake kwance saman katifa da sauri ta miƙe tsaye, gabanta ya bada wani durum damm damm damm, lokaci guda kuma zufa ta keto mata, hawaye sukayo ma zufa raki, jikinta ya fara kyarma, ta kasa kallon sadiq, sai ja da baya ta farayi, tana saman katifar bata sauka ƙasa ba,

Wani ƙasƙantaccen kallo ya bita dashi, jawahir kuka ta fara rerewa mai sauti tana cewa sadiq yayi haƙuri dama yau zata tafi gda, tsawa ya daka mata wanda yasa Auwal dake waje ya fita da gudu, idan kika sake magana saina ɓare maki baki na faɗa maki, wato iskancin naki har ya kai da kama gda ko?""",,,,,,

jawahir zatayi magana ya wanka mata mari, yace ba nace kada ki sake magana ba, duƙar da kanta ƙasa tayi hawaye suna ta zuba daga idon ta, sadiq yace wato ke kinajin balaga shi yasa kika kama ɗaki ko?""",,,, jawahir dai batace komai,

yace uhun hada wurin siyar da abinci, yayi maki kyau, kina tunanin duk inda kika tafi bazan gano ki ba?""",,,,,, kinga duk kin gama gujegujen gaki a gabana, kinga yanxun idan zan kasheki babu wanda yaji babu wanda ya gani, kawai idan an tashi za,ace kin tafi yawon karuwanci kin mutu, cikin kuka jawahir tace don Allah kayi haƙuri yace ba nace kada ki sake man magana ba?""",,,,,, tashi yayi ya fito inda Auwal ya ajiye abinci ya ɗauka ya koma ɗaki,

Yana shiga yace mata taxo taci abinci, niko nace haba ina ai abincin baya ciwuwa, jawahir tace ta ƙoshi, zaro mata ido yayi sannan yace ta tashi taci idan kuwa ba haka ba, zataji a jikinta, jikinta yana ƙarma tace nidai na ƙoshi,

yace idan na sake cewa kici saina lalata maki fata da duka na faɗa maki, jawahir aka taho simi simi ta zauna, ta ɗauki abincin ta fara ci, tana ci tana kuka, shi kuma kwanciya yayi saman katifar kanshi yana kallon silin, ya ɗauki ƙafa ɗaya ya ɗora samaɓ ɗaya, yana kallon jawahir ta wutsiyar idinshi,

Jawahir sai kuka take jin abincin take kamar dutse, dan daƙel yake wucewa a moƙoshinta, ta rasa yanda zantayi ta fara kakarin amai, yace kiyi koba amai ba?"",,,, kima sani idan zakiyi shi kiyi a cikin abinci dan duka sai kin cinyeshi na faɗa maki,

Cikin kuka jawahir tace du Allah ka barni , nidai banajin yunwa, kallonta yayi da sauri ta ɗauke idonta daga wurin, yace kici fa, tun kafin raina ya ɓaci, jawahir tace wayyo Allahna dan Allah ka barni sai anjima zanci, tashi yayi ya zare belt in jikinshi, tana ganin haka da sauri ta jawo abincin tayi ta cusawa , saida ta cinyeshi tass,

Belt ɗin ya maida sannan ya koma ya kwanta, bayan ya kwanta ne, yace yaushe rabonki da sallah?""",,, jawahir tace yauma nayi, yace zo nan inga idan kina sallah, gaban jawahir ya faɗi, tace tsakani na da Allah jiyane da shekaran jiya banyi ba, yace naji zo nan, tashi tayi ta nufi inda yace mata tazo,

tana zuwa ta durƙusa, kallon fuskarta yayi ita kuma ta rufe idon ta, yace ƙarya kike baki sallah, jawahir tace inayi, yace ki rantse da Allah, dan yasan tana tsoron rantsuwa, jawahir tace ai na faɗa maka gaskiya, yace bana san gaskiyar nace kice wallahi kinayin sallah, haka zakice zan yadda, jawahir tayi shiru, sadiq yace lallai to yaushe rabon da ki kalli gabas?"",,,,,, wato duniya ta shagalar dake ko?""",,,,,,, yace mina faɗa maki game da sallah?"",,,,, jawahir tayi shiru, yace aiko yau zakici ubanki a gidan nan,

Kukan jawahir ya ƙaru, wani mari yakai mata wanda yasa taji ɗimuwa, miƙewa yayi ya cire belt ɗinshi yayi mata shegen duka, tun tana kuka kirki har muyarta ta shaƙe, ta koma kukan awaki heeeyyy ya diddira mata da ƙafarshi, taci ubanta sosai, sanna yace kuma na hana ƙarya ba"a daina ba ko?"",,, cikin disasshiyar murya tace na daina, yace to ina tsarabar london, jawahir tace aini banje london ba,

Yace kinje maza kawo man abinda kika samo sannan ki faɗa man abinda kikayo, jawahir tace wallahi ƙarya nake, banje ba, sadiq yace aini da gaskiya ne, dan na hanaki ƙarya, da tsawa yace ta tashi maza maza ta kawo mashi, jawahir sai kuƙa take tana bawa sadiq haƙuri, wayarshi dake ringing ya ciro daga aljihu , bayan ya duba ne, ya ɗauka, yace yawwa sameni a katsina road yayi shiru sannan yaci gaba da cewa idan kazo wurin akija hotel kirani ina zuwa, yace to sai kaxo,ya kashe wayar,

Inda jawahir take zaune ya kalla sannan yace kika ƙara kallo saina cake wannan munafukin idon , ɓarauniyar banza kawai dake, sakara wanda bata sallah, aike kin halaka da yawa, gacin haƙƙin mutane ga zalin wa iyayenki ga rashin sallah, aike babu ke ba zaman lafiya, idan wannan rayuwar kika zaɓa sai kin gyara idan har kina san ganin ci gaba a rayuwarki yarinya,

Kirane ya sake shigowa wayarshi, bayan ya ɗauka yace to yana zuwa, bayan ya gana wayarne, yace ma jawahir ta tashi taje tayi wanka kuma kada ta ɓata mashi lokaci , kafin in irga ukku kin fito, da sauri ta miƙe ta shige toilet, shi kuma tsakar gida ya fita,

A gaggauce tayi wanka tana fitowa tana shiri amma tsine ma sadiq take, sai addu"a take Allah yasa ya mutu, ta huta, daga waje yace baki gama ba har yanxun?"",,,,, da sauri tace ganinan zuwa, ƙasa ƙasa tayi magana tace ba"ayin saurin azzalimi kuma bazan yafe maka ba, ko zakaci da wuta balbal, ta murguɗa bakinta, sannan ta saka kaya, ta ɗauki hijabi ta saka ta fita,

Yace muje, tabi bayanshi sumi sumi, suna fita yace dawo tana nan, kusa dashi ta koma suka jera sukaci gaba da tafiya kai idan ka gansu ka rantse zaman lafiya ake, nan kuwa zaman doya da manja ne,

Haka suka tafi har wurin akija hotel, tun daga nesa ta hango motar da abokin sadiq yaxo da ita, murmushi ta farayi tana kallon ƙarawa motar kallo, a ranta tace lallai babban yaro ne, wannan motar tunda na ganta a gidansu sadiyya sai yanxun na sake ganin ta, sadiyya ɗiyar tsohon gwamna, "yan uwansu hafsat,

Suna isa wurin sadiq ya bashi hannu suka gaisa, sannan jawahir ta gaishe shi, abokin yace wannan ce madam ɗin?"",,,, tsaki sadiq yayi sannan ƙanwata ce, yace okey wanda kke bani labari?""",,,,,, hararshi sadiq yayi, shima shiru yayi, sadiq yace Ey itace wanda batajin magana ba, kallonshi jawahir tayi yace ko kinaji ne?"", batayi magana ba, yace dake ɓake nace kinajin magana?""",,,,,,,, taɓe baki tayi sannan tace Eh,

Ɗan warewa sukai gefe, sun ɗan daɗe suna magana, sannan suka dawo tare, makullin mota sadiq ya miƙawa jawahir makullin mota ta ansa, abokin sadiq ya bata kuɗi, tace A, a, sadiq yace ke bansan kilbibi ki ansa, tace wallahi bata ansa, yayi juyin duniya taƙi karɓa, bankwana sukayi, sannan sadiq yace ma jawahr muje,

Tayi gaba zungui zungui, yace ina zakije ne?"",,,,, tace gida, tsaki yayi sannan ya nufi wurin motar yace ta buɗe, buɗe motar tayi yace muje, tace ina zamuje?"",,, gida zamu,

idanuwa jawahir ta zaro tace kayana fa, ɗaure fuska yayi yace wane kaya kuma?"",,,, kuka ta fara tana cewa don Allah kayi haƙuri ina da abunda zanyi zuwa gobe sai mu tafi don girman Allah ka rufa man asiri,

Yace naji , yanxun ina zakije ne?"",,, tace idan ake siyar man da abinci, yace mi zakiyi a wurin?"",,,, tace kuɗina zan ansa sai in siyar da tukwanen, sadiq yace a,a, ki bar masu tace ai kuɗin suna da yawa, yace ni zan baki wasu, tace to sai kayana da katifa yace ki ɗauki kayan amma katifar ki ba wani, tace to yanxun fa magrib akeyi, yace Eh a haka zamu tafi kuma kece zaki kaimu gida, kuka jawahir ta fara,

Yace bari ganin a bakin hanya ne, baya hana inci gidanku muje, shiga tayi shima ya shiga, taja motar, sai tasha, suna zuwa ta fita da gudu, sadiq yana kallonta, tsaki yayi tare da cewa Allah ya sawaƙe, kila yarinyar can bata da hankali , tana zuwa, tace a bata kuɗin ta, suka tattara suka bata, sannan tace to zasuyi waya, aci gaba da kula da komai, sukace to, inda zarto take zama taje tace mata ga katifa ta nan na bar maki aro idan na dawo zan ɗauki abuna, zarto tace to, tana juyowa zata tafi taga sadiq gabanta tsaye, da sauri ta juya wurin zarto cikin sayin murya tacr nabarma ma duka katifar,

kallonta yayi sannan yace muje wurin abincin suka koma, suna zuwa jawahir tace komai na bar maku bazan sake dawowa ba, godiya sukayi, suna godiya wa sadiq, suna tafiya mota suka koma, sai gidan jawahir, haka ta tattara kayanta da abinda tasan tana buƙata, taje ta jibga a motar, sadiq dai yana ta kallon ikon Allah, saida ta gama ɗaukar duk abinda take so, sannan yace suyi sallah, sallah magrib sukayi bayan sun gama , suka shirin tafiya, jawahir ce taja motar suka tafi, sadiq yana gefe, ita kuma ta tafi bindige sai bala"i take da mota bisa titi yau su innasco ana da manyan baƙi,,,,,,

Ɗan abu kaɗan zata kuskure sadiq zai hauta da bala"i, sai masifa yake mata duk jinta take a takure, sai kuka take, shi kuma ya wani jirge ya ɗauƙi ƙafa ɗaya ya ɗora saman gaban motar, jawahir wani ƙululu ya zo mata a maƙoshi, kuma dama dan ya ƙuntata mata yayi haƙa kuma ta shaƙa,

Wayarshi dake gefe tana ringing, yace duba waye yake kirana?"",,,, jawahir tace Yaya da wane hannu?"",,,,, duk wanda kike so zaki saka, parking tayi sannan ta miƙa mashi wayar, bai ansa ba, ya wani basar, tace na gaji, yace ranar da kikaxo waye ya kawoki?"",,,,,, tace ni, yace to muje, tace ai na gaji ne, ka tuƙa in huta, yace an gaya maki ni drivernki

14 / 28