Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

WANDA BAIJI BARI BA Rayuwar Ƙarya da Nadama by MEELAT MUSA

Author :  MEELAT MUSA Category :  African Stories & Novels

Chapter   3 / 28

6K to 9K   out of 83K words

yin haka, inna ce ta shigo ɗakin da kofi a hannunta, miƙawa jawwahir tayi ita kuma ta miƙa hannun ta karɓa , tana dubawa taga koko ne, tsaki tayi ta taɓe fuskar ta tace haba innasco tsakanin da Allah kamarni a gidan nan za"abani tsari inyi kalaci dashi don Allah?""" tana maganar tana nuna kanta, inna tace shinwai da kike man wannan zaɓin kece kika kawo ayi maki abinda kike so?"""

Jawwahir tace ai baki gaya man kina so ba, idan kikai haƙuri ai na kusa fara aiki, inna ta zuba ma jawwahir ido tana kallonta, ɗago kai tayi ta kalli inna sannan tace kin wani zuba man ido kina kallona kamar kinga wata sabuwar halitta, inna tace ai sabuwar halittar na gani tunda kin zama mai baƙin hali,

jawwahir tace tou pha yau kuma wannan sunan na samu?"" inna tace kullu addu"ar shiriya nake maki saboda wannan ba turba mai kyau bace kika ɗora ma rayuwarki wallahi, idan baki hankali ba zaki fuskanci matsala a rayuwarki,

Jawwahir tace matsala kuma ta nawa??"" ai na gama zama cikin matsala tunda dai nazo cikin talauci,

Inna tace kidai ɗauki duniya da sauƙi idan har kina so rayuwa tazo maki da daɗi, yawwa yawwa tou fa ci gaba Allahu akabar jawwahir duk itace take faɗin haka, tace ikon Allah idan muna biki zamu ɗauke ki kije ki riƙa wa"azi, dan na lura kina san jaddada gaskiya, tsaki inna tayi sannan ta ɗauki kofin kokon da jawwahir ta ajiye saman gado ta fita,

Kallon inda wayarta take dan kira ne ya shigo, tana ɗauka taga alhaji ne, tsaki tayi sannan tace shege uban cusa kai bari kuma inji da wace yaxo, wayar ta ɗauka sannan ta fara magana cikin yanayin bacci, alhaji yace ranki ya daɗe ashe ma baki tashi bacci ba?"""

tace ummm, yace dama maganar number ne, jawwahir tace haba ina sane ban manta ba, amma ka bari kawai insha Allah zan turo maka bara in gama bacci yace tom, da haka sukai bankwana ta kashe wayarta,


tsaki tayi sannan tace wannan ɗan iskan wato so yake ya ƙure ƙarya mai haɗama, tsaki tayi sannan tace idan yasan wata baisan wata ba,

wayarta ta ɗauko ta shiga neman number hafsat bayan wani lokaci ta ɗauka, jawwahir tace mata ƙawata zan shigo idan Allah ya kaimu don Allah ki kaini gidan yayan mamanki, hafsat tayi dariya sannan tace baki bari sai biki?"" jawwahir tace nidai inaso inje dan ki gabatar dani bana so ranar biki inje inyi ta raɓe raɓe gara ki gabatar dani kowa yasanni, tace kada ki samu damuwa Allah ya kaimu da rayuwa muje, jawwahir tace amin sannan ta kashe wayarta,

jakar kuɗin data dan faro wurin alhaji ta ɗauko, kuɗin ta shashshafa sannan tayi masu kiss tace da sannu zakuyi rayuwar jin daɗi zan kashe ku ta hanyar da kukafi buƙata, murmushi tayi sannan ta rufe jakar kuɗin ta ajiye,

agogo ta duba taga 9:22am ɗan gajeren tsaki tayi sannan ta fito tsakar gida, ta yage baki tana hamma gami da miƙa, da sauri ta sauke hannuwanta ƙasa dan ganin sadiq, tsaki tayi sannan tace gafa aljarabatu tsutsar zaure bari inji yau kuma da wace yaxo ,

Inda take tsaye ya nufo, kallonshi take har yanxun shima ita yake kallo baiyi magana ba, saida ya matso dab da ita, sannan ya shaƙo wuyanta ya jijjiga ta ya buga mata kai da bango, ta tafi ɗimuwa ta wani lokaci , idanuwanta suka kawo hawaye , cikin yanayin wahala tayi magana da disashshiyar murya kamar wanda take shirin tafifa lahira tace sadiq mi nayi maka?"" baiyi magana ba ya zare belt in jikinshi yaci gaba da dukanta, yana dukanta yana cewa da maganar gini da maganar soka ma inna wuƙa shine laifinki, kafin ki kashe ta gara ke in aika ki lahira kowa ya huta, dukanta yake babu ji babu gani, dakel tayi magana cikin kuka tace ke innas ni nace zan soka maki wuƙa?"" inna tace Eh ai da kanki kikace tayi haƙuri wuƙar ta kusa shan jini, cikin kuka jawwahir tayi murmushin ƙarfin hali sannan ta riƙe belt in ta kalli sadiq tace kada ka sake dukana,

yace idan na sake mi zakiyi?"" tace hukunci zan ɗauka da hannuna dan idan wuƙar bata sha jinin innas ba zata sha naka, wannan shine karo na ƙarshe da zan sake faɗa maka ka fita harkar jawwahir idan ba haka ba wallahi nice *ajalinka* jin wannan kalma yasa sadiq ya haɗiya miyau dakel lokaci ɗaya kuma zuba ta keto mashi, belt inshi ya fara maida a jikinshi dan duk abinda jawwahir tace zatayi aikatawa take, dan haka ya yanke ma kanshi hukuncin ya fita harkar ta,

Yana gama sa belt inshi ya fita daga gidan, yana fita tayi tsaki ta kalli inda inna take zaune, da runanin idanuwanta da suka sha kuka suka gaji, ta ƙura ma inna ido, kallon ya ishi inna ta miƙe ta sake wuri, inda ta koma taci gaba da kallonta, inna taga bata daina kallonta ba, don haka ta ɗauke fuskarta daga saitin jawwahir tana kallon wani wuri daban, tsaki jawwahir tayi sannan ta ɗaga ɗan yatsanta ma nuni tace idan har baki kiyayeni ba ta girgiza kanta sannan tace jini zaiyi ambaliya a gidan nan,

Shin wai da wane ɗaukar alhaki zakiji?"" ku baku bani ba, na tashi ina neman na kaina kunsa man ido, kuma dan na wasa "yar wuƙata sai ciki ya ɗuri ruwa?"" to kici gaba da haɗani da sadiq kinsan Allah hmmm kinma dai san sauran,

Inna tace duk abinda kike man sai Allah ya saka man, Lbanza wadda bata sallah duk ranar da kika mutu Allah maƙabartar anna zansa a rufe ki,

Duk duniya jawwahir ta tsani ayi mata gorin sallah , dan haka abin yayi mata ciwo , tsaki tayi sannan tace shin sai ina ruwanki da sallah ta?"" aikinki haihuwa tunda kuma kin kawoni duniya ai kinyi ƙoƙari daga nan kuma mun raba jaha, idan ma banyi sallah ba ina ruwanki da sallahta kabarinki daban nawa daban,

inna bata sake magana ba, jawwahir taci gaba da cewa ai sallah nasan ko guda nawa akeyi a rana kuma nasan ko raka"a nawa ake yi a kowace, inna dai tayi banza da ita,

Nan ta yini zaune ƙofar ɗaki abun yana mata baƙin ciki, saida aka kira sallahr la"asar sannan ta tashi tayi wanka akayo alwallah akai sallah ta shirya sannan ta fita dan samun abinda zata ciwo ma cikinta,

tana fita daga gida inna tu ƙokacin da take sallah abun ya bata dariya, dan duk sanda tayi mata gorin rashin sallah sai tayi sallah, idan tayi a ranar washe gari batayi sai kuma lokacin da aka sake mata gori,

ita kuma tana fita, ƙofar gidan su *honey j* ta tsaya , ta kirashi a waya yaxo, tace don Allah ya bata aron motar shi, zataje wuri cin abinci, yace mata saidai suje tare dan yasan halinta yanxun nan tana iya dawowa tace ɓarayi sun tareta sun kwace motar, ɓata fuska jawwahir tayi sannan tace to muje babj damuwa, cikin gidansu ya koma ya ɗauko motar ya fito, yana fitowa yace ta shigo su tafi, ta shiga suka ɓace daga wurin kamar walƙiya,

abinci mai rai da lafiya suka ci , suna gama cin abincin yace suje yawon miƙe ƙafa, haka suka tafi sukayi ta shawagi a cikin gari, har aka kira sallah isha"i, sannan suka nufo gida, a ƙofar gidansu ya kaita, sannan ta mashi saida safe, shima yayi mata fatan alkairi ta fita ta shige gida shima ya nufi gidanshi,

Inna da bacci ya fara ɗauka taji shigowar jawwahir da sauri ta miƙe tsaye, ta fara murtsike idanuwa, jawwahir tace innasco ya dai?"" inna tace lafiya qalau, murmushi jawwahir tayi da gefen bakinta sannan tace kwanta kiyi baccinki wuƙar nan na mayar da ita wa wanda ya ara man, a daidai lokacin data haye saman gado, inna kuma ta koma saman "yar katifarta tayi kwanciyarta,


*****

Da safe, jawwahir na zaune tsakar gida tana waya da hafsat dan tafiyarsu gidan tsohon gwamna , suna cikin waya awakin inna su kuma sai meyyy meyyyy mayyyyy meyyy, hafsat tace kina ina haka ne?"" dan ita jawwahir babu ƙawarta data taɓa zuwa gidansu idan kace zaka zo yanxun ta fara cewa zasuje *egypt* ko sunje abuja, tun ana kwakwar zuwa gidansu har aka gaji aka barta,

jawwahir tace naɗan fito ne ina cikin anguwa dad ne ya fitar da zakka nake rabawa talakawa, hafsat tace okey, to bara na bari ki gama sai kinzo anjima jawwahir tace to , sallama sukai ta ajiye wayarta,

Tana miƙewa tsaye ƙofar gida ta nufa, tana mita lallai nine za,a tona man asiri, kam ina waya anajin kukan tumaki ta girgiza kanta sannan tace lallai wata rana nima akuyar za,a ɗaukeni, daidai lokacin da ta iso ƙofar gidan wani maƙocinsu,


bayan sun gaisa tace mashi yaxo ya sayi tumakan gidansu, yace to, suje yayi masu kuɗi, yace to haka jawwahir ta tuso ƙeyarshi gaba har suka iso gida, haka suka kutsatso har cikin gidan suka shiga cikin garke, ya faɗa mata ko nawa ya siya, tace kawai ya bayar ya bata kuɗin dan shi dama sana"arsa kenan, haka ya tusa ƙeyar dabbibin ya tafi, inna bata nan bare tayi magana,

yana tafiya taje ɗaki ta ajiye kuɗin, sannan ta fito taje tayi wanka, tayi shiri mai kyau , ɗan ƙarya ya samu dama jawwahir ta wanku, wanka tayi ba na wasa ba kuma shigar da tayi ta dace da jikinta, wanka tayi na, na wuce raini, tunda dama ƙarya ce aikinta, bare tasan babban gida zasu, haka ta buɗe jakarta ta cika ta da kuɗi,

Tana fitowa daga ɗaki wayarta ta fara ƙara tana dubawa hafsat ce, murmushi tayi sannan tace yawwa kawai ku jirani a bakin hanya ina zuwa, taci gaba da cewa kema nace ku jirani miye kuma sai kin biyo man , tom kada ki damu gani nan gab da bakin titin,

Tsaki tayi sannan ta kashe wayar tace shegiya uwar kwakwa ke dole sai kinxo nan , kin gaji ki gama kwakwar taki, haka tayi ta mita da tsegumi har ta iso bakin titi, tun daga nesa ta hango motar su sunyi parking daidai inda babanta yake kasa icce,

kam lallai ɗaure fuskarta tayi gam kamar ta hango ajalinta, tana isowa bakin titin baba ya fara cewa ke jawwahir ina kuma zakije?"""""""""""""
Copied By
YAYA HAYAT
(admin
Hayat hausa novels
Hausa novels and fashion
Cool novel, makeup and kitchen1⃣
Cool novel, makeup and kitchen2⃣
AND
Cool novel, makeup and kitchen3⃣)


WHATSAPP NO:
+2349030159301

[1/17, 7:35 PM] Jamila Musa Ws: ☄
☄☄
☄☄☄
🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥
*WANDA BAIJI BARI BA*
🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥

☄☄
☄☄☄

*AMEENCI WRITER'S ASSOCIATION* 📚✍🏻

*MEELAT MUSA* 🌹

*PAGE* 7

*****
*B*aba yaci gaba da cewa jawwahir ina magana nace in zakije kuma?"" jawwahir ta sake tsuke fuska gam, taci gaba da tafiya, har ta isa bakin mota zata shiga hafsat tace mata jawwahir mai maki magana ya biyoki mi yake so ki bashi ne?"" tsaki jawwahir tayi taɗan yarfa hannu sannan tace "yan maulane kinsan su basu san yau da gobe ba, bara ki gani, juyawa tayi ta kalli baba sannan ta buɗe jakarta, ta ciro 3k ta miƙa mashi, tayi ƙasa ƙasa da murya tace don Allah baba nace idan ka ganni da mutane ka daina nuna kasanni, haba wai miyasa kake so ka kunyata ni cikin mutane,

Kallo baba ya bita dashi sannan yace ina mahaifinki kike wulaƙantani?"" tsaki jawwahir tayi sannan tace ai nasan kaine ka haifeni kuma kaima kasan ni ɗiyarka ce amma don Allah ka daina man magana wallahi ni kunya nake ji ace kaine babana, anshi ta miƙa mashi kuɗin baba ya riƙe ta juya tayi gaba, tana zuwa ta buɗe motar ta shige, drivern su hafsat yaja su sai gidan tsohon gomna,

Baba yana tsaye har yanxun inda jawwahir ta barshi wasu hawaye suka zubo mashi daga idonshi ya kalli kuɗin hannun nashi sannan ya girgiza kanshi yace Allah ka shirya man jawwahir Allah ka rabata da wannan rayuwar ƙaryar da ta saka kanta, wanda har take baƙin cikin ta nuna ni a matsayin mahaifinta, hawayen ya goge sannan ya koma saman ɗan bencinshi inda yake zama wato wurin sana"arshi inda yake siyar da iccen shi,

Su jawwahir an samu yanda ake so, a gidan tsohon gwamna an wani game bisa kujera one seater idan ka ganta ka rantse itace ɗiyar gdan , sai wani basarwa take, hafsat ce ta fara gabatar da jawwahir wurin "ya"yan uwanta wato a gdan gwamna wanda baya ci, sannan hafsat ta gabatar da sadiyya a wurin jawwahir sadiyya ta miƙawa jawwahir hannu suka gaisa, jawwahir ta riƙe hannun sadiyya gam tana kallonta sannan tace niko kamar na taɓa ganinki,

Sadiyya tayi murmushi sannan tace a ina kika sanni?"" sai a lokacin jawwahir ta saki hannunta , itama ta koma ta zauna a wurin zamanta, jawwahir tace kamar mun haɗu dake a *meldives* ne ko *mexico* ɗan gajeran tsayi jawwahir tayi sannan tace nadai manta, sadiyya tayi murmushi sannan tace ba mamaki aikinsan haka abun yake sai ka haɗu da mutum kama rasa a ina ka taɓa ganinshi, jawwahir tace haka ne, haka dai sukai ci gaba da fira daga baya suka tashi suka fito dan ɗaukar hotuna,

Bayan sun gama ɗaukar pictures ne jawwahir tace ma sadiyya mu gani in ɗan tura sunman kyau, sadiyya tace babj damuwa ta miƙa mata wayar, jawwahir na karɓar waya contacts in sadiyya ta shiga, ta fara neman number baban sadiyya, haka tayi ta lalubawa har ta gano number, tilashin mutum abinda yasa kanshi ɗaff jawwahir ta hardace number cikin ƙoƙan kanta, kasancewar number speacial ce kundai sannan number manya yanda take,

bayan ta gama hardace number ta ɗan tura hotuna sannan ta bawa sadiyya wayarta, saida suka tashk zasu tafi jawwahir tace sai mun dawo biki idan kuma bana nan daga baya zanzo maku Allah yasa alkairi, sadiyya tace,

haka suka rantayo suka fito waje dukansu, sadiyya ta masu rakiya har wurin da suka ajiye motar su, hmmm jawwahir ƙarya, kunsan nawa ta bawa "yan sanda da suke gadin gidansu sadiyya?""

tou dubu ɗari ta basu su raba, wannan yasa sadiyya ta gane jawwahir babbace don haka tace mata bani contact inki , jawwahir tace tom ta karanta mata number tayi save sannan ta kira jawwahir itama taga number inta, hmmm duniya kenan wato rayuwar kwarya tabi kwarya ce, haka suka shige mota suka tafi, jawwahir uwarki tana can tana fama da yunwa amma kinxo waje kinnemi suna, Allah ya sawaƙe,

hafsat tace gda zamu kaiki ne?"" jawwahir tace aaaa ki ajiyeni a cidcap company , zanga wani , hafsat tace to, saida sukazo sannan jawwahir ta sauka tayi ma hafsat godiya da addu"ar Allah huta gajiya, jakarta ta buɗe 10k ta bawa drivern su hafsat godiya yayi sosai sannan ta shige wurin Alhaji,

Tana shiga office ɗin alhaji baya nan, saboda haka wuri ta samu ta zauna saman kujera, wayarta ta fiddo tana "yan latse latse, har Alhaji ya shigo, bayan ya zauna ne jawwahir ta gaishe shi, ya amsa, sannan tace waini banma tambayeka mi zakai da number dad ina ne?"" wai tsohon gwamnan ne dad inta, saboda yayan dad inta ne tace,

alhaji yace ai da ina da number shi gogewa tayi wallahi amma yanxun zan kirashi a gabanki ince mashi kece kika bashi number na, jawwahir ta zaro ido tace ka rufa man asiri don Allah zaiman faɗa ne yace ina bada number shine, alhaji yace kada ki damu babu abinda zai maki Allah tace nidai ka rufa man asiri don Allah, hankalin jawwahir ya tashi sai zufa take duk da ac ɗin dake office ɗin tashin hankali Alhaji ya hango kwance cikin idon jawwahir,

alhaji yace to babu damuwa bazan faɗa mashi ba bani, jawwahir ta fara karanta mashi number bayan tayi mashi dogon kashedi,

tana gama faɗa mashi ya shiga neman wayar, tana shiga ringing ɗaya biyu zuwa ukku, aka ɗauki wayar ranka ya daɗe inji alhaji haka dai suka ci gaba da waya da alama dai kowa yasan kowa, bayan sun gama wayar ne Alhaji yace kai naji daɗi sosai dan haka nine zan baki kyautar mota kyauta , dan naji daɗi number nan, ajiyar zuciya jawwahir ta sauke sannan tace na gode kuma kaman alƙwari idan na gama makaranta zaka ɗaukeni aiki a companyn nan, alhaji yace kada kiji komai ai zama da irin ku a wuri alkairi ne, nayi maki alƙawari zan ɗaukeki da zaran kin gama secondry sch, jawwahir tayi dariya, shima alhaji godiya yayi mata, sannan sukai bankwana, yace gobe ta dawo ta ɗauki mota, tayi godiya sannan ta bar office ɗin,

*ina jawwahir tasan alhaji ne?*

jawwahir idan baku manta ba nace maku "yar cusa kai ce, idan tana san ta danfare ka zata iya zuba miliyan ita kuma idan ta tashi sai ta kwashi miliyan biyar idan ta dan fareka zata ɓace baka ƙara ganinta saboda bata yadda kowa yasan gidansu idan kayi mata waya kullum sai tace tana ƙasar waje kamar wata tsuntsu kullum ita rayuwarta saman jirgi,

alhaji yasan jawwahir a makarantar su, lokacin da yakai ziyara ne a wurin principal ɗinsu, saboda buɗewar idon jawwahir da shiga manyan mutane, yasa tasan suturun manyan mutane kuma take gane mutumin da yake cikin hutu, haka tasan motoci, kuma ita a gdansu ko keke babu,

pricipal yayo ma alhaji rakiya ita kuma ta wani malaminsu ya aiko ta, a bakin office suka haɗu, kasancewar jawwahir ta goge tana ganinshi ta wani yage baki la dad, ashe da rabon zamu sake haɗuwa?"" daga prnpl har alhaji tsayawa sukai suna kallon jawwahir,

taci gaba da cewa rabona dakai tunda muka haɗu a *pakistan* alhaji yabi jawwahir da kallon dariya tayi sannan tace kila dan ina cikin schuniform ne baka ganene ni ba, hmmm alhaji shima da yake ɗan duniya na gurzawa a mujalla ya ware idanuwanshi yana ma jawwahir wani irin kallo, gabanta ya faɗi tace Allah dai yasa kada ya yarfani,

Taci gaba da zance zuci tace dan naga mai kuɗi ne na nuna nasan shin dan in ƙara martaba a idon makaranta , kuma fa bata taɓa ganinshi ba tsabar shishigi ne kawai irin nata,

tana tunani taji alhaji

3 / 28