Author : MEELAT MUSA Category : African Stories & Novels
so tafiyar jawwahir ba, dan jawwahir tana burgeta kuma bata gajiya da kallonta, kunsan hausawa sunce idan kana san abu har abada baka baka ganin matsalar shi,
fita sukai da ita da hafsat , hafsat itace taja motar suka bar gidan, bayan ta ajiye jawwahir ita kuma ta wuce wurin anso masu kayansu,
tana shiga ciki ta wuce office ɗin Alhaji, bayan gaisuwa yace mata ina ta shige kwana biyu?"" tace taɗanyi rashin lafiya ne, alhaji yayi mata sannu , shiru na wani lokaci jawwahir tana zaune saman kujera alhaji yace ai biki kuke ko?"" jawwahir tace mashi Eh yace to idan kun gama kixo ki ɗauki motar ki kin ganta can daga ciki ya nuno mata motar sannan yace kuma bana nan zan bar sallahu , jawwahir tayi godiya sosai sannan tatashi ta fita dan taga kiran wayar hafsat tasan ta dawo kenan, tana fita hafsat ta ɗauketa suka koma gidan biki,
Cikin ƙarya irin ta jawwahir haka duk shigar da akayi ta saka taje ta cewo bashi dan fita kunyar idon duniya kuma ta fita, ita bata biyan bashi bare hankalinta ya tashi, haka dai aka sha shagalin biki lafiya aka gama,
ranar da zasu tafi sadiyya ta haɗa ma jawwahir abun arxiki gaskiya ta kashe mata kuɗaɗe sannan ta sheda mata cewa insha Allah sai taxo mata ban gajiya, jawwahir tace Allah yasa lokacin tana nan, sadiyya tace amin, ta karɓi sabuwar numberta tayi godiya sosai dan haka lokacin da zata rabj da jawwahir ita dai Allah yasan bataji daɗi ba, hafsat ta ɗauketa bayan sun fito ne tace ma hafsa hassu ajiyeni a inda kkka saba, zan anso saƙo idan na gama zanzo ta gidanku,
hafsat tace to, tafiya sosai sukai har suka iso companyn su Alhaji, hafsat ta sauke jawwahir , tana sauketa ta nufi ciki ita kuma hafsat ta nufi gida,
Da sallama jawwahir ta shiga cikin office ɗin alhaji, amsa sallamar yayi yana cewa oyo yoo yanxun nake shirin kiranki, jawwahir tace ai na hutashshe ka tunda naxo, alhaji yace gaskiya, tasowa yayi daga inda yake zaune ya nufo wurin jawwahir, ita a tunaninta fita zaiyi saboda haka ta ɗan matsa jikin bango dan ya wuce, amma ina kusa da ita ya matsa ta sake ja baya, shima matsawa yayi sosai lokacin da jawwahir ta dangane da jikin bango,
Alhaji yakai hannunshi ya riƙo mata ƙugu, jawwahir tace miye, kamar jira yake tayi magana don haka bakinshi ya haɗe da nata, abunda tunda jawwahir take a duniya ba,a taɓa mata ba, iyakar tashin hankali hankalin jawwahir ya tashi, bata gama tsinkewa da lamarin alhaji ba, saida taji hannunshi cikin rigarta, daƙel jawwahir ta zare bakinta daga nashi dan ji take kamar zatai amai wannan wace irin ƙazanta ce?"" tayi ma kanta tambaya,
Hannunta alhaji yaja ya nufi saman kujera ya zaunar da ita jawwahir da hawaye ya cika mata ido ta kalli alhaji tace wannan wane irin wulaƙanci ne?"" alhaji cikin disashiyar murya yace an faɗa maki ana hawan mota a banza ne?"" yayi wani sakaran murmushi hankalin jawwahir ya tashi yanda taga gaba ɗaya alhaji ya fita hayyacin shi,!
haka alhaji yaci gaba da murzar jawwahir san ranshi ita kuma sai kuka take tana bashi haƙuri hannunshi ya sake kawai cikin rigar ta yaci gaba da wasa da dukiyar fulaninta, yaudai jawwahir taga iskanci tsanar ruwanshi, cikin kuka tace alhaji ba haka nake ba, idan da nasa kaina wannan harkar da tuni na ɓalle nabar gida, dan idan na tashi abuja na nufa baki ɗaya dan acan zanje in samu manyan alhazawa, dan bazan zauna anan ba inyi karuwancin wahala, iskanci da baya da riba bare uwa,!
Alhaji yace yo ai ko kinje abujar mune zaki gani, danni kwallo ce babu inda ban juyawa , a daidai lokacin daya kai hannunshi ya shafo ƙasanta, tsaki yayi lokacin da ya gane bata sallah ajiyar zuciya yayi a ranshi yace ba komai yarinya zan baki mota amma ko ba yau ba sai kinji jikinki, haka dai yayi ta juya jawwahir kamar waina a saman tanda, dama duk wanda baiji bari ba ai rayuwa zata kaishi inda baya tunani, saida alhaji ya gama mulmule jawwahir dan san ranshi ya gaji, sannan ya saketa,
makullin motar ya ɗauko ya bata, jawwahir tace ka barshi, gaban alhaji ya faɗi saboda yasan idan dai bata anshi motar nan ba haƙiƙa yama shirya asarar datafk haka, kallon jawwahir yayi sannan tace miyasa zan barshi?"" tace ai nice nace ka bari ba?"" har yanxun hawaye ke fita daga idonta, Alhaji yace kiyi haƙuri wannan mota da sunanki na siyo saboda haka kiyi haƙuri ki amsa, tsaki jawwahir tayi sannan ta nufi hanyar fita, tana taɓa ƙofa taji ta a rufe gamm,
ta juyo ta kalli alhaji tace malam buɗeni, alhaji yace idan har baki amsa ba yau saidai ki kwana a office ɗin nan, yaci gaba da cewa kuma nayi vidio kaff idan baki karɓa zan nuna shi wa sadiq, hankalin jawwahir ya tashi ta dawo ciki da sauri tace ma alhaji ina kasan sadiq?"" lokacin da hawaye sukaci gaba da karakaina a idonta, miƙa hannunta tayi ta anshi key in motar sannan ya buɗe mata ƙofa, tana fita da gudun bala"i ta isa wurin motar da alhaji ya nuna mata, tana zuwa ta buɗe ta shiga tabar companyn,
tana fita alhaji yayi dariya wanda duk abinda ya faɗa ma jawwahir ƙarya ne, shi baida hankali dazai ɗauki vidion kanshi ya watsa a duniya?"" dariya yayi daidai lokacin da yake zama saman kujera, hannunshi yakai daidai gemunshi ya murza sannan yace sadiq , lallai tana tsoronshi , shifa alhaji baisan sadiq ba amma duk cikin binciken jawwahir an faɗa mashi tana da yaya wanda take tsoro kamar ajali, saboda shi alhaji tuni yasan wace ce jawwahir a saman tafin hannunshi,
ajiyar zuciya ya sauke sannan yace wato kina zalinci wa al"umma amma baki yadda ki saɓawa Allah, saboda zina babban saɓone kuma katotuwar halaka ce, duk wanda baya san zaman lafiya a rayuwarshi to ya kusanci zina, idan kuwa ya aikata fa haƙiƙa ya tashi aiki, Allah yasa mu dace,
Jawwahir tana fita daga comparny, wuri ta samu tayi parkig bayan ta fito daga cikin motar ta duƙa taci gaba da zazzaƙo amai kamar zata amaye hanjinta sai kuka take tana ta bani ta lalace dama sadiq yace mata karuwa ina ga yaga wannan babban sabo wanda ko a gaban wani takejin tsoronshi to mi zatace ma ubangijin ta?"""
Hawaye ya sake zubo mata, ta gogesu cikin tashin hankali tace ashe kenan yau da bana period da alhaji ya kacaccala man rayuwa, saboda tsabar rashin galihu a saman kujera zai fasadi dani, ta sake fashe wa da kuka tunda jawwahir ta fara *4 1 9* bata taɓa haɗuwa da baƙar rana irin yau ba, kuma yaune ranar farko da ta fara dana sani a rayuwarta, ta tsine ma alhaji yafi cikin kwando, kuma ta ɗauki alƙawari ta gama da alhaji har abada niko nace ƙarya kike, tunda dai mugunta kika saka a rai ai bama kiga komai ba,
Alhaji har yanxun yana Office zaune gabanshi sai faɗuwa yake saboda jawwahir ba ƙaramar muguwa bace, baisan kuma da wane salon zata zo mashi ba, lallai baisan jawwahir bahagguwa bace da kwata kwata bazai tunkareta ba, amma yanxun miye mafita?"" nidai nace ai sai ka nemi jawwahir ,
miƙewa tayi daga inda ta gama amai, motar ta kalla sannan tayi murmushi, tace a bayyane saboda ke ?"" namiji ya taɓa man jiki, ni , ni jawwahir saboda motar namiji ya haɗa bakinshi da nawa, saboda ke ta sake nuna motar tace sannan tace ni namiji ya taɓa ma nono ba ta hanyar aure ba, wasu hawaye masu zafin bala"i suka sake zubowa daga idon ta , cikin kuka tace wallahi ka taɓo maka kanka bala"i nace bazan sake zuwa ba, saina dawo saina dandaƙe maka yatsu saina ɓare maka baki gida biyu, da ƙarfi take maganar sannan ta halbi tayar motar da ƙafarta da ƙarfi sosai, sanann ta shiga motar ta nufi gidansu hafsat, tana zuwa tayi horn mai gadi ya buɗe mata, ta sulala ciki, bayan tayi parking tana cikin motar har yanxun bata fito ba,
wayarta ta fiddo ta kira hafsat tace mata gata gidansu tazo ta ajiye motar ta, zata bawa mai gadi makullin ya bata sauri take, hafsat tace ai ban gida amma gab nake da gidan yanxun,
jawwahir tace to mu haɗu a wajen, hafsat tace tom, fitowa jawwahir tayi daga cikin motar ta kulleta sannan ta nufo waje , tana fitowa bata daɗe da tsayuwa ba saiga hafsat saboda haƙa motarta taje ta buɗe ta shiga sannan tace kaini titin gidanmu, hafsa ta juya da kam motar ta suka nufi unguwarsu jawwahir, ganin da tayi ma jawwahir kamar tana cikin damuwa yasa bata mata magana ba, har ta ajiyeta, jawwahir ta miƙa mata makullin motar tace ki ajiye man, hafsa tace to ta karɓa jawwahir ta fita daga motar ta shiga kwanar unguwarsu,
Bayan ta fita hafsa tace komi akai mata ne oho?"" taci gaba da cewa ba abin ka tambayeta ba masifar ta ƙare kanka, to Allah dai ya sawaƙe, taja motar ta tayi gaba,
A zauren gidansu ta tsaya ta goge hawayenta, sannan ta shiga cikin gdan babu ko sallama, yau kwanan jawwahir huɗu bata gda sai yau ta dawo, tana shigowa cikin gdan baba yace jawwahir daga ina kike?"" ko inda yake bata kalla ba ta wuce ɗaki, inna dake kching jin an anbaci jawwahir yasa ta fito da sauri lokacin data fito tuni jawwahir ta shige cikin ɗaki,
Kallon baba inna tayi sannan tace kace jawwahir, yace ga lbanzar can cikin ɗaki, a daidai lokacin da jawwahir ta fito da towel jikinta, kwando ta ɗauka sannan ta nufi bakin rijiya ruwan da inna taja ta juye sannan ta wuce danyin wanka,
inna tabi jawwahir da kallo , tana nan tsaye tana kallon ikon Allah tama kasa magana, baba yayi alwalla ya fita, ita kuma inna taci gaba da aikin gidanta,
Jawwahir tana fitowa daga wanka, tayo ɗaki tana zuwa bayan ta gama shirinta tsaff tasa kayan baccinta ta haye gado tayi kwanciyarta, kuka jawwahir tayi har ƙarfinta ya ƙare, saboda haka tayi haƙuri tayi shiru,
duk abinda ake gidan nan jawwahir taki ta fito, tana ɗaki, inna ta gama abinda take bayan baba ya dawo, tabi shi ɗakinshi dan ita dai halin jawwahir ya isheta, ace kamar jawwahir ta kwana huɗu bata gida ina taje?""
sadiq kuma wani abokinshi yayi mashi waya cewa jawwahir ta dawo, yace ai zaizo gidan, dan kwana biyu wanda bai ganta ba, yana tambaya saidai kawai ace taje kyauye, wannan zamani an daina kiwon dabba mutum ake kiwo,
Sadiq jikinshi har ƙarma yake ya iso gida danji yake tafiyar da yake kamar ana dawo dashi baya, saboda haka cikin ɓacin rai sadiq ya shigo gida, shima baiyi sallama ba gani inna bata tsakar gidan, saboda haka yana shigowa ɗakin inna yayi ma tsinke,
Yana shiga jawwahir taji alamar mutum ne ya shigo tana cikin bargo har yanxun, wayarshi ya fiddo daga cikin aljihun wando ya haska fitila, inda jawwahir take kwance yaja ya yaye bargon , lokacinnda taji an taɓa bargon ta tabbatar ma kanta babu wanda zai mata haka sai sadiq wani ɗan guntun fitsari taji ya zubo mata, idanuwata buɗe suke kam sai gabanta dake faɗuwa, saboda har yanxun bata daina kuka ba,
Kallonta yayi sannan yace ta tashi ta kunna fitilar ɗakin, shiru tayi kamar bataji abinda yace ba, ya sake cewa har sau nawa zan faɗa maki?"" jawwahir ta sauko daga saman gado taje ta kunna fitilar har yanxun yana tsaye ita kuma tana kunnawa bayan ta dawo bakin gado hularta ta ɗajka ta saka sannan ta haye saman gado ta kwanta bargo taja ta sake lulluɓewa, sai zare idanuwa take tana addu"a a ranta Allah yasa ya fita,
bata gama ma addu"ar ba taji ya sake yaye bargon, idonta ya sauka saman fuskarshi, shi kuma hannuwanshi ya ɗora saman gadon ya maidata tsaki ya, ma"ana hannuwanshi suka maida ita tsaki, ya ware su ɗaya a gefen damar ta ɗaya a gefen haggun, ya ɗuko da kanshi yana kallonta wasu hawaye suka zubo daga idonshi suka sauka saman fuskarta, jawwahir data rufe idon ta taji saukar wani abu mai zafi da sauri ta buɗe idon ta, ganin sadiq yana hawaye hankalinta ya tashi,
Tana ƙoƙarin miƙewa zaune hannunshi yasa ya sake kwantar da ita, yanda yake kallonta yasa gabanta yaci gaba da faɗuwa, har yanxun sadiq hawaye zubowa suke daga idonshi suna zuba saman fuskar jawwahir hankalin jawwahir ya tashi sosai saboda bata san dalilin da yasa sadiq yake kuka ba,
kuma tunda yace ta kunna fita har yanxun yaƙi yayi magana, bare ma tasan abinda tayi, amma ya wani zo ya duko kanta sai kuka yake mata,
buɗe idonta tayi taga har yanxun ita yake kallo da sauri ta sake rufe idonta, ah ah, wai miye haka ne?"",,,, jawwahir taji har yanxun sadiq bai tafi ba, ta sake buɗe idonta har yanxun ita yake kallo , jijiyar goshin shi ta tashi gaba ɗaya ya canja mata kamanin ƙarfin hali tayi cikin wani irin yanayi tace don Allah miye?""", sadiq yace jawwahir waye ya haɗa bakinshi da naki?""" idanuwa jawwahir ta zaro, faɗuwar gabanta ta ya sake ƙaruwa lokaci ɗaya kuma tsoro ya bayyana a fuskarta, tana ƙoƙarin tashi ya sake maida ta ya kwantar da ita, cikin tashin hankali jawwahir tace waye yace maka ya haɗa bakinshi da nawa?"""
Sadiq da yake kallon jawwahir yace ai bama bakin kaɗai ya haɗa ba , wannan shine mai sauƙin faɗi dan ki sani duk abinda kika ko akayi dake inaji a jikina, sai a lokacin ya tashi sannan ya juya bayanshi dan niyar fita da sauri jawwahir ta sauko daga saman gado tasha gabanshi tana kuka tace rufa man asiri kada ka faɗa ma kowa wannan maganar don girman Allah kaga kai ɗan uwana ne, ka rufe man asiri don Allah, hannu shi yasa ya janye jawwahir gefe ɗaya sannan ya fita yabar ɗakin kafin ta fito har yabar gidan,
wato tama san tayi kenan, kukan sadiq ya ƙaru wato abinda yaji da gaske ta farun kenan,
jawwahir fita tayi da gudu tayo ƙofar gida, tana leƙowa taga sadiq yayi nisa sosai, dan haka gidan ta rufe sannan ta dawo ɗaki ta kashe fitila, ta haye saman gado, tana kwanciya tace wato alhaji ni zai tona ma asiri, kuma ya rasa wanda zai faɗama sai maƙiyina, jinjina kanta tayi sannan tace biyu kenan, kuma duk saina rama su dan bazan yafe maka ba, hakan dai taci gaba da saƙawa da kwancewa, har bacci ya ɗauketa,
Ban garen sadiq kuma yanda yaga dare haka yaga safiya, niko bansan dalili ba,..................
[1/17, 7:36 PM] Jamila Musa Ws: ☄
☄☄
☄☄☄
🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥
*WANDA BAIJI BARI BA*
🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥
☄
☄☄
☄☄☄
*AMEENCI WRITER'S ASSOCIATION* 📚✍🏻
*MEELAT MUSA* 🌹
*PAGE* 11
*****
*K*o da safe jawwahir abinda sadiq ya gaya mata yasa ta kasa fitowa kwata kwata, tana ɗaki duk abin duniya ya dameta, jawwahir tace kilama ya gaya ma innas innalillahi wa"inna ilaihir raji"un, kai aiko da har abada na daina zaman gidan nan,
Tsaki tayi sannan tace wallahi alhaji ka bani dani tunda har ka faɗa ma sadiq maganar nan saina saka kukan da har abada hawayen bazasu goge ba sai ka bar sararin duniya,
Jin an shigo ɗakin yasa tayi saurin rufe idon ta, inna tace jawwahir anshi lokacin da take miƙo mata kuɗi, juyowa tayi amma ta kasa haɗa ido da inna, 500 inna ta bata tace gashi tayi abinci ita zatayi tafiya jikin hajiyarta yayi tsanani, jawwahir tace kema ki dawo da ita nan mana,
Inna tace ai baza ta dawo ba, kuma tunda gasu yakunbo a wurinta idan na ɗaukota zasu ga kamar na raina masu, jawwahir tace to aje nan, kuɗin inna ta ajiye sannan ta fita taci gaba da shirin ta, tana gamawa tayi jawwahir sai ta dawo,
Tace don Allah innasco kada ki daɗe pha, tsayawa inna tayi sannan tace ke idan kika tafi naki yawon basai na ganki ba?"" jawwahir tace ai dani dake ba ɗaya ba, inna tace tosai naga damar dawowa, jawwahir tace to Allah ya sawaƙe, kuma idan har kika kwana ma kafin ki dawo kakaff kayan ɗakin saina siyar,
Inna tace ki maida hankali , tana faɗin haka ta fice, inna tana fitowa wani abokin sadiq ta gani tace mashi don Allah yaje ya kira mata sadiq ta fita a gida, dan ta kira wayarshi bata shiga, yace to,
Inna tana tafiya tana tunani wallahi jawwahir fa tana iya siyar da kayan kamar yanda tayi niyya, wata zuciya tace mata ta koma ta tusa ƙeyarts gaba ta tafi da ita, wata zuciyar tace ta barta kada ma ta tafi da ita kuma abun ya zamar mata matsala da surutu a cikin mutane dan duk yanda mutum baya tunani jawwahir ta wuce wurin,
Jawwahir tana ganin fitar inna inda ta ajiye kuɗin ta kalla ta ɗauki ɗari 500 ɗin tsaki tayi sannan tace "yar san banza duk cikin ɗari biyar za"ai abinci rana ayi na dare tsaki tayi sannan ta miƙe ta fito wanka tayi ta shirya, tayi waje,
Bakin hanya taje ta kashe kuɗin nan kafff sannan tayo gda, tace idan kin dawo sai kici haƙuri, danni ban zaunawa in dafa wani tuwon banza can baki da aiki kullum tuwo kullum towo sai kace ƙaton kauye, lokacin da jawwahir ta dawo gida, ta shiga dube duben inda zataga abinda zata siya wanda inna zataji babu daɗi a ranta, niko nace idan aikinki ɓata ma wani rai wata rana kema sai kin rasa inda zaki saka rayuwarki,
ta karaɗe gdan tatas bata ga abin ɗauka ba, don haka haƙura tayi ta koma ɗaki tayi kwanciyarta,
ita kuma inna har yanxun hankalinta ya kasa kwanciya, haka ta shiga neman wayar sadiq har ta samu, bayan ya ɗauka tace mashi yaje gida ta bawa jawwahir kuɗi tayi masu abinci yaje ya tsareta kada ta fita kuma kada ya barta ta ɗauki wani a gidan kuma yasa ta dafa abincin idan ta gama yakai ma malam, wato baba,
sadiq yace to, bayan sun gama waya da inna ya tashi a gajiye, wanka ya farayi sannan ya shirya yayo gidansu,
jawwahir tana kwance tana tunanin irin bala"in da zata saka alhaji saidai tayi tsaki idan zuciyarta ta kawo mata shawarar banza, daga kwance ta jawo jakarta