Author : MEELAT MUSA Category : African Stories & Novels
isa wurin ne , sadiq ya miƙe mashi hannu su gaisa, bai haɗa hannu da sadiq ba, saidai yaɗan rusuna, ya gaishe da sadiq, gaisuwa sadiq yayi mashi, da fatan Allah ya ƙara haƙuri,,,,,,
yayi godiya,,,,,sadiq yace yawwa maganar wata yarinyace da kasa aka kame, wai tana da hannu a cikin kisan Alhaji,,,, kallon sadiq yayi sannan yace Eh, amma ai duk an saki kowa, saboda an gano wanda ya kashe shi, sadiq yace wannan ba damuwa ta bane, an saki kowa amma ita miye yasa ba"a saketa ba?"",,,,,, yace ranka ya daɗe kayi haƙuri, sadiq yace muje,,,,,,,a daidai lokacin daya shiga mota, shima shiga yayi suka tafi,,
a hanyarsu ta tafiya ne yake ba sadiq labari cewa ai matar babansu ce tasa aka kasheshi saboda wasu dalilai nasu can na mata, kuma itace ta faɗa da kanta, sadiq baiyi magana ba, haka yayi ta rattafa surutunshi har suka isa,,,,,
Suna isa ɗan alhajine ya fita, yabar sadiq a mota, can dai sukayi "yan maganganunsu sannan aka ciro jawahir, ana fito da itane tabi duk wanda yake da wurin da kallo, batayi magana ba, dan tunda aka kama jawahir batayi magana ba, baƙin ciki da takaici kamar ta haɗiye zuciya ta mutu, wani ɗan sanda ne yace kije, tsaki tayi sannan ta fita daga wurin,
Tana fita waje, ɗan alhaji ne yace ga wanda yaxo ɗaukar a cikin can, batayi mashi magana ba, wurin motar tayi ma tsinke dan ganin wanda yazo cetonta,,,, tana isa bakin motar sadiq ta gani, gabanta ya faɗi, kallonta yayi sannan ya fita daga mazaunin tuƙi yayi ya zagaya ya koma gefe , kallonshi jawahir tayi sosai sannan tace a ranta mai kyau da kyau yake inji jakki da yaga magon doki, gaskiya sadiq ya haɗe da yawa, kuma kayanma sun mashi kyau, wata zuciyar tace ke shine yayi ma kayan kyau ba, ba kayan sukai mashi kyau ba,,,
Jiki a sikwane ta shiga motar sannan taja, suka bar wurin, a ranta magana takeyi ko miyasa sadiq baya tuƙi da kanshi idan tana mota?"",,,,,,, bayan sun fara tafiya sosai, sannan sadiq ya kalleta yace da nace kada ki ɗauki komai na larba kikace ai bana babana bane ko?"",,,,, to inga na baban naki wanda yake dole naki ne, kinja ma kanki shiga rijiya,
baban nawa yaje ya cito rayuwarki, jawahir dai batayi magana ba, yaci gaba da cewa to mi kika ɗauka ne?"",,,,,, jawahir ko inda yake bata sake kallo ba, tuƙi takeyi abinta, dan ta ɗauki alwashi tana komawa gida miji zata fitar kawai tayi aure ta hta,,
jin tayi shiru yasan shima sadiq ya basar da lamarinta, suna isa gda yace basai ta shiga da motar ba, zai fita yanxun, bayan ta gama faking ne, suka fita dukansu,,,,,,
Jawahir na gaba sadiq yana bayanta, har cikin gda, suna shiga daga inna har baba suna nan, jawahir bata tsaya yin magana da kowa ba, tayi cikin ɗaki, tana zuwa kayan jikinta ta cire hijabi ta saka don fita yin wanka, an fara hankali kenan,,,
Tana fita babane yace jawahir Allah ya kyauta gaba, ubangiji ya tsayar nan, murmushi jawahir tayi amma batayi magana ba, ruwa taja ta shige wanka, tana fitowa sadiq yana zaune a ƙofar ɗaki saman kujera tayani gulma yana cin abinci,
Ɗaki ta shige, tana shiga tace innas kiyi magana wa sadiq don Allah kayana ya bani, tun lokacin da na dawo kano kayan suna cikin motarshi, sadiq dake zaune yanajin jawahir murmushi yayi a ranshi yace muguwa na bata tsoro , miƙewa yayi tace sake cewa innasco gayacan zai fita, inna tace sadiq ɗauko mata kayanta,,,,, sadiq yace ƙarya take inna da kanta taje ta ajiye,,,,,,, inna tace to kisa wasu kayan mana, jawahir tace to ai komai nawa yana ciki duk abinda zan buƙata yana wurinshi,,,,,
sadiq yace zo muje ki ɗauko, jawahir tayi shiru, inna tace kije ki anso, kallonta tayi sannan tace innas so yake ya dakeni idan na bishi,,,,,,,,,,,
inna tace sadiq ka kawo mata, yace wallahi idan har bazata zo da kanta ba, wallahi yau naba kayan idan ya wuce yau zan ƙonasu wallahi, yana faɗin haka yayi waje,,,,,
Jawahir tace innasco ya tafi fa, inna tace to kije ki anso mana,,,,,,, tsaki jawahir tayi sannan ta ɗauki wasu riga da sikat sunma yi mata kaɗan,,,,,,, ta saka, sannan ta ɗauki wata shareriyar hijabi ta saka,,,,, wani niƙaf ta ɗauka ta saka, dan tanajin kunyar fita haka, dan kamar ta shekara tana jinya haka ta koma,,,,,,,,
tana ɗaurawa tayi waje,,,,, sadiq ta gani tsaye a ƙofar gida suna gaisa da wani abokinshi,,,,, hango honey j tayi ya fito daga gida,,,,,, wurinshi ta nufa, suka gaisa, yace kwana biyu bana jinki, jawahir tace Eh nayi tafiya ne, yace ina kika je?",,,,,tace ba bincike, tana faɗin haka tayi gaba,,,,,
tafiya takeyi, shi kuma yana gamawa mota ya shiga yabi bayanta,,, tana isa ƙofar gidan ta tsaya tana jiran isowarshi,,, bayan ya iso ne, ya buɗe gida, ya shiga da sallama, yana shiga itama shiga tayi,,,,,,,,,ɗaki ya shiga, ita kuma tana tsaye,,,,,, bayan wani lokaci ya fito, sannan yace ta shiga ta gyara ɗakin, jawahir tace wane irin gyaran ɗaki kuma nayi wanka?"",,,sadiq yace ni ina ruwana da wani wanka?"",,, wankankin banza?"",,,,,
jawahir tace don Allah kayi haƙuri wallahi banda lafiya, miya sameki?"",,,,,, cikin kuka jawahir tace duk an bubbuge man jikina wallahi ciwo yakeyi,,,,,,,, kusa da ita ya matsa sannan ya yaye niƙaf ɗin ya kalleta, ita kuma ta aje idonta ƙasa tana ci gaba da kuka,,,,,,,,
sadiq yace to miye na kuka?"",,, kawai bazakiyi sharaba ko?"",,,,to sai kice man bazaki shara ba, jawahir tace nidai ba haka bane kayi haƙuri don Allah yace to naji zo ,,,, hannunta ya kama suka shiga cikin ɗakin,,,, bayan sun shiga ya zaunar da ita saman kujera a farlo shi kuma ya shige ciki, kayanta ya tattaro mata sannan ya fito, shima zama yayi sannan yace , faɗa man abinda kikayi aka sakaki a rijiya?"""""""....,,,,
Kallonshi tayi sannan tace ai kayi man baki, to bakinne ya bini, yunwa ta isheni ba,a bani abinci sai nayi aikin wahala kamar wata lebira, ganin haka kawai na ɗauki kaza fa na ɗauka ta ƙarasa maganar da yamutse fuskarta tayi wani kalar ban tausayi, hawaye suka zubo mata daga idonta tace, shi kenan fa, sai tace duk wanda ya ɗaukar mata kaza saita haukata shi wallahi,,,
ni kuma naji tace zata haukatani yasa nace mata nice, kawai ta nannaɗeni ta sakani a rijiya, wani irin kuka jawahir ta saki sannan tace kuma duk kaine kaja man,
ɗaure fuska sadiq yayi sannan yace kikaja ma kanki dai ɗauki kayan ki tafi, miƙewa tayi ta sake ɗaure niƙaf ɗinta, ta tattara abinda take iya ɗauka tayi waje,,,,,,,,,,,,
bin bayanta yayi da kallo sannan yace munafika wannan yarinyar wallahi baƙin halinta ita kaɗai tasan abinda yake cikin zuciyarta kullum kamar ta Allah amma dama takeso ta samu taci gaba da zungura iskancin ta san ranta,,,,,,,,,,,,,
Ita kuwa tana zuwa gda, ta ajiye kayan , wayarta ta ɗauka, ta fara kiran honey j, bayan ya ɗauka suka gaisa tace kaxo gobe idan Allah ya kaimu ina san magana dakai , yace to Allah yasa rayuwarmu takai, tana kashe wayar tace yawwa kafin wannan azzalimin ya mayar dani kauye sai inyi aurena abuna,,,,,,niko nace wane sakarai zai aureki ?"",,,,,,,,,sulalacewa tayi saman gado ta fara baccin wahala...............,
[1/17, 7:44 PM] Jamila Musa Ws: ☄
☄☄
☄☄☄
🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥
*WANDA BAIJI BARI BA*
🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥
☄
☄☄
☄☄☄
*AMEENCI WRITER"S ASSOCIATION* 📚✍🏻
*MEELAT MUSA* 🌹
*PAGE 23*
***
*G*ari yana waye wa, jawahir aka tashi akayi sallah, bayan ta gama wayarta ta ɗauka ta kira honey j, cewar yaxo yanxun, ja"afar yace tun yanxun?""",,Allah dai ysa lafiya?"",,,,jawahir tace nidai kaxo, yace to bbu damuwa gani nan zuws insha Allah,,,,, tana kashe wayar, miƙewa tayi ta fara canja kaya,,,,,,,,
Inna ce ta shigo ɗakin jawahir ta gaishe ta, inna tayi mamaki amma ta kanne ta ansa, zama tayi a sama kujera sannan ta kalli jawahir tace mata ina zakije tunda safe haka ?""",,,,,
Murmushi tayi sannan tace nayi baƙo ne,,,,,inna tace wane irin baƙone wannan wanda baya baccin safe?"",,,,,,, jawahir tace aike da yake innas ce kyace haka,,,,, inna tace lallai, a daidai lokacin da wayar jawahir ta fara neman agaji, ɗauka tayi sannan tace gani nan zuwa,,,,bayan ta kashe wayarne inns tace don Allah jawahir kada kije ko ina idan kin sallami baƙon ki dawo kinji?"",,,,, kai kawai ta ɗaga mata sannan tayi waje............,,,,,,,,
Tana fita a zaure ta tsaya, sannan tace ma honey j bisimillah, shigowa tayi suka gaisa bayan sun gaisha ne, shiru na ɗan wani lokaci , jawahir tace uhum dama kasan kiran da nake maka ne?"",,,,, yace A, a, jawahir tace dama zance maka na tashi aure ne, idan ka shirya ka turo,,,,,,,,,,,
Idanuwa honey j ya zaro sannan yace haba jawahir ke idan akace maki zanyi aure yanxun ai kinyi mamaki, jawahir tace miye abin mamaki?"",,,,,kaine kace man zaka aureni, kuma ka hanani tsayuwa da kowa, kasan kuma inajin maganarka sosai tunda ina sanka Allah ya sani zan zauna lafiya,,,,, kuma zanyi biyayya a gareka sosai,,,,,
Honey j aka wani yamutsa fuska sannan akace a gaskiya jawahir kiyi haƙuri ni wallahi a ƙafa aka ɗaura man ke saina kwanceki na ruga, jawahir tace saboda ni mayya ce ko miye?"",,,,,, yace kawai saboda baki da tarbiyyane baki da kamun kai daman inajiran zuwan wannan ranar ne in sanar dake,,,,,
A gaskiya bazan iya aurenki ba kiyi haƙuri,, ni auren zuminci ma zanyi ɗiyar ƙanin babana zan aura yarinya mai natsuwa da tarbiyya mai jin maganar iyayenta, keko sai kiyi rabin shekar bakya nan,,,, ga damfara gacin bashi, ga karuwanci, miyau ya tofar a gefe sannan yace Allah ubangiji ya tsareni da aurenki a mafarki naga na aureki saina kashe kaina,
juyawa yayi zai fita, da sauri jawahir ta riƙo rigarshi ta durƙusa saman guyawunta wani irin kuka ta saki mai taɓa zuciya, sannan tace tsakanin ka da Allah ni mazinaciya ce?"",,,,,nan so nawa kana nemana da fasiƙanci amma naƙi in amince da hakan?"",,,,kace kaine zaka aureni ashe dana biye maka da ina nan cikin baƙin ciki, ka rufa man asiri don girman Allah honey j ka taimaki rayuwata kada kace baza ka aureni ba, bayan kasan ka gama da rayuwata, kowa yasan.........,,,ganin sadiq tsaye yasa bata ƙarasa maganar ba,
wani ƙasƙantaccen kallo yayi mata , ita kuma da sauri ta miƙe tsaye kallon ja"afar yayi sannan ya kalli jawahir data kama shi ta riƙeshi gam, yana sake kallon ja"afar da sauri ja"afar ya sauke idonsa ƙasa,,,,,
Jinjina kanshi yayi sannan ya sake kallonsu , lokaci ɗaya kuma yanayinsa ya canja, dakel ya haɗiya miyan bakinshi, sannan yayi cikin gda cikin ɓacin rai,,,,,,,,,
yana shigewa ja"afar yace sakarni banza, kada ma wani yayi tunanin nemanki nake, kwace jikinsa yayi sannan ya fice daga zauren,,,,,,,,, ita kuma jawahir haka sulale tayi cikin gida,,,,,,,,,
sadiq shi kuma a lokacin yake fitowa daga ɗakin baba,,,,,da sauri ta shige ɗakin inna,,,,,, tana shiga ɗaki saman gado ta kwanta ta saki wani irin kuka wanda duk wanda yake gidan saida ya fito waje,,,, da gudu innas ta shigo ɗakin tana tambayar lafiya?""",,,,,,,,
Jawahir batayi magana ba, sadiq yace ma inna tafiyarki ni nasan matsalarta,,,,,,, inna tace bata da lafiya ne?"",,,,,,, sadiq yace Eh kuma nine kaɗai nasan ciwonta,,,,, inna tace to Allah ya bata lafiya,,,,,,tana faɗin haka tayi waje..........inna tana fita, sadiq yayi tsaki, sannan yace kaɗan kika gani sai kin rasa wanda zai aureki da wannan ƙazantattar rayuwar taki, waye zaiso ya auri fasiƙar mace?"",,,, sai wanda baida magaya wallahi,
Kinga ya gaya maki gaskiya yayi kwanjonki, duk abinda kike taƙama dashi ya ganshi ya sanshi yaji shi, to miye baƙo a wurin shi?"",,,,jawahir zatayi magana ya ɗaga ƙafarshi yakai mata wani irin halbi, wanda yasa ta koma ta kwanta da sauri cikin wahaltuwa, sadiq yace na rantse da Allah tunda nake ban taɓa jin ban ƙaunarki irin yau ba, na tsaneki da nasan idan na kasheki ban da laifi wallahi da nine ajalinki,,,,,,
Ja"afar ya saba maki da abinda kike so?"",,,,,, har kike tunanin ku dauwama a hakan,,, to ya lalata ki ya kawai maki da duk abinda wata ɗiya mace take tunƙaho dashi,,,, wane mutunci zakiyi ne?"",,,,kuma duk namijin da yaxo yana sanki haka zai gaɗa mashi wannan banzar?"",,,,mi zakayi da ita ne?"",,,, kinga kin cuci kanki kin cucu rayuwarki,,,, koni naga wani yaxo yana sanki saina bashi shawara kada ya aureki, lokaci da ake nuna maki ki gyara gani kike ba"a ƙaunar dama rayuwa haka take dan duk wanda baiji bari ba, haka zata kasance mashi,,,,,,,
kallonshi jawahir tayi marinta yayi sannan yace idan kika sake kallona saina zaro wannan munafikan idon sakara ballagar mace, jakka ma irin ki sannin ta ina amfani?"",,,, kuma kinsan Allah ko ƙofar gida na sake ganinki saina ƙaryaki , tsaki yayi sannan ya fita daga ɗakin,
yana fita jawahir ta sulale saman gado a hankali ta kwanta sannan ta sake fashewa da kuka,,,,, sadiq daya kusa fita daga gidan yace kuka ma ai yanxun kika fara shi ,
Yinin ranar nan haka jawahir ta yini tana kukan baƙin ciki inna tayi juyin duniya ta faɗa mata abinda yake damunta amma ta ƙiya baba shima yayi rarrashin ya gaji,, haka suka haƙura suka bar jawahir, dan yau baƙin ciki ma ya hanata cin abinci,
***
*B*ayan sati dayin haka, jawahir daka ganta kasan bata tare da natsuwa, duk ta wani hirgice, gaba ɗaya bbu natsuwa a tattare da ita,,,,, jawahir duk yanxun ta gane matsalarta, don haka aure kawai take so tayi, wata zuciyar ta bata kawai ta kira Auwal,,,,, ta faɗi mashi buƙatarta,,,,,,Idan yana da ra"ayi akanta sai ya aureta kawai ta huta, da tsangwama dan shiga goma fita goma, sai sasiq ya daketa, ko mari ko kwanya ko harbi ko duka da belt gaba ɗaya bata da kwaniyar hankali, dan tun tana iya maida mashi martali har ta gaji ta haƙura don gara ta haƙura ta zauna anan idan tace zata koma kauye canma jau, idan ta sake tafiya wani gari shima jau, don haka ta haƙura ta zauna, idan taji sadiq yana shigowa da gudu take barin tsakar gida ta shige ɗaki, idan kuma tana ɗaki taji shi sai tayi sauri ta kwanta ta rufe idon ta kamar mai bacci,,,,,,,
Wayar Auwal ta fara kira, saida ta kusa tsinkewa sannan ya ɗauka, bayan sun gaisa ne jawahir tace Auwal kwana biyu?"",,,, yace wallahi kuwa, ai ina ta kiran wayarki kullum a kashe jawahir tace Eh nayi tafiya ne,,,, yace ina kikaje ne?"",,,,, tace garin babana , yace Allah sarki to kuma yanxun wuri ya ƙure dama bikina nake so in sanar dake gobe ne ɗaurin aure, jawahir tace to Allah yasa alkairi, ubangiji ya bada zaman lafiya, yace ameen sai munyi magana, jawahir tace to, kashe wayarta tayi,
sannan ta sauke ajiyar zuciya,,, wani hawayen takaici ne ya zubo mata daga ido sannan tace haka rayuwa take wani na nema wani ya samu, wata zuciyar tace ta kira Ahmad a legos wata zuciyar tace kedai duk ki bar kowa idan Allah ya kawo maki iyaka sai kiyi airenki, haka ta haƙura ta ajiyar wayarta, amma a ranta ta yanke shawarar komawa isilamiya dan neman ilimin addi,ni, niko nace daga baya kenan ,,,,,,
***
*J*awahir komai ta gama shiryawa don haka yau zata fara zuwa isilamiya, tayi shirinta cikin shiga mai kyau bayan ta gama saka uniform ɗinta ta kalli kanta a madubi, wasu hawaye suka zubo mata daga idonta, da hannunta ta goge sannan ta saka hijabinta, ta ɗaura niƙaf, jakar isilamiya ta ɗauka sannan ta fito tsakar gida, tace tace innasco munje sai mun dawo, inna tace to Allah yasa ki dawo lafiya, jawahir tace amin,
Haka tasa kai ta fice daga gidan, tana fita ja"afar ta gani ko inda yake bata kalla ba ta raɓashi ta wuce, dan dama ita ba wani sanshi takeyi ba, kawai rashin uwane za,ayi uwar ɗaki, haka ta wucewarta abunta tayi isilamiyya,,,,,,,,,
Suna tashi isilamiya wata zuciyar tace kawai tayi gidansu Hafsat, wata zuciyar tace rufa ma kanki asiri yana can yana jiran dawowarki idan kika daɗe kinsan sauran, haka ta biyo hanyar gida ta taho,
Da sallama ta shiga, tun a zaure take jin ƙamshin wani irin turare, wannan dai ba na sadiq bane, ɗakin inna tayi ma tsinke, tana shiga wata "yar gayu ta gani zaune kana ganinta kasan ta gama hutuwa, baka gajiya da kallonta saboda ta ɗaurayu sosai takai "yar gayu sosai gaskiya, sallama jawahir tayi ta shiga ɗakin, inna ce tace mata kin dawo ne?"",,,, jawahir tace umm,
kallon inda baƙuwar take zaune tayi sannan tace sannu?"",,,, cikin yanga da yauƙi tace yawwa, baƙuwar ta kalli inna sannan tace wannan ne jawahir?"",,,,,inna tace Eh, kallonta jawahir ta sakeyi sannan tayi wani shu"umon murmushi, ita za,a gaya ma iskanci?"",,, wai wannan ne jawahir?"",,,, hijabinta ta cire sannan ta ɗauki wata hula ta saka, itama sake kallon jawahir tayi sosai yana sake kallonta, zama jawahir tayi saman gado ta ɗauki wayarta dake ringing,,,,,,,
bin jawahir tayi da kallo tare da kallon wayar dake hannunta, jinjina kai tayi a ranta tace lallai itama fa babbar yarinya ce,
Kundai san jawahir dan haka itama cikin izza da isa ta fara magana,,,,,, ya kike kawata?"",,, hafsat tace banza kixo gobene sa bikina, da sauri jawahir tace tsakaninki da Allah?"",,,,, hafsat tace wallahi, jawahir tace to babu damuwa zanzo in Allah ya yadda, hafsat tace to sai najiki, jawahir ta kashe wayarta,,,,,
inna tace jawahir kinsan ta ne?"",,,,bako jawahir ta taɓe sannan tace A, a da kanta tayi alama, inna tace yayarki ce, jawahir tace ta ina kuma?"",,,,,, inna ce wanda sadiq zai aura ce, wata irin faɗuwar gaba jawahir taji tare da tashin hankali wanda daga inna har baƙuwar da suna ganewa lallai sunsan jawahir taji bala"i, lokaci guda kuna zufa ta zubo mata,,,, daure tayi sannan tace da kyau daga haka bata sake magana ba,
Tashi tayi ta fita tsakar gida, tana fita zama tayi, bata daɗe da zama ba, sadiq ya shigo, sallama yayi amma ko inda yake jawahir bata kalla ba, dukar da kanta tayi tana kallon ƙasa, wasu hawaye suka zubo mata, raɓa ta yayi ya shige ɗaki,
wani ɓangare na zuciyar jawahir yace toke banda abinki miye ma na wani damuwa?"",,,Azzalumi zaiyi aure ai kin huta,,,, murmushi jawahir tayi sannam tace a bayyane haka ne ,,,,,,,
miƙewa tayi ta ɗauki buta ta nufi bayi, shi kuma sadiq yana shiga ɗaki bayan sun gaisa,