Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

WANDA BAIJI BARI BA Rayuwar Ƙarya da Nadama by MEELAT MUSA

Author :  MEELAT MUSA Category :  African Stories & Novels

Chapter   10 / 28

27K to 30K   out of 83K words

bayar ba, ubanda yasa kace zaka siya shine dalilin da zan siyar maka, yace to kuma yanxun ai nace na fasa tace kai ƙarya kake wallahi duk faɗin garin kano banga ɗan durin uwar da zaisa bazan siyar da abincin nan ba,

Kallonta mutumin yayi sannan yace gaskiya ke baki da kunya kuma baki da tarbiyya, dariya jawwahir tayi sannan tace kallarni sama da ƙasa kaga dama nayi maka kama da mai tarbiyya?"" ka ganni a tasha ina siyar da abinci kuma ko mayafi babu ai kasan nakai tantiriyar marar kunya kuma wanda tarbiyya bata raina ba, mutumin yace Allah ya haɗaki da gabanki, jawwahir ta sheƙe da dariya hada guda, ayyuri yuriyuriiiii, sannan ta tafa hannunta, tace zaka ɓace a wurin nan kosai na farke maka ciki?"""

To bani kuɗi na, jawwahir tace idan ka sake man maganar kuɗi saina caka maka wuƙa ka mutu uban kowa ya huta, rigarta ta ɗaga ta zaro wata ƙatuwar wuƙa sannan ta zareta daga cinin gidanta har ɗaukar ido , wal wall, ta tun kari mutumin da gudu ya wuce,

Dariya tayi sannan tace sadiq ma na buwaye shi bare kai sakaran banza, haka dai taci gaba da ɗibar albarka kana ganin ta kaga tantiriyar "yar tasha,

Runfar da take siyar da abincin ta koma taci gaba da mita,

****
*J*awwahir zaune a cikin ɗakinta saman wata yaɗiyar tabarma, kayan shafane baje a gabanta, saida ta ɗauko wancan ta dangwala anan ta ɗauko wancan ta cakala a can, haka dai tayi ta shafe shafe har ta kammala sannan ta miƙe taje ta buɗe wani buhu ta zaro kayan da zata saka,

Doguwar rigar atamfa ta zura, sannan ta ɗauki wani ƙaramin gyale wanda bai sauka saman ƙafaɗarta ba, ta yafa, ta ɗauko wata kafirar jaka ta kwama tare da wasu takalmi masu tsinin tsiya ta saka,

wayarta ta ɗauka tayo waje, ƙofar ɗakinta taja ta kulle sannan ta kalli inda wata mace "yar duniya take tana shan sigari , jawwahir tace hajiyata barka da sararawa tana ƙarashe maganar da buɗe idanuwanta kaff, ita kuma hajiya ta furzar da hayaƙin sigarin cikin sigar iskanci,

sannan tace babbar yarinya sai ina haka ?"" wannan wanka naki ai yana bani tsoro, jawwahir kallon kanta tayi sannan tace hajiyata kenan, hajiya tace nifa inda zakije nake tambaya , jawwahir tace wani gara na samu zanje in tsomashi ruwa, hajiya tace a,a ashe yarinya ta faso gari?"" jawwahir tace har yanxun ina nan yanda kika sanni wanke gara kawai zan in dawo gida,

A daidai lokacin data ci gaba da tafiya, hajiya ta ɗago muryarta tana cewa a dawo lafiya an mata, jawwahir batayi magana ba, ta fice daga gidan,

Tana fita, Auwal yana hangota ya taso daga inda yake, ita kuma ta nufi inda ya ajiye motar shi ta buɗe ta kashe gidan baya, shima shiga yayi mazaunin driver yaja motar suka ɓace daga wurin kamar walƙiya,

Jawwahir wayarta ta fiddo ta fara kiran wanda zataje wurinshi, bayan ya ɗauka jawwahir tace kana ta ina ne?"" yace ina gida nane, jawwahir tace to ba muradin zuwa cikin gida muna nan waje dan haka mu haɗu a wurin yace gani nan ina fitowa,

Sun ɗan daɗe sannan ya fito, jawwahir na ganin shi itama ta buɗe mota ta fito, daga ita harshi suka jingina jikin motar, jawwahir tace barka da dawowa babbar harka, dariya yayi sannan yace ai na ɗauka anan zaki kwana?"" jawwahir tace ba buƙatar kwana, yace to maganar tsarabarki kuma fa?"" jawwahir tace ɗauko man ina nan ina jiranka,

Alhaji yace to maganar auren namu kuma fa?"" jawwahir tace kaifa kacika zumuɗi , shin wai yanxun idan nace ka fito ka aureni don Allah dangina fa?"" sai ka aureni ba tare da sanin su ba?"" yace wannan ba damuwa bane, ai auren duka na sati ɗayane zamuyi"""""

jawwahir tace nikam gaskiya bana auren sati ɗaya yace miyasa ne?"" tace saboda haramunne, yace waike miyasa kin cika taurin kai don Allah?"""" jawwahir tace mi ka gani ne?""" yace kince baki zina to dan na bada kuɗi an ɗaura mana aure miye laifi na?"" jawwahir tace baka dashi amma ka bari zanyi tunani, ɗaure fuska yayi sannan yace to gaskiya kiyi tunani mai kyau, jawwahir tace kada ka samu damuwa, yace to, motar ta koma ta shiga, shi kuma yana cewa sai ta dawo goben, ba tare da jawwahir tayi magana ba, Auwal yaja motar suka bar wurin,

A ƙofar gida yayi parking, ita kuma jawwahir ta ciro kuɗi ta bashi sannan tayi mashi godiya, ansa yayi shima godiya yayi ita kuma ta fita daga motar ta shige cikin gida,

lokacin data shiga babu kowa a tsakar gidan don haka ɗakinta ta buɗe ta shige, tana shiga ta maida ƙofa ta kulle, kayan jikita ta cire tayi ɗaurin gaba, sannan ta zauna ta jingia da bango tana tunanin wace hanya zata huɗo ma wannan sakaran?""

Shidai Alhaji Bishir ya haɗu da jawwahir ne a wata super market bayan taxo nan garin kano, kundai san hali don haka tana ganinshi ta fara cewa am kaine ko?" ta nuna shi da yatsanta, sannan taci gaba da cewa rabona dakai tun a canada ashe zamu sake haɗuwa?"" ta ƙarasa maganar tana murmushi, shima dariya yayi da yake ɗan duniya ne , sai yace kinga kuma nayi missing contact naki, jawwahir tace iyya swry a daidai lokacin data fara karanta mashi no, haka ya ɗauka , sukayi sallama,

Alhaji bashir tunda ya tafi yake tunanin wata hanya zai biyo dan yaga ya samu nasara kan jawwahir?"" amma duk inda ya biyo mata sai ta zille, shine yace idan ya dawo daga tafiya zasuyi aure, lallai saiyau yake cewa kuma sati ɗaya zaiyi ya saketa?"" murmushi jawwahir tayi da gefen bakinta, sannan ta sulale ƙasa ta kwanta, tana faɗin Allah ya kaimu goben lafiya idan baka da hankali zan nuna maka iya nawa makircin,

***
*T*unda asuba wayar jawwahir ta fara rururi dan haka cikin bacci ta lalubota, ta duba mai kiranta, A Bashir , hmmm tace a daidai lokacin data kara wayarta a kunne, ta fara magana cikin yanayin bacci, barka da safiya, yace barka dai,

jawwahir tace wannan irin kira haka tun safe?"" sai kace kayi mafarkina?"" dariya yayi sannan yace wallahi mafarki na, cikin gadara yace mafarki nayi wai kinzo gidana kin rungumeni, sannan kika raɗa man a kunnena wai zaki aureni, dariya jawwahir tayi sannan tace ya akayi kasan abinda yake cikin zuciyata?"" yace shaƙuwa ce, jawwahir tace to yanxun na tashi bara sai anjima ma haɗu, yace to, kashe wayar tayi sannan tace zakaci uwariyanka,

Miƙewa tayi ta shige toilet tayi wanka ta wanke bakinta, sannan ta fito, tana fitowa tayi shirinta sosai , ta fito sharr abunta, jakarta ta ɗauka dan tafiya wurin sana"arta,

A kasuwa inda take siyar da abincin ta cikin runfarta dan ƙare yake da maza, ita kaɗaice mace, wanda abincin dama ita dafa mata akeyi sai ita taje ta siyar,

cikin tashanci jawwahir take magana, da mutane, gaba ɗaya babu natsuwa a tattare da lamarinta, harka dai kasuwar taci ta tashi tana gamawa ta tattara kuɗinta, ta irga sannan ta fitar da wanda zasuyi siyayya ta basu sannan kuma ta fitar da ribar sannan ta sallamasu tayi gida.........

Da fito ta shiga gidan , hajiya da wani ƙato da take kwance saman cinyarsa a tsakar gida bisa benci , ta dunƙula wani irin zagi na marasa kamun kai , tace in sani babbar yarinya da gani duniya ta maki daɗi, jawwahir take idan kina san makaman labarai biyoni ɗaki ki anshi kasonki, kashe sigarinta tayi sannan ta miƙe tabi bayan jawwahir, ita kuma buɗe ɗaki tayi sannan suka shige gaba ɗayansu,

bayan sun shiga suka zauna, wata irin dariya jawwahir tayi sannan tace hajiyata albishirin ki?"" hajiya tace goro, jawwahir tace wani jiƙaƙƙan tsoho na samu dan haka yau zan ɗaurayeshi fesss zan ƙwalƙwali rabona dan haka idan na dawo na baki sauran labarin,

Hajiya tace miya sa sai kin dawo?"" jawwahir tace saboda ke shu"uma ce, ina iya haɗaku yanxun abinda zan samu kafin in isa wurinshi ki rusa man bajet, hajiya tace wallahi bazan maki haka ba, jawwahir tace yi haƙuri don Allah barni kawai saina dawo,

Tana kaiwa nan ta miƙe ta shige toilet, hajiya duk hankalinta ya tashi kada jawwahir taki haɗata da sabuwar tsintuwar don jawwahir lamarinta kullum yana rikita ma hajiya tunani don kullum da sabouwar sheƙa take zuwa,

Hajiya "yar bariki ce amma barikin nata marar aji, barinki da zaka bata sigari kawai ka biya buƙatar , itama ta baro gidan iyayenta akan wasu dalilai tace zata faɗa ma jawwahir amma har yanxun bata bata labari ba,

Jawwahir tana fitowa wanka ta shirya, a gaggauce turare ta fesa ba wata kwalliya tayi sosai ba, ta tattara tarkacenta da zata ɗauka sannan tace hajiyata muje zan rufe ƙofa, hajiya tace don Allah to bani ɗari biyu inci abinci, dariya jawwahir tayi sannan tace wancan na waje bai baki ba?"" hajiya tace bar ɗan iska ƙanzo da ƙuli ya kawo man, dariya jawwahir tayi sannan tace to kije ki kwaɗa kici, muje muje sauri nake kada ya gaji da jirana ya tafi.........

miƙewa tayi suka fito waje jawwahir ta rufe ƙofa, sannan ta matsa kusa da kwarton hajiya, tace haba yayana?"" kai don Allah haka ake harka ne?"" inama amfanin karuwanci irin naka?"" saika kawo ma hajiyas ƙanzo?"" amfani miye zaiyi bare harkai kai kaji zamzam?""

Dariya yayi sosai sannan yasa karan sigarin hannunshi a baki yaja, ya riƙa feso ma jawwahir hayaƙin, ita kuma tari ta fara kulll kulll yace yane?"" cikin maganar daba, jawwahir tace amana takai maka babban yaya, nidai na wuce saina dawo, har zata wuce ya riƙo gyalenta yana cewa dawo , baya baya ta dawo sannan tace sake man gyale, a sharuɗɗan rayuwata bana so ana taɓani idan kuma ka kuskura ka sake zakaji babu daɗi,

Yace to naji bamu kuɗi, tsaki jawwahir tayi sannan tace na hanaku kuje ku nema ne?"" kawai dai kuma addu"a idan na samu yanda nake so in baku gwanjon wani alhaji mai zafi, idan hajiyar taka ta iya riƙe sitiyari sai ku gudu tare ku tsira tare, tana kaiwa nan tayi gaba,

hajiya tace Allah ya kare maki sharri babbar yarin an buga dake an barki, haka dai tayi ta zugata jawwahir tanajin kanta yana mata girma,

Tana fita daga gidan napep tahau, dan yau aiki zata fita bata buƙatar tafiya da Auwal, haka ta faɗa ma mai napep inda zai kaita, don haka yaci gaɓa da sharara gudu bisa titi har suka isa, ya paka ya ajiyeta, ta sallameshi, sannan ta fita,

tana fitowa tama alhaji waya tana ƙofar gida, yace ta shigo tace a,a, daga waje dai, yace to miyasa baza ki shigo ba?"" jawwahir tace idan kayi haƙuri ma ai duka duka abin yazo kusa, don haka kada ka samu damuwa mu haɗe kawai a waje, Alhaji yace to gani nan zuwa, kashe wayar yayi sannan ya saka kayanshi yayo waje wurin jawwahir,

tana ganinshi tayi murmushi tana faɗin barka da fito babbar giwa, duk wanda ya ganka yayi bamkwana da damuwa, ni da ganin gwamna gara ganinka, angon jawwahir bada kanka asare tana ɗan haɗa hannunwanta kamar irin yadda ƙauraye suke yi, wata irin dariyar shaƙiyanci yayi sannan yace kai bakijin magana gaskiya,

jawwahir tace baka ma tantance ba sai ranar zamu angwance, dariya yayi sosai sannan yace mike tafe dake ne?"" dariya jawwahir tayi sannan a ranta tace zakaci ubanka baka san jawwahir ba,

Gyara tsayuwarta tayi sannan tace abinda ya kawoni shine, magana ta farko dai na amince zanyi auren mutu"a dakai kamar yanda ka buƙata, magana na biyu kuma, zan yanka maka sadaki sai kuɗin lefe da sauran abinda zanyi hidima, alhaji yace nawane sadakin naki?""" jawwahir tace ga kai ga fata ai ba"a tambayar mi aka yanka!!""" kallarni sosai kaga nayi nawa ne?"""


dariya Alhaji yayi sannan yace aiko miliyan aka bayar kinyi, jawwahir tace bugu da ƙari ma nayi sannan yanda ka ganni a hakan haka nake zam zam, alhaji yace keko miliyan ɗaya tayi yawa jawwahir tace miliyan ɗaya zaka bayar sadaki idan ba haka ba auren na fasa, ga zunibi ga saɓon Allah?"" ai gara ka bani da yawa dan isan naci dayawa,

ajiyar zuciya alhaji yayi sannan yace naji zan bayar, maganar lefe kuma jawwahir ai basai anyi ba ko?"" idanuwa jawwahir ta zaro sannn tace ai rashin lefe daidai yake da fasa auren nan, alhaji yace to naji zan baki 500k jawwahir tace haba sai kace wata zawara don Allah?"" ta ƙarasa maganar tana taɓe bakinta, Alhaji yace gaskiya haka zan bayar, yana maganar yana ɗaga murya,

kicin kissa jawwahir tace to naji bari ɓata ranka zan karɓa, taci gaba da cewa saura kuɗin kayan ɗaki, Alhaji yace gaskiya auren ba wani daɗewa zaiyi ba, kayan ɗaki nami kuma?"" tsaki jawwahir tayi sannan tace to barshi dani dakai dama waye ya damu da auren?""wallahi idan babu kayan ɗaki banayi kaga tafiyata idan ka shirya ka kirani, tana faɗin haka tayi gaba,

ganin da gaske take zata tafi yasa Alhaji yace jawwahir bata tsaya ba taci gaba da tafiya, yace haba kefa kina da matsala ki tsaya muyi magana mana, tsaywa jawwahir tayi ba tare data juyo ba, Alhaji matsowa yayi kusa da ita, yasha gabanta sannan yace yanxun ya kike so ayi ne?"""

jawwahir tace bani yanda kaji zaka iya kawai, Alhaji yace bari in ɗauko maki , jawwahir tace to idan kaje ka taho man da tsarabar dakayo man, shima baiyi magana ba, ya shige cikin gda, yana shigewa jawwahir tace sai kunci ubanku masu lallata tarbiyar yara, wato ni zakai auren mutu"a dani ko?"" hmm dani kake zance,

fitowa yayi daga gidan yaxo gabanta ya tsaya wani trolly bag ya bata yace ga tsaraba, ta ansa sannan tace kuɗin barsu ka turo man su kafin in isa gida, account number nata ta bashi, sannan tayi gaba...............,


Jawwahir kuwa tana zƴwa gida tace ma hajiya saurara inajin alart zan baki numbershi sauran bayanin saiya biyo daga baya..................
[1/17, 7:41 PM] Jamila Musa Ws: ☄
☄☄
☄☄☄
🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥
*WANDA BAIJI BARI BA*
🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥

☄☄
☄☄☄

*AMEENCI WRITER'S ASSOCIATION* 📚✍🏻

*MEELAT MUSA* 🌹

*PAGE 15*

****

*J*awwahir bata gama tunani ba, taji an fara dukan katangar ɗakin ta gam gam gam ƙatt ƙatt ƙatt, hawayen da suka taru a idonta suka zubo mata, hankalinta ya tashi sosai ganin ana rufasa wurin kuma kuɗin da ta samu tayi ginin nan bashi taciyo su har yanxun bata biya kuɗin ba, miyan bakimta dakel yake wucewa a maƙoshin ta, dan ji tayi kamar ma babu hanyar wucewarshi, bata sake kallon inda sadiq yake ba, ta wuce inda aka watso mata kayanta, wurin kayan sawarta ta nufa ta durƙusa, ta fara tsinatarsu tana kuka,

Sadiq da wutsiyar idonshi yake kallonta, yanda take ɗaukar kayan tana kakkaɓewa sadiq yaji ta bashi tausayi, amma dole ya dake ya haƙura, dan jawwahir sai an nuna mata jan ido zata gyara halinta,

Ɗaukar kayan take tana sawa a motar ta, duk abinda tasan zata buƙata a mota take sakawa, saida ta gama kwashe wa kakaf, sannan ta fita daga gidan,

Tana fitowa gidan wata dillayi taje, ta kirawota, tace taxo ta siyi kujeru da katifa da labulaye da tv, tace to , jawwahir tace Allah dai yasa kina da kuɗi a hannun ki?"" tace babu damuwa, haka suka rantafo sukayo gida,

Tunda jawwahir take a duniya tana iskanci yaune ranar farko data fara dana sanin rayuwarta, suna shigowa hannen dillayi tayi ma kuɗin jawwahir kuɗin, jawwahir tace ta siyar kawai ta bata, tace to,

Haka hanne tasa aka kwashe mata kayan aka kai mata gida, sannan ta bawa jawwahir kuɗinta,

Har yanxun jawwahir kuka take, duk tayi wata sukuku , sadiq duk inda tayi kallonta yake, dan ta bashi tausayi, ɗakin inna ta shiga, tana shiga sadiq ya bita, ita kuma wuƙarta ta ɗauko, tana juyowa ta buge da sadiq, kaucewa tayi, ba tare da tayi magana ba, zata fita daga ɗakin ya riƙo hannunta ya dawo da ita cikin ɗakin, saman gado ya zaunar da ita, sannan ya ɗago fuskarta , yace kiyi haƙuri, banyi haka dan in wulaƙanta ki ba, kiyi haƙuri kinji jawwahir?"" kallonshi tayi sannan tayi magana cikin kuka tace babu komai ya wuce, kayi haƙuri , sadiq yace to ina zakije yanxun?"" jawwahir tace mi ka gani ne?"" yace naga kin saka kaya a mota?"" dariya jawwahir tayi cikin kunar raina, abin ya mata zafi amma ta wayance, tace babu wani inda zanje kawai zanje in siyar da kayanne in biya mutane bashin su, sadiq yace nawa ake binki, jawwahir tace sai naje dai zanji, sadiq yace to faɗa man masu binki zan biya su, jawwahir tace to ngd , bara in dawo sai muyi lissafi, ta miƙe, sadiq sake riƙota yayi ya zaunar da ita,

Sannan yace hada wuƙar da zaki yanka ni da ita zaki siyar?"" kai kawai ta ɗaga mashi, yace to kada ki siyar ni zan siya nawa?"" jawwahir da ranta ke ƙuna kamar zuciyarta zata kama da wuta, dan duk maganar da take ma sadiq ƙarfin haline, yanxun ma daurewa tayi sannan tace idan kaine kake so ka ɗauka kyauta na baka, sadiq yace aini bana san kyauta gaskiya, jawwahir tace to ajiye idan na dawo sai muyi ciniki, sadiq yace tom, wuƙar ya ansa sannan ya mayar da ita inda take,

Ta miƙe da nufin fita, sadiq ya sake jawota, yace zauna bance kije ko ina ba, ina zuwa, jawwahir cije lemonta na sama tayi, ba tare da tayi magana ba, fita sadiq yayi cikin sauri yabar gidan, jawwahir tana ganin ya fita ta fito, inda tayi gini an rusa shi baki ɗaya, babu wata alamar an taɓa ajiye ɗaki a wurin, wani baƙin ciki ya sake turniƙe jawwahir,

wuri motar ta , ta nufa, biro da paper ta ɗauka ta fara rubutu kamar haka,

```na gode sosai da irin karamci da kukai man , dan idan baku ba babu wanda zai iya zama dani, kace ma babas da innasco ina godiya sosai dan gaskiya sunyi namijin haƙuri wurin jawwahir, mamana da babana suma ina masu fatan alkairi, gidanku babu wanda zaisa gini saikai ɗan gidan na gode sosai, kuyi haƙuri insha Allah daga yau baza ku sake gani na ba, bare in ɓata maku rai, kuma kada kusha wahalar nemana dan na riga nayi nisa, nima zanje in nemo iyayena, ngd jawwahir babana da mamana, zuwa

10 / 28