Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

WANDA BAIJI BARI BA Rayuwar Ƙarya da Nadama by MEELAT MUSA

Author :  MEELAT MUSA Category :  African Stories & Novels

Chapter   15 / 28

42K to 45K   out of 83K words

ne?"",,,,,,,,,

kuka jawahir ta fara, juyawa yayi ya kalleta sannan yace muje, tace wallahi na gaji duk jikina ciwo yake man, yace kinje kinci zalin wani yayi maki duka ko?"",,,,, ni babu wani ruwana da ciwon jikin ki muje, bata sake magana ba, kuma bata ja motar ba, a fusace ya juyo yakai mata wani mari sannan yace idan kika bari na sake magana saina tillaki waje motar ta takaki,

Goge hawayen fuskarta tayi sannan taja motar cikin zafin rai, yace Oho dai saikin kaita, idan ma mutuwa ne tare zamu mu mutu, ita dai kuka kawai takeyi, yace idan kin samu wani wuri ki tsaya muyi sallah, batace komai ba, yace dake nake magana, cikin sanyi tace to,

A ranta kuma tace bazan tsaya ba munafiki azzalimi, haka taci gaba da sharara gudu saman kwalta, ,,,,,,, har Allah yasa suka iso lafiya,

to suna shigowa cikin unguwarsu honey j ta fara gani, a ranta tace Allah sarki, haka tana ta kallon unguwa tare dajin wani farin ciki a ranta, lokacin da suka iso ƙofar gida sadq ya fita ya buɗe get, ta sulala da motar, innas da bacci ya fara ɗauka da sauri ta fito daga ɗaki , sadiq bayan ya rufe get ɗin yayi wurinta,

jawahie tsaki tayi har yanxun tana cikin motar, tace aikin banza ashe dai babu abinda ya canza, haka ake har yanxun get ɗinma tun wanda na saka ne, lallai nima zan siyo tawa motar sai kasan inda zaka ajiye taka, hawaye suka zubo daga idonta dan tuna abinda sadiq yace mata,

anan gidan babana ne, nine nike da ikon yin gini bake ba, kije can gidanku, buɗe motar da akayi ne yasa ta dawo daga duniyar tunani, sadiq ne yace ke kuma mi kike baza ki fito ba,

Cikin kuka jawahir tace gidan babana nake so a faɗa man in tafi, inna tace wace irin magana ce wannan?"",,,,, cikin tsiwa jawahir tace ba maganarki bace, fizgota daga cikin motar sadiq yayi tare da harbinta, ta tafi tangal tangal, inda take ya nufa, ya cakumota yace waye ba magansrshi ba?"",,,,,,

Murmushi takaici jawahir tayi sannan tace na manta fa an taɓo maka mama, inda inna take ta kalla tace kiyi haƙuri , kaima Allah ya baka haƙuri ɗan masu gida, babane ya fito daga ɗaki da sauri jin maganar jawahir, yana cewa jawahir kece, hannu ta ɗaga mashi tare da cewa ga wanda ya kamata kace shine bani ba, cikin zafin rai sadiq ya isa inda take tace idan ka taɓani saina nakasa maka rayuwa, idanuwa sadiq ya zaro tare da cewa nine zaki nakasawa rayuwa?"",,,,,, niko nace dan taga mutane,

dake nake, nace nine zaki nakasa wa rayuwa?"",,,,, kusa da ita ya matsa yana cewa to nakasani, nace ki nakasa ni mana, baba yace sadiq barta, jawahir tace dama ana da yanda za,ayi da nine?"",,, kawai baƙin ciki yasa anje an dawi dani, towai dole saina zauna ne?"",,,,,,, gidan ubana zan tafi, baba yace wace irin magana ce wannan?"",,,, waye baban naki bayan ni?"",,,,,, murguɗa baki jawahir tayi sannan tace ni bakaine babana ba, ai sadiq yasan inda gidanmu yake tunda shine ya faɗa, sadiq yace waike wa kike ma rashin kunya?"",,,,, tace dakai nake dan kaine daidaini, abunma dariya ya bashi yana kallon jawahir, yace to muje ɗaki saiki faɗa man haka, tace baza,a shiga ɗakin ba anan za,ayi, yace to muje waje sai ki faɗa man, kamo hannunta yayi ta fizge, yace kixo muje mana tunda kin kawo ƙarfi,

Inna tace ya kyaleta, jawahir tace kada ma a barni mana, dan kinsan duka zanmai shi yasa kikace ya barni, baba ɗaki ya tafi itama inna tabi bayan mijinta, tsakar gida ya rage daga jawahir sai sadiq, suna shiga ɗaki ya matsa kusa da ita, yace nine zaki nakasa ma rayuwa?"",,,,,, faɗa maɓ mi zaki man wanda zaisa in nakasa, jawahir tayi shiru yace dake nake, tayi shiru, yace wato so kike in dakeki ko?"",,,,, kuka jawahir ta fara, tana kallon ƙofar ɗakin baba, hannunta ya riƙe , ta toge, yace wuce muje, ta cije, yace zaki wuce kosai na.....bai kara maganar ba tabishi suka tafi ɗaki,

sjna shiga ya kunna fitilar ɗakin har yanxun yana riƙe da hannunta, hijabin jikinta ya cire mata, sannan ya zauna, itama ya zaunar da ita, kallonta yayi ta ɗauke kanta, hannunshi yasa ya juyo da fuskarta tana fuskantar shi, sannan yace wai nine zaki nakasa?"",,,, waye ya koya maki haka ?"",,,,,,, shiru tayi yace gidanku kike so?"",,,,, kai ta ɗaga mashi alamar E, yace to kiyi haƙuri insha Allah nine zan kaiki dama ai nine na kawoki, kuma zan mayar dake a inda na ɗauko ki, kin yadda?"",,, tace E, yace bazaki sake gani na ba, kin yadda tace E, murmushi yayi saboda bazata gane karatun ba,

Miƙewa yayi zai fita daga ɗakin tabi bayanshi da kallo, tana tsine mashi a ranta, tare da mashi addu,ar mutuwa kowa ya huta, shi kuma yana fita wurin mota yaje ya ɗauki abinda zai ɗauka sannan ya fice daga gidan,

Ita kuma yana fita , ta kwanta, sai ƙarewa ɗakin kallo take saidai tayi tsaki , har bacci ya ɗauketa, shi kuma sadiq yana zuwa gida wanka yayi, bayan ya gama ne, yasa wata baƙar jallabiya, ya kwanta, tunanin jawahir yake wai zata nakasa shi, wannan wace irin kalma ce,?"",,,, tsaki sannan yace kai gaskiya yarinyan nan mahaukaciya ce, tsaki ya sakeyi tare da kauda babinta a ranshi,

***

*S*adiq daga masallaci gidan su inna yayo, shima baba ya dawo daga masallaci suka gaisa, baba yace sadiq lafiya?"",,,,,na ganka gida haka?"",,,,, sadiq yace baba don Allah idan bazaka damu ba, yarinyar nan tunda baka bari a hakunta ta, to kuyi haƙuri a maida ta gidansu, inna dake ɗaki ta gama sallah ta fito, tace ka rufa man asiri idan har muka mayar da jawahir da wannan halin tsakani da Allah kowa sai yayi turr da halinmu, sadiq yace to inna nidai kinga ba zama nake ba, baba yace kudai kuyi mata addu",a ƙuruciya kowa da irin tashi, sadiq yace to yanxun abinda za,a ku barta zan ɗauketa in kaita kauyen yau, zance mata tayi kwana goma zanzo in ɗaukefa, inna tace to shikenan,

Tashi yayi ya nufi ɗakin inna, jawahir sai bacci take, tana jan rago kanajin yanda take baccin kasan tanajin daɗin shi, wani irin duka yakai mata wanda yasa ta miƙe firgigi tana rarume rarume, hararta yayi tsaki tayi ganin sadiq, yace wa kike zagi?"",,,,, tace ni ba zaginka nayi ba, yace sakara tashi kije kiyi sallah, turo baki tayi sannan tace ban sallah, kallonta yayi sosai sannan yace mi kika ce?"",,,,,, sai yanxun ta gane sadiq ne ma ba inna ba, da sauri ta sauko ta fita, tsaki yayi sannan ya kwanta saman gadon,

ita kuma tana fita tace Allah ya isa, ina baccina zaka wani tasheni inyi sallah, haka tayi ta gunguni har tayo alwallah taxo tayi sallah, bayan ta gama tace ina kwana, ?"",,,,, yanda tayi ina kwanar irin ta anshi karka rasa ne, bai ansa ba, ganin ya kwanta saman gadon yasa ta koma saman kujera tana kwanciya yace tashi munafika kiyi addu,a Allah ya rabaki da wannan baƙin halin,

tace ai nayi yace ni banji ba, to abinda nayi tsakani na da ubangijina sai kaji, yace dan inji idan da gaske kin faɗa ne, yace idan naji miye?"",,,, kinga nima sai in taimaka maki da addu",a, dama inayi, batayi magana ba, tayi kwanciyarta saman kujera,

harta kwanta yace zo , tashi tayi taje kusa dashi shima tashi yayi zaune sannan yace kije kiyi wanka, mu tafi, tace ina?"",,,,,,,,, yace kauye, tace ai basai nayi wanka ba, yace haka zaki tafi? "" tace E, yace to muje, jawahir tace tun yanxun?"",,,, yace yo sai yaushe?"",,,, tace nidai sai anjima yace ƙarya kike wallahi yanxun zamu tafi, innasco?"" ta fara cewa zata fita ɗakin ya riƙota yace wallahi sai anje yanxun zamu tafi, ya miƙe tsaye jawahir ta fara kuka ita bata zuwa, taci gaba da kiran innas,

ina ta fito daga ɗakin baba, tana cewa lafiya?"",,,, jawahir sai so take ta tafi wurinta amma sadiq ya riƙe mata hannu, inna tace miye?"",,,, jawahir tace kinga zai kaini kauye, kiyi mashi magana wallahi , inna tace sadiq ka kyaleta, sadiq yace babu ruwanki inna barta dani take zancen, ganin inna batace komai ba, yasa jawahir ta fara kiran babs baba daga ɗaki yace miye?"",,,, tace kayi ma sadiq magana , wai kauye zai kaini, baba yace abubakar, sadiq yace na"am, yace ka barta mana, sadiq yace baba ƙarya take cewa tayi muje mi dawo, dan haka zamu dawo anjima,

Ganin babu wanda ya ɗauki mataki yasa jawahir haƙura, sadiq yace ta shiga suje, bata da yanda zatayi ta shiga kuma itace zataja motar, tanaji tana gani taja motar suka bar gidan, kuka ta farayi amma sadiq ya kanne, haka suka hau titi suka ibi hanyar kauye garinsu kare,...............,,,,
[1/17, 7:44 PM] Jamila Musa Ws: ☄
☄☄
☄☄☄
🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥
*WANDA BAIJI BARI BA*
🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥

☄☄
☄☄☄

*AMEENCI WRITER"S ASSOCIATION* 📚✍🏻

*MEELAT MUSA* 🌹

*PAGE 21*

***

*H*ar suka isa babu wanda ya sake magana, saidai shi da ake yawan kiranshi a waya, jawahir sai tsine mashi take tana Allah ya isa, niko nace ba kece kika jawa kanki, ba kince gidanku ba?"",,,, to kije idan zaman kauye riba ne,

Lokacin da suka isa kauyen daidai ƙofar gidansu jawahir sadiq yasa tayi parking, bayan ta gama parking ne, yace Alhamudulillah munxo, jawahir tace to, yace muje, kafin ta fita ta miƙa mashi makulin motarshi, yace ta riƙe zai ansa, su jawahir aka fito jiki a sanyaye ta ƙarewa gidan da aka kira da sunan gidansu , wato wata ƙaramar katanga ce, wanda ko akuya saita tsallaketa, kuma ƙofar gidan babu kyaure, wasu tumakine suka fito da gudu daga cikin gidan wata ƙanwar jawahir wadda suka baba ɗaya ta biyosu a guje, da sauri ta matsa gefe ɗaya sannan tace toupha, kallon sadiq tayi shi kuma ya tsuke fuska, yace muje,

Tace kaine zakaje ai, yace to gaba yayi jawahir tana biye dashi, wata matace ta gani da ɗaurin zani iya ƙugu babu brezia babu riga, an saki gaba a balgazance ana tafiya, girgiza kai jawahir tayi sannan ta sake kai dubanta ga sadiq ya basar sai dariya yake cikin ranshi, dan duk abinda yasan zaiyi ma jawahir taji haushi shine yake mata, waiko zata canja amma kullum kamar ƙara zuga ta akeyi,

Haka sukayi ta wuce mutane, da yake gidan ƙaton gidane kowa da shiyyarshi, har suka isa wurin su jawahir, baban jawahir ne ya fito da wasu buhunna a hannunshi , yana ganin sadiq ya faɗaɗa murmushin shi, yana masu sannu da zuwa, tare da cewa larba kawo tabarma ga baƙi daga birni, wanda aka kira da larbe tace to gamu nan maraba marabanku, a daidai lokacin da take fitowa da tabarma a hannunta ta shinfiɗa, sadiq ne ya cire takalminshi ya hau sama ya zauna, amma jawahir ta gefen sadiq tace ta tsugunna kusa dashi, kamar zata shiga mashi cikin ciki, gaisuwa aka fara baban jawahir yana tambayar sadiq ya ƙasashen waje?"",,, yace Alhamdulillah , baba yace ance ka samu aiki Allah ya tsare sadiq yace amin, sai yanxun jawahir tayi magana cikin kuka tace ina kwana, baba yace lafiya qalau ya karatu?"",,,,,,jawahir tayi shiru, sai sadiq ne yace karatu lafiya qalau ko?"" ya kalleta yana murmushi, kana ganin abun kasan da gayya yake yi, baba yace larba kawo masu fura, tace to , tashi tayi ta koma ɗaki ta ɗauko kwaryar fura, ta kawo , a gaban sadiq ta ajiye, ya buɗe furar yasha lude ɗaya, sannan yace ma jawahir taxo tasha tace ta ƙoshi,

Dariya yayi sannan yace haba keko kixo kisha mana, akwai daɗi, da tana ganewa da bata sha ba, kusa da kwaryar furar ta matsa, ta ciko lude takai bakinta hancin ya juyo mata tsami, tana kaiwa bakinta da sauri ta ajiye lude, tana ɓata fuska, sadiq yace miye?"",,,,,, bakinta ta taɓe bata sake magana ba, har sadiq ya gama ya miƙe, kuɗi masu yawa ya bawa baba shiko baba sai godiya yake ita kuma jawahir kyautar kuɗin ya bata mamakiyos wannan kuɗin ina sadiq ya samu?"",,,, niko nace kina can yawo sadiq ya kuɗance, kodan kinga gidan su innas ba gyara,

inda take tsugunne sadiq ya kama hannu ta, ta miƙe yace suje,,,, tayi mashi rakiya kayanta yana a mota ta ɗauko, baba yace nan zata kwana ne?"",,,,,,, sadiq yace Eh zata zauna nan zanyi tafiya ne, idan na dawo zanzo in ɗauketa, matsa man tayi sai na kawo ta gda, jawahir data matse fura a bakinta saidai ta kalli wancan da ido ta kalli wannan,

haka sadiq yaja hannun jawahir har wurin mota, suna fita ta zubar da furar ta fara amai, sadiq ko dariya yake dariyar da tunda jawahir take bata taɓa ganin yayi irin ta ba, saida ta gama aman sannan ya bata ruwa ta wanke bakinta, sai dariya yake mata, jawahir tana gama tace bani kayan nawa, ka sauko man su duka, yace A, a, kiyi haƙuri goma zan baki ya ƙarasa maganar tare da ɗaga mata gira, but ya buɗe ya ciro mata kaya da kanshi sannan ya miƙa mata, juyawa tayi zata koma gida, yace zo, bata juyo ba, taci gaba da tafiya, sadiq yace bakiji ina magana?"",,,,,,,, banza tayi mashi, dariya yayi sannan yabi bayanta,

ita kuma lokacin takai cikin gda harta zauna saman tabarma, kusa da ita ta zauna sannan yasa hannunshi a aljihu ya ciro kuɗi yace anshi, jawahir cikin kuka tace bana so, yace yi haƙuri ki ansa kinji , jawahir tace bana so, saman jikinta ya ajiye mata, kuɗin ta ɗauka da sauri ta saka mashi a cikin aljihun gaban rigarshi , sannan tace da in kashe kuɗinka gara yunwa ta kasheni,

Sadiq yace ji nan, bana so kixo shima baba kina sayar mashi awaki kamar yanda kika siyar dana inna, jawahir cikin masifa tace idan na siyar na babanka ne?"",,,,,, wani mahaukin mari yakai mata , sannan yace nine zakice na babana ne?"",,,, kada Allah yasa ki ansa, dan kinga ana lallaɓaki zaki rainawa mutane hankali?"",,,,, tsaki yayi sannan ya miƙe yabar gidan,

yana fita jawahir ta kwanta saman tabarma tayi ta kuka tana harbe harbe, shi kuma yana fita yaja motarshi yabar ƙofar gidan da ƙura,

Tuƙi yake amma hankalinsa yana wurin jawahir sai yanxun yaji dama bai barta ba, wata zuciyar tace koma ka ɗaukota, wata zuciyar tace barta kafin ka dawo tayi laushi, dan matar babansu jawahir "yar bala"i ce bata da imani ko ɗaya a ranta, itace take dukan jawahir lokacin tana ƙarama kuma ta gama da babansu jawahir, tsaki yayi yana ɗauki wayarsa dake ringing,

yana fita ita kuma da gudu ta fito daga gidan ganin sadiq ya tafi da gaske yasa ta fasa wata irin ƙara wanda duk mutanen dake gidan saida sukayo kanta suna tambayar lafiya?"""",,,,,, kuka jawahir take tana turjewa ƙasa, wai ita za,a rainawa wayau tayi rayuwar kauye sai kace wata akuya?"""",,,,,,

larba ce ta fito daga ɗaki cikin masifa ke kiyi ma mutane shiru nan ne gidan ubanki kuma anan zakiyi rayuwa shegiya, kike wani yage ma mutane baki toni nan ko ƙaramin yaro baya mana kuka bareke ƙatuwa aure bana aihuwa baɗi,

kunsan rashin kunyar jawahir cikin masifa tace anje anyi idan kinji haushi ki rufe man baki ta ƙarasa maganar da murguɗa baki, ai bata gama rufe bakin ba, jawahir taji ruwan duka da icce, saida larba tayi mata lilis sannan tace bake ba ni ko ubanki bai isa ya faɗa man haka ba,

kuma ki sani a gdan nan idan na shata layi ubanki ma bai isa ya tsalka ba, dan haka ki ajiye wannan birni idan ba haka ba, ni nan nice ajalinki , idanuwa jawahir ta zaro tana kallon larbe , tace kalleni da kyau nice nan na gagari ubanki uwarki ma data matsa nice na tura banza duniyar mutuwa, kema idan kika zo da hauka zan turaki ki isketa, jawahir taga inda akafita masifa da bala"i don haka ta koma gefe ɗaya ta durƙusa, taci gaba da kuka,

Wata ƙatuwar tulu larbe ta ɗauko tace wa jawahir taje maza maza ta kawo mata ruwa, babu gardama ko rashin kunya ta ɗauki tulun ta fita daga gidan ba tare da sanin ina zataje ba, tana fitowa daga cikin gdan taga wata mata , tana ganin ta ta rungumeta, ita jawahir bata san ko wace ce, ba, matar tace jawahir, kallonta jawahir tayi sannan tace ina kwana?""",,,,, cikin girmamawa,

matar ta ansa, sannan tace yaushe kika zo?"" jawahir ta fashe da kuka sannan tace mata yau naxo, matar tace mi kika zo yi?""",,,,,,,, jawahir tace hutu naxo, matar tace miya kawoki?""",,,,, jikin jawahir ya fara karma tace tsotsayi ya kawoni, tace ina zakije?"",,,, tace ruwa zan ibo, matar tace muje in rakaki,

suna tafiya matar ta fara bata labarin larbe, ai wannan matar sai kinyi hankali dan larbe bata da gaurayen imani, jawahir cikin rawar baki tace mi tayi ne?"""",,,,,, matar tace kidai ki yaye kuma ki guji cin abincinta, jawahir tace idan banci ba a ina zanci ne?""",,,,,,, matar tace to bara kiji kaɗan daga cikin aiki larba,

Wani aurene babanku yayi, matar ta haifi yaro namiji larba ta tada masifa da tashin hankali tunda ita bata taɓa aihuwar namiji ba, haka ta hura wuta saida aka saki matar nan sannan kuma tace yaron nan saidai itace zata riƙe shi,,,,

Haka babanki ya anshi yaron nan ya bawa larba yana nan zaune wurin larba, ranar nan in faɗa maki jawahir kawai taje ta samo kinsan kulɓa?""",,,, jawahir tace miye kulɓa?"",,,,, matar tace wani abune shine yake haifar maciji, zakiga jikinshi kalala ne, to shi ta samo in faɗa maki tayi ferfesu dashi, takai ɗaki ta ajiye,

to wata ɗiyarta tana dawowa ta shiga ɗaki taga ferfesu kawai ta ɗauka ta cinye, bayan Ashiru ya dawo daga kiwo tace yaje ɗakin ta wuri kaza ya ɗauko nama yana nan ta ajiye mashi, kuma kada ya bari maryamu ta gani, saboda itace take sa,a ɗaya da ashiru,

Yace to haka ya tafi ɗaki ya duba bai gani ba, ya ƙara dubawa bai gani ba, yace ban gani ba, tashi tayi a masifa ta nufi ɗaki, ta duba bata gani ba, ta fito tana kiran maryamu tana zuwa tace kinga nama a ɗaki?"",,,, maryamu tace nacinye,,,, sai larba ta

15 / 28