Author : MEELAT MUSA Category : African Stories & Novels
ta buɗe ta, taga babu ko sisi a ciki, dan haka tashi tayi da zumar tafiya ɗakin baba taje ta ibo gero ta siyar dan ta samu kuɗin abin hawa, saboda yau akwai inda zataje takai takardun gida na boge ta samo kuɗi,
A hanzarce ta shiga ɗakin baba ta zubo gero cikin buhu tiya ukku, tayo waje , geron ta ajiye a ƙofar ɗakin baba ta nufi ɗakin inna dan ɗauko hijabinta, tana ɗauko hijabi tayo waje ta ɗauki buhun data zuba geron, ta nufi hanyar fita,
a zaure suka haɗu da sadiq, kallo yabita dashi sannan yace mata ina zaki?"" cikin in"ina tace surfe zata kai, tana magana tana sinne kai ƙasa kamar munafika, yace wuce ki maida kada akai surfen , tace ai idan innas ta dawo zatai faɗa ne, yace ke har tsoron faɗan wani kike?"" tsawa ya daka mata yace kije ki mayar nace,
jiki babu daɗi jawwahir ta taho tana gunani ƙasa ƙasa take magana tana cewa Allah ya isa munafiki, kuma insha Allah ma baza a samo maka aikin ba, shidai baiji abinda take cewa ba, har ta shige ɗakin baba, tana shiga ta maida geron inda ta ibo shi, sannan ta fito,
yace ina kuɗin cefanen da aka baki ne?"" jawwahir tace ni ba"a bani kuɗi ba, yace ƙarya inna take maki ne??"" jawwahir tace wai kuɗin innas?"" ai bsni tayi inyi break, sadiq yace nawane kuɗin?"" tace idan ban manta ba ni ko 500??"" yace dan kin ɗauki mutane "yan iska kece zaki cinye ɗari biyar kaff a cikin ki?"" jawwahir tace ai ba roƙonta nayi ba itace ta bani, yace zakici gidanku kau, a baki kuɗin kiyi girki dan baki da kunya kije ki kashe su?"""
jawwahir tace to aini bansan cewa aikai inyi girki ba, caff inji sadiq sannan yaci gaba da cewa to idan suka dawo su miye zasu ci?"" jawwahir tayi shiru yace dake nake magana, shiru tayi, kanshi ya ɗaga sama yana tunanin irin azabar da zaiyi ma jawwahir wato yarinyar nan dai kullum kwatanci da nuniya ake amma kamar ana ƙara zugata,
Sauko kanshi yayi sannan ya kalli inda take tsaye ,girgiza kanshi yayi sannan yace wuce muje ɗaki, jawwahir tayi tsaye yace dake nake magana, tace ban zuwa ɗaki ni, yace wuce muje da ƙarfi yayi maganar kamar maƙoshin shi zai fito waje, jawwahir ta wuce simisimi, yabi bayanta, suna shiga yace ta kama kyauren ɗaki da hannunta ta riƙe sannan ta ɗage ƙafafuwan ta sama, jawwahir ta ɗauka hakan sauƙi ne, dan haka tayi yanda sadiq yace tayi kallonta yayi sannan yace idan ta kuskura wallahi ta sauke ƙafarta ƙasa jikinta zai jiye mata babu daɗi, tana maƙalewa shi kuma ya koma saman gado ya kwanta yana kallonta, dan ita baya ta bada bata iya ganin abinda yake bayanta shi kuma yana kallon bayanta amma baya iya ganin fuskarta ,
Bayan ya kwanta yace yau anan zaki yini tunda bakijin magana, ni na gaji da dukanka amma idan kika sha wahala ko bana nan idan ance ki daina abinda kike zaki riƙa kiyayewa,
lallai ashe abun ba sauƙi bane fitar haƙori jawwahir tun tanayi na marmari taji hannunta ya fara sagewa, cikin siwa tace yi haƙuri yace bazanyi ba, jawwwahir tace wallahi zan sauko, yace sauko wani yace kada ki sauko ne?"" cikin hayani da hauka jawwahir tace haba sadiq wannan zalinci ne, yace ke kika zalinci wasu?"" wasa sabon fari jawwahir fa ta farajin bala"i, ta fara kuka shi kuma dariya kawai yake daga kwance, jin hannunta zai kare yasa ta saki kyauren ta sauko, da sauri ya miƙe ya matsa inda tayi ya wanwanka mata mari saidai yayi mata dukan da ta kusa amai sannan yace ta tashi ta koma kuma idan ta sake saukowa abinda zai mata sai yafi wannan, jikin jawwahir sai ƙarma yake saboda azaba, da sauri ta kama ta sake maƙalewa, yace ni kuɗin abinci na kawai zan daka idan inna ta dawo ita kuma sai ki faɗa mata inda kikai nasu ita da baba,
kuka jawwahir take sosai saboda wannan abun da sadiw yasata akwai azaba, haɗashi take da Allah tana kuka ga majina ta fara fito mata saboda azaba, sadiq yace ta rufe mashi baki idan ya sake jin maganarta sai ya sakata cikin rijiya, jawwahir tace wallahi banyi shirun sai kayi ta cin zalin ɗina kuma ka hanani inyi kuka, wayyo Allah tace da ƙarfi wallahi bazan yafe ba, yace aini bansan ki yafe man, kema mutum nawa kika cuta wanda basu yafe maki,??""
sadiq wayarshi ya fiddo ya kira wani abokinshi sannan ya faɗa mashi abinda yake buƙatar a kawo mashi, wanda jawwahir zatayi girki, yace to, bayan ya gama wayar ne, yace mata mi akace ki dafa ne?"" tace tuwo kuma ni bazanyi tuwo ba, yace sai kinyi wallahi kuma idan kika gama sai kinci shi, jawwahir tace nashi 3, yace wallahi ki rufe man baki, sai kuka take amma a ranta tsine ma sadiq take,
jawwahir na maƙale saman kyaure har yaron da aka aiko ya kawo cefanen sadiq ya fita ya anso, bayan yaron ya tafine, yace taje tayi wanka taxo ta ɗora sanwar , jawwahir da sauri ta sauko, yace munafika yau banda zaki abincin nan wallahi niyata sai na sumar dake sannan inbar gidan nan,
ita dai batayi magana ba ta wuce taje tayo wanka bayan ta gama, ta dawo ta shirya, sannan ta fita dan ɗora sanwa, zokaga jawwahir a kicin duk ta tashi hankali sai kace tana dafa duniya, tabi ta haukata kicin ɗin ta ƙazantar da ko ina, ga hayaƙi ya isheta, sai hawayen wahala ke fita daga idon ta, haka dai ta jagwalgwala tuwon ta gama, sadiq yace ta tattara duk kayan data tasan ta ɓata ta wanke, tace to, saida ta wanke komai sannan yace ta share gidan, haka ta share gidan, sannan yace taje ta zubo tuwon taci,
tace ai batajin yunwa, yace ai dama yafi daɗin shiga idan ba"a ra"ayin shi, jawwahir tace wanka zatayi yace aje ayi wanka,
tana shige bayi tayi zamanta, tace ɗan iska ka gaji da zaman jirana kayi tafiyar ka, sadiq daya gaji da jiran jawwahir bata fito ba, ɗaki ya shiga ya kwanta, bai daɗe da kwanciya ba bacci ya ɗauke shi,
Ita kuma tanajin shiru ta ɗauka ya tafi, saboda haka tana fitowa wanka da gudu ta shigo ɗaki, tana zuwa ta ganshi, shi kuma yanda ta shigo a ɗakin ne ya tashe shi, tsaki yayi sannan ya gyara kwanciyarshi dan bacci yake ji sosai, saboda jiya baiyi bacci ba, a gaggauce jawwahir ta shirya tana gama shirinta ta fice daga gidan,
tana fita da gudu ta isa bakin titi tana tafiya tana juyowa kada sadiq ya biyo ta, tana zuwa napep tahau , tana jiga tayi ajiyar zuciya tace nida dawowa gidan nan saina huta, gobe sai inga ubanda zaka daka munafikin Allah,
Jawwahir gidansu hafsat ta nufa, data gaya mata zata kwana hafsa taji daɗi sosai, dan ita Allah yana haɗa jawwahir da ƙawaye masu santa tsakani da Allah,
Sadiq bai farka bacci ba harsai da inna ta dawo ta tashe shi, tace miyaja mashi baccin bayan magrib?"" gashi har an fara kiran isha"i, salati sadiq yayi dan ganin dare yayi, inna tace mashi ina jawwahir?"" yace wallahi bacci yake baisan inda ta tafi ba?" salati inna tayi sannsn tace ka rufa man asiri ka nemota hadiza zata zo kada tazo ta samu bata nan aje ayi ta balbaɗani a dangi, dama duk halin jawwahir mutane sun fara sani sai cewa ake na lalata ma yarinya tarbiyya kuma wallahi nidai Allah ya sani tsakank da Allah naƙe riƙe da ita, .
ran sadiq ya ɓaci ganin halin da mahaifiyarshi take ciki, dan inna kuka take, yace kiyi haƙuri inna zata dawo, ni banda number wayarta kuma ba lallai bane idan na kira ta ɗauka, inna tace innalillahi ina zan saka kaina ni *Hauwa"u* sadiq yayi ta bawa inna haƙuri, daƙel ya samu ta haƙura sanann ya fita yabar gidan,
sadiq yana fita yace itama inna ta maida masu ɗiyarsu ta huta wannan yarinya ai sai ta kashe mutum, cikin unguwa ya shiga ya samu number ja"afar ya kirashi yace ya taimaka ya turo mashi number jawwahir, yace to, bayan sun gama wayar ya tura mashi, a daren duk kiran da sadiq yayi ma jawwahir bata ɗauki waya ba, haka ya haƙura,
*****
Da safe bayan sadiq ya dawo masallaci, ya fara kiran jawwahir amma bata ɗauka ba, ita kuma jawwahir tana can tana wanka, batama san ana kiranta ba, haka dai ya gaji da kira ya haƙura,
Gida yaxo ya gaya ma inna, jawwahir bata ɗauki waya ba, inna tace to saidai tayi sauri ta koma kauyen, dan inna bata faɗa ma baba ba, cewar jawwahir bata kwana gida ba, inna haka ta sake ɗingima tayi kauye,
ganinta yasa hadiza tace da zanje amma tunda kinzo bari kawai inyi tafiyata wani lokancin na sake dawowa zanzo, inna taji daɗin haka sosai,
****
satin jawwahir ɗaya rabonta da gida, ana can makaranta an fara rubuta exam, itako hafsa tana jin daɗin zama da hafsa, jawwahir kuwa hankalinta kwance , kuma tayi alƙawarin baza ta dawo gida ba sai taji sadiq yabar ƙasa saboda akwai wani couse da zaije *brazil* tayi alƙwarin bata sake yadda su haɗu, tun baba bai gane jawwahir bafa nan ba har ya gane, saboda haka shidai addu"ar shiriya kawai yake mata,
***
Satin jawwahir biyu a gidansu hafsa hankalin ta kwance bata fuskatar wata matsala , ranar nan suna waya da *honey j*yace mata sadiq yayi tafiya, yau satinshi ɗaya, jawwahir taji daɗi sosai saboda haka tace insha Allah gobe zata dawo gda dan taji daɗin tsula tsiyarta,
Da safe zasu tafi sch ta faɗa ma maman su hafsa zataje gida mamansu hafsa dai taji babu daɗi tace ta bari babansu hafsa ya dawo sai suje tare jawwahir tace ba komai dama wani yayanta ne ya matsa mata kuma yanxun baya nan amma idan yawo zata dawo, mama tace,
A sch bayan sun fito paper ne jawwahir tace ma hafsa idan na buƙaci motar na zan maki magana sai ki taho maɓ da ita a sch, hafsa tace babu damuwa, jawwahir napep tahau tayo gida, itama hafsa gida ta nufa,
Jawwahir tana zuwa gida inna ta samu a tsakar gida tana aiki, batayi mata magana ba, ta raɓa ta , ta shige ɗaki, inna tabi jawwahir ta sameta a ɗakin tana cire sch uniform inta, tace jawwahir ina kika je sati biyu da kwana ɗaya?"" jawwahir tace haba ina gidan su hafsa fa, inna ta zauna ta fara ma jawwahir nasiha, tana kwatanta mata amma duk inda inna ta ɓullo sai jawwahir ta dakushe maganar, inna tace ki rufa ma kanki asiri ki daina abinda kike wannan rayuwar ba rayuwar kirki bace, jawwahir tace to,
koda baba ya dawo shima nasiha yayi ma jawwahir amma duk a banza,
****
Satinta ɗaya da dawowa gida, wata ranar alhamis da rana inna tana zaune a tsakar gida taga mutane sun shigo ga jawwahir a bayansu , tana nuna masu inda za"a fasa a saka get, inna tace jawwahir mi zakiyi ne?"" jawwahir tace gidan gayu za"mayar da gidan, inna tace wato ana cewa ki bari bakya bari dai ko,?"" hannu jawwahir ta ɗaga ma inna tace idan baki iya gani don Allah ki fita kibar gida, inna tayi shiru sai yanxun takejin haushin tafiyar sadiq dan daya nan duk wannan iskanci jawwahir baza tayi ba,
Haka akaci gaba da aiki get mai kyau da tsada aka saka gidan su inna , kuma haka jawwahir tasa aka saka ma gidan interlock , tayi ma gidan kwaskwarima, tace idan ta huta zata sake kayan ɗakin inna, kuma babu wurin wanda zataje tayo *4 1 9* sai wurin Alhaji don haka ita kaɗai tasan tarkon data ɗaura mashi,
Bayan sati biyu da gyara ne jawwahir ta anso motarta da alhaji ya bata, tazo ta ajiye a gidansu,
Hmmm idan dai mutun baiji bari ba, tofa bazai ƙijin hoho ba,
[1/17, 7:37 PM] Jamila Musa Ws: ☄
☄☄
☄☄☄
🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥
*WANDA BAIJI BARI BA*
🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥
☄
☄☄
☄☄☄
*AMEENCI WRITER'S ASSOCIATION* 📚✍🏻
*MEELAT MUSA* 🌹
*PAGE* 12
****
*Y*anxun jawwahir duk inda za"a da motar ake tafiya, wallahi idan ka ganta sai ta burge ka, burinta ya cika hankalinta ya dawo wuri ɗaya, yanxun abinda ya rage mata so take ta gama rubuta ssce exam sannan ta samu aiki office ɗin Alhaji ta rama abinda ya faɗa ma sadiq alhalinma alhaji da idonshi bai taɓa ganin sadiq ba, kuma bai taɓa magana dashi ba,
*W*ayar inna ce take ta kururuwa a ɗaki ita ɗaya tana neman mai bata agaji ita kuma inna tana bayi tana wanka , jawwahir dake tsakar gida tayi saki tace ayi ta kiran mutane mai kiran ma ko zuciya baya dashi, ɗakin ta shiga ta ɗauki wayar , ganin number babu suna ne yasa ta ɗauka,
Sallama akayi daga ɗayan ɓangaren, jawwahir gabanta taji ya faɗi duk inda taji wannan muryar baza ta taɓa mantata ba, a lokacin da ya sake cewa hello, jawwahir tace waye, jin muryar jawwahir yace mahaukaci yaushe kika dawo?"" jawwahir tace kaine mahaukaci, dariya sadiq yayi sannan yace idan ba tsoro ba ki bari in dawo ki faɗa a gabana, tsaki jawwahir tayi sannan ta murguɗa bakinta kamar tana ganin shi sannan tace haba ai kan mage ya waye, yanxun saidai in baka wahala, sadiq yace ba na hanaki kiyiman tsaki ba, hmm ina nan zuwa zaki gane kurenki, jawwahir tace to daga gane kurena sai mi?"" yace hmm zan kamaki , tace ai sai ka kamani yanxun, tana faɗin haka ta kashe wayar dariya sadiq yayi sannan ya sake kiran wayar a daidai lokacin da inna ta shigo ɗakin,
Jin ƙarar wayarta yasa ta shigo da sauri ta ɗauki wayarta, tana ɗaukar wayar jawwahir tayi waje,
****
*K*wanci tashi babu wuya a wurin Allah, yau Allah ya yadda su jawwahir sun gama ssce exams insu, zo kaga farin ciki wurin ta kanta sai haƙin rashin kunya yake fitarwa, ji take daidai take da kowa , saboda haka tayi ma ƙwayenta alƙwarin haɗa masu partyn candy, a haka dai kowa ya kama gabanshi itama jawwahir gidansu tayo,
a gida yau jawwahir ta hana kunnuwan inna zaman lafiya, ita kaɗai ta kure volume sai iskanci take, abunma bai mata daɗi ba dan babu mai tayata, ita kuma ta raina gidansu bare ta kira ƙawayenta suxo a cashe gaba ɗaya, dan tunda jawwahir take babu ƙawarta data taɓa zuwa gidansu,
haka ta yini tana shegan takarta, inna dai rayuwar jawwahir tana bata mamaki,
***
*Y*au kwanan su jawwahir huɗu da gama scndry sch, kuma jawwahir ta tado fitina sai ta gina ginin ɗakinta, inna babu juyin duniyar da batayinda jawwahir ba, amma tace wallahi ko za"a sake yaƙin ƙuhudu sai ta gina ɗakin nan,
Inna tace ma jawwahir wai ina ma take samun kuɗin ?"" wato har yanxun baki daina halinki ba?"" jawwahir tace idan baki san kici arziki innas a raba gidan nan nidai a bani kaso na, baba daya shigo yaji hayani inna yace ma tayi shiru idan ta isa tayi ginin,
yana gama maganar ya shige ɗakinshi inna ta rufa mashi baya, jawwahir sai masifa take tana cewa kuma wallahi babu wanda ya isa ya hanata gina ɗakin daga inna har baba babu wanda ya sake mata magana, taci gaba da haukarta ita ɗaya a tsakar gida, baba yace ma inna ta daina tada hankalin yau sadiq zai dawo shi yasa baiyi mata magana ba,
to koda inna ta fito itama bata sake bi takan jawwahir ba, taci gaba harkar gabana, amma tana mamaki miyasa sadiq bai faɗa mata zai dawo ba?"" yinin ranar dai jawwahir bata rufe bakinta ba, kuma duk inda inna tayi sai ta bita tana cewa an nuna mata banbanci ita ba"a santa yanxun dan san kai ga sadiq can an kaishi ƙasar waje shi yayi kuɗi taci gaba da cewa insha Allah nima sai na zama mai kuɗi tunda gani yanxun na sayi mota kuma zan fara aiki, inna dai batayi ma jawwahir magana ba, haka ta gaji da haukanta taje taja ruwa ta shiga wanka,
tana fitowa ta wuce inna tana waƙa sai habaici take ma inna, sannan tana shiga ɗaki ta kunna waƙa ta kure volume tana bin waƙar har ta gama shirin ta tsaff bayan tasa kaya taci gaba da iskancin ta, inna abin yayi mata yawa dan haka ta ɗauki hijabinta ta fita daga gidan,
lokacin da jawwahir ta leko dan taji inna shiru sai taga bata nan, dariya tayi sannan tace naci gari da yaƙi, komawa tayi ɗaki , saman gado taje tahau ta , kwanta wayarta ta ɗauko tayi "yan latse latsen ta sannan ta ajiyeta a saman cikinta haka tayi ta miƙi miƙi da ido har bacci, ya ɗauketa ga waƙa ta kure volume kamar hauka,
ja"afar na gani sadiq da sauri ya fara kiran wayar jawwahir dan ya faɗa mata ga sadiq nan yana gaisawa da mutane zai shigo gida, jawwahir bata san waya na ringing ba, baccinta take cikin kwanciyar hankali dan tunda ta gama scndrsch iskanci kullum kamar ana aiko mata da sabo,
Lokacin daya shigo gida sallama yayi tayi amma shiru, babu wanda ya amsa mashi ɗakin inna ya nufa, dan yasan wancan haukan baya bari taji abinda akeyi a waje, shi kuma ja"afar yana can sai kiran wayar jawwahir yake, shi kuma sadiq yana shiga ɗaki ƙashe waƙar da jawwahir ta kunna yayi, dan baima lura tana kwance ba, har zai fita yaji ringing ɗin waya, dan haka dawowa yayi ya ɗauki wayar , abinda ya gani an rubuta jikin number ya bashi mamaki, *honey j* taɓe baki sadiq yayi tare da ɗaga girar shi ta dama yace honey j, lallai yarinya, zai ajiye wayar yaji wani kiran ya sake shigowa, ɗauka yayi ba tare da yayi magana ba, ja"afar yace jawwahir ga yayanki nan ya dawo kinga yanda ya koma?"" tsaki sadiq yayi sannan ya kashe wayar,
Kallon jawwahir yayi , tsaki yayi sannan yace wai fitina kenan, kamsr mai hankali amma sai tana ido biyu zaka ga tsabagen hauka, kusa da gadon ya matsa ya ƙura mata ido sai kallonta yake , ita kuma jawwahir baccinta take bata ma san yanayi ba, wata zuciyar tace ya mareta wata kuma tace ya barta, har zai fita ɗakin yaji kawai bara ya tasheta