Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

WANDA BAIJI BARI BA Rayuwar Ƙarya da Nadama by MEELAT MUSA

Author :  MEELAT MUSA Category :  African Stories & Novels

Chapter   5 / 28

12K to 15K   out of 83K words

karuwa ma irin ki, wannan kallama tayi ma jawwahir muni, da ta dunƙulo wani luƙeƙen zagi ta zazzage ma sadiq amma dole tayi shiru, hawaye ya zubo mata daga idon ta a ranta tace ni sadiq yake dan gantawa da mazinaciya?"" yanda ta sake maimaita kalmar abun ya sake sawa hawayen suka sake zuwa, tsaki yayi sannan ya miƙe yabar ɗakin , jawwahir kwanciys tayi taci gaba da kuka mara sauti, wai ita ɗan uwanta yake cewa karuwa, lallai kuka jawwahir take sosai, amma babu wanda yake jin sautin kuka,

kundai san dama hausawa sunce wanda baiji bari ba, lalƙai bazai ƙi jin hoho ba, to idan dai bataji bari ba, saboda haka kullum sai taji hoho tunda wanann rayuwar ta zaɓar ma kanta, niko nace bakima ga komai ba,


sadiq yana fitiwa yace ma inna saida safe, tace Allah ya tsare hanya,

Bayan baba ya dawo , inna ta gama abinda take har ta shigo ɗaki ta kwanta , jawwahiɗ bata daina kuka ba, baƙin ciki ya ishi jawwahir ta rasa inda zafa sa ranta sai kuka take, inna taji shashsheƙar kukanta tace jawwahir miye?"" kamar jira take inna tayi mata magana ta ɓarke da wani irin kuka mai sa kaji tausayin mutum da sauri ta sauko daga saman gado taxo kusa da inna ta faɗa jikinta sannan tace innas wai nice sadiq yake cewa karuwa, innas mi nayi ma sadiq yau saida yayi man duka ya tsine man albarka yace man Allah yasa in mutu, inna tace duk inji sadiq?"" jawwahir tace Eh, inna ta bata haƙuri tace taje ta kwanta zai dawo ya sameta, tashi tayi taje ta koma saman gado daran yaudai baƙin ciki baibar jawwahir tayi bacck ba,
[1/17, 7:36 PM] Jamila Musa Ws: ☄
☄☄
☄☄☄
🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥
*WANDA BAIJI BARI BA*
🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥

☄☄
☄☄☄

*AMEENCI WRITER'S ASSOCIATION* 📚✍🏻

*MEELAT MUSA* 🌹

*PAGE* 9

*****

*K*oda safe baƙin cikin abinda sadiq yayi mata ya hanata fitowa tunda ta fito da sassafe tayi burush ta koma ɗaki bata sake fitowa ba, tana ɗaki sai kuka take inna tayi rarrashin duniya har ta gaji,

Wannan baƙin ciki ya hana jawwahir cin komai , haka kuma taƙi zuwa makaranta, ji take ina ma tana iya kashe sadiq data huta baki ɗaya,

Wannan dalili yasa duk wanda ya kira jawwahir a waya bata ɗauka, tun daren jiya alhaji yake kiranta dan yaga bata zo amsar motar da yayi mata alƙwari zai bata kyauta amma taƙi ɗaukar wayar,

Inna duk ta shiga damuwa saboda jawwahir taki fitowa taci abinci kuma taƙi fita bare ma inna tasa ran idan ta fita ta samu mai bata taci, jawwahir data tuna kalmar da sadiq ya faɗa mata sai ta sake kware baki kamar tana shirin shela sannan tayi ta kuka, inna tayi rarrashin duniya har ta gaji, yinin yau dai jawwahir haka ta yini a ɗaki wayarta kuma daga baya gajiya tayi ta kasheta dan abun duniya ya dameta,

Inna ta buga ma sadiq waya ta zageshi tatas sannan kuma tace wallahi komin dare idan ya dawo yaxo tana neman shi, haƙuri ya fara ba inna sannan yace insha Allah zaizo,

Ɗaki inna ta dawo sannan tace ma jawwahir kiyi haƙuri zaizo ya sameni , jawwahir cikin shashshekar kuka tare da jan majina , tace innas waini ce karuwa fa?"" ta sake fashewa da kuka, inna tace kiyi haƙuri ai shiyasa tunda kika koya ma kanki wannan halin idan na faɗa maki bakyaji jawwahir saboda rayuwa shi yasa idan kunyi abunda ba daidai ba ake kwatanta maku, amma sai ku gani kamar kaunarku ne ba"ayi, to dama duk wanda baiji bari ba ai sai ya jawo ma kanshi abinda zai hanashi zaman lafiya,

Inna taci gaba da cewa tunda kinsa ma kanki wannan halin lallai ki tanadar ma zuciyarki wurin ajiye baƙin ciki, jawwahir dai kuka take bata sake magana ba, inna ta gaji da bata haƙuri ta fice a ɗakin,

10:01pm sadiq ya shigo gida da sallamarshi , inna har bacci ya fara ɗaukarta, daga kwancen bata tashi ba, ta amsa sallamar kusa da ita sadiq yaje ya zauna, ya gaisheta ta amsa, sannan yace kince idan na dawo inxo,

Inna tace Eh, mi jawwahir tayi maka ne?"" yace tace nayi mata wani abu ne??" inna tace ina tambayarka kana tambayana?"" sadiq yace aini babu wani abu da nasan nayi mata, ya ƙarashe maganar yana taɓe bakinshi,

inna tace to gata can ta kusa mutuwa dan duk yau bataci abinci ba saboda ka ɓata mata rai miyasa kake faɗin munanen maganganu akanta ne?"" sadiq yace mi nayi mata ne, inna tace ban sani ba,

sadiq yace to kirata ki tambayeta tunda gani sai ta faɗa maki idan nayi mata wani abu, baba dake ɗakinshi yace Abubakar?"" sadiq ya amsa sannan ya miƙe ya nufi ɗakin baba, bansan abinda baba yace mashi ba, yana fitowa kicin ya nufa ya ɗauko abinci ya nufi ɗakin inna,

Jawwahir tunda taji shigowar sadiq , kuma tasan inna ta kirashi tayi mashi faɗa, tasan kanta zata ƙare don haka tanajin yayi sallama tsoro yasa bacci ya ɗauketa,

shi kuma lokacin daya shigo ɗakin fitilar ɗakin ya kunna haske ya bayyana gaba ɗaya, saman gadon yaje ya zauna ya ɗora ƙafarsa ɗaya saman gadon ya miƙeta ɗayar kuma tana ƙasa, bayan ya zauna ya buɗe abincin dariya yayi dan ganin abinda aka dafa,

kuma yasan jawwahir sam ta tsani cimar gidansu dan haka dariya mugunta yayi sannan yace zakici ubanki yarinya abinci ya iba yakai bakinshi yaji babu wani daɗi, ya sake murmushi sannan ya girgiza kanshi , daidai wuyanta yakai mata duka, da sauri ta buɗe idonta zata fara ihu, yace yima mutane shiru,da sauri ta daɗe bakinta,

Ɗaure fuska yayi sosai sannan yace ke har haushi kikeji dan ance ma "yar iska?"" ƙarya nayi ba ita bace?"" kin sani , ya nuna ta, sannan ya nuna kanshi yace nima na sani, dan haka tashi kici abinci, nima yanxun ban shirya kasheki ba, amma kibi sannu lokacin yana zuwa,

miƙewa jawwahir take da niyar yi zata sauka daga saman gadon yayi ƙasa ƙasa da murya kamar mai raɗa yace ina zakije?"" ta nuna mashi alamar zata zubar da miyau a bakinta, zaro idanuwanshi yayi sannan yace haɗeshi, da sauri ta bada ƙutttt dariya sannan ya sake tsuke fuskarshi ya tura mata robar tuwon dawane da tsanwar miyar kuka, yace bisimillah, jawwahir ta fara hawaye, yace miye?"" tace banacin tuwo tayi maganar cikin kuka, yace idan kinci miye?"" tace zanyi amai, yace ni kuma idan bakici ba, zan daɗe maki baki in ɗaukeki in tafi dake , inje inyi ta gana maki azaba, idan na gaji kuma inje inyar dake a daji kura da zakuna su cinyeki,

a ranta Allah tsine ma sadiq kawai take, yacd uhum ci, jawwahir zatayi magana, inda take ajiye wuƙarta ya kai hannunshi ya ɗaukota nuna mata alamar yankewa yayi sannan yayi wani ɗan ƙaramin fito,

haka jawwahir ta tusa tuwon dawar nan da miyar kuka tana ci tana kuka zufa na zubo mata, shi kuma sadiq a ranshi daɗi kawai yake ji, dan tun ranar data sa "yan sanda sukai mashi duka yayi alƙawarin tayi bankwana da farin ciki harsai ranar data bar gidansu, dan haka yayi alƙawari duk abinda yasa bata so shi kuma shi zai mata , kuma yanxun ya gano bata san kalmar karuwa aranshi kalmar ta koma sunan ta, idan dai ba,a gaban mutane ba,

kuka jawwahir take sosai sadiq kuma ya rantse sai ta cinye tuwon nan, tana ci tanayin kamar zatai amai kuma yace idan har tayi amai shima sai ta shanyeshi, kuka take sosai ita dai inna baccin ta take bata san wainar da ake toyawa ba,

hankalim sadiq bai kwanta ba, saida jawwahir ta cinye tuwon nan kaff yace har miyar sai ta shanye, hawaye sai zubowa suke shi kuma dariyar ƙeta kawai yake mata, saida ta gama sannan ya tashi daga saman gadon yace ta biyo shi ta rufe gidan, daɗe bakinta tayi dan amai kawai yake shirin zubawa, suna fitowa tsakar gida yaga tana wata irin tangal tangal ɗaure fuska yayi sosai yace idan har kikayi amai ko bayan na tafi idan nazo da safe zaki gane kurenki, da sauri ta ɗaga mashi kai alamar gamsu, sannan ya fice daga gidan, yana fita ta rufe ƙofar da gudu ta shigo wurin ginin da tasa aka fara mata sadiq yasa aka rusa , anan tayi ta zazzaga amai tana kuka, saida ta amaye tuwon nan kaff hankalinta ya kwanta, ƙasa tasa ta rufe wurin da tayi amai ɗin sannan taje ta wanke bakinta, ta nufi ɗaki tana ƙara tsanar sadiq a ranta,

shi kuma yana fita daga gida dariya yake sosai dan yau yaji ya more mata, yasan sarai da taci tuwo gara ta kwana da yunwa koma ince yunwa ta kasheta, sadiq yana cikin farin ciki ganin ya samo hanyar dazai hanawa jawwahir zaman lafiya,

haka jawwahir tayi ta kuka , har ta gaji tayi bacci ,,,,

****

*B*ayan sati ɗaya da faruwar haka, jawwahir tana jiran sadiq yayi tafiya taje ta anso motar da alhaji yai mata alƙawari, har taciwo bashin kuɗin da zata sa ma gidansu get, dan ta riƙa shigowa da motar ta,

Ita kuma tana ɗaki tana waya, sadiq ya shigo , sai sallama yake dan inna bata nan ita kaɗaice a gidan ita kuma hankalinta ya tafi kan wayarta sai zunkuɗa ƙarya take kamar yanda ta saba zataje umara ƙarshen satin nan, daga can zata wuce china, sadiq na tsaye yana jin ikon Allah dad ɗinta zai siya mata mota ƙarshen satin nan, da alama dai tanajin daɗin wayar, da wanda take wayar tayi mashi alƙawarin zata bashi kuɗi za zarar dad ya turo mata kuɗi kada yaji komai,

tana ɗaga ƙafa sama tana dariya juyowar da zatayi ta ganshi rufe bakinta tayi gaba ɗaya sannan tayi ƙarfin hali tace ma wanda suke wayar jira zanba mai aiki albashinta, sannan ta kashe wayar, ta window ta leƙo ta fara kiran innas , taji shiru,

dan tana waya inna ta fita, tace mata ta shiga maƙota amma hankalin nacan wurin ƙarya, kallon sadiq tayi sannan ta sake matsawa kusa da windown ta sake cewa innasco, da ƙarfi ta faɗa, hawaye ya fara taruwa a idon ta, sannan tayi ƙarfin hali tace yaya inayini, kallo yabi ta dashi gabanta sai faɗuwa yake,

hannunshi ya miƙa alamar ta bashi wayar, wani irin zagi ta gunduma a ranta sannan tace kam wato ni zai tona ma asiri?"", matsawa yayi kusa da ita, ganin bata da mafita yasa tayi saurin buɗe wayar ta cire layin ta jefashi cikin bakinta ta tattaune,

wani irin halbi sadiq yakai mata wanda saida yasa ta kwanta, da ƙafarshi ya taka mata ƙafa, yace ni zance ki bani abu ki cinyeshi?"" to yanda kima taune shi kema yau haka zan kware maki fatar jikinki sannan inbi ta in barbaɗe ta da yaji, ta kasa magana saboda harbin da sadiq yayi mata har yanxun ta kasa dawowa cikin hayyacinta,

wayar ya ɗauka ya fita da ita a tsakar gida, yasa dutse ya dandaƙeta sannan ya tillata cikin rijiya, ya fice daga gidan,

jawwahir tasha kukanta tana nan kwance a inda sadiq ya barta ta kasa tashi har inna ta dawo, inna tana shiga ɗaki taga jawwahir kwance, tace jawwahir miye ya sameki?"" jawwahir tayi shiru sai hawaye dake zubowa daga idon ta, inna tace wani abu akai maki ne?"" jawwahir ta daure tace ba komai innasco, inna tace to Allah yasa haka, sannan ta fita taci gaba da aikin gda,

jawwahir tana kwance saida ta saƙa ta kwance Allah kaɗai yasan masifar da tayi niyar shukawa sadiq ita kaɗai tasan mafita,

***
Jawwahir ta samu ta fita, taje ta samo "yar ƙaramar waya da layi da ita take amfani dan sadiq yace idan ya sake ganinta da waya yanda yayi ma wayar haka zai mata, jawwahir kuma tana tsoron sadiq kamar mutuwa dan kullum da sabon nau"in azabar da yake zuwa mata dashi,

****

*J*awwahir taci adonta cikin shiga ta alfarma kallo ɗaya zakai ma suturar kasan ba suturar banza bace tasa, ta haɗu iyar haɗuwa, kuma kayane masu tsadar gaske, idan ka ɗora idonka kanta baka marmarin ka sauke shi, saboda haɗuwarta, komai zam zam, kuma ko ina ciff ciff, cass taci adon ta wallahi,

Wayarta ce ta fara ringing, ganin mai kiranta yasa tayi azamar ɗauka hafsaf ce, wato bikin gidan tsohon gwamna, banda suka ƙara ma bikin kwanaki da tuni anyi an wuce wurin, hafsat ta sheda mata tafa zama cikkn shiri yanxun suma zasu taho, jawwahir tace to,

Bayan ta gama wayar sai ƙara gyarawa take , tana jin daɗin wannan rana, za"aje a gwangwaje , ta shiga ɗaki dan ajiye wani zaninta taji sadiq ya shigo yana waya, salati tayi tare da addu"a, Allah yasa kada ya hanata zuwa, dan neman shiga ta fito ta gaisheshi kallonta yayi da idanuwanshi masu sa mutum yaji bacci yace ina zaki?"" tace hafsat ce, dama wai shine suna zasuyi wai biki, yace ke kuma gayyar na soɗi zakije ko?"" jawwahir tace ba gayyar soɗi bane, yace to baza kije ba, gaban jawwahir ya faɗi das dass tace kayi girman Allah ka rufa man asiri wallahi bama zan daɗe ba, ina zuwa kawai zan dawo yace a a, ɓafa fuska tayi kamar mai shirin kuka sanndn tace wasu yayunsu sunayi alfahari da ƙannensu kaima kayi alfahari dani ina so ka yabeni dan ina da biyayya, kabarni don Allah inje, baiyi magana ba har yanxun kallonta yake taci gaba da cewa kuma zanyo maka tsaraba ma, taɓe baki yayi yace bazanci ba,

Wayarta da take jikinta taji ta bara zuuuuu zuuuu dan a silent ta saka saboda shi, tanaji tasan ko waye, don haka tace don girman Allah ka barni inje, baiyi magana ya fita daga gidan, tsaki tayi tace aikin banza,

gyalenta da jakarta taje ta ɗauko sannan ta fito tace hajiya innasco sai na dawo, inna tace to, jawwahir ta fita da sauri daga gidan, ashe shi kuma sadiq zuwa yayi yaga ko ja"afar zai kaita , yaga baya ma gari lokacin daya dawo gida ya samu babu jawwahir ya fara faɗa, wai inna ta barta ta fita biɗiɗ yanxun cikin dare, niko nace kwantar da hankalinka yau ma ba"a gidanku zata kwana ba,

Sadiq sai cewa yake komin dare yana nan ta dawo sai ya zaneta, ni ko nace sannj sarki ƙarfi,

jawwahir kuwa tana isowa bakin titi su hafsat suka ɗauketa sai wurin kamu............€€€
[1/17, 7:36 PM] Jamila Musa Ws: ☄
☄☄
☄☄☄
🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥
*WANDA BAIJI BARI BA*
🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥

☄☄
☄☄☄

*AMEENCI WRITER'S ASSOCIATION*📚✍🏻

*MEELAT MUSA* 🌹

*PAGE* 10

***
*H*ar yanxun sadiq ya kasa zaune ya kasa tsaye, idan inma ta shiga kching saidai ya bita yace anbar yarinya ta tafi ke kanki bakisan ina ta tafi ba, yanxun idan wasu suka xo suka samu bata nan sai anje kuma ance bata zama gida, inna dai bata mashi magana ba, taci gaba da aikin ta,

Duk inda inna ta nufa haka sadiq yake binta yana mata mita, kamar ƙaramin yaro , inna ce tace ya tafi ma yaje yayi sallah an kira magrib, yace shi yau babu idan zaije a gidan nan sai jawwahir ta dawo,

Su hafsat na ɗaukar ta, suka wuce wurin kamu, lokacin da suka isa wurin ya cika dam duk inda ka ware idonka a wurin kowa yanaji da kanshi ne, kuma babu sakarai dan duk wanda yake wurin yasan hannunshi , babu talaka kowa shegen kanshi ne, banda jawwahir dan ita babu wanda yasan inda ta dosa, amma fa ta saje da mutanen wurin abu ɗaya zaka duba idan dai kana ganewa hutu, dan idan kasan hutu kana ganin jikin da yake hutawa kasanshi,

Amma suturar da jawwahir ta saka ya ɓoye rashin hutun ta, sadiyya taxo ta tari jawwahir ta nuna farin cikinta zuwa wurin bikin gdansu, sannan tace idan ta kira wayarta bata samu, jawwahir tace ta canja layine wancan anyi masji nauhi kuma "yan maula suna damunta ne sosai,

Sadiyya tace to sake saman nunmberki anan, jawwahir tace kibi a hankali ai a gidanku zamu kwana, sadiyya tayi farin ciki matuƙa, haka akaci gaba da shagalin biki, ashe shegiyar yarinyar nan tana da kuɗi sosai a jakarta?"""

Haka jawwahir ta buɗe bakin jakarta taci gaba da ɓarin kuɗi tayi liƙe sosai saboda jawwahir ta iya abu na neman suna, kyautar da bata lada, kuma ka tashi bada abu kaba mawaƙi?""

Shi kanshi mawaƙin da suka ɗauko saboda yanda yaga jawwahir tana hauka da kuɗi yasa aka tambayo mashi sunan ta, haka yaci gaba da kirarata yana zuzuta ta, jawwahir wannan abu sai ƙara mata ƙaimi yake haka taci gaba da ɓarin nera,

Sadiyya taje ta jawota, yan maula ko suka biyota, haka taci gaba da bada kuɗi wuri fa gaba ɗaya ya ɗauka jawwahir,

bayan an gama shagalin kamu sadiyya ta ɗauki jawwahir a mota suka nufi gidansu, hafsat kuma ta nemi jawwahir kuma ta kira wayarta amma bata shiga, haka yasa ta kira sadiyya ta tambayeta tace suna tare hafsat tace gata nan ita zuwa gdan,

koda suka dawo gida mutane da dama suna san ganin jawwahir saboda gaba ɗaya ta tafi da imanin mutane a wurin party, niko nace ki gama iskanci tsaff sadiq zaici uwarki

da daddare sunyi fira sosai kamar da yanda jawwahir ta saba haka taci gaba da zunkuɗa masu ƙarya, masu ƙaramin tunani duk ta halakar dasu, dan kowa ya ɗauka abinda take faɗi gaskiya ne, haka sukai ta firarsu daga baya kuma kowa yayi bacci,

a gida har yanxun sadiq yana nan zaune yana jiran dawowar jawwahir, sai mita yake kamar tsohon makoho, babu yanda baba baiyi dashi ba ya tafi amma yace wallahi sai jawwahir ta dawo ya zane mata jiki sannan zai tafi, niko nace ka shirya shirin kwanaki dan jawwahir ma ta manfa akwai gdanku a rayuwarta,

*****

*T*unda safe hafsat kowa ya tashi yayi sallah to ita dai jawwahir dama ba kullum take sallah ba, amma anci sa"a yau dai period take, amma da ba haka ba, ita gaskiya ba wata sallah take ba, idan kaga tayi sallah ko anyi mata gori ko kuma taga mutane sosai shine sai tayi saboda kada ace batayi ba,

To bayan sun gama abinda suke anyi break hafsat tace ma jawwahir zataje ta karɓo masu ɗinkinsu, jawwahir tace to ta jira su fita tare, ta ajiyeta a cidcap company idan ta dawo sai taje su wuto tare, hafsat tace to, sadiyya dai bata

5 / 28