Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

WANDA BAIJI BARI BA Rayuwar Ƙarya da Nadama by MEELAT MUSA

Author :  MEELAT MUSA Category :  African Stories & Novels

Chapter   27 / 28

78K to 81K   out of 83K words

su ganka hankalinsu ya kwanta,,,,

bai sake magana ba, dan haka ita ta basar dashi,,,,

suna isa gida, bayan jawahir tayi parking tace muje ko?"" sadiq baiyi magana ba, ya buɗe motar ya fita,, itama fita tayi tabi bayanshi har suka shiga ciki,,,,,,

Suna shiga inna ta taso da sauri tana cewa ya akayi ne?""" sadiq ya kalli jawahir ita kuma taɓe baki tayi ba tare da tace komai ba,,,,,

inna tace baka lafiya ne?"" jawahir tace da masassara ya dawo, shine nace yazo inkaishi allura,,,, inna tace to ku tafi sai kunxo nan kuma?"" jawahir tace ai zowa nayi mu tafi tare ki riƙeshi kinsan kukan allura yakeyi,

sadiq yace waike wasa nake dake?"" dariya jawahir tayi sannan tace ai baka da abokiyar wasa saini, muje,,, tsaki sadiq yayi sannan ya zauna, suka gaisa da inna, bayan sun gama gaisawa inna ta kawo mashi abinci yaci,

Yaci ɗan kaɗan jawahir tace idanma zaka buɗe ciki kayi tatul kaci dan idan nakaika haka zance duk a cacceka man kai sai kayi ladaf, kallonta sadiq yayi amma baiyi magana ba,,,,,

Inna ce ta shigo tana cewa tunda kun gama ku tashi ku tafi dare yanayi,,,, sadiq ne ya fara miƙewa ya fita,,,,, ita kuma jawahir ɗaki ta shiga wai bata hau gadon innas ba,,,,

saida taje ta soke saman gadon sannan ta fito , tace mun tafi,,, inna tace kedai kika sani,,,,

Da ɗan gudu ta fita har ta isa wurin mota sadiq yana tsaye ya jingina da mota, tana zuwa ta buɗe tace muje,,,

tsaki sadiq yayi sannan ya shiga, yana shiga taja suka bar gidan, .......
[1/17, 7:46 PM] Jamila Musa Ws: ☄
☄☄
☄☄☄
*WANDA BAIJI BARI BA*

*AMEENCI WRITER"S ASSOCIATION* 📚✍🏻

*MEELAT MUSA*

*Domin samun ƙayatattun littattafanmu sai ku nemu a shafinmu na facebook wato*

*AMEENCI WRITERS NOVELS GROUP*

*Allah ya baki lafiya ƙawata ASMEENAT XEEYAN Allah kuma yasa zakkar jikine,*

*PAGE 47*

***

*S*una isa asbiti bayan tayi parking sadiq yace kada ki fito ina zuwa,,

Batayi magana ba shi kuma ya buɗe motar ya fita,,,, yana fita jawahir tayi tsaki tace sai nazo ka shiga ɗin ,

Sadiq yana shiga bayan yaga likita ya faɗa mashi abinda yake damunshi likita ya rubuta mashi magunguna a cikin asibitin ya siya sannan ya fito,

Sadiq yana zuwa ya buɗe mota ya shiga, jawahir tace har an gama?""" yace Umm dariya jawahir tayi sannan ta daki sitiyarin motar tace bani na kashe zomon ba,,,,,,,

Shi kuma a tunanin sadiq tana nufin ba itace tasa ya saki khadija ba, ita kuma nufinta ba itace tasa akayi mashi allura ba,, niko nace banda abinka ina jawahir tasan ka saki matarka,,,,,,,

Tsaki sadiq yayi sannan yace ni bana san abinda kike man gaskiya, jawahir tace ni kuma irin wannan nake so,,,

Sadiq yace to muci gaba idan na gaji ni nasan maganinki,, jawahir jin sadiq yace yasan maganinta tayi shiru bata sake magana ba,

Har suka iso gida jawahir bata sake cewa tufff ba, bayan tayi parking sadiq ne ya fara fita yayi cikin gida, ita kuma wayarshi daya bari ta ɗauka da tata, sai magungunanshi sannan ta rufe motar tayi ciki itama,,,

Lokacin da jawahir ta shiga itama ɗaki ta shiga sadiq yana kwance, bayan ta shiga sadiq yace ta kawo mashi ruwa yasha maganin,

Turo baki tayi sannan tahau saman gado, sadiq cikin sanyi yace jawahir cewa nayi fa ki kawo man ruwa insha magani, jawahir tace bacci nike ji,

Tsaki sadiq yayi sannan yace ki tashi ki kawo man ruwa ko?"" yayi maganar ne cikin ɗaga murya sosai, a tsorace ta sauka daga saman gadon taje ta kawo mashi ruwan,

Saman bedsite ta dungurar da ruwan, yace miƙo man mana, tace kai komai sai kayi kwance sai anyi maka haba, a daidai lokacin da take ƙara hayewa saman gado,

Sadiq tashi yayi ya ɗauki ruwan yasha maganin sannan yace saina ƙara aure tunda baki da kunya,,, jawahir tace daga ban baka ruwa ba sai kayi fushi?"""

Yace Eh, sauka tayi daga saman gado ta ɗauki ruwan tana cewa anshi yaya, sadiq yace abinda nasha, maganin, zama tayi kusa dashi ta ɗora kanta saman kafaɗarshi tace don Allah kayi haƙuri,,,,

Yace bazanyi haƙurin ba, inje in auro inyamura mai ƙarfi, wanda zata riƙa goyani idan banda lafiya tayi man wanka ta bani abinci a baki a maidani dan gata,,,,,

jawahir tace da Allah yaya kayi haƙuri, sadiq yace kuma idan kikaman rashin kunya in zauna a gefe insa ta lallasa man ke,,,,, mai ƙarfi zan auro wanda zata ɗaga manke sama da hannu ɗaya tayi maki duka,,,,,,

tunda ni yanxun dan na daina dukanki kike raina ni ko?"" jawahir tace na bari, murmushi yayi sannan yaja jawahir saman gado , suka kwanta bacci,,,,

Tunda safe jawahir ta tashi ta fara haɗa abinda zasuyi break, dan sadiq yace bata sanyin aiki, amma idan yayi aure komai matar zatayi mashi, to yau ana kicin ana ta ƙokari,,,,

Aiki take sosai, dan sadiq ya lura jawahir mahaukacin kishi gareta, saida ta gama komai sannan ta gyara kicin ɗin ta goge duk inda ta ɓata ta tattara komai ta wanke,,,

ta dawo farlo ta share ta goge fess, ɗaki ta koma a lokacin sadiq ya fito wanka,,, da sauri ta isa wurinshi towel ɗin dake hannunshi yana goge jikinshi ta ansa tana goge mashi,,,,,

Da kanta ta shafa mashi mai, ta gyara mashi kanshi, ta ɗauko mashi kaya yasa,

Bayan ta gama ta gyara gadon ta share ɗakin sannan ta shiga toilet dan wankewa, saida ta wanke sannan tayi wanka ta fito,

Tana gama shiryawa ta fita farlo anan ta samu sadiq yana kalaci, cikin tsiwa tace kai koni da nayi banci ba saikai?""

Dariya sadiq yayi amma baiyi magana ba, tsaki tayi a daidai lokacin da take zama ta fara kalacin itama,,,,,

suna gamawa ta tattara komai taje ta wanke ta mayar da komai mahallinsa, ta dawo,,,,

Sadiq na zaune yana kallon jawahir sai dariya yakeyi a ranshi,,, tazo ta wuce shi ta shige ɗaki,,,,

Saida ta gama abinda takeyi ta fito, inda sadiq yake zaune itama taje ta zauna kusa dashi sannan tace yaya don Allah makaranta zan koma, kallonta sadiq yayi baiyi magana ba,,,,

Jawahir taci gaba da cewa, inyi karatuna so nake in zama "yar jarida, tsaki sadiq yayi sannan yace bari sai kin ƙara hankali, jawahir tace banda hankali yanxun?""

Yace inafa kikaga hankali, shekara sha bakwai, jawahir tace yanxun sha takwas nake dashi, sadiq baiyi magana ba, jawahir ta ɗauki wayarta dake ƙara,

dariya tayi sannan ta ɗauka tana cewa hasssu, zata tashi sadiq ya riƙota ya zaunar da ita,,,, jawahir tace ya kuka koma gida?"" tace lafiya qalau, hafsat tace ke banza bakice mana anyi waje da tunkiyarki?""""

cikin rashin mahimta jawahir tace waye tunkiya na?""" sadiq dake zaune yayi dariya kuma ya gane abinda hafsat take nufi, wato ya saki khadija itace tunkiyar , murmushi yayi sanna ya sake ,, kallon jawahir, yayin da take ƙara cewa ai banda tunkiya,,,

Hafsat tace sakara kishiyarki, tsaki jawahir tayi sannan tace waye ya faɗa maki a daidai lokacin da jawahir take kallon sadiq, ɗan lumshe idonshi yayi, sannan yayi murmushi,,,

hafsat tace fatima take faɗa man, banza labarin labarine sai mun haɗu,,,, jawahir tace to Allah ya kyauta, ubangiji ya tsare mu a gidan aurenmu,

hafsat tace amin sannan ta kashe wayarta,,, sadiq yace kinsan Allah idan bakiyi hankali ba saina rabako da wannan hassun banzar, gulmarta tayi yawa,,,,

Jawahir batayi magana ba, sadiq yaci gaba da faɗa wa jawahir sai ƙarawa yakeyi, kamar zai daketa, ganin abun na sadiq baya ƙarewa ta tashi da gudu tayi ɗaki,,,,,,

shima binta yayi yana ci gaba da faɗan, kuka jawahir ta fara tana cewa haba yaya nifa bani na tambaya ba, itace ta kirani take faɗa man,,, cikin tsawa sadiq yace gashi tace sai kun haɗu akwai labari sosai,,, wannan wace sakarar magana ce?"""

kema gulma kikeyi shi yasa idan anji gulma ake faɗa maki, to idan baki kiyayi wannan gulmar banzar ba , saina gajajjala ki a gidan nan na faɗa maki,,,,,

jawahir bata sake magana ba, taci gaba da kuka, sadiq yace rufe ma mutane baki da nayi magana sai kiyi ta wani kukan munafinci, cikin kuka jawahir tace don Allah yaya nifa bani nace ta faɗa man ba,,,,

kusa da ita sadiq ya matsa da sauri ta rufe idonta tana duƙar da kanta ƙasa,,, fizgota sadiq yayi ya miƙar da ita tsaye da sauri ta buɗe idonta hawaye naci gaba da zubowa daga idonta tana kallon sadiq,,,,,

Da hannu ɗaya ya riƙeta hannu ɗayan kuma yana nunata, yana cewa duk abinda aka faɗa akan ta ƙarya ne, kanshi ya nuna da hannunshi sannan yace nine kaɗai zan faɗa maki magana ki yadda ko waye ya faɗi wani abu ƙarya yakeyi,,,,,

nine na saketa kuma nine nasan abinda tayi na rabu da ita, dan haka ki kiyayi kanki na faɗa maki, daga haka bai sake cewa komai ba ya wurgar da ita saman gado ya fita daga ɗakin,,,,,,,,,,,,
[1/17, 7:46 PM] Jamila Musa Ws: ☄
☄☄
☄☄☄
*WANDA BAIJI BARI BA*

*AMEENCI WRITER"S ASSOCIATION* 📚✍🏻

*MEELAT MUSA*

*Domin samun ƙayatattun littattafanmu sai ku nememu a shafinmu na facebook, kudai ku nemi*

*AMEENCI WRITERS NOVELS GROUP*

*PAGE 48*

***

*J*awahir tana ganin sadiq ya fita itama miƙewa tayi ta fita farlon, tana fita shi kuma a daidai lokacin da yake fita daga farlon,

Itama binshi tayi ta fita, har wurin mota, yana ƙoƙarin shiga yaga jawahir tsaye tana kuka, harararta yayi sannan yace miye?""

Da sauri jawahir ta matsa kusa da sadiq ta shige cikin jikinshi sosai ta kifa fuskarta a saman ƙirjinsa tana ci gaba da kuka,

Ɗagota sadiq yayi jawahir ta kalleshi cikin kuka jawahir tace yaya don Allah miyasa baka so na?""" taci gaba da cewa duk abinda nayi dana laifi da wanda ba laifi ba faɗa,,, ?

Idan baka sona ka faɗa man , lokaci yayi da zansan matsayina a wurina, idan baka sona ka faɗa man zanyi tafiyata in fita daga rayuwarka kaima ka huta, idan kuma kana so na ka faɗa man halina wanda baka so sai in daina , ta ƙara maganar cikin sigar tausayi,,, murmushi sadiq yayi sannan ya matsar da ita gefe ya koma ya shiga mota yaja yabar gidan,,,,,,,,

Jiki a sanyaye jawahir taja ƙafafuwanta ta koma cikin gida, wata zuciyar tace tayi tafiyarta tabar sadiq tunda baya santa wata zuciyar tace kiyi haƙuri, tunda ko kin tafi a gidansu zaki koma,

Tsaki jawahir tayi sannan ta tashi ta shiga ɗaki, hijabinta ta ɗauka da makullin mota, duk ɗan abinda tasan zata buƙata ta ɗauka ta sa a jaka, sannan ta fita tana ci gba da kuka,,,,,

Bayan ta shiga mota tabar gidan, tafiya tayi mai nisa, sannan tayi parking a bakin wata santa ta fita,,,,

Wani gida tayi ma tsinke, bayan ta shiga suka gaisa da matar gidan sannan tace mata mai unguwa yana nan?""

Tace Eh yana ciki shiga,,,, jawahir ta miƙe ta shiga ɗakin, bayan sun gaisa tace mashi don Allah gida nake so zan siya, mai unguwa yace tou, wane iri kike so ne?"""

Cikin damuwa jawahir tace kawai dai wanda zan zauna nake so,,, mai unguwa yace to akwai gida anan baya, da aka saka a kasuwa, muje ki gani idan kina so,,,,,

Jawahir tace bama sai na gani ba ina so, nawa ne kuɗin ?"" mai unguwa yace miliyan huɗu da dubu ɗari takwas, jawahir tace to ina so,,, muje inga gidan,,,,,,,

Mai unguwa ya ɗauki rawaninsa yasa sannan ya ɗauki tabarau ɗinsa ya saka, suka fita,,,,, bayan sunje jawahir taga gida tace yayi mata tana so, mai unguwa yace to ta kawo kuɗi, jawahir tace to bara taje ta kawo mashi,

Mai unguwa yace to, jawahir ta tafi,,,,, bata daɗe da tafiya ba, mai unguwa ya buga ya faɗawa mai gida cewa an samu mai sayen gida taje zata kawo kuɗi,,,,,,,,

Yace to idan tazo ayi mashi magana, mai unguwa yace to,,,,,,

jawahir kuwa sai bayan azahar ta koma gidan mai unguwa da kuɗinta a mota, bayan ta koma ta shiga amma bata fiddo kuɗin ba,,,,,,

bayan ta shiga mai unguwa yace to bara a kira mai gidan, jawahir tace to, tana nan zaune mai unguwa yayi ma mai gidan waya , yace a jirashi yana zuwa,,,,,,

Ba,a ɗauki wani lokaci mai tsawo ba, yazo, bayan yazo ya sanar da mai anguwa yazo, mai unguwa yace ya shigo ciki, fita yayi daga mota ya rufe sannan ya shiga cikin gidan,,,,,,,

Jawahir da sauri ta miƙe tsaye tana raba idanuwa kamar tayi ma sarki ƙarya, saidai ta kalli mai unguwa ta kalli sadiq,,,,,,,

Shima kallonta yayi da alamar tuhuma,,,,,, da sauri jawahir ta duka ta ɗauki makullin mota, zata wuce sadiq ya riƙeta, yace mi kika zo yi a gidan nan?"""

Mai unguwa yace ranka ya daɗe kasanta ne?"" murmushi sadiq yayi sannan yace mata tace, mai unguwa yace ai itace zata sayi gida,,,,,

Kallon jawahir sadiq yayi sannan yace mi zakiyi da gida ne?"" batayi magana ba, ta fizge jikinta tayi gaba, da sauri sadiq yabita ya sake riƙota, cikin ɗaga murya yace bakiji ina magana ne?"""

Tsaki jawahir tayi sannan tace sakarmin hannu, sadiq yace bazan saki ba, mi zakiyi da gida ne?"" nake tambayarki,,,,

Jawahir tayi shiru,,, sadiq ganin faɗan bayayi yaja jawahir suka fita daga gidan, a zauren gidan ya tsaya, ya jawo jawahir a jikinshi cikin tsigar rarrashi yace jawahir waye zai sayi gida ne?"""

jawahir tace ni zan siya, sadiq yace mi zakiyi da gida?"" jawahir tace saboda na daina sanka yanxun, sadiq yace tou , jawahir taci gaba da cewa kuma bazan sake komawa gidanka ko gidanku ba, sadiq yace miyasa?"""

jawahir tace ina so in fita rayuwarku dakai da gidanku baki ɗaya, itama motar zan maido maka idan na gama abinda nakeyi, hannu sadiq ya miƙe mata tare da cewa bani makullin motar,,,, bashi jawahir tayi bayan ya anshi makullin yasa aljihunshi yaja hannun jawahir suka fita,,,

Suna zuwa wurin mota sadiq yace shiga , jawahir tace bazan shiga ba, sadiq yace kiyi haƙuri ki shiga kinji yayi maganar cikin sigar lallashi,,,,,, jawahir tace haƙurina ya mutu nida gidanka babu rantsuwa babu baki , gaban sadiq ya faɗi,,,, sannan ya sake kallon jawahir yace kiyi haƙuri jawahir don Allah ku tafi gida,,,,

Tsaki jawahir tayi sannan tace nifa gaskiya bazan sake komawa ba,,,,,, buɗe man motar in cire kuɗina zanje in sayi wani gidan ba dole sai naka ba, taci gaba da cewa ai bansan naka bane da bazan siya ba,,,,,,

cikin yanayi damuwa sadiq yace jawahir yi haƙuri, tace haƙurinmi zaka bani?"" tunda baka so na?"" sadiq yace waye yace bana sanki?""
[1/17, 7:46 PM] Jamila Musa Ws: ☄
☄☄
☄☄☄
*WANDA BAIJI BARI BA*

*AMEENCI WRITER"S ASSOCIATION* 📚✍🏻

*MEELAT MUSA*

*Domin samun littattafanmu sai ku nememu a shafinmu na facebook* 👇🏻

*AMEENCI WRITERS NOVELS GROUP*

*Allah sarki mace mai kamar maza ga karamci ga mutunci ga iya mu,amula da mutane gaskiya kina da mutunci sosai dole ne inyi turjiya in gaisheki kuma in maki fatan alkairi, Alkairin Allah ya daddanneki alkairi ya isoki har garin bauchi, wai wace ce wannan?""" hmmm aikuma kunsan REAL MAI DAMBU ce, marubuciyar littafin YARO MA NAMIJI NE, marubuciyar KISHIYATA JIHADI NA, kai gaskiya na gaisheki, na gaisheki, nagaisheki sosai, bama jameela musa ba kaɗai AMEENCI WRITER"S ASSOCIATION, duk suna gaisheki albarkacin jameela musa, { meelat musa }*

*PAGE 49*

***

*J*awahir tace ai ido ba muduba yasan ƙima, yaya yau nake tare dakai?"" tun ina yarinya nake tare dakai kuma duk abinda kake man na ƙiyayya nasanshi,

Da sauri sadiq ya rufewa jawahir baki da hannunshi, idonta daya kawo hawaye ta ɗaga tana kallonshi,,,,, sannan takai hannunta da niyar ta janye hannunshi daga bakinta dan tana so tayi magana ne,,,,,,,,

Amma ta kasa saboda yafita ƙarfi, kuma riƙon da yayi mata bada wasa yayi ba,,,,,,,, hawayen daya taru a idonta ya zubo mata, a daidai lokacin da sadiq yake cewa ina sanki,,,,,,,,,

Wallahi ina sanki sosai, ina maki so bana wasa ba, tunda Allah ya halicci rayuwata da ƙaunarki aka halicceni jawahir, ki daina cewa bana sanki,,,,,, lumfasawa yayi sannan yaci gaba da cewa,

Kuma kike cewa zaki rabu dani, kin kuwa san abinda kikeyi?"" yaci gaba da cewa to bara kiji in faɗa maki, duk wanda yace zai rabani dake to haƙiƙa rabani dake jawahir tamkar yanke alaƙane tsakanin lunfashi da rayuwa,,,,,,,

Hannunshi ya janye daga saman bakinta sannan ya ɗurƙusa saman guyawunshi yace na roƙeki da kiyi haƙuri don Allah, a daidai lokacin daya haɗa hannunwansa biyu , alamar neman gafara,,,,,,,,

Tsaki tayi sannan ta taɓe bakinta,,,,, sadiq yace ki yadda dani, duk abinda na faɗa maki bana ƙarya ina faɗar gaskiya nane,,,,, cikin tsiwa jawahir tace ni duk wannan ladabin bazaisa inji tausayinka ba, ko zaka maida man jiki kunnuwa nasan baka ƙauna na,,,,,,

Idanunwan sadiq da sukayi ja sosai, ya buɗe su yana kallon jawahir cikin yanayin ta tausaya mashi,,, tsaki jawahir tayi sannan ta juya da niyar tafiya,,,,

Da sauri sadiq ya miƙe yaje yasha gabanta, sannan yace jawahir miyasa haka ?"" cikin kuka jawahir tace ni gaskiya banayin aure dakai, na gaji kowa yayi haƙuri da kowa, kaje ka auri wanda kake so nima inje in auri wanda nake so,,,,,,,

murmushi sadiq yayi da gefen bakinshi sannan yace ni inada hankali kuma nafiki tunani shekaruna da naki bazasu taɓa zuwa ɗaya ba,,,,,,, kinga ni ɗan uwanki ne, mu haɗu kawai mu rufa ma juna asiri jawahir,,,,,,

Kina so na,,,, na sani kuma nima ina sanki,, tsaki jawahir tayi sannan tace waye yace maka ina sanka?"", murmushi sadiq yayi sannan ya ƙara matsawa kusa da jawahir ya jawota jikinshi ya rungumeta sosai , sannan yace keko mana nafa san komai, nidai kiyi haƙuri,,,,,,,,

jawahir tayi shiru, dago fuskarta sadiq yayi yana kallonta ido cikin ido sannan yace ki kalleni a haka idan kika ce bakya so na, na yadda,,,,, jawahir tayi shiru, sadiq yace cene sadiq bana sanka bana kaunar ka, idan kika faɗi haka to nasan da gaske kike,,,,,,,,

Jawahir tayi shiru,,,, dariya sadiq yayi sannan ya saketa daga jikinshi tare dakai mata ɗan dukan wasa a jikin kafaɗarta, hannunta ya riƙo tare da ɗan murzawa, sannan ya ciro makullin motar daga aljihunshi yace daga nan kije gida ki anso mana abinci tunda baki tsaya kin dafa ba,,,,,

Jawahir tace ni gaskiya bazanje gidan innas ba, murmushi sadiq yayi sannan yace miyasa?"" tace haka nan, yace to kije kiyi girki, tace ni gaskiya banayin girki,,,, sadiq yace to tafi gida zanzo yanxun insha Allah,

Jawahir tace to kace ma mai unguwa na tafi, sadiq yace to, saida jawahir ta shiga mota ta tafi sannan sadiq yayi dariya ya tafa hannunshi tsalle yayi sannan yace Yeeeechhh tare dakai duka tafin hannunshi na haggu da hannunsa na dama sannan yayi

27 / 28