Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

WANDA BAIJI BARI BA Rayuwar Ƙarya da Nadama by MEELAT MUSA

Author :  MEELAT MUSA Category :  African Stories & Novels

Chapter   12 / 28

33K to 36K   out of 83K words

inci uwarka, kanta yayi da wuƙar ita kuma ta ruga da gudu ɗaki dan ɗauko wuƙatar ta, cikin tsotsai Alhaji yana ƙoƙarin kaucewa amma ina?"" tuni wuƙa tayi cikin alhaji, a daidai lokacin da zarto ta fito daga ɗaki da wuƙa, tace kam bala"i,?"""

ka kashe shi?"" lallai yau kaima saina kashe ka, ta ɗaga wuƙar ta sara wa reza, shi kuma ya yanketa a hannu, haka dai sukai ta yanke yanke, har kowa yaji jiki suka zube a ƙasa, zarto ta suma, shi kuma reza yaja jiki yabar gidan, shi kuma alhaji ya mutu...............,


jawwahir ita kuma daga kasuwa tayo gidan, dan ida tattara kayanta, tana shigowa taga zarto da alhaji ƙasa wanwar, tashin hankali , jawwahir duƙawa tayi kusa da zarto dan ta lura tana sauke lunfashi cikin wahala tana tallabota dan tambayar miya faru amma ta sake tafiya luuuuuuu,

Sa sauri jawwahir ta miƙe zatayi waje, "yan sanda ta gani a gabanta tsaye, jikinta ya fara ƙarma , cikin rawar jiki jawwahir ta fara magana, kana ganinta kasan ta ruɗe, wani ɗan sanda ya daka mata tsawa yace wato kinyi kisa amma zaki gudu ko?"" kuka jawwahir ta fara sannan tace wallahi banice na kashesu ba, tsawa ya sake daka mata wanda yasa jawwahir ta tafi duniyar ɗimuwa, kafin ta dawo duniyar masu tunani , aka tattara ta da ita dasu zarto alhaji akayi waje dasu............,

A cikin motar "yan sanda aka saka jawwahir tana kuka tana rantsuwa ba itace ba, amma babu mai saurarenta, haka aka tafi da ita , su kuma suka zarto da alhaji akai asibiti dasu,

bayan "yan gwaje gwaje likitoci sun tabbatar da mutuwar alhaji, ita kuma zarto ana bata taimako dan ganin an ceto rayuwarta,

Jawwahir kuwa suna zuwa state c i d, bayan bincike bincike sunga lallai jawwahir zata raina masu hankali saboda haka saida akayi mata shegen duka harta suma, sannan akai gidan yari da ita, dan sai zarto ta dawo hayyacinta zasu ci gaba da bincike, an ajiyeta gudun kada ta gudu.........,


shi kuma alhaji an miƙa gawarshi ga ahalinsa an sallaci gawarshi kamar yanda addini ya tanada,

*****

*A* gidan su innasco kuwa yau kowa cikin tashin hankali yake sai koke koke akeyi dan hajiya kaka ta ansa kiran mahalicci, gida ya cika tanƙam da dangi "yan uwa da abokan arxiki, sai koke koke akeyi,

bayan an dawo daga kaita makwancinta ne, ƙanwar maman su tace aje makarantar su jawwahir a ɗaukota, inna tace ita bata san makarantar ba, sadiq yakaita kuma baya nan, hadixa tace to tunda duk dangi sun haɗu itama da an ɗaukota anyi alhini da ita, inna dai tace ayi haƙuri har dawowar sadiq,

***
*S*atin jawwahir ɗaya a gidan yari amma kullum tana ansar mummunan hukunci, zaman gidan yari baya mata daɗi tana cikin masifa da wahala ga jawwahir baki ya saba cin mai daɗi, tana fuskantar horo mai tsanani,

Gashi kuma har yanxun zarto bata farfaɗo ba, jawwahir azaba ta isheta, don haka yau jawwahir anyi alwallah ana sallah sai yau ta gane mahimmancin sallah,

addu"a jawwahir take Allah ya bitar da ita daga ƙangin wahala, jawwahir ta gane lallai taurin kai ba, yau ta fara nadamar halin banzan ta, amma a ƙarƙashin ranta gurinta idan ta fita lagos zataje, dan can anfi samun kuɗi ,


****

*H*ar akayi sadakar arba"in sadiq yaƙi yaxo yace aiki ya riƙesu sosai kuma a makarantar su jawwahir babu wanda ake bari ya ɗauki wani sai wanda ya kawoshi, haka dai inna hadiza ta gaji da nacinta har ta gaji ta koma,


inna ko ta buɗe wuta wallahi duk inda jawwahir take sai an gano ta, idan kuwa ba haka ba alo tsiya alo danja,

***
*J*awwahir tana cikin musiba, lallai zaman gidan yari zaman bala"ine, jawwahir sai addu"a take Allah ya raba kowa da zuwa gidan yari,

Tana zaune ta zabga tagumi sai kuka take, tana fyace majina, zama tayi kusa da jawwahir sannan ta taɓo jawwahir, ɗago kai jawwahir tayi ta kalleta sannan ta sake fashewa da kuka, tace wai miyasa rayuwa take tsanantawa?"" matar tace ke kika tsanta ma rayuwarki, kamarki miyasa kika bar gida?""" jawwahir tace kai wallahi rashin godiyar Allah, yanxun gashi ina tunanin idan na fita in tafi lagos ashe ma rayuwata ta ƙare , jawwahir ta fashe da wani irin kuka sannan tace wai kasheni za"ayi ƙsrshen watan nan,

matar tace mi zakiyo lagos?"" jawwahir tace neman kuɗi, tace waike miye sana"arki?"" jawwahir tace dan fara, sai kuma inci bashi amma bazan biya ba, tace mi zakiyi da kuɗi?"" jawwahir tace miliyan hamsin nake so in tara sannan in koma gida, matar tace to yanxun miliyan nawa kika samu?"" jawwahir tace ina da miliyan shabiyar, da wani abu, matar tace idan kina san kuɗi ga hanya mafi sauƙi,

da sauri jawwahir ta ɗago kanta ta sake kallon matar, sannan tace miye?"" tace zaki iya ne?"" tace zan iya komai amma bana iya zina, dariya tayi sannan tace amma kuma kika kashe mutum?"" jawwahir tace bani na kashe ba, matar tace to yanxun idan zaki iya tafiya dani zan fitar dake daga gidan nan, mu fara safarar mutane, idanuwa jawwahir ta zaro sannan tace mukaisu ina?"" tace gidan yankan kanu........."" ai bata ƙarasa maganar ba jawwahir ta some............
[1/17, 7:42 PM] Jamila Musa Ws: ☄
☄☄
☄☄☄
🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥
*WANDA BAIJI BARI BA*
🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥

☄☄
☄☄☄

*AMEENCI WRITER"S ASSOCIATION* 📚✍🏻

*MEELAT MUSA* 🌹

*PAGE 18*

***
*G*anin jawahir ta tafi duniyar suma yasa ta lallaɓa ta sulalle tabar wurin, nan tabar jawahir ita kuma ta kama gabanta,

Jawahir tana nan wurin shanye kamar a banza ƙanxo a faranti, haka kowa yayi ta harkar gabansa kowa abinda ya damesa yake yi ba harka wani kake ba ,

Bayan ta tafi daga wurin har tayi nisa komi ta tuna kuma ?""" dawowa tayi da ruwa taxo ta yayyafawa jawahir birgigi ta miƙe ganin matar yasa jawahir ta sake komawa ƙasa luuuuuuu, ruwan hannunta ta juye mata duka a jikinta, sannan ta yada robar tabar wurin""""""

"""" Jawahir kuka kawai takeyi, tashi tayi cikin sanyi jikin wurin fanfo ta nufa, tana zuwa ruwa ta iba ta wuce, sai kuka takeyi,"""""""", wani wuri ta samu ta tsugunna tayi alwalla , bayan ta gama ta nufi ɗakin su,

""" tana shiga wata tace mata ina kika shigene?""" kamar jira jawahir take tayi mata magana ta fashe da kuka sai kuka take batayi mat magana, wuri ta samu aka fara sallah,

""""Zarto ana gadon asibiti an baza "yan sanda masu gadinta, dan jawahir tace itace kaɗai zata bayar da shedarta, kuma lokacin da aka ibawa jawahir ya kusa cika jawahir tana cikin tsaka mai wahala, dan idan har zarto ta mutu lallai itama da mutu.........,,,,,,,,

****
*I*nnasco ce a tsakar gida zaune kana kallonta kasan tana cikin damuwa da tashin hankali abubuwa sun mata yawa, ga baban jawahir ya kunne wuta ɗiyarshi zai ɗauka ya mayar da ita can gida yayi mata aure wai yarinya ta garɗame duk sa"ointa sunyi aure sai ita,

Kuma inna ta faɗa mashi tana makaranta amma yace aje a cireta a bashi ɗiyarshi tunda ba wani ya haifa mashi ita ba, wannan matsalar itace take damun innas yanxun,

Wayarta dake ringing itace ta farko da ita daga duniyar tunani, tashi tayi ta matsa kusa da wayar ta ɗauka, gaisheta yayi amma bata amsa ba, sai hawaye dake bin fuskarta., inna mi kike ma kuka?""" Sadiq idan har baka zo ka nemo man yarinyar nan ba, ban yafe maka ba, tunda kaine silar jefata cikin wannan masifar,

Sadiq yace subahanallah inna duk miya kawo haka?""" wani irin kukan takaici inna ta saki sannan ta kashe wayarta baki ɗaya,

Jin an kashe waya yasa sadiq sake kiran wayar amma sai yaji ance a kashe take, bakinshi ya taɓe sannan yace inkon Allah bama zata bari in faɗa mata zan dawo ba, banda ma abin inna sai a kama neman yarinya kamar wata allura, tsaki yayi sannan ya ajiye wayarshi lallai idan kika bari na gano saina mayar dake inda na ɗauko ki, mtsww,

***
Yau hankalin jawahir yafi na kullum tashi, gudu takeyi a tsakiya filin gidan yari binta ake amma an kasa kamata, kuma da an riƙeta saita sulɓe kamar wata maciya, saida ta bige wancan tabi ta kan can ta dire, tana gudu tana ihu kamar hauka sabon kamu,

Wai baza ku kamata bane?""",,,,, wani ne yayi magana ranka ya daɗe bata kamuwa, binga ya ciro daga ma"ajinta sannan yace ke da ƙarfi ya faɗa dakata, idan kika sake guduwa zan harɓeki na faɗa maki, tsayuwa tayi ƙam ita batayi gaba ba, kuma batayi baya ba, haka ta tsaya a wurin,

dukansu suka matsa wurin da jawahir take tsaye gabanta yasha kallonshi jawahir tayi shima ita yake kallo, cikin rawar jiki tana zubar da hawaye dole ta baka tausayi ƙiri ƙiri kanaji kana gani ace za,a raba ka rayuwarka?"" ai akwai tashin hankali,,,,

cewa yayi zonan cikin tashin hankali da hargowa yayi maganar, jiki a saɓule jawahir ta matsa kusa dashi ta durƙusa, cewa yayi miƙe, ta tashi tsaye tayi tana kallonsa, yace kuje da ita,

Jawahir tana ji tana gani aka sake kafa mata ankwa, akayi wurin mota da ita, da bingu ake tsaron ta kamar wata wadda ta tashi gari gudu,

Kotu aka nufa da ita dan yaune ranar yanke hukunci, idan zarto ta bayar da shedar gaskiya, jawahir tayi free idan kuwa akasin haka itama za"a sheƙeta kamar yanda ake tunanin ta sheƙar da alhaji zuwa duniyar mutuwa,

Kotu ta cika maƙil da mutane, bakajin motsin komai sai ƙarar fanka, kowa yayi ma alƙali zuru danjin wane irin hukunci zai yanke, a gefe ɗaya kuma ga zarto zaune kamar ɗan bitin bitimi, dan sanda da yace zai harbe jawahir shima gashi,

Alƙali ne yayi magana jawahir lokacin da kika iba mana ya cika miye shedar taki?""" mutanen dake zama gaban alƙali ne ɗaya daga ciki ya miƙe tsaye yace mai girma mai shari"a yana tambayarki waye shedae naki?""",,,,,,

Cikin kuka jawahir tace ranka ya daɗe ni bansan abinda ya faru ba, na dawo daga kasuwa ne, ina shiga gida na samesu cikin wannan yanayin , ina ƙoƙarin fitowa ne saiga "yan sanda suka kamani,

Idan zarto take zaune jawahir ta kalla sannan tace don Allah hajiyas kifaɗa masu tsakani da Allah nidai ki fitar dani daga wannan masifar wallahi ina iya mutuwa kafin a kasheni dan zuciyata cike take da dana sanin haɗuwa dake,

Alƙali ya sake magana a karo na biyu cewa waye shadarki?""", jawahir tace ranka ya daɗe gata can, ta nuna inda zarto take zaune,

Alƙali yace kece shedar jawahir?""" zarto tace nice yamai shari"a, alƙali yace tan da sa hannu a cikin kisan Alhaji bashir ne?""" zarto ta kalli inda jawahir take sannan tace ba itace ta kashe shi ba, amma itace ta haɗani dashi,

Alƙali yace idan ba itace ba waye ya kashe shi?""", zarto tace rezane, kuma yana hannunku, Alƙali ya buƙaci a fito dashi, bayan an kawo reza, alƙali yace wannan ne?""" zarto tace shine,!!!""""",,,,,,,,

Alƙali ya kalli inda reza yake yace kaine ka kashe shine?""" reza cikin maganar daba yace nine, yana yin magana yana ɗaɗɗage baki irin dai yanda "yan tasha sukeyi, alƙali yace ko zaka faɗa mana dalili?""""

reza babu tsoro ya rantafo bayani tun haɗuwa Alhaji da zarto, ya ƙara da cewa kuma shi bada gaskiya ya kuma sake kora ma alƙali bayani, bayan "yan rubuce rubuce alƙali yace wannan koto mai alfarma ta wanke jawahir daga laifin da ake zarginta, dan haka kotu ta sallami jawahir, ai alƙali bai gama rufe bakinshi ba, jawahir ta tattara zaninta ta zuƙa da gudu, alƙali yace a kamato, jawahir tace ranka ya daɗe kuma mi nayi don Allah ta fara kuka?""""",,,

Alƙali yace bakiyi komai ba, amma ai ban baki izinin tafiya ba, jawahir tace to ranka ya daɗe, wuri ya nuna mata tayi tsaye, reza kuma an yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya,

bayan alƙali ya gama kaff kotu kowa ya kama gabanshi alƙali yace ma jawahir ta biyoshi, inda alƙalin yabi tabi bayanshi,

ta wata ƙofa suka bi suka shige, wani ƙaton farlo suka shiga, suna shiga ya ajiye takaddun hannunsa, sannan ya juyo ya kalli jawahir , da hannu ya nuna mata wuri yace ta zauna,

ɗan ɗosana ƙugunta tayi kaɗan ta zauna, shima zama yayi, bayan ya zauna ya kalli jawahir sannan yace miyasa kike dambara?"""jawahir tace waye yace maka ina yi?""" kallonta yayi baiyi magana ba, ita kuma kanta ta sadda ƙasa tana kallon yatsun hannunta,""""",


yace magana nake maki kinman shiru, jawahir tace E danfara kaɗai nake amma bana kisa, sannan kuma inacin bashi bana biya, kuma dan farar da nake ai mutanen suke bani goyon baya, ɗago kanta tayi tana kallonshi danjin abinda zaice,

yace to miyasa kika ce mutane sune suke baki goyon baya ne?""", murmushi jawahir tayi sannan tace, kaga banda doɗewar basira irin ta mutanen zamani, duk abinda nake kai masu nace ana siyawarwa kaza, basa bincike subi abin haka suga da gaske ne?"""""kowa idon sa ya rufe dasan duniya, idan na yanka masu kuɗi sai su bani, idan sun daina ansa nima zan daina yi, shiru tayi tana jiran abinda zaice, kallon jawahir yayi sannan yace,

to gaskiya kiji tsoron Allah duk haƙƙin wanda kaci idan har bai yafe maki ba, kina cikin halaka, jawahir tace to Allah dai yasa mu dace, na gode da nasiha, ta miƙe tsaye, cewa yayi to ai ban gama ba, jawahir tace kaga banda wani bussiness dakai an kamoni ance nayi kisa ka bincika kaga banyi ba, to ka barni ina sauri lagos zan wuce, yace to sauka lafiya, amma kafin ki tafi ina so ki bani number ki plx,,,,,,,,,,,

Ta faɗa mashi ya rubuts sannan ta fice daga Office ɗin, girgiza kai yayi bayan fitar jawahir yace Allah ka shirya mana zuri"a, wannan yarinya mai ƙaranci shekaru ta saka rayuwarta har ƙalla inama anfani?""",,, tsaki yayi sannan yayi save in number nata,

hajiyarta tawa kuwa kai sai ƙara hawa yake, ni kuma ina binta a baga ina busa iska, napep tahau, tasha ta zarce inda take siyar da abinci, bayan taje abinci tasa aka zuba mata taci tayi ƙat, sannan ta buƙaci a bata balances, haka aka tattara kuɗi aka danƙawa jawahir, ta ansa tayi sannan ta nufi gidan data bada ajiyar kayanta,

tana zuwa suka gaisa da matar, bayan sun gama gaisawa jawahir tace hajiyas kinjini shiru kwana da yawa ko?""",,, hajiyar tace E ai naji duk abinda ya faru ina maki jaje Allah ubangiji ya kyauta na gaba, jawahir tace amin,

hajiya tace nidai shawarar da zan baki da kiyi haƙuri ki koma gaban iyayenki, duk abinda zakiyi kiyi a gabansu dan shiga duniya ba naki bane, jawahir tsaki tayi a ranta sannan tace shegiya "yar sa ido, amma a fili sai tace nima shawarar da nayi kenan hajiya, zan koma gida amma kiyi haƙuri kayan nawa dai ki ajiye man zanzo in ɗauka daga baya, hajiya tace to babu damuwa,

Godiya jawahir tayi sannan tayi ma hajiya sai anjima, hajiya tayi mata fatan alkairi, jawahir tana fitowa tsine ma hajiya albarka ta farayi,

tana shegiya koke kika samu kika fara neman kuɗi baza ki bari ba, hada ki koma gida gaban iyayenki yanyan yan yan, tana kwaikwayon maganar ta, tsaki tayi sannan tace banga ubanda zaisa bazanje lagos ba, ko uwar tawa ma cewa tayi Allah ya tsare idan baza kiman addu"a ba, kada kiman baki, tsaki tayi sannan ta murguɗa bakinta, tana tafiya tana sabbatu har ta iso idan Auwal yake tsayuwar jiranta,

Bayan sun gaisa ne, jawahir tace yaushe jirgin namu zai tashi ne?""",,,, Auwal yace mata sai gobe da marece idan Allah ya kaimu, jawahir tace to Allah ya kaimu lafiya, Auwal yace amin,

har jawahir ta juya zata tafi, Auwal yace mata ranki ya daɗe , ina da magana, a fusace jawahir ta juyo sannan tace idan kasan magana ne akan tafiya lagos kada kaman, bansan masifa wallahi kowa an saka man ido sai kace neman kuɗi a kaina farau ne?"""mtsww , Auwal yace Allah ya baki haƙuri, jawahir tace haba bana san surutu wallahi sai anzo an kafa man baki?"""",,, tana faɗin haka tayi gaba,

Auwal ya bi jawahir da kallo, yace lallai sai ya lallaɓa ya ɗauki number hafsat da take bashi labari ya kirata yace ta bashi number gidansu jawahir, dan gaskiya abunta gaba yakeyi idan har ta shiga ruɗe lagos haƙiƙa dawowarta sai Allah,

Jawahir kuwa tana tafiya, gidan data kama haye taje, tana zuwa wanka tayi, ta sake kaya, sannan ta fita, zaga gari,

Bata dawo gida ba, sai 9:12pm, tana dawowa, Auwal ta gani tsaye a ƙofar gidan, jawahir tace Auwal lafiya ?"" mi kake anan ne?""",,,, yace ba komai kawai inaso ki dawone, muyi fira, murmushi jawahir tayi sannan tace to kayi haƙuri abinda nayi maka ɗaxu wallahi haushi ka bani ne, Auwal yace ba komai ai ya wuce, jawahir tace yawwa, to saida safe dan inajin bacci Auwal yace to Allah yasa mu tashi lafiya, ta shige cikin gida shima Auwal tafiya yayi ,

****,

*T*unda safe jawahir tana tashi wanka tayi, sannan tayi shirinta mai kyau, ta kalli kanta a madubi , murmushi tayi sannan ta shafa gefen fuskarta, tace kiyi haƙuri kinji jawahir naisa taxo kusa, muna gamasa da lagos sai mu koma gda musha shagalimu, murmushi ta sakeyi sannan ta fita,

Kasuwa inda take siyar da abinci taje, kasuwa fa ta kafu sosai, kuma Allah yasa ma neman albarka, kuma ana kula dashi yanda ya kamata dan wanda jawahir ta saka "yan kauyene sosai saboda ƙurewa da jawahir tayi wurin san abun duniya, saida taje gidajen iyayensu, sannan ta sheda masu cewa ita bata asara kuma bata san asara ba, idan aka ɓata mata dukiya lallai shanaye zata ɗauka, kuma sun tabbatar ma jawahir da ta kwantar da hankalinta babu matsala,

To tana nan zaune ana ta siye da sayarwa, tana kallon mutane a ɗaɗɗage, ita mai shago, kuɗin jakarta ta fidda ta irga sannan bayan ta gama ta mayar a jakarta,

Auwal ne ya shigo suka gaisa, bayan sun gaisa ne yace uwa ɗakina don Allah ki ara man wayarki na yarda wayana na rasa a ina na yar, in kirata inji, bata kawo ma ranta komai ba , ta miƙa mashi wayar, fita yayi, da sauri ya ɗauki number hafsat sannan ya dawo mata da wayar, ansa tayi tare da cewa ka gama ne?"" yace mata E,

tana nan zaune har lokacin tafiyarta yayi, saboda haka , jakarta data take

12 / 28