Author : MEELAT MUSA Category : African Stories & Novels
man kunne da zancen banza,,,,tana faɗin haka ta kashe wayar, taci gaba da cewa sakarcin banza anje an ganni sai miye?"",,,
shi kuma sadiq tana kashe wayarshi yace zan dawo zakiji a jikinki, wato iskancin naki duk ya tashi daga inda yake kin koma bin malamai, ai sai kije kiyi rayuwarki ce ba tawa ba, duk haryar da zanbi in gyara maki rayiwarki bakiji, duk wamda rai yayi ma daɗi babu kamar maishi, Allah ya shiryeki,,,,,,
****
*A*n gama gyaran gidan su inna komai na gidan sabo aka saka, anfa haɗa gidan sosai, an wani sa "yan aiki a gidan an da masu kula da fulawas da masu gadi an wani maida innas da babas "yan gatan tsofaffi, amma ba,a fitarwa jawahir da ɗaki ba, sai maganar gidan ake sosai duk inda ka wuce sai kaji ana maganar gidansu innas, sadiq ya gatanta iyayenshi sosai,,,,
***
*B*ayan sati biyu da gama gyaran gidan su hafsat da sadiya sukaxo, suka nemi alfarmar wurin inna zasu fara rabon kayan biki,,,,,, inna tace to nidai bani nake hanata fita ba, sadiq ne., jawahir tace babu wani sadiq kawai malama idan kin barni ki barni yana can yasan wata wainar da ake toyawa ne?"",,,,, nasan lallaɓawa zakiyi ki faɗa mashi, inna tace bazan faɗa ba, Allah ya bada sa,a,,,,,,,
Bayan inna ta fita ne, jawahir tace haba ni bansan wannan abun yanxun nan zakiji ta lallaɓa ta faɗa mashi, sadiyya tace hafsat kirashi ki nemi alfarma,,,,, hafsat tace to bara muji kinsan shima wani lokaci sahun keke ne,,,,,,,,,,,
Kiran sadiq ta fara, harta tsinke bai ɗauka ba, sai daga baya ya biyo kiran,,, hafsat ta ɗauka, suka gaisa tace mashi ya london?""",,,,,,,yace lafiya qalau,,,,,, hafsat tace don Allah yaya zamu fara gayyar biki shine nazo neman alfarma, nayi ma jawahir magana tace in tambayeka,,,,,, dariya sadiq yayi sannan yace bani ita,,,,,,, miƙawa jawahir wayar tayi,,,,, gaishe shi tayi, sadiq yace bazakije ba, jawahir tace don Allah ka taimaka man , yace idan na dawo zankije amma idan ban dawo ba, bazaki ba,,,,,, jawahir tace kai kada Allah yasa ka bari, ta kashe wayar,,,,,,,,
Hafsat tace kema miye haka don Allah?"",,,,tsaki jawahir tayi sannan tace ni banso inyi ta lallaɓa mutum yana raina man hankali, idan lokaci yazo kawai kuxo mu wuce,,,,,,,
Haka dai sukayi "yar firansu, daga baya suka tashi jawahir tayi masu rakiya har bakin get inda suka ajiye motarsu, bayan sun tafine, itama ta koma gida,,,,,,,,,,,,
***
*A*n fara shagalin bikin hafsat, don haka jawahir anje an ciro kuɗi a banki tayi anko tayi komai, amma tunda aka fara shagalin bikin bata sa anko ba, sabbin ɗinkuna tayi dasu ta shagale, ta raƙarƙashe abunta,,,,,,, kuma tunda aka fara shagalin biki jawahir dama gidansu hafsat ta koma da zama, sai yau da aka gama bikin ta dawo gda,,,,,,,,
***
*A*bin jawahir kuma ya sake turewa don yanxun abinda ta koya ma kanta bin malamai don neman mijin aure, saboda duk ƙawayensu sai aure sukeyi, ita kuwa ta rasa wanda zaice yana santa, bare ya aureta,,,, hassana kullum ƙara ɗorata takeyi, sai zuga ta takeyi, islmaiyyar ma ta daina zuwa,,,,, kuma sun kusa sauka, babu juyin duniya inna batayi ba ta koma amma ta murje idonta, haka ta haƙura ta kawo ido ta zubawa jawahir,,,,,,,,
***
*K*wanci tashi babu wuya a wurin Allah, yau shekarar sadiq huɗu da tafiya,,,,,,,,,, kuma har yanxun yaƙi ya dawo,,,,, baba kuma yace lallai saidai yayi aure dan zaman nan ƙasashen waje baida daɗi idan mutum baya da mata, sadiq abinda baba yacewa sadiq shi har yanxun bai samu matar da tayi mashi ba, baba yace to ina ita hadizar ne?"",,,,sadiq yace baya santa ai dama baice zai aureta ba,,,,,,, baba yace to yanxun yaushe zaka dawo ne?"",,,,, sadiq yace saura shekara ɗaya ya dawo, baba yace to lallai bazai yuwuba, haƙiƙa sai yayi aure,,,,, sadiq yace baba ya bashi nan da sati ɗaya zaiyi shawara, baba yace to idan bakayi shawara ba, ni zan yanke hukunci, sadiq yace to, suna gama wayarne baba yasa aka kira masji jawwahir,,,,, bayan tazo ne, yace mata to lallai kema ki fidda mijin aure,,,,,
gaban jawahir ya faɗi das das dasss, lokaci guda idonta ya kawo hawaye, sannan tace babs aini yarinyace ban isa aure ba, baba yace da,a kauye kike yanxun ai anyi maki aure,, jawahir tace nidai babs saina sauke alqur"ani sannan, inna dake gefe tace abinda kin daina zuwa makarantar, jawahir tace nidai don Allah a janye maganar aure yanxun,,,, baba yace sabo mi?"",,,,,jawahir tace saboda banda mai aurena,,,,, murmushi baba yayi sannan yace idan dai mijin aurene kin samu,,,,, tashi kije,,,, miƙewa jawahir tayi tabar farlon,,, tana fita da gudu ta nufi ɗakin innas,,,,
Tana fita, inna tace shi kaɗai zai iya saita ta, baba yace amma kullum sai an kawo ƙara ko?"",,,,, inna tace nidai ai gara ta tattara dan bakiji yanda ake man maganar na riƙe yarinya taƙi aure ba,,,,,,,, baba yace to ai sai ayi mata,,,,,
Jawahir kuwa tana zuwa ɗaki wayarta ta ɗauka ta kira hassana, ta faɗa mata yanda sukai da innas , ,,,, hassana tace to nidai shawara zan baki kada ki sake ki yadda ayi maki airen dole,,,,,jawahir tace shin ai banma samu mijinba, hassana taci gaba da ɗora ta tare da bata shawarar banza, wanda jawahir taga lallai haka shine mafita,,,,,,,,,
***
*B*ayan wasu kwanaki ne, baba ya sake tuntuɓar sadiq maganar aure, yace shidai bai samu wanda tayi mashi ba har yanxun, baba yace to ni na samar maka,,,, sadiq yace wace ce?"",,,baba yace jawahir,,,,,da sauri sadiq ya miƙe tsaye yana cewa baba ka rufa man asiri a aika gdansu hadizar,,, baba yace saidai ka aureta daga baya, amma sati mai zuwa zan ɗaura aurenka da jawahir,,,, da sauri sadiq ya ciro tissue dake gefenshi ya fara goge zufa,,,,, shi kuma baba ya kashe wayarshi,,,,,
sadiq da sauri ya fara kiran number hadiza,,,, bayan ta ɗauka suka gaisa, sadiq yace kince kinaso na ba?"",,,,,, hadiza tace E, sadiq yace kin shirya aure yanxun?"",,,,hadiza tace sosai ma,,,,,,, sadiq tace idan Allah ya kaimu ƙarshen satin nan zanzo,,,,,,, tace yawwa, yana kashe wayarshi hadiza ta tashi ta fara murna tana rawa, dan farin ciki,,,,
lokacin da maganar auren sadiq taxo kunne jawahir ɗan ƙaramin hauka tayi, saida ta daka tsalle ta some, kamar mai kamun aljannu, hankalin inna ya tashi sosai, amma baba yace tayi banza ta ƙaleta,,,,, jawahir kuwa an daina cin abinci an shiga tashin hankali sai cewa takeyi an cuceta, yamanza,ayi anhaɗata aure da sadiq?"",,,,,, nanma idan yan dukanta babu mai bashi haƙuri kawai an gaji da ita, so ake ta mutu,,,,,,,
ta daina wa kowa magana a gida,,,,, wannan dalilin kuwa baisa aka fasa ci gaba da biki ba,,,,,,,,,,, sadiq ya kira jawahir yace mata wallahi ko tasa a fasa auren nan ko kuma idan ta bari akayi auren saiya kasheta, kindai san halina na faɗa maki?"",,,,,, wani irin kuka jawahir ta saki, sadiq yace wallahi yarinya kuka ma yanxun kika dan aurena dake kamar mutuwace na faɗa maki, idan har kina san ci gaba da rayuwarki kada ki sake ki bari a aura maki na faɗa maki wallahi,,,,,,,, yana faɗin haka ya kashe wayarshi,
wani irin ihu jawahir ta saki sannan ta faɗi ƙasa tayi ta harbebe , amma baba yace duk abinda zatayi kada inna ta kuskura tayi mata magana,,,,,, ita kaɗai takeyin hauka babu mai tanka mata,,,,,,,
duk wanda yaga jawahir yasa tana cikin tashin hankali tabi ta rame tayi baƙiƙƙirin,,, duk ta hirgice kuma ga bala"in kulle kwata kwata bata fita, bare taje tasan mafita,,,,,ta kira hassana tace taje wurin malam ta faɗa mashi halin da ake ci, amma hassana tace malam yace sai ya kwanta da ita, sannan aikin zaici,,, haka dai ta haƙura tasa ma ranta salama, dan duk wata hanya da zatabi tabi batada mafita,,,,,,
Haka ta kira hafsat ta faɗa mata, hafsat ta tausaywa jawahir sosai,, sannan ta bata haƙuri da shawara, amma ganin zatayi mata wa,azi yasa ta kashe wayarta,,,,,hafsat da kanta ta kira sadiyya ta faɗa mata,,sadiyya tace towai miye?"",,,, hafsat ta fara bawa sadiyya irin azabar da sadiq yake wa jawahir, amma cewa tayi to wai miye a ciki don Allah?"",,,,,,,,sadiyya tace Allah ya kaimu zamuje musha shagalin biki,,,,,,,
***
*Y*au ne daren ɗaurin auren jawahir da sadiq umar azuba,,,,,, sadiq yana can hankalinsa yaƙi kwanciya,,,,, kuma baba yayi juyin duniya ya dawo amma sai yace bai gama abinda yake ba,,,, ba wani gayyar dangi akayi ba, amma an sanar da baban jawahir da larba duk sunxo,, sai ƙanwar maman su jawahir wato kuma kanwar inna, hadiza,,,,, haka dai ake hidimar biki babu bara ba aboki,,,,,
Haka akayi hidimar biki babu ango, jawahir kuwa tana cikin tashin hankali,,,,, bata da mafita, haka ta sanya wa ranta salama,,,,, kuma bata faɗa ma hafsat ranar aurenta ba haka sadiyya ma bata sani ba,,,,,,,
bayan an gama biki da kwana ukku duk kowa ya tattara ya koma gida,,,,,, gida ya rage daga innas sai babs , jawahir dai tana ta fuskantar damuwa,,,,,,,,,,,,,,,
Hankalin jawahir ya ƙara tashi sosai jin ance sadiq gobe zai dawo,,,,,, jawahir tana cikin damuwa sosai da tashin hankalinta yafi na kullum tshi sosai,,,,,,,,bata san yanda zasu ƙare da sadiq ba idan yaxo,..................
[1/17, 7:45 PM] Jamila Musa Ws: ☄
☄☄
☄☄☄
*WANDA BAIJI BARI BA*
*AMEENCI WRITER"S ASSOCIATION* 📚✍🏻
*MEELAT MUSA*
*PAGE 26*
***
*J*awahir ce kwance saman gado tana ta tunani wanda ita kanta batasan dalilin yinshi ba,
Inna ce ta shigo ɗakin tare da sallama, amma jawahir ko inda take bata kalla ba, dan gaba ɗaya haushin kowa na gdan takeji,
Ga takura an hanata fita, kuma tayi waya da hassana tazo ta anshi kuɗi taje wurin malam dan a murtsike aurenta da sadiq amma har yanxun shiru kullum hassana kuɗi take ansa amma har yanxun babu wani canji,
Inna dake tsaye tace jawahir kije inji malam, cikin jin haushi tace naji, inna cikin sanyi tace jawahir baki lafiya ne?""
Murguɗa baki tayi sannan tace ai saura hauka zan fara,
Inna tace subahanallah haukanmi kuma?"" jawahir ta fashe da kuka sannan tace kalli can, ta nuna wani wuri da hannunta, inna ta kalla,
Jawahir tace kinganshi?"" inna tace waye?"" jawahir cikin kuka tace aljanine, inna cikin zabura tace aljani kuma?""
Jawahir tace Eh, tunda aka ɗaura man aure da sadiq yake kwana nan ɗakin yace idan har sadiq bai sakeni ba, shine ajalina,
Dan shine yake sona kuma shine zai aureni, inna tace ke har kin fara ganin aljani da idonki?"
Jawahir tace gashi kema kin ganshi da idonki, inna tace ni ban gani ba, jawahir ta tashi ta miƙe, tsaye saman gado sannan ta riƙa nuna wani wuri da hannunta anan aljanin yake,
Tsaki inna tayi sannan tace bari inje in faɗawa malam, miƙewa tayi sannan ta fita daga ɗakin,
Tana fita jawahir tayi tsaki sannan tace fitinaniyar tsohuwa mai ɗa ɗaya, tsaki ta sakeyi sannan ta koma ta kwanta,
Inna kuma tana zuwa ɗakin baba ta faɗa mashi abinda jawahir tace, tsaki yayi sannan yace barni da ita, tunda ma abin nata ya zama iskanci yau idan Abubakar ya dawo wallahi bazata kwana a gidan nan ba, har nayi rantsuwa,
Naso tazo da na gaya mata abinda takeyi, inna tace haba malam kayi haƙuri kada ta tafi yau, baba yace wallahi sai ta tafi,
Kinma san abinda takeyi yarinya nan?"" ashe hassana ɗiyar gidan malam nuhu take ba kuɗi tana zuwa wurn malamai wai a raba aurenta da Abubakar,,,,
Idanuwa inna ta zaro tare da dafe ƙirjinta, tace jawahir ɗin da kanta?"" baba yace cikin unguwa ake faɗi,
Kuma kinsan bata mata ƙarya, tunda lokacin da batayi ba batace tayi ba, to idan Abubakar ya dawo sai ya tafi da ita can kuma ya rabata da hassanar,
Inna tace gaskiya jawahir halinta sai ita, baba yace barta dani take zancen,
Baba yace kima ce mata ta tashi ta tattara duk tsiyar da tazata tattara kafin ya iso,,,
Inna tace ka faɗa mashi ne?"" baba yace Eh, nayi magana dashi zai kawo man sakarcin banza, na faɗa mashi wallahi yau jawahir bata kwana gdan nan,
inna tace to, adaidai lokacin da take miƙewa ta fita tabar ɗakin ba tare da ta sake magana ba,
tana zuwa ɗaki tace wa jawahir malam yace maza ki tattara ya naki ya naki, kafin zuwa sadiq, jawahir tace ina zanje kuma?""
inna tace gdanki zaki, har yanxun tana kwance kuma bata juyo ba, tace ina ne gdana?""
inna tace gdan mijinki, hmmm jawahir tace tare da ci gaba da cewa yo waye yace maki ina da aure?"
inna tace ban gane ba?"" jawahir tace ke a garinku haka ake aure?""
ke har kin yadda nayi aure?"" aure ba sa biki, babu lefe , ba taron mutane , ba party, ba,a raƙashe ba, ba,a girgije ba, babu wani tsalle ko ɗaya, sannan uwa uba ba miji, wai ni za,ace amarya?"" yo ko zawara ce anyi man wannan wulaƙanc sai kace ɗiyar da bata da galihu?""
Inna tace to idan kinje can gidan naki kin faɗawa shi sadiq ɗin, jawahir juyowa tayi tana kallon inna sannan tace innas fita harkata ,
inna tace na fita, amma malam yace duk abinda kike buƙata maza ki tattara komai anjima zaki tafi gdanki,
jawahir dariya tayi sannan tace ina "yan ɗaukar amaryar ne?"" inna tace zaizo, bada daɗewa ba, jawahir tace ke saboda Allah ki taɓa ganin wannan shirme irin na babs ne?""
tsaki tayi sannan tace ni banma san abinda nayi ba, inna bata sake magana ba, ta fita tabar ɗakin,
jawahir kuwa cewa tayi babu inda zanje,,, baba daya fito daga ɗakinshi yaji maganar jawahir ɗakin inna yayo ,
yana shiga, kallom jawahir yayi sannan yace sai kin tafi yau yauɗin nan wallahi, ashe har kina da kuɗin bin malamai,
duk tarbiyyar da ba taki ba, kin ɗauko ta kin ƙaƙabawa rayuwarki saboda san zuciya, to ki tattara zaizo ya tafi dake, tayi shiru,
baba saida yayi mata tatas sannan yabar ɗakin, yana fita ta fasa wani irin ihu sannan tace idan ina yadda Allah ya tsinan wannan ai zalinci ne,
nine za,ayi wa aure haka sai kace wata shegiya, bikin kowa ana party a lalace sai bikina za,ayi bikin "yan kauye?""
kowa bikinta taji daɗi saini da ba,a ƙauna, ban taɓa ganin bikin da babu sadaki ba sai nawa,,,,
Babu wanda ya sake tankawa jawahir haka tasha haukanta, dan iskanci tana sakin maganganu yanda ranta yake so amma babu wanda ya tankawa jawahir,
Tsaki tayi sannan ta kalli agogo 9:30pm, wani irin kuka ta sake saki, sosai, da gudu taje ta hau saman gado saida tayi kukanta ta gaji sosai, sannan ta sauko,
Tana saukowa taje ta ɗauki wayarta ta kira hassana, bayan hassana ta ɗauka jawahir cikin bala,i da masifa, da nuna tsananin ɓacin ranta, kamar hassana tana kallonta,,,,,
Tace ke dan uwarki shine kika zo kika haɗani da babs ko?"" to duk ranar dana ganki wallahi saina ci uwaki sosai na faɗa maki, hassana tace jaka idan kin isa kixo yanxun ki sameni,
Mai baƙin hali "yar danfara, mai cin bashin tsiya,,, jawahi tace naci kona uwarki ko na ubanki naci bazan biya ba, kuma inda na gode ma Allah aina bari, kefa baki da aiki sai bin maza "yar iska maiyin cikin shege,
Hassana tace naje nayi iskancin jikinki ko nawa?"" kema ai ban hanaki kiyi ba, kuma ni nake bayarwa ayi iskancin a bani kuɗi, ke kuma saida kici na wani, kuma da kike cewa kin bari ai azaba kikaji ba dan Allah kika daina ba,
jawahir tace gafara can jaka banza mai wari ko wanka bakiyi,, hassana tace naji, kuma idan kin haihu ga uwarki da jini ina nan ƙofar gidanku ki fito ki sameni,
jawahir tace idan kin isa ki shigo ciki, hassana tace bazanzo ba, amma kixo ki sameni, jawahir tace da yake kinsan duka zan maki shine bazaki zo amma kin iya zuwa kiyi munafinci, shegiya karuwa, ta ashe wayrta,,,
Jin motsin mutum bayanta yasa ta juyawa da sauri,,,, murje idon ta tayi cikin sauri ta sake murje idon ta, tare da girgiza kanta, ta sake rufe idon ta murza ta buɗe,,,,, har yanxun tsaye yana mata wani matsiyancin kallo, wanda yasa taji cikinta yana juyawa,
cikin rawar baki tace yaya,,,, yace keda wa kike zage zage?"" cikin rawar jiki tace ba kowa, ta juya zata shige ciki yace zo nan,
cikin kuka jawahir tace don Allah kayi haƙuri,,, tayi ciki da gudun tsiya, shima a hanzarce ya bita, saura kaɗan ta shige ya fizgota, wani zazzafan mari ya sauke mata tare da cewa munafika wuce mu tafi,,,,,,,,,,
Cikin ruɗewa jawahir tace ina zamu?"" yace ban sani ba, duk ta sake ruɗewa, tana kallon sadiq, dan bata san ina zasu ba""
Ganin yana matsowa kusa da ita yasa ta fara ja baya, dan gaba ɗaya yayi mata wani iri, da sauri ta jawo hijabinta ta saka, taa cewa gata, yace muje,,,,
Itace tayi gaba yana bin bayanta, tana fita, tayi hanyar ɗakin baba, yace ina zaki nan?"" tsayuwa tayi, bata ci gaba da tafiyar ba, yace muje, yayi gaba tabi bayanshi,,
Suna tafiya tana kallon bayan sadiq gabanta sai faɗuwa yakeyi, ko tunanin mi takeyi ne?""
suna isa wurin motar ya miƙa mata makullin mota,, cikin kuka tace mi zanyi dashi?"" yace muje,,,,,,,,,
ansa tayi ta buɗe motar , shiga yayi sannan ta shiga tana kuka, sai ƙara kallon gidan takeyi, a ranta kuma sai Allah ya saka mata take cewa, tunda take bata taɓa jin wannan rainin hankalinba wai amarya takai kanta gidan miji,
Tsaki tayi a bayyane, ko inda take bai kalla ba, wayarshi yake yi, tare da cewa gani nan zuwa gdanku kiyi haƙuri ,,,,,,,
jawahir saida suka fita daga gidan ta fara tafiya ta fice daga santar anguwansu, a bakin titi tayi tsaye da mota, sannan tace ina zamu je?"" da hannun ya nuna mata,,,,,,,, tabi hanyar,,,,,,,
ita kuma inna tanajin tafiyar su sadiq ta fara kuka,,, ɗakin ta tashi ta taho, tana shiga duk taji ɗakin yayi mata wani iri,,,,, kuka inna takeyi sosai tanajin kewar jawahir,
Ɗaki ta shiga, a gefen gado ta zauna sannan ta saki wani irin kuka,,,, sai taji dama anan sukayi zamansu,,,,,,, duk taji babu daɗi, shima baba yaji duk wani iri, kuma yayi wa sadiq faɗa sosai, amma bai faɗa mashi tana tura hassana wurin malamai ba,,,,,,,
tafiya sukai sosai, har suka shiga cikin wata unguwa da jawahir duk yawonta bata taɓa zuwa ba, wuri ya nuna mata tayi parking, sannan ya fiddo wayrshi, yayi kira tare da cewa gani a ƙofar gida,,,, yace okey ciki zamu shigo?"" to ba damuwa, ya kashe wayar