Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

WANDA BAIJI BARI BA Rayuwar Ƙarya da Nadama by MEELAT MUSA

Author :  MEELAT MUSA Category :  African Stories & Novels

Chapter   4 / 28

9K to 12K   out of 83K words

yace yawwa zo inji ina kika shige kwana biyu banji ki ba, wai ajiyar zuciya tayi sannan tabi bayanshi, a bakin motar shi suka tsaya , alhaji yace ta bashi numberta haka ta faɗa mashi ya rubuta, shine ma haɗuwar jawwahir da alhaji,


abinda yasa ma tarayyar tasu tayi sanyi saboda shi alhaji mabuƙaci ne sosai ma"ana manemin mata ne, to isakncin yafi ƙarfin na jawwahir ita dai bata sata, sannan bata sallah amma kuma bata zina, kawai dai aikinta ƙarya shishigi ga masu kuɗi, sai fa *4 1 9* dan ta kure wajen iya danfara, wannan kenan,

Kullum alhaji yana ɗana mata tarko amma tsallakewa take, ko tv inta daya karɓa ya bata miliyan ɗaya yasan ƙarya take babu wata ƙasa da ake neman ta kawai kallonta yake dan yayi alƙawari zataji a jikinta ,

Jawwahir a gajiye ta iso gida babu ko sallama kamar yanda ta saba, tunda daga zaure ta cire ɗan kwalin kanta ta shigo ciki, baba yana zaune da buta a gabanshi da lama alwallah zaiyi a gefe kuma sadiq ne sai innasco data zabga tagumi kamar wadda aka aiko ma saƙon mutuwa,

haka ta raɓa su zata shiga ɗaki sadiq yace ke zo nan dan ubanki, tsayuwa tayi ba tare da ta juyo ba, sadiq ya daka mata tsawa yace bakijk ina magana ne?"" jawwahir ta juyo ta ɓata rai sannan tace idan naji miye?"" yace ke har kin isa kiga baba kice ya daina nuna yasanki a cikin mutane?"" tsaki jawwahir tayi sannan tace waida saboda wannan abun ne kowa yaxo ya zauna?""

Shi baban ba cewa yake dama mutuwa nayi ba,shine yanxun dan anga Allah yayi man rufun asiri sai azo kuma a fara man hassada?"" nace ban ganeshi ba sai mi?"" ban ganshi ba kuma bazanma ƙara gane kowa ba, idan anji haushi a ƙoreni daga gidan, tsaki tayi sannan ta shige ɗaki, tana gunguni,

sadiq ya tashi da ɓacin rai ya shiga cikin ɗakin kafin ya isa wurinta har ta ɗaga rigarta ta zaro wata irin wuƙa, ta cireta daga cikin gidan ta, sannan tace idan bakayi hankali ba wallahi niɗin nan tana bubbuga ƙirjinta to wallahi nice ajalinka,

tayo kanshi sadiq yayi tsaye, dan ta ɗauka zai matsa ne, tsaye yayi yana kallonta, wuƙar ta maida cikin gidan ta sannan ta ɗaga rigarta ta sukata inda ta ɗauko ta, sadiq yace kalma ɗaya ta fita a bakinki wato ki daina cewa kece ajalin mutum idan kuwa ba haka ba wata rana wannan kallamar itace farkon abinda zai hanaki zaman lafiya, idan kunne yaji jiki sai ya samu sassauci , wanda kuma baiji bari, hausawa sukace bazai ƙijin hoho ba,

dan haka bada kuɗin mutumin da kikaje kika ce ya taimaka maki an kwantar da inna asibiti zaki siya mata magani, jawwahir tace ko bala"i da kwabashui yaxo a wurin baza ta bayar ba, sadiq yace haka ne abun?"" tace gashi ma kaji,


kusa da jawwahir ya matsa daidai moƙoshinta ya riƙe gam tun tana iya ihu har ta fara wani irin gurnani, inna da sauri ta shigo ɗakin ta riƙe sadiq tace ya saketa kada ya kasheta yace wallahi ko ranta zai fita bazan saketa ba sai ta bada kuɗin mutane, lokacin da wani kunfa ya fara fitowa daga bakin jawwahir, inna tace saketa malam ta fara kiran sunan baba, tana cewa taho za"ayi ɗanyen aiki, da gudu ya shigo ɗakin inda sadiq yake rike da wuyan jawwahir yaje yace sakar mata wuya, sadiq yace baba don girman Allah kabar yarinyar nan ai tace ko bala"i yaxo baza ta bayar ba, ka barta in nuna mata ni nafita masifa a lokacin da jawwahir ta fara shure shure idanuwan sadiq gaba ɗayansu sun canja sun koma jajaye saboda tsabar masifa, yace zaki bayar ko sai na zaro maƙonshin kowa ya huta, jawwahir ta riga tayi nisa bata jin abinda sadiq yake cewa wasu hawayen wahala suka fara gangarowa daga cikin idon ta, jikinta ya saki gaba daya sannan sadiq ya saki maƙoshin jawwahir ta faɗi ƙasa riffff,

inna ta fara cewa ka kasheta ka huta, zaka jawo mana bala"i a gari ace ka kashe ɗiyar mutane, baba shima cikin kuka yace ɗiyar mutane ka kashi sadiq?""

lokacin daya kalli inna yace mata maza taje ta kirawo ja"afar yakaisu asibiti, sadiq cikin ɓacin rai yace wallahi babu inda za"aje da ita sai ta mutu kowa ya huta, inna ta ɗaga hannunta ta sauke ma sadiq a fuska sannan tace ni zaka jowowa wulaƙanci a cikin mutane?"" sadiq yace ai wannan halin da kuka saka mata ido takeyi shine abinda zaisa ace kun cuci rayuwarta , za"ace da iyayenta suna raye da bazasu bari ta shiga wannanan halin ba,

Shi icce tun yana ɗanye ake lanƙwasa shi , kullum a ƙofaɗ gidan nan kamar wani gdan shara"a , to wallahi yau ko ta farfaɗo ta farfaɗo a wahala idan kuma ta mutu ta huta ma rayuwarta, ,

inna da baba kuka kawai suke a gaban jawwahir suke durkushe, baba ne yace ma inna ta ibo ruwa su gani, tana miƙewa sadiq yace babu wanda zai shafa mata ruwa gara ta mutu mutuwarta shine kwanciyar hankalin kowa,...........................
[1/17, 7:35 PM] Jamila Musa Ws: ☄
☄☄
☄☄☄
🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥
*WANDA BAIJI BARI BA*
🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥

☄☄
☄☄☄

*AMEENCI WRITER'S ASSOCIATION* 📚✍🏻

*MEELAT MUSA* 🌹

*PAGE* 8

*****

*I*nna tace bani hanya kafin ranka ya ɓaci sadiq yace inna don Allah kibar yarinyar nan wuce ni wallahi duk na tsani rayuwarta ko ganinta bansan yi wallahi, inna wuce sadiq tayi ta nufi wurin tukunya ta ibo ruwa sannan ta dawo ɗaki , baba ya anshi ruwan ya fara shafa ma jawwahir ta fara sauke ajiyar zuciya, yaci gaba da shafa mata ruwan saidai tace ummmm ummm hawaye nabin idon ta, a hankali ta fara buɗe idonta ta fara ganin baba ya kasu kusan biyar haka ta riƙa ganinsu biji biji sannan ta maida idonta ta rufe, inna ce tace tashi in kamaki ki koma saman gadon, jawwahir tayi banza da ita, kuma taji ba bataji ta,

Inna da baba tashi sukai suka fita daga ɗakin ita kuma jawwahir tana jin sun fita, ta fara kuka tun tanayi kuka a hankali har ta fara ɓarke baki tana ihu kamar mahaukaciya, sadiq daga waje yace idan baki ma mutane shiru ba wallahi nazo jikinki sai ya baki labari munafikar banza, cikin kuka da jin haushi jawwahir tace anje anyi kuma saina yanka ka gida ukku,

Sadiq yace taso waye ya baki haƙuri, tasowa tayi jiri yana ibarta ta fito daga ɗakin tana cewa tunda ba"a sona yau saina faɗa cikin rijiya, inna ta fito da sauri daga ɗakin baba tana cewa kiyi haƙuri jawwahir , jawwahir tace wallahi saina faɗa tunda ba"aso na a gidan nan, sadiq ya taso daga inda yake zaune yaje ya kamo hannun inna bayan ya riƙe hannun ta sannan ya kalli jawwahir yace faɗa ba"asanki ai baƙin halinki yaja maki maza ki faɗa idan kin faɗa ance maki zamu daina rayuwane,

tsaki jawwahir tayi sannan tace to sake dukana, yace ai kin daku tunda kin leƙa lahira kin dawo, kuma wallahi da safe ina zuwa kafin ma inyi maki magana da kin ganni ki kawo man kuɗin mutane idan kuwa ya jinjina kanshi, tsaki jawwahir tayi sannan tace kuma wallahi koba yau ba saina faɗa rijiya, sadiq bai sake magana ba, haka taja jikinta ta koma ɗaki,

tana shiga ɗaki a gajiye ta haye saman gado, bacci wahala yayi gaba da ita, shima sadiq yayi ma inna saida safe , inna tayi mashi fatan alkairi,

****

*D*a safe inna bayan ta gama haɗa abinda zasu ƙarya , bayan ta gama kammalawa taje tayi wanka saboda sauri take zataje kauyensu, saida ta gama shirin ta tsaff sannan ta tashi jawwahir tace ta tashi ita zata taje anguwa ta kula da gida kuma kada ta sake ta fita, wahalar da jawwahir tasha jiya wurin sadiq ma bata barin ta fita ko ina, dan haka inna ta ɗauki hijabinta da jakarta ta fice daga gidan,

jawwahir na ganin inna ta fita kuma tace kada taje ko ina, ita dama abinda ba"aso shi takeyi dan haka lallaɓawa tayi ta tashi taje ta ja, ruwa ta shiga wanka, tana fitowa daga wanka taga sadiq tsaye ƙofar ɗakin inna yasa hannunwanshi cikin aljihun wandonshi, cikinta taji ya fara wani gulllll gulululu, dan jawwahir muguwar matsoraciya ce, jikinta ya fara ƙarma ita tsoronta ma kada ya kasheta dan jiya da babu inna da baba yanxun data can ta baƙunci lahira,

inda take tsaye ya kalla yace zo nan munafika, jawwahir tace ai yanxun zan ɗauko maka kuɗin lokacin daka shigo ina wanka ne, yace wankan kin banza, do nan nace jiki na ƙarma idanuwanta sun cika da hawaye kwandon ta ajiye a wurin da take tsaye ta fara tafiya kamar wanda kwai ya fashe mawa a ciki, ta bayanshi tayi niyyar bi ta raɓa ta wuce ɗaki ,

Ya daka mata tsawa yace ba nace kixo nan ba, jiki a sanyaye tace ai zowa zanyi, yacd to ki bari in sake maki magana, ajiyar zuciya tayi sannan ta zagayo ta gabanshi ta tsaya, yace sa idonki nan, jawwahir ta kasa ɗago idonta, yace bakiji ina maki magana ne?"" nace ki saka idonki a nawa, yayi mata maganar cikin tashin hankali, jawwahir ta ɗaga idonta ta kalli sadiq, wani irin tashin hankali da tunda tazo duniya bata taɓa jin irinshi ba sai yau, tsoro ne ko mi?"" abinda tayi ma zuciyarta tambaya kenan, da sauri ta sauke idon ta ƙasa, yace mi nace maki?"" ta sake ɗago idonta ta kalleshi abinda taji da farko shi ta sake ji yanxun, da sauri ta sake sauke fuskarta ƙasa yace wallahi idan na sake maki magana uwaki zakici, jawwahir ta fara kuka tace nidai don Allah kayi haƙuri kuma ai zan baka kuɗin ka bari inje in saka kayana,

Sadiq yace dama kina da kunya ne?"" sakaran banza ballagaza wanda bata da tunani kazamar banza, ya sake daka mata tsawa maza kije ki kawo man kuma idan na irga ukku baki kawo ba sai na zaneki sannan in bar gidan nan, jawwahir jiki na ƙarma ta shiga ɗaki da gudu tana cewa wayyo Allah na bani nidai ba"aso na, kuma Allah sai ya saka man, sadiq yace mi kika ce?"" a lokacin daya shigo cikin ɗakin,

Da gudu ta haye saman gado ta ɗauko jakarta, ta buɗe, ta fiddo kuɗin, gaban sadiq ne ya faɗi ganin kuɗin da jawwahir ta fiddo da sauri ya cire glass ɗin idonshi yana zaro idanuwa, shima saman gadon ya hau hannunshi yakai ya karɓi jakar hannunta, yana cewa ke iskancin naki har ya kawo nan?""

Jawwahir tace ai ba kuɗina bane , ɗaure fuska yayi sannan yace na waye?"" jawwahir tace na ƙawata ne, yace wace ce ƙawar taki?"" tace baka santa ba, yace ai yau zansan ta, jawwahir tasan halinshi yana iya tisa ƙeyarta gaba yace sai takaishi gidansu ƙawar don haka ta fara tunanin wace ƙarya zatai mashi,

Yace wai ke don Allah miyasa mahaukaciya ce?"" ina kika samo wanann kuɗaɗen?"" jawwahir tace bashi na ciwo su, sadiq cikin sanyin murya yace keko mi zaki dasu?"" jawwahir tayi shiru, yace dake nake magana, hawaye ya fara zubowa daga idonta dan tasan kashinta ya bushe, ƙoƙarin sauka take daga saman gadon shi kuma ya riƙe mata ƙafa gam, yace dake nake magana kada ki ɗaukini sakarai, jawwahir tayi shiru, kam abin ya kufular dashi wani irin mari yakai mata harsai da kanta ya daki bango, sannan yayi magana da ƙarfi yace gidansu uban wa kika samo kuɗin nan nace,?"" jawwahir cikin kuka tace rancensu nayi, wani marin ya sake kai mata saida bakinta ya fashe, sannan ya sake cewa a ina kika samo?"" yana magana yana zaro idanuwa,

hankalin jawwahir ya gama tashi dan taga sadiq ya koma kamar bashi ba, cikin kuka tace don girman Allah yaya kayi haƙuri tana haɗa hannuwanta, yace yaya ma kenan?"" wato yau nine yayan naki?"" zaki faɗa man ina kika samo kuɗin nan kosai na kasheki, ya ƙarasa maganar cikin tashin hankali gaba ɗaya yanayin sho ya canja, idanuwanshi kamar an hura masu wutar azaba, jawwahir jikinta sai ƙarma yake tace kayi haƙuri kada ka kasheni don Allah ina san rayuwata wallahi, hawaye suka ci gaba da kwararowa daga idon ta ga jini sai zubowa yake inda ya fasa mata,

yace jawwahir na tsani rayuwarki kema kanki na tsaneni kuma idan baki faɗa man gaskiga ba yau basai gobe ba saina kasheki, kamar yanda kike cewa kece ajalina yau nine zanyi ajalinki, hankalin jawwahir ya gama tasho dan ta gama tsorata da sadiq , ta sake cewa ka rufa man asiri zama yagi saman gadon sannan ya jawota ƙiyyy , ya matso da ita kusa dashi yana kallonta da idanuwanshi masu bata tsoro , yace inajinki faɗa man daidai lokacin da yake kallon agogon hannunshi yace idan kin faɗa man zan barki idan kuwa ba haka ba, yanxun saura minti 5 in aika ki ƙiyama na faɗa maki,

Jawwahir bakinta yana ƙarma tace tsintarsu nayi, wani irin marin da yasa ta hango azaba ya sake mata yace ke ni zaki maida sakarai?"" idan kika bari na sake maki magana hannunshi yakai saitin maƙoshinta yaje jawo shi zanyi in kashe ki na kashe banza, kiyi mutuwa irin ta karnuka dan rayuwarki bata da amfani cikin al"umma, zufa ta keto ma jawwahir, ta haɗiye miyan bakinta kamar ta haɗiye kunama, kuma tasan idan ta faɗa ma sadiq gaskiya ta sake jefa kanta cikin tashin hankali,

kallonshi tayi sannan tace nidai na faɗa maka gaskiya amma idan kwana na ya ƙare sai ka matar dani, dama nasan tunda kace ka tsani rayuwata mutuwa zanyi ta ƙarasa magana fashewa da kuka, yace rufe man baki munafikar Allah ke sai naci ubanki a gidan nan, tashi ki fita kiba mutane wuri da sauri ta sauko daga saman gado tayo waje da gudu tana fitowa ta yage baki wayyo na Allah zai kasheni wayyo Allah, sadiq ya leƙo daga ɗaki yana kallonta ta rufe baki yace zo nan ki zauna ya nuna mata wani wuri da hannunshi , tahowa tayi taxo ta zauna yace idan na sake jin bakinki na lahira sai yafiki jin daɗi,

Shiru tayi shi kuma ya koma cikin ɗakin, kuɗin ya tattara sannan ya irgasu dubu ɗari takwas da cass"in, tsaki yayi sannan ya saka a aljihunshi ya fito, idan take zaune yaje yakai mata harbi da ƙafarshi ya hargarbeta sannan yace kuma zanje in dawo yanzun nan,

yana fita jawwahir taje ta ɗauko wuƙarta tace kuma idan ka dawo kafin ka yanka ni nice zan yanka ka kowa ma ya huta azalimin banza, Allah yasa ka mutu kafin ka dawo, dan iska shi yasa ka rasa ubanda zai ɗauke aiki, kuma duk matar daka aura ta bani ta lalace Allah yasa ka samu wanda zata baka guba a abinci kaci ka mutu, haka dai tayi ta tsine ma sadiq albarka,

Fitowa tayi ta ƙara wanka, sannan taje ta shirya, tace kuma saina fita inga ubanda ya isa ya hanani, ita kaɗai take ta surutu kamar taɓaɓɓa, doguwar rigar matarial tasa kuma ta anshi jikinta sosai wani ɗan ƙaramin gyale ta yafa wanda dashi da babu uwarsu ɗaya ubansu ɗaya, waya tayi ma honey j, gata nan zuwa suje suci abinci, yace saita fito,

Tana fita ƙofar gidansu ta tsaya, shi kuma ya fito da mashin rover rover ya ɗauketa suka tafi,...............,


bayan sun gama cin abincin suna zaune tace mashi honey j nidai gaskiya guduwa zanyi in bar gidanmu, lemon daya sha ne ya maidoshi da sauri duk ya ɓata mashi jiki, ja"afar yace miyasa?"" jawwahir ta fara kuka tace wallahi kwanan nan sadiq yasa man ido, kuma har yanxun yaƙi tafiga koɗan sararawa inyi, ja"afar yace kiyi haƙuri don Allah kada ki tafi, jawwahir tace to idan dai bai daina shiga harkata ba saina sa an sace banza, anje an jefar dashi cikin ruwa kifi da kada su cinyeshi kowa ya huta, yace to kiyi haƙuri kiyi zamanki kinji jawwahir, tace ai tunda ka bani haƙuri nayi, amma da innasco da babasco bazan sake masu magana ba, tunda sunaji suna gani yake man azaba, ni ba"aso na, ta sake fashewa da kuka,

Ja"afar dai sai haƙuri yake bata, yana rarrashin ta, sannan suka miƙe ya ɗaukota sukayo gida, a ƙofar gida ya ajiyeta, tayi mashi godiya, sannan ta shige cikin gida,

Tana shiga taga inna zaune , ko inda take bata kallaba bare tace mata ta dawo, inna tace ina kikaje?"" tsaki jawwahir tayi sannan tace inda kima aikeni, inna tace idan dai wannan bokon tasa kike man rashin kunya wallahi saina sa sadiq ya hanaki zuwa, jawwahir daga ɗaki tace Eyy asa ya hanani saboda anga na kusa zama mai kuɗi ake man hassada wallahi duk ɗan baƙin ciki saidai ya kasheshi, inna tace to shikenan bari yaxo sai ki faɗa man haka a gabanshi, jawwahir tace yaxo shima ai banajin tsoronshi, inna tace yawwa gashi nan ma, sadiq, jawwahir ta ɗauka da gaskene shine yaxo saboda haka tayi shiru, jin bataji maganar sadiq ba yasa tace idan ya isa ya shigo nan ya sameni, tana rufe bakinta taji sallamarshi, da sauri ta lallaɓa ta haye saman gado,

Shi kuma yana shigowa, bayan ya zauna suka gaisa da inna yake ce mata ana neman su abuja dan haka tasa shi a addu"a, inna tayi mashi addu "a tare da fatan samun nasara, godiya yayi sannan ya miƙe, har zai fita yace juyo ba tare da yayi ma inna magana ba, ya shiga cikin ɗakin ta, jawwahir najin kamshin turarenshi alamar dai ya shigo da sauri ta ɗauke nunfashin ta ɗaff, wayarshi yasa ya haskata idanuwanta sai farfarfar suke alamar idon ta biyu yace tashi munafika, jawwahir tayi shiru ta sake rufe idanuwanta gamm, yace bakiji ina magana, ɓata fuska tayi kamar mai shirin kuka, yace tashi zaune, miƙewa tayi ta zauna , ya haske mata ido da hasken fitilar wayarshi ita bata iya ganinshi amma shi yake ganinta, sannan yace mi na gaya maki game da bin wacan ɗan iskan?""

jawwahir cikin tsoro kuma tasan tunda inna tana nan bzai daketa ba, yace dake nake, tace ai ba ɗan iska bane, hmmmm yace sannan yace aike baza ki faɗi gaskiya ba, tunda abokin sana"arki ne, kazamar

4 / 28