Author : MEELAT MUSA Category : African Stories & Novels
wata "yar rawa ta shegantaka yana murmushi saida ya gama , sannan ya saita kanshi ya shiga gidan mai unguwa, bayan sun gama abinda suke sadiq yayi ma mai unguwa ɗan alkairi yayi ta godiya, sannan shima ya fita yaja motarshi yayi gida,,,,,,,
Lokacin da jawahir ta isa gida ko parking ɗin kirki batayi ba, ta shige ciki, tana shiga kicin ta shiga, ta ɗora girki, sannan ta shiga ɗaki ta gyara shi dan babu abinda tayi tabar gidan,,,,,,
saida ta gama sannan ta zauna a gefen gado tana tunanin rayuwa,,,,,, zuciyarta ce tace jawahir ina shawartarki da ki rufawa kanki asiri kiyi zamanki tare da sadiq,,,,,,
Abinda ya wuce a baya ki daina kallonsa ki fuskanci rayuwa,,,, kema kanki kinyi cutawa mutane da dama amma sunyi haƙuri abin yaza tarihi,,,,, wasu kin biyasu wasu kuma sun yafe maki, tuna nau,in azabtuwa da kikasha saboda tsabagen san abun duniya,,,,
ya kamata ki manta da baya ki fuskanci yanxun, ki tubarwa Allah shine mafita, ajiyar zuciya jawahir tayi a daidai lokacin da wasu hawaye masu zafi suka kwararo mata daga cikin idonta,,,,,,,,,,,
sadiq dake tsaye gabanta, tun lokacin da ta fara tunanin yake kallonta bama tasan yazo ba,,,,,, zama yayi kusa da ita, sannan ya jawota jikinshi, ɗaga ido tayi ta kalli sadiq sannan ta fashe da wani irin kuka mai kama hankali,,,,,,,,,,,
Cikin tausawa sadiq yace miye kuma?"" jawahir ta kasa magana sai kuka takeyi,,,,,, sadiq yace ni bansan kuka , ko wani abu nayi maki ne?"" jawahir ta girgiza kanta, sadiq yace to kiyi haƙuri idan nine insha Allah bazan sake ba,,,,,,, a daidai lokacin da yake goge mata hawayen idonta,,,,, sannan yace miye kikeyi a kicin yana yin ƙauri,,,,,,
Sai yanxun ta tuna ta ɗora girki da sauri ta tashi ta nufi kicin, shima binta yayi, yana ƙara bata haƙuri yana rarrashinta, tare da maganganu masu kwantar da hankali,,,,,,,
to haka rayuwar sadiq da jawahir taci gaba da tafiya cikin jin daɗi da kulawa, yayin da duka bangarori biyun suke nunawa junansu kauna,,,,,,,,,
to sadiq ya tashi tafiya, hankalin jawahir ya tashi sosai, kuma yayi ta shirya su tafi tare amma tace ita bazataje ba, ya tambayeta dalili amma tace ba komai, sadiq ya damu sosai itama taji duk babu daɗi amma haka nan bazataje ba,,,,,
Jawahir tace kaima duk abinda kke samu anan sai kayi ta tafiyar nan kawai kayi zamanka anan mu zauna tare,,,,,,,
murmushi sadiq yayi sannan yace tayi mashi fatan alkairi,,,, haka sadiq ya tafi jawahir tana kewar mijinta sosai,,,,,,,
tafiyar sadiq da sati ukku Allah yayi wa larba rasuwa, wato matar baban jawahir, kuma batayi wani rashin lafiya ba, ƙarar kwana ne kawai, da inna da baba haka jawahir ta kwashesu a mota suka tafi kyauye dan gaisuwa,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,
[1/17, 7:46 PM] Jamila Musa Ws: ☄
☄☄
☄☄☄
*WANDA BAIJI BARI BA*
*AMEENCI WRITER"S ASSOCIATION* 📚✍🏻
*MEELAT MUSA*
*Kunemu AMEENCI WRITERS NOVELS GROUP a shafinmu na facebook don samun littattafanmu masu ƙayatarwa, kudai ku nememu kada ku bari a barku a baya*
*Gaskiya wannan nakune ban haɗaku da kowaba ƙawayena amanata, ASMEENAT XEEYAN tare da UMMU FARHANA ina maku fatan alkairi gaskiya sosai,*
*Saffa One ina tare dake har abada saboda keɗin ta dabance a cikin babban birnin ruhi na, ina tare dake* 👍🏻
*PAGE 50*
***
*S*aida su jawahir sukayi sati ɗaya a ƙauye amma itadai dai a daddafe tayi shi dan gaba ɗaya ta kasa gane miye yake damunta?"""
To kwanaki suna tafi sosai, jawahir dai yau da lafiya gobe babu, kullum idan sunyi waya da sadiq take faɗa mashi bata lafiya, kuma yace taje asibiti amma sai tace ita dai basai taje ba,,,,,,,,
Inna ta gane dai jawahir tana da ciki, saboda yanayin yanda take tafiyar da al,amurranta, ga wani ɗan banzan kwaɗayi da takeyi, dan haka tasawa jawahir ido kuma tana bata shawarwari, amma inna ta kasa faɗawa jawahir tana da ciki, kuma bata faɗawa kowa ba,,,,
Haka dai rayuwa taci gaba da tafiya jawahir tanajin daɗin rayuwarta sosai, dan bbu abinda yake damunta a gidan innasco saidai tayi wanka taci tasha tayi sallah ta haye gado tayi baccinta abinta,,,,
To haka kwanaki sukaci gaba da tafiya watanni suna shuɗewa, jawahir ciki ya fito sosai, dan haka itama ta gane ciki ne da ita, ciki fa yayi girma sosai,,,,, dan haka sun fara zuwa asibiti awo,,,
To jawahir ce keyin waya da sadiq, tace don Allah nifa ka dawo haka nan, ni banajin daɗin zaman gidan nan, sadiq yace miyasa?"" tace yaya nifa ciki nake dashi kullum da hijabi nake zama wallahi kunya nakeji innas da babs kallona fa sukeyi,,,,,
Dariya sadiq yayi sosai sannan yace kawai fa tsarguwane,,,,, babu wani kallonki da sukeyi,,,, dariya jawahir tayi sannan tace watanka fa takwas don Allah ka dawo haka nan, sadiq sai kin aihu zan dawo,,,,,,,
Jawahir tace to Allah yasa muna da rayuwa, sadiq yace amin, kuma Allah ya baki lafiya Allah ya sauƙeki lafiya jawahir,,,,, tace amin yaya, haka sukayi ta fira daga baya kuma sukayi sallama,,,,,
Kwanci tashi babu wuya a wurin Allah cikin jawahir ya shiga watan aihuwa, dan haka ta faɗawa sadiq, shi kuma duk yabi ya gigice akan cikin nan dan haka sadiq sai turo kuɗi yake kamar baisan darajarsu ba,
Jawahir tace ya barsu haka nan, anyi komai amma sadiq kamar ƙara tunxurashi takeyi, gaba ɗaya yabi ya firgice, kuma yace insha Allah cikin satin nan zai dawo,,,,,,,,
to jawahir duk abinda tasan zata buƙata ta siya, don haka aihuwa kaɗai ake jiran zuwanta,,,,,,
Jawahir tana kwance tana baccin rana, innace take mata magana ta tashi taci abinci, ai jawahir kamar jira take inna ta tasheta, tana tashi ta fara salati tana murƙushe murƙushe tana kuka sosai,,,,,,
inna tace lafiya jawahir?"" cikin kuka tace innas kinsa man ciwo fa,,,,, inna tace wane irin ciwo kuma?"" tace marata da bayana ciwo,,,, ai inna batayi magana ba, jawahir ta fara kwarara amai,,,,,,,,
Da sauri jawahir ta sauko daga saman gado tana riƙe inna tana kuka sosai,,,, inna ta fara salati cikin kiɗima, tace bari inje in samo wani yakaimu asibiti, jawahir ganin inna zata fita ta riƙeta sosai tana cewa kada ki tafi innas,
rakani toilet zanyi fitsari,,,,, inna ta kama jawahir sukayi toilet, suna zuwa jawahir ta durƙushe ƙasa , inna da sauri ta fito dan samo mai kaisu asibiti, tana tafiya tana mita,,, wai data iya mota da takai jawahir asibiti,,,,,,
haka ta fita ta gama shawagi a anguwa amma kamar anyi ruwan mutane an ɗauke,,, dan haka gidan wata maƙociyarsu ta shiga ta faɗa mata halin da jawahir take ciki, don haka tare suka rantafo sukayo gidan inna,
Shigarsu inna farlo kenan kiran wayar sadiq ya shigo, inna batabi inda wayar take ba, sukayi ciki da ita da wanda suka shigo tare, suna shiga tun a ɗaki suka fara jiyo kukan jariri,,,,
Da sauri suka ƙarasa ciki, matar itace ta shige cikin toilet ɗin, dan haka ta fara cewa a kawo reza, jakar da jawahir ta haɗa dan zuwa asibiti a ciki aka ɗauki reza da zare, aka yanke cibiya, aka ɗaure bakinta,,,
inna tasa ruwan zafi akayi wa jariri wanka, itama mai jego ta gyara jikinta,,,, innace ta gyara go ina, da inda jawahir tayi amai da toilet inda ta aihu,,,,,,,,
saida komai ya zama daidai jawahir ta gyara jikinta, tasa kaya, shima jariri aka gyareshi aka zugeshi cikin kayan sanyi, jawahir mai jego aka haye saman gadon sarauta,,,,,,
Inna tana fita daga ɗakin jawahir jikinta har kyarma yake ta kira sadiq, saboda tarin miss call nasa data gani a wayarta,,,,,, yana ɗauka bbu ko gaisuwa tace na haihu, dariya sadiq yayi sannan yace yau kuma da wannan kika zo?""""
jawahir tace wallahi, sadiq yace ban yadda ba, jawahir tace bara in tsinkuli jaririn kaji, da sauri sadiq yace ke ke miye haka?"",,,,,, dariya jawahir tayi a daidai lokacin data girgiza jaririn da ƙarfi, aiko yace Inya inya inyaaaa inyaaaaaa, sadiq yace wallahi tunsa kika mashi saina rama mashi idan dawo, dariya jawahir tayi sannan tace ba komai ai gero ya saba ganin ruwa tunba na surfe ba,
Taci gaba da cewa wallahi akwai wahala aihuwa,,, dariya sadiq yayi sannan yace dama ina nan , a wace asibiti kika aihu ne?"", tace a gida a toilet , salati sadiq yayi sannan yace kika haifar man ɗa a toilet?"",,,, amma baki da hankali wallahi, tsaki jawahir tayi sannan tace tunda ka gaji da wayar sai anjima ta kashe,,,,,
Haka jawahir tayi ta kira tana faɗa ta aihu, take faɗawa ƙawayenta, ta faɗawa zarto kuma ta faɗawa auwal yace zai kawo matarshi,
to jawahir dai tana samun kulawa sosai a wurin innas , domin itace take mata wankan jego, niko nace uwa kuma uwar miji, tana samun kulawa sosai, shi kuma baba kullum idan ya dawo yana ɗakin innas wurin jariri,,,,,,,,,,,,,
ranar suna kuwa ansha taro sosai, kowa da kowa yaje, can naga su asmeenat xeeyan da ummu farhana, da saffa one kai har meelat musa fans na gani, naga real mai dambu, kai kowa ma yaje, ameenci fans suma duksun hallara, zarto da hafsat da sadiyya duk sunje, amma babu angon jego sadiq , haka aka sha taron suna lafiya, ɗa yaci Umar wato sunan baban sadiq,,,,,,,
zarto kuwa tazo da makaman yaƙi na gyara sosai, ta kawo wa jawahir,,,,, haka akasha suna kowa ya kama gabanshi cikin jin daɗi da addu,ar Allah ya sauki duk wasu masu juna biyu lafiya, kuma ya shirya mana zuria,
Saida jawahir ta gama wanka sannan sadiq ya dawo, kuma yau ya tattara matarshi suka tafi , a gidan khadija anan suka koma, anyi ma gidan gyara sosai an ƙayatashi , da da mukaje ganin gidan ummu farhana cewa tayi anan zata zauna, dakyal asmeenat xeeyan tajata muka koma Ameenci writer,s,
Hmmm bayan gida ya rage na masoya, wannan filin kuma na ma,aurata ne, kamar yanda sadiq yayi alƙawarin saiya ramawa *NAWAF* tsinkulin da jawahir tayi mashi ya rama , sannan kuma aka buɗe shafin ma,aurata, nima dai nace saida safenku,,,,
Watanni sun shuɗe sosai, hankalin jawahir yakai ƙololuwar tashi ganin irin tarin arxikin sadiq jawahir tayi kuka sosai, ta kalli sadiq tace yaya dana san zakayi arxiki haka da ban bawa kaina wahala ba, wurin ganin na tara abun duniya,,,,,,
Ni nawa baiyi man rana ba, gashi sai wahalar banza danasha , ga arxiki har gida yazo, lallai idan Allah bai ajiye maka ba, baka isa ka ajiyewa kanka ba,
sadiq yace Allah ubangiji ya wadatamu da arxiki na halal, jawahir tace amin,
Sadiq dai yanxun an zama shahararren ɗan kasuwa, sunan sa ya zaga duniya, sadiq ya zama kicima sosai yasha round ya zagayo yazo sama yayi tsaye kowa zai wuce saiya ganshi, saboda kuɗi,,,,,,,,
jawahir kuwa tanajin daɗinta sosai, hankalinta kwance dan sadiq ba ƙaramin ƙauna yake wa jawahir ba,
Bayan wasu shekaru, sadiq ne da nawaf da nawwara wato mai sunan innas, sai amir mai sunan babanta, sai kuma khalifa mai sunan sadiq, suna zaune a farlo suna fira,,,,,,,,
Jawahir dake kwance da sauri ta miƙe tsaye, sadiq yace lafiya?""" nuna mashi har farlo tayi, shima kallon ƙofar yyi dan ganin abinda jawahir take kallo,
jawahir ta kalli sadiq sannan tace mi tazoyi a gidan nan?"",,,, dariya sadiq yayi sannan ya rungomo jawahir ta baya ya ɗora kanshi saman kafaɗarta, daidai kunnenta yayi magana yace biko tazo,,,,,,,,,
Khadija tace jawahir ya kike,,,,, jawahir tace lafiya qalau, my ya kke,?"" kallonta sadiq yayi amma baiyi magana ba,,,,,, amma har yanxun idanuwanshi suna kan khadija,,,,,, jawahir ce tace ya akayi ne?"",,,,, khadija tace ba komai nazo zan wuce nace bara inxo mu gaisa,,,,, jawahir tace to mun gode,,,,,,,,,
nawaf ne yace momy wace ce?"""",,,,sadiq tashi yayi daga saman jikin jawahir ya tattara yaran sukayi ciki,,,,,, jawahir ce tace zauna,,, zaman khadija tayi, jawahir ta shiga ciki, ta kawo mata lemu, bayan ta gama, jawahir ta shiga ɗaki ta haɗo mata tatalim da tara na arxiki, ta bada kuɗi masu yawa,,,,,
Khadija tayi godiya, tare da ma jawahir fatan alkairi,,,, ta tashi ta tafi,,,,
Tana tafiya jawahir ta sauke ajiyar zuciya tace kai Allah yasa mu dace,,,,, daga ciki sadiq yace jawahirrrrrrrrrrrrr,,,,, da gudu tayi ciki,
ganin zasu raina man wayau nima na tsaya anan,,,,,🔚
🔚
🔚
Alhamdulillah, ni *JAMEELA MUSA* nake cewa ku kasance tare, dani, sai Allah ya hɗamu a sabon littafina,
Nake cewa ku kasance tare dani, 💋 vyeeeeeeee