Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

WANDA BAIJI BARI BA Rayuwar Ƙarya da Nadama by MEELAT MUSA

Author :  MEELAT MUSA Category :  African Stories & Novels

Chapter   2 / 28

3K to 6K   out of 83K words

MUSA* 🌹

*PAGE* 4

****

*T*a daɗe da fita sannna ta dawo da wasu mutane guda biyu , inna ta fito daga ɗaki tace wa"an nan fa?"" mutane da jawwahir ta shigo dasu tace kada wanda yayi mata magana, nuna masu wuri ta fara yi, wai nan zasu gina mafa ɗakinta,

Inna tanajin anyi maganar gina ɗaki, ta tsaya tana kallon jawwahir, inna ta kasa haƙuri tace jawwahir wane irin gink zaki kuma?"""" ɗaure fuska tayi sosai sannan tace ba nace kada ki sake man magana ba?""" tana maganar tana zaro ido sai kace itace uwar inna ce ɗiya,

Inna tace ai ba gidanki bane bare kice zaki gina ɗaki, sai ki bari sai kinyi naki sannan kiyi yanda kika dama,

Baba ne yayi sallama ya shigo gidan, ganin mutane tsaye a gidanshi abin ya bashi mamaki, kallon inna yayi yace mata lafiya?""" inna tace wai jawwahir ce zata gina ɗaki, baba ya kalli jawwahir yace ɗakin uwarki zaki gina?"""

Nan gidana ne, nine na siyi abuna ba wani ya siya man ba, yana magana yana ɗaga hannunshi alamar nuna faɗin gidan shi da kuma jaddada ma jawwahir gidan gashin kansa ne ba na wani ba,

Jawwahir tace to ai kasan ina da gadonka ka ko?""" baba yace ai sai ki bari saina mutu sannan, jawwahir tace abinda nake jira amma naga har yanxun nesa bata zo kusa ba,

Baba kallon jawwahiri yayi sannan ya nuna kanshi yace ni kike ma fatan mutu?"" jawwahir tace idan baka san mutu sai a raba gadon gidan a bani kaso na, baba yace aiko na mutu baki gado na, dariya jawwahir tayi sannan tace hmmm dama wanda ya mutu zai dawo, daka ga yanda zan mayar da gidan nan idan ka mutu,

Ta ɗaga hannun ta alamar nunawa zansa a ruguje gidan nan kaff, ayi man ginin zamani sannan kuma duk bangon ko wane ɗaki zansa a ɓarke manshi a maƙala man *AC* insa ƙaton get da arna masu gadi, sannan kuma ina karnuka su riƙa gadi na,

Baba yace kinyi asara tunda kare zaiyi gadin ki , murmushi jawwahir tayi sannan tace ba asara bace jin daɗi ne, kai kuma sannan kana can ciki kabari an danne mana kanka da ƙasa, ni kuma in haye saman kujeru na alfarma in riƙa asawaki da naman kaji,

Baba yaji anbun yafi ƙarfinshi saboda haka yace gida dai tunda gidanshi ne babau ubanda ya isa yayi mashi gini, itama ba ta sake ma baba magana ba, ta juya taci gaba da magana da masu aikin gina mata ɗaki,

Saida suka gama sannan ta sallamesu gobe suxo su fara mata aiki,

Yinin ranar haka jawwahir ta yini tana ta "yan maganganunta, saida taje wajen garke tumakin inna ta tsine masu albarka , inna dai batayi mata magana ba,

Da daddare inna garin kwaki ta jika da ƙulli, duk kashedin da jawwahir tayi ma inna bata jiba saboda haka garin ta zuba tace mata gashi taci, jawwahir ta ɓata fuska kamar zatai kuka tace lallai innas yau na tabbatar baki kauna ta, ni zaki jiƙa gari ki bani?"""""

Tun ina karama banci abu mai gina jiki ba, yanxun na samu na ɗan fara cin kaji da lemo da yought mai kyau ni zaki kawo ma gari inci ya shanye man jinin jiki?"" hmmm aiko awakinki kika bawa wannan garin kin ɗauki alhakinsu bare ni da kike taƙamar kin haifa, inna dai batayi magana ba haka jawwahir ta ƙare iskancinta inna bata sake magana ba,

Har 10:02pm jawwahir na tsakar gida, inna tace taxo ta kwanta tace bata ƙara shifa ɗakinta sai an gina mata nata, inna tace ga tabarma ki kwanta, jawwahir tace barta yau a tsaye zan kwana, inna ta shige ɗaki tabar jawwahir tsakar gida, haka ta gaji da tsayuwa ta kwanta ƙasa,

Da safe kuma a ƙofar ɗakin inna taje tace ta miƙo mata kayan makarantar ta, dan baza ta sake shigowa ɗakin ba, inna ta tattaro kayan ta watso mata, dan ta gaji da iskancin jawwahir,

Jawwahir dariya tayi sannan ta tattara kayan tace oh O Oho a haka dai za"abarmu wallahi, inna dai batayi magana ba,

Data gama shirin sannan masu gini sunxo, ta basu kuɗin bulo da yashi da suminti, sannan ta tafi makaranta,

Yau ko honey j bata tsaya jira ba, dan abin mai zafine, napep tahau tayi tafiyarta,

Lokacin da aka tashi makaranta, ba gida ta nufo ba, wata ƙatuwar ma"aikata ta nufa, tana zuwa wani Office ta shiga, kallo ɗaya zakai ma mutumin kasan hutu ya gama zaunawa a jikinshi suka gaisa,

Bayan gaisuwa jawwahir tace ranka ya daɗe wata ƙaruwa ce na kawo maka, yace ina jinki, jawwahir tace kasan wata tsohuwar tv da,akayi da mai kwaure?"" yace Eh yasanta, jawwahir ta gyara zama tace kana da irin ta ne?"" yace ah ah wani abu ne?"" tace ni na samo ɗaya dakel , yace mi ake da ita, tace neman ta ake sosai wanda ya kawota miliyan biyar za"a bashi,

Alhaji ya gyara zama yace da gaske?""" jawwahir tace gaskiyar magana kenan, nima lokacin da naje *venezuela* naga ana kaita su kuma can suna bada kuɗi sosai, to nazo na sameta dakel nama ɗauka kana da irin ta da siye zanyi,

Yace nawa zaki siya ne?"" jawwahir tace to tunda kaine ai sai in siya miliyan shidda tunda kana da mutumci, Alhaji yace Allah sarki shi yasa nake sanki wallahi kina kawo man ƙaruwa jawwahir tace ai babu wani damuwa, yanxun ma, idan kana da miliyan ɗaya ka bani don Allah sai in kawo maka tv ɗin ka ajiye idan na kawi maka sai ka bani,

Alhaji yaji kuɗi saboda haka yace babu damuwa, yaushe kike san kuɗin ne?"" tace idan da hali yau, alhaji yace to babu damuwa, ki kawo tvn tace ni yanxun abubuwa sun man yawa amma zan dawo anjima ma kawai in kawo maka,

Alhaji yace to, jawwahir tayi godiya sannan ta baro office ɗin,

Kai tsaye gida ta nufo, tana zuwa abinda idon ta ya gane mata shine ɗakin da aka fara gina mata ake rushewa , ga kuma sadiq zaune a gefe, da gudun bala"i ta isa wurin ta fara cewa kai malam lafiya?"" baku san kuɗi aka sa aka gina ba?""

Sadiq yace tunda kina da kuɗi gobe ma sai kisa a sake gina maki wani, inda sadiq yace zaune ta kalla murmushi tayi da gefen bakinta , tace hassada ta ƙarasa maganar tana ɗaga girarenta, sadiq yace anyi hassadar ko zakiyi maganain abun ne?"" jawwahir tace yanxun nan kuwa basai anjima ba,

Schbag inta kawai ta yadar a tsakar gida ta fita da gudun bala"i, gudu take sosai kamar wanda taɓin hankali ya sama, tana isowa bakin titi, napep tahau, bata zame ko ina ba, sai police station, tana zuwa ta fara rattafa masu masu bayani, tana kuka yanda take maganar dole ta baka tausayi, wani ɗan sanda ya bada hilux ɗaya yace aje a taho da sadiq, saboda jawwahir tace basu haɗa komai ba haka nan yaxo gidansu yake tayi mata asara idan tayi gini ya rusa shi, ta ƙara da cewa ita marainiya ce da tayi mashi magana kuma yace duk ubanda ya tsaya mata ya ganshi, ranka ya daɗe shi yasa nazo wurinku kubi man haƙƙina dan ku masu adalci ne,

Ɗan sanda yace haƙiƙa kuwa kinzo inda za"a share maki hawayenki, yace ma "yan sanda maza kuje ku kamo mana shi, da sauri suka fito su dukansu suka shiga mota hada jawwahir,

Jawwahir tayi bake bake a cikin mota tana gaba sai nuna masu hanya take har suka tun karo cikin unguwarsu,,,,,

Suna zuwa tace to su jira ta shiga ta kirawo shi, suka ce mata to, tace idan ba haka ba yaji na ɗauko ku guduwa zaiyi, suka ce to, haka jawwahir ta shiga cikin gida tace ma sadiq idan ka isa biyoni waje,

Shi kuma cikin rashin sanin abinda take magana yace miyasa dole sai waje?""" jawwahir tace idan har kai ka cika mai ƙarfi kazo waje mu raba fili, sadiq bai sake magana ba, sabida haka wani ƙaton dutse a gabanta ta ɗauka ta jefa mashi, shi kuna da gudu ya taso ya biyo ta,

Tana ganin ya biyota ita kuma tayo waje da gudu, suna fitowa tace yawwa kunga banzan nan kuka ma man sakarai , haka suka danƙe sadiq suka jefa mota, itana jawwahit motar ta hau suka nufi station,

Suna isa sadiq yana san yayi magana amma jawwahir tace kada su barshi yayi magana dan yace ya raina "yan sanda, hannu tasa cikin brezer ta ta fiddo kuɗi ta basu tace tana so a lilƙisa mata shi yanda idan ance yayi mata sikanci gobe zai kiyaye ta, tun tana nan akafara cima sadiq uwa , ita kua ta juyo tayo tafiyarta gida,






Kam lallai wannan wace irin rayuwa ce? Muje sannu muga irin iskancin jawwahir, dan hausawa sunce wanda baiji bari ba?"" lallai bazai ƙijin hoho ba,💋

☄☄
☄☄☄
🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥
*WANDA BAIJI BARI BA*
🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥

☄☄
☄☄☄

*AMEENCI WRITER'S ASSOCIATION* 📚✍🏻

*MEELAT MUSA*

*PAGE* 5

****
*J*awwahir tana zuwa gida ko sallama babu haka ta shiga ban kaɗai ban kaɗai, inna tace mata ina sadiq daya biki?""" dariya jawwahir tayi sannan tace hajiya innasco kenan, ai babu wanda zai taɓa jawwahir ya zauna lafiya, yanda nayi asara yau sai sadiq yayi asarar jinin jikinshi gaba ɗaya, dan naje na bawa "yan iskan kuɗi suyi mashi shegen duka dan idan ya dawo zai gane cewa jawwahir *fitilar sharri ko ba mai ina kai safe*

Tana faɗin haka ta faɗa ɗakin inna ta kinkimo tv ta fito, wani tsunma taje ta ɗauko ta fara kakkaɓewa, inna tace ita kuma ina zakije da ita ne?""" jawwahir tace gadona nake fiddawa kinga lokacin da zaki wuce lahira kila lokacin ina ƙasashen waje kila ina irin su , *England* ko *serbia* ko *texas u s a* ko *mexico* ko *california u s a* ko *japan*haka dai tayi ta lissafo ƙasashe, har ta gaji sannan tace kinga ai gara inci rabo na in tada molaƙa,

Inna tace to tunda ba ubanki ne ya siya man talabijin in nan ba, baza ki ɗaukar min kayana ba, wannan tv tun ta aure na ce, har kin iya lokaci ɗaya kixo ki rabank da abuna?""""

Jawwahir tace ai shi yasa nace da sauranki, lumfasawa tayi sannan ta dafe ƙirjinta, bayan wani lokaci ta ɗago fuskarta ta kalli inda inna take tsaye sannan tace innasco?""" inna ta kalleta, jawwahir tace kinsan abinda ake cewa plasmer?"" inna tace gulasmer?""" dariya jawwahir tayi sannan tace talabijin bango, ita wannan yanxun an daina yayinta, zanje in siyar da wannan in siyo wanda ake yayi kinji innas, ta ƙarashe maganar tana buɗe idanuwanta cikin sigar iskanci da rashin kunya,

Inna tace nida bansan ta bango nafi san ta girke, jawwahir tace to bari inje in siyo maki, daidai lokacin da ta kinkimi tv zata fita, inna ta riƙeta, tace ajiye man kayana, ɗaure fuska jawwahir tayi sannan tace ke bari ganin ina lallaɓa ki amma kina wani haye man, zaro idanuwanta tayi sannan tace sakeni kafin tumbinki yasha iska, da sauri inna ta saki jawwahir, tana sakin ta jawwahir tayi dariya tace ashe baki san mutuwa,

Tsaki tayi sannan tace malama bani wuri, inna ta matsa ta kinkimi tv tayi waje, tana fita ƙofar gida tasa almajirai suka ɗaukar mata ita suka kaima mata bakin titi, napep ta hau ta nufi office ɗin alhaji,

Mai napep in tasa ya ɗaukar mata tvn har cikin office, bayan ya ajiye ta sallameshi , bayan ya tafi tace ma alhaji ranka ya daɗe gata, amma don Allah ina ƙara ja maka kunne kada kayi man sakaci da dukaya, alhaji yace kada ki samu damuwa, jawwahir tace bani kuɗin to,

Wata jaka ya jawo ya bata , ta riƙe a hannunta, sannan tace ni alhaji da mota zan siya, miye shawarar ka?"" tayi maganar cikin yanayi tausayi tace abubuwa sunman yawa saboda dad har yanxun yana *london* kuma wani lokaci driver baya zuwa da wuri yana kaini sch, so ina so in siyi motar,

Alhaji yace gaskiya ki siya yafi kyau a haka, jawwahir tace ni nextweek ma *india* zanje dan muna da biki gidan tsohon gwamma, alhaji yace ashe kinsan shi?"""

Murmushi jawwahir tayi sanann tace ai dashi da dad inmu mamansu ɗaya babansu ɗaya, alhaji yace ki taimaka man ki bani number shi don Allah, gaban jawwahir ya faɗi , amma ta dake ta basar, tace swry nabar ɗaya wayana a gida, amma insha Allah zan turo maka, yace babu damuwa,

alhaji yace jawwahir jawwahir gaskiya familynku babban family ne, jawwahir tace sosai, alhaji yace to cikin yayun gwamna waye babanki a ciki?""" nan ma dakewa tayi sannan tace dawa dawaye ka sani ne?"""

alhaji ya fara yo mata lissafi , saboda ita dai bata san kowa ba, dan haka tace lallai to cikinsu da waye nayi maka kama?""" alhaji kawai canka yayi ya faɗi sunan wani, jawwahir dariya tayi sannan tace ai daɗina dakai kana ganewa, a daidai lokacin da ta miƙe tsaye,

Alhaji yace to maganar motar fa?"" jawwahir tace ina so, munyi waya da dad yace inje wurin wani yayanshi ya siya man motar ni kuma muna da arziƙinmu bana so ina dogara da kuɗin gidan wani saina dad, amma nace kawai zan samu rance idan ya dawo sai ya bani in biya,

Amma idan aka siya man motar miliyan 2, idan dad ya dawo zai bayar da 3milion, alhaji najin haka yace to aini zan siyo motar nan, jawwahir tace to babu damuwa ka siyo kuɗinka zasu zo hannunka,

Jawwahir tace bara in wuce gida, Alhaji yace to, yana ƙara jaddada mata maganar number tsohon gwamna, tacd kada ya samu damuwa,

tana fitowa abin hawa ta tare , tana shiga, gabanta ya fara faɗuwa lallai wannan alhajin ɗan iskane a gidan uwar waye zan samo number gwamna"""???""

tsaki tayi tace ɗan iskan wato shi yama fink ƙusa kai kenan lallai,

har ta iso gida tsine ma alhaji take dan bata san ta ina zata fara nemo number ba,

tana shiga gida da "yar jakar kuɗinta matse, ta tadda sadiq zaune a tsakar gida, wata "yar munafikar waƙa ta fara, har zata wuce yace ke zo nan, tsaywa tayi ba tare data juyo ba, miƙewa tsaye yayi ya matsa kusa da ita, yana fuskantar ta,

yace jawwahir wannan wace irin rayuwace kika zaɓar ma kanki?""" tayi shiru, yace idan kina rufa ma kanki asiri ki rufa ma kanki asiri ki tsaya inda Allah ya ajiye ki, wannan rayuwar da kika ɗauka ba hanya bace mai bullewa, kinje kinsa an dakeni,?"" har abadan duniya baki da kamata mune zamu faɗa maki gaskiya, mutanen duniya saidai su tsine maki albarka,

jawwahir tace yawwa anzo wurin kawai dai kace kana so ka tsine man albarka ne , kuma sai ka tsaya kana ta laɓe laɓe?"" kawai kace jawwahir Allah ya tsine maki albarka shikenan, dan ka tsine man sai akace maka zan lalace ne?"" hmm kacu gaba da shiga harkata, idan har baka kiyayeni ba saina sa an tsiyaye maka idanuwa kama rasa wanda zaiyi maka jagora, tsaki tayi sannan tack gaba da tafiya, tana cewa kuma gobe zansa aci man gaba da gini idan lafiyar jikinka ta isheka sai kasa a sake rusawa,


sadiq tsaki yayi saboda a gajiye yake idan yace ma zai daketa shine zai wahalar da kanshi, dan haka fita yayi yabar gidan,

ita kuma tana shiga ɗaki kayanta ta cire, sannan ta zaro wata katuwar wuƙa daga ƙugunta, ƙofar ɗaki tazo ta zauna saman kudinka ta fara wasa ta, tana cewa udan ba"a daina sa mana ido ba, haka zamu shige cikin maƙoshin mutum, takai wuƙar wurin bakinta tana ma kiss tana kallonta kamar wata ɗiyarta, taci gaba da cewa nasan kina nan kinajin ƙishirwar jini, kiyi haƙuri nayi kashedi dan *duk wanda baiji bari ba tofa lallai bazai ƙijin hoho ba, haka bahaushe yace*

Dariya tayi sannan ta miƙe tace bara muje muyi wanka saboda ɓacin rana, kwando ta ɗauka ta nufi bayi,

ita kuma inna tana gefe taji kashedin jawwahir gabanta sai faɗuwa yake Allah dai yasa ba ita da zata yanke ba,

Jawwahir na fitowa daga wanka, ta kalli inda inna take taga duk ta takure wuri ɗaya, abin ya bata dariya ta fara kwalkwala dariya har abin ya bawa inna tsoro, inna ta kasa kallonta sai kallon ƙasa take jawwahir tace hajiya innasco halan yauma tuwo kikai mana ko?""

inna tace ban sani ba, dariya jawwahiɗ tayi sannan tace ai duk laifinki ne, ga awaki kin wani kama kin ɓoye sai kace rayuwarki , hajiyata ki fito dasu kawai kice daɗi ki tada molaƙa ko kin zama rayayya, inna tace dan ubanki yanxun mutuwa nayi?"" jawwahir ta ɗaure fuska sannan tace ai banbancinki da matacce idanuwanki kawai da suke lufashi,

inna bata sake magana ba jawwahir ta shige ɗaki tana shiga ɗaki ta sake sheƙewa da dariya , tace muguwa ashe bata san mutuwa, ji yanda idanuwanta suke wani far far, tana nuna yanda idon inna yakeyi cikin madubin da take kallon kanta tana kwaikwayon maganar inna, haka tayi ta iskanci daga baya tayi shirin kwanciya bacci ta haye gado,


inna tananan zaune har baba ya dawo , yana dawowa inna cikin tsoro ta fara gaya mashi jawwahir zata kashe ta, baba yace ƙarya take dan ubanta , inna tace hada ceman *wanda baiji bari ba, wai bazai ƙijin hoho ba*

Baba yace barta dan ubanta da kanta take, kuma kada ki kuskura ki nuna mata kinajin tsoronta idan ba haka ba zata hana maki zaman lafiya, inna tace to, haka baba yayi ta rarrashin inna da kalamai masu daɗi, daga baya suka tafi ɗaki dan kwanciya bacci,


*na gode ku kasance tare dani*

☄☄
☄☄☄
🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥
*WANDA BAIJI BARI BA*
🔥🔥🔥🔥🔥🔥��🔥

☄☄
☄☄☄

*AMEENCI WRITER'S ASSOCIATION* 📚✍🏻

*MEELAT MUSA* 🌹

*PAGE* 6

*****

*T*unda safe jawwahir ta tashi tayi wanka, mai ta shafa da "yar powder tana zaune tana duba agogon hannunta saboda yau basu da makaranta,

Wayarta ta ɗauko ta kira ƙawarta hafsat wanda itace ta gayyace ta bikin gidan tsohon gwamna, ta kirata bayan sun gaisa tace mata hafsat wai bikin da zamuje don Allah ya kuke dasu?""" hafsat tace mata wani abu ne?"" jawwahir tace inaso kawai in sani ne, hafsat tace matarshi ce yayar mamana uwa ɗaya uba ɗaya, jawwahir tace to kina da ƙawa a cikin yaran gidan?"" hafsat tace mata Eh, jawwahir tace to babu damuwa,

Bayan sun gama wayar jawwahir tayi ajiyar zuciya, ita kaɗai tasan dalilinta na

2 / 28