Author : MEELAT MUSA Category : African Stories & Novels
na gani,
jawahir tace dani dake aga kasasshe,,,,, dan idan zaki cika gidan nan da jawahir bazaki je ba, ta saman rubun zanbi in wuce,,,,,,, wallahi saina je,,,,
Inna tace zan kira sadiq ɗin ai,,, jawahir tace idan na gano maki lamabar ko?"",,,,, inna tace idan baki gano ba na shiga maƙota su kamo man lamabar, jawahir tace ai suma duk daɗone irin ki,,,,,,
Tsaki inna tayi sannan ta fita daga ɗakin,,,, jawahir tace baki aje komai ba sai fitina,,, baki zuwa naga inda zaki tana kwaikwayon maganar inna, tsaki tayi sannan tace dani dake anga gwani,
***
*T*unda asuba jawahir tanayin sallah bata koma bacco ba, duk abinda tasan zata buƙata ta ɗauka,,,, wayarta ta ɗauka ta kira sadiq,
Cikin yanayin bacci ya ɗauki wayar, jawahir cikin zakuwa tace yanxun zan tafi!""" sadiq yace to Allah ya tsare hanya,,,,,, ki kula,, jawahir tace yawwa ngd, ta kashe wayarta,
Bayan jawahir ta kashe waya sadiq ya tashi cikin yanayi bacci da idonshi bai gama washewa ba,,,, ya juya inda khadija take kwance bai ganta ba,,,,
Da sauri ya murje idonshi tare da ƙara ɗaga bargo bata nan,,,,,, miƙewa yayi ya nufi toilet, bai sameta ba,,,,, gaban sadiq ya faɗi tare da cewa ina ta tafi kuma?"""
dan khadija ko fitsari zata sai ta tashi sadiq ta faɗa mashi,
[1/17, 7:45 PM] Jamila Musa Ws: ☄
☄☄
☄☄☄
*WANDA BAIJI BARI BA*
*AMEENCI WRITER"S ASSOCIATION* 📚✍🏻
*MEELAT MUSA*
*Domin samun littattafanmu sai ku nememu a group ɗinmu na facebook a*
*AMEENCI WRITERS NOVELS GROUP*
*PAGE 36*
***
*Y*ana ƙoƙarin fita farlo yaji wayarshi tana ringing da sauri ya koma dan ɗaukota,,,, jawahir ce,,,, yana ɗauka cikin kuka tace yaya kaga babs yace bazanje ba,,,,,
Sadiq yace to kiyi haƙuri idan na dawo sai inkaiki,,,, cikin kuka jawahir tace nidai idan ba yau ba bana so,,,,,, sadiq yace jawahir baba yace bazaki je ba,,,,,
Jawahir tace nidai yauɗin nan nake so,,,, ajiyar zuciya sadiq yayi sannan yace bani baban,,,,,,, tace ka kirashi da kanka kace kaine kace inje, sadiq yace to, sannan ya kashe wayarshi,,,,,
Sadiq yana kashe kiran jawahir ya kira baba, bayan sun gaisa ne, yace baba nine na aiki jawahir zata anso man wani saƙo,,,, baba yace bana so wata matsala tazo kuma ayi ta cewa kaza kaza,,,,,,
Sadiq yace baza a samu ba insha Allah, baba yace to Allah ya kyauta, sadiq yace ameen, sannan ya kashe wayar,,,,
Kiran jawahir yayi sannan yace jawahir kada ki kwana, kinji na faɗa maki?"" tace ai dama ba kwana zanyi ba, yau zanje yau zan dawo, sadiq yayi mata fatan alkairi sannan ya kashe wayarshi,,,
Tana gama waya da sadiq ta fito, tace innas yadai?"" inna tace Allah ya tsare, jawahir tace zanyo maki tsaraba, inna tace to,,,,, sai kin dawo,,,,,,
Jawahir tana zuwa ta shige mota taja abuɓta sai kanon dabo tunbin giwa,,,,,,
Sadiq kuwa ya nemi khadija tayi mashi ruwa tayi tsaki,,, don haka komawa yayi ɗaki ya zauna a gefen gado yana tunanin inda khadija ta tafi,,,,,,
Sadiq wayarshi ya ɗauka ya kira wayar khadija, amma sai yajita a kusa dashi tana ringing, hankalin sadiq ya sake tashi sosai, danshi idan ansashi neman khadija baisan ta ina zai fara ba,,,,,
Khadija kuwa tana can hankali ta kwance tana sheƙe ayarta abunta,,,,, tama manfa da lamarin wani sadiq ɗin banza can,,
Jawahir kuwa tana can ta ibi hanyarta hankalinta kwance tana tafiyarta cikin nasara da jin daɗi,,,,
Sadiq ganin zaman baya mashi yasa shi tashi fita,,,, don nemo khadija,,,,,
Banban suka sha,,,, dan sadiq yana fita jawahir ita kuma tayo gda, saboda haka basu samu haɗuwa ba,,,, tana dawowa wanka tayi taci gayunta abunta, sannan ta kama gado ta haye,,,,,,
Jawahir kuwa tana isa kano, gdan zarto ta wuce,,, zarto tayi farin cikin ganin jawahir kuma taji daɗi sosai, bayan sun gaisa, jawahir tace hajiyata kinsan abinda yake tafe dani ne"??"
zarto tace A, a, jawahir ta bata labarin aurenta, da irin abinda sadiq yake mata sannan tace, abinda nake so yanxun ki koya man yanda ake kula da miji,,,,,,,
zarto tayi wani irin ihu,,,, tace in sani tawa,, wato da kika tashi baki tsaya wurin kowa ba, sai kika taho wurina,,,,, jawahir tace sosai, saboda naga idan namiji yana tare dake bayan rabuwa dake saboda kula,,,,,,
Zarto tace haka ne,,,,, yanxun kiyi kalaci sannan mu fara,,,,,, jawahir tace tou,
sadiq saida yasha wahala harya gaji baiga khadija ba, dan haka ya haƙura yayo gda,,,,,,
yana zuwa ya shigo a gajiye, yana sauke numfashin gajiya,,,, ganin khadija kwance saman gado yasa sadiq cewa daga ina kike?""""
girgiza ƙafarta daga kwance sannan tace , nine zaka tambaya daga inda nake?""" irin maganar da sadiq ya taɓa faɗa mata ta maimata mashi,,,,,,
dariya sadiq yayi sannan yace ni nake da ikon tambayarki saboda nine na ajiyeki kuma nine na kawo ki london, kuma kula da rayuwarki ta zama dole a gareni,
Khadija tace so nawa kake kai mutum wurin yafika sanin wurin?"" sadiq yace ai ba wannan mukazo yi ba, aurenki nakeyi,,,, khadija tace to idan ka gaji basai ka sauwaƙewa kanka ka huta ba,,,,,
Sadiq yace Allah ya baki haƙuri duk abin baiyi zafi haka ba,,,, khadija tace lallai idan kana san zama dani dole sai ka ɗauke idonka daga gareni,,,,, na faɗa maka,,,,,
sadiq yace to,,,, khadija tace kuma idan kana da buƙata bada dubu ɗari dan fita zanyi, dariya sadiq yayi sannan yace A, a bana buƙata, tace ka huta,, yace ba komai,,,,,,
Miƙewa khadija tayi tana ƙoƙarin barin ɗakin sadiq yace ina zakije kuma yanxun?""" khadija tace ba nace ka fita daga harkata ba,,,,,
Sadiq yace bana fita daga harkarki saina faɗa maki,,,,, idan har kina ƙarƙashin ikona babu inda zakije,,,,,,,,, khadija tsaki tayi sannan tace an faɗa maka ni jawahir ce?"" itace ka raina kake dukanta kamar jaka, take tsoronka kamar mala,ikan mutuwarta,,,,,
Niko ban buguwa kuma baka da ranar da zanji tsoronka,,, sadiq yace duk miya kawo wannan maganar ne?"""
khadija tace dan idanma kana da ƙudurin dukana saika kiyayeni, sadiq yace ni ba aikina dukan mace ba,,,, itama jawahir da kike magana na daka, ƙanwatace , yar uwatace, rayuwata ce, banyi saida ita kuma itama batayi saida ni,
Kuma jawahir ko tana aure a wani wuri tayi laifi a gidan aurenta ni zanje in hukunta , saboda nine nasan darajarta,,,,,
khadija tace karuwar data gama balbaɗewa a hanya, maza suka gama jagalgalata kamar karya,,,,,,
Kallonta sadiq yayi sannan yace ba jawahir bace karya kece karya, dan kinsan yanda na sameki,,,,, kuma kika ce in rufa maki asiri na ɓoye maki ke banda baki da kuny a gabana zaki riƙa aibata man "yar uwa?"""""
[1/17, 7:45 PM] Jamila Musa Ws: ☄
☄☄
☄☄☄
*WANDA BAIJI BARI BA*
*AMEENCI WRITER"S ASSOCIATION* 📚✍🏻
*MEELAT MUSA*
*Domin samun littattafanmu sai ku nemu a group ɗinmu na facebook a*
*AMEENCI WRITERS NOVELS GROUP*
*PAGE 37*
***
*K*hadija tace naje na wulaƙanta ai dama wulaƙantattace, sadiq yace idan kika sake faɗin magana mai muni akan jawahir wallahi wallahi wallahi, saina maki rashin mutuci,
Ganin yanda sadiq yayi maganar ne, babu alamar wasa, yasa khadija kama kanta,,,,, sadiq yaci gaba da cewa,,,
Nine kike rashin kunya ba,, to kiyi iyakarki ni, amma kada ki kuskura ki sake tsalle iskanci yana sauka kan jawahir,,, kuma tunda abun ya zama iskanci ki shirya jibi idan Allah ya kaimu zan maida ki nigeria,,,,,
Khadija tace haba my?""" duk miye yayi zafi haka?"" ko inda take sadiq bai sake kallo ba yayi waje,,,,,,,,
Wayarta ta ɗauka ta fara kiran ƙawar banza,,,,, ta faɗa mata yanda sukayi da sadiq tace riƙe dai ƙawata ku dawo nigeria sai a sake shirya makaman yaƙi,,
Khadija tace to ƙawata ngd sosai,,,,, bayan khadija ta kashe wayarta, ƙawarta fati tayi dariya sannan tace haba yarinya dani kike zance,,,,,,
Yanda banda aure kema kin dawo mu zauna tare , ko abokiyar yawon gari na samu, ta sake sheƙewa da dariya sannan ta tashi daga wurin,,,,
Jawahir kuwa suna gamawa zarto ta ɗora, tayi ta bawa jawahir shawarwari tare da yanda ake kula da miji, da ƙara nuna mata mahimmanci haƙuri,
Dan ita rayuwa ba kullum ake samun abinda ake so ba, bayan sun gama ne zarto ta bata wasu kayan mata tace tayi amfani dasu suna da kyau kuma suna taimakawa wurin taka rawar rayuwar ma,aurata,
Bayan sun gama ne jawahir tace to suje kasuwa, dan ance kada ta kwana, haka suka shiga kasuwa jawahir tayi ta siyayyar kaya masu kyau da tsada, wai itama tana haɗa lefenta tunda sadiq baiyi mata ba,
Shima sadiq haka ta samu ƙananan kaya masu ta siya mashi sosai saboda shi ma,abocin san ƙananan kaya ne, turaren da yake amfani dashi dai bata samu ba, amma ta samu mai kyau da tsada ta siya mashi,,
Saida suka gama da kasuwa sannan sukaje gidan Auwal, suka gaisa da amarya, jawahir tayi masu dan alheri sannan ta nufi inda ake siyar mata da abinci, taje suka gaisa wurina komai yana tafiya daidai,,,,,, tayi masu fatan alkairi ta basu kuɗi sannan sukayi sallama,,,,,
Jawahir saida ta maida zarto gida ta bata kuɗi masu yawan gaske sannan ta kama hanyar gda,,,,,,,
Jawahir tana isowa kafin ta fita daga mota ta kira sadiq , bayan ya ɗauka suka gaisa tace mashi na dawo, yace to sannu ya gajiya?""" tace lafiya qalau, sadiq yace to a huta gajiya, tace yawwa,,,,,,
Saida ta kashe wayar sannan ta fita daga motar, mai gadi tasa da masu bawa flowers ruwa suka shigar mata da kaya ciki,
Inna sai murna take jawahir taje tafiya ta dawo ba,a nemota ba,,,, dariya jawahir tayi sannan tace waike innasco haka zanyi rayuwa ai ana samun sauyi,,,
Inna tace gaskiya naji daɗi, duk kayan ne nan?"" jawahir tace kema na siyo maki, inna tace naji daɗi ɗiyata tayo man tsaraba,,,
bayan sun shiga jawahir ta fidda tsaraba ta bawa innas nata tace gana babs a ajiye mashi, inna tayi godiya sosai, ita kuma jawahir wanka tayi sannan tayi sallah isha,i ta kwanta bacci,
***
*I*nna ce take ta kai kawo saboda yaune sadiq zai dawo, ita jawahir bata sani ba bai gaya mata ba, kuma inna bata faɗa mata ba,,,,,,
inna saida a gyara can a goge can, ita kuma jawahir fitowa tayi tana cewa innas zanje wani wuri saina dawo,,,,,
Inna tace don Allah kada kije ki samu wuri kiyi zaune,,,,, jawahir tace bazan daɗe ba insha Allah,,, inna tayi mata fatan alkairi,,,,,
jawahir tana fitowa da ja"afar ta haɗu yana ɗaga mata hannu, dariya tayi sannan taci gaba da tafiya bata tsaya ba,
Ta madubin take hangoshi yana ta ɗaga mata hannu tsaki tayi sannan tace banza, bani ka cuta ba kanka ka cuta gaskiya,,,,,
Shagon ɗinki ta taje takai ɗinki, bayan ta gama daga nan kuma ta wuce gidan hafsa,,,,,
Da gudu hafsat ta fito jin tsayuwar mota, ganin motar jawahir yasa ta rugowa da gudu tana cewa jawahir kece?"""
jawahir dariya tayi sannan tace nice mana, hafsat tace banza mu shiga kisha labari,,, dariya jawahir tayi sannan tace muji alkairi,,,,
bayan sun shiga hafsa tace yau ko ruwa bazan tsaya baki ba, labari zan baki mai yawa,,,,,, jawahir tace ina jinki,,,,,,
Hafsat tace jawahir kinsan fati muguwar ƙawa?""" jawahir tace na santa,,,,,, tace itace ƙawar khadija, jawahir tace to ina ruwana?"""
Hafsat tace ke banza kinsan su khadija sune sukaje suka kashewa fati aure, kuma suka bi mijin sukayi ta lalata dashi,
jawahir tace Allah ya kyauta,,,,,, hafsat tace to ita fatin ta ɗauki alƙawarin saita rama abinda sukayi mata,,,, ta kwashe labari kaf ta faɗawa jawahir wai mijinta idan ya nemeta sai ya bada kuɗi,,,,,
tsaki jawahir tayi sannan tace Allah ya sawaƙe,,, haka dai hafsat ta kwashe duk labarin zaman takewar auren khadija da sadiq, da kuma faɗa mata yau zasu dawo,,,,,
Jawahir tace ni baima faɗa man zai dawo ba,,,,, hafsat tace bari in kira maki fatin kiji, jawahir tace nidai babu ruwana matsalarsu ce ba tawa ba,,,,
hafsat tace ke banza ce bari mu kirata muji wace ake ciki yanxun,,, jawahir ta miƙe tana cewa gaskiya hassu kin canja hali ni kinga tafiyata,
Hafsat tace tsaya kiji, jawahir tace wallahi bazanji komai ba, tayi tafiyarta,,,,, niko nace su jawahir anji boni,
jawahir tana fita daga gidan hafsat gidanta ta nufa,,,, tana zuwa bayan tayi parking, ta shige ciki, tana zuwa kayan jikinta ta cire ta samu wani zai ta ɗaura,,,,,,
saida ta gyara gidan nan tas, ta share ta goge fesss sannan tabi ɗakin da turaren ƙamshi ta sa,,,, sannan ta shiga tayi wanka ta maida kayanta ta tafi gdan inna,,,,,,,,
tana komawa inna tace jawahir kin daɗe , ina kikaje?""" jawahir tace mota ta lalace innas, inna tace ikon Allah, daga haka bata sake magana ba ta shige ciki.............
[1/17, 7:46 PM] Jamila Musa Ws: ☄
☄☄
☄☄☄
*WANDA BAIJI BARI BA*
*AMEENCI WRITER"S ASSOCIATION* 📚✍🏻
*MEELAT MUSA*
*Domin samun littattafanmu sai ku nemu a group ɗinmu na face book*
*AMEENCI WRITERS NOVELS GROUP*
*PAGE 38*
***
*I*nna tabi bayan jawahir ta shiga ɗaki, tace jawahir sadiq ya dawo yace kina ina nace na aikeki!""",,,,, jawahir tace to,,,,,,,
Inna tace yaje ya ajiye khadija kila ya dawo yanxun, jawahir tace Allah yasa ya dawo lafiya,,,,
Inna tace ameen an gama abinci idan zaki ci, jawahir tace ni banajin yunwa,,,,,,,, inna tace to shikenan,,,,,,,
Inna fita tayi daga ɗakin, jawahir kuma toilet ta shiga tayo alwallah dan gabatar da sallah isha,i
Bayan jawahir ta gama sallah, ta tashi ta koma saman gado ta kwanta,,,,,, bata daɗe da kwanciya ba, taji maganar sadiq yana gaisawa da masu aiki,
Bayan ya gama taji shi ya shigowa farlo yana sallama,,,,, daga can take amsa sallama,,,,,,, jin maganar jawahir ciki yasa sadiq shima ya shiga ciki,,,,,,
Jawahir dake kwance, ta tashi zaune tana murmushi,,,,,, shima wani kasalallan murmushi yayi mata a daidai lokacin da yake matsawa kusa da ita, ya zauna a gefen gado,,,,,,,,
Bayan ya zauna tace sannu da zuwa,,,,,, bai amsa hannunsa yasa ya jawota jikinshi,,,,, ya rungumeta ya ɗora kanta a ƙirjinsa shi kuma ya ɗora kanshi saman kanta,,,,,,,,
Sannan yace ina inna ta aike?"" jawahir tayi shiri dan bata san ina zatace ba,,,, sadiq yace tashi mu tafi gida to,
Jawahir tace yaya nan zan kwana, sadiq yace yi haƙuri mu tafi,,,,, jawahir tace nidai gaskiya sai gobe,,,,, ɗagota yayi yana kallonta sannan yace bakiji daɗi na dawo ba?""""
Tace naji, yace bakiyi murna dana dawo ba?""" jawahir tace nayi,,,,, sadiq yace to muje don Allah,,,, ya ƙarasa maganar ciki sigar tausayi,,,,,,
Jawahir tace yaya na siyo maka kaya masu kyau,,,,,, murmushi sadiq yayi tare da cewa inye ɗan gayen ba,,,, mu gani,,,, sauka tayi daga saman gadon taje ta ɗauko mashi kayan ta kawo,,,,,,
Dariya sadiq yayi sannan ya ansa yana ɗagawa,,, jawahir tace to ka saka mu gani, yace ina , ba anan za,a nuna ba sai munje gida mun kulle ƙofa,,,,,,
Dariya jawahir tayi saboda yanda sadiq yayi maganar ne yayi mata wani iri,,,,,,, shima dariya yayi sannan ya miƙe tsaye , tare da cewa muje ki bar kayan anan gobe zanzo in ɗauka mana,,,,,,
Jawahir tace bari zan haɗa mana,,,, sadiq yace don Allah kada a tsaya haɗa kayan nan jawahir muje,,,,,,,,,,,, jawahir tace yanxun nan zan haɗa fa,,,,, sadiq yace bazaki gane ba,,,, muje gobe sai zan kawoki da kaina,,,,,,
Baki jawahir ta taɓe,,,,, sannan tace to bari inci abinci ,,,, sadiq yace kada kici abinci muje zan dafa maki,,,,,,, ya ƙarasa maganar yana ma jawahir wani irin kallo wanda karatun bazata ganeshi ba,,,,,,,,,
Tace to ina hijabin ,,,,, tsaki sadiq yayi yaja hannunta, tana cewa hijabina fa,,,,, bai sake magana ba,,,, suka fice daga ɗakin,,,,,,,,,,,,
A hanzarce yake jan hannunta,,, har sukaxo wurin motar, da kanshi ya buɗe ya jefeta,,,,, sannan ya zagaya ya shiga yaja motar suka bar gdan,,,,,,,,,,,,,,,,
Wayarshi dake ringing yace ma jawahir waye yake kirana ne?""" tace innas ce,,,, dariya sadiq yayi sannan yace bar innas ɗin nan ,,,,,,, wani kiran ne ya sake shigowa,,,,,,,
yace jawahir kashe wayar nan,,,,, jawahir tace kaidai ka ɗauka kaji,,,, murmushi yayi sannan ya kalli jawahir yace ɗauki kice ina tuƙi,,,,, jawahir tace ba ruwana kaida ake kira baka ɗauka ba saini?""""
murmushi yayi da gefen bakinsa bai sake magana ba,,,,,,, har suka isa gida,,,,,,,
suna zuwa bayan sadiq yayi parking,,,,, suka fita dukansu,,,,,,,,, jawahir ce a gaba sadiq yana bin bayanta,,,,, har suka shiga ciki,,,,,,,,,,,,
suna shiga sadiq yaja jawahir suka shiga cikin ɗaki,,, a gefen gado suka zauna,,, sannan sadiq ya faɗawa jawahir buƙatarshi a gareta tare da tambayarta nawa zai bata?""""
kallonshi jawahir tayi duk da ƙaranci shekarunta ta fuskanci sadiq yana cikin wani yanayi,,,, dan haka tace Allah ya sawaƙe,,,,,,, ina matarka kuma idan zaka kwanta dani saika biyani kuɗi?"""
to miye amfanin auren?"" ai shine banbancin aure da karuwanci,,,,,,,, ita karuwa zuwa maza da dama suke zuwa kuma dukansu ta ɗauke masu buƙata su kuma su biyata,,,,,,,
wata tanayin karuwanci dan buƙatar kanta wata kuma tanayi da son abun duniya.............
[1/17, 7:46 PM] Jamila Musa Ws: ☄
☄☄
☄☄☄
*WANDA BAIJI BARI BA*
*AMEENCI WRITER"S ASSOCIATION* 📚✍🏻
*MEELAT MUSA*
*Domin samun littattafanmu sai ku nemu group ɗinmu na facebook*
*AMEENCI WRITERS NOVELS GROUP*
*PAGE 39*
***
*J*awahir taci gaba da cewa sadaki ka bayar ka aureni dan haka ni bana buƙatar kuɗi Allah nake so ya biyani danshi kaɗai yake da abinda zai bani,,,,,,,
Ina neman gafara akan dakon zunubin da nayi a baya,,,,, kuma ina neman gafara da shiriya mai ɗorewa,,,,,,
Miƙewa jawahir tayi ta fara cire kayan jikinta,,,,,, kallo sadiq ya bita dashi,,,,, cikin tausayawa,,,,,,,,, da mamakin halinta,,,,
Saida ta gama sannan ta matsa kusa da sadiq,,,, murmushi yayi sannan yayi mata wani irin kallon, wanda yasa ta jin kunya,,,,,,,,
Jawota sadiq yayi jikinshi, yana farin ciki,,, ita kuma jawahir tsoro ne ya bayyana a fuskarta, idonta ya cika da hawaye,,,, cikin tausayawa sadiq yace babu wani abu ki yadda dani bazan cutar dake ba,,,,,,,
Cikin kuka jawahir tace to,,, janta yayi suka hau saman gado sosai, daga nan wasan nasu ya canja saloooo,,,,,,,,
Niko komawa nayi farlo na samu wuri na zauna dan filin ɗakin na sadiq da jawahir ne,,,,,,,,
Bugun ƙofar akeyi ana ƙarawa,,,, babu sassaci kuma abun baya neman ƙarewa,,,
Sadiq ne ya fito da gajeren wando jikinshi tare da cewa waye?""" khadija tace nice,,,,, taɓe baki sadiq yayi sannan ya buɗe ƙofar,,,,,,,,
Da sauri ta shigo cikin farlon kamar an jehota,,,,, sadiq shi kuma ya ɗaure fuska babu alamar wasa sannan yace ya akayi ne?""" khadija tace wannan wane irin wulaƙanci ne?""""
Wannan wane irin cutane?"" wane irin zalinci da cin amana ne?"" sadiq yace miye?""" khadija tace kawai sai ka taho nan ?""" murmushi sadiq yayi sannan yace mu tafi,,,, ina zuwa,,,,, wuri khadija ta samu ta zauna ,
Dan tasan idan ta shiga ɗakin jawahir tana iya ci mata uwa,,,,, sadiq yana shiga ya rufe ɗakin,,,,, jawahir dake kwance tace ma sadiq waye?"""
Ba tare daya kalli inda take ba, yace sweetheart ce, jawahir