Author : MEELAT MUSA Category : African Stories & Novels
tayi hauka, har zai koma yaji inna tayi sallama, da sauri ya fito daga ɗakin,
Inna sai murna take ɗanta ya dawo, tayi farin cikin ganin sadiq yanda ya koma gaba ɗaya ya canja, tabarma ta shinfiɗa mashi ya zauna sannan ta kawo mashi ruwa, ya ɗauka yasha ɗan kaɗan, sannan ya kalli inna yace inna yanaga gidan nan ya koma haka?""
waye ya gyara shi?"" gaban inna ya faɗi saboda tasan itama tana sakaci wurin kula da halin jawwahir, kallon sadiq tayi sannan tace jawwahir ce, idanuwa sadiq ya zaro yace jawwahir kuma inna?"" waccan motar fa?"" inna tace itama tata ce, ɗaure fuska sadiq yayi lokaci guda zufa ta keto mashi, sannan yace waye wansa ya siya mafa mota?"" ita kuma jawwahir ta baza kunne dama tasan ranar da sadiq zai dawo ta ɗauki motar takai ta ɓoye ta, shima dan yaxo yaga halin da take ciki shine dalilin daga sa bai gaya na inna zai dawo ba,
Miƙewa yayi sannan yace haba inna kuma sai ku zuba ido kamar jawwahir da mota waye ya siya mata?"" inna ta miƙe tsaye cikin damuwa tace wallahi sadiq ban sani ba, idanuwa sadiq lokaci ɗaya suka sake launi dan sadiq wata irin zuciya gareshi, duk iskancin jawwahir shine ma yake ƙanƙwasa ta amma bayan haka da yanxun ta wuce haka,
kallom motar ya sakeyi sannan ya kalli inna yace kamar jawwahir tazo ta fasa gidan nan tasa get ta kawo mota da interlock ta saka amma inna a rasa waye zai hukunta ta, ƙarfin wa tafi ne a gidan nan?"" wannan maganar itace ta farkar da jawwahir daga baccin da take, cikin tana ne taji ya fara zuuuuuuu kululu hankalinta ya tashi yanda taji maganar sadiq ma yasa jikinta ya mutu ta kasa tashi, tana kwance har yanxun wace ƙarya ma zatayi dan fitar da kanta, hawaye ya fara zubowa daga idon ta dan tasan yau ne ranar lunfashin ta na ƙarshe,
Kuka jawwahir ta fara lokaci guda ta nemi miyan bakinta ta rasa da maƙoshinta gaba ɗaya ya bushe , wani kashi kashin wahala taji ya taho mata a daidai lokacin da taji inna nacewa kada ka daketa na faɗa maka, jawwahir najin haka da sauri ta sauko daga saman gado, a lokacin da sadiq ya shigo ɗakin tana ganinshi da sauri ta durƙusa ƙasa tana kuka hannunta ta haɗa wuri ɗaya ta fara cewa bara in faɗa maka gaskiya, wani irin kallo sadiq yayi mata wanda yasa ta saki fitsari, jikinta sai kyarma yake sadiq yace mina faɗa maki ne?"" dake nake?"" yayi maganar cikin hayani wannan karon jawwahir cewa tayi bafa tawa bace ba, ajiya aka kawo man sassauta miyarshi yayi sannan yace ita wanda ta baki ajiya a gidansu babu wurine?"" saike da kika raina naki iyayen ?"" jawwahir kallon inda inna take tsaye tace innas don Allah kiyi magan......""" kafin jawwahir ta ƙara maganar sadiq ya shaƙota, lokacin da jawwahir taji sadiq ya shaƙota tsananin tsoro yasa ta suma,
Inna tace sadiq ka ƙale yarinyar nan, yace haba inna wai sai kice a barta jawwahir mi take siyarwa za zai siya mata mota,?"" wai miyasa ma lonacin da take iskanci baku faɗa man ba?"" fita yayi daga ɗakin ƙara kallon motar yayi sannan yace Allah yasa rayuwarmu takai gobe, zata kwamce bata zo duniya ba, yana faɗin haka ya fita daga gidan,
Yana fita inna tana matsawa kusa da jawwahir taji ta taka lema, dubawa tayi tace wato futsarin wahala tayi, inna tace to yaƙin uhudu bai zo ba, amma gaki a some a banza a wofi, idan ance ki bari bakya ji, niko nace ai jawwahir bata ga komai ba,
fita inna tayi taxo ta zuba ma jawwahir ruwa sannan ta janyeta gefe ɗaya ta goge wurin,
sadiq yana zuwa gidan shi ɗaki ya shiga, yana shiga saman kujera 2seater ya kwanta, kanshi na kallon silin ɗin ɗakin, hawaye yake sosai yana baƙin cikin irin wannan hali na jawwahir, shin wai wace hanya ma zaibi ya gyara mata rayuwatar?"" gyara kwanciyarshi yayi saman hannun shi na dama, sannan yaci gaba da kuka sosai, haka yayi ta kuka har abokinshi kalilu ya shigo ya sameshi, wanda tare suke dashi a gidan na sadiq, kalilu tsayuwa yayi ganin sadiq na kuka, yace mai gida ya da kuka kuma?"" daga dawowa?"" kai da zakayi farin ciki sai kayi damuwa?"" sadiq yace cikinshi yake mashi ciwon dan duk duniya sadiq baya san ya faɗa na wani halin jawwahir idan da hali ma har inna jawwahir da ta gane da ta daina wani abun a gabansu, haka yasha kukanshi har ya gaji kuma yayi alƙwari a ranshi gobe sai yayi mata dukan dasai tayi jinya,
****
*J*awwahir tunda ta some jiya sai yau da safe ta farfaɗo, ganinta kwance a ƙasa yasa ta fara tuno abinda ya faru jiya, ajiyar zuciya tayi wato sadiq ya dawo, da sauri ta miƙe taje tayi wanka ta fara shirin barin gidan, saida ta shirya tsaff, ta fito da sauri har ta kusa kawo zaure ta tuna tabar wayarta a ɗaki da sauri ta ruga ta ɗauko ta, inna na mata magana amma bafa bi ta kanta ba, tana shigowa zaure ta ganshi tsaye ya rungume hannu a ƙirjinshi wanshi, saura kaɗan ta bugeshi ma, kallonta yayi sannan yace bakiji ana kiranki?""
jawwahir tace ai dama yanxun zan koma yace to muje tayi gaba zuuuiiii zuiiiii shi kuma yabi bayanta, suna shiga jawwahir tayi ɗaki da gudu, bayan sadiq ya gaishe da inna shima ɗakin innar ya shiga, jawwahir dake kuka ganin sadiq yasa ta ɗauke nunfashin ta, zama yayi kusa da ita, sannan yace mata kalleni, ɗago kai tayi tare da ɓata fuska tace kayi haƙuri don Allah, yace ai ba wani abu nace maki ba, kawai nace ki kalleni, abinda jawwahir ta tsana sadiq yace ta kalleshi idan ta kalleshi ji take kamar zata suma,, ya gane bata san haka shi yasa shi kuma yake horata ta haka, idan ya daketa to taƙi ta kalleshe ne,,
Yace bakiji ina magana?"" jawwahir tace don Allah kayi haƙuri, yace wato jikinki yana maki ƙaiƙayi ko?"" jawwahir tace ah ah, yace to kallarni , jawwahir tace don Allah kayi haƙuri hawaye suka zubo mata daga cikin idonta, hmmm yace sannan yace ina kika samo mota?"" jawwahir tace saye nayi, yace to bani maƙullin ,,,, tashi tayi ta ɗauko mashi yace wuce muje, jawwahir tace ina?"" yace muje nace maki?"", jawwahir tace to, miƙewa yayi sannan yayi gaba jawwahir tabi bayan shi, suna fita yace ma inna zaije ya dawo, tace to, wurin motar ya nufa jawwahir taje ta buɗe get , sannan tazo ta buɗe motar sadiq ya shiga, itama shiga tayi sannan ta fitar da motar ta fito ta rufe get in sannan ta koma ta shiga, sadiq yace muje, jawwahir tace ina zamu yace muje kawai, tafiya jawwahir ta fara tafiya da mota, saida suka hau titi sannan sadiq ya nuna mata hanyar da zata bi, sannan suka fara tafiya............
[1/17, 7:38 PM] Jamila Musa Ws: ☄
☄☄
☄☄☄
🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥
*WANDA BAIJI BARI BA*
🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥
*AMEENCI WRITER'S ASSOCIATION* 📚✍🏻
*MEELAT MUSA* 🌹
*PAGE* *13*
***
*H*aka yaci gaba da nunawa jawwahir hanya da hannunshi ba tare da tayi magana ba, tafiya sukai mai nisa, yanda suke shigewa cikin lungunna yasa jawwahir ta fara tsoro, abinda ya faɗo mata a rai shine, ban shirya kasheki ba amma da sannu ni zan zama ajalinki, innalillahi wa"inna ilaihir raji"un, tace daidai lokacin data taka wani wawan burki, kallon ta sadiq yayi ba tare da yayi magana ba, ita kuma ta maida dubanta gabanta, ita kuma ba tare da ta kalli inda yake ba,
Har yanxun baiyi magana ba don haka jawwahir cikin tsoro tace yaya mai ya ƙare kallonta ya sake yi sannan yace dama mai yana ƙarewa a motarki?"" jawwahir tace nima bansan babu ba, sadiq yace to fita, buɗe mota jawwahir tayi ta fita, zagayawa yayi ya koma mazaunin data tashi sannan yace ta shigo,
Jawwahir tace aaa, aeh basai na shigo ba, kallon nisan wurin takeyi idan zata fita lallai akwai aiki, kallon sadiq tayi ta fara kuka tace don Allah na bari, yace kinyi laifi ne?""jawwahir tace ah ah, yace to miyasa kike bada haƙuri bayan kinsan baki laifi ba?"" jawwahir tace wai dan na gaji ne, yace to naji kuma nayi haƙuri shigo,
Jawwahir ta zagaya ta buɗe motar sannan ta shiga, ta rufe motar , shima shigo da ƙafafuwanshi yayi cikin motar sannan ta ya rufe ƙofar, bayan ya rufe yasa lock, sannan ya kalli jawwahir yace kinsan abinda nake so dake?"" tace ah ah, yace ashe kinsan baki iya iza wutar kika hurata ko?"" jawwahir bata fahimci abinda yake nufi ba, saidai tace kayi haƙuri,
Yace kince a gabana zaki ce man mahaukaci, to faɗi, jawwahir tayi shiru, yace kuma nace kada kiyi gini shine kika ce ko yaƙin uhudu yaxo sai kinyi?"" na hanaki damfara bazaki daina ba ko?"" yau sai kin faɗa man a ina kika samo wannan motar wallahi wallahi wallahi, kinji wallahi ukku?"" idan har baki faɗa man ba billahillazi la"ilaha illahu yau baza ki koma gida ba, kuma gobe idan Allah ya kaimu zanyi tafiya, idan na tafi sai nayi shekara ɗaya zan dawo , saboda haka zan kulleki babu abinci babu abinsha anan yunwa zata kamaki har ki mutu ki bushe tsuntsaye su cinyeki kowa ya huta,
Gaban jawwahir sai dukan ukku ukku yake, kuma yanda sadiq yayi magana babu wasa sannan kuma yayi rantsuwa, kuma ko baiyi rantsuwa shi magana ɗaya yake yi, idan yayi baya canjawa, kuka jawwahir ta fara sosai, bai sake magana ba, sai kuka take tana shan majina amma har yanxun bai sake kallonta ba kuma bai sake magana ba,
Jawwahir tace kai ɗan uwana ne, ka rufa man asiri zan faɗa maka, baiyi magana ba, amma yana kallonta, rufe idanuwanta tayi sannan tace Alhaji ya bani ita, sadiq yace mi kikayi mashi ya baki?"" jawwahir tace number na bashi ya bani, sadiq yace daga bada number sai ya baki wannan ƙatuwar motar kinsan ko miliyan nawa take?"" jawwahir tace iyakar abinda na sani kenan,
ita kuma abinda yasa ta faɗa mashi haka tunanin ta tunda Alhaji yace zai fada mashi a tunaninta ya faɗa mashi shi yasa ta faɗa ma sadiq gaskiya,
yace shi kuma get da kika sa a ina kika samo shi?"" jawwahir tace bashi na ciwo shi, yace wurin wa?"" tace mutumin baya nan , ina yaje?"" tace yayi tafiya, girgiza kanshi yayi sannan yace shi kuma interlock fa?"" tace duk shine yake siyarwa, sadiq ya kunna motar yaci gaba tafiya,
Tafiya yayi sosai har suka isa ƙofar wani gida, bayan yayi parking yace ta fito, jawwahir ta sadaƙar dan ta haƙura da rayuwa, bayan ta fito sadiq ya ciro wani makulli ya buɗe ƙofar yace ta shiga yana zuwa, jiki babu daɗi jawwahir ta shiga, shi kuma wurin motar ya dawo, bayan motar ya buɗe ya ɗauko wata igiya, sannan ya rufe motar ya shiga gidan ya kulle,
Idan nace maku zan tsaya in faɗa maku iya azabar da sadiq ya bawa jawwahir zan ɓata lokacina, amma saida ya ɗaureta da igiya gam, sannan ya ɗauko wasu bulali daya tana da yayi mata shegen duk, harbi tasha shi saida tayi luguf sanann ya zauna yace mata ke har guda nawa kike?"" idan an faɗa maki magana kin raina ma mutane hankali?"" to yau babu wanda yaji babu wanda zai gani anan gidan zan kasheki, ya nuna mata wata rijiya da hannunshi yace kinga can?"" jawwahir sai kuka take ta kasa magana yace duk gawawwakin mutane ne , saboda haka kema yanxun zan ɗauke ki in jefa ki ciki kowa ya huta, jawwahir zatai magana yakai mata wani nushi a baki, da sauri ta sauke kanta ƙasa ga azaba ga hannunwan ta ya ɗaure, sadiq yace ƙarshen marar jin magana kenan , duk wanda baiji bari ba, to babu ranar da rayuwarshi zata zauna lafiya,
jawwahir tayi shiru sai mazurai take, ga ƙafarta da sadiq ya taka mata da ƙarfi kila ma ta kare, saida ya gama kasheɗin shi sannan yaci gaba da dukanta, saidai yaga jawwahir ta daina nunfashi sannan yaja kasa ya fita daga gidan, motar ya buɗe ya jefata ciki, sannan ya rufe gida, yaja motar suka bar wurin,
Lokacin da sadiq ya iso gida inna bata san abinda ya faru ba, ita dai shi kaɗai taga ta gani don haka yana fitowa wurinta yaje, tace mashi ina jawwahir?"" yace tama zuwa, bankwana yayi ma inna yace yau zai wuce, inna tace tun yau?"" yace Eh, kuɗi ya bata masu yawa sannan ya fita daga gidan,
Inna taci gaba da hidimar gabanta, dan aiki yayi mata yawa, kuma gashi dare ya fara dan gaf ake da kiran sallah magrib, inna tama fitowa daga kicin taga kamar motar a buɗe matsowa tayi dan ta rufeta, ganin jini yana zubowa yasa tayi saurin buɗe motar da sauri dan ganin miye??"" jawwahir ta gani kwance ko nunfashi batayi wani irin salati inna tayi ta kwara ihu tayi waje da gudu a kawo mata ɗauki ɗiyar amana ta mutu,
Sadiq kuma yana fita daga gidan inna ko gidanshi baije ba, ya ƙara ma wandonshi iska dan tuni ya manta daya fita daga cikin garin,
Inna data fita tana ihu, ja"afar ya fara ganin ta, sai wasu abokan sadiq, haka duk sukayo wajen inna tace suje suga abinda ta gani, haka suka rantaɓo sukayo cikin gidan, gankn halin da jawwahir take da sauri ja"afar yace inna su shiga mota suje asibiti, inna mayafi kawai tajawo saman igiya, ɗaya daga cikin abokan sadiq suka buɗe get, ja"afar ya fice da gudu,
asibiti mai kyau yakai jawwahir kasancewar asibitin kuɗine babu wani ɓata lokaci aka shiga ceton ran jawwahir, ita dai har yanxun bata san inda kanta yake ba,
Ranar dai daga inna har ja"afar a asibiti suka kwana, koda baba ya dawo abokan sadiq suka faɗa mashi abinda ya faru amma dole baba ya haƙura tunda baisan asibitin da suke ba, kuma inna tabar wayarta a gida,
***
Kwanan jawwahir biyu a asibiti amma har yanxun bata buɗe idonta ba bare ma tasan tana duniya ko a ƙiyama take?"" gaskiya jawwahir tana jin jiki sosai""""""!!!!!
Baba kuma ja"afar ne yaxo yakai shi asibitin ya tausaya ma jawwahir a halin daya ganta, amma babu wanda yasan yanda abin nan ya faru, ita dai inna tasan babu wanda yayi ma jawwahir wannan abun sai sadiq, halim da jawwahir take dole duk taurin ranka idan ka ganta sai ta baka tausayi, ko kuma ka zubar mata da hawaye,
Ranar da jawwahir ta kwana huɗu a asibiti ta fara buɗe idon ta a hankali a hankali, idan ta buɗe sai ta rufe, inna tana cikin damuwa sosai kuma tace ma baba kada ya faɗa ma kowa don Allah azo aga halin da jawwahiri tace ciki ta bani , amma a bari ta farfaɗo ita dai tasan tare suka fita da sadiq, batasan yanda hakan ta faru ba, baba yace ba komai insha Allah zata samu sauƙi,
kalilu abokin sadiq da kanshi ya kira sadiq ya faɗa mashi halin da jawwahir take ciki, da kwanakin da tayi har yanxun bata farfaɗo ba, sadiq yace Allah ya sawaƙe, kalilu yace amin,
Sadiq har a ranshi baiji daɗi ba, kuma shi baiyi haka dan cuta ba, wai yayi ne dan jawwahir ta daina abunda take, amma yanxun daya ji halim da jawwahir take ciki ya shiga cikin damuwa, tsaki yayi sannan ya tashi daga inda yake zaune yace ai halinki yaja maki da lokacin da aka ce ki daina da kin bari duk da haka bai faru ba, tsaki yayi sannan yace Allah ya ƙara ma wanda bayajin bari,
***
satin jawwahir ɗaya a asibiti Allah yasa ta fara samun sauƙi, amma bata iya cin komai, tea kaɗai take sha, sai ƙafarta data ce ma inna tana mata ciwo, kuma likitoci sunyi bincike sun faɗa ma inna buguwa ce, kuma an bata magunguna, jawwahir tunanin irin azabar da zatayi ma Alhaji duk shine ya haɗa wannan masifar sai kuma idan ta gama dashi shima sadiq sai taga bayanshi, kunji halinko,?"" wanda akai ma haka basai ya haƙura ya bari ba, tunda ance ta bari ai sai tayi haƙuri, hmm wanda baiji bari ba, lallai yana cikin wahala,
***
Satin jawwahir huɗu a asibiti aka basu sallama, dan ta samu sauƙi sosai kuma yanxun jinta take koda zaki tana iya ƙarawa bare sadiq kayan banza,
****
satin su biyu da dawo daga asibiti, kashedi na farko da sadiq yayi mata maganar gina ɗaki ne, dan haka ta ɗaura ɗamara dashi zata fara, dan haka wanka tayi taci uban gayunta, ta ɗauki wasu takaddun gida na boge wanda babu gidan kawai sawa tayi aka mata su, ta fito a tsakar gida tace ma inna innas mun tafi nema ayi mana fatan alkairi, inna batayi mata magana ba, wannan ba damunta yayi ba, almajirin da yake ma inna wanke wanke jawwahir tasa ya buɗe mata get, sannan ta fice daga gidan,
Tafiya tayi mai nisa sosai, har ta iso inda zataje, bayan tayi parking ta buga waya abinda tace kawai taxo wurin, to babu damuwa sai kaxo, ta ɗan daɗe sannan mutumin da tayi waya dashi yaxo, dama sun gama magana don haka bashi takaddun gidan tayi shi kuma ya bata adadin kuɗin data tambaya, sannan tace bayan wata biyar zata dawo ta bashi kuɗin shi, yace to, hauka ɗaya da yayi shine baibi jawwahir yaga inda gidan yake ba, kawai ya anshi takaddu gani yake ya kama, kuma banda sakarci babu shedu babu komai,
daga wurin shi gidansu hafsa ta nufa, tajeɓta ware kuɗin da zasuyi partyn candy, sannan ta nufi gidan wani bilo ta bada kuɗin bulo da siminti da yashi sannan ta bada address ɗin gidansu , haka da ta shiga daddage ma kuɗi uwa saida ta kashe mai isarta sannan tayo gida,
****
*T*un 8:05am masu aikin gina ma jawwahir ɗaki suka zo, haka aka ɗora gini da inna da baba dai babu wanda yayi mata magana, dan kullum abun nata ƙara gaba yake, sati biyu akai ana gina ma jawwahir ɗaki , an gina mata parlour da bedroom sai bathroom, kuma an fente ɗaki fess , saboda haka jawwahir abinda take so yanxun kujeru da gado da plasmer duk dai abinda zai ƙayata mata ɗakin tana nema,
Dan haka