Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

WANDA BAIJI BARI BA Rayuwar Ƙarya da Nadama by MEELAT MUSA

Author :  MEELAT MUSA Category :  African Stories & Novels

Chapter   16 / 28

45K to 48K   out of 83K words

fasa ƙara tana ihu ta kuka ta shiga ukku ta kashe kanta,

aiko jawahir kafin rana ta faɗi tuni maryamu ta kunbura ta fara tsatstsagewa haka yarinyar tayi ta fashewa jikinta yana tsagewa, yarinyarnan ta mutu, amma duk wannan baisa larba tayi ladabi ba,

maman ashiru tanajin labari taxo ta ɗauki ɗanta, don haka sai kin kula, kinga nayi nan, ga wurin ruwa can kije ki iba kinji ko?"",,,,,,,,, jawahir tace nagode , bayan ta tafi ne, jawahir tace lallai kinga ishara, shi yasa idan zaka gina ramin mugunta kayi shi ɗan ƙarami dan ta gina babba gata nan ta faɗa saman, ta rasa "yarta, ta huta, tsaki tayi a daidai lokacin data tsugunna a bakin ruwa ta saka tulun ta fara iba,

Lokacin da sadiq ya isa ƙofar gida wani dattijo ya gani tsugunne, parking yayi sannan ya fito da niyar shiga cikin gida, mutumin yayi mashi sallama, sadiq ya amsa, suka gaisa, mutumin yace don Allah jawahir nake nema, sadiq yace lafiya dai?""",,,,,

mutumin yace dama takardun gidan na dawo mata dasu ta bani kuɗina ina da wani uziri dasu, sadiq yace yaushe ta anshi kuɗin ne?""",,,,,,,,,, yace an daɗe ne sosai gaskiya, sadiq yace nawa ne kuɗin?"",,,,,,,, mutumin yace dubu ɗari biyu ne, sadiq yace ansar takardar yayi ya duba, yaga ba wata takardar gida bace ba kuma ta fili bace,

abinda aka rubuta a jikin takardar shine, tsoho kayi wauta daka bani kuɗin ka, wanda kaba ya karanta wannan saƙon zai faɗa maka haka, idan kuma kayi gigin zuwa gdanmu ka faɗa ma azzalimi dakai dashi duk zanyi maganinku,

tsaki sadiq yayi sannan yace baba data baka baka bawa kowa ya gani ba?""",,,,,, baba yace babu wanda na bawa, iyalina ce bata da lafiya shi yasa ma na buƙaci kuɗin, sadiq yace to, motar ya koma ya ɗauko kuɗin ya bashi, ya ansa yayi godiya ya tafi, shi kuma gida ya shiga,

Sallamar sadiq yasa inna fitowa daga kicin tana mashi sannu da zuwa, ansawa yayi sannan yayi mata barka da aiki, ta nasa, inna tace ina jawahir ne?"" yace ya barta a kauye inna tace bazai yuwu ba, saiya koma ya ɗaukota, sadiq yace kiyi haƙuri kwana goma kawai zatayi, inna tace sam sadiq yace don Allah ki barta zanyi tafiya gobe sati ɗaya zanyi idan na dawo zanje in taho da ita, inna tace Allah yasa rayuwarmu takai,

jawahir tayi sallama da tulu tiƙi tiƙi akanta, ta shiga gida, larba ta fito daga ɗaki tace dan uwarki sai yanxun kika dawo?""",,,, jawahir tace na tadda layi ne a wurin, larba tace layi dan ubanki famfo ne?""",,,, jawahir tayi shiru, cewa tayi kama man in sauke larba tace idan saina kama maki ki kwana dashi a haka,......

Sadiq kuwa yana fitowa daga gidan inna gidanshi ya nufa, yana zuwa kayan jawahir ya ciro daga mota, yakai ɗakinshi ya ajiye su, sannan ya ɗauki motar ya maida gidan inna,,,,,, ya ci abincin rana, sannan yabar gidan,

gajiya tayi da tulun saman kanta dan haka ta fara kacaniyar saukewa, saidai ta jingina da wannan bango ta raɓa nan, tana dubarar saukewa amma ta kasa, saboda haka tana cikin haka akayi rashin sa"a tulun ya taɗi ƙasa cusss ya fashe, da gudu larba ta fito daga ɗaki, ganin tulunta ƙasa wanwar yasa ta fara zungura uwar jawahir zagi,

jawahir tace to ai nace ki sauke baki sauke ba, ni kuma na gaji, tace wato da gangan kika fasa ko?"",,,,, jawahir tace dama anayin abu dan san raine?"",,,,,,, larba tace to kinjawa kanki yau babu ke babu abinci wallahi saidai ki kwana da yunwa,

jawahir batayi magana ba, ta wuce taje ta samu wuri ta zauna, larba ta ƙara masifarta da bala"i, amma jawahir bata sake kallon inda take ba,

to banan gixo ke saƙar ba, da daddare jawahir ta kasa bacci, dan ɗaki biyu ne, ɗaya na baba ɗaya na larba, amma da jawahir ta shiga ɗakin korota tayi tace wallahi baza ta kwanar mata a ɗaki ba, tunda ta fasa mata tulu, jawahir tanaji tana gani larba ta korota waje,

ga masifar sanyi ga baba abun kwanciya, kuma babu abinda zata shinfiɗa ta kwanta akai bare ta lulluɓe ga yunwa na damunta, azaba goma da ashirin ta dami jawahir, kayan da sadiq ya bata nata, sune ta ɗauko ta ɗauki doguwar riga ta shinfiɗa a ƙasa, sannan ta samu wata hijabi ta lulluɓe,

wasu hawaye masu zafin bala"i suka gangaro mata daga idonta, abinda ta fara tunawa jiya kamar yanxun tana nan ta haye saman gadon inna ta lullɓe da ƙaton bargo, ta goge hawayen ta, sannan taci gaba da tunani rayuwa daban daban, haƙiƙa duk wanda baiji bari ba, lallai yana tare da masifar rayuwa, duk rashin jin bari shine yakaita haka, da tayi haƙuri ta gyara halinta da ta zauna lafiya, da kowa,

kuɗin da gareta a account ta fara tunani, sannan ta sake goge hawayenta gata dai a duniya amma basu mata amfanin komai, ta kuntata wasu dan ita ta gyara tata rayuwar amma Allah ya hana mata jin daɗin, wani tunani tayi wanda yasa ta kuka sosai,

Wato da mutuwa tayi haka zata tafi tabar kuɗin taje ta samu azaba mai tarin yawa a wurin Allah, wanda kuma sukaci sunci halak, ajiyar zuciya tayi sannan tace ya zama dole in gudu daga gidan nan inje inbiya mutane haƙƙinsu ko dan in samu tsira saboda babu abinda ya hanani zaman lafiya nake ganin masifu sai cin haƙƙin mutane da nayi,,,,,,,,,,

Tashi tashi taje tayi alwallah ta kama salah wanda itama bata san dalilin yinta ba, gadai kuɗi ta danfare amma Allah ya hana mata cinsu,

***

*H*ar gari ya waye jawahir bata daina sallah ba, haka baba ya wuce ta yaje masallaci har ya dawo jawahir sallah take, haka ya wuceta ya shiga ɗaki , har hantsi ya fito jawahir bata daina sallah ba, baba daya fito zai fita kasuwa, yace waike sallah bazata ƙare ba?"",,,,,, kamar jira jawahir takeyi baba yayi magana ta ɓarke da kuka, baba yace lafiya?""",,,,, larba ta fito daga ɗaki tana cewa har wani lafiya kake tambayarta?""",,,,,,, ka wani zo ka tasa ta gaba sai kallo kake da Allah tashi kaje inda zakaje, haka baba ya miƙe simi simi ya fice daga gidan,

larba ta kalli jawahir sannan tace wannan kayan fa?"",,, cikin kuka jawahir tace nawa ne, larba tace kawo su nan munafika, tattara kayan tayi ta nashe su duka, sannan ta koma ɗaki, jawahir tana wurin ta haɗa kanta da gwuiwa sai kuka take,

Sadiq a kan hanya sukai sallar asuba, sun tun kari abuja haiƙan dan dan jirgin ƙarfe goma zaibi, zuwa *netherlands* dan akwai abinda zai kaishi sati ɗaya zaiyi ya dawo,

***
Kwanan jawahir huɗu a kauye sai fuskantar azabobi take iri iri babu wani cimar kirki sai uƙuba da masifa, sai tsangwama, jawahir dai yanxun har kiwo ake zuwa, gaba ɗaya ta firgice idan ka ganta ka rantse tayi shekara, dan larba bata sauƙaƙa mata,

*Y*au an tashi da wani irin gagarumin tashin hankali a gidan Alhaji, wato Alhajin da jawahir taso tayi aiki a comparnyn shi, wanda sukai faɗa tace saita ga ƙarshenshi,

to yau haka wanda ba,asan ko su waye ba, sukaje har gidanshi sukai masji yankan rago, kuma yace ya basu kuɗi sukace basa buƙatar kuɗi ko wani abu rayuwarsa kawai suke so, don haka saida suka daddatsa alhaji suka mashi gunduwa gunduwa, kamar kifi,

to gida dai ya cika kowa da abinda yake cewa, wani baban ɗanshine "yan sanda suke ma tambaya, ko Alhaji yana da wasu abokan hamayyane?""",,,,,,, yace shidai mutum ɗayane ya sani, ya faɗi wani abokinshi, haka dai kayi ta tambaya tare da ci gaba da binci ke,

Wani ƙanin Alhaji ne yace to duk wanda aka san yana da matsala da Alhaji aje a kamashi idan an kamosu bincike zai nuna ko waye,

Haka akaci gaba da binci abokan aikin alhaji sukace akwai mata yarinya wanda a gabanshi ta faɗi tace sai taga ƙarshen Alhaji kuma itace ajalinsa, akace to a bari a fara suturta shi sannan asan abunyi,

haka aka shirya alhaji akaje aka kaishi makwancinsa kamar yanda addini ya tanada, bayan an dawo ne daga jana"iza, yan sanda suka fara kame duk wani aka san yana da matsa da Alhaji dan bincike idan aka gano mai laifi sai a hukuntashi,

Motar "yan sanda ce a ƙofar gidansu jawahir, yaro aka aika yayi sallama da mai gidan, bayan wani lokaci ya dawo yace ance baya nan, yace koma kace jawahir tazo, ya dawo ance bata nan,

Inna ganin aiken yayi yawa yasa ta fito da kanta, ganin "yan sanda tsaye yasa gabanta faɗuwa, ta fara tambayar lafiya?"",,,,,, sukace suna neman jawahir ne, inna tace mi tayi ne?"",,,,,, suka kora ma inna bayani tare da cewa zasuyi bincike,

Inna tace bata nan taje kauye, wani yace wato tasan tayi laifi shi yasa ta gudu ko?"",,, suna nan suna magana baba yaxo don an faɗa mashi "yan sanda a ƙofar gidanshi shine dalilin da yasa ya taho,

tsanan tawa sukai sosai, baba yace aje a taho da jawahir ɗin inna tace babu wanda zai kama jawahir ya ɓata mata suna tunda batayi ba, jawahir bata kisan kai don haka suje can su nemo wanda ya kashe shi amma badai jawahir ba, abin dai tun anayi na hankali har ya koma bala,i bala,i ganin za,a tara masu jama"a, baba ya shiga motar suka nufi kauye dan ɗauko jawahir,...............

suna tafi inna ta duƙe a wurin ta fara kuka, tana cewa malam kada kaje dakai za,a tonawa ɗiyar "yar uwata asiri?"",,,,,, kuka inna take sosai , da sauri ta miƙe ta nufi cikin gida, da sauri ta shiga ɗakinta wayarta ta ɗauka ta fara kiran wayar sadiq, tanayi tana kuka............
[1/17, 7:44 PM] Jamila Musa Ws: ☄
☄☄
☄☄☄
🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥
*WANDA BAIJI BARI BA*
🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥

☄☄
☄☄☄

*AMEENCI WRITER"S ASSOCIATION* 📚✍🏻

*MEELAT MUSA* 🌹

*PAGE 22*

***
*S*ai kuka take yi, amma wayar sadiq bata tafiya haka ta haƙura ta daina kiran, fitowa tayi sanye da hijabi tayi ƙofar gda,

""",,,,,, tana fita ƙofar gdan su ja"afar ta nufa wato honey j, tana tsaye sai fama nocking take amma shiru, """"",,,,,,,,,,,,,,,

Haka ta gaji tayo gda, dan bata san inda zata nufa ba, tana dawowa gda wayarta ta ɗauka taci gaba da aikin neman sadiq"""""""",,,,,,

Bayan sun isa kauye ne, baba da kanshi ya shiga cikin gidan su jawahir, da sallama ya shiga,,,,,,,,,, larba ta fito cike da masifa tare da kunduma zaki tana tambayar uban waye?""",,,,,,,,,,,,

Ganin baba yasa tace wai dakai ne?"",,,,,,maraba, baba bai amsa ba, yace ina jawahir?""",,,,,,, larba tace jawahir ai na kashe ta,,,,,, idanuwa baba ya zaro tare da tambayar kinyi me?"""",,,,,,,,, tace kasan mutuwa?""",,,,, baba yace haƙiƙa amma har yanxun ban ɗanɗana ɗacinta ba tunda bata zo kaina ba,,,,,,,

Larba tace to haƙiƙa yaudai jawahir ta riga mu gidan gaskiya,,,,,,baba yace tana ina ne?"""",,,,,,,nuna mashi inda wata tsohuwar rijiya take tare da cewa tana cikin can,,,,,,,,,,,,,

Da sauri baba ya nufi wurin rijiyar yana kiran jawahirrrrrrrrrrrrrrrrrrrr wayyo Allahna, tare da sakin sautin kuka, innalillahi wa"inna ilahir raji"un, wannan ihun da baba yake shine yayi sanadiyyar jawo hankalin duk wani mutumin dake cikin gdan akayo kan baba dake ta ƙoƙarin faɗawa cikin rijiya,,,,,,,,,

mutane na haɗuwa aka fara tambayar ba"asi, cikin tashin hankali baba yace jawahir ta mutu,,,,, a cikin rijiyar nan,,,,,,,,,,, wani mutumin ne,,,,,,,, yace waye ya sakata ne?"""",,,,,

Larba daga gefe tace nice nan ta ƙarasa maganar tare da zaro idanuwanta,,,,,,,, mutumin yayi kanta tare da cewa waike miyasa baki da imani ne?"""",,,,,,,,,,,, ba an baki haƙuri ba?""",,,,,,,,,,,,,,

tace ai ni bana ɗaukar ƙaddara, kuma idan har ba"a biyani kuɗina ba, haka zan yanyana naman jikinta, in babbaka shi a wuta,,,,,,,,,,,,wata matace ta shigo cikin gdan da gudu tare da "yan sanda da suke bin bayanta,,,,,,,,,,,,

Suna cewa ina rijiyar take?""",,,,,,,, maza a samu mai shiga rami ya fito da ita, mutumin da yayi wa larba magana shine ya shiga cikin rijiya aka fito da jawahir,,,,,,,,,,,

ana fitowa da ita, baba ya rungume jawahir yana wani irin kuka mai tada hankali kamar zai mutu,,,,,,,,,,,,,,,ɗaya daga cikin "yan sandan ne yace malam muje, baba ya saki jawahir sannan ya miƙe tsaye cikin kuka yace haƙiƙa yau da sadiq yana nan dasai yaga bayanki,,,,,,,,,dasai ya kasheki kamar yanda kika kashe mashi "yar uwa,,,,,,,,,

Kallon ɗan sanda yayi sannan yace kamar yanda ta kasheta kuje da ita itama sai anga bayanta,,,,,,da gudu larba tayi wurin wata ƙatuwar tukunya data ɗaura saman wuta tana jirane dama ruwan su tafasa taje ta kwararawa jawahir,,,,,,,,,

tana zuwa ruwan ta ibo don ƙona "yan sanda, wani ɗan sanda ne, yayi kanta tare da halbata ta baya, ruwan suka ɓare saman jikinta,,,, wayyo wayyo wayyo na lalace, haka kawai larba take cewa,

ganin ta ƙonu ne yasa aka ɗauki jawahir suka bar gdan,,,,,,,,,,har yanxun baba kuka yake kamar ransa zai fita, ita kuwa larba tana can sai burgima take babu wanda yabi ta kanta,,,,,,,

Cikin "yan gidan nasu ne, wani yace larba kinga yanda ya ƙare maki,?,,,,,,,,haka zakiyi ta lalacewa, kowa na gidan haka suka wuce suka bar larba kwance cikin wahala, sai kuka takeyi,,,,

su baba na isa asibiti aka wuce da jawahir,,,,, bayan an kaita "yan sanda sukace lallai a duba masu a tabbatar masu da idan ta mutu?""",,,, dan macece mai hatsari,,,,,

bayan """yan gwaje gwaje likitoci suka tabbatar cewa tana da rai amma tana cikin mawuyacin hali, bayan an bawa jawahir gado ne, suka shedawa baba ya tafi gda, idan jawahir ta farfaɗo sun gama bincikensu zasu dawo da ita,,,,,

baba yace kai babu wani inda zanje,,,,,,,,,dan hauka zan tafi in barku da ɗiyata?""",,,,,don haka duk abinda zakuyi kuyishi a gabana,,, , haka akaci gaba da bawa jawahir agaji baba kuma yana gefe yana kallon ikon Allah,

Haka inna ta gaji da kiran wayar sadiq ta haƙura, kuma ga baba bai dawo ba, hankalinta gaba ɗaya ya tashi, ta rasa miye mafita?""""",,,,,,,,,,,,

Sai da daddare sosai sannan baba yazo gda ya faɗa mata halin da jawahir take ciki, don haka baba ya gaya mata asibitin da jawahir take taje wurinta ta kwana, to haka inna ta shirya ta tafi dan kiwon mace sai mace, inna ta tafi baba kuma ya zauna a gda,,,,,,,

***,,,,,,

*K*wanan jawahir biyu a asibiti ga "yan sanda suna gadinta, inna kuma tana kula da ita sosai,,,,,,, jawahir tana samun sauƙi tun ranar data farko "yan sanda sukayi kanta suka fara mata tambayoyi game da kisan Alhaji,

jawahir saidai ta bisu da ido amma bata iya magana, dan bama tasan inda maganar tasu ta dosa ba, haka sukayi ta ma jawahir magana amma bata iya cewa komai,

inna tana ta kula da jawahir sosai, amma bata san abinda yasa larba tayi wa jawahir haka ba, kuma tana so tasan dalili, ga "yan sanda dake faman tsaronta kamar wata kwamishina,

Haka dai jawahir taci gaba da jinyarta tare da danasin halinta, kuma tace ta bari amma miyasa baza a barta ta zauna lafiya ba?""",,,,,,,,, tana zaune tayi jugum sai hawaye yake zubo mata daga idonta,,,,,,, komi take tunani Oho?""",,,,,,,,,

Su kuma "yan sanda ganin jawahir ta samu sauƙi yasa suka tattara ta suka tafi da ita Office don gabatar da bincike, suna zuwa babu wani ɓata lokaci aka fara bincikar ta amma tayi shiru, taƙi tayi magana, ganin batayi magana ba, akace a sakata cell a rufe,,,,,,,, haka aka kamata ƙiƙi ƙiƙi akayi ciki da ita, amma jawahir batace komai ba,,,,,

Inna kuma tana komawa gda ta sanar da baba an tafi da jawahir baba yace to Allah ya sawaƙe ubangiji ya shiryar da ita, dan sudai basu da mafita, kuma basu da wasu manyan da zasu fito da ita, dama itace "yar neman asan da ita, kuma tana can an rufe,,,,,,,

larba kuwa tana ɗan jun sauƙi kuma ta ɗauki alƙawari idan ta warke sai taxo har binni ta kacaccala rayuwar ɗan sanda daya ƙonata,,,,,,,

***

satin jawahir biyu a magarƙama amma har yanxun taƙi tayi magana da kowa, ayi dukan anyi azabar amma kamar ba ita akeyi ma ba, duk wata wahala da ƙeta anyi ma jawahir amma baƙin ciki ya hanata tayi magana, saida idan ance kina da sa hannu a kisan alhaji zata girgiza kai alamar A, a, idan ance babu ke a ciki, zata ɗaga kai alamar E, tana dai fuskantar horo da tsanana amma saboda kangara taƙi tayi magana bare ma a gane nufin, don haka tattara sukayi suka ajiye, amma kullum da irin na"un azabar da take ɗauka,,,,,,,

***

*W*atan jawahir biyu a magarƙama ta rame tayi baƙiƙƙirin dole idan ka ganta sai ta baka tausayi, babbar matsala dasu innas suke fuskanta idan sunje ba"a barinsu suga jawahir hankalinsu ya tashi sosai, duk sun koma wasu kalar ban tausayi suma,

inna ce zaune a tsakar gida tayi zugum tunanin jawahir kawai takeyi, kuma tana mamakin babanta da har yanxun bai biyo yaji lafiya ba?"",,,,, tana cikin tunani taji maganar Sadiq, yana cewa lafiya inna?"",,,,,,

da sauri ta ɗago kanta tana kallon inda maganar take fitowa, tana ganin shi tace sai yau kaga damar dawowa?"",,,, kuma saboda tsabar wulaƙanci ka kama waya ka rufe?"",,,,, to lallai yayi maka kyau,

sadiq ya isa kusa da inna ya zauna sannan yace miye?"",,,,inna tace ka ɗauki jawahir kaje ka kaita kauye kuma kace kwana goma zakayi yau watan ka biyu , to gashi yanxun an kamata wata ɗaya da sati biyu tana can an garƙameta, hawaye suka zubo daga idon inna sannan tace kuma saboda wulaƙanci ubanta ko ya biyo yaji lafiya?"",,,,,tunda yasan da "yan sanda akaje ɗaukarta,

sadiq yace wai mi tayi ne?"",,,,,,inna tace kwashe komai ta faɗa masa, sannan yace to miyasa ita larba ta saka ta a rijiya ne?"",,,,,,inna tace ai jawahir taƙi tayi magana, tsaki yayi sannan yace kila wani abu nata ta ɗauka ta siyar tunda kinsan halinta dai, inna tace koma miye dai ai bai kamata haka ba, idan da ƙarar kwana ai sai ta mutu,,,,,

inna taci gaba da cewa nidai munje amma sai ace mana muyi haƙuri an kusa ƙare wa, sadiq yace yanxun tana ina ne?"",,,,, inna ta faɗa mashi, yace yana zuwa, miƙewa yayi ya fita daga gidan,,,,,,,,

yana fita waje mota ya shiga, gidan Alhaji kai tsaye ya nufa,,,,,,,bayan yaje yaro ya samu ya tura shi yace ace ana sallama da wani a gidan,,,

yaron bai daɗe ba ya dawo, babban ɗan alhaji ne biye a bayan yaron, suna fitowa yace ma yaron ina me nema na yake ne?"",,,,,,, yace gashi can, yace to, wurin sadiq ya nufa tare da sallama, bayan ya

16 / 28