Author : MEELAT MUSA Category : African Stories & Novels
kada ta fita, tsaki tayi sannan ta juyo, ko inda take sadiq bai sake kallo ba,
raɓata yayi ya fita daga gida suma mutanen da suke tare suka bi bayanshi,,,,,, suna fita wani mutum sadiq ya gani bayan sun gaisa ne, yake cewa don Allah jawahir fa, sadiq yace tana ciki, lafiya?"",,,,, yace ina san ganinta ne,,,, sadiq yace tayi maka wani abu ne?"",,,,
yace E dama takardun gidan nan ne na dawo mata dasu ta bani kuɗina, hannu sadiq yakai ya anshi takardun, zaro ido yayi ganin takardun gidansu ne da suke ciki, innalillahi wa"inna ilaihir raji"un, sannan sadiq yace nawa ne kuɗin?"",,,,,yace miliyan ɗaya ne, kanshi ya jinjina sannan yace lallai yarinyar nan, komawa yayi cikin gida yana shiga inda jawahir take tsayi yayi mata wata irin yayima,
ba jawahir ba har inna hankalinta ya tashi tana cewa lafiya?"",,,, yace ma inna lafiya qalau ina zuwa, jawahir jin damƙar da yayi mata yasa ta ci gaba da kukan da takeyi, kallonta yayi sannan yace rufe ma mutane baki , da sauri ta ɗauke numfashinta, sukayi zaure,,,,
A zaure sadiq ya tsaya sannan yace ma mutum shigo kada itace wannan?"",,,,, shigowa yayi cikin zauren ya kalli jawahir sannan yace itace ranka ya daɗe, sadiq yace yawwa, kallon jawahir yayi sannan yace bashi kuɗinshi, cikin kuka jawahir tace dan uwarka na baka dubu ɗariya ɗaya ai, yace E, tace to yau banda kuɗi kaje sai gobe ka dawo,
sadiq yace yanxun nan zaki bashi kuɗinshi, jawahir tace to ai kuɗin sai naje bank kuma ka hanani fita,,,,, yace to zan ranta maki ki saki gobe goben nan zaki bani abuna, idan kuwa ba haka ba, zanyi maki dukan kuɗina,,,, jawahir tace bashi zan baka,,,,,,, ansar takardar gidan yayi sannan ya saki jawahir, ta tafi tangal tangal,
shi kuma sadiq yace ma muyumin muje,,,,,,,,,,suna fita jawahir tayi cikin gda, inna tana tambayarta lafiya?"",,,,, jawahir tace ba komai, tayi cikin ɗaki,,,,,,,,
tana zuwa saman gado ta hau ta kwanta sannan taci gaba da kuka mara sauti, a zuciyarta take cewa haƙiƙa wannan halin saina barshi idan kuwa ba haka ba, ina cikin bala",i haka jawahir tayi ta kuka tare da tirr da wannan halin nata, yinin ranar dai cikin takaici tayishi,
***
*W*ashe gari jawahir bayan tayi wanka ta shirya, kayan islamiya ta saka, bayan ta fito tace ma inna , saina dawo idan na mun tashi islamiya zanje in cirowa sadiq kuɗi, inna tace kuɗin mi?"",,,,,,, jawahir tace shine ya aikeni, inna tace to sai kin dawo, tace to, kai tasa ta fice daga gidan,
Tana zuwa islamiyya, ana tashi gidansu hafsat ta wuce da uniform a jikinta, taje tayi mata Allah yasa alkairi, nan suka haɗu da sadiyya, aka sha fira sosai,,,,,,,,
hafsat tace ina yayankin nan mai sa ma mutum faɗuwar gaba?"",,,,dariya sukayi gaba ɗaya sannan suka kashe, jawahir tace ko jiya saidai mukayi faɗa ma, hafsat tace kam aini bana iya zama gida ɗaya dashi, dariya jawahir tayi sannan tace saboda mi?""",,,,hafsat tace kinsan sanda kika godun nan?"",,,,,ta bata dai labari hafsat tace wallahi daya zo kusa dani naji numfashina yana sama sama, gaba ɗaya suka sake sheƙewa da dariya,
jawahir tace ai jiya shine ya hanani zuwa, hafsat tace wai jawahir tace cewa idan na fita, zaibini wai ya takani da motar, hafsat tace ni wallahi tsoro yake bani, sadiya tace waye shi?"",,, hafsat tace bara in nuna maki hotonshi, jawahir tace Uhun sannu ke har wani hotansa kike iya ajiyewa?"",,,,,, sadiyya ta anshi wayar, adaidai lokacin data kalli wayar, ajiyar zuciya tayi sannan tace yana dai da kyau, kuma ɗan gaye ne, jawahir tace kinji wata magana?"",,,,ke harma wani yayi kyau,,,,,,,,kike cewa, haka dai sukaci gaba da gulmar sadiq,,,,,,,,,,
Jawahir kuwa sai tsine mashi takeyi wai ta tsanashi, sadiyya tayi murmushi sannan tace nidai ban tsaneshi ba, ina sanshi, jawahir tace lallai kina sanshi?"",,,,tace wallahi ina sanshi, jawahir tace ai da wannan jakkar da zai auro mana gara ki aureshi ke kina da kirki,,,,,,,, haka dai suka ƙare iya shegensu, daga baya jawahir ta tashi tafiya, hafsat ta shiga ta ɗauko mata kayan sa biki, sannan sukayi mata rakiya tahau abin hawa,,,,,,,
jawahir na tafiya hafsat tace ma sadiyya wallahi ki rufa ma kanki asiri, kinsan Allah idan kika ganshi sai kinji kamar zakiyi kuka, taci gaba da cewa baya dariya pha, sannan baki iya kallonshi, sadiyya tace nidai ina sanshi, hafsat tace to bara inji yana ina muje dake idan zaki iya faɗa mashi, sadiyya tace to ba damuwa, ganinsa kawai zanyi, hafsat tace yawwa, a daidai lokacin data kara wayarta a kunne, haka ta ƙari ringing harta tsinke bai ɗauka ba, bayan ta yankene ya biyo kiran,,,,,
Hafsat ta ɗauka bayan sun gaisa ne, tace yayanmu kana ta ina ne?"",,, zanzo in kawo maka kayan sa bikina, sadiq yace kinga bana kusa gaskiya, hafsat tace E aida mota muke kana ina?"",,,,, murmushi sasiq yayi sannan ya faɗa mata inda yake,,,,,,, hafsat tace to insha Allah muna zuwa yanxun yace no wahala,,,,,
tana kashe wayar tace ma sadiyya muje to, kayan sa bikin ta iba sosai sannan ta ɗauki makullin motarta suna shiga hafsat ta ibeta da ƙarfi sai wurin sadiq,,,,,
Jawahir kuwa bayan ta ciro kuɗin sadiq gida tayi kai tsaye,,,, zata shiga cikin gida ne, taga ja"afar yace yana cewa jawahir ɗan tsaya mana ina da magana dake,,, ko inda yake jawahir bata kalla ba ta shige gida,,,,,,, tana shigewa yace ji banza har wani aji gareki?"",,,tunkiya uwar tanɓale, wai nan har wata islamiyya ake zuwa, ga banza dai anyi ma jaki wanka,
tana shiga gida, tayi ma inna barka da gida, sannan ta wuce ɗaki, tana zuwa kayan ta cire sannan ta ɗauki kuɗin data ciro ta tusa su gaba tana kallo wata zuciyar na cewa kada ki bayar wata zuciyar tace kyaci dukan banza, kuma ki bada kuɗin da bala",i tattara kuɗin tayi ta ajiye sannan ta kwanta,,,,,,,
Su hafsat suna isa inda sadiq yace zasu sameshi, hafsat tayi mashi waya,,,, yace su zo wuri kaza da kaza yana nan ,,,, tare suka fita, daga hafsat har sadiya,, suna fita suka wuce inda yace masu yana nan,
bayan sunje ne, hafsat tayi mashi waya cewa sunxo wurin, yace to yana zuwa, suna nan zaune suna jiranshi, zuwa wani lokaci saiga sadiq ya fito, gaban sadiyya ne ya fara bada daram daram dammm,,,, da sauri ta kalli hafsat , bayan yaxo ya zauna hafsat ta gaishe shi amma sadiya kasa magana tayi, itama hafsat ɗin a ɗaɗɗare take maganar,,,, bayan sun gama gaisawa ne, hafsat ta bashi kayan sa bikin , yace to ajiye anan ngd sosai, Allah ya nuna mana lokaci, hafsat tace amin,
zama sukayi babu wanda ya sake magana, sadiq ne ya fiddo wayarshi taci gaba da latsawa,,,,,, ganin sadiya bata magana shima sadiq yayi shiru, yasa hafsat cewa yaya zamu tafi, ba tare daya kallesu ba, yace yawwa,,,,,miƙewa hafsat shi kuma hannunshi yasa a aljihu yayi masu ɗumtsiya,,,,, cikinsu aka rasa mai matsawa ya anshi kuɗin,,,, wani dake zaune kusa dashi ne, yace ya basu,,, godiya sukayi sannan suka fice daga wurin,,,,,,,
A cikin motar hafsat ce take tayiwa sadiya dariya, saidai tayi dariya ta daki sitiyarin mota,,,,,, sadiya tace kam lallai wannan zakine, kinji ina ganinshi yanda naji?"",,,,, dariya hafsat tayi sannan tace to kindai gani, sadiya tace lallai na jinjinawa jawahir, hafsat tace ai shi yasa yake dukanta kamar jaka,,,, kinsan jawahir taurin kaine da ita, kallom sadiya tayi sannan tace ga number, murmushi sadiyya tayi sannan tace tasha zamanta,,,,,
suna fita, sadiq yace ma wani ku ɗauka ku raba,,, shima wayarshi ya ɗauka da makulin motar yayo gda,,,,
A ƙofar gida ya haɗu da inna zata shiga maƙota barkar aihuwa,,, yace a dawo lafiya,,, tace yawwa shi kuma ya shige gida,,,, jin sallamarsa yasa jawahir miƙewa da sauri ta ɗauko kuɗin inda ta ajiyesu,,,,,,,,
ƙoƙarin fitowa takeyi a daidai lokacin daya shiga cikin ɗaki, kallonta yayi sannan yace tunda aka tashi islamiyya ina kika tsaya?"",,, jawahir cikin in,ina tace kuɗin na anso maka, zama yayi gefen gado sannan yace ina kika samo su?"",,,,,gaban jawahir ya faɗi, lokaci guda zufa ta fara zubo mata, yace dake nake magana,,, jawahir tace nawa ne,,,,
Sadiq tace bana hana ƙarya ba?"",,,cikin kuka tace wallahi nawa ne, ba wurin kowa na samo ba,,,,, sadiq yace naji amma ina kika tara su?"",,,jawahir tace tun lokacin ina kano ne,,, kanshi ya girgiza sannan yace da kyau,, shi yasa kike cewa ke mai arxiki ce?"",,shiru tayi, yace to ki ajiye man zan karɓa,,, tace to,,, ɗaukar kuɗin tayi ta mayar inda ta ɗauko su, kall ya bita dashi yana girgiza kai shi kaɗai yasan abinda yake tunani, tana ajiye kuɗin tayi harya fita,,, yace ina zakije?"",,, tace a tsakar gida zan zauna, yace dawo, batayi musuba ta koma , zata zauna saman kujera yace ta dawo nan, kusa dashi ya nuna mata taje ta zauna,
bayan ta zauna yace kawo man jikar islamiyarki,,, gaban jawahir ya faɗi,,,,,, kallonta yayi cikin wani irin yanayi wanda karatunta bai kawo nan ba,,,,,,,
Tashi tayi ta matsa kusa da jakar tana san ta cire wani abu a ciki, yace ke nake jira,,,,, da sauri ta ɗauki jikar tayo waje da gudu, da sauri ya tashi shima da gudu yabi bayanta,,,,,, tana ƙoƙarin tillar jakar a rijiya, ya jawo ta, ya wurgar da ita, gefe ɗaya, ya ɗauki jakar,,,,,, hannunta ya riƙe suka koma ɗaki,,,,,
ina tuni jawahir ta fara kuka, hankalinta ya tashi ta fara haɗa sadiq da Allah kada ya buɗa jakar nan ya rufa mata asiri,,, sadiq yace miye a cikin jakar ne?"",,,, jawahir tace ba tawa bace, yace ke ina taki ne?"",,,cikin kuka tace nidai kayi haƙuri don Allah, yace wai miye bakya so a gani ne?"",,,,,,,, jawahir kusa dashi ta matsa ta riƙe jakar gamm,,,,,,
Yace saki , jawahir tace don Allah ka saki , yace idan na sake maki magana zakiji a jikinki, jawahir tace ka rufa man asiri don Allah, yace to miye a cikin jakar ne?"",,, cikin kuka jawahir ta saki jakar, zazzageta yayi saman gado sannan ya fara ɗaga komai ɗaya bayan ɗaya,
ga jawahir ya riƙe da hannu ɗaya, hankalin sadiq ya tashi ganin abinda jawahir take boyewa, lokaci guda kuma idonshi ya kawo hawaye, sannan ya maida dubanshi ga jawahir da sauri ta durƙushe ƙasa, ta fara kuka dan tasan duk iya rantsuwar da zatayi ma sadiq baiza yadda ba,,,,,,,,, kuka take sosai tana cewa na rantse da Allah ba nawa bane, wallahi wata ƙawatace ta bani ajiya,,,
wani gigitaccen mari yakai mata sannan yace ita da bata raina iyayenta ba?"",,,,,, cikin kuka jawahir tace wallahi saida na tafi sannan tace man tayi ajiya a jakata, faɗa sukeyi,,,,,,, kallon littafin ya sakeyi wai ingaccen sirrin jima"i,,, kallom jawahir ya sakeyi sannan yace ni wallahi harna gaji da dukanki, idan an hanaki nan sai kiyi nan, idan an taro can sai kiyi can,,,,,,
Kallon ɗayan abun yayi sannan yace comdom, lallai jawahir da sauri ta duƙar da kanta ƙasa dan tunda take bata taɓa jin kunyar sadiq irin yau ba,,,,,,, cikin kuka tace na rantse maka da Allah ba nawa bane wallahi,,,,,,
sallamar inna sukaji, da sauri sadiq ya tattara jikar ya mayar ama sauran ya saka a aljihunshi,,,,,jin inna ta shigo yasa jawahir ta fara kuka sosai,,,,, daga tsakar gida inna tace miye kuma?"",,,, a daidai lokacin data ke zama saman tabarma,,,,,,,,
Cikin kuka jawahir tace innas waidaga yaga wani littafi ingantaccen sirr........sadiq ya daɗe mata baki, sannan yace ke baki da hankali ne?"",,,,,, inna tace mi?"",,,,sadiq yace inna barta,,,, inna tace kudai kuka sani,,,,,,,,,,,, kallon jawahir yayi sannan yace baki da hankali ne?"",,,,, ita kuma ƙoƙarin ɓamɓare hannun sadiq take daga bakin ta, amma ƙarfi ba ɗaya,,,,,,,,,
Hannunshi yasa cikin aljihu ya ciro wayarshi dake ta kuka,,,,,,, ƙara matse jawahir yayi sosai a jikin bango da hannu ɗaya ya ciro wayar , bayan ya ɗauka , ne yace wai miye?"",,,,,, bayan wani lokaci yace haba nace zanzo ,,,, bayan wani lokaci kuma yace jibi zan tafi wani abu?"",,,,,,,to ina wani abu zan kira,,,,,ya kadhe wayar,
sakin jawahir yayi sannan ya fita daga ɗakin, yana sakinta da sauri ta faɗa saman gado taci gaba da kuka,,,,dawowa yayi sannan yace da ban dakeki ba kike man kuka?"",,,, shiru tayi bata sake kukan ba, fita yayi yabar gidan inna tabi bayanshi da kallo, saida ya fita sannan ta shigo ɗakin, jawahir da sauri ta tashi tayi wurin inna tana cewa kice ya bani abun mutane,,,,
Inna tace to bari ya dawo, kiyi haƙuri, nace maki ki daina shiga harkar sadiq amma kinƙi, cikin kuka jawahir tace ai shine ya shiga harkata, inna dai haƙuri ta bawa jawahir dan bata san abinda ya haɗasu ba,,,,,,,,
***
*R*anar da sadiq zai tafi yace ma jawahir idan ta sake ta fita, idan ya dawo ko yaji labari zataci gidansu,,,,,, tace islamiyar fa?"",, sadiq tace na soketa, tace to soketa ɗin mu gani, yace gashi na faɗa maki, idan dai kinajin tashe rishin kunya ki fita, in dawo wani yace man ya ganki kinsan Allah ranar hmmm, jawahir tace idan ina san wani abu fa?"",,,, yace sai kiyi haƙuri,,,,,,, ina kuɗina ?"",,,,,, ɗauko kuɗin tayi ta kawo mashi,,,,,, duba kuɗin yayi sannan yace to ki ajiyesu,,,, jawahir tace to, ɗaukar kuɗin tayi inda ta ɗauko, sannan sadiq ya fiddo kuɗi masu yawa ya bata,,,,, jawahir tace ita dai bata so,,,, yace miyasa?:",,,,,,, tace haka nan,
wani kasallan murmushi yayi sannan yace to ki ajiye idan kin kashe shikenan idan baki kashe ba, na dawo sai ki bani,,,
Jawahir batayi magana ba, sadiq yace sai na dawo, batayi magana ba, ya fice daga ɗakin,,,inna ce take ta fama ma ɗanta addu,a, harya fita daga gidan,,,,,, yana fita jawahir tace wai mun rabu dakai alzango, rawa ta farayi sannan tace mun sarara kafin ka dawo,,,,,,,
***
*T*afiyar sadiq da wata ɗaya aka fara aiki gidansu inna, jawahir ta samu abinda take so, dan gidan gaba ɗaya aka rusa shi, gina na zamani da ƙayatarwa aka ɗauko masu, innas da baba da jawahir kuwa gidan da sadiq yake zama suka koma da rayuwarsu,,,,,
ganin an fara ƙanƙara masu gida ne yasa jawahir ta fara neman mutane suxo gidansu,, niko nace ina ruwan ba saban ba,,,,,,,,,,,,,
Duk kashedin da sadiq yayi wa jawahir bata fasa zuwa islamiyya ba, karatu ya miƙa jawahir an fara samun ilimi duk wata rawar kai yanxun ta rageta, ta samu natsuwa amma babban tashin hankalinta ita da aure take so, ganin duk abokanta sunayin aure yasa duk tabi ta tashi hankalinta,,,,,,,,,,,,
Jawahir ce ta fito daga ɗaki tana cewa innas saina dawo, inna tace ina zakije ne?"",,,,,,, jawahir tace zan sjiga maƙota wurin hassana, inna tace subahanallah yanxun kuma jawahir can kika koma?"",,,,,, jawshir tace haba keko innasco miye na tashin hankali haka don Allah?"",,,,, yanxun zan dawo, tana faɗin haka ta fice daga gidan,,,,,,,,..................
[1/17, 7:45 PM] Jamila Musa Ws: ☄
☄☄
☄☄☄
🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥
*WANDA BAIJI BARI BA*
🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥
☄
☄☄
☄☄☄
*AMEENCI WRITER"S ASSOCIATION* 📚✍🏻
*MEELAT MUSA* 🌹
*PAGE 25*
****
*T*ana shiga gidansu hassana, sallama tayi, bayan sun gaisa da maman hassana ne, tace hassana na nan?"",,,,,,daga ɗaki hassana tace wuto gani nan, jawahir aka tashi simi simi aka shige ɗaki,,,,
Tana shiga hassana tace kema don Allah sai yanxun zaki zo?"",,,,,, jawahir tace kiyi haƙuri, hassana tace yama sunan saurayin naki ne?"",,,,,,,jawahir tace ai su biyu ne, shidai ɗayan sunan sa Ahmad ɗayan kuwa bansan sunan sa ba,,,,,,, amma alƙali ne,,,,,, hassana tace to muje,,,,,,,,,,, miƙewa suyi su dukansu suka bar gidan,,,,,,,,,
Jawahir ta haɗu da hasana a islamiya take faɗa mata tana so tayi aure amma babu mijin aure, shine hassana tace zata kaita wurin wani malaminta,,,,, dan hassana batajin magana, kuma itace wanda ta saka wannan littafin cikin jakar jawahir,,,, kuma ta raina iyayenta , raini na haƙiƙa,,,,,,,,
Don haka cikin kuɗin da sadiq ya bata a cikinsu ne ta ɗauka, suka tafi wurin biye biyensu,,,,,,, sun daɗe suna tafiya a abin hawa sannan suka isa wurin,,,,,,,,
Bayan sunje ne, hassana ta gabatar da jawahir a matsayin baƙuwa, sannan ta ɗora da cewa itace wanda nace maka zan kawo maka,,, kallonta malamin yayi sannan ya kalli hassana yace kin faɗa mata ƙa"idojinmu?"",,,,, hassana tace A, a, amma yanxun saika faɗa mata,,,,,,,,,
Kallon jawahir yayi sannan yace ƙa"ida ta farko itace, shine saina kwanta dake,,,,,,, cikin rashin fahimtar abinda yake cewa jawahir tace ya kwanciya kuma"?"",,,,, yace zan kwanta dake kamar yanda ma"aurata suke yi, jawahir tace kai malam babu wata hanya mafi sauƙi?"",, nidai wannan taƴi man girma,,,,,,,,,,,,
Kallon jawahir yayi sannan yace A, a, wannan itace mafita, jawahir tace nidai zan bayar da kuɗi ko nawa kke so gaskiya amma banzanyi iskanci ba,,,, malamin yace ba aure kike so ba,,,,, kallon hasana yayi sannan yace ku tashi kubani wuri,,,,,,,,
Hassana tace malam tsaya, jawahir ki yadda, dukafa 10minutes yayi yawa, jawahir tace gaskiya nidai A,a, malamin ya dakawa jawahir tsawa, wanda tasa taji kanta na juyawa,,,, cikin murya mai bada tsoro yace to tunda kika kawo mana raini da taurin kai dukansu babu ke babu aurensu, bazasu sake nemanki ba har abadan duniya,
hassana tace malam kayi haƙuri kallon hassana yayi yana zaro idanuwa sannan yace ƙarya take ni za,a kawo ma raini ne?"",,,,ku tashi ku bani wuri,, haka jawahir ta miƙe jiki a sanyaye ta fita daga ɗakin malam hassana ma bayanta tabi, suka fito, suna fitowa suka hau abin hawa, hassana sai bala"i takeyi wa jawahir,,,,,, amma jawahir ta kasa magana sai kuka take,,,,kafin su iso gida tuni masassara ta lulluɓeta, sai kuƙa takeyi,,,,,
Suna tsayawa, a ƙofar gida jawahir ta sulale tayi cikin gda, tana zuwa ko sallama batayi ba, ta shige ɗaki babu abinda take tunani sai tashi ki bawa mutane wuri dukansu babu mai sake nemanki babu mai aurenki a cikinsu,,, wasu hawaye suka zubo mata,,,,,,, lallai takai kanta,,,, shigowa inna tasa tayi sauri ta goge hawayenta,,,,,,,
Inna tana shigowa tace jawahir ansa sadiq ne,,,,,,,, tana miƙa mata waya,,,,, cikin sanyi jawahir ta ansa sannan ta kara a kunnenta,,,,, tace hello, sadiq yace ina kikaje yau?"",,,,,jawahir tace unguwa yace wace unguwa kika je?"",,,,,, an kirani an faɗa man inda aka ganki,,,,, waike dai bakijin magana dai ko?"",,,, jawahir tayi shiru, sadiq yace na rantse da Allah idan baki daina fita ba wallahi jikinki zai baki labari na faɗa maki,,,,,,
tsaki jawahir tayi sannan tace to aisai ka dakeni, yace to shikenan idan na dawo ki faɗaman haka, jawahir tacebda Allah malam kada ka cika