Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

WANDA BAIJI BARI BA Rayuwar Ƙarya da Nadama by MEELAT MUSA

Author :  MEELAT MUSA Category :  African Stories & Novels

Chapter   22 / 28

63K to 66K   out of 83K words

gama jawahir tana riƙe a jikinshi wai kada ta tashi tayi mashi wani abu,.

Yunwa ta tasheshi daga bacci, a gajiye ya buɗe idonshi sannan ya kalli jawahir dake bacci,

ajiyar zuciya yayi sannan ya fara tashin ta, buɗe idanuwanta tayi tana kallon sadiq, yace tashi mu tafi , jawahir tace ina?""

Sadiq yace yunwa nakeji, ki tashi muje gda muci abinci, jin an anbaci gda yasa jawahir saukowa daga saman gado da sauri,

shine ya fara sauka daga saman gadon ya nufi toilet, bakinshi ya wanke da fuskarshi sannan ya fito,

Itama shiga tayi ta wanke fuskarta da bakinta ta fito, lokacin data fito sadiq ya goge fuskarshi da towel, yana ƙara shafa turare,

ita kuma tana zuwa hijabinta ta ɗauka tayi gaba, saidai ya gama abinda yake, sannan ya fito,

Yana fitowa yace muje, shine yayi gaba yana wata irin tafiya mai ɗaukar hankali, jawahir tabi bayanshi da kallo, tana binshi itama tana tafiya,

suna zuwa, wurin motar ya buɗe ya shiga, saida ya kunne motar sannan ya koma gefe kamar yanda ya saba, jawahir ta shiga taja motar suka bar gidan,

suna tafiya sadiq ne yake waya cewa zanzo jawahir zan ajiye gda, ina zuwa yanxun insha Allah,

Sannan ya kashe wayarshi, haka taci gaba da tafiya, sadiq yana gefe, har suka iso cikin unguwa,,,,

Sadiq yace a ƙofar gida zaki sauka, zanje wani wuri in dawo, batayi magana ba, har ta iso ƙofar gida, tana zuwa tayi parking ta fita,,,,,,,

Tana fita sadiq ya koma mazaunin data sauka , yaja motar yabar ƙofar gidan,,,,,

yana tafiya itama ba gida ta shiga ba, da sauri tabi motar har ta isa bakin titi, ta samu abin hawa
[1/17, 7:45 PM] Jamila Musa Ws: ☄
☄☄
☄☄☄
*WANDA BAIJI BARI BA*

*AMEENCI WRITER"S ASSOCIATION* 📚✍🏻

*MEELAT MUSA*

*PAGE 30*

***

*S*hiko sadiq da gudun bala,i yake tafiya da mota, itama jawahir cewa take mai napep ya ƙara wuta,,

Gudu yake na fitar hankali, dan sadiq yayi masu nisa sosai, shi kuma sadiq baisan jawahir tana binshi ba kwata kwata,

Saida sukayi tafiya sosai, sannan sadiq yayi parking a bakin titi, daga nesa jawahir tace tsaya nan, mai napep ya tsaya,,,

Tana kallon sadiq wata mace ce, tazo ta buɗe motarshi ta shiga, tana shiga yaja sukayi gaba,,,,,

Jawahir ta dunkula wani babbakeken zagi sannan tace bi man munafiki da sauri, mai napep ya ƙara wuta sosai kamar salansar napep ɗin zata fita,

Haka sukayi ta wuta sosai bisa titi, tafiya akayi sosai, sannan sadiq yayi parking da motarshi bakin wata ƙatuwar super market,

Jawahir dake cikin napep ganin sadiq ya fita ko kallon mai napep batayi ba, ta fice daga cikin napep ɗin ta nufi inda motar take,

Tana zuwa ta buɗe motar, khadija ganin jawahir gabanta ya faɗi, cikin masifa jawahir ta fizgo khadija daga gaban motar ita kuma ta shiga ta zauna,,,,,,,

Shi kuma mai napep matsowa yayi yana cewa hajiya kuɗin, cikin faɗa jawahir tace nawa ne?"" zaka dameni ne?"""

Mai napep yace 1k tsaki jawahir tayi sannan tace bari mai motar nan yaxo,

Sadiq yana fitowa, da sauri ya ƙaraso wurin , zai shiga mota yaga khadija tsaye tana kuka,,,,,

Kallonta yayi sannan ya zagaya wurin da take tsaye yana tambayar lafiya?""

Nuna mashi jawahir dake gaban motar tayi ta wani kashe, sai shaƙar iska takeyi, tana iskanci,

Buɗe gaban motar yayi ya fizgo ta, sannan yace khadija shiga, tazo zata shiga jawahir tace wallahi idan kika shiga sai naci uwarki, sadiq ya kalli jawahir yama rasa abinda zaice,,,,

Fizge hannunta tayi daga hannun sadiq sannan tace bani kuɗi inba mai napep, sadiq yace bazan bada ba,

Jawahir ta kalli mai napep sannan tace malam ya baka kuɗinka,,,,

Mai napep ya kalli sadiq amma ya kasa magana, ya ɗauke idonshi daga wurin sadiq, jawahir matsawa tayi kusa da sadiq,

Wani irin wulaƙantaccen kallo yayi mata wanda ya hanata tashi mashi magana,,,,,,,

Kallon mai napep ɗin tayi sannan tace don Allah kayi haƙuri ka tafi, mai napep baiyi magana ba ya juya zaiyi tafiyarshi sadiq ya kirashi,,,,

Bayan ya dawo ne, ya sadiq ya koma mota, kuɗi masu yawa ya ɗauko ya bashi, zubewa yayi yana godiya, sosai amma sadiq bai sake bi takanshi ba,,,,,,

Ya nufi motar ya shige, ita kuma khadija ta buɗe mota ta shiga, jawahir da gudu taje ta buɗe motar sannan ta fizgo khadija da ƙarfi,

Sadiq yace wai jawahir miye haka?"",,,, cikin tsiwa da nuna komi zai faru saidai ya faru , jawahir tace yau sai an faɗa man wanda akafi so tsakanin ni da ita?"",,,,,

Idanuwa sadiq ya buɗe sosai yana kallon jawahir,,,, itama idanuwanta ta buɗe sosai kamar yanda sadiq yayi tana kallonshi,,,,

Sadiq yace wai miyasa kike man wannan abun ne?"" jawahir tace wallahi sai an faɗa man idan ita kake so zanyi haƙuri inyi tafiyata wallahi,

idan kuma ni akeso a faɗa man inji, khadija dai tayi tsaye tana kallon ikon Allah,

Sadiq kallon khadija yayi sannan yace shiga muje, har zata shiga jawahir ta sake fizgo sannan tace idan kika ga kin shiga motarnan saidai idan kece yake so,,,,,

Zagayowa sadiq yayi sannan yace jawahir sakarta, jawahir tace bazan saketa ba wallahi, sai idan kace itace kake so,

sadiq yace ku dukanku ina sanku, jawahir tace sai ka faɗi wanda kafi so, sadiq yace wannan wane irin fitina ne jawahir?""

Jawahir tace fitina?"" ai yau babu kai babu ɗaukar wannan ƙoɗaɗɗiyar a motar nan, idan har kana san ganin ƙarshe fitina ɗaukarta in gani,

Sadiq matsawa yayi kusa da khadija yayi magana, jawahir tace ga banza anma jaki wanka, baidai damar ace ana santa gaba, dan bata kai ba,,,,,,

Khadija zuwa tayi ta ɓuɗe gaban mota ta shiga, jawahir ta ƙara fizgota, tana fizgota sadiq ya riƙe jawahir sannan ya mammareta sosai, yaje ya shiga mota yaja suka bar jawahir a wurin,,,,,,,,

Suna tafiya jawahir ta goge hawayen dake zubo mata daga idonta, wayarta ta fara kiran number sadiyya, ba ɓata lokaci sadiyya ta ɗauka, suka gaisa, bayan sun gaisa ne, jawahir tace don Allah ina wuri kaza kixo ko ɗaukeni,

sadiyya tace to gani nan zuwa,,,, sannan ta kashe wayarta,

shi kuma sadiq yana zuwa ya ajiye khadija gda, ya dawo dan ɗaukar jawahir,,,,,,,,

amma ina kafin yazo tuni saddy tazo ta ɗauketa sunyi gdansu,,,,,,,

Sadiq yana zuwa ya tambayi wani ko yaga wata mai kama kaza da kaza?""",,,,, yace Eh yanxun wani mai mota ya ɗauketa, sadiq yace mai mota kuma?"""

yace Eh, sadiq yace wace hanya suka bi?"""" ya nuna mashi, sannan sadiq ya tambayi kalar motar, ya faɗa mashi number motar, yace bai sani ba,

sadiq ɓarke yaja motar yabi hanyar, gudu yake kamar zai tashi sama, amma san baiga mota mai ɓishi ɓishin motar ba,,,,,,,,,,,

wayarshi ya ciro, ya fara kiran wayar jawahir, amma jawahir bata ɗauka ba, text ya tura mata,

```jawahir kiyi haƙuri ki ɗauki waya zanyi magana dake idan annabi ya isa dake```

bayan ya tura text ɗin , ta gani shi kuma ya sake kiran wayar,,,,,,,,,,,,,,,
[1/17, 7:45 PM] Jamila Musa Ws: ☄
☄☄
☄☄☄
*WANDA BAIJI BARI BA*

*AMEENCI WRITER"S ASSOCIATION* 📚✍🏻

*MEELAT MUSA*

*PAGE 31*

***

*S*adiyya tace jawahir ki ɗauki wayar mana don Allah ,

Jawahir ta goge hawayen idonta sannan ta ɗauki wayar, tana ɗauka sadiq yace kina ina ne?"""

Jawahir tace ina gida, sadiq yace wane gidan?"" jawahir tace gdanka,

Sadiq yace tsakaninki da Allah kina ina?"" cikin kuka jawahir tace kace idan Annabi ya isa dani na ɗauki waya, to na ɗauka,

Maganar in faɗa maka inda nake duk bata taso ba, tana faɗin haka ta kashe wayarta,,,,

Sadiyya tace haba jawahir miye haka?" sadiq tsaki yayi sannan yace wannan yarinya bata san ba,a kashe man waya ba?""

Tsaki yayi sannan ya sake kiran wayar, wannan karon sadiyya ta ɗauka, dan jawahir ta shiga toilet,

Tana ɗauka sadiq yace ina mai wayarne?"" sadiyya tace tana toilet, sadiq yace kuna ina ne?""

Sadiyya tace tana gdanmu, ina ne gdan naku?"" ta faɗa mashi, sadiq yace gani nan zuwa,

Yana kashe wayar gdansu sadiyya ya taho, bayan ya iso ne ya kira wayar jawahir,

Jawahir zata ɗauki wayar sadiyya tayi sauri ta ɗauka, tare da cewa kazo ne?"" sadiq yace E amma ban shigo ciki ba,

Sadiyya tace ina zuwa, tana kashe wayar tace wa jawahir zo muje,

Jawahir tace saboda nazo gdanku zaki man wulaƙanci ?" sadiyya tace kash ba haka bane kiyi haƙuri kixo muje,,,,

Jawahir tace to gaskiya bazanje ba, sadiyya ta zauna tace jawahir kuyi haƙuri, kixo muje kinga hankali gdanku zai tashi,

Wani irin kallo jawahir tayi wa sadiyya, a daidai lokacin da kiran sadiq ya sake shigowa, sadiyya ta ɗauki wayar tare da ceqa gamu nan zuwa yaya,,,,,

Sannan ta kashe wayar, sadiyya zuwa tayi ta kira momynsu, momy tazo tayi wa jawahir nasiha, ta bata haƙuri,

Dan su basu san jawahir tayi aure ba, bayan an gama nasiha wa jawahir suka miƙe suka fita, dan tafiya inda sadiq yake jiransu,,,,,,

Tunda suka fita sadiyya take ƙara bawa jawahir haƙuri, duk da bata san abinda takeyi wa kuka ba,

Har suka iso wurin da sadiq yayi parking, shi kuma sadiq yana hango jawahir ya buɗe gaban motar ya fito,

Sadiyya ta gaishe shi, ya amsa ba yabo ba fallasa, inda jawahir take tsaye, ya nufi wurin, sadiyya tasa dukanta zaiyi, da sauri ta juya tana cewa sai anjiman ku,

Sadiq yace yawwa, amma jawahir batayi magana ba, sadiq yana matsawo kusa da jawahir, yace waike miye yake damun kwalwarki?

Jawahir batayi magana ba, da kanshi yaja hannunta, yaje ya buɗe gaban mota ya sakata, sannan ya zagaya ya shiga yaja suka bar wurin,

Tafiya suke sosai, idan yayi magana wa jawahir bata mashi magana, dariya yayi sannan ya fara wasa da motar saman titi, amma jawahir ko inda yake bata kalla ba,

haka yayi ta tuƙin ganganci, har suka iso gda, suna shiga jawahir da gudu ta fita tayi cikin gda,,,,,,

saida yayi parking sannan ya fita shima yayi ciki, yana zuwa farlo ya sami jawahir tsaye, ance inna bata nan,,,,,,,

sadiq zama yayi sannan yace ma mai aikin inna ta kawo masu wani suci,

ita kuma jawahir ganin akwatina sunfi hamsin masu ɗan bura,uban kyau da tsada, sai ƙara kallonsu takeyi sosai,

Bayan an kawo masu abinda zasuci sadiq yace ma jawahir tazo taci yana sauri, zuwa tayi ta zauna tare sukaci, suna gamawa ya miƙe yace wa jawahir suje,,,,,,,,

Haka ta tashi tabi bayanshi, amma a ranta tana san tasan akwatinan nan na waye?"""

ba dama ta tambayi sadiq, yanxun ma shine yaja motar, suka tafi gda,

har suka isa gdan babu wanda yayi magana har suka isa,,,,,,,,,

***

*B*ayan satittika da faruwar hakan, jawahir tana kwance tana bacci, wayarta dake ta ringing, ta shi ta jawota cikin yanayin bacci ta ɗauka,

Hafsat tace jawahir baki da mutunci wallahi, cikin maganar bacci jawahir tace mi nayi maki hassu?"" hafsat tace ashe yayanki yayi aure baki faɗa man ba?"""

jawahie tace yaushe yayi auren ne?""" hafsat tace bansan iskanci, kusa shagalin biki a raƙashe amma sai a manta damu?""" ai na ɗauka mun zama ɗaya,,,,,,

jawahir tace nifa ban gane ba, hafsat tace to ke kina ina akayi bikin ne?""" jawahir ta faɗawa hafsat, unguwar da take,,,, hafsat tace to wallahi yaya yayi aure, kuma anyo biki na faɗa a idon duniya,,,,,,,,

Jawahir ta tashi zaune da sauri, sannan tace hafsa kina ina ne yanxun?"" hafsat tace ina gdana, jawahir tace gani nan zuwa,,,,,,, hafsat tace sai kinxo,

a gaggauce jawahir tayi wanka, ta shirya, ta ɗauki makullin motar sadiq da gudu ta fito ta nufi inda ake ajiye motoci,,

Mai gadi yace hajiya "yar laɓao yace kada a barki ki fita, kallonshi jawahir tayi sannan tace naci uwarku dakai da "yar laɓai ɗin,,,,,

Mai gadi yayi shiru jawahir taci gaba da zungurawa uwar mai gadi zagi, yayi muƙuyi, jawahir tace zaka buɗe man hanya ko saina ci uwarka?""

yace hajiya bafa inda zakije,,,,,, jawahir tace bakai ba ko wanda ya ajiyeka bai isa ya hana in fita ba, ganin jawahir ta rikice sosai, yasa ya fiddo wayarshi dan kiran sadiq,,,,,,

jawahir ta shiga mota, ta tada tayi kan mai gdi da ita haiƙan,,,, ganin jawahir zata kasheshi yasa ya ruga da guda sosai,,,,,,,

tsaki jawahir tayi sannan ta fita ta buɗe get ɗin, ta dawo ta shiga motar tabar gidan,,,,,,,,

a hanya jawahir tace lallai sadiq yakai babban ɗan iska, ni zai wulaƙanta ?"" ashe yayi aure shi yasa ya daina kwana a gda?"" tuƙi jawahir take amma kuka takeyi sosai,

tana isa gida hafsat, ciki ta shige da motar har bakin farlon hafsat, sannan ta fita, da sauri ta shige ciki, tana sallama,,,

hafsat dake kicin da sauri ta fito tana oyo yoo ƙawata,,,,, jawahir da gudu taje ta faɗa jikin hafsat ta fashe da wani irin kuka, mai taɓa zuciya...........

Cikin damuwa hafsat tace miye ya saka kike kuka ƙawata?"" jawahir tace dole inyi kuka, duk ni na jawowa kaina,

hafsat da tun farko na zama mai natsuwa haƙiƙa da na auri duk irin namiji dana ke so a duniya, amma saina taso cikin wata irin rayuwa, na ɗauki rayuwar ƙarya na ɗaurawa kaina,,,,,

Na saka kaina cikin rikicin duniya,,, na hana zuciyta zaman lafiya, duk namijin daya zo wurina aka faɗa mashi halina baya sake dawowa,,,,, ta sake farkewa da kuka sosai,

tace hafsat sai yanxun nake dana sanin halina, yanxun nake burin in gyara amma lokaci ya ƙure man,,,,,,,,,

hafsat tace wai miye?
[1/17, 7:45 PM] Jamila Musa Ws: ☄
☄☄
☄☄☄
*WANDA BAIJI BARI BA*

*AMEENCI WRITER"S ASSOCIATION* 📚✍🏻

*MEELAT MUSA*

*PAGE 32*

***

*C*ikin kuka jawahir tace hafsat azzalimi fa ba yayana bane!"""""

Idanuwa Hafsat ta zaro tare da kallon jawahir sosai,,,,,,, jawahir tace mijina ne?""" idanuwa hafsat ta sake zarowa tare da jan jawahir suka zauna saman kujera,

Hafsat tace mijinki kuma?"" yaushe kukayi auren?"" murmushin takaici jawahir tayi sannan ta bawa hafsat labari amma ba duka ba, ta ɓoye wani abun,,,,,,

Hafsat tace lallai jawahir, kuma shine duk baki faɗa ba?"" jawahir tace kiyi haƙuri,

Hafsat bazan ɓoye maki komai ba, tun kafin ayi man aure da azzalimi nake sanshi,

Amma nasan yanda ya tsaneni baya ƙauna na, kuma da akayi mana aure dashi nayi tunanin zai so ni, ashe baya so na,,,,,

Hafsat tace kiyi haƙuri jawahir yaya yana sanki, cikin kuka jawahir tace ba komai kada ya soni ma,,,,, amma dole zanyi haƙuri in zauna, dan idan na bar gdan sadiq,,,,

Kinga ai ban isa in koma masu gda ba, sannan kuma banma san ina zanje ba,,,,,, cikin tausaywa hafsat tace kiyi haƙuri komai yayi farko zaiyi ƙarshe,,

Jawahir tace haka ne,,, wace unguwa yake zama da matarshi ne?"" hafsat ta faɗa mata tare da gaya mata irin ƙanƙareren gdan da sadiq ya gina ana maganar gdan a gari,

Ta ƙara da cewa kuma ya kashe kuɗi kamar baisan zafinsu ba,,,,,,, hafsat tace kuma gobe zai tafi da amaryarshi london,

Jawahir tace to ba komai Allah ya kaimu lafiya, hafsat tace amin, tashi hafsat tayi taje ɗaki ta ɗauko ma jawahir kalandar biki,,,,,,,

Cikin takaici jawahir ta kalli calander ta sake kallo,,,,, daga sadiq har khadija suna cikin farin ciki, hoton sunyi kyau sosai,,,,,,,,

Murmushi jawahir tayi cikin yanayin damuwa, sannan ta miƙawa hafsat tace na gani, Allah ya basu zaman lafiya, daga haka bata sake cewa komai ba, ta miƙe ta fita daga farlon,

Tana fitowa ta shiga motar ta ƙarawa bujenta iska,,,,,,, hafsat jawahir tana fita saida taji tausayinta dan tasan yanda so yake bare kaso wanda baya sanka,,,,,,

Shi kuma mai gadi yana faɗawa sadiq jawahir ta fita,,,, ya ɗauko khadija suka taho gdan tare,

Ita kuma jawahir wuta takeyi sosai saman titi, tana tafiya tana goge hawayen idonta da tissue, idan ka ganta zakaji tausayinta,,,,

Sai yanxun jawahir takeyin dana sani, tace haƙiƙa an ɗora hanyar kirki amma duk na boɗare, dama duk wanda baiji bari ba, haƙiƙa bazaiƙi jin hoho ba,,,,,

Dana kasance mai halin kirki lallai da rayuwa bata kaini haka ba, sake goge hawayen tayi sannan tace lallai wuri ya ƙure man,,,,,,,, amma haƙuri zanyi dan banda inda zanje,,,,,,

zan jure duk wulaƙancin da sadiq zaiyi man, kafin in samu mafita,,,,,, haka taci gaba da balbala gudu harta iso gida,,,,,,,

tana isowa, tayi horn, a bakin get, mai gadi yaje ya buɗe mata ta shigo,

tana shigowa bayan tayi parking, ta fita,,,,, rufe motar tayi sannan ta nufi ciki,

A bakin ƙofar parlo taji ƙamshin turaren sadiq dan haka dole ta koma baya ta saita kanta sannan ta shiga da sallama,,,,,,,,

Gabanta ne yayi wata mummunar faɗuwa ganin abinda sadiq yake yiwa khadija, amma saita basar tace sannunku da hutawa,,,,,,,,,,

khadija dake kwance saman jikin sadiq tace yawwa ƙanwarmu barka da dawowa, wani marigayin murmushi jawahir tayi ba tare da ta sake cewa komai ba, tayi ciki,

Sadiq yace jawahir zo nan, dawowa tayi tana kallonshi amma batayi magana ba,,,,, sadiq yace daga ina kike?"""" har yanxun yana rungume da khadija jikinshi,

wani wulaƙantaccen kallo jawahir tayi mashi sannan tace ka aikeni ne?""" taɓe baki yayi tare da girgiza kanshi alamar A,a, murmushi jawahir tayi da gefen bakinta sannan ta juya ta shige ciki,

zuciyarta tana mata wani irin bala,in zugi, tana tsalle kamar zata faɗo ƙasa,,,, tana shiga ta cire hijabinta, sannan ta shige toilet,,,,,,,

tana shiga ruwan ta kunna, suna fara zubowa, ta fashe da wani irin kuka mai tada hankali, saida tasha kukanta sosai harta gaji sannan ta watsa ruwa ta fito,,,,,,,,

tana fitowa taga sadiq kwance a gefen gado,, ba tare data kalli inda yake ba, ta matsa bakin madubi tayi tsaye, tana kallon kanta,,,,,,,

Tashi sadiq yayi ya matsa kusa da inda jawahir take tsaye, juyowa yayi da ita ta fuskance shi, sannan yasa hannunshi ya riƙo ƙugunta,,,,,,,

da ɗayan hannunshi ya ɗago mata fuska, tana kallonshi, ɗago kanta yayi sannan yakai fuskarshi daidai tata,,,,,,,

Yace kukan mi kike?""" cikin mutuwar jiki jawahir ta girgiza kanta, alamar ba komai, sadiq cikin damuwa yace ai najiki a toilet, jawahir da idon ta ya sake cikowa da hawaye, tace sabulu ya shiga man ido,,,,

Ɗaukarta yayi tsagwayam yayi saman gado da ita,,, saida ya hau tsakiyar gadon sosai sannan ya kwantar da ita,,,,,,,,,

Durƙusawa yayi saman gadon sannan ga sake jawo jawahir yasata tsakiyarshi, ya raba ƙafafunshi yanda yayi mata abun yasa taji kunya ta rufe idonta,,,,,

shi kuma hannunshi yasa ya cire towel ɗin jikinta,,,, da sauri ta rufe gabanta da hannunta, murmushi yayi sannan ya haɗa hannuwan nata ya riƙe so da hannu ɗaya,,,

Yana kallon ƙirjinta,,, kiciniya ta fara yi dan kwace hannunta amma ta kasa,,,,, shi kuma kwanciya yaɗanyi saman jikinta kaɗan rabin jikinshi a saman gado,,,,,

sannan yace kukanmi kike yi?""" jawahir tayi shiru, sadiq yace wurin wa kika je?""" a daidai lokacin daya kai hannunshi yana taɓa gashin kanta,,, wai ko zaiji lema,,,,,,

jawahir tace ba wurin wanda naje, abinda kke zargi ni bashi ne damuwata, kaine ya dama wanda har baka iya haƙuri ko ina kaje saika nuna maita,,,,,,

wani

22 / 28