Author : MEELAT MUSA Category : African Stories & Novels
firgitarwa,,, jafar kuka ya fara yana bawa sadiq haƙuri sannan ya faɗa mashi yanda sukai da jawahir,,,,,,
tsaki sadiq yayi sannan yace daga yau sai yau idan na sake ganin ko kallonta kayi saina tsiyaye maka idanuwa babu tausayi na faɗa maka,,,,, cikin gamsuwa jafar yace to,
sadiq yace fito man da jakarta, jiki na ƙarma ya tashi ya fiddo jaka da wayar jawahir ya buɗe motar sadiq ya saka ya rufe,,,, sadiq kuma shiga mota yayi yayo gdansu inna,,,
baba yace ki wuce ki tafi,,, jawahir tace , tou fita tayi daga ɗakin cikin kuka ta nufi hanyar ƙofar gda,,, dan tasan yau babu abinda zai hana sadiq yayi mata lullusar fitar hayyaci,,,,
tana fitowa daga gida tana tafiya tana kuka,,,,,, shi kuma tun daga nesa ya hangota,,,,, dan haka da gudu yayo kanta da mota, da sauri ta raɓe gefe guda,,, bata daɗe da matsawa ba, sadiq yahau wurin da mota,,,,,,
cikin kuka jawahir tayi ajiyar zuciya, tare da gode ma Allah lallai da bata matsa ba, da sadiq zai iya kasheta kenan,,,,,,,
yana tsayawa yace idan kinga dama ki shigo, cikin kuka jawahir ta nufi motar tana kuka, tana shiga ta fara bawa sadiq haƙuri,,,, amma ko inda take bai kalla ba,,,,,,, taci gaba da kuka tana magiya,,,,,,
wani irin birki sadiq ya taka ƙuuuuuuuu,,,, wanda har kan jawahir saida ya daki gaban motar, sannan yace idan kika sake man kuka saina ɓare maki baki biyu, ya ƙarasa maganar yana fiddo duka idanuwanshi,,,,
Jawahir ta ɗauke nunfashi bata sake ko tari mai ƙarfi ba,,,,, amma hawaye sai zubowa suke daga idonta,,,,,
[1/17, 7:46 PM] Jamila Musa Ws: ☄
☄☄
☄☄☄
*WANDA BAIJI BARI BA*
*AMEENCI WRITER"S ASSOCIATION* 📚✍🏻
*MEELAT MUSA*
*PAGE 43*
***
*T*afiya sadiq yake sosai da mota har suka isa gda,,,, a bakin get ya sauke jawahir tare da cewa kada kiyi bacci zan dawo yanxun,,,,, cikin kuka tace touuuu,,,,
Daga haka bai sake magana ba yaja motar yabar gidan,,,
Da gudu jawahir ta shige ciki tana kuka, dan tasan idan har sadiq ya dawo saiya zaneta,,,,,,, kuka takeyi sosai har ta shiga bata tsagaita ba,,,, niko nace sadiq batake yake ba, abubuwanne sunma kanshi yawa yau,,,,,,,
Yana zuwa gdan khadija a farlo ya zauna, har yanxun bata dawo ba,,,,, yana nan zaune yana waya,,,,,
Sadiq yafi awa biyu yana zaman jiran dawowar khadija,,,, baƙin ciki kawai yake addabar mashi zuciyarshi,,,
Wayarshi dake ƙara ya duba dan ganin mai kiranshi, jawahir ce,,,, tsaki yayi sannan ya ɗauka yace ya akayi ne?""",,,,,,,
Cikin kuka tace yaya bacci zanyi , don Allah kada ka dakeni,,,,,, sadiq yace kada kiyi bacci kuma ina ganinki daga nan idan kikayi bacci na dawo to ɗinki,,,,
Jawahir tace to yaya inyi ɗan kaɗan?""" yace to kiyi ɗan kaɗan,,,,, tace to saika dawo, yace yawwa, ya kashe wayarshi,,,,,,
Cikin isa da gadara ta shigo farlon da gudu tayo wurin sadiq tana cewa myyyyyyyyyyyyy,,,, adaidai lokacin data faɗa saman shi,,,,,, wani somammen murmushi sadiq yayi sannan yace barka da dawo gimbiyar mata,,,,,,
Khadija tace kai yau ansha wahala a daidai lokacin da take cire gyalen jikinta,,,, cikin nuna kuƙawa sadiq yace waye ya baki wahala ne?""",,,
Khadija tace mota ta lalace ne,,, kuma nayi ta kiran wayarka a kashe,,,,, sadiq yace gaskiya, na kashe wayarne nayi bacci,,,, saida ta gama barikinta kaffff sannan sadiq yace kai nima yau naji abunda na daɗe banji ba,,,,
Kuma naga abinda na daɗe ban gani ba,,,,, khadija tace miye my?""" sadiq yace wani abokina yayo man waya yace man matarshi ya kama da ƙato wai idan nine wane hukunci zan ɗauka??"""""?
Khadija tace to ya kace a daidai lokacin da take kwantawa saman sadiq,,,,,,, sadiq yace ce mashi nayi ai bani ne ba,,, da zan iya kamanta abun,,,,,,,,,,
Khadija tace niko dani ce saki ukku zan mata, ta ƙara maganar cikin hauka da rashin sanin inda maganar sadiq ta nufa,,,,,,,,
Sadiq yace to idan kika bata saki ukku alhalin tana tuba fa?"" da nadamar abinda tayi tare da ɗaukar alƙawarin bazata sake ba fa?""""",,,
Khadija tace ƙarya takeyi saita sake saki ukkun shine daidai da hukuncinta,,,,,, murmushi sadiq yayi sannan ya ɗaga khadija daga jikinshi ,,,,,,, tace my miye haka?"""
Sadiq baiyi magana ba, ya miƙe tsaye sannan ya nufi ɗakinshi, dan yaba khadija zaɓi ne, data ce saki ɗaya shine zai bata idan tace biyu shine zai ba, kuma har yace idan ta tuba fa?""" lallai ashe bazata daina halin ba?""""
Wani gajiyayyen murmushi sadiq yayi sannan ya matsa bakin mirrow anan ya rubutawa khadija saki ukku, kamar yanda ta faɗa da bakinta,,,,,
Yana dawowa farlo ta taho cikin yanga da yauƙi,,, zata rungumeshi yaja baya da sauri, sannan ya miƙa mata takardar sakin,,,,,,
Tace kuɗin ne?"" nifa bana san ceak, sadiq yace aishine yafi dacewa dake,,,, a daidai lokacin da take buɗewa,,,,,,, idanuwa ta zaro tare da cewa na jawahir ne?"""
sadiq yace sunanta kikaga na rubuta?""" tace khadija kasa, daga nan sadiq bai sake magana ba, wani irin ihu khadija tayi tare da sulalewa ƙasa somammiya,,,, inda ta faɗi ya tsallaka ya ɗauki key ɗin motarshi da wayarshi yayi gidan uwar gida jawahir,,,,,
Tun a mota yayi mata waya ta tashi yana zuwa,,,,,,,, tace to,,,, tana gama wayar ta ɗauki kaya tayi ta lodawa a jikinta, wai idan ya daketa bazataji zafi ba,,,,,,,
sadiq yana isowa bayan yayi parking, ya shiga, jawahir najin shigowarshi kukanta ya ƙaru,,,, har farlo anajinta, sadiq bayan ya shiga ya kulle ƙofar sannan ya shiga, jawahir na ganinshi ta miƙe da sauri tanaci baba da kuka,,,,,,,
sadiq yace wai miye wannan sakarcin ne?""" niko nace ai ba itace tasa ka saki matarka ba,,,,,,,,,
jawahir tayi diffff sadiq yace sauko daga nan,,,,, sauka tayi da sauri ta matsa kusa dashi ta riƙeshi tana kuka,,,,,,,,,,
Riƙeta yayi sannan yace miye?""" jawahir tace wallahi shine tace inxo ya rage man hanya,,,,,, sadiq yace to, sai kuma miye tace kafin in shiga kazo, yace daga nan kuma sai miye?"""" tace don Allah yayana kayi haƙuri adaidai lokacin da tame kwantar da kanta saman ƙirjinshi,`,,,, tana cewa kada ka dakeni don Allah,,,,,,,,
Ɗagota yayi daga kwanciyar da tayi saman jikinshi sannan yace to muje, yaja hannunta suka matsa wurin gado, zaunar da ita yayi a gefen gado sannan shima ya zauna,,,,,,,,,,,,,,,,
[1/17, 7:46 PM] Jamila Musa Ws: ☄
☄☄
☄☄☄
*WANDA BAIJI BARI BA*
*AMEENCI WRITER"S ASSOCIATION* 📚✍🏻
*MEELAT MUSA*
*Domin samun littattafanmu saiku nemi group ɗinmu a shafinmu na facebook*
*AMEENCI WRITERS NOVELS GROUP*
*Asmeenat Xeeyan wannan page naki ne ke kaɗai saboda keɗin ta dabance a wurina, farin cikin ki shine alfahari na,*
*Ummu farhana ina tare dake sosai kema kece maudi"ina*
*Saffa one kina raina saboda yanda kike nuna kulawa a gareni, ina tare dake kuma inajinki har cikin babban birnin ruhina*
*Gareki Fatima Abubakar A First jinjina ta musamman a gareki alkairin Allah ya daddanneki*
*PAGE 44*
***
*B*ayan sadiq ya zauna ya kalli jawahir sannan yace to ki rufe man wannan bakin sai wani ƙara yageshi kike kina ma mutane kuka,,,,,
Jawahir ta rufe bakinta da sauri tare da ɗora hannunta saman bakin ta riƙe leɓɓenta gam,,
Wani gajiyayyen kallo sadiq ya saukewa jawahir sannan yace tashi ki cire wannan kaya da kika jibga kamar hauka sabon kamu,,,,,,,
Da sauri jawahir ta tashi ta fara rage kayan jikinta tana kuka,,, sadiq yace wai ba nace bana san kuka kukannan ba?""
Cikin kuka jawahir tace nidai bana so kayi man duka kallonfa sadiq yayi sannan yace ai kinyi laifi kuma dolen nan sai kinji a jikinki, ya ƙarasa maganar yana wasa da idanuwansa,,,,
Jawahir tace yaya kasa Allah a ranka wallahi babu kyau zalinci, murmushi sadiq yayi da gefenki bakinsa sannan yace ke abinda kikeyi kyautawa ne?"" cikin sakata jawahir tace towai miye ma laifina?""" ta ƙarasa maganar tana dire dire,,,,,
Miƙewa sadiq yayi ya matsa kusa da jawahir sannan ya riƙeta, yace nine nake cuta ?"" jawahir tace nifa ba haka nake nufi ba,,,, sadiq yace to ya kike nufi?""
Tace kawai ina cewa kayi haƙuri ne,,,, sadiq yace to nayi, zo ki kwanta, jawahir tace ni banajin bacci,, sadiq yace ni kuma bacci nakeji,,,,
Jawahir tace to ka tafi gida mana, yace anan zan kwana, jawahir tace yau kuma?"" miyasa sai anan zaka kwana?"" sadiq yace saboda shima nan gidana ne, jawahir tace ai tunda kayi aure ka daina kwana anan sai yau?"""
Rufe mata baki sadiq yayi da hannunshi sannan yajata suka matsa wurin gado, da kanshi yayi mata nuni data hau sama,,,,
hawa tayi ba tare data sake magana ba, shima sadiq hawa saman gadon yayi, bayan ya kwanta ya jawo jawahir jikinshi sosai, sannan ya fara magana,,,,,
Jawahir don Allah kisa natsuwa a rayuwarki, ki tsaya tsaye sosai ki fuskanci rayuwa, ki sani ita rayuwa takonta canjawa yakeyi, duk haukar mace idan tayi aure natsuwa take samu, don Allah ki natsu kisan kin girma,,,,,
Turo baki jawahir tayi sannan tace wai mi nayi maka kuma?"" sadiq yace ba abinda kikayi man nasiha nake maki, jawahir tace to idan ban natsu ba kuma ya zakayi dani?""
Sadiq yace sai inyi ta haƙuri wanda kuma bana iya haƙuri sai in zaneki ciki da waje,,, jawahir tace to ai saika zaneni tunda kaima bakayin hankali da natsuwa,,,,,
hmmm sadiq yace daga haka bai sake magana ba, jawahir taci gaba da mita sai rishin kunya takeyi wai dama tunda yazo yana wani kwantar dakai tasan ba dan Allah ba,,,,,
shidai bai sake magana ba, tsaki tayi sannan ta juya mashi baya, shima tsaki yayi sannan ya juyota da ƙarfin tsiya, ya juyota tana fuskantarshi yace ke yarinya daga yau kada ki kuskura ki sake juya man baya,
Ni ban juya maki baya ba saike?"" cikin masifa jawahir tace naje na juya da Allah kaika cika masifa wallahi, da sauri ya ɗaga hannunshi da niyar kai mata mari amma kuma komiye ya hanashi?"" saiya runtse hannu yana kallon jawahir,,,,,,
Dariya jawahir tayi sannan tace azzalimi ya fara hankali,,,,, bai sake magana ba yaja bargo yaci gaba da bacci,,,,
saida ta tabbatar sadiq yayi bacci sannan ta tashi zaune saman gadon ta kurawa fuskarshi ido tana kallonshi,,,,,,,,
Wayarta dake gefenta ta jawo da niyar yi mashi photo, tana ɗauka hasken flasher ɗin ya shiga idonshi da sauri ya buɗe idonshi yana kallon jawahir,,,,,,,
baiyi magana ba , ita kuma ta basar tana cewa wannan fitilar yaya bata haskawa sosai,,,,, yace ai hoto cikin dare bayayin kyau,,,, daga haka bai sake magana ba, jawahir tace waye zai ɗaukeka hoto Allah ya sawaƙe,,,,, shidai bai sake magana ba, yaci gaba da baccinshi,,,,,
itama haka ta gaji ta sulale saman gado taja bargo , taci gaba da bacci,,,,,,,,,
[1/17, 7:46 PM] Jamila Musa Ws: ☄
☄☄
☄☄☄
*WANDA BAIJI BARI BA*
*AMEENCI WRITER"S ASSOCIATION* 📚✍🏻
*MEELAT MUSA*
*PAGE 45*
***
*T*unda safe jawahir ta tashi bayan tayi sallah ta gama, ta fara tashin sadiq wai ya tashi ta gyara ɗakinta, a hankaliya buɗe idonshi ya saukesu saman jawahir,,,,,
Tace Ey cewa nayi a tashi zan gyara gado, baiyi magana ba ya ɗauki pillow da bargo ya fita,,,,, parlour ya koma ya kwanta saman kujera 3seater,,,,,
Ita kuma tana gama gyaran gado ta share ɗakin ta goge,,,, tasa turaren ƙamshi, fitowa tayi ta rufo ɗakin da makulli, sannan ta sake zuwa gaban sadiq ta riƙe ƙugu tana cewa yaya tashi zan gyara,,,,,,
Miƙewa yayi ya ɗauki tarkacenshi ya nufi hanyar ɗaki yana zuwa ya taɓa yaji ƙofar a kulle, juyowa yayi sannan yace waye ya rufe?"""
Jawahir tace nice nan, yace to zo buɗe,, tace anƙi a buɗe daga nan ka wuce gdanka,,,,,,, sadiq yace wannan wane irin iskanci ne wai?"""
Tace ai gaskiya ne, nidai ka tafi baƙi zanyi, tsaki sadiq yayi sannan yazo ya ajiye bargon da pillow yace to ɗauko man makullin mota na,,,,,,,,
Tace gashi acan na ajiye ta nuna mashi da hannu, wurin da makullin yake yaje ya ɗauka ya tafi daga farlon,,,,,,,
Tana ganin ya fita da sauri tabishi tana cewa yaya wasa nake maka fa,,,, baiyi magana ba yaje ya ɗauki motarshi yayi tafiyarshi,,,,
Taɓe baki jawahir tayi tare da ɗaga murya tana cewa a sauka lafiya,,,,,,, dawowa tayi taci gaba da aikinta, dan hafsat da sadiyya zasuzo,
Sadiq kuma gidanshi ya nufa,,,, tun a bakin get yaga motoci,,,, da mamaki har yayi farking, bayan ya gama ya fita ya nufi ciki,,,,,,,
Tun kafin ya shiga ciki yajiyo kukan khadija, sai haƙuri ake bata,,, ɗaure fuska yayi sosai sannan ya shiga cikin farlon,,,,,,,
Fatima ya gani a gefe tana cewa kedai khadija tunda an sakeki kiyi haƙuri ki tashi mu tafi,,, a gefe kuma wasu maza ne, su huɗu,,,,,,,,,
A gadarance sadiq ya shige dukanshi a farlon sannan ya kalli inda mazan suke amma baiyi magana ba,,,,, wani ne yace ranka ya daɗe barka da safiya,,,,,,
Sadiq baiyi magana ba sannan ya kalli inda khadija take zaune tana kuka ga fatima a gefenta sai cewa takeyi tashi muje,,,,,,,
Cikin isa da gadara sadiq yace ya akayi ne?"" a daidai lokacin da yake zama saman kujera ya ɗauki ƙafa ɗaya saman ɗaya ya ɗora,,,,
Fatima cikin in da inda tace "yar laɓai ƙawatace tayi man waya an saketa,, sadiq yace Ey, tace to shine tace muzo,,,, sadiq yace wane iskanci yasa aka kawo man maza a gida?""""
Maida dubanshi yayi wurinsu sannan yace ku fitar man daga gida,,,,, babu wanda yayi magana suka juya suka fita daga farlon,,,,,, sadiq yace ku kuma mi kuke so ne?"""
Cikin kuka khadija tace my ka rufa man asiri don girman Allah kada ka rabu dani a daidai lokacin da take rairafe tana matsawa kusa da sadiq,
Tana matsawa ta kama ƙafafuwan sadiq tana ƙara fashewa da kuka,,,,, ɗauke ƙafafuwanshi sadiq yayi ya ɗora saman kujera, sannan yace ku tashi kafin in fara fushi ku fitar man daga gidana,,,,,,,,
khadija tace zan tafi amma saina gama idda,,,, sadiq baiyi magana ba, ya miƙe ya shiga ɗakinshi, yana shiga ya kulle ƙofa, kwanciya yayi danyin bacci,,,,,,
sadiq yana shigewa fatima tace ma khadija ke banza ce, wannan ƙwaƙwa aisai ya rainaki, danice ke yana sakina bazan kwana a gidan ba, ki tashi kawai muyi tafiyarmu idan muka tafi zaifi gane darajarki,,,,
haka dai fatima tayi ta ɗora khadija ita kuma da yake kwanyar ba komai sai ƙaramin tunani don haka tashi tayi taje ɗaki ta haɗa kayanta suka loda a mota suka bar gidan,,,,
ita kuma jawahir tana gama gyaran gida ta shige kicin tayi masu hafsat lafiyayyen girki, bayan ta gama taje tayi wanka,,,,
Sadiq bayan ya gama bacci yayi wanka yana fitowa daga wanka yaji wata irin masassara ta sauko mashi, don haka dolenshi ya koma ya kwanta dan gaba ɗaya yaji kamar zai sharce lahira, yana kwanciya yaja bargo ya lulluɓe, Idanuwanshi sukayi ta zubar hawaye saboda wahala,,,,,,,
Yeeeeee ƙawata sannunku da zuwa wo,,, jawahir ce take yima su hafsat sannu da zuwa tare da rugawa tana rungumesu, hafsat tana ta farin ciki sadiyya ma dariyar takeyi ,,,
Haka suka rantafa suka shige farlo, anan suka yada zango, jawahir ta shiga ta fara jido masu abincin data tanadar masu ruwa da lemo, bayan anci ansha aka fara fira,,,,,,
haka suka yini suna fira tare da nishaɗi, saida sukayi sallah isha"i sannan suka bar gidan jawahir,,,,,,,
bayan jawahir tayi masu rakiya ta dawo, wayarta ta ɗauka ta fara kiran sadiq,,,,,,,,
Saida wayar tayi ringing ta ƙare, bai ɗauka ba ita kuma ƙara kira tayi, sadiq bai ɗauka ba, dan haka sai tayi haƙuri bata sake kira ba,,,,,,,
[1/17, 7:46 PM] Jamila Musa Ws: ☄
☄☄
☄☄☄
*WANDA BAIJI BARI BA*
*AMEENCI WRITER"S ASSOCIATION* 📚✍🏻
*MEELAT MUSA*
*Domin samun ƙayataccin littattafanmu sai ku nememu a shafinmu na facebook wato*
*AMEENCI WRITERS NOVELS GROUP*
*PAGE 46*
***
*A*jiyar zuciya jawahir tayi tare da zama a gefen gado tayi tagumi tace to azzalimi kuma ko lafiya?"""
Tana cikin tunanine taji wayarta na ƙara, cikin zaƙuwa ta duba, ta ɗauka ma sadiq ne, tsakiya tayi a daidai lokacin data ɗauka tace innas yane?"""
Inna tace dama cewa zanyi lafiya naga banga sadiq ba,,,,,,
Jawahir tayi shiru inna taci gaba da cewa kuma na kira wayarshi ba,a ɗauka,,,,,
Jawahir tace yayi tafiyane yabar wayar a gida,,,, inna tace ina ya tafi ne?"" jawahir tace yaje abuja,,,,, inna tace to ai irin wannan sai mutum yaji babu daɗi,
Jawahir tace gaskiya, amma insha Allah yana dawowa zai kiraki, inna tace to Allah ya dawo dashi lafiya, jawahir tace amin,,,,,
Bayan ta gama waya da inna tayi ta kiran wayar sadiq,,,,, shi kuma yana kwance ciwo ya isheshi,,,,,
Jawahir taci gaba da kira taƙi gajiya, a wahalce sadiq ya miƙa hannunshi ya jawo wayar daƙel,,,,,
Yana ƙoƙarin kashe wayar baki ɗaya, yaga jawahir ce,,,,,, a gajiye ya ɗauki wayar , cikin yanayin wahaltuwa yayi magana,,,,,,
Jawahir tace yaya kana ina ne?""" cikin jigata yace ina gida,,,, jawahir tace to miye ayita kiranka baka ɗauka ?""
Yace banda lafiyane, to idan baka lafiya yaya baza kayi waya bane?"" innas sai kira takeyi nace baka nan kaje abuja,,,,
Tari sadiq yayi sannan yace kirata kice banda lafiya,,,, jawahir tace bayan nayi ƙarya nace kana abuja, cikin disasshiyar murya sadiq yace ai kowa ya san kin iya zungura ƙarya,,,,,,
Jawahir tace aikai matsalar ka kenan, ana maganar arxiki sai ka kawo wata magana, ta ƙara maganar tana tsaki,,,,,,,
Sadiq yace to taho kixo ki ɗaukeni,,, jawahir tace ni nasan inda zan ganka ne?"" ƙwatance sadiq yayi wa jawahir tace to gata nan zuwa,,,,, bayan sadiq ya kashe wayar ya daddafa ya tashi ya shiga toilet,,,,
Ita kuma tana gama wayar makullin motar ta ɗauka , dan tafiya ɗauko azzalimi,,,,,,
Bayan sadiq ya fito daga toilet , wata ƙatuwar rigar sanyi da hula yasa, saboda sanyi yakeji sosai, bayan ya gama ya fito farlo yana jiran zuwan jawahir,,,,,,,,
Ita kuma tana isowa unguwar, tayi mashi waya tazo, ya fito, yace waishi bazai iya fitowa ba sai tazo ta kamashi,,,,,,
Jawahir tace ashe ko lallai kana da aiki, ƙato dakai ina ni ina iya kama ka?"",,,,,, sadiq yace du Allah kixo, jawahir tace kai nidai gaskiya bazanzo gidanka ba, matarka tace wani abu,,,,,,
murmushi sadiq yayi mara sauti sannan yace gani nan zuwa,,,,,,, bayan ya kashe wayar ya miƙe ya fita daga farlon,
A bakin get mai gadi ya gaishe shi, sadiq ya ansa, sannan yayi gaba,,,,
jawahir tana hango shi taci gaba da tahowa da mota, tana zuwa wurinshi daga ciki ta buɗe motar tare da cewa shigo,
A gajiye sadiq ya shiga, sannan ya rufe motar, bayan sun fara tafiya jawahir tace miya sameka?"" ba tare da ta kalli inda yake ba,,,,,
Baiyi magana ba, jawahir tace bakaji ina magana ne?"", sadiq yace banda lokacinki, dariya tayi sannan tace ai dana sani banzo ba, na barka sai ka suma ka rasa mai kaika asibiti,
yace yanxun ma zaki iya mayar dani tunda bakiyi nisa ba, murmushi tayi sannan tace nikam nasan arxiki, yanxun nan gidanku zan fara kaika, innasco da babs