Author : MEELAT MUSA Category : African Stories & Novels
Copied By
YAYA HAYAT
(admin
Hayat hausa novels
Hausa novels and fashion
Cool novel, makeup and kitchen1⃣
Cool novel, makeup and kitchen2⃣
AND
Cool novel, makeup and kitchen3⃣)
WHATSAPP NO:+2349030159301
☄
☄☄
☄☄☄
🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥
*WANDA BAIJI BARI BA*
🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥
☄
☄☄
☄☄☄
*AMEENCI WRITER'S ASSOCIATION* 📚✍🏻
*MEELAT MUSA* 🌹
*PAGE* 1
***
*Rayuwar ƙarya ce tasa ma kanta, sannan kuma bata ɗauki duniya da sauƙi ba, iyayenta basu da hali amma ita ala doƙe sai tayi rayuwa irin ta masu kuɗi, iyayenta basu da hali amma dole sai tayi makarantar kuɗi, ganin rayuwar data ɗauka yasa mahaifiyarta take mata nasiha, amma wanda yayi nisa baya jin kira*
*Ba anan ta tsaya ba, zuwanta makarantar kuɗi yasa taga yanda "ya"yan masu kuɗi suke rayuwa hakan ya ƙara hura mata wutar halin data sa kanta, ta raina cimar gidansu, sannan duk inda taji mai kuɗi ko wani fitattace wanda duniya tasan dashi yanxun nan zatace ɗan uwanta ne,*
*tayi ma duniya babbar iba, saboda haka duk inda ake biki na masu kuɗi ko suna, kana buɗe idonka saika ganta, ba,a nan ta tsaya ba, wannan rayuwar tasa ta cin bashi idan taci bata biya, sannan kuma ta ƙware wajen 4 1 9*
*Ko hutu akayi idan kuɗin makaranta sukai mata tsaye , ko ƙawayenta sunce kwana biyu bata zo ba, sai tace tayi tafiya ƙasashen waje, idan kuma taga mahaifiyarta da abu ta zura mashi ƙahon zuƙa bawai tayi sata ba, ah ah da ƙarfin tsiya zai zama nata*
*Idan kuma taji biki duk inda zataje ta samo kuɗin anko sai tayi, kai wannan wace irin rayuwa ce?"""" hmmm muje dai muji*
****
*W*ani ƙayataccen wurin cin abinci ne, kana ganin wurin cin abincin kasan bana yara bane, wuri ne da aka tanada dan masu kuɗi suxo su more kuɗin su , dan mai waƙa yace kuɗi da maciji maganin su kashewa,
Jawwahir a gefe zaune tare da wata tsohuwar fitilar kwai kusa da ita, a gabanta kuma ga lafiyayen abinci da lemu, wayarta a hannunta a kunnenta kuma ta saka earpies, glass ɗin idonta ta cire ta ajiye a gefe sannan ta fara cin abinci,
Tana ci tana latsa wayarta, saida ta gama cin abincin tsaff sannan tasha lemon ta, jakarta ta jawo taga duka naira 100 ne a ciki, murmushi tayi sannan ta tattara kayanta ta tashi a wurin,
Saida ta miƙe tsaye har ta fara tafiya sannan tasa glas ɗinta a fuskarta, inda ake biyan kuɗi taje, ta tambaya nawane kuɗinta?"" dubu biyu, tace okey,
To yanxun gaskiya banda kuɗi a hannuna dan shigowata gari kenan tana magana tana taɓe baki, taci gaba da cewa kaga abinda ya bani wahala nan, ta ɗaga fitiƙar kwan hannunta, tace ka taɓa ganin ta ne?"""
Yace Eh, tace ko kana da irinta ne?"" tana magana tana ɗan buɗe idanuwanta yanda take maganar ta nuna abun yana da mahimmanci, yace banda irin ta, jawwahir tace ashsha, ai yanxun nemanta ake, idan ka kawo ta miliyan ɗaya cass za"a baka, dan akwai wani abu da turawa suke nema a cikinta,
Nan nigeria ne ake bamu ita mu bayar da miliyan ɗaya mu kuma idan muka kaita ƙasashen waje muna samu miliyoyin kuɗi, ɗan tsaki tayi sannan tace riƙe fitilar inje in ciro kuɗi a banki in dawo,
Yace to ya karɓi fitilar ita kuma fita tayi, tana fita shi kuma yaji ance miliyoyin kuɗi ake siyen fitila kuma tace daƙel ta samo ta, saboda haka sai ya ɗauke fitila yaje ya ɓoye,
Jawwahir tana fita ita kuma, bata sharce ko ina ba, napep tahau, ta faɗa mashi inda zai kaita, ya ɗauketa suka tafi, bayan sunje ta sauka wata super market ta shiga, tana shiga wurin wani taje ta bashi wayarta tace ya riƙeta ya bata dubu ukki yanxun nan zata dawo,
Yace to, karɓar wayar yayi sannan ya bata kuɗin, ta dawo ta hau napep tace ya mayar da ita inda ya ɗauko ta, yace to, suuuuuuuuu har suka iso wurin,
Bayan ya ajiyeta, ta sallameshi , da sauri ta shiga wurin, inda ake biyan kuɗin taje cikin sauri tace yawwa malam ga kuɗink bani fitalar sai waya ake yo man, ana jirana, ɗan dube dube ya shiga yi wai baiganta ba,
Idanuwa jawwahir ta zaro tace lallai babu zaman lafiya, domin anan waa yanxun nan ance man an ƙara man dubu ɗari biyu akai saboda haka ko fitilata ko kuma insa a kulle man kai,
Yace haba hajiya ai duk abun baikai haka ba, yanxun tunda ta ɓata sai mu raba asara, idanuwa jawwahir ta zaro tace asa me?"" aini bansan asara ba haka kuma bansan ƙaddara ba,
Kawai fitila na zaka bani, yace hajiya kiyi haƙuri bara in baki dubu ɗari takwas kiyi haƙuri da hakan tunda ƙaddara ta faɗa mata don Allah, tsaki jawwahir tayi sanna tace nidai kawai kaja man asara, amma banda yanda zanyi bani, amma bana karɓar ceak zunzurutun kuɗi nake so, yace kada ki damu, ina zuwa,
Tafiya yayi ya shiga wani wuri, bayan wani lokaci yazo da kuɗin ya bata, ta karɓa, ta irga, sannan tayi tafiyarta daga wurin, tana fita ya ɗauko fitalar yace banza, sai inkai in samu kuɗina, niko nace ba jawwahir bace banza kaine banza,
Jawwahir tana fitowa ta hau abin hawa, inda ta bada wayarta taje, ta bashi dubu ukkun data karɓa, shi kuma a bata wayarta, sannan tayo gida da kuɗin ta jimmm a jaka,
Tana dawa gida, ko sallama babu haka ta shige ciki, inna tace jawwahir ki dawo ?"" tace umm, ɗaki ta shiga ko takalmin ƙafarta bata cire ba, ta haye saman gado, kuɗin ta fiddo ta sake irgawa, sannan ta kece da dariya tace jakki dan uwarka idan miliyan ɗayan gaskiya ne, zan barka haka ne ka bani dubu ɗari takwas?"" uhm Allah yasa kaje da fitilar wani wuri a zaneka , daria tayi sannan ta haɗa kan kuɗinta ta ajiye, wayarta ta jawo ta fara kiran wata ƙawarta,
Bayan sun gaisa tace mata gobe insha Allah zan shigo sch kinsan bana nan naje *solvenia* jiya na dawo, tace Allah ya kaimu lafiya, tace ameen,
Kam lallai wannan wace irin rayuwa ce? 🤔uhum muje sannu a hankali,
☄
☄☄
☄☄☄
🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥
*WANDA BAIJI BARI BA*
🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥
☄
☄☄
☄☄☄
*AMEENCI WRITER'S ASSOCIATION* 📚✍🏻
*MEELAT MUSA* 🌹
*PAGE* 2
*Allah ya baki lafiya halima yahya ubangiji yasa zakkar jiki ne, Allah ya baki ladar jinya*
*****
*J*awwahir saida ta gama latse latsen wayarta tana kiran ƙawayen ta cewa ta dawo daga *solvenia* sannan ta cire kayan jikin ta, towel ta ɗauro ta fito tsakar gida,
Saboda gayunta da iskancin ta, inna haka ne sunan da suke kiran mahaifiyarsu dashi, amma ita haushin yayyen take ji da basu kiran ta da irin *momsy* irin su *momy* ko *mama* ko *ammi* ko *mami* ko *mamma* ita wannan abun baƙin ciki yake mata, saboda haka ita idan zata kira *inna* saidai tace mata *innasco* ko kuma tace *innas* ita ala dole sai tayi gayu, a cikin ƙawayenta kuma idan tana bada labarin gidansu zata *mom* ɗin da *dad* haka take cewa,
Jawwahir tana fitowa ta kalli inda inna take zaune tace innas lafiya naga kinyi jugum?"" sai kace an aiko maki da saƙon mutuwa, inna tace ai da saƙon mutuwa aka turo man zaifi man sauƙi akan turbar da kika ɗora rayuwarki, tsaki awwahir tayi tace ai ku matsalar ku kenan baku ma mutum fatan alkairi kullum sai addu"ar ƙaryarshi ta ƙare,
Kujera ta samu tayani gulma ta zauna tana kallon inna tace innasco lura da wani abu ɗaya a rayuwa ita fa dama kika ganta so ɗaya take zuwa a rayuwa,
Yanxun dana biye maku haka zan zauna babu ilimi, tunda shi wancan tsoho Allah yasa matatciyar zuciya ne dashi baya iya nema ya wani ɓige da kasa icce a bakin titi, sai inje in nemo,
Bakinta ta taɓe sannan tayi ƙasa da maganarta cikin yanayin kuka tace ni wallahi kunya ma nake ji ace shine babana,
Idanuwa inna ta zaro tace iskancin naki har yakai nan kuma?"" jawwahir tace ai tuni na wuce nan, ke innas ashe baki karatun jawwahir daidai,
Inna tace idan kina
rufa ma kanki asiri ki daina wannan rayuwar ki bari, ita rayuwa duk abinda Allah ya nufa zaka samu saika sameshi, idan kikai haƙuri kika zauna a gida Allah zai kawo maki,
Jawwahir tace wallahi babu abinda zan samu idan na zauna shin yauma nake zaune gidan ne?"" ai kinga ban samu ba, amma idan mutum ya miƙe zaiga samu idan kuma ya zauna zaiga zama,
Miƙewa tayi tsaye ta ɗauki kwandon wanka, tace wallahi innas wancan awakin naki idan basu daina man kuka idan ina waya ba Allah duk sai na tattara "yan iska na siyar, danni yanxun ina gama makarantar nan zanje inje in samu aiki , kuma mota zan siya,
Inna tace aikin uwarki, wane sakarai zai ɗauke ki aiki da takardun ƙaramar makaranta, { secondry sch } jawwahir tace innasco baki san ɗiyar taki takai ba, ai wani babban comparny ne, za"a ɗauke ni aiki na baban abokina ne,
Inna tace baban abokin ki kuma?"" tsaki jawwahir tayi tace ai wanda baije makaranta ba baya ganewa shi yasa nace ki koma ko yaƙi da jahilci kiyi dan idan na faɗi magana ki riƙa gane inda tayi.........""" daga nan bata sake magana ba ta shige bayi,
Ajiyar zuciya inna tayi tace Allah ubangiji ya shirya ki, ina dabbonta suke ta kalla wasu hawayen baƙin ciki ya zubo mata dan tasan rabuwarta dasu yaxo, tunda har jawwahir tace suna mata kuka idan tana waya,
Inna tace to nidai ai ba bakinsu zan ɗaure ba, amma dole inma Sadiq waya yaxo yaci uban yarinyar nan,
Da "yar waƙa ta fito daga cikin kewayen , haka ta taho tana raira waƙarta har ta shige ɗaki, inna ta bita da kallo tana mata addu"ar shiriya, inna tace Allah sai ya baka "ya"ya amma kowa da irin halinshi, Allah ubangiji ka shirya mana zuri"a, lokacin da inna ta jiyo jawwahir ta kunne waƙa da sifiku ta ƙure volume, tashi tayi daga wurin ta nufi wurin bisashen ta dan basu abinci,
Jawwahir tana gama shirinta, gado ta haye, dan ita ko sallah bata tsayawa yi bare ma tayi ma kanta addu"a,
Inna kuma tana fitiwa daga garken awakinta, waya tayi ma sadiq yaxo tana neman shi, yace to amma baya gari idan ya shigo insha Allah zaizo saboda yanxun dare yayi inna tayi amshi addu"a da fatan dawowa lafiya,,,
*******
*T*unda safe jawwahir tana tashi wanka tayi ta fara shirin tafiya makaranta, dan suna shire shiren fara s s c e, sabida haka kuma ta samo kuɗin da zata biya na jarabawa, inna ce ta shigo ɗakin da rubar tuwo a hannunta,
Gaban jawwahir ta ajiye tace kici tunda ban dama koko ba, wata "yar munafikar dariya jawwahir tayi daidai lokacin da take ɗaure zariyar wandon ta, tace hajiya innasco kenan, waye zaici wannan ?"" inna tace ke,
Idanuwa jawwahir ta zaro tace Allah ya sawaƙe inci tuwo ke yanxun don Allah innas baki man faɗa inci tuwo in tafi abun tsotsayi inyi amai ai kin gama ja man raini wallahi , dan gajeren tsaki tayi daidaii lokacin data ɗauki jakar makarantar ta tayi gaba,
Tana fitowa baba ta gani ba tare da ta kalli inda yake ba tace barka da aafe *babasco* tsaki baba yayi sannan yace zo nan dan uwaki , ɗaure fuska jawwahir tayi sannan tazo gaban baba tayi mashi tsaye, yace haka zan gaya maki magana tsawonki ya kere nawa?""" sauri nake na makara makaranta idan na dawo na biyo ta kasuwar, bai sake magana ba, ita kuma ta fice daga gidan..................
Inna ce ta fito daga ɗaki tace kayi haƙuri yau zansa sadiq yayi mata shegen duka dan mu huta kwana biyu, baba yace Allah dai shirya ubangiji ka shirya mana zuri"a, ameen,
Fatan alkairi gareku masoyana, 💋 kune alfaharina farin cikinku shine nawa, 💋
☄
☄☄
☄☄☄
🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥
*WANDA BAIJI BARI BA*
🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥
☄
☄☄
☄☄☄
*AMEENCI WRITER'S ASSOCIATION* 📚✍🏻
*MEEELAT MUSA* 🌹
*PAGE* 3
*****
*J*awwahir tana fita ƙofar wani gida ta tsaya, tana daɗe tana tsaye sannan wata ƙatuwar mota ta fito, da sauri ta matsa kusa da motar glass ɗin motar ya sauƙe, tace haba don Allah kayi sauri wallahi ina ganin kamar na makara yau,
Murmushi yayi sannan yace to shigo muje, da sauri ta zagaya ta buɗe gaban motar ta shige shi kuma ya figi motar a 360, ƙura kuma tayi masu rakiya,
Wannan daya ɗauki jawwahiri maƙotansu ne, iyayenshi basa zama a gari sosai shi kuma yana zaune sabida karatu yake, kuɗi garesu sosai a gidansu, jawwahir taxo ta nemi alfarma ya taimaka ya rufa nata asiri ya riƙa kaita makaranta,
Dan bata shiga makarantar ba sai da tayi j,s,c,e sannan ta shiga makarantar kuɗi, to shine yake taimakawa yakai ta, idan bai samu lokaci ba ko yana rashin lafiya idan taje makaranta zata ce yayanta baya lafiya, sunan sa *ja"afar* saboda tsabar yaudara take kiranshi da *honey j* dan tace ɗan yayan dad ne, kuma dad ɗinsu yake riƙonshi, tace ya mutu kanta ita kuma bata aurenshi gaskiya,
Lokacin da suka isa makaranta ya ajiyeta ,godiya tayi mashi sannan ta fita, tana fita ya tafi, ita kuma ta nufi gungun ƙawayenta, sai sannun da zuwa ake mata tare da fatan ta dawo daga *solvenia* lafiya,
Wasu kuma suna cewa ina tsaraba, jawwahir tace tsaraba su bari sai an tashi sch kowa ya faɗi abinda yake so sai ta siya masu, haka dai ta tusa su gaba taci gaba da zungura masu ƙarya, wai su dad da mom sun tafi *australia* da tare zasu amma saboda exam da zasu fara ne ba"a tafi da ita,
Amma tana gamawa zata bisu dad yace su haɗu a *edmonton canada* haka dai taci gaba da zazzaga masu ƙarya, daga baya kuma tace wata ƙawarta hafsat babu biki ne?"""
Hafsat tace akwai biki mana amma ankon yayi tsada da yawa jawwahir tace ba damuwarta bane, nawa ne kuɗin ankon shin inane ma ake bikin inji idan yaman?"" hafsat tace gidan tsohon gomma ne, jawwahir tace haba zamu fasa ,
Nawane kuɗin?"" hafsat tace gaskiya idan dai zakije kawai hajiyata ware ma bikin nan dubu ɗari ukku in haɗo maki ankon farty da deaner, murmushi jawwahir tayi sannan tace idan mun tashi sch zan baki, ƙawayen su dake wurin suka ɗauki shewa yayi masu mura ai suke da majina, taken da suke wa jawwahir kenan, dariya tayi sannan suka wuce class,
Lokacin da, aka tashi break taje ta biya kuɗin jarabawa , ta dawo class,
Ana tashi makaranta kuma ta tattara ƙawayenta suka tafi wata super market tace kowa ya ɗauki abinda yake so, haka kowa ya zaɓi abinda yake so, su dama "yan gayu anci komai a gida an ƙoshi saboda haka choculets suka ɗauka da ɗan abinda dai mutum yayi ra"ayi,
Haka akai mata bill kuɗi masu yawan gaske ta biya, tunda tana da kuɗin da tayo danfara jiya, bayan sun gama ta bada dubu ɗari ukku kamar yanda hafsat tace, haka sukai ban kwana kowa ya kama gabanshi,
Napep ta hau tayo gida, tunda ga nesa ta hango ƙofar gidansu da mutane, tsaki tayi sannan tace shege idan dai kaine ko uwarka ta dawo duniya bazan bayar da kuɗin nan ba,
Tana isowa, taga malam sani , yace yawwa ga "yar banzar nan ta dawo, jawwahir tace kaine ɗan banza, ni ba ɗiyar banza bace da sadaki aka auro uwata ta haifi ɗiyar sunna, malam sani yace bani kuɗina, jakarta ta buɗe tace kaga ina da kuɗi?"" yace Eh tace to na ƙarfin babbar bala"i ne idannkana da wanda ya tsya maka yazo ya karɓa,
Babanta yace ke jawwahir basu kuɗinsu kinsa an tara man mutane a ƙofar gida cikin unguwa duk inda na wuce ana zagina, dariya jawwahir tayi sannan tace kaine kaci bashin?""" yace ah aha, dafa ƙirjinta tayi sannan tace nice naci bashi kuma bazan biya ba,
Malam sani yace ai shi yasa na taho maki da hukuma, dariya jawwahir tayi sannan ta kalli inda "yan sanda suke tsaye tace da wa"an nan "yan iskan kuratan ka ɗauko man wanda idan na hunce duk saina masu jegen duka, baba yace jawwahir basu kuɗin su, yace dubu goma ne, jawwahir tace 10k ne kuma wallahi idan dai wanda ya mutu zai dawo to zan bayar da kuɗin nan,
Inda "yan sanda suke taje jakarta ta buɗe ta basu 5k tace suje susha ruwan sanyi, ana basu kuɗi suka wuce daga wirin, inda malam sani yake ta kalla sannan tace ɗan tsoho ka bani kunya saboda dubu goma kake ta wani tada jijiyar wuya,
Idan ka bayar da zakka ya kake ji?"" malam sani yace ai wannan haƙƙin Allah ne na fitar jawwahir tace nima shine ka bani, na gode, tana faɗin haka tayi cikin gida, malam sani yayi ta Allah ya isa, sannan ya tafi,
Lokacin da jawwahir ta shigo gida sadiq ta gani zaune da wasu irin dorinai a gabanshi , gabanta ya faɗi amma ta basar ta wuce, zata shiga ɗaki yace ke zonan dan uban da ya haifeki, dariya tayi sannan tace nifa nace ka fita a harkata idan ba haka ba wallahi zansa a ɗaure man kai,
Yace bazan fita harkar ba dan ubanki, tace kada ka sake zagina, yace zaki rama ne?""" tace ɓacin rana ake gudu, yace to nace ubanki, tace kaima ubanka tunda uba baifi uba ba, tana magana tana burguɗa baki, lokacin data zage shi, wani ɓacin rai ya baibaye mashi zuciya, dorinar ya ɗauka yaci gaba da zabzabga mata babu ji babu gani, tun jawwahir tana iya rama wa har tayi laushi sannan yace kuna dan ubanki kin daɗe baki kwashe awakin kika siyar ba,
Murmushi tayi cikin yanayi wahala tace wato saboda wa"ancan mayunwatan tumaki aka dake ni?"" yanxun na gane dalili, girgiza kanta tayi sannan tace da kyau, har yanxun tana wurin ta kasa tashi, sadiq shi kuma fita yayi yabar gidan,
Yana fita jawwahir cikin wahala da nishi tace wallahi tunda kika sa aka dakeni saina siyar dasu kisa a kasheni don Allah, kuma daga yau kada ki kuskura ki sake man magana tunda baki kauna ta, inna bin jawwahir tayi da kallo, ta tashi a gajiye tayi ɗaki,
Tana zuwa kayanta ta cire sannan taje tayi wanka, bayan ta shirya waje ta fita ta kira almajiri ya wanke mata kayan makarantar ta, tana bashi tayi waje...........................
Ku kasance tare dani💋
☄
☄☄
☄☄☄
🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥
*WANDA BAIJI BARI BA*
🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥
☄
☄☄
☄☄☄
*AMEENCI WRITER'S ASSOCIATION* 📚✍🏻
*MEELAT