Author : Maryamah Mrs AM Category : Drama
beji
shigowar kiranta ko message ba gashi yanzu dayan dare ta kusa idan banda bata da
hankali ai yaci ta kira taji ko lafiya ya taho ko be taho ba amma ina da dai ya
mata alqawarin kudi ne be cika ba da yanzu ta ishe shi da kira kamar yaci bashin
ta. Kwafa yayi a ransa yana jin kaman gobe ya juya Lagos kawai tunda zuwan nasa
beda muhimmanci tunda bata damu ba.
Haka ya daddafa ya kwanta kafin ya samu bacci ya daukeshi.
Gidan Addah
Wuni Addah tayi tana bankawa Amira jiqe jiqen yan bori da magungunan mata ko tsoron
halin da take ciki kar wani abu ya sami babyn basayi, bata haquraba seda Amiran ta
fara sheqa Amai tukunna aka koma cushe cushe dana hayaqi. Bayan maganin gurin Wizy
ta tura an sake karbo mata wasu duk ta banka mata a cewarta gara a hada hannu da
yawa ayi maza buqata ta biya.
Babu lissafin zuwa ta gyara gida bare aje ga batun yi masa girki sukayi zaman su na
jira yazo da kansa yace su tafi tunda a kwanakin ta sami kansa suna abin arziqi dan
kiran da tayi masa jiya da daddare ma kuka ta saka masa akan ita dai yazo tana
missing nasa in ba haka ba zata hawo jirgi ta zo Lagos sedai Anty ta basu daki.
A lokacin yasha mamakinta dan shidai Rashin kunyar Amirah na daure masa kai ko
kadan bata jin nauyinsa wanda sam ba haka Asmaβu take ba. Maβu bata masa irin
wadannan maganganun gatsal ta dai san signs da signals da take amfani dasu wanda
suke balaβin burge shi da qawata zuciyarsa dan kullum cikin qara masa sabon ilimi
take amma ita wannan se zance a baki ba abinda ta sani idan an zo wajen.
Se bayan Magriba ta shirya taci uwar kwalliyarta dan tasan zuwa sannan ya sauka
Gombe. Ita sam tunanin taje ta gyara gida be zo mata da daman duk sanda zezo shi
yake tuna mata to jiya da be magana ba itama tunda tsaftar ba damunta tayi ba se
bata je ba a ganinta ai befi sati uku da zuwansa na qarshe ba gidan beyi datti ba
ai. Tana zaune Adda na qara karanta mata yanda zaβa yi suna jiran zuwan Bashir
shiru se ji sukayi ana rufe qofar gidan ta kalli agogo 12 saura.
Seda gabanta ya fadi sanda taga missed call dinsa tun wurin bakwai ya kirata. A
yanda ta lissafa sunyi waya sanda ze taso yace mata yanzu zasu taho kenan lokacin
da ya sake kira yana Gombe ai ita yaci ta kira taji ya sauka.
To yanzu ya zatayi ta kirashi ne ko Aa haka tayi ta wasi wasi bata ko iya tankawa
Addah dake faman sababi naqin zuwan Bashir din ba har tana da safe zata je ta samu
uwarsa taji dalili dan baze ja mata asara ba wallahi.
Ita dai Amira daki ta shige ta chanza kaya dan Addah tace karta kuskura tayi wanka
ance se ya kwanta da ita tukunna saboda abubuwan da ta sassaka, haka ta kwanta tana
zullumin haduwarsu dan dai ta haqura bazata kirashi yau ba gara ta bari da safe se
taji duk yanda ake ciki tasan dai ta kwafsa tabbas dama yaya ana lallabawa ne kuma
yanzu ta sake ballo musu ruwa.
Tunanin qaryar da zata yanka masa in sun hadu ta shigayi amma duk wadda ta hado
seta ga ze dago ta qarshe ta fawwalawa Allah kawai ta kwanta duk yanda goben tayi
shikenan.
Washe gari Bashir tun qarfe takwas ya nufi gidansu, tun daga waje yake jiyo tashin
muryar Addah data taso Amirah a gaba suka taho gurin Dada dan jin ina Bashir ya
maqale dan ita bata magana a hankali. Bacin ransa ne ya nunku wato har sunada
kwarin guiwar kawo qarar sa kenan ko? Se kawai ya juya dan bama ya so ya shiga yayi
abunda ran kowa seya baci dan haka se kawai ya juya da niyyar fita, ya rigada ya
makara dan tuni Addah ta hango shi ai kuwa ta shiga taratsin kiran sunan sa akan ya
dawo bashida zabi ya juyo jin Dada ta saka baki fuskar nan a dinke kamar wanda yaga
mutuwarsa ya nemi guri ya zauna yana muzurai.
Kallo daya yai wa Amirah data duqar dakai kamar munafuka dan bata so suka hadu a
gidan ba yanzu se yace ita ta kawo qarar bayan wallahi Addah ce, seda tace kar suzo
amma taqi gashi yanzu ta ja matana jangwam.
ππππππππππππππππππππππ
WATA KISHIYAR π₯°πΉ
(ALKAHIRI CE KO SHARRI)
ππππππππππππππππππππππ
Na Maryamah_Mrs AM
(Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah)
Page 10
Kansa a duqe yana jin yanda Addah take surfa balaβi kamar wadda akayiwa wani abu
magana daya biyu seta zagi Asmaβu da ya rasa me ta tsare mata a rayuwa. Shifa Addah
na bashi mamaki wallahi, idan ya tuna fuskar data zauna da Maβu ada da kuma
bayyananniyar fuskarta ta yanzu. Qiri qiri ta babbake ta hanashi magana bare ya yi
nasa qirafin qarshe ma se suka dora masa laifin ai shi ya kamata ya biya ya dakkota
tunda yasan halin da take ciki.
Baqin ciki kamar ya fashe lokacin da yaji Dada tana cewa Amirah ta tashi ta bishi
su tafi yanzu se ya miqe yai waje fuu yayi waje ba tareda ya shiga ya gaisa da
Mahifinsa da kuma Abokiyar zaman Dadan ba. Har suka dauki hanya be ko kalli Amirah
data takure saboda tsoron abinda ze mata ba, ita dai bata so akace ta biyo shi ba
dan su basusan Bashir bane shiyasa.
Tasan shirun sa ba Alkahiri bane dan haka ta saka ido tana jiran karbar hukunci har
suka isa qofar gidan. A waje yai parking ya kashe motar ya fito yana gaba tana
binsa a baya. Da key dinsa ya bude palour ta takaicin sa ya nunku ganin tarin datti
a palour kamar wanda akayi biki dan robobin lemo ne da take away pack ko ina.
Waiwayowa yayi ya kalli Amirah da jikinta ya fara rawa dan ita se yanzu ta tuno da
bridal shower din bikin Qawar ta da sukayi sati biyu daya wuce a nan din, kuma koda
suka gama bata gyara ba ta bari akan se ze zo tazo ta share aam kuma ta manta. Nan
da nan ta fara inda inda tana tattaro rantsuwa dason yi masa bayani ya katse ta
βZan fita wallahi ko mutuwa zakiyi kafin na dawo ki tabbatar kin gyara gidan nan
har compound ki fita ki share, in kin ga dama karkiyi ko kuma ki kira wani ya taya
ki zaki gane wane ne Bashir shashasha da bata san ciwon kanta baβ yai maganar cikin
fushin da har a muryar sa take ji kafin yasa kai ya fita.
Ita kam indai iya hukuncin kenan ma ai tazo da sauqi, tasan Yaya Bashir da qazanta
ko yaya yanzu zaβa ji kanku kuma shi in kayi masa laifi yayi magana abun nada sauqi
amma idan muskilancin nan ya motsa se yafi shekara yana azabtar dakai ba duka ba
zagi to ita gara yai mata hargagin ya bata horo shikenan tasan ya wuce.
Hijabin ta ayije ta debo kayan shara. 3 Bedroom ne a part dinta kowanne da toilet a
ciki biyu nata se nasa daya, Madaidaicin palour,kitchen da store a ciki se Dining
area. Nasa dakin ta fara gyarowa ta nutsu sosai dan gudun kuskure, ta share ko ina
ta wanke toilet sannan tayi mopping. Bedsheet ta shimfida ta cire tsohon ta boye
dan tasan ya gani se yayi magana ya hana ta barin Bedsheet a gado in bata nan amma
taqi ji sedata kunna Ac ta tsaya tana maida numfashi, iya nan tayi amma harta gaji
amma tasan idan batayi da kyau ba ma kanta ta jawa.
Har zuciyarta tace tabar dakunanta ta gyara palour kawai da Kitchen wata zuciyar ta
ce mata ko sama sama ne tayi tasan yanda yake a kusan nan tsaf ze leqa ko ina.
Dakin baqi ta fara shiga Ba shara ba komai ta hau moping, toilet dinta ruwa ta
watsa bata wanke ba taja ta rufe ta shiga Bedroom dinta. Yana nan a hargitsensa
yanda ta tafi ta bari, kan gadon kayan gugar da aka kawo mata ne bata shiryasu a
wardrobe ba, babu lokaci dan haka ta tattara ta watsasu duk gugar ta hargitse.
Bedsheet din shima ta chanza ta hau moping bayan ta kwashe kufunan data sha wani
lemo wani fura harda ledar balangun dataci ana gobe zata tafi ta manta bata dauke
ba da sauran a ciki ya bushe.
Tana bude toilet dinta kuwa zarni da warin kayan wankin data tara suka bugota dan
ita fa a qasa take tsula fitsarinta ga Tiles da kama zarni, kaya kuwa nan take
watsar dasu har kuwa da inner wears dinta seta tara ta rasa na sakawa sannan zata
wanke.
A farko tsabar wauta da rashin hankali ma harsu take hadawa a wanki se randa Allah
yakai idon Bashir ya gani yai mata tatas tareda jan kunne me qarfi sannan ta fara
wankewa daga baya kuma ya siyamata washing machine ta ringa wanke qananun abubuwa
kayan sawa kuma suna da me wanki duk sati yake zuwa.
Sau daya ya taba bata singlets da Boxers dinsa ta wanke masa a injin ta hadasu a
ruwan dattin kayanta qarshe dai se zubar dasu yayi daga nan kuma be sake bama sedai
ya wanke da kansa.
Kayan ta tattara ta wanke bayin sama sama ta fito. Palour ma ta nutsu dai ta gyara
kitchen kuwa da tasan ba shiga yake ba janyowa tayi ta kulle bayan ta kwashe
kwanukan data bari da abinci a ciki duk sun rube kitchen din se doyin abinci yake
seta watsasu a shara dan bazata iya wanke wa ba.
Tana tsaka da sharar compound ya shigo hannunsa dauke da ledoji daga gani abinci ne
a ciki, seda gabanta ya fadi Allah yasa karya shiga kitchen neman plate dan ruwa da
lemo a kwai a fridge din Dining. kallo daya ya mata ya shige palour abinsa.
Yafi babu sunan gyaran nata, centre table yaja ya dora abincin dan ko karyawa beyi
ba ya fita dama ya zauna akan kujerun da suka fita hayyacin su kamar wanda suka
shekara goma bayan ko cikakkiyar shekara beyi da chanza mata su ba lokacin waccen
Haihuwar da tayi ne. Yana dab da kammala cin abincin ta shigo tana jan qafa tayi
budu budu da qura dan da gaske ta gaji
Kallonta yayi ya danji tausayinta kodan cikin dake jikinta se ya dan sassauta murya
yace βkije kiyi wanka ga abinci kiciβ.
Dan jim tayi, me ta tuna kuma tace βtohβ ta shiga dakinta. Kwaskwarima tayi ta
chanza kaya tareda fesa turare ta fito, ya tashi daga palour dan haka ta zauna taja
abincin taci. Harta gama ta tattara gurin be fito ba dan haka ta bishi tasan yana
dakinsa.
Yana kwance akan gado jikinsa sanye da rigar wanka yana waya da su Jafar da Maβu ta
kira shi bayan sun gaisa ta basu. fuskarsa dauke murmushi saboda maganar da Jafar
din yake gaya masa, beji ahigowarta ba se sautin tsakin ta daya ji kafin ta dora da
fadin
βAikin banza saboda rashin Adalci ma bazaβa bar mutum ya samu lokaci da mijinsa ba
se an tauye shiβ dan a zaton ta da Asmaβu yake wannan murmushin.
Mamaki ne ya kamashi, seya janye wayar daga kunnensa bayan yayi wa Jafar sallama
yana kallonta, bata bari sun hada ido ba ta nufi qofa da niyyar fita ya tsayar da
ita
βWace aikin banzan waye kuma mara Adalcin?β Ya tambayeta muryarsa a kausashe. Dukda
a tsorace take amma seta dake dan Tayi amanna aikin su fa ya fara tasiri akan sa,
murguda baki tayi gefe sannan tace βto in ba rashin Adalci ba nameye zata wani
kiraka yanzu kuma...β bata samu qarasa ba saboda dukan daya kawowa bakinta Allah ya
sota ta duge dukda haka ya same ta a goshi ta dafe gurin.
βFita ki bani guri kafin na illata ki wawuyar yarinyaβ ya fada cikin tsananin bacin
rai ai tuni ta fice dan tasan fushinsa tabbas dukda sau daya ya taba marinta amma
bata fata abinda ze sake sakashi sauke hannunsa a jikinta dan bataji da dadi ba.
Tana fita ta kira Addah ta saka mata kuka tana gaya mata yanda sukayi, Addah data
rasa abinda zatace ta danna mata Ashar kafin tace βkina zaton badan munje gaban
uwarsa ba ze saurare ki da wuri ne? To wallahi in kika janyo mun asara bakiyi aiki
da abinda yake jikinki ba ni dake neβ ta kashe wayar dan takaicin Amirah nema yake
ya sa mata hawan jini.
Ita komai se ance mata ga yanda zatayi in banda wauta har se an ce mata ta
lallabashi ma yau din nan sannan zatayi kai wannan kayan takaici da yawa suke.
Goge hawayen tayi ta shiga tunanin ya zatayi yanzu? A yanda ya fusatan nan tasan
tabbas ze iya mata komai amma bazata yi asarar lokacin nan ba dan itama tana
biqatar aikin nan yaci kodan ta fara zuba ikonta yanda take so, dole ganin ba
mafita ta nufi dakin da taraddadin abinda zata tarar tasan dai baze daketa ba dan
ba dabiβarsa bace dukan mace yanzu nema take tunzura shi harya kawo mata mari wani
lokacin.
Bashir
Yana zaune a gefen gadon ya dafe kansa da hannu bibbiyu, shidai tunda ya auri
yarinyar nan yai bankwana da farin ciki, idan ita bata baqan ta masa ba se taja
Asmaβu ta baqanta masa ta dalilin ta dama wai haka qarin auran yake ko kuka shine
beyi dace data gari ba??
Yana jin sanda ta turo qofar dakin ta shigo, be dago ba dan besan kuma meze mata ba
se jin saukar ihun kukanta yaji. Dagowa yayi ya kalleta tana zaune dirshen a qasa
tana kuka reras ga hawaye da majina nabin fuskarta. Baqin ciki to uwar me yamata
kuma ai shi ya kamata ma yayi kukan abubuwan datake qunsa masa ko.
Yaso ya shareta amma cikin jikinta da gargadin likita suka saka shi fasa yin haka
saboda hawan jini ne yai sanadin dan cikin ta ya mutu a wancan lokacin. Amirah nada
ciwon hauhawar jini a lokacin da mace take da ciki wanda gado tayi a gurin Addah
kuma likita ya tabbatar masa shine silar mutuwar jaririn data haifa dan ita ma
Addan haka takeyi.
Haihuwarta goma Amma Amira da Ummi ne kadai suka tsaya wasu tun a ciki suke mutuwa
wasu data haifesu.
Dukda haka seda ya barta tayi sannan cikin tsawa ya ce mata βwai kukan na uban
menene? Me nayi miki?β
Dan tsagaita kukan tayi tana jan dogayen ajiyar zuciya, seda yaja lokaci sannan ya
waiwayo ya kalleta tareda miqa masa hannunsa alamar tazo da sauri kuwa ta miqe ta
nufeshi gaba daya ta fada jikinsa seyai saurin dagota jin wani kamar qari qari
takeyi kai harda qaurin hayaqi ma yaji,. kofar toilet ya nuna mata yana cewa βmujeβ
ya tasata a gaba suka shiga.
Yana tsaye ya saka ta salle jikinta sau uku har gashin kanta seda ta wanke wanda
rashin gyara yake hanashi abin kirki dan itama Amirah tana da gashi sedai bekai na
Maβu ba. Seda ya tabbatar da ya duba duk wani lungu da saqon da datti ze buya yaga
ya fita sannan ya sata a gaba tayi brush, shidai ko iya haka aka barshi ai sakayyar
da Asmaβu tace se Allah ya mata gata nan yana gani.
Indai yana son kasancewa da ita ta kwanciyar hankali tofa se ya tasata tayi wanka a
gabansa shi wai dama haka matan suke ne Asmaβu ce daban a ciki be sani ba?
Tunda yake be tabajin wani wari daga jikinta ba koda kuwa ta kwana batayi wanka ba.
Maβu me tsafta ce komai nata a tsaftace take yinsa ita kuwa wannan har fargabar cin
abincinta yakeyi.
To yarinyar da yanzu zata fito daga wanka amma kajita tana tsami, ashe da daya ke
ganinta tsaf dan baya matsar tane daga nesa yake jiyo qanshin turare kawai.
Fitowa sukayi ya nuna mata mai da turare yace ta saka ta shirya ranta a dagule
shikenan sunyi asarar komai yanzu amma yata iya dole tayi yanda yake so. Daga nan
dai suka shige daga ciki.
Asmaβu
Jafar ne ya miqa mata wayar bayan da ya kashe
βHar kun gama maganar shine ka kashe baka bani baβ ta fada tana qoqarin sake
dialing dan tana so ta gaya masa zasu fita anjima se maganar Jafar din ta katseta
βShine ya kashe ai kaman Anty Amirah ce naji tana masa maganaβ. Kallon yaron tayi
kaman shine Bashir din wani abu na sukan zuciyarta, wato ya kashe wayar saboda
matar sa tana gurin ko?
βAi shikenanβ ta fada a fili kafin ta tashi ta shige dakinta. Kwanciya tayi ta rufe
idonta, tana so ta dena damuwa akan wasu abubuwan amma ta kasa.
Yanzu ne take fahimtar ba rashin tawakkali yake saka mata suyi ta tashin hankali in
an musu kishiya ba Aa abinda ake ci gaba da yi maka yau da kullum yafi zafin yin
Kishiyar dan shi na lokaci daya ne ya wuce amma banbancin da zaβa dawwama ana nuna
maka shi yake hasala zuciya har wasu su kasa shanyewa ayita tashin hankali dasu.m
https://chat.whatsapp.com/DpZYwM6HCjs7WDTCBPkyj0
ππππππππππππππππππππππ
WATA KISHIYAR π₯°πΉ
(ALKAHIRI CE KO SHARRI)
ππππππππππππππππππππππ
Na Maryamah_Mrs AM
(Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah)
Page 11
Wannan karan dai Amirah ta samu yanda take so dan Har ranar Monday da safe da
Bashir ze tafi basu sake samun sabani ba. Tayi iya qoqarinta wurin ganin ta
tsaftace ko ina kaman yanda yake so shima ya sake da ita sosai ya mori weekend
dinsa dukda dai a wannan bangare fa ya dade da cirewa Asmaβu hula dan kuwa tayi
zarra amma itama Amirah babu laifi yana samunta yanda yake so.
A bangaren girki ne dai tunda yazo be ci abincinta ba gidan Dada yake tafiya yaci
na rana na dare kuma ya siyo idan ze dawo saboda shi tun usuli dama baya cin
abincin me ciki gani yake wannan Amai da tofe tofen da sukeyi har cikin abincin
yana shiga.
Ko Maβu dakyar ya fara cin abincin ta lokacin da tana da cikin Aliyu shima seda ya
ware lokaci ya tsaya akan ta ya tabbatar da ingancin yanda takeyin sannan ya saki
zuciyarsa dukda ita bata fiya yin ciki me Amai ko tofe tofen miyau ba.
To balle wannan da kullum tana tafe da Gwangwani wani Saβin ma tana magana bakinta
cike da yawu yana zubowa seda yai dagaske ta dena yace ta ringa samun wani abun ci
tana sawa a bakin ze hana taruwar yawun sannan fa ya samu lafiya se kuma liqe liqen
chewing gum din da ta koma ci wani lokacin har kan kujera ko kan carpet yarda shi
takeyi ba abinda ya dame ta.
Bashir Tun ranar Asabar dinnan basu sake waya da Asmaβu ba, ita bata kira ba shima
be kirata ba tadai yi masa text kan zasu fita ran Saturday da Sunday kaman yanda
suka saba yace to tareda aika mata da kudi dukda bata tambayeshi ba.
Ranar lahadi da yamma ya dauki Amirah sukaje gidansu, A nan ya barta suka fita da
Amiru qaninsa daya zo daga Katsina a ranar can yake aiki yana zaune da iyalansa.
Bayan isha ta idar da Sallah tana zaune Dakin Fainusa qanwar Bashir ce da take
zawarci, Fainusan bata nan taje bikin qawarta Dada kuma tana dakin Baban su Bashir
taje bashi maganin sa na dare.
Bangaren shiru seda