Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Wata Kishiyar Complete Hausa Novel by Maryamah Mrs AM

Author :  Maryamah Mrs AM Category :  Drama

Chapter   49 / 80

144K to 147K   out of 238.5K words

suka shiga
mota ba seda Jafar yace masa

"Abbi mu tafi mana karmu makara" sannan ya shiga ya tafa motar, tuqi kawai yake
amma ikon Allah ke tafe dasu a haka ya samu ya sauke su ya wuce aikinsa da bashi da
tabbacin ze iya tsinana komai yau idan yaje

To Bashir tsautsayi da Asara Allah ya kiyaye 😂😂


Assalamualaikum Barkanmu da wannan lokacin AUNTY ZEE TAKU CE ,Ina uwar gida Amarya
da yanmata albishir gareku

BONONZA; BONONZA;BONONZA;

Nazo maku da SAHIHIN MAGANIN CIRE TUMBI CIKIN SATI DAYA ZAKI BAN LABARI,KINCI GAYU
ANA TAMBAYARKI YAUSHE ZAKI HAIHU TUMBI YA HANAKI ADO DA KWALLIYA SHA KURUMINKI NAZO
MAKI DA MAGANI CIKIN SATI DAYA ZAKI BAN LABARI ZAN DANDANA MAKU SHI AKAN RABIN
KUDINSHI DAGA NAN ZUWA SATI DAYA 7K DUK ROBA DAYA KI BIYA 3500 KI MALLAKI NAKI NAN
DA SATI DAYA ZAI KOMA 7K


MAGANIN BREAST WANDA ZAICIKO MAKI DA TUWON NONO DAN ALLAH KIJARABA ZAKIZO KINA
GODIYA DAN DUK WADDA TA GWADA SAITA DAWO MANYAN MATA SUKE GYARA KAMAR YANDA
KUKASANI 8K YAKE ZANKARA TALLATA MAKU SHI KI BIYA 4K KI MALLAKI NAKI
KI BIYA TA WANNAN ACCOUNT DIN KITURA MAN SHAIDAR BIYA
3968303018
ZAINAB SHU AIBU
FCMB
08162859027


🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟


WATA KISHIYAR 🥰👹
(ALKAHIRI CE KO SHARRI)
🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟

Na Maryamah Farouk
(Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah)


Wattpad @MaryamahMrsAm

Page 46

ASMA’U
Bacci nasha sosai abuna se Asuba na farka zuciyata wasai kamar wadda aka daukewa
wani nauyi daga kanta. Yanzu babu wani sauran abu a tsakanina da Bashir, aure dai
ya qare shima kuma yasan da hakan sedai muyi Addu’ar Allah yasa hakan shi yafi mana
Alkahiri gaba daya.

Muna cikin karyawa da yara da tun sassafe suka zo Abokin aikina Prince Yemi ya
korani, shaf na manta da yau zamuje gurin wasu mutane ne da muke nema su saka saka
hannun jari a kamfanin mu seda ya kirani yake tambayar na shirya tunda wucewa
zamuyi base mun biya ta office ba.

Mota ta jiya can na barota dan haka nace masa dan Allah ya biyo ya dauke ni kawai
tunda muna ta Area daya ba a wani dade ba kuwa se gashi yazo.

Haka kawai ranar naji ina son yin kwalliya, kodan yanzu na tabbatar da bani da wata
igiya akaina ne oho.
Straight gown na saka ta Atamfa blue datayi bala’in bin jikina amma bata kamani ba
nayi dauri na a gaban goshi na yafa shantili yellow daya dace da Atamfar na kawo
baqin takalmi hill da yar jaka itama baqa na saka, nayi kyau kwarai kamar wata yar
late twenties idan ka ganni bazaka ce na ajiye tarin yaran da suke gabana ba.

Tare muka fito da yaran dukka sanda Yemi yazo dan nasan duk inda Bashir yake yanzu
ya yi shirin fita shima. Dukda qasan zuciyata se naji kamar be dace yau ma ya sake
ganina tareda wani ba amma babu yanda zanyi haka na fito, Yemi yana da faran faran
da kuma tsokana, yana ganina nan da nan ya shiga tsokanata wai nayi kama da
sarauniya, ya karbi jakar hannuna harda bude mun qofar mota na shiga Yara natayi
mana dariyar ganin yanda abinda Yemin yakeyi, to su ina ruwansu basu dauki hakan da
wani abu ba ko dan wai ace ina da aure be kamata yayi mun haka ba.

Ina kallon yanda Bashir ya bimu da kallo da yanda ya zaburo mota yabi bayan mu
sedai Alah yasa tundaga gate din Estate muka rabu kowa ya kama hanyar sa. Muna tafe
muna tattauna abinda zamujeyi lokacin, seda muka sake biyawa ta gidan Olivia muka
dauketa tana ganina se wani washe baki takeyi ni kuwa daga gaisuwa ban sake kulata
ba muka ci gaba da tattaunawar mu da Yemi.

Mun isa Guest house din mutumin da zamu je yiwa tallan, tun daga Bakin qofa zaka
san me gurin ya ci ya tada kai. Harabar gidan kanta cike take da motoci na alfarma
kana ganinsu kasan ba hawan su akeyi ba kawai dai an siya an ajiye saboda an rasa
abinda za’ayi da kudin haka aka shigar damu wani palour me kama da reception muka
zauna muna rarraba Ido dan gaba dayan mu wasu qauyawa muka zama da ganin Aljannar
duniya.

Olivia kuwa da Patrick da muka tarar a can Selfie suka shiga dauka abinsu nida Yemi
ne wai mukan dan kame kan mu muna kallon gurin seda muka kwashe awa biyu cif muna
jira kafin aka yi mana iso gurin mutumin.

Wato wata hadaddiyar daula muka sake tararwa, palour ne qaton gaske na alfarma da
fadarsa ma bata bakine kaini fitulun da aka saka ma kadai sun ishe ni kallo wallahi
haka muka nemi kujeru muka zazzauna su kansu irin na yan gayun nan ne harda wani
guri da ake dannan wa su koma gado ga abin tausa kai masu kudi dai sunji dadi
abinsu.

Anan ma seda muka sake jiran kusan minti Ashirin har seda muka fara qosawa sannan
mamallakin gidan ya fito, Farine sosai dan tsurut dashi dagani ya hada jini da
fulani seka rantse dan aiki ne, badan hotonsa da yake a palour ba da bazan yarda
gurinsa muka zo ba.

Cikin girmamawa muka gaishe ni ina ta mamakin wai yanzu duk wannan uwar daular ta
wannan dan firit din mutumin ce, yana nan lange lange kamar baya cin abinci se kudi
kamar zasu kashe ni.

Nice me bayani, haka na dage na ringa watsa masa bayanai akan muhimmancin saka
hannun jarin da zeyi da kuma ribar da ze samu akan hakan, na gama bayani na tsaf
yana ji se gyada kai yake kamar qadangare yana kallona, seda na qare tas na zauna
Yemi ya dora da nasa se mutumin nan jin mu kawai yakeyi bece komai ba.

Gaba daya se jikin mu yayi sanyi, sosai kamfani yake da buqatarsa mun kuma saka rai
da samun nasa amma da alama bayanan namu basu shige shi ba tunda gashi ya mana
shiru, haka muka fara tattare takaddun mu kowa fuskarsa ta chanza yanayi, wayarsa
ya dauka yayi kira ko minti biyar ba’ayi ba sega wnai mutum ya shigo daganinsa kaga
Lawyer.

“Kuje dasu ayi ku kammala deal din a zuba ko nawa suka buqata babu matsala” mutumin
ya fada har sannan idonsa akaina, ai kamar zamu taka rawar murna haka muka shiga
zuba masa godiya yanda kasan wadanda yayiwa wata gagarumar kyauta ko da yake
kyautar ya mana dan Allah kadai yasan kudin da zamu zamu akan qulla yarjejeniyar
nan.

Muna shirin tafiya ya tsayar damu, PA dinsa ya kira se gashi shima da jaka ya ajiye
a gabansa, da ido ya nunawa PA ya budeta se gani mukayi yana zaro rafofin daloli ya
miqawa ko wannenmu daya sannan ya sake dauko complement card aka bani se kawai na
karba ina juyashi a hannuna dan basan me zanyi dashi haka dai mukayi sallama muka
tafi tareda Lawyer muka wuce kamfani.

Ranar cikin farin ciki na dawo gida jakata cike da daloli, a hanya na tsaya wani
shopping mall na siyawa yara kaya kowa set biyu designers masu kyau nima se gani
ina lissafi da dollar irin na yan gayu, seda na gama diban kayan idona ya sauka
akan wasu singlet da boxers na maza, har na kai hannu na dakata zuciyata na
tambayata

“Wa zaki daukarwa?”
“Allah sarki Baban Ali, da yanzu harda kai za’aci kudin nan” na fada a fili ina
wucewa bangaren turaruka na dibi wanda nake amfani dasu sannan na quce gurin
takalma na daukarwa Amnah wani me shegen kyau da zata hada da gown din prom din su
da za’ayi wannan Juma’ar me zuwa.

Sosai na kashe kudi, niqi niqi na wuce gida da kaya ina zuwa na tarar da yaran duka
suna nan muka shiga dasu ciki, plates din Abinci dana gani ya sakani cikin sigar
wasa nace

“Wai ku baku iya zama a gidan mu sedai kuzo nan ku cinye mana abinci kullum toh
gaskiya ya isheku haka kun mayar da Yah Amnah kuku meye amfanin Antyn ku da bazata
girka muku ba”.

“Tab ai wallahi Mami bata da amfani kuwa, ni tausayin Abbi ma nakeyi kar ulcer ta
kamashi dan rabon danaga yaci abinci a gidan nan tun kina nan fa” Jafar ya fada
yana zaro kayan cikin ledar, ban tankashi ba, na bisu da kallo yanda suka rude suna
murna kowa yana daga kayan sa se kawai na shige dakina na barsu.

A gefen gado na zauna ina tunanin meyasa Amirah bata girki? Su yara basu da matsala
tunda gashi suna ci a nan amma Bashir fa me yake ci shi da sam bashida jumurin
yunwa
“Ina ruwanki idan ma ruwa yake sha” zuciyata ta rayamun, sena miqe ina qoqarin cire
rigata wayata dake cikin jaka ta hau qara.

Cirota nayi na duba, Number ce wata irin special Number kamar me ita ne ya zabi
abarsa dakansa na dubata dakyau batayi mun kama da wadda na sani ba dan haka na
mayar da wayar na ajiye dan ban fita daukar wayar da ban sani ba.

Message ne ya shigo bayan data katse an rubuta “ki daga wayar, wanda kukayi
yarjejeniyar kasuwanci ne” se nayi saurin nemo Number zan kira dan a zatona
Barrister dazu ne a raina ina Allah yasa ba wata matsala bace ta faru kuma dan har
an karbi account Number mu a kamfani za’a saka mana kudin aikin mu na kuma gama
lissafin kudin sabuwar motata zan cika dasu yanzu idan aka fasa ai mun ga bonu.

Kiran daya sake shigowa ne yasa na dakata, na daga tareda yin sallama.
Seda akaja aji kafin wanda ya kira yayi magana cikin harshen hausa yace
“Meyasa baki kira ba tun bayan da muka baki kati dazu”.

Wayar na cire daga kunnena na sake dubawa, number ce idan kuma banyi qarya ba kamar
wannan dan tsamurmurin mutumin da mukaje gurinsa dazu sena mayar da wayar kunnena,
cikin dari dari nace

“Bangane wa yake magana ba”.

“Oh babu laifi, sunana Ambassador Mutallab Ali” ya fada

Seda na zauna akan gadona na qara riqe wayar dakyau kafin nace

“Ranka ya dade barka da dare, ina fatan dai ba wata matsala aka samu da takaddun da
muka bayar ba?”

“Aa, idan da harkar data shafi aikice ko kudi wasu ne daban suke gudanar mun da
ita, wannan kuwa abune daya shafe ni ya shafi rayuwata dan haka ni da kaina zanyi
shi. Ba tareda bata lokaci ba tun zuwan da kukayi dazu na ganki kuma kinyi mun a
matsayin matar aure, idan kin aminci ina so na cike mata ta hudu dake amma dukka
matana ba tare suke ba, kowaccen su qasar da take zama ta banbanta data yar uwarta
dan haka kema zaki zbai inda kike so ki zauna ne ni bani da damuwa da hakan”.

“Ikon Allah se kallo” na fada a zuciyata, a fili kuma sena samu kaina da cewa
“Ranka ya dade kayi haquri amma ni matar aurece”.

“Asma’u kenan, baki da aure domin suffarki ta nuna kamala. Babu yanda za’ayi ki
fito da irin shigarki ta yau alhalin kina da aure dukda hakan ba wani abu bane ga
amma na tabbatar da ko shi mijinki baze taba bari ki saka kayan da zasu bayyanar da
kyanki haka ki tafi qulla alaqar kasuwanci da wasu maza ba ko da yake bansan irin
mijin da kike aure ba”.

Mamaki ne ya kamani kwarai, ya akayi ya san sunana sannan har ana iya gane macen da
bata da aure daman tunda dai ni banyi kala da budurwa ba bare yace sannan daga kira
ka fara zayyana mun wani zancen aure harda wasu matansa uku ni Asma’u ce zan fita
daga gidan me daya na fada wa uku Allah ya mun tsari.

Kai duk ba wannan ba Allah na tuba ina ni ina wannan mutum haka firit kamar ruwan
aski? Ai wallahi ko qaruna ne shi qarewar kudi yanzu dai in rabu da Namiji Kamar
Bashir naje na auri wannan busashshen da na kasa tantance tsufane ya figeshi haka
ko kuwa abinci ne baya ci kai qilama sickler ne kaga kuwa Bashir se yayi mun dariya
dakyau.

“Kinyi shiru Asma’u baki ce komai ba” ya katse mun shirun. Dabara ce ta fado mun ta
yanda zamu rabu lafiya tunda dai shi wannan ya wuce mutumin da zance zan wulaqanta
ko na kora dan haka nace masa

“Tabbas ranka ya dade mun rabu da mijina amma gaba daya be wuce sati biyu da
faruwar hakan bama kaga ban gama iddah ba yanzu baze yuwu na saurari wani namiji
ba”.

“Hakane, toh babu damuwa zan jira dan na yaba kuma rabona ce ke, ki turamun da
account Number dinki yanzu za’a saka miki saqo”

“Babu komai na gode Rabka ya dade na dazu daka bamu ma ya isa”

“Ni nayi niyya idan kuma baki turo ba zanyi waya har kamfanin naku yanzu su turamun
daga can” ya sake fada, gaba daya maganar tasa ta gundureni, dan haka da sauri nace

“Toh shikenan zan tura maka yanzu, Nagode Allah ya qara arziqi” qit na kashe wayar
ban ajiyeta ba seda na dannan masa block, na dakko katin daya bani nabi duk
numbobin jiki nayi saving dan karma ya kira da wata Number na daga ban san shi
bane.

“Haka kawai toni ko auran zanyi ai ba irin ka zan aura ba” na ringa mita ni kadai
na shige bayi.

Ina sallar Isha su Abdallah m shigo da gudu yacemun wai nayi baquwa, seda na
sallame kafin na fita wajen da hijabin jikina ina mamakin wacece wannan zata zo
mana da dare haka.

Turus nayi ganin Amirah dake tsaye farar fuskar nan tayi jajir kamar ma mari tasha.
Cikeda fitsara ta waiwayo tana cewa
“Wallahi kijawa Yaranki kunne dan ni ba jakar su bace da zan ringa dafa abinci su
tsallake au qi ci kuka ubansu yazo yana mun fada kuma wallahi duk abinda aka mun
akan su zan rama ehe”.

“Yanzu qara kika kawo ko jan kunne kika zo kiyi mun? Wai ma bana gaya miki karki
sake shigowa gidan nan ba? Ina ruwana da shirgin ku mena hada dake da zaki shigomun
gida kina fadamun magana.

Naga alama kin kwana biyu jikin ki be fada miki ba toh kiyi a hankali idan ba haka
ba kuwa sena ladabtar dake tunda naga ke baki da hankali ba kuma ki da tunani,
abinci kuwa a gidan ubansu suke ko suci ko kar suci dole ki dafa ki ajeye musu idan
kuma kinqi kinsan sauran base na gaya miki ba, wuce ki fita tun ban lakada miki na
jaki ba anan” na qarasa ina nuna mata qofa, nazata zata sake magana se naga ta juya
tana qunquni ta fita a fili na fuskar ta

“Mara kunyar banza, ai da kin tsaya na koya miki hankali. Ku kuka (na juya kan
yaran) daga yau ku ringa tsayawa a gidan ku kuna cin abinci idan baqu qoshi ba se
kuzo nan ku qara kunji ko”.

“Wallahi Mami bata iya abinci ba, jiya fa data saka wani kifi a spaghetti har yanzu
ina jin qayarsa a wuyana qarshe fa a bola ta juye abincin kowa yaqi ci” Jafar ya
fada kafin nayi magana Faridah tayi caraf tace

“Waifa doyar da bamu ci da safe ba ta dumamawa Abbi shine ya ringa mata masifa,
yanzu ma yana daki a kwance Kamar Bashida lafiya ina ga kuma yunwa yake ji, Mami ki
bamu abinci mu kai masa dan Allah”.

Tsayawa nayi ina kallonta, dagaske Bashir bashida lafiya to me ya same shi? Na san
dai yunwa tana iya kwantar dashi dan sam bashida jimirinta toh amma ni ina ruwana
meye nawa a ciki shida ya dakko yar gwal ai seta dafa ta bashi.

Da zasu tafi Faridah da shegen naci seda ta dibar wa Bashir Friedrice da pepper
chicken din da Amna tayi ga hadin kosulo abin dai ba’a magana na qara musu da zobo
roba biyu sadaka nace ta kai masa.

BASHIR

Gaba daya haka ya wuni a office ya rasa me yaje masa dadi, ga damuwar rabuwarsa da
Ma’u da se yanzu abin ya fara dukansa daya tabbatar da ta kufce masa se yayi da
mugun gaske kafin ta sake dawowa hannunsa.

Ya rasa wa ze gayawa damuwarsa, a wannan karon be karbi shawar Bala ba gani yake
kamar bazata fiddashi ba, amma wani lokacin idan ya tuna irin son da Ma’u takeyi
masa se yaga kamar duk buyagin iska kawai takeyi na dan lokaci zata sakko su koma
zaman su.

Wai ma shi me yayi mata ne? A iya saninsa laifi ta masa ta qi bin unarninsa kuskure
daya da yayi shine daukar matakin saki a cikin fushi kuma har biyu, daya sani hutu
ya bata na lokaci ya fita sabgrta har se ita da kanta ta dawo ta nemi shiri ta kuma
yarda da sharadin daya bata kafin su daidaita amma yanzu ya lalata komai, ya bi
rudin shedan ya rabu da Ma’unsa.

Ita wadda Shedab din yayi masa kururuwa akanta gashi nan ya dakko ta idan bada
gasha shi babu abinda take yi ko iya horon yunwar da take masa aka barsu na shekara
daya yasan dakyar idan bazatayi ajalinsa ba wai shi wannan wane irin bala’ine yake
tun karar rayuwarsa.

Wayarsa ya dauka ya shiga neman Number Amiru qaninsa da tun ranar da zancen sakin
Ma’u yaje Gombe ya kirashi dan yaji menene gaskiyar zancen ya kuma tabbatar masa da
anyi daga ranar basu sake magana ba.

Ya kirashi sau ba Adadi amma Amirun baya dagawa daga baya ma blocking dinsa yayi,
haka Naziru ma baya amsa wayarsa to yan uwansa ma kenan kuma shi bashi da sauran
wani shaqiqij Abokin da ze tattauna wannan matsalar in banda Balan se Abubakar da
ko giyar wake yasha be isa ya tun kare shi a yanzu ba.

Abdulkarimu ne ya fado masa a rai, ba bata lokaci ya danna masa kira kuwa akayi
sa’a ta shiga seda ta kusan tsinkewa kafin ya daga wayar

“Alhaji Bashir yaushe rabon da ka nemeni tunda giwa tayi lafiya ka samu kan Madam
shikenan ka watsar dani” Abdulkarim ya fada bayan da suka gaisa. Seda Bashir yaja
numfashi kafin yace

“Abdulkarim ina cikin Bala’i na rasa yanda zanyi wallahi ka taimaka mun”

“Allah yayi mana maganin abinda ya damemu, lafiya dai Bashir meya sameka haka kake
dangana kanka da Bala’i?”

“Abdulkarim hau ce ta hauni, nabi dokin zuciya na saki Ma’u gashi yanzu harta gama
iddah ban mayar da ita ba na rasa inda zan kama ji nakeyi kamar zan haukace, yanzu
har ta fara kula wasu Mazan sau biyu ina ganin ta a motar Maza Abdul” ya qarasa
maganar kamar ze fashe da kuka saboda yanda yakejin zafi a duk sanda ya tuna ganin
da yayiwa Ma’u na jiya dana yau din.
Salallami Abdulkarim ya ringayi yana cewa
“Ka saki Ma’u Bashir wace irin hau ce kai kuwa take binka haka ka rasa matar da
zaka saka a rayuwa se Asma’u, Asma’u fa Bashir toh wallahi babu ruwana, abu daya
zan iya maka inyi maka Addu’ar Allah ya taqaita maka wahala na kuam roqeshi karya
maido maka da Asma’u rayuwarka dan baka san darajarta ba”

“Idan Allahn naka ne seka roqeshi karya dawo mun da ita din, na kiraka ka bani
mafita shine zaka zageni kayi mun fatan tsiya ko? Daman nasan ba qaunar zama na da
ita kake yiba, to dakai da duk sauran masu jin dadin abinda ya faru kuna

49 / 80