Author : Maryamah Mrs AM Category : Drama
ta shafe da hadaddun turarukanta da ita
kadai tasan wadanda take mixing da duk bala’in kwakwkwafin mutum baze taba cankar
wane turare bane.
Abaya ta fitar Baqa tareda mayafinta ta ajiye a gefe saboda yaranta maza ne, dukda
qanana ne tana takatsantsan da irin shigar da zata fita gabansu da ita. Qugin
motarsa data jiyo ya sakata saurin dora abayar ta yafa qaramin veil dinta akanta
tareda zura slippers din ta ta nufi waje dan ta taro su.
Bashir
Fitowarsa daga mota yayi kyakykyawan gani, Ma’un sa ce kamar wata yar budurwar
Balarabiya, tundaga nesa ya fara shaqar qamshin da takeyi wanda be taba jin sa a
jikin wata mace ba bayan ita. Tamasa kyau yanda tayi rolling mayafin ya zagaye
kyakykyawar fuskarta tareda bayyar da gaban gashinta daya ke nan luf a kwance ya
qara qawata kwalliyar tata.
kallonta yake har besan sanda wayar hannunsa ta subuceba. Yana jin yanda yaran suke
zuzuta kyan da tayi amma nasa bakin kamar wanda aka sakawa qaton kwado a ka kulle
ya kasa koda budeshi se idanu daya zuba mata kawai.
Qarasawa gaban sa tayi ta durqusa tareda dakko masa wayar da ya yar bata miqa masa
ba se jinta yayi gaba daya ta rungumoshi, saitin kunnensa ta furta “Welcome home SH
(sweet heart)”. Kamar wanda ta tsoma a ruwan qanqara haka ya daskare a gurin yana
jin kamar ya shide saboda muryarta da kuma numfashinta daya sauka a cikin kunnensa.
Hannunsa ta kama ta zura masa wayar kafin ta juya tabarshi da shaqar qamshinta,
batayi ko taku biyar ba taji an janyota ta baya yai mata wata kyakykyawar runguma
tareda sauke mata kiss a gefen wuyanta da mayafi be ida rufewa ba.
Zaro ido tayi tana riqe hannunsa, “Baban Ali a waje fa muke” ta fada ganin gogan na
neman kauce hanya 😂 se a sannan ya farga dan shifa a lokacin ita kadai yake gani se
kuwa yaja hannunta qii suka shige cikin gidan dan tuni yaran suka kama gaban su.
Mantawa yayi da batun wata yunwa da gajiya daya kwaso suka shige dakinsa kai
tsaye , ai be ida birkicewa ba seda yai arba da ainihin kwalliyar Ma’unsa tuni
labari ya chanza .
Basu fito ba se qarfe goman dare, Babu kowa a palour alamar yaran harsun kwanta.
Ma’u da duk tayi laushi ta nemi kujera ta zauna Bashir kuwa Dining ya wuce dan se
yanzu yake jinsa kamar ze fadi saboda yunwa. Ya manta sam rabonsa da abinci tun na
safe. A Babban plate ya juyo dukka abincin ya sakko da shi inda take ya ajiye
sannan ya koma ya dakko kwanon Fish din da Amna ta gasa.
Yana ci yana bata a baki har suka cinye se wani tarairayarta yakeyi kamar kwai,
yanda yake rawar jiki da ita se yake tuna mata da lokutan baya a sanda yana Bashir
din Ma’u kafin zaman majalisa da sababbin abokai ya sauya mata shi zuwa wani mutum
na daban. Tana tuna irin gata da tarairayar daya ringa nuna mata a shekarar farko
ta aurensu. A lokacin ya kan sakata taji tamkar tafi kowacce mace dacen miji duk
kuwa da bata samu yanda take so ta bangaren kayan more rayuwa ba amma soyayya da
tattalinta da ya ringayi yafi mata komai dan dama ita ai dan soyayya ta aure shi
bawai kudi ba.
Suna gama cin abincin dakin suka koma, ta gaji tibis dan haka ta haye gado ta
kwanta yana matsa mata jikinta. Wayarsa ce tayi qara, a tare suka duba sunan Amira
da ta gani yana yawo yasa ta dauke kanta. Satar kallonta yayi karaf kuwa suka hada
ido, haka kawai yaji wani abu kamar nauyin Asma’u ya kamashi cikin son basar wa ya
dauke idonsa ba tareda ya amsa wayar ba.
Kiran da ya yanke wani ya sake shigowa ya sakata cewa “ka daga mana ba kiranka
akeyi ba” seya dauki wayar, be zauna anan ba ya fita falo. Da kallo ta bishi tana
qoqarin hana shedan yin tasiri akanta “Itama matarsa ce matsayinmu daya da ita” ta
fadawa kanta sejin hawaye kawai tayi suna bin fuskarta.
Bata san randa zata dena jin zafin yankan bayan da suka mata ba. Da ace wata can
Bashir ya aura koda cikin dangin nasa ne damuwarta bazata kai haka ba amma fa
Amirah, Amirah data dauka tamkar Amna. Yarinyar da ta gama sanin sirrinta ciki da
waje ita ya auro mata a matsayin kishiya se kawai ta rushe da kukan takaicin da duk
sanda ta tuna yanda auran Bashir ya kasance seta yi shi.
Babu wanda ze gane zafin da takeji se wadda aka kwatantawa irin abinda akai mata,
se yanzu take ganin dalilin da yake saka wasu matan aikata abubuwa da dama akan
kishiya ko ma mijin kansa dan wallahi in akayi maka wani abun in ba me qarfin imani
da tawallaki ba se kaji kamar bazaka yarda ba se ka dauki mataki. Har bacci ya
dauketa Bashir be shigo ba se Asuba ta farka ta ganshi a bayanta.
Ko a fuska bata nuna masa komai tayi sallah a dakin sannan ta fita gurin yara dan
jiya basu samu ko yin magana ba. Seda ta hada musu abinci suka shirya tareda zama
suka fara breakfast sannan ta koma dakin ganin Baban Ali be fito ba.
A tsaye ta ganshi yana zuge jakar da yake tafiya da ita Gombe, dauke kanta tayi
kamar bata gani ba tana cewa”Sun shirya fa gasu can sun fara cin abinci basu jiraka
ba” tayi gaba da niyyar shigewa toilet dan bata so yai mata maganar tafiyar sa
sedai tun kafin ta shiga ta jiyo shi yana cewa
“Ke zaki dauko su daga school yau zan wuce Gombe ne daga office bazan dawo ta nan
ba” ba tareda ta juyo ba tace masa “Allah ya tsare ka gaishe su” tai shigewarta
abinta.
Bin kofar yayi da kallo kafin jiki a sanyaye ya dauki Laptop bag dinsa da jakar
kayan ya fita, seda ya kaisu mota sannan ya dawo shima ya hau Dining din amma se ya
kasa taba komai.
Shiru yayi yana kallon yaran suna cin abincinsu har suka gama Ahmad ya kalleshi
yace “Abbi ina Mami zamu tafi”
“Kuje mu tafi wanka take yi” ya fada yana miqewa. Har sun fita ya juyo zuwa cikin
gidan, Bayaso su rabu da bacin rai kodan albarkacin farin cikin data bashi a kwana
biyun nan. Harya kama Handle din dakin shegiyar zuciyar da take masa famfo ta zugo
shi “to me kayi da zaka ke bata haquri ma?” Zuciyar ta raya masa, Seya saki qofar
ya juya kawai.
Asma’u da ke zaune tana jiran tsammanin zuwan Bashir ya rarrasheta, ajiyar zuciya
ta sauke jin an taba qofa harda qara narke fuska tana ayyana abinda zatayi ta
gigitashi se taji shiru, the next thing ko se jin tashin motarsa tayi ta yaye
window da sauri har sun wuce se qurar daya tayar, baki bude take kallon motar harya
qule mata, “Hmmm” ta sauke numfashi kawai ta shiga shafa mai, bataso ta tuna abun
ma bare ranta ya baci ita dai addu’arta idan Bashir nada rabon ganewa to Allah ya
maido shi kan hanya.
Gombe gidan Addah
A daren ranar da Bashir ya turo musu da kudi tayi ta kiran Number da Malam Wizy ya
basu bata samu ba, bata haqura ba tayita gwada Number har washe gari amma shiru
gashi ta kira wayar Hajia Balaraba ma a kashe.
Jikinta dabe gama warwarewa bane ya hanata fita ta bari akan zuwa talata tasan ta
warke seta je gidan Hajia Balaraban ta dai ci gaba da kiran wayar tasa ko zata samu
cikin Sa’a kuwa ranar Laraba da safe tana kira ta shiga.
Ta gama ringing ba’a dauka ba seda ta sake kira aka daga. Muryar wata tsohuwa taji
daga ji taji duniya har ta gaji tana cewa “kai ku duba nan waye ya bugo, Wizy da
qaninsa Iliya suna zaune a dakin Kakarsu daidai lokacin sunzo gaishe ta, miqa wa
Wizy wayar tsohuwa tayi tana sake cewa ya duba ga gani.
Sallama Adda ta sakeyi, fes Wizy ya gane muryarta se yai saurin datse kiran ya miqe
yana cewa Kaka yana zuwa.
Can wani lungu ya buya yayi recharging wayar kaka ya dannanwa Adda kira.
“Salamu alaikum malam ina wuni” ta fada cike da zumudi
“Lafiya lau dawa nake magana” ya tambaya irin be gane ta din nan ba
“Nice Malam wadda Sani ya kawo mu (sunan da Me Napep ya gaya musu kenan)
“To to hajia ya gida naji ki shiru da alama buqata ta fara biya kenan”
“Wallahi malam na danyi rashin lafiya ne kwana biyu kuma na kikkiraka ma wayar a
kashe” Addah ta fada
“Eh wallahi kwana biyu kam na kashe waya dan na shiga halwa ne inata ayyukan ku
dafatan ana ganin haske ko”
“Sosai kuwa Malam ya fara samuwa”
“To haka ake so yanzu to ya akayi?” Ya sake tambayarta.
“Dama na samu wasu kudin ne nace bari na turo a ci gaba da aikin mu sameshi gaba
daya”
“Kin kyauta kuwa ai ina tabbatar miki idan aiki ya kammala hajia nasan indai kin
riqe amana har ni dinnan se kin mun kyautar kujerar hajji” Wizy ya fada yana
tsallen murna jin wata banzar zata fado.
“Insha Allahu kuwa malam yanzu dai ka bada akawun a tura kudin nan ayi a ci gaba”
“Ba matsala da mun aje waya zan turo miki” sukayi sallama yana qara karanta mata
qanzon kurege.
Harya fara typing account details dinsa wani tunani ya kawo kansa, idan ta tashi fa
za’a Iya tracing dinsa ta banki, se yai saurin gogewa ya danna mata kira. Tana
dagawa yace
“Hajia nace kudinnan ki cire su, akwai yaro da na aika qauye ya siyo ragunan wasu
aiki bari naji in be tafi ba se ya biyo ya karba kawai ya wuce” da haka sukayi
sallama.
Minti kadan ya sake kiranta yace ze turo yaro, nan ta zayyana masa Address ashe ma
basu da nisa ya ma gane gidan daya daga cikin yaran mijinta abokinsa ne. Isma’il me
Napep ya dannawa waya suka tafi tareda wani qaninsa me suna Nasiru da yai shigar me
zuwa kasuwar qauye. Ko kafin su Iso Adda ta aika Ummi an ciro mata 80k kudin rago
biyu yaro na zuwa ya shiga har palour ta ta bashi kudi ya jefa a buhu ya fice.
Gaba suka qara aka tsaya kowa aka bashi rabonsa ya zuba a Aljihu Malam Wizy ya zare
sim din Kaka ya ballashi biyu ya zubar yana cewa “mun tatseta ya isa haka” suka
sheqe da dariya.
To Addah Allah ya maida Alkahiri ya kiyaye na gaba
🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟
WATA KISHIYAR 🥰👹
(Alkhairi CE KO SHARRI)
🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟🌟
Na Maryamah_Mrs AM (Marubuciyar Rubutacciyar qaddarah)
Page 9
Gombe
Ana kiran magriba Bashir ya shiga gidan sa na Gombe, tun qarfe hudu da rabi suka
sauka tazarar tafiyar daga Akko zuwa Gombe ta kaishi Magriba.
A qofar gidansa Me Taxi din daya dauko shata daga Airport ya sauke shi ya fito
dakyar yana jan qafa ga yunwa ga gajia tiqis saboda yau yasha aiki a office ga kuma
tafiya dukda a jirgine.
Yana qoqarin bude get din a ransa yana ayya Allah yasa ma ta dawo gidan dan yana
daga ciki rashin sanin ya kamatan Amirah a duk sanda zezo hankalin ta be taba gaya
mata tazo ta gyara gida tayi girki dan tarbarsa ba se in ya tuna mata. Dama can
tun tana yarinya yasan qazama ce ta gaske daga baya ne zama da Asma’u ya sa tadan
chanza tareda koyar wasu abubuwan amma dukda haka tsaftar biri gareta. Zata yi
wanka ta gyara jiki amma fa duk dattin guri haka zatayi zamanta.
Yana jefa qafa busassun ganyayen bishiyar da suka zube ne suka masa Maraba.
Compound din ya hada uwar qura dama ga shi an fara Sanyi da Hazo a garin. Takaici
ya qume shi danya tabbata bata dawo ba kenan.
Bangaren Asma’u ya nufa dan yasan yace zeje dakinsa na part din Amiran ma ransa ne
ze qara baci. Seda ya kunna wutar bangaren sannan ya bude palour ya shiga da
Bismillah. Komai na nan a kintse yanda ta barshi, cike da gajiya yake daga
qafafunsa ya haye benen da ze kaishi dakinsa. Nan dinma fes dashi ya saka hannu ya
yaye ledar da take shimfidawa akan Katifa bayan ta cire bedsheets din saboda qura
sannan ya zube kayan daya shigo dasu.
Toilet ya fada ya dan daurayeshi yayi wanka tareda dauro Alwala ya fito. Harya idar
da sallah beji alamar waniya shigo gidan ba ransa ya qara baci amma seya danne
kawai ya janyo wayarsa ya kira Qaninsa Naziru ya kawo masa motarsa dayake amfani da
ita anan. Bayan ya kashe se yayi dialing number Asma’u, deep down yanajin kaman
dazu da safe be kyauta mata ba.
Har wayar ta qaraci ringing dinta bata daga ba, ya sake kira nan ma shiru se ya
maida akalar kiran zuwa ga Amirah dan yaga alamar hankalinta ragaggene. Ai a qalla
yaci ta kira taji yazo ko kuwa tunda tasan da zuwan nasa yau amma still itama bata
dauki wayar ba.
Ajiye wayar yayi a kan gado cikinsa na cigaba da qugin yunwa shikadai se sakin
qwafa yakeyi da ayyana hukuncin da ze dauka akan Amirah. Kusan minti 20 Naziru ya
kirashi ya iso, se ya dauki wallet dinsa da keys ya saka a Aljihu ya fita. Naziru
na ganin sa ya fito daga motar da niyyar bude get ya shigar masa da ita Bashir din
ya dakatar dashi da cewa
“Muje ka kaini naci abinci yunwa nake ji”.
Suna tafe babu me cewa qala kowa da kalar tunanin da yakeyi a zuciyarsa, Naziru ne
ya datse shirun da tambayar Yayan nasa Su Aliyu yace suna lafiya. Wani restaurant
ya kaishi be fita daga motar ba ya bawa Naziru ATM yace ya yiwo musu take away ya
karba ya tafi a ransa yana mamakin meya faru Amira batayi masa girki ba, tunawa
yayi da tana da ciki se yai zaton ko shi ya hanata girkin amma dai ko yaya ne mutum
ya taho gari ya gari har Lagos ai ko Indomie ta daure ta girka masa shidai ya siyo
abincin ya fito.
Bashir kuwa bayan Fitar Naziru wayarsa ya zaro ya duba ko wata daga cikinsu ta biyo
missed call dinsa amma yaga wayam. Na Ma’u be dame shi sosai ba dan yafi gasgata
bata kusa da wayar ya santa sarai ko fada suke bata qin daukar wayar sa sedai ta
daga tayi shiru amma ita wannan yarinyar fa?
In tana da hankali ai ita ya kamata ta kirashi ko amma gashi haryanzu ana neman 8
na dare bata kira ba. Har qofar gida Naziru ya kaishi ya shiga da Motar kafin ya
fito yai masa sallama da niyar wucewa ya tsaidashi yace su shiga ciki.
Har saman ya kaishi yace ya gyara masa dakin dan baze iya kwanciya a ciki haka ba
Bashir akwai tsafta koya datti yake a guri baya so abinda yake qara Masa son Ma’u
kenan tsabtar ta ciki da waje ya jinjija mata ta wannan fannin sosai.
Har palour seda Naziru ya gyara tsaf ya goge ransa fal mamaki dan ya tabbatar yanzu
Amirah bata gida to ko bata san ya zo bane? Shidai ya gama tattara komai ya tsaya
jiran yayan nasa daya shiga daki ya fito. Kudi ya bashi yace ya hau mota tareda ce
masa idan yaje gida ya cewa Dada seda safe ze shigo ya bishi ya kulle qofar ya
dawo.
Yana shiga palour Asma’u ta kirashi se ya qarasa kan kujera ya zauna dakyau yana
amsa wayar.
Asma’u.
Lokacin da Bashir ya kirata wayar ta na hannunta tana chatting da Umaima yayarta ce
da suke Uba daya amma ita take bi a cikin gidansu. Akwai shaquwa sosai tsakaninsu
dan kusan bata da Aminiya ma sama da ita. Hira suke yi tana gaya mata tafiyar
Bashir din Gombe da yanda suka rabu.
“Ma’u kenan nidai bazan gaji da ce miki ki qara haquri akan wanda kikeyi ba, zuwa
yanzu inda sabo ma ai yaci ki saba da wannan mood swings din nasa, ki watsar
lamarin sa idan yayi dariya kiyi in ya daure kema haka. Ki kuma ci gaba da addu’a
idan ma wani ne yake shiga tsakaninki dashi Allah ya miki maganin sa” cewar Umaima.
Tana cikin yi mata reply kiransa ya shigo tacewa Umaiman “kinga ma yana kira”
“Ki daga kiji me zece”
“Barshi kawai bazan daga ba se zuwa anjima sun kwanta zan kirashi” cewar Ma’u.
Dariya Umaima tayi tana cewa
“Haba ai kuma ba zaki biye mata ku taru ku zama daya ba tunda ke kinsan abinda ya
kamata, ki daga kuma karki nuna masa wani bacin rai ko wani abu dukda nasan ki ma
Ma’ulle akwai sanin ya kamata ai” tayi maganar cikin sigar tsokana. Da “toh” Asma’u
ta amsa ta ta kashe Datan bawai dan zata amsa kiran ba dan ta qudurce a ranta seta
koyawa yarinyar nan hankali taji idan abinda take mata da dadi yanda take kiransa
duk sanda taga dama kamar ita kadai take dashi.
Yanzu nema ta rage ada bata tashi kiransa wataran se sha biyun dare sun kwanta
bacci, farkon wannan cikin nata ma lokacin tana laulayi akwai ranar da suna tsaka
da soyayyarsu wurin 2 na dare ta kirashi wai ta kasa bacci se Amai take shine ta
kira shima ta tashe shi.
Baqin ciki kamar Asma’u ta fasa ihu har bata san sanda ta fizge wayar ta tuttura
mata ashar ba kuma saboda rashin adalci irin na Bashir qarshe ita yaji haushi akan
me zata zageta bata ga cewa lalura ce ta sakata kiransa ba ranar kwana tayi tana
kukan baqin ciki ai kuwa seda tayi masa yajin kusan wata dakyar ya shawo kanta ta
sakko.
Sedata mula dan kanta ta gama komai sannan ta shiga daki ta kirashi, a yanda ta
lissafa yanzu dole suna zaune ne suna hutawa dan haka tayi niyyar jan hirar har se
illa masha Allahu harda loda kati a wayarta saboda tsaro (Sorry Ma’u wrong timing
😂😂😂😂).
Lafewa ta sakeyi a cikin gado sanda ya amsa wayar ta gaishe shi da tambayar ya
hanya ya amsa mata da lafiya lau.
Rai rai ta saki jiki suka ringa hirar da sun manta rabon da suyi irinta, shi
mamakin yanda ta sake kamar ba abinda ya faru ita mamakin yanda yake amsata sosai
kamar ba Bashir ba yau ba Miskilancin nan babu baqin rai. Yanda take masa shagwaba
kamar wata sweet sixteen yana biyeta gaba daya tagama narkar dashi a zaune, Hira
tayi dadi tama manta da batun wai dan ta musgunawa kishiya yasa ta kirashi sema
kwantowa kansu ruwa da sukayi gaba daya ta rudashi da salon da take masa magana
shima ya rudata da masa salon, dakyar suka rabu a wayar lokacin 12 harta gota shima
Asma’u ce ta kashe ganin yana neman sakata a uku to ai shi ga matar sa nan itafa
sedai ta kama pillow batasan Gogan har ya fita shiga tashin hankali ba.
Haka ta kwanta tana juyi Kafin bacci ya saceta ranta fes koba komai dai Ta qunsawa
Amirah.
Bashir
Yana zaune bayan sun gama wayar se zufa yake sharewa duk da sanyin Ac daya karade
palour dan gaba daya Asma’u ta warware masa notin kai. Dakyar ya miqe ya nufi
fridge din daya kunna tun dazu ya dakko ruwan sanyi ya kwankwada yana sauke ajiyar
zuciya Haushin Amirah na sake ninkuwa a Zuciyarsa har ya gama wayar nan