Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Wata Kishiyar Complete Hausa Novel by Maryamah Mrs AM

Author :  Maryamah Mrs AM Category :  Drama

Chapter   77 / 80

228K to 231K   out of 238.5K words

gani na ba sedai in har ke da kanki kika gayyato
ni” ya sake fada.

“Yanzu daman tuntuni kawai abinda kake jira na fada kenan? Duk magiyar dana ringa
maka ba abinda nake nufi ba kenan?” Na fada

“Baki fito kince Yusuf kazo ba, amma Yanzu da kika fada zaki ganni, kuma duk ranar
dana zo ranar zaki tare ki tabbata Ango nake babu maganar daga qafa sena kwashe
gara yanda....”

“Kai dai baka da kunya wallahi” nayi saurin katse shi jin yana neman ya saki layi
kuma.

“Ai bazaki tabbatar da bani da kunya ba se rabda kika zo hannuna Asmy, kedai ki
shirya mun ki kuma nemi Tissue dozen dozen saboda wannan kukan sangarta da
shagwabar da kike yi ina tabbatar miki ranar zakiyi me dalili”.

“Seda safe, na fada ina rufe fuska ta da Pillow”
“Kiyi bacci cikin Amince Wife, I love you”
“Love you more” na fada tare da aika masa da Kiss me qara irin me tara tsigar jikin
nan kafin nayi saurin yanke wayar.

Ina kallo ya sake kira amma naqi dagawa daga qarshe ya rubuto saqon yana cewa
“Kinci Bashi Asmy ki shirya biyan sa”

Dariya nayi bayan dana karanta nayi juyi ina sake ruqunqume pillow da yake jikina.
Idan aka ce mun a rayuwata zan sake son wani Namiji bayan Bashir tabbas zance
qaryane amma se gashi cikin dan taqin lokaci komai ya canza.

Wata irin sanyayyar soyaya ya ringa gwada mun da ban ankare ba seda na kai tsakiya
ruwa yasha kaina kafin na fahimci na kusa nitsewa a cikin kogon sonsa. Zuwa yanzu
nayi amanna da Yusuf shine cikon rayuwata, duk wani mafarki da burina na gudanarda
rayuwar aure me cike da farin ciki da walwala ina hasko ta a tareda Yusuf fatana ya
kasance har gidan auran mu, wannan qaunar dana ke gani a gurin sa ta zamo ta
gaskiya har qarshen rayuwar mu dan na tabbatar idan har na samu akasin haka daga
gurin Yusuf, a irin yanda ya rigada ya gama illata zuciyata tabbas bazan sake
moruwa ba.

Washe gari ta kama Asabar babu aiki, tun sassafe nake aikin mulke mulken Dilka da
kurkum da Anty ta hadamun nakeyinsa sau uku a sati, cikin abinda befi wata daya da
farawata ba ni da kaina idan ina zuba ruwa a jikina bana so na dena saboda yanda
fatata take wani sulbi da sheqi kamar jikin tarwada.
Inagamawa nayi wanka na zura doguwar riga harda safa na tafi gidan Anty na dubata
bata da lafiya.

Allah me yanda yaso bayan tsahon shekaru da suka kwashe suna neman haihuwa se gashi
Allah ya kawo musu dukka su su biyun a lokacin da basuyi tsammani ba daga ita har
Abokiyar zamanta suka samu ciki bayan da suka gwada wani maganin sanyi da ANTY ZEE
MAMAN MUJAHID take siyarwa.

Tabbas na yaba da kyan maganin ni kaina saboda daga sanda na fara shansa Al’adar da
nayi ta farko nasha mamakin abubuwan daya wanko mun dan seda nayi zato ko har
sannan akwai ragowar barin da nayi da be gama fita ba tunda ba’ayi mun wankin ciki
ba seda na kirata take gaya mun babu komai datti ne kawai banyarda ba seda naje
Asibiti suka sake tabbatar mun da mataccen jini ne ya fita babu wata matsala.
Tabbas magani yayi ina kuma ina shawartar duk wata me matsalar sanyi ko abinda ya
shafi Al’ada ta gwada, masu matsalar haihuwa kuma ba’a barku a abaya ba, shi magani
dace ne idan Allah ya amince se a samu.(Ga masu buqata suna iya tuntubar Anty Zee
Maman Mujahid akan 08162859027 Allah yasa a dace).

Ina shiga ta fara dibana wai Amarya.
“Kinga yanda kike wani sheqi da walwali kuwa Ma’u, ki daga qafa haka dan Allah
karki saka Bawan Allah ya zauce fa idan ya ganki” dariya na sheqe da ita bayan da
na zauna ina cewa

“Kai Anty kin fiya zolaya wallahi, ya jikin na ganki ma da sauqi ba kamar jiya ba”.

“Kinsan abin seda haka se kanayi kana dan qara wa abun gishiri bakiga yanda
Yallabai duk yabi ya kidime ba har tausayi yake dan bani wallahi amma gara ya gane
ba’a samun Da da sauqi ai” ta fada tana murmushi

“Kai Anty kema fa kin iya mugunta, karna manta ina wannan dakan na gama da wadancan
duka” na fada dan karna tuna abinda ya kaini.

“Kai Ma’u, kai Ma’u nidai babu ruwana wallahi karkije ki kashe musu Da ana zaune
qalau tam”

“Anty gara ka kankaro mutunchi baka san ya matarsa take ba kinsan dai halin mazan
nan namu” na fada ina duba wayata da naji saqo ya shigo,
“Ki duba whatsapp dinki na tura miki saqo” na gani daga Yusuf.

“Banga laifinki ba qanwata gara ka kankarowa kanka mutunchi wadannan mazan zamanin
masu ido a tsakiyar kai. Jira nake kawai ku tsaida ranar tariya ai sannan ne zamu
fara shiri na gaske, badai mace a gaban ki ba wallahi sedai su biyo baya” hannu ta
bani muka tafa ina cewa “se Anty na”.

Whatsapp na shiga ina bude chat dinsa naga wata yar banzar sticker daya turomun ni
kunya ma ya bani har seda na rufe ido na, Wani Pdf document na gani na bude,
catalog ne na wani Kamfanin siyar da kayan daki na qasar Turkey sena danna masa
Audio call ya katse ya turo mun da cewar na masa chat.

“Wannan fa na menene?” Nayi tagging document din.

“Ki duba ki zaba, Four bedroom duplex ne da falo biyu, ragowan abubuwan dole se
kinje kinga gurin, ki tayani zabar Gadaje guda biyu nawa da Set din kujera, bana
son Royal” ya maido mun da amsa. Sena bude kayan na fara dubawa.

Ajiye wayar nayi a gefe dan ban gane abinda yake nufi ba, siya mun zeyi ko kuwa
yana gaya mun irin kayan da yake so a saka masa a gidan sa ne tunda naga yanzu
saboda rashin kunya irin ta maza qiri qiri suke fadar irin gadon da suke so ko siya
musu.

Na dan jima muna hira da Anty kafin nayi mata sallama na tafi bayan ta bani Dakan
da naje karba da wata zuma data ce na ajiye amfaninta ba yanzu ba wai ita Scorpion.
Ina fitowa daga gidan muka yi kicibus da Bashir ya fito daga gidansa, Kallo daya
yayi mun yayi qasa da kansa harga Allah seda naji wani iri, murmushi na qirqiro
harya gota ni nace masa

“Baban Ali barka da rana?”
“Barka dai Ma’u ya gida ya aiki?” Ya bani amsa kamar yana jira na gaishe shi. Se na
amsa masa da lafiya kafin naci gaba da tafiyata a jikina ina jin yanda ya bini da
kallo har na shige gida na kullo qofa, Allah kenan meyin yanda yaso a sanda yaso.

BASHIR
A cikin watanni ukun nan ya samu canji sosai a rayuwarsa dujda seda yayi da gakse
gurin jinyar zuciyarsa kafin komai ya daidaitar masa sakamakon Addu’a da irin
nasiha da a kullum Ahajinsu yake kan yi masa akan muhimmancin yarda da qaddara
musamman irin tasa da shine silar komai.

Kusan duk wani abu na yaransa ya dawo hannunsa yanzu a gidan suke komai, tsakaninau
da gidan Ma’u sedai suje suyi wasan su dare yana yi Aliyu ze hado kansu su dawo.

Zaman sa da Amirah dai ba dadi babu wuya akace lahirar kare, bayan zaman wata daya
da ya barta tayi a Gombe ta dawo dole ya kafa mata sharuddan da in har tana son
zaman lafiya dashi dole ta bi to anyi dace ta dauka musamman saboda a Gomben ma da
sukaje kwananta daya a gidan Dada babanta ya samu labari yace ta tafi gidan su can
tayi zaman jegon dan baze sake sakin wani abu daya shafi Yayan sa a hannun Fattu
ba.

Zaman da tayi da matan Baban nata sam ba me dadi bane dukda ita ta quntata kanta
dan a gurinsu su basu da wata matslaa sam. da fari ta farayi musu rashin kunyar da
suka saba sanda Addah tana nan suka taka mata birki se duk tabi ta tsangwami kanta
bata sakewa da kowa haka duka tayi zaman ba dadi gashi babu inda take zuwa babu
kuma me zuwa gurinta, Anty Binta Amaryar Alhajinsu ce ta dauki ragamar gyarata dayi
mata wanka har na wata dayan kafin babu Arziqi ta tattara ta koma Lagos bayan
dogayen sharuddan da Bashir ya gindaya mata akan zamansu dan ko Addah da take gidan
Anty Talatu ana ta dibar tsiya bata san da komawarta ba se bayan ta tafi dan duk a
shirinta tare zasu koma ai kuwa tasha zagi ta kuma tabbatar mata tana tafe dan ma
yanzu tana shirye shiryen yin auran kisan wuta ne kamar yanda wani sabon Malami da
Tatu ta kaita wajen sa ya gaya mata tayi kafin a gama aikin da zaa karkato da
hankalin Alhaji Murtala kanta ta koma dakinta.

Tasha matuqar wahala sosai da irin sabon salon zaman nasu dan yanzu duk wani abu da
cikakkiyar matar aure zatayi a gidan ta shi takeyi, girki sau ukun nan seta dora
kuma ba irin na ganin dama da takeyi a da ba, shiyake gaya mata abinda yake so ayi
ko yaran daya fuskanci bata iya wasu abubuwan bama makarantar koyon girki ya kaita,
gyaran gida kuwa haka take wuni ta dauke wannan ta gyara wannan a haka ma dan yaran
sam ba masu bata guri bane.

Badan ma ta kasa sakin zuciyarta ta jasu a jiki ba da ko su sun isa su ringa taya
ta aikin gidan idan suna nan tunda duk abinda suka saba yiwa uwar su ne. Sauqin ta
daya Bashir ya rage wannan fada da hargagin da yake mata da tayi kuskure ada, dukda
yanzu shiru shirun sa ya dada qaruwa ne ko da yaushe ya zauna shi kadai zaka lura
yayi zurfi a cikin tunanin amma ko laifi tayi masa cikin lumana yake fahimtar da
ita kuma babu laifi a yanzu yana kyautata mata daidai da yanda itama take kyautata
masa shida Yaran data fuskanci yanzu sune komai nasa dan yawan ci idan suka samu
sabani to akan abinda ya shafi yara ne.

ASMA’U

Sati daya tsakani Yusuf ya gaya sanar mun a ko wanne lokaci yana iya dawowa sannan
kafin lokacin yana so aje a duba gida dukda har sannan ban rigada na zabi kayan
dayace shi ze siya ba, ina jira zanje Gombe na zauna da yan uwana naji shawararsu
akan na barshi ya siya din ko mu zamu siya da kanmu.

Daya matsamun akan zancen aje a ga gida Anty Ladi na kira na gaya mata suka hadu
ita da Junaidiyya da Anty Nasiban Yaya Abubakar se Zahra suka je ganin gidan. Na
Bauchi kuma daga Gombe su Yah Fati suka tafi suka hade da Hajia Alawa qirjin biki
suka gano gidan.

Wayyo Allah ranar kam nasha surutu harna gode Allah na santin gidan da suka ringayi
ga Videos da suka dauko suka ringa turawa dangi.
A bakin su Anty Ladi nake jin gida daya zamu zauna tareda matarsa a Abujan dan na
Bauchi kowa da gidanta na sani amma a Abujan bangaren kowacce daban dan a cewarsu
ma tazarar dake tsakani ta isa a gina wani gidan a gurin filin wasanni ne ne da
Garden harda swimming pool yayi a tsakiya se a bangaren ko wacce mace yanada dakuna
biyu da palour banda wani qaramin flat da yayi a farkon gidan inda ze ringa sauke
Jama’ar su yan siyasa se kuma Boys quarters a bayan gida.

Wannna zuwa ganin gida da akayi ya taso da guguwar zancen tariya kuma dan daman
sunce duk ido kawai suka saka mun, yanda kasan auran budurwa haka yan uwana suka
hau shirye shirye, Yusuf ya kafe akan zuba mun kaya a gidansa na Abuja kamar yanda
ya rigada ya sakawa Intee haka kuwa akayi, kamfani sukaje suka tsara yan uwana kuma
suka shirya mun na Baushi dan kwandala ta bata shiga ciki ba gudummawarsu suka hada
data abokanan arziqi suka mun kaya na yar gata har kuka seda nayi da naga Video
gidan bansan da me zan saka musu da irin qaunar da suke nuna mun ba sedai Muyi
Addu’ar Allah yaci gaba da hada kanmu har mutuwa.

Dagaske dai Yusuf yaqi dawowa Nigeria har aka tsayar da ranar tariyata sati biyu
masu zuwa ya kuma qi bari muyi magana balle na tuntube shi naji makomar aiki na ko
kuwa dai an zuba kaya ne kawai a Bauchi da Abuja saboda idan zuwa ya kama mu.

Ranar Juma’ar daya rage saura sati daya tariyata kuma a ranar nake son daukar hutu
tunda zamu tafi Gombe gaba daya zuwa Lititin dan yara sunyi hutun Aliyu ne kawai
zamu bari saboda ze rubuta Jamb.

Bayan dana karbi takardar hutuna da suka bani har wata uku aka sake qaramun da wata
da ban san kota mecece ba. Da wuri nayi sallama da abokanan aikina na kama hanyar
gida dan ina so na tsaya na bada wasu kaya a Tasha da za’ayi mun gaba dasu.

Se yamma na shiga gida, ina cin abinci muna waya da Yusuf, ni yanzu na haqura da
tambayar sa yaushe ze dawo ma tunda abin nasa ya zama wulaqanci, zancen hutun da
aka bani daya mun dazu yasa takardar da aka bani ta fado mun a rai. Farida nacewa
ta dakko mun su a cikin jakata, ina budewa na zaro ido ganin takarar transfer ce
zuwa Headquarter mu ta Lagos harda qarin girma.

“Yusuf kai ne ko?” Na fada kamar zanyi kuka.
“Oh ni dai naga takaina me kuma nayi Asmy duk wani laifi ace nine, nine me?” Ya
fada

“Transfer akayi mun zuwa Abuja nasan wallahi kaine bayan ba haka mukayi da kai ba
kai kace zaka barni na zauna a Lagos”

“Ni babu ruwana su sukace miki da saka hannuna a ciki? Qila sun duba miki ne inda
mijinki yake amma ni babu ruwana a ciki” ya fada yana yar dariya.

Duk se naji raina ya baci, yanzu kenan dagaske zan bar yarana na tafi wata rayuwa
daban ba tare da su ba? Me yasa tun farko yayi mun qarya yace ze barni na zauna
tare dasu

“Kinyi shiru Asmy, dagaske nake miki bani na saka ba amma idan kina so se na je na
nemi alfarma idan ze yuwu su barki a inda kike, amma bakya ganin hakan da sukayi
kamar yafi hankali na ze rabu da yawa ni Ina Abuja Intee tana US ke kina Lagos bani
da hutu kullum ku tausaya mun mana” ya fada kamar zeyi kuka.

“Uhm, shikenan bari naci abinci mayi magana” na fada na kashe wayar.
Goggo na kira, tana dagawa na saka mata kuka ina cewa
“Goggo kin gani ya saka anyi mun Transfer zuwa Abuja bayan shi yamun alqawarin ze
barni a Lagos yanzu kuma yazo ya canza gaskiya ni bazan yarda ba ku kirashi kuyi
masa magana”.
“Wallahi Wallahi Wallahi sau uku kenan Asma’u kika sake kirana akan wannan shirme
da rashin hankalin naki sena ci ubanki. Ke se an fara miki zaton kinyi hankali se
ki sake kwanto wani sabon diban Albarkar naki ko? Da dab ubanki idan yace ki zauna
se ki zauna ke? Me zakiyi ashe baki cire Bashir daga ranki ba? To Shikenan ki ci
gaba dayi keda Allah kiyiwa kanki sanadin da zaki mutu a banza ki tafi wuta da
auran wani akan ki zuciyarki tana ga wani shashasha da be san darajar ki ba wawiya
kawai” Goggo ta fada cikin bacin rai

“Ni ba haka nake nufi ba ni babu ruwana da wani Bashir kawai saboda yarana nake so
na zauna a nan kum....”

“Se kinci kutumar ubaki dake da yaran Asma’u idan baki rufe mun baki ba, ai daman
na fadawa Qarami wannan lambon da kikayi mu saka ido na tabbatar indai Ke din dana
sani ce sekin nuna halinki, to bari kiji ni na kira Yusuf din na gaya masa yasa ki
bar aikin gana daya ma amma yace Aa za dai ayi miki canjin guri dukda kun rigada
kunyi yarjejeniyar zaki zauna a inda kike.

Naga alamar so kike ki mayar dashi kamar dan da kika haifa se yanda kika ce za’ayi
ko to ni bazan saka ido ina kallonki kina iskancin da kika ga dama ba, ko ki
tattara kibi mijinki ko ki bar aikin gaba daya kuma na rantse da Allah babu dan da
zaki dauka ki riqe, ita kanta Faridar dana ce an fasa ki hadasu da Amnah zasu koma
gurin qarami dan ubanki ki je kiyi zaman aure Idan kinga dama kiyi abinda ba haka
ba zan tabbatar miki da shirun da nake yi bawai dan ban iya bane ko kuma kunfi
qarfina nima na iya maganin ko wanne dan Banza” Goggo ta fada cikin matuqar fada da
hargagin da ban taba jinta tana yi ba.

Bata barni ma na sake magana ba ta kashe wayarta, wannan abun ya sake dugunzuma mun
hankali, wayar Yusuf na sake kira yana dagawa na fara magana cikin kuka ina cewa

“Yusuf me yasa munyi Alqawari zaka saba sannan kaje ka hadani da mahaifiyata tun
farko ai bani na roqa ba kai da kanka kace zaka barni na zauna kusa da yarana se
Yanzu dakaga na rigada nazo hannunka zaka canza magana me yasa”

A dake ya fara magana yana cewa
“Kinaji Asmy bana son ki jawo abinda ze sa mu fara samun sabani tun daga yanzu.
Koma me nace miki a da yanzu Goggo ta tayar da wancan hukuncin tayi nata dan haka
idan beyi miki ba kina iya zuwa ki gaya mata ni kuma duk abinda tace dashi zanyi
amfani. Ki duba na tura miki da saqo saboda hidimar biki idan baze isa ba se ki
gaya mun”

“Bana so me zanyi da kudinka kuma ni babu inda zanje in dai kana son auran mu sedai
ka biyo ni Lagos idan ba haka ba kowa ya kama gabansa” na bashi amsa

“Tunda ke kike aurena dole na biyo ki ai, kudi kuma ki zubar idan bakya so wannan
ba matsala ta bace” ya fada tareda jan tsaki ya kashe wayarsa.

Lallai ma wannan mutumin tun daga yanzu? Ashe daman duk kwantar da kan daya ringayi
na qaryane se yanzu ze fara fito mun da halinsa na ainihi kenan shikenan zamu gani.

A dole badan naso ba muka tafi Gombe ranar Lahadi, Nama na kadai ya rage su taru su
cinye dan tuni Goggo ta gama yayata musu na rasa yaushe ta koyi wannan halin ita
kuma duk abinda nayi seta fada musu bayan tasan daman qiris suke jira dani.

Har ranar Laraba babu abinda nayi daya shafi lalle ko kitso dukda da har walima
muka shirya yi ranar Alhamis tunda ran Juma’a za’a kaini can Bauchi amma da me
Lallen ma tazo korar ta nayi ina ta baqin rai gashi Gogan tun ran Juma’ar nan be
sake kirana ba kuma ya dawo naji labarin a bakin Jafar.

Ina kwance a dakin Hajiya Babba Sumayya babbar Yar Alawiyya ta shigo tana cemun
“Mami wai kije kinyi baqo a waje”
“Wane baqo kuma kin sanshi?” Na tambayeta ina tashi zaune, se tace mun
“Eh Baba ne”
“Baba?” Na fada da sigar tambaya.

“Baba na gidansu Baba Naziru fa” ta bani amsa.
Ikon Allah, me Baba yazo yi gidan mu a daren nan kuma? Na tambayi kaina. Hijabi na
na saka har qasa na fito, a can falon baqi na tarar dasu, Baban, Bashir yasha uban
baqin

77 / 80